Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shiga dan duba abinda Alfie ze turo mata

"We're here Sir" driver din ya bude mai kofa,ita kuma ta bude ta fita da kanta

"Inna lillahi wa inna ilahir raji'un, Bank ne office din" ta fada da dan karfi


Ita da bata taba zuwa koh hanyar shiga banki bah,

"Ya Allah ka taimakamun,kasa kar inyi messing up a rana ta farko"

Takowa tayi a hankali ta nufi kofar shiga meh circle dinnan

Gaishe da security din dake tsaye a wurin tayi, sai ya amsa yana mata murmushi sannan ya latsa button din kofar ta bude

Thank you tace kafin ta taka a hankali ta shiga kaman nitsewa zata in ta saki nauyinta

Tsaye tayi a cikin wurin tana zaro ido dan kofar ta rufe kuma taga ba wani abu dake faruwa

"Fito kinji" security din yace mata bayan kofar data bi ta shigo ta bude

Kaman ta fara kuka haka taji dataga wasu sun shiga kuma ba'ace su fito bah

"Bari mu sake gwadawa" wannan karon data shiga sai ta runtse eyes dinta gam tana addu'a

Gyaran murya taji sai tayi saurin bude ido, wani mutum ta gani yana mata alaman ta fito,ajiya zuciya tayi kafin ta shiga bank


Daidai lokacin da yake addressing ma'aikatan bankin

"Me been here all of a sudden may make you all to question the why of it, am only going to be here till my grandmother gets back,until then i expect the best from you guys"

Nan sukayi mai tafi sannan aka nuna mai office dinshi,yana shiga ya jira ta shigo,

"Husna" ta tashi tsaye daga inda take zaune

Da kai yayi mata alaman ta shigo, saida ya zagaya ya zauna saman kujerar shi sannan ta shigo


"Kinyi magana da Alfie koh"
Ta daga kai tana cewa yes

"Good, seat down and prep me on today's agenda"
Jawo kujerar tayi ta zauna

Booting computer din gabanshi yayi sannan ya kalleta yaga wasa da yatsunta kawai takeyi

"Husna be active your on a job not a date, i joke around but i take work seriously "

Ya koma kan computer din

"Sorry Sir"
"Ehsaas" ya fada ta sake cewa sorry kawai


"Meye password dina?" Ta zaro ido


"Did you read any of the things Alfie sent you?" Ta kalleshi da eyes waje

Sannan ta girgixa kai

'Akwai matsala' ya fadama kanshi

'Be smart Asma'u,shi a wurinshi koran ki ba komai bane bah"

"Am sorry Sir, I'll do everything right" bata kalleshi bah ta mike da sauri ta fita waje ta sake kiran Alfie


"What?" Kaman dama yasan itace

"He wants you to call his grandmother's secretary and then send everything to me,include the password to her computer" taji yana maganar nan nashi na sauri abu kadan kawai ta jiyo


"Why do i have to do it, your hes new PA" da alamu wannan beji dadi data maye girbinshi bah


"Fyn I'll do it" ya katse call din

Bata koma office din bah saida yayi emailing abinda take bukata kuma ta karanta kafin ta shiga office din


"Password din shin__"
"Type it in" ya juyo mata da keyboard din

Dan dukawa tayi tana latsa letters din daya bayan daya, shi kuma yan yatsunta zara zara yake kallo

'She's perfect in every way ' ya bige da kallon ta saida tayi magana

"Do you need anything Sir" jawo kujerarshi yayi ya matsa jikin table din

"Get me coffee, and you get back we are going to train you to say my name"
Da kanta a kasa ta fita daga office din, tsoron shiga kofar dazu ne yasa ta tuno ta bar jaka a office dinshi


"Sorry, i forgot my bag" bata shiga office din sosai ba ta fizgo jakar ta fita

Abin dariya ma ya bashi, yin komai takeyi kaman ace ke! Da karfi ta gudu


Mota ta shiga tace driver ya kaita in da zata siya coffee

Ita kuma ta maida hankali wajen karanta abubuwan da aka turo, tanayi tana rubuta important ones din cikin littafin ta

Kaman meeting dinshi na gobe da event din da aka gayyace shi na friday, tayi mamaki dataga account numbers dinshi da pin's din ATM, wani abin da bata taba amfani da shi bah

Dora kai tayi saman kujerar dake gabanta, dan dariyar driver din taji, data dago sai ya daina

"Karki damu kanki,ban taba ganin mutum meh saukin kai kaman shi bah" dan murmushi tayi sannan tace ta gode

"It's best in kika siya coffee da thermo flask babba"

Ita ina mah ta iya hada coffee, gashi babu wani kudi ita a tare da ita

"And ga wannan" ya miko mata wallet

"A cikin mota ya barshi jiya,sai kiyi amfani dashi ki siya duk abinda ze bukata"

A hankali ta bude wallet din, sai kuma ta rufe tunda private abu ne wallet,



Wani babban supermarket ya kaita sannan yace ze jirata a mota

Tafiya takeyi kaman cinyeta za ayi a wurin ido waje,

"Can i help you?" Ta juyo da saurin tana kallon sales boy din

"Meh kike bukata"
"Ahmm,coffee, some sugar"

Kafin ta gama magana yace ta biyoshi

"Ga duk abubuwan da zaki bukata" kallon komai takeyi,sannan ta mika a hannu a hankali kaman tana tsoron abinda zata taba din

"Gashi" ya bata dan basket karami

"Excuse me" ya dawo wirinta
"Ina son thermo flask kuma" yace mata yana zuwa ita kuma ta cigaba da karanta abubuwan

Data gama zaba sai dauko mata condensed milk da full cream

"Zaki bukaci wannan mah" tnx tace mai sannan ta dauko mug da teaspoon

By the time dataje wurin biyan kudi ta dan rage tsoro, da aka fada mata kudinta sai taga bata da kudin biya

Wallet dinshi ta dauko daga jakarta,sannan ta zaro wani ATM dinshi,dan taga suna amfani dashi

"Tnk u tace" bayan ansa komai cikin leda an bata


Da sallama ta shiga office din
"Where have you been?" Ya tambaya tana sa kai cikin office din

"Naje siyo wannan abin" ta ciro wallet dinshi ta doramai saman table

Dauka yayi ze bude sai tayi magana

"Am sorry nayi amfani da ATM dinka wurin biyan kudin abubuwan nan" ta fiddo su daga cikin leda

"Driver dinka yace inyi amfani dashi wurin siya"
Abinda beh tabayi bane bah yayi ranan, kirga kudin cikin wallet dinshi


Yana sane ya barma driver wallet din yace ya bata ,dan yana so yasan in ze iya trusting dinta

'Don't be happy just yet, ka bari kaga in honesty ne policy dinta'


"Keep this" ya fiddoshi daga karkashin table inda ya kirga kudin

"Duk abinda zan bukata you buy it from here" girgixa kai tayi

"You keep it when i need it I'll ask for it"

Waje ta fita dan neman ruwan zafi

"Use the dispenser" wata ma'aikaciya ta nuna mata

Office dinshi ta koma tunda dama akwai a ciki

"Gashi" ta mika mai bayan ta hada coffee din kaman yadda zaka hada tea,saidai maimakon madara sai ta cream

"Do you need anything sir" ta tambaya bayan ya sha yace yayi

"No"
Mikewa tayi ta fita waje, mota ta koma ta zauna tana rubuce rubucen ta,


Shi da yace ta zama PA dinshi saboda ya dinga ganinta kullum kuma koda yaushe gashi yayi kusan awa 7 beh ganta bah

Suna dawowa daga wurin sallah ya ganta zaune cikin mota

"Are you done for the day Sir" ta tambayeshi daya shigo motar


"Yes we can leave" sai da sukai hotel dinshi yace a fara kaita gda

"Same time tomorrow" ya leko ta window yana fadamata
"Yes"


kofan gdan kaka suka ajeta sai ta shiga cikin.
[3/9, 10:58] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜ BRILLIANT WRITER'S ASSO πŸ–Š


πŸ‘†πŸΏ

Take notice fah ppl, am now officially part of an extinguished writers asso and i am glad i got accepted, so this page is yours, All members, tnk vry much.


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


1⃣4⃣.


Daga gdan kaka sai tayi gdansu dan sanar da mamanta yadda first day of work ya kasance,


"Mama na dawo" ta shiga da fara'a dan ita a ganinta tayi job well done yau

"Kaman ya kin dawo, bacan zakiyi ta zama ba har sai an daura aure" itama daura fuska tayi, sannan tace bazan bari wannan zance ya batamin mode dina bah

"Mama na dawo daga wurin aiki nake cewa" ta zauna ta ciro bag dinta daga hijab ta aje saman tabarmar da mama ke zaune


"Aiki?" Mama tayi looking surprised

"Wurin aiki manah mama, ashe bank ne mah office din" bata rufe baki bah Baba ya fito daga daki

"Aiki kuma Asma'u ba tareda mun sani bah" gabanta ya fadi,sai lokacin itama taga wautarta, tasan tabbas da Baba sai ya kirata a waya


"Wani post na gani ana neman ma'aikata koh bakada experience, kawai sai na gwada applying" ta jira dan taji abinda zatace kuma koh wani karyar ze kara forming a brain dinta


"A banki kuma koh baka da experience?" In ji Babanta, faduwar gabanta ya karu


"Nima nayi mamaki danaga a banki ne" ta sake yin shiru dan bata san meh zatace bah kuma su ita suke jira ta cigaba

"Ban fada muku bah saboda bana so inje banci interview din bah, kuma ya zama baku ji dadi bah" taga Baban ta yayi murmushi

"I have the smartest daughter in the world, kuma koda baki ci interview din bah nasan badan baki da kokarin bane bah, sai dai dan qualifications dinki ne basu kai bah"

"Ai batace taci bah tukunna" inji mamanta

"Koh kinci" ta daga kai dan har wani abu ya tsaya mata a makoshi yin magana na nufin fashewa da kuka


"But ya akayi kika samu aiki, koh results din ssce bakya dashi"

"Identification kawai suka bukata, kuma ba wani job bane bah filing papers din da akayi amfani dasu ne a wurin" Babanta kawai taga yaji dadi


"Mama ya akayi,bakya murna ne" Mama ta girgixa kai


"Asma'u aure zakiyi fah, kamata yayi ace mun killace ki a cikin gda,ba mu barki kina yawo a kan titi bah, kin san ance amarya da tsautsayi"

Aranta tace dama tsautsayin ya fada mata koh a fasa auren, kuma sai tayi saurin yin istigifari


"Barta tayi tunda ta samu opportunity dinnan,kuma har an dauketa aiki" Mama ta juya wurin Babanta


"Auranta saura kwana takwas fah" tayi saurin gyara mata


"Sati biyu ya rage fah"
"Kullum ne saura sati biyu" ta dan dukar da kai kasa


"Gobe juma'a ya kamata in siyo dabino mah na manta, tunda daga gobe saura sati daya"

Ji tayi kaman kasa ta tsage ta hadiyeta, dan ta tsani maganar aurentan nan, kuma ba da wani bama sai wannan meh halin marar kyau


"Ni dai zan wuce haka, zamu fita da Asma'u" ta mike tsaye dan taga maganar auren ya dauke musu hankali


"Toh ki kula da abinda ya kaiki Asma'u" daga kai kawai tayi alaman toh kafin ta koma gda


"Yar arziki irin albarka" in ji Ma'u dake kwashe shanya

"Har wanki kikayi yau, da kin bari sai asabar sai in tayaki" Ma'u ta tsaya da kwashewa

"Ai dama ke zakiyi min gugar" dan dariya tayi tana girgixa kai


"Daga ina kike haka" ta bude baki zata fadamata sai ta tuno yayyanta basu san irin labarin data ba iyayensu bah


"Yah Allah ka yafeni bada san rai na fadi zancen da ba haka bane bah" sannan tayi dialing number din yaya Abba tayi mai bayani


"Kuma na bata daku ku biyun" sannan ta kashe wayanta data ji dariya ma yakeyi



"Mama na kira" ta tashi ta bi Ma'u zuwa dakin Mamar su

Nan aka hau yi mata bayanin kayan abubuwan da aka karbo mata da kuma yadda zata sha su


Batace uffan bah har aka gama yi mata bayani

"Kin ji yadda nace koh" tace uhm da kai kasa


"Mama ni banga kazar meh maganin bah" Ma'u ta fada tana daga ledojin maganin kaman aciki zata gani


"Dauke hanun ki" mama ta dan buge mata hannu
"Tashi kuje Asma'u, kuma kar inji ance ba kyasha, dan zaki ga bacin rai na, kuma yau zaku fara dilka"

Su Ma'u harda tsalle dan yana cikin abubuwan da takeson yi

"Mama kin karbo turarukan kwabawa dashi" Mama ta harareta


"Muje namecy, ji nake kaman nice amaryar"


Ringing din waya suka ji suna shiga cikin dakin

"Kin canza ringtone ne namecy" ta dauko mata jakar daga inda ta rataya ta


"Ni ban canza" rufe baki tayi kafin ta karasa maganar sannan ta fizgi jakar daga hannun Mau

"Da naje wurin aiki na canza ringtone din" ta fada tana latsa wayar daga cikin jaka


Tasan bazata iya kashewa bah dan business related calls ne kuma ga wayar hannunta ya zama dole ta ansa calls din


"Ma'u bari inje wurin kaka in dawo"

"Baki fadamin aikin da kikeyi din bah" alamu tayi mata da ta bari in ta dawo


"Gwara mah da kika zo yanxu, kalli can makociyata ta kawo wai a baki" wani abu ne cikin leda

"Zanin gado ne, saboda haka ki biya ta wurinta kiyi godiya,kar kiyi mata irin halin mamarki anayi bata gani, balle ta gode"

Toh ta amsa dashi tana godiya kafin ta samu wuri ta zauna daga can gefe


"Naga sai wani sintiri kike yimin kwanan nan,ganin kwakwaf kike zuwa yi koh meh" da murmushi ta girgixa mata kai

"Yanxu ina kusa da ke ne kaka, shi yasa nake lekowa koh akwai abinda zan tayaki da shi"
Kaka dai tayi tsaki tana yatsina fuska


"Shiga kitchen din ki doramin tuwon dawa,da miyar kuka meh wake a ciki"

Ta mike dan dama abin da takeso kenan

Tana gama dorawa ta fara amsa calls din dake shigowa sannan kuma ta kira wanda suke missed calls, sai gab da Maghreb ta koma gda, inda zakwadin hada dilka yasa Ma'u mancewa da zancen aikin da takeyi


"Sir" abinda tace kenan tana shiga motar, dama tana zaure bata shiga ciki bah dan kar kaka tayi korafi


"Good morning, and how many times do i have to say it, it's Ehsaas for you"

Ta gaishe shi sannan ta tambayi dalilin kiranshi da Ehsaas


'Because i like the way you say it' amma a fili sai ya hade fuska


"You just questioned your boss, and it's a privilege for you to call me by my name" ya fada kaman ranshi ya bashi


"Sorry sir" ya zaro ido, "am sorry i mean Ehsaas"
"Say it again" ta kalleshi suka hada ido sai tayi saurin yin kasa da kai

"Ehsaas" yace good

"Keep saying it" ya dan kishingida jikin window ya rumtse idanu


Tun tana fada a kai kai har ya kai sai ta dade sannan

"What is dat" ya nuna littafinta da fuska ya mutse kaman dodone


"Schedule dinka nake rubutawa a ciki dan kar in manta" ya kalleta sannan book dinta


"You can't be using dat" ya fada da dariya a muryar shi

"Bari muje in shirya sai a san yadda za'ayi da wannan abin" ya sake nuna littafinta


Ita sai lokacin ta lura ba suit ne jikinshi bah, sweatpants ne da T-shirt ash color sai wani hoodie baki daya dora sama


"Muje" ya fadamata da akayi parking

"With all due respect sir" ya katse ta

"I think you need more practice, say my name 10 no 20 more times" ya harde hannu saman kirji

"Am sorry, i won't say it again" beh motsa daga inda yake bah dan haka ta fara


Murmushi ya hau yi saboda style din da takeyi wajen kiran sunan
Ita kuma gajiya ce da haushi yasa take kira duk yadda taso
"Good, what were you saying" ya tashi daga inda ya jingina

"I said why do i have to pick out a suit for you everyday?"
Ya juyo da dan mamaki

"Bcos it's your job" wow tace sannan ta bude kawai tana zaro wanda ya tari gabanta


"Anything Else" tana juyowa yana kokarin cire tee dinshi, sai ta juya kawai ta fita


"My morning coffee?" Ya tambaya yana zama a cikin motar


"I'll get you one now" ta koma cikin hotel din tayi requesting coffee


"Uhmmm" ta fada dan karta kira sunan shi kuma sai tayi sa'a ya juyo

"The made breakfast for you and would be delighted if you could honor them with your presence" bata fuska yayi hade da

"Ugh" yace
"Hanyar baka hakuri ne mah last time da sukayi breakfast dat wasn't to your liking" yi yayi kaman ta takura mai


"I'll get coffee" ta juya ta koma cikin hotel din

"I'll eat" taji muryarshi daga bayanta


"On one condition only if you'll join me" ta dan matsa gefe

"It's not necessary" ta fada a hankali

'I want to spend more tym with u' ya fada a ranshi a fili kuma


"l have already said it and it's final"


Binshi tayi zuwa dining area din hotel din,inda babu wasu mutane sai su kadai

"Miss meh zaki so a kawo maki" ta dan gyara zama kafin tace tea da bread kawai


"No, get something else" ya fada hannu harde a kirji

"Ni abinda nakeso kenan" ta fada murya kasa kasa

"She'll have wht am having" har waiter din ze tafi ta dawo dashi

"A bani cornflakes da juice" ta dan kalleshi ta gefen ido

"And a slice of bread if it's not too much" ta fada dana squeezing yan yatsunta

"And some eggs too" ya fadama Waiter din

Tare aka kawo musu inda ana gama jera mata nata tace tnx,shi kuma saida ya dan dana

Sunnyside up eggs dinshi,sausages da French toast kafin yace it's okay

Waiter din ya tafi da murmushi,ita kuma ta mika hannu meh kyarma zata dauki spoon tasa cikin cornflakes dinta sannan tasa madara da sugar, kuma ga fruits da nuts an kawo mata tayi garnishing


"Kisa bananas din da nuts,zakiyi enjoying dinshi" kadan tasa sannan ta debi spoon daya tasa a baki

Ta rasa inda zata sa kanta dan basai an fada bah tasan ita yake kallo, ga abinci tana so taci amma ya tsareta da eyesπŸ‘€

"You should eat, you have a meeting scheduled for 10:am" taga ya juya idanu yana wannan

"Ughhhhhh" din alamun an takura shi

Ita dai ta samu yadaina kallonta har ta shanye cornflakes dinta sannan ta danci quarter din kwanta

Shi kuma saida yayi clearing plates dinshi tas,amma wai 'its okay'


"Ina mah nace zamuje" ya juyo gareta da suka shiga mota

"Office, 10:am meeting" ta tuna mai sai ya girgixa kai


"New phone for you" ya fadama driver

"Sir,saboda kai meeting din ya kai har yau kuma old friend din Grandma dinka ne"

Ya dade bece komai bah har driver din ya kashe motar

'I want to spend more tym with her that's why i hired her,not to work' ya tura baki yana surutu shi kadai


"Fyn lets go, call the manager tell him to arrange everything I'll need"
Tana fiddo wayan ta kalleshi


"Am so sorry i forgot to give you your phone yesterday" ta fada tana mika mai

Kujerar driver ya dan buga
"Give her my other phone" ana bata yace ta hada ta rike


"Keep this with you,after every days work then you give me this" ya nuna iPhone din

Kenan BlackBerry din jiya ta rike tana aiki dashi,

'Wannan wani irin mutum ne,ansa wayar mah aiki ne' ta dai sa cikin jakar ta


Koh awa daya beyi a cikin meeting din bah sai gashi cikin motar


"Am done for the day lets buy you a new phone"
"Sir i have a phone, and I'll use this for your work,i don't need a new phone" hannu ya mika mata tace what

"Lets see you phone" bata ji komai bah ta dauko mai yar techno dinta

Beh mah karba bah

Please Login or Register in order to submit comment