Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dinshi


"Granny Ma ba laifinta bane bah"

😭😭😭😭😭😭😭 kawai takeyi tana bata hakuri


"Hakuri yaci Uwa****, wallahi ki kiyayeni wani abu makaman cin haka ya faru, Sai naci uba** daya haife ki"


Juyawa yayi yana so ya share mata hawaye


"Karki damu da granny ma ta danji tsoro ne"

Matsawa baya take yana binta

"Are you okay?""" Ya tambaya voice dinshi cike da damuwa


"Muje asibiti a baki fulll body check up"

Ba hajia ba har yan aikin da suka zo sakamakon ihun Asma'u saida suka saki baki galala suna kallon wannan ikon Allah,


"Husna stop running away from me" ya fada kaman zeyi kuka 😟😟😟


"Pls ina so in san if you're okay" tsayawa tayi tana daga mai kai


Bata san hannunta na rike da inda aka mareta bah saida yayi yunkurin cire hannun


"Am okay, seeeEee" ta fada da fake smile😁


"Face dinki " yasa hannu ze shafa inda sawun hannu ya fito


"Ka barshi kawai" ran hajia yayi matukar baci, in ka kalli fuskarta bazaka gane bah sai ka lura da yanayin numfashinta, hade da hannunta data damtse πŸ‘ŠπŸ»πŸ‘ŠπŸ»πŸ‘ŠπŸ»



"A gama da ita kaeai" harara tabi Secretary dinta dashi,

Shi kuma ya bi ta gefen Hajia ya wuce rai bace, duk da ta dan murmusa mai kuma ta mika hannu ya rike,



"Kin debo ruwan dafa kanki"
Tana tunkarota takai guiwowi kasa tana rokoπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»,


Ta kowani side hajia ke maketa, tanayi tana huci da masifa



"Harkin isa inyi maki alfarma ki nemi watsamin kasa a ido, prison din mah ya kamace ki, shegiya meh idanu kaman na mujiya, kuma kiyi gaggawan sakan man jika, maitar ki bazata kama shi bah"



Ta hankadata har sida ta dangana da kasa


"In shaa Allah bazan sake irin wannan gangancin bah"
Kanta a kasa tana kuka meh tsuma zuciya


"Kinga yadda Ehsaas yayi shunning dina yanxun nan, jst bcos i slapped dis trash" ta kara yunkuri zata kai mata duka


Sauri tayi ta tsaya saboda muryar shi data tsinkayo


"Anyone?? " ya fada da karfi

Take masu aikin dake tsaye wurin suka hanxarta danjin abinda yakeso


"Ku dawo nan" ta nuna Asma'u

"Bazan fasa saki yimai aiki bah, saidai ina baki shawara da koma menene kika sargafa mai yake bibiyar ki, toh ki je ki cire tun muna shaidar juna nida ke"

Hajia tayi gaba abinta, secretary dinta ta kalli Asma'u fuska yatsine ta harareta sannan tace hmmm tana bin bayan hajia


"Salamu Alaikum, you called" yana jin muryarta ya fito daga dakin

"Jikin ki dinne" ta girgixa kai, saida ta wanke fuskarta sannan ta shigo dakin nashi


"Grandma dinka is sad, bataji dadi bah" ya kalli gefe yana pouting πŸ™πŸ»β€β™‚,


"Please, damuwa ta shiga shi yasa ta yanke hukunci da sauri, kaima ai kace ba laifinta bane bah tsoro taji"

Ya juyo yana kallonta, sai tayi kasa da kai

"Dan Allah ka shirya kuje event din kaga ana tsammanin ku" ta nufi dakin shi dan fiddo mai kaya

"Kayi hakuri wani lokaci in shaa Allah zan biku , amma yau kayi hakuri secretary din kakarka zata fadama duk abinda kake bukatar sani"


Every movement dtayi akan idanshi so yake ya gano in akwai wani ciwo a tattare da ita

'Kaman she's okay, Alhamdulillah '

Ya dauki kayan data fiddo

"Toni ai bance zanje bah" yadda ya fada da turanci yasa shagwaban kin fitowa sosai ,


"Dan Allah manah, pls" ta marairaice kaman zatayi kuka


"Ki kalli idona sannan ki kira sunan, karkiyi tunanin ban lura bakya san kiran sunana bah"

Ta Dago amma ta kasa kallonshi

"Toh kawai kije kice mah Granny ma, ni bazan iya zuwa bah" ya juya baya, tayi saurin zuwa gabanshi, ya kara juya mata baya yana murmushi

"Baxata ji dadi bah, in kayi haka"

Ya turo baki yadda ya saba, in yasan ze samu abinda yakeso

"Okay toh, fadamin abinda nakeson jin, karki manta" ya nuna eyes dinshi da finger daya πŸ‘‰πŸΏπŸ‘€


Ajiyar zuciya tayi ta dago ta kalleshi suka hada ido,

"Ehsaas dan Allah ka fita tare da granny ma"

Tana dukar da kai shi kuma ya lumshe eyes dinshi, baki har kunne

'You are special Asma'u, My Husna ya zama dole in sameki , kunyar ki kadai ya isa sani zaucewa' a cikin mind din shi harda kiss tayi blowing mai 😘,


"Bari in baka wuri ka shirya"
Beyi musu ba ya barta ta tafi

"Granny Ma!! !" Yayi murmushi suna hada ido

"Na shirya, ina fata ranki beh baci bah kuma baki ji haushi na bah" ya dukar da kai yana turo baki


"Of course not my grandson " ta shafa face dinshi

Tayi ma secretary din ta alaman su tafi


"Lets go" ta sakala hannu cikin nashi kafin suka tafi.



"Granny ma basai kun kira kowani Dr bah pls"

Ran hajia a bace suka shigo gdan

Asma'u da ta dage wurin hada musu lunch bayan ta bi dakunan su meh ciki da parlor ta gyara, taji shigowar su


"Ina Husna" ta boye cikin kitchen din da taji tambayar shi


"Call her for me, kila itama tayi targade din Granny Ma" tana jin yace targade tasan fadowar su daga stairs ne sanadi


Hannu ta dora saman bakiπŸ™ŠπŸ™ŠπŸ™Š


"Am. Dooomed ni Asma'u, ta kare min yau dinnan"






βšœπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š





πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

NA KHALEESI,
DA NOBLE JUDGE


πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



2⃣7⃣.



"Mu gani" ta mika hannu aka dora mata IPad a sama

"Wannan ne babba yana da aure,wannan ya gama University a A.B.U Zaria, Business Adminstrations ya karanta but acahaba yakeyi da napep,
Sai wannan shima gana tuka napep din,sannan yana zuwa University shima A.B.U dinne but Agriculture yake studying"

Hajia tayi tsaki

"Na rasa ta inda matsiyatan nan suka shigo manah lyf, ki samu daya daga cikin biyun nan ya dandana azabar da jikana keji"
Ta maida mata IPad din kafin ta mike saman gado


"Hajia Ehsaas yana daurewa ne kawai da hannun nan,har baccin dole ya kwanta yi dazu da rana"


Ta shigo da sallama sannan ta dora tray din abincin data kawo saman table din dake kusa da gado

"Barka da yini hajia" ta fada tana serving dinta


"What the heck is that?" Ta fada ihun daya sa Asma'u yadda serving spoon


"Yi hakuri hajia, naga bakici abincin dazu bah dana kawo,sai nayi tunani kila na gda zefi maki dadi"


Hajia tasa cokali ta debi loma daya ta kai baki,

Saida ta kalli secretary dinta saboda dandanon daya ziyarci bakinta,

Da yake Asma'u bata gani bah sai ta ya mutsine fuska,

"Next time ki fadamin abinda zaki dafa kafin kiyi"

Tace toh sannan ta matsa gefe dan ba hajia daman cin abinci,

Faten wake ne yasha ganye ga dry fish,hanta da tsokokin nama,


Secretary sai hade miyua takeyi dan kanshin abincin kawai ya dameta,


"Wannan fah?" Ta matso da sauri dan taga meye


"Garlic bread ne danayi baking da olive oil, saboda yana da magani sosai, kuma wasu suna hadawa da shi wurin cin faten wake"

Sannan tayi slicing yanka uku ta aje mata gefen plate dinta


Hajia dai ranar taci tayi nak,dan ta dade bata samu abincin daya tado mata da taste buds dinta bah


"Kinsan dai Ehsaas baze ci wannan abin ba koh"

Ita ta manta mah da irin abincin da yakeson ci

"Eh Hajia nashi daban ne"
Sannan tayi gaba a ranta tana mai mamaki hajia bayi magana akan targaden Ehsaas bah, kuma bata dora mata laifi bah.




"Bakiga abinda ya sameni bane bah" tsaye ta ganshi kitchen din, tana shiga ya tunkarota yana tallabo hannunshi


"Wallahi zafi wrist dina keyi har yanxu"

Hannun ya kumbura yayi ja, duk laifinta take gani na karyar dataso yi

"Sannu kaji" ta fada da muryar tausayi

"Shi kenan" ya fada da surprise

"Bazakiyi min abinda kikayimin rannan n bah, shi yasa nace ba,an je asibiti bafa". Ya fada da shagwaba


" wannan kaman dole sai kaje asibiti" ya make kafada

"Toh mu gani" ya iso inda take, bowl meh fadi ta cika da ruwan zafi sannan tasa clean white towel ta fara gasa mai


"Arghh, ouchh uhhhh" sai ta tsaya tana kallon shi


"Wai kai koh kunya bakaji kaketa ihu kaman karamin yaro" ya zuba mata red eyes dan beh san abinda tace mah


"Sorry kaji" ya zata abinda tace da hausa ne ta maimaita sai ya kara bata face kaman zeyi kuka


"Akwai zafi sosai ne Husna" ta dauki bowl din zata zubar da ruwan


"Ai an gama,gobe da safe kaje asibiti gsky". Ya sake make kafada

"Sai dai ke gobe da safe ki zo ki sake dubamin" ya fada da murmushi


"Meh zakaci?" Ta fada tana bude fridge


"Koh me kika ciyar dani" ta daga kai taga kallonta yakeyi da murmushi

"Abincin dazu da rana ta dumama mai,dan shi bece bah"

Jawo bar stool din dake cikin kitchen din yayi ya zauna


"Toh mu fara" ya bude baki

"Bakiga hannuna bane bah" πŸ˜–πŸ˜£πŸ˜–πŸ˜£πŸ˜–πŸ˜£,

Badan taso bah ta matsa kusa dashi tana diban spaghetti din da meatballs sauce tana bashi a baki


"Water" tace sorry tana hanxarin daukowa


Saida ya cinye plate dinshi tas sannan ya sha juice


"Tnk u Husna" tace bakomai


"Sai da safe" ba musu shima yace sai da safe kafin ya nufi dakin shi,


"Am sorry ban san kana nan bah" tayi saurin warware daurin tayi mah hjab dinta ta baya


"Ki cigaba da aikinki,ni voice dinki kawai nake sauraro" ta sake dora kai saman counter din cikin kitchen din yana jira ta cigaba da karatun qur'ani


"Na takuraki koh" ya fada kaman mejin bacci

"Aa, dama yau friday ne kuma ban samu na karanta suratul kahfi bah dana gama sallah, shine nake yi yanxu da ina aiki"


Shi kanshi beh san ma'anar kallon da yakeyi mata bah, amma yasan akwai birgewa aciki

"Ni ban haddace bah tukunna, zuwa juma'at na iya off hand"
Ya fada yana noke kai


"Kayi kokari ai" ya dago da fara'a

"You think so" ta kara daga mai kai

"Thank you, ban samu na sauke Quran bah har yanxu, ina jin kunya kar mutane su sani"

Ta dago daga nika waken da takeyi


"Babba dani haka" ya fada yana kai kanshi kasa


"Ba abin jin kunya bane bay, tunda kana so ai malami kawai zaka nema"


Bata ankara bah ta ganshi gabanta


"Malami koh malama" ya diga gira yana kallonta


"Toh yaushe zamu fara karatu malama" saura kadan ta sack bowl din hannunta


"Yessss nayi sabuwar malama, in dan na dawo daga masallaci zanzo muyi magana akai, yanxu bari inje in fadama mommy yaaayyyyy"

Tsaye ya barta da idanu waje,har ya dade da tafiya baTa iya tabuka komai bah,



"Ashe ka tuna kanada Mahaifiya ?" Shima ya kwaikwayi muryarta


"Kasan tun yaushe rabonka daka tuna dani" ya maida wayan hands free

"Allah not a day passes by that i don't think about you mom"

Ya shafa keyar shi dan zancen Asma'u yakeson sakowa nxt


"My lovely mom,am so happy" ya fada gado yana jawo wayar


"Momma's boy,fadamin abinda ke saka farin ciki"

Hannunshi ya kalla wanda yayi targade da yadda yaji kaman kar hannun ya warke saboda special kulawar daya samu daga Asma'u

Hannun ya sumbata kafin yayi magana


"Mom, am sooooo in love, the girl is like" ya tsaya jan numfashi


"Mom yarinyar tayimin, kuma kema zatayi maki, bakiji yadda nakejinta a raina bah"

Mamanshi ta cire wayar tana kallon P.A dinshi Alfie

"Ya fada maka akwai yarinyar da yakeso"
Alfie ya girgixa kai


"Mom kina jina" tayi saurin ansa wa da Eh


"Son fadamin sunanta dana babbanta, am sure babu wanda zaki hada zumunci da mu, a yau mah sai in sa aje gdansu dan sanar da iyayenta batun ka, tell me ya sunanta"


Ya kware baki zece Asma'u, sai sunan ya sarke mai a wuya


Da hanxari ya kashe call din


"Mom batason ina wani abu da talaka, duk yadda Husna ta hadu a komai Mom baxata yarda da ita amatsayin surika bah tunda basu da kudi"

Wayar ya wirga yana oh my God


A bangaren mahaifiyar shi kuma tasa a ranta cewa zata kira kakarshi taji yarinyar dake cikn rayuwar danta.





⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

KHALEESI
DA NOBLE JUDGE.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



2⃣8⃣.


Hankalin shi yaki kwanciya,har suka je masallaci yana tunanin yadda ze samu mafita,


"Alfie" ya lalubi aljhun shi yaji ba waya, tsaki yayi dan yasan ya manta wayar ne


"Kace wani abune sir" saidai yayi tsaki kafin ya girgixa kai


Suna shiga gdan ya nufi dakinshi,

"Ta san wani abu akan Husna"
Abinda ya tambaya kenan ana daga wayar shi

"Wacece Husna, Sir" ajiyar zuciya yayi

"Good,Mom nada wani personal meetings yau"
Ya kalli agogonshi yana kokarin gano meye time yanxu a wurinsu

"Tana da call da Mamanta anjima"
Kashe kiran yayi ya fara neman layin Asma'u amma baya shiga,daga karshe akace switched off


"Granny Ma" yana shiga dakin ya iska Asma'u tsaye daga gefen kujerar da Hajia Turai ke kishingide

"Ya akayi grandson" ya kalli Asma'u

"Ina da magana dake" yayi kokarin nuna bacin rai a tare dashi

"Meh kike jira kuma" hajia ta fada da hausa

Asma'u tace excuse me kafin ta fita,

Dama tausa takeyi mah hajia,ya katse su,yanxu sai taje ta nemi abinda zata sa ma cikinta, ita bada azumi bah amma ta yini da yunwa,


"Granny Ma,in mom ta tambaya karki fadamata komai akan Asma'u"

Ya fada a hankali yana dan kallon kasa

"Meh yasa, ka gano bata dace da kai bane bah koh meh"
Ya girgixa kai

"Ina da plans din da nakeyi ne tukunna, idan na gama sai mu gaya mata,but for now muyi shiru kawai"


Hajia tayi mamaki amma ta amince mai a baki kawai, a zuci kuma tace in dai ka cigaba da fifitata akan kowa kam sai na rabaku da kaina batareda mahaifiyar ka ta sani bah,


"Ke kuma" ya fada yana kokarin daure face

"Meh yasa bakya ansa call dina, bana jin dadi fah in kina shareni"

Wayarta ta dauko ta duba missed calls

"Ni kam dai baka kirani bah"
Yace What!

Sai kuma yaga wayar hannunta


"Ina dayan wayanki" nan ta tunomai baya hannunta kuma


"Hold this" ya bata wayar hannun shi sannan ya koma dakinshi


"Gashi,kisa chaji kuma" ya kawo mata charger

"Dan Allah ka karbi abunka,ni bana bukatar wannan wayan"

Ta gaji,ga faduwa daga stairs dinnan duk yasa mata ciwon jiki, ga yunwa hade da ciwon kai sannan ga hawa sama da saukowa,hade da dafa abinci, bata da karfin da zatayi magiya da spoilt brat kaman shi


"Duk lokacin dana kira bana samunki" karba kawai tayi ta aje dan bazata iya dealing dashi bah yanxu


"My handπŸ˜–, kuma yunwa nakeji" ya miko hannun dan ta rike sannan yayi wani katuwar hamma


"Kaje asibiti dan Allah, kaga yanxu zan dafa muka lunch" ta fada batareda ta kalli inda yake bah,


"Hannun ya daina zafi mah" batace dashi komai bah

Turo baki yayi

"Toh bani wani snack kafin ki gama" ya fada da shagwaba

Fridge ta bude ta dauko yogurt ta bashi,sannan ta koma kan aikinta.


"Wata yarinyace marar aji madam, nasan hakane daga yadda take ansa call,ba manners"

Ya koma gefe yana harde hannuwa,bayan ya gama kitsa karya da gaskiya ya fada


"Kace P.A dinshi ce koh" Alfie yace wai bah


"Ka turamai sabon assistant yanxun nan, sannan muga schedule dinshi"

Ya mika mata ipad din hannun shi


"Ka cike duk free lokacin nan da yake dashi,kada ka bashi ko da second daya ne daze samu daman mu'amula da ita"

Ya hau aikin da maman Ehsaas ta sashi dan kwata kwata baya san Husna,


Garlic bread din shekaranjiya take ci da sauran coconut, Ginger and pineapple cocktail din yau da safe,


Kafin ta gama kazar da take gasa musu yayi,oven ta bude ta jawo tray din sannan tayi garnishing kafin ta maida ta rufe ba tareda ta kunna bah,


"Assalam Alaykum" ta shiga duk da ba'a ansa bah


"Ga abincin ranan Hajia nan"
Ta fadama meh aikin data leko daga dakin

"Za'a bata,ki tafi" ta daga kai kafin ta koma kitchen


Abincin shi ta dauko zata kaimai saita hada da wauar daya bata, tana dan tabata ta kawo wuta, wani email ta gani a notificationπŸ“§,


"Salamu Alaykum" bayan ya ansa kaman ansa shi dole sai ya kalleta dan yaga in ta gano fushi yakeyi

"Ni bana magana dake" ya kara cuno baki, yanxu dataci abinci ta danji karfi sai ta samu daman murmushi,


"Toh ga abincin ka nan,in ka huce kaci" ta fada da hausa kawai sai gani yayi ta mike zata tafi


'Husna bakya tausaya ma masoyi ne wai' ya fada a ranshi


"Gashi wannan kana da sako" ta mikamai wayan sai ya hada da hannunta ya rike


"Sirr" ta kwace hannunta
"Yaushe zamu fara karatu" ya sauko daga saman gado yana barin wayan acan,


"Top chef ce ke Husna, kin iya dafa abinci"
πŸ“±ta dauko sannan ta bude email din


"Bazamu samu daman karatu bah dan aiki zeyi maka yawa" dariya yayi dan ya zata so take kawai taki zama malamar shi



"Wai da gaske kike" ya πŸ™„
Ta mika mai wayan


Take ranshi ya baci
"Meye ma'anar abinda ka turo"

"Ba saida nace ka rabani da duk wani aiki bah, meye wannan shirman dake cewa zanje"

Alfie ko word daya beh samu yace bah dan fada kawai yakeyi mai


"In ka kasa aikin ka fadamin ni sai in samu wani"
Sai lokacin yayi shiru


"Kayi hakuri pls sir,mamanka ne tace in saka a duk meetings din da zataje"

Girgixa kai ya fara yi

"Tell her am busy" ya kashe wayan yana jefar wa

"Maman ka ce koh baka son kayi abinda tace,in dai beh saba mah addini bah,toh kayi hakuri kayi,Allah zeyi rewarding dinka"


Ta barshi da wannan sannan ta fita.





⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

NA KHALEESI,
DA NOBLE J.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



2⃣9⃣



Da BOYAYYEN KUDIRI shi was simple, abu daya ne watau auren Asma'u,
Yanxu ya karu,
Lokaci yayi daze fara aiwatar da abubuwan da zasu bashi daman kasancewa da Husna dinshi,

Tun da sukayi waya da mamanshi ta kara bashi list din irin matan da takeso ya rasa sukuni,

Yar gdan manyan mutane, kuma masu fada aji,
Duka family dinsu Asma'u masu rufin asiri ne



Please Login or Register in order to submit comment