Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



2⃣1⃣.



Asubar farko yazo yayi mata knocking, beh tafi bah har saida ta bude kofa ya ganta sannan,

πŸ‘œ data fito da ita daga gdansu ta dauko, daga Qur'an sai dan akwatin yan kunnen dolen da ya damka mata sai wayarta dake ciki,


Karatun Qur'an ta koma gefe tanayi, da gari yayi haske kuma sai ta aje bayan tayi addu'a,

Wanka ta mike ta shiga dan yau a gaban mamanta takeso ta kwana,

Dan tsorata tayi sakama kon kwankwasa kofar da akayi, da sauri tasa hijab ba tareda da daura dan kwalin ta bah.

"Good Morning sunshine🌞" ya fada da murmushi

Kamar yadda ta saba ganinshi kullumda suit,yauma shine a jikinshi, wani green meh duhu sosai ne suit din sai πŸ‘” red color meh haske sosai


"Kinyi kyau Husna" gashin kanta daya leko yasa shi fadan haka,

"Bazaki ce tnk u bah" dukar da kai ta karayi tana dan bata rai


"Allah kinyi kyau ne shi yasa na fada" kauda kai tayi gefe bayan ta tamke fuska,

"Gda zan koma yau" ta fada cikin small husky voice dinta


Beji dadin voice din nata bah yau,saboda abinda ya furta

"Ni babu inda zan kaiki" ya fada rai bace


"Dama ni da kaina zan koma" kara bata rai yayi

"Ance min in koma gda" sai ya kalleta da mamaki

"Wa yace ki koma gda?" Bata ansa bah sai ya kara maimaita tambayar wannan karon da babbar murya

"Tunda shi din baya nan ba gdanmu zan koma bah kenan" kaman zatayo kuka ta fadi haka


'Dan Allah ku barni in tafi,koh zan samu kwanciyar hankali'
'Dan Allah Husna ki daina guduna manah'


"Shine mah yace in koma" tayi karya duk dan ya barta ta koma

"Shi wah?" Kaman ta fara kuka taji

"So kike kije wurin shine koh meh" kaman ta dago ta kalli meh magana dan bata tabbata voice din Ehsaas din bane bah


"Am coming" yana tafiya taje ta dauko yar jakarta ta rataya,hade da murmushi a fuskarta



"Saidai in ta wani hanya sukayi communicating Sir, dan muna lura da calls din dake shiga kuma su fita daga wayarta"

Cire wayar yayi daga kunnen shi,

'Kawai so take ta barni' ya fada cikin ranshi


Bayan ya tabbatar da har yanxu ba'a ji wani duriyar mijin nata bah,
Cikin gda ya koma da rai bace

"Ehsaas my grandson" murmushi ya sakan mah kakar tashi


"Granny Ma" ya isa wurinta yana rungumeta


"what's wrong, naga fuskar taka yau ba annashuwa" kaman ta bashi go ahead ne sai ya marairai ce kaman zeyi mata kuka


"Bah Husna bace bah" ita har ta manta mah dayace yazo da wata wai ita Asma'u

"Kaina cikin giza gizai yake Ehsaas, sai ka yaye min su kafin in san abinda ke faruwa"

Nan ya fada mata komai tundaga farkon haduwar su har zuwanta nan


"Tsaya ka kara fahimtar dani" ta fada dan ta tabbatar in Asma'u family din mutumin data KUDIRI aniyar yima yaga yaga ne


"Yes Granny Ma, Mijinta ne ya saci gift dinki"
Kwatance baban Asma'u tasa yayi mata


Hamdala tayi a ranta dan, tana jin dadin saukin dayazo mata cikin plan dinta


"Granny so take ta tafi,and i don't want that" yayi mamaki da batayi magana akan san da yakeyi ma matar aure bah


"Ehsaas jekayi relaxing sannan ka turomin ita Asma'u din"

Dan koni bana so ta tafi,ta fada a ranta

Da gudu ya haura sama ya taho da Asma'u, taso ace ya basu wuri, amma no wahala ba jinsu zeyi bah

πŸ‘‰πŸΏP.S ( Ehsaas baya jin hausa ina rubuta maganar shi da hausa ne kawai dan novel din hausa ne wannan, in akayi magana da hausa zan rubuta cewa da hausa akayiπŸ‘πŸ»)


"Karbi wannan" Hajia ta fada da hausa ba tareda ta amsa gaisuwarta bah

"Kin iya karatu dai koh" ta fada da murmushin dole 😁

Asma'u ta ansa hade da maida mata murmushi itama


Saura kadan ta yadda iPad din kasa

"Granny Ma menene?" Ya tambaya da turanci duba da yadda Husna ta rude lokaci daya

"Granny Ma" ya fada da dan karfi ganin abinda ke jikin IPad din

"Look at her" Hajia Turai ta fada tana cunno baki


"Meh yasa zatayi mamaki in bata san menene bah" sai abin ya daure mai kai


"Husna akwai abinda ya kamata ki sanar dani"

Bata dubesu bah ta cigaba da karanta abin da aka nuna mata


STOLEN aka rubuta in Caps,sannan aka nuna hoton sarka da yan kunnen hade da zobe da awarwaro

$9.6 MILLION DOLLARS


karkarwa hannunta ya fara,

"Mijinki ya sata daga gdan nan" daga kai tayi ta kallesu da jajayen eyes dinta

Koh ba'a fada bah tasan shi ya sata tunda har ya bata

"Amma ka cuceni da baka fadamin asalin abinda ya kawoka cikin lyf dinmu bah" ta fada da hausa tana kallon shi da hawaye na bin kumatun ta


"Husna ba laifinki bane bah, baki san abinda yayi bah kema, ni nasan babu sa hannun ki a ciki" ya fada da turanci


"Gashi" bude bag dinta tayi ta dauko dan akwatin,dukkannsu gwalalo idanu sukayi 😳😳😳


"Last time dana ganshi ya bani wannan" kishi ya hana Ehsaas ya tsaya jin sauran,dan hangosu yayi tare yana bata gift din,harda murmushi ya hangota tanayi,

Rufe idanu yayi yana tafiya saboda bacin rai


'Ni nakeso in zama meh saki farin ciki, shi waye da zeyi kokarin zama naki, you are mine'. Ya banko kofar dakin shi

Hajia Turai kuma wani mugun murmushi takeyi, dan rabon da wani abu yasata nishadi kaman haka harta manta,


"A cire batun zoben da abin hannun da babu" ta rufe akwatin da dan murmushi

"Mu koma kan sarkan kawai"
Asma'u ta girgixa kai

"Ni abinda ya bani kawai kenan"

Tabe baki Hajia Turai tayi


"Yan uwan ki na kusa kusa kaman su nawa ne".


Baki na rawa ta lissafo danginsu wadan da sukafi mutunci, dan ta zata bincike zasuyi koh zasu gano salisu


"Da zan hada ke da dukkan mutanen da kika lissafo in kai ma yan yankan kai, kudin Nigerian da zasu biyani dashi baze siya sarkan nan bah"


Jin an hado family dinta yasa ta kai guiwwowi kasa tana hada hannuwa πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»


"Ina hadaki da mahalicci daki kyale mu, bamu san komai akan wannan abin da yayi bah"

Hajia tayi wani dariya harda tafa hannuwa


"Kai dama ina da hanci danayi gudah, ke da babanku duk haka kuke sai kuri koh, ni Turai ze ce mah yasan right dinshi a matsayin shi na dan kasa, yasan da mutanen da nake harka, wadan da zasu sa ya bace bit a nemeshi a rasa"


Asma'u ta dake hade da mikewa tsaye

"Allah ya fiki" mari ta ji a face dinta


"Hannu na ya dade yana kaikayi, in da ba fuskar ki bah toh na babanki"

Mamaki yasa ta kallon hajia da sauri


"As i was saying, kafin dabanci irin na talaka da basu da manners yasa in tsaya" ta kara gyara rigarta


"A hannun ki wannan ya fito, saboda haka zan oya tsareki anan,ko kuma in kaiki police station"

A lokacin ta fadama kanta rabon shan wuya ne yasa tunda gate din gdan ya bude hankalinta yaki kwanciya, gabanta ya dinga faduwa, ashe makomar kenan,



"Bake kadai bah yanxu har matsiya tan dangin naku zan iya sawa a kama,sannan in bada kyautan muhalin ku ga mashaye ,yan iska, karuwai, ku kuma ku koma bara da kwana a bakin titi"

Allahumma A'jir ni Fi Musibati Wakhlif Ni Khairan Minha, ta hada Inna lillahi Wa inna ilai hi Raji'un,


"Ai dama saida na fadama wannan tsohon naki cewa bara ya kamance shi" ta juya zata tafi


Da sauri ta mike kwance kasa tana kama kafafun hajia Turai,


"Zanyi maki koh menene amma dan Allah ki kyale iyayena da yan uwana, basuyi maki komai bah, nice matar shi kuma hannu na kika karba,ki fanshe kudin ki a kaina"

Wani kyarma jikin hajia keyi saboda jin dadin abinda ke faruwa



"Diyan nan aiko kasar waje na kaiki karuwanci bazan fanshi kudi na bah"

Sai kuma ta tsaya tana tunaniπŸ€”πŸ€”πŸ€”

"Kuma kin san meh, sex sells fah" ta fada tana John n jina kai

Dora hannuwa Asma'u tayi saman kai,dan koh ji bata sanyi balle tayi imaging kanta a wannan halin

Tsoro da kyarma ya shigeta,dan ganin yadda Hajia ke magana koh a kwalar riganta balle jikinta


"Shima din sai kin tsufa a harkar baki biyani kudina bah" hannu ta harde a kirjinta

"Toh ya muke ciki"
Tashi tayi daga kasan da take kwance tayi kneeling

"Ki barni anan zan zama baiwarki har karshen rayuwata,amma sai kinyi alkawarin kyale min yan uwana da iyayena"

πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ» "Pls"


Hajia shiru tayi tana tuno wata kyakyawar face din,so innocent kaman na Asma'u din nan , farkon ganinta da ita cikin kaya yaga gaggu,amma data tashi bata barta da komai bah sai diyarta


'Bazan tausayawa ko wani talaka bah, na koyi darasin da har in kwanta damata bazan manta shi bah'


"Hmmmmm, amma dai shekarun annabawan farko gareki koh, in bah haka bah ai bazaki taba biyana bah"

Asma'u batayi kasa a guiwwa bah ta sake yin magana


"Yadda zan zama baiwa a gareki haka, yayana jikoki na, in duka zuri'ata bauta za'a haifo su suyi ma taki zuri'ar,baza'a fasa bah har sai na biyaki komai, to the last penny, bazan rage bah"


Bacin rai da haushi ya har zuko hajia ta kifa mata wani lafiyayyan mari,

"Ni zaki nuna mah isa, har an yiki, koh uwar data haifi uwarki bata isa ta tsaya gabana ta fadamin abinda kike fada bah"

Huci hajiya keyi, ta dade rabon da tayi zagi haka, kuma tsanar Asma'u ya kara tsiro a zuciyarta dan har yafi tsanar da takeyi wa yarinyar data tuno,


"Sai kin ji dama ba'a haifo ki bah, ki rubuta ki aje mah zuri'ar ki bautar da kika siya masu da kudin ki"


Hawayen mah ya daina zubowa,kawai kukan takeyi.






⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

BY KHALEESI,
& NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’






Am dedicating this page to you lovelies, naji dadin comments din ku and am happy Boyayyen Kudiri ya samu karbuwa a wajen ku,



Naphysar😘
Abdallah hafsat😘
Hajara kassem😘
Naja'at sani 😘
And most especially KHALEESI's Forum😘😘


2⃣2⃣.


Tsaye suke sun jera layin a farfajiyar gdan sun kai kusan mutum 50, duk sanye da black and white na masu aikin,masu gadi ne da masu kula da CCTV cameras din gdan ne kawai basa ciki,


Tana hakimce saman wata kujerar meh kaman massage chair,ga wani katon umbrella da ake rike mata,


"Rabinsu babu wani hidima da sukeyi sai tawa, dayan rabin kuma Ehsaas sukeyi ma aiki, daga yau ke zaki maye gurbin masuyi min aiki"

Alama Hajia tayi ma masu aikin da su tafi, sunfi awa daya da rabi a tsaye suna jiran isowarta,amma dan wannan abin ta fada sannan tayi dismissing dinsu,


"Meh ke faruwa anan?" Ya shirya cikin wani sabon suit din, coat din samane beh sa bah,amma harda tie a wuyanshi


"Muna dan hira da Asma'u ne" ta maida mai da turanci itama


"Husna badai maganan tafiya gdan bane bah koh" dukar da kai tayi tana share hawayenta


"Asma'u zata fara yi manah aiki a matsayin maid dina ne" ta fada tana kallonta


Dukawa kasa tayi zata dauki izinin tafiya


" Husna get up!, grandma ban yadda da wannan tsarin bah nidai" dan murmushi Hajia tayi


"Gaka ga ita nan ai, bani na sata dole bah" dan dagowa tayi taga kallon da Hajia keyi mata


Cikin turanci ta fara magana saboda shi

"Nice na zabi hakan Sir,saboda abinda mijina yayi maku, gsky banji dadi bah"

Safa da Marwa ya fara saboda sabon kishin daya tasomai, da kyar ya samu ya iya manta bacin ran da kishin dazu ya sashi, gashi yanxu kuma tana mai magana akan wani mijinta,kaman dagangan takeyi,


"In dai kina gabana ki daina mentioning mijinki Husna"
Bacin rai karara a face dinshi

Hajia ta rike haba,tana mamakin irin wannan abu


"Kuma ba fault dinki ne bah, karki daura ma kanki laifi,dan haka tashi ki koma daki"

Ya fada yana nuna kofar shiga gdan


"Hajia ta shawo kaina akan in zauna anan,tunda da aure na in na koma gaban iyayena bazasuji dadi bah, na yadda zan zauna ne kawai in zata bari in dinga yi mata aiki,dan kar samun wurin yayi yawa"

Hajia mah gira daya ta daga sama🀨🀨

'Lallai wannan yarinyar ja'irar gaske ce, ji yadda take tsaro zance,dole kam na nisan taki da jikana kafin ki nisan tashi dani'

Ehsaas dai har yanxu beh yadda da zancen zamanta a matsayin meh aiki bah


"Grandma i don't like this" ya fada da wannan shagwaban daya zame mai jiki, kaman yana son yin kuka


"Ehsaas zo kaji" ta jashi cikin gda, sai bata fuska yakeyiπŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–


"Naxata so kake ta zauna" ya daga kai kawai

"Ina ganin kaman bata saki jiki da mu bane bah,shi yasa baxata zauna cikinmu bah, ka bari with time zata bar aikin da kanta"

Ya dukar da kai kasa, dan tallabo face dinshi tayi


"Amma in bakaso tayi aiki sai mu sallameta ta tafi,dan aikin ne kawai zesa ta tsaya"


Ajiyar zuciya yayi wanda ke nuna alamun ya saduda,


'In ta wannan hanyar ne kawai zan iya kasan cewa dake har in cinma BOYAYYEN KUDIRI na akan ki toh hakan zanyi'

"Amma ni zata dinga yi ma aiki, me and only me,no one else"

Hajia ta daga kaida eyes din mamaki😨😨😨


"Husna come in toh,nayi rehiring dinki a matsayin P.A dinah" ya fada da smile


"Ki hada tare da duk wani abu da yake so kinayi, a takaice dai duk wani aiki namu ke zaki dinga yi " ita kadai ta tagane abinda ta fada tunda shi bah hausa yakeji bah


Ta daga kai sau daya sannan ta mike, bata san yadda akayi bah sai gannin shi tayi a gabanta yana lakato tears dinta,


"Granny ma kuka takeyi, mai yasa take kuka?" Ya tambaya da turancin shi na British


"Kaga ga ita nan ai sai ka tambayeta" ta watsa mata harara da suka hada ido


"Am just Happy da Allah yasa baku kujeni bah,tnk u Hajia tnk U Sir"

Murmushi yayi yana ciro hanki daga cikin aljihun shi,

"Kin fara koh" πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰,ya fada da tsokana


"Now say my name twenty times, kuma dan Allah nxt time ki kara cemin Sir" matsawa baya tayi daya kawo hanki din ze goge mata hawaye



"Goge da kanki toh" karba tayo ta goge sannan tace zata wanke ta maido mai,


"Bani abu na" tafin hannu ya mika mata,sai ta doramai



"Muje kiyi freshen up dan yau sai mun siyo maki kaya"

Gaba yay ya shiga cikin gda,

"Kisan matsayin ki baiwata,idan kikayi gigin sabawa umarni na, zaki gamu da mugun bacin rai"



"Muje Husna manah" ya dawo baya yana mata alamu data taho



"Ki san abinda zaki fadamai,dan bazan dinga kwana dake under d same roof bah"
Tsoron shiga gdan ya kamata, ta rasa wani direction zata nufa taji sanyi a ranta,



Wayarta ta fiddo tana dialing number mamanta, hawaye yasa bata ganin numbers din da kyau dan haka ta kashe,


Kara kira tayi bayan ta goge hawayenta, wani kukan yazo mata,sai ta kashe,na ukkun ne call din ya shiga kafin ta kashe


"Salam Alaikum" ta fada da tana rufe baki


"Asma'u har kin taho ne" taji farin ciki a muryar mahaifiyar ta

"Mama" sai kuka

"Asma'u meh ya faru, inna lillahi wa inna ilahi raji'un,kiyi min magana"
Jin muryar maman tata da alamar kuka yasa tayi shiru


"Mama bazan samu dawowa bah" mamanta ta cigaba da kuka


"Mama matar gdan meh kirki ce,itace ta bani aiki sannan ta bani shawarar zama anan shi yasa bazan dawo bah"

"Asma'u" mamanta ta kirata da babban murya


"Kin san dai baki da wanda ya kaini a duniyan nan koh" da kuka ta bata amsa


"Toh ki dawo abinki,mun gode da kulawarta,amma bazan bar yata a inda ban sani bah"

Ajiyar zuciya tayi sannan ta goge hawayenta

'Babu abinda nake fata kaman in ganni a jikin ki mama, hakan kuma na nufin zan jawo maku bacin rai'


"Mama kin san abinda ya kara sani kuka?" Ta fada da dan dariya

"Cewa tayi kuzo kuga muhallin mu,shine farin cikin ganin ki ya sani kuka"

Dariyar dataji daga bangaren mamanta ya sata farin ciki


"Shagwaban da bakiyi bah da shi kike koya yanxu" itama dariyar tayi


Motoci guda biyu taga an fiddo, da wasu security a ciki


"Mama in nasa kati zan sake kira" nasiha mama ta tsaya yi mata wanda ya kara sata kuka,


Sai aikin share hawaye take tana tafiya, jinta tayi a jikin mutum, har ana kara rungumota, kara ta saki tana han kada mutumin.





⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI,
NA KHALEESI,
& NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Yabon gwani ya zama dole,ko kuma ince gwanaye,

Gwanintar ku da bajinta kesa nake kara alfahari da jin dadin kasancewa cikin ku ⚜B.W.AπŸ–Š, Allah ya kara basira da dankon zumunci,

Kisses to u all😘😘❀❀😘😘❀😘.


A koda yaushe daukaka da bunkasar yan uwa musulmi muke fata, zanyi amfani da wannan damar dan miki fatan Alkhairi
😍RUKAYYA HASSAN OTHMAN😍

Allah ya bada sa'a, ya kuma shige mana gaba a dukkan al-amurran mu, ya biya manah bukatun mu na Alkhairi,Amin



2⃣3⃣.


"Dan Allah kayi hakuri am sorry" ta duka itama dan har kasa ya kai

😳😳😳😳😳,
"Ashe haka kike da karfi" ya fada idanu waje


"Pls am sorry" tana so ya tashi tsaye saboda securities din da suka tun karo su


"Ku kyale mu" shima dukawa yayi da guiwowin shi a kasa kaman yadda tayi,

"Am sorry na baki tsoro,kina ta kuka ne bakima san ina nan tsaye bah"

πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»
"Dan Allah ka tashi tsaye" mike wa yayi yana son kama hannayenta data hade wuri daya

Ita kuma tasa hijab dinta tana gogemai wandon shi daya baci daya duka

"Husna ki bari,kina bani kunya"

Ya fada da dariya,sannan yayi gyaran murya yana magana cikin harshen daya iya na turanci


"Granny Ma ta bani address din wani boutique da zaki so"


Please Login or Register in order to submit comment