Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mace meh aji wayyaya,wacce take da certificates daga waje, Asma'u koh na secondary din mah bata rike bah

Asma'u nada kyau,da diri, sai kuma ya tuno beh taba ganinta bah hijab bah,

Dama shi hakanan mah sai ya kasa bacci,ballantana yanxu da akwai abinda ze hanashi shut eye😴😴😴,


Fitowa waje yayi dagashi sai wandon pajamas da singlet,
Ta baya wurin servant quarters ya zagaya,sannan ya samu wuri ya zauna,


Koda na cinma plans dina a banza zasu kasance in ban nemo mijinta bah, ina bukatar ya saketa ko zan samu damar soka kai cikin zuciyarta,πŸ’˜,


Zan jira har sai na gama da plan dina na Mom sannan,koda ban ganshi bah sai a raba auren a Court,ya dafe kai dan ko duka duniya zasu taru baya tunanin Asma'u zata yadda da divorce din kotu.

Ajiyar zuciya yayi yana kallon sama, hoton beautiful night din ya dauka, sky din yayi duhu, taurari sai shining sukeyi ga jaririn wata ya fito,

Ita ya tura mawa
*kin taba zama kawai ki yaba tsari da kyan wani abu,ni nasan na taba* sannan yayi sending mata,duk da yasa wayar bata wurinta,


Duk ya gama shirin yadda komai ze faru, amma hankalin shi beh kwanta bah dan yasan komai na Allah ne,kana naka Allah na nashi, shi yasa ya zauna a wurin kawai yana mika godiya ga mahalicci.


"Salamu Alaykum" ta shiga bayan ya ansa sallamar

"Good Morning" ta fada da fara'a duk da bashi take kallo bah

"Ina kika shiga tun dazu" daga kafadu tayi kafin ta ansa mai

"Ina can ina bacci" ta fiddo mai suit din daze sa

"Ana jiranka a waje, kayi bakuwa" kallonta yakeyi yana son gano dalilin daya sa tayi mai karya,

"Husna,in akwai wani abu da kike bukata kiyimin magana"
Yau taga ya zama wani serious, koh gaisuwarta beh ansa bah gashi yana ta binta da wani kallo da ba irin wanda ya saba yi mata bah


"Kin san ni na kawo ki nan hakkin kula dake ya zama nawa"
Ya taso ya nufo in da take tsaye

"Kai ka kawoni nan amma wannan haka yake , ba dole sai ka dora ma kanka kula dani bah"
Ta mike tana shirin tafiya,dan ta duka tana jeramai takalmin dazesa

"Ni na kawoki amma hakkin kula dake na akanshi koh" kishi karara a face dinshi da voice


"Kin san meh,kawai ina tsoron daukan Alhakin ki ne" beh bari tace komai bah ya koma fun chirpy self dinshi,



"So malamata yaushe zamu fara karatu,kin san wannan dalibin naki an barshi a baya sosai"

Fitowa tayi ta barmai dakin,


"Gashi nan zuwa" ta fada mah matar dake tsaye cikin suit meh skirt iya guiwwa.

Refreshment ta kawo mata sannan ta koma kitchen tana jira su bukaci abincin safen su,


Tare da kakarshi ya sauko itama tayi tsaf cikin wani leshi black da ash color,


"Good Morning Sir" ya ansa yana mata nuni da hannu alamun ta cigaba


"Assistant dinka ceni" yace Oh! Yana jin jina kai


"Ba'a sanar dake cewa bana bukatar sabuwar assistant bah"
Matar tace Aa,sai Hajia tasa baki


"Ehsaas kana bukatar qualified P.A ma harkokin ka" ya jin jina


"Na sani granny ma,shi yasa zanyi amfani da naki,tunda har aikin ki zan dauke maki,su kadai sun ishe ni"

Hajia Turai ba karamin farin ciki hakan yasata bah , dan tana so gaba dayan duniya kowa yasan da zaman jikanta.

"Ehsaas hutu kazo yi,zan ma mamanka magana ta kyale ka gsky ka huta"

'Ba abinda naso ji kenan bah,amma wannan yafi mahmah'
Jikinta ya shige

"Wallahi Granny Ma aikin yayi min yawa"😩😩😩😩

Hajia ta bata fuska, toh fah kar abin ya tabarbare

"Karka damu Ehsaas zan gyara komai" ya kara shigewa jikinta

"Tnx Granny"

"Gashi in ji Mamanka" ya karba yana bude dan akwatin

"Yes, favorite car din ya iso" har yayi hanyar waje ya koma ya bi hanyar kitchen


"Ka shirya,a kawo maka breakfast ne" ya girgixa kai

"Yaushe zamu fara karatu, ina so ki bani time sosai fah,kila sau biyu a rana zamu dinga yi ko"


Abincin shi kawai ta jera mai a gaba, pancakes da Scone's sai coffee da juice


"Bari in kai mah Hajia nata in dawo" saida ta dawo sannan ya jawo mata barstool

"Zauna muci tare" zama tayi amma bata ci bah

"I have eaten" ya dan dade yana kallonta, a ranshi yana fata ba karya takeyi mai bah

"Okay, baki bani ansa bah,yaushe zamu fara karatu"
Sai da ta danyi dariya kafin ta ansa

"Ni kam bazanyi bah,ka nemi wani teacher" tashi ma tayi ta tafi abinta,


"Ina bukatar taimakon ka"
Daga gira daya yayi😏😎😏
"Kin tabbata help dina kike bukata"

Ta daga kai da sauri sauri

"Ni Ehsaas ba wani bah"

"Pls i need your help" jin kaman zatayi kuka sai ya zama serious

"Ya akayi"

Nan ta fadamai yadda Hajia tace ta ba kifayanta na cikin aquarium abinci,

"Dukkan su da kike gani anan rear collections ne" bata dai fadamai wannan part din bah


Suna zuwa parlor din hajia yaga duk kifayan sunyi kasa basa yawo kuma


"Kaman nayi over feeding dinsu sun mutu"

Dariya kaman ya kufce mai datace tayi over feeding dinsu


"Yap,kanan sun mutu kam"
Ta rufe baki da hannu

"Na shiga uku ni Asma'u" ta fada da hausa

"Flushing dinsu kawai zamuyi yanxu"😳😳😳😳

Ya kara tsoratata


" kayi wani abu toh manah" wani dariyan yaso kufce mai


"Ni meh zan iya yi Husna, ay sun rigada sun mutu" ta zo wurin aquarium din tana dan bubbuga glass din


Har ya dan ji tsoaro kar 🐠🐠 din su tashi


"Amma akwai abinda zan iya yi" ta baro wurin ta dawo gabanshi, har kallonshi takeyi


"Amma nima sai kinyi min wani abu" ta hada hunnawa πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»



"Koh meh kakeso in shaa Allah zanyi maka"

Ya tunkarota da wani killer smile

"Anything fah kika ce" ya hanata ja baya ta hanyar kamo mata hijab dinta

Har tayi dan kara kuma tayo saurin rufe bakinta tana daga kai


"Abubuwa dayawa nakeao a wurin ki Husna" ya fada da small husky voice


"Baza kayi min dan Allah bah" ta fada tana turo baki da kasa da kanta


"Kice kin yadda zaki zama malama ta" suka hada ido kafin ta saukar da kai


"Ba takura in bazakiyi bah,nima sai in fasa neman maki mafita,kuma kin san yadda granny ma ke san rayuwar ruwan nan kuwa, tab" ya juya ze tafi

"Zanyi toh" murmushin victory yayi

'Ai dama nasan zakiyi ne'

"Muje dakina toh akwai sauran abubuwan da nakeso kiyi min"
Ta matsa baya tana girgixa kai


" har kin canza shawara kuma" ta sake girgiza kai

"Lets go" ya matsa su tafi dan kar 🐠🐠🐠🐠 din su fara yawo kuma daga hutun da sukeyi


"Zauna" ta samu kujer can gefe ta zauna


"Ga wayar ki, nasa an nemo maki tunda da hannun ki zaba"

Tace ta gode sannan ta nuna hanyar kofa


"Toh muje ka duba kifayen" saida yazo daf da ita kaman ze hada face dinsu

"Kin cika tsoro dayawa" sannan ya matsa baya


"Yanxu zansa azo a canza kifayen don't worry"

Zaune sukayi shiru babu meh cewa komai,

"Lets watch TV,koh
kin manta da maganar fishes dinnan" .




⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š





πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.


πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

STΞ©RΞ¨, Ξ£DITIΞ G Ξ²Ξ¨ ΠΩβLΞ£ δΊ…UÐGE ,
Ο‰RITIΞ G KHΞ”LΣΣSI.




Dedicated to BaRrIsTeR MeEnAsH,
Allah ya bar kauna da zumunci, comments dinki sun sani jin dadi soasai tnk u,❀.
❀
Congratulations REAL MEH DAMBU, akan kammala littafin ki KISHIYATA JIHADINA, ALLAH ya sauke ki lfy ya kara maki basira, yasa mu amfana da darussa da fadakarwa dake cikin littafin ki.
❀
Sis Hajara Allah ya kara mah aunty'n sauki ya bata lfy, sincerely Naja'atu Sani.❀.



3⃣0⃣



Agogo ya kalla sannan ya saurara,dan yasan yanxu zata shigo,

Kwana akayi ana ruwa,yanxu yanayi garin sanyin dadi,daidai shigewa cikin blanket kayi ta bacci kaman bah gobe,

Yana jin an bude kofar parlor yayi saurin hawa saman gado ya lullube, ta taba shigowa yin aiki taga idonshi biyu tayi mai wani silly excuse sannan ta tafi,


Saida ya bari ta shigo daki bayan ta gama aikin da takeyi a parlor sannan yayi magana

"Waye nan?" Ya tashi zaune saman gadonshi


Baya ta juya mai tana kara jan hijab dinta ya rufe fuska

"Magana nakeyi" ta duka zata dauki kayan aikinta


"Nasan kece Husna" kawai sai ta cigaba da aikinta

"Baki da abin cewa kenan "Yi hakuri na tashe ka daga baccin ka"

Bata san ya taso ba sai ji tayi ya dafata yana juyo da ita tayi facing dinshi


"Duk ranar da muka fara karatu ka tunamin in maka wa'azi akan wannan" ta cire hannayen shi daga kafadunta


"Yaushe kike tsammanin zamu fara karatu, bayan kullum buzzing kike kaman wani kudan zuma🐝🐝🐝" ya fada da rai bace

"Kazo ka cemin mu fara karatu kaga ban baka tym din da zamu dinga yi bah"

Ya kalleta irin kar kiyi wasa da hankali na🀨🀨🀨🀨


"Kafin muzo kan krtu mah tukunna, fadamin dalilin da yasa kike house keeping, wa yasa ki????"

Ya tsareta da eyes kaman ya dago da kanta dan yasan in karya zatayi mai

At the same time kuma yaji wannan yanayin da yake fadawa in suka hada ido,watau lup dup din zuciyar shi ya linku sannan yaji ko wani gaba na jikin shi yayi weak


'Dan ni akayi ki Husna, shi yasa nake jin electric shock a jikina da kin kalleni'


Ya manta da abinda suke magana akai ya bige da zuzutata a cikin mind dinshi

"Ina yin wannan aikin ne saboda bazan iya komawa baccin safe bah" ta katse mai fantasy din da yakeyi

"ban saba bah kuma Granny MA tayi tayi in bari, kawai dai ina son yi maku wani abu ne saboda kulawar da kuke bani"


Saman gado ya koma ya zauna,

"Duk abin nan da kikeyi ba dole bane bah" ta daga kai hade dacewa

"I want to, nasan sai kayi korafi akai shi yasa bana so ka ganni". Ya murmusa mata

"Bana son ki sha wahala ne ai" tayi murmushi da kanta kasa


"Na gode,ka koma baccin ka,baza ma kasan ina nan bah"

Zata dauki kayan aikinta ta tafi ya dawo gabanta


"Meh ya rage kiyi?" Murmushi kawai tayi mai, sannan ta canza topic


"Kazo anjima bayan an gama cin abincin rana sai muyi karatu, amma ni mah daliba ce sai kayi hakuri"

Ajiyar zuciya yayi yana kallonta ba tareda yace komai bah

'Ji nake kaman in sace ki in gudu' ya cigaba da murmushi yana ayyana wasu abubuwa a ranshi


"Bari inje inyi abinda nasa kai na, sai ka tashi daga bacci"

Janyota yayi saura kadan ta fada jikinshi

"Weather din is perfect for sleeping past 12 pm, dan Allah ki bari muyi bacci"

Kokarin kwace hijab dinta takeyi sai ya rike hannunta ya fara janta zuwa gadon shi,

"Ka kyaleni right now, ni bana jin bacci" ta fada tana tirjewa hade da jan hannunta


Karfi ba daya bah dan haka ya jata har bakin gado sannan ya zaunar da ita,


"Karka kara tabani" ta fada kaman zatayi kuka da idanun da suka fara kawo ruwa


"Tabaki ne kawai bakya so in kara yi" ta daga kai tana mikewa daga saman gadon


"Toh ki dinga yin abinda nace" ya turata ta fadi saman gadon


"Dan Allah ka kyaleni" ta fada da muryar kuka

"Ya Ilahi, har kin fara kuka kuma" dukawa yayi a gabanta sannan ya sa hannu ze share mata tears


"So nake kawai ki huta Husna, na lura bakya yin bacci isasshe"

Kaman ta bude baki tace mai zata kwanta a dakinta, amma tasan taurin kai gareshi, abinda yakeso kadai za'ayi


"Koh kefe" ya dauko handkerchief ya bata dan ta goge hawayenta, hannu ya mika mata ta bashi,


Yana juya mata baya ya dora saman face dinshi, sannan yaje ya bude drawer yasa kusa da dayan data taba goge hawaye dashi

"Bari in kashe fitila sai muyi bacci koh" da sauri ta mike zaune

"Aa Dan Allah karka kashe" yayi dariya yana cewa okay


Yana kwanciya saman gadon ya hau kallonta,duk da baya ta juya mai, basai an fada bah itama tasan kallonta yakeyi,


"Ki saki jikin ki dani Husna, kuma In shaa Allah zanyi kokarin hana kaina yin wani tunani da beh dace bah"

Ta rumtse ido tana neman tsari daga shaidan azzalumi,


'Allah ka hada ni da wani irin murdadden mutum, bana so in zargeshi ba tareda nasan koh shi wani irin hali yake dashi bah, dan iska ne koh tsaban sangarta ne ke damunshi, Allah ka karemu daga sharrin mashe ranta, Amin'


Ba bata lokaci ya fara bacci, ita kuma ciwon kai kawai ta kwaso sakama kon kukan da tayi, bata wani huta bah,


Aikinta ta cigaba dayi, tana plannin yadda zata tsere mah irin wannan haduwa da sukayi yau,


"Har kin tashi" uhmmm tace ta cigaba da wanke bandakin

"Meh akeyi da wannan,?" Ya dago toilet brush

"Na gama amfani dashi" sai ya dawo inda take tana wanke kwamin wanka

"Kawo inyi wannan to"
Ta girgixa kai
"Ka barshi kawai" kwakule brush din yayi daga hannunta,
"Stubborn girl kawai" hadda wani lakatan mata hanci


"Akwai wanda ya kaika rashin jin magana ne" ta fadi da hausa


"Fassara min abinda kikace, in kika ki fada zan bar aikin nan" sai ta mika hannu ya bata scrubbing brush

"Toh fadamin sai in ba ki "
"Cewa nayi kaima baka ji" murmushi yayi sai ya cigaba da aikinshi


'Hakan na nufin ni dake mun dace,πŸ•ΊπŸ»πŸ•ΊπŸ»πŸ•ΊπŸ»πŸ•ΊπŸ»' ya karkada kanshi

Ita tayi duk sauran aikin daya rage dauraye tub din mah ita tayi


"Ke hard worker ce,ni bayana har ya gaji" rufe baki tayi tana murmushi

"Dariya kikeyi min koh" ya fada da dariyan shima bayan ya gama mika

"Bazaki bar yimin dariya bah koh" bata ankara bah taji ya watsa mata ruwa da hannu

"Meye hakan" ta daga hannu tana kare kanta


"Payback" ya cigaba da watsa mata ruwan daya taru cikin basin

Ba shiri ta fito da dan gudu,yana binta

"Eyyyeh, biri kam yayi kama da mutum, sai ki zumbula hijabi kaman duka kenan, wai ke saliha, bayan kin shige dakin namiji kina wasan masoya koh, toh hawainiyar ki ta kiyayi ramata, Ehsaas yafi karfin ki nesa ba kusa bah,yaushe ruwa ya zama sa'an kwando, ji wani ikon Allah"

Yadda take maganan babu alamun fada a muryarta yasa shi murmushi kawai,

Asma'u dukawa kasai tayi ta gaishe da hajia da turanci sannan ta cigaba


"Wallahi hajia saida nace mai kema bakya son ina yin aikin nan, gashi yanxu ze jikani a banza ya sani mura" ta fada da yar dariya

Jikin Hajai ya makale

"Abinda nake cewa kenan ai, kar ya saki mura" itama ta fada da turanci

Shi kuma sai fara'a yakeyi


"Jeki canza kaya ki sameni a dakina" da murmushi tace toh, duk da tsoron daya ziyarci zuciyarta


"Granny Ma,kinzo tashi na daga bacci ne" abinda taji yana fada kenan da zata fita.




⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’

BOYAYYEN KUDIRI .

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


STΩRΨ,ΣDITIΠG βΨ
ΠΩβLΣ J,
Ο‰RITIΞ G KHΞ”LΣΣSI.


DΞ£DICΞ”TΞ£D T0

Meelat Musa ta Real Mai dambu, Allah ya bar mana ke ya kara basira, muna yinki sosai.

Ummu Affan Allah ya kara sauki, ya baki lfy da duk musulmai marasa lfy,

Asmeenat and Raheema Allah ya bada sa'an exams wanda kukayi, da masu zuwa,
Amin.




3⃣1⃣.



A hankali ta bude kofar dakin hajia, bayan tayi sallama a parlor ba'a ansa bah,

A kasa ta sameta zaune ta tankwashe kafa tana washhh

"Hajia" tayi salati tana dukawa kusa da ita

"Sannu Hajia" ta taimaka mata suka mike tare

"Sannu hajia"
Ta ja mata bargo sannan ta fita

Da sallama ta shiga cikin falo sannan ta tsaya bakin kofa tayi wani sallama
"Shigo Husna dama ina jiran ki, wani suit zansa yau"

"Granny Ma dinka bata jin dadi" ta fada daga bakin kofa

Yana bude kofar ya wuceta da sauri

"Meh ke damunki" ya zauna gefen gado yana taba goshinta ga damuwa a fuskar shi

"Lfy ta lau Ehsaas wallahi jiya na manta ban sha kuma na shafa magani na bah"
Ya dafe kai πŸ€¦πŸ»β€β™‚sannan ya fara yi mata fada da sanyin murya

"Ka barta manah, bata jin dadi fah" ta fada a hankali

"Okay " yace kafin ya koma duban kakar tashi da zufa ya keto mata lokaci daya

"Sannu granny ma" kitchen taje ta hado mata tea meh kauri kuma daidai sha ba zafi ta kawo

"Tnk u Husna" ya karba daga hannunta sannan ya dan tada kakar tashi zaune ya bata tasha da magani

"In kawo maki abinci koh hajia" ta fada tana tsaye daga gefe

"Barshi in na tashi daga bacci husna" tace toh sannan ta dauko maganinta na shafawa

"Ka tafi office din manah, yanxun nan na wartsake" ta fadamai dataga yayi tagumi

"Bazan barki ke kadai bah, waze kula dake" ya fada☹

"Ga Asma'u nan"
Ya zauna baya da niyyan tashi

"Karka damu, zan kula da ita sosai kuma in naga ciwon na karuwa zan kira a take" yayi mata murmushi

"Nagode husna" sannan yayi mah kakarshi Allah ya sauwake ya tafi


Zama tayi tana mata tausa a kafa, har wahalallan bacci ya dauketa,

Tausayin halin da hajia take ciki, yasa tayi tagumi tana kallonta, acikin ranta kuma tana mata addu'an samun sauki,


Kitchen ta koma tana dafa mata abinci, sannan ta tattara kayan hajia dake bukatar wanki ta wanke mata,

Tun tana dafa abinci take zuwa dubata har ta gama wanki,

"Ayyah Allah ya bata lfy" ta amsa da Amin

"Allah mama tausayinta nakeyi, kila haka take fama da ciwon babu wani kusada ita balle ya bata kulawa"

Mikewa tayi daga inda take zaune wurin ❀ flowers

"Kice ina yi mata ya jiki, kuma" mamanta ta tsayar da ita daga kashe wayan

"Abba da Mukhtar na nan zuwa" 😰

"Yaushe zasu zo" ta tambaya murya sarke

"Akwai abinda sukeyi shirya wa, amma da sun gama zasu zo, kinga sai suga inda kike koh" tace Eh

"Sai Anjima toh, a gaishe da su"
Sukuku ta haura sama ta nufi dakin hajia

War tsakewa tayi dataganta kishingide da gado

"Sannu hajia, akwai inda keyi maki ciwo ne" fuskarta cike da damuwa hade da kulawa

Hajia kuma ta kalli hakan a matsayin kinibibi

"Mamana tace in gishe dake" ta fada da fara'a

Hajia tace lallai wannan yarinyar munafuka ce a ranta, koh halin da takeci bata sanar da iyayenta bah kenan,

Ni dana so ta fada musu dan su san abinda nake mah shalelen su,

"Abincin mah sai nace kikawo min" da sauri ta mike tana bada hakuri,

Data kawo abincin saida ta kai hajia bandaki ta wanke baki sannan ta dafota

Please Login or Register in order to submit comment