Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayi hakuri, bazan kara yin irin haka bah"
Ya kalli gefe kaman beh yadda da abinda tace bah,

"Wallahi bazan kara bah, dan Allah ka kalleni" taje gaban shi tana kokarin karkato da fuskarshi gareta,

"Am sorry, pls forgive me"
Hada goshin su yayi wuri da,
"Tsoro naji jiya dana dawo baki tarbeni bah, kuma aka cemin baki fito bah, sannan na ganki cikin wani hali Husna, i just got scared, take na hango rayuwata babu ke a ciki Husna"
Muryar shi ta fayyace raunin da ya tsinci kanshi ciki a lokacin,

"I love you so much Husna" shigewa jikinshi tayi tana goge hawayenta a rigar shi,
"Say u love me" ta make kafada
"Bazan fada bah tunda ka sani kuka"
Shagwaba ya fara yi mata yana plsssssss,
Janshi tayi zuwa ga abinda ta shirya mai, tana bashi a baki yana zuba mata shagwaba, da wasa da wasa kuma ta rabashi da coat dinshi, belt da takalmi wai dan kar yaje aiki,

"Su Wifey meh akeso ayi min neh yau, naga kin kasa aje hannunnki wurin ki"
Kunya taji ta kauda kai,

"Ka zauna a gdan manah sai ka gano" ta kashe mai ido daya, idanu waje yake bin bayanta da kallo data tashi,

Through out the day beh je ko ina bah, sabon shafin soyayya suka bude kaman saurayi da budurwa,

Duk abinda yakeyi na tanadin abinda zeyi mata anjima neh, ita kuma ta dage ta shirya harda shan abubuwan tsiminta dasa sexy night gown, dan tasa a ranta za'ayi wasan dare,
Ta rigashi kwanciya, daya zo sai ya kashe fitila kawai yayi kwanciyar shi koh inda take beh kalla bah,

Yana jin duk motsin da takeyi da yanayin yadda take fidda numfashi, har zaune ta tashi ta shiga bathroom sannan ta dawo ta kwanta,

Cije lebenshi na kasa yakeyi dan kar dariyar shi ta fito tasan idan shi biyu,
Daina jin nishadin yayi daya lura da gaske a takure take, kuma taki yin abinda yakeso, watau ta fidda kunya ta nunamai tana bukatar shi,

Ajiyar zuciya yayi sannan ya tashi zaune, fitilan gefenshi ya kunna, dunkule ta wuri daya sai numfashi take fiddawa sama sama,
"Husna" ta bude ido kafin ta ansa mai,
Alama yayi mata data tashi zaune, haske beh wani gauraye dakin bah, amma saida ta jawo bargo tana rufe santala santalan kafafunta dake bayyane,

"Wifey akwai abinda nakeso in fada maki"
Tace uhmmm tana jan kafafunta zuwa kirjinta,

"Kin ganni koh wifey, in ina son abu i take it"
Ya dan jira yaga in ta kama hanyar inda zancen nashi ya dosa,

"Akwai abinda kike bukata koh?, kina bukatar Mijinki" bata karyata bah,amma kaman kasa ta tsage a inda take, koh kyaftawa takiyi balle ta dago da kanta,

"Bamu jima muna biya ma juna bukata bah wifey, amma har na karanci komai gameh da ke" matsowa yayi ya rike hands dinta,
"Karki dauka banjin dadi neh, saidai ina so in tabbatar da jirgi daya muka hau kuma muka sauka"

Dama beh sa riga bah sai ya dora hannayenta saman pecs dinshi,

"Ina son inji kina tabani, inji hannayen ki a ko ina na jiki na dan ni mallakin ki neh kiyi yadda kikeso dani"
Bata saki jiki ta maida kirjin shi allo bah hannunta kuma chalk,

"In kika kira sunana sai in rasa duk self control dinah, a hada da dan tabani da kikeyi Husna it drives me wild"

Rigar datasa meh siririn hannun ce, sai ya sabule su daga jikinta, take rigar tayi kasa wurin kugunta, hannu tasa zata kare kirjinta,

"Na yaba kuma ina son abinda na gani, in kika kare kanki daga idanu na wifey bakiyi min da kanki adalci bah"
Sauke hannayenta tayi kasa ta bashi full view din abinda yakeso, dago da fuskarta yayi suna kallon juna, kasa cigaba da kallon shi tayi,

Sarrafa kirjinta ya fara da hannu da baki, saida ta fara amsar sakon abinda yakeyi sai ya tsaya chak,

"Kina bukatata a daren nan wifey" ya sake tambaya har sau biyu, da bata ansa bah sai ya juya mata baya ze kwanta,

"Am sorry, pls" ta fada numfashi na sama sama,

"Ina bukatar ka mijina, kishir ruwan da kai kadai zaka iya kashemin"
Juyowa yayi a sannu yana kallonta kafin ya jawota saman shi,

"Meh ze hana ki karbi abinda kikeso" ya rada mata a kunne,
A hankali ta fara kissing dinshi a baki,
"Nasan kina son fiye da haka" data daga mai kai sai ya kashe fitilan daya kunna, iya kar kwarin guiwwan da take bukata kenan, bayan ya kashe fitila sai ta fara abinda take so, a daren ita ta zama pilot kuma ta gano tana san hakan,

"I love you so much my heart beat" fuskar nan ta haska, duk sai murmushi sukeyi mah juna,

Labari ya canza da garin Allah ya waye ta sha after pill dinta, ciwon kai ranar harda amai taji yana taso mata,
"Sannu Husna" ya duka yana dan shafa mata baya, ita kuma sai kwarara amai takeyi, saida tayi aman ta samu sauki,

"Dan Allah mu koma gda" koh baki bata dauraye bah ta fara kuka tana rokon shi ya mai dasu gda..










⚜B.W.AπŸ–Š
[5/11, 19:27] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š





πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
Story and writing
NOBLE JUDGE,
Editing by
KHALEESI.



6⃣0⃣.




Abin hannun shi ya kalla sannan ya kalleta kwance saman gado,

Cikin jirgi da suna dawowa gda yaga ta dukufa tana ta rubutu a cikin wani littafi meh brown leather cover da igiyar daurewa,

"Meh kike rubutawa?" Kaman ya san baxata fadamai bah, saita daure littafin kawai tana murmushi,

A lokacin yayi magana da Alfie ga meh da Admission din daya ce ya neman mata a A.B.U,
Beh san dalilin daya sa beh iya ganin tana son abu beyi mata bah,
Ga Admission letter din a hannun shi, ba nata bah ma ita kadai harda wannan kawar tata da suke yawan magana a waya,

Yasan ba karamin farin ciki zatayi bah in ta gani, saidai shi yana kokwantan bata, yana jin kaman ya nema mata wani makarantar a Abuja maimakon Zaria,

Fitowa yayi daga dakin da admission letters din cikin envelope, jiya mah da ciwon kan ta kwana, kuma hakan ya tabbatar mai da zargin da ya tsinci kan shi dayi, na sai ya kusanceta take ciwon kai,
Tun da suka dawo batayi bah sai jiya, yan awowi kadan bayan sun gama faranta ma juna rai,


"Mom yau Dad ze dawo fah" ta gaban shi tabi ta wuce cikin sauri, kanshin turarenta neh mah ya dawo dashi daga duniyar tunani,

"Nasani Ehsaas, meh yasa kaga nake ta sauri haka, badan inyi in gama abubuwan da nakeso bane bah kafin ya zo"
Zata tafi yayi saurin binta,

"Toh Mom fadamin abinda kikeyi sai in taimaka maki, bana da wani aiki dayawa a office" wani murmushi tayi meh nuna isa,
"Don't worry My son, ina dealing da wasu mutane neh, karka dade a office kaji"
Tayi gaba yana binta a baya,

"Mom kinyi bako" ta tsaya har Mom tace toh kafin ta koma kitchen dan cigaba da dafa abinci,

"Tana zuwa" ta aje mai ruwa da juice
"Mijin ki fah?" Ya tambaya daga tsayen da yake, hakan sai ya tuno mata da wani data sani,

"Yana wurin aiki" ya daga kai sau daya, sannan ya harde hannuwa a bayan shi,

"Har kun fara zuwa daya bayan daya koh, ni ba ku nakeson gani bah"
Hannayen shi harde a bayan shi, fuskan nan kaman beh taba murmushi bah,

"Ka zauna manah kai ai bah bako bane bah" bece komai bah sai tayi yar dariya

"Badai turoka tayi bah"
Saida ta zauna sannan ya fara magana,

"Baki san illar abinda kikeyi bah, kuma baki san abinda ya faru bah,
Zan maki uxuri saboda wannan dalilin"
Tayi mai kallon up and down,

"Banda lokacin yi maka barazana, dan kai ba sa'an yi nah bane bah, da uwarka nake son yi"
Ajiyar zuciya yayi sannan ya taka zuwa inda take,

"Saida kika sa mahaifiya ta kuka yau, ba abinda kike tuhumarta da yi yasata kuka bah, abinda tayi a baya yasata kuka,

Kuma banji dadin haka bah, dan haka zan hada ki da Allah karki yi abinda zakiyi regretting har karshen rayuwar ki"
Bushewa tayi da dariya,
"Ka san meh regret yake nufi kuwa,
Abinda zanyi nadama akai shine in kyale wannan matar, banda wulakancin da bakin cikin data cusa min harda mahaifina ta kashe"
Da sauri ya katse ta,

"Baki da wani proof din itace, kuma am warning you ki kyale mahaifiyata alone"

"Shikenan Amyr
tunda bazata fito face to face ta fuskan ceni ba zamu hadu a kotu, karshen satin nan neh shiga ta farko koh,
Data rufa ma kanta asiri munyi abinnan mu biyu, amma sai ta zabi in fallasata kowa na duniya yasan ita ta kashe mijinta"

"Meh?!!!!" Da sauri sauri Hajia ke saukowa daga stairs

"Meh kika ce?"
Beh kalli hajia data shigo bah sai magana daya cigaba,

"Ban so bin ta wannan hanyar bah, amma baki bani wani zabi bah, duk abinda ya biyo baya ke kika jawo, karki manta da haka,
In baki yadda bah ki tambayi Raees yasan ni fiye da kowa a duniyan nan, i don't give idle threats, i pay my debts in full"

Sai kuma ya juya ga Hajia ya gaisheta da Fara'a kaman ba shine ya gama magana bah,

Daya shigo ta kalleshi sai taga kaman yayi kuka, hmmm tace,da itace taga mahaifiyar ta na kuka itama ai zatayi kukan koh,
'Wai meh Mom keyi neh, bata taba neman ma kanta abokai sai makiya'
Hmmmm ta sake cewa ta cigaba da aikinta,
Koh minti biyar ba'ayi da tafiyan Amyr bah sai ga Dad,

abinda ya katse tambayoyin da Hajia keyi ma Mom kenan,

"Komai lfy dai koh naga kaman na katse wani abu dana shigo" Murmushi sukayi mai kafin Hajia tayi gaba, ita kuma Mom ta tsaya wurin shi,

Saida ta gama duk abinda takeyi kafin ta baro kitchen, lokacin har yayi wanka yana hutawa,

"Ya jikin ki daughter?" da fara'a tace Alhamdulillah

Tafiya tayi ta gaya ma Mom ta gama dan taje tayi serving mijinta da kanta,


Tana shiga daki taja wayarta, text din kalamai masu dadi da karfafa guiwwa ta tura mai sannan ta fadamai baban shi ya iso,

'Kaman kin san text dinki nake jira , ina kan hanyan dawowa,
P.s karki manta da Hug da kiss dinah, ina binki bashin na safe ga na yanxu'
Dariya tayi tana fadawa saman gado,
"saidai ka cigaba da bina bashin dan Dad na falo bazan je inyi rashin kunya bah"
Ta karasa da murmushi tana sake karanta text din,

"Wifey" da sauri ta tashi zaune,
"Ina falo kizo ki bani sannu da zuwa ta" da gudu ta mike ta isa bakin kofa shi kuma ya juya ze koma falo,

"Hubby sannu da zuwa" kafin ta karasa ya juyo

"Allah baki isa bah, sannu da zuwa meh" ya hura mata kiss 😘 sannan yayi hugging kanshi πŸ€—,

"Shi nakeso" ya juya da sauri yana yin kasa,
Kofar shigowa yaje ya tsaya,
Ajiyar zuciya tayi ta taka cikin sanda kaman barauniya tana labewa dan kar wadanda ke dining area su ganta,

"Rashin kunya kiri kiri" in ji Mom,

Dariyar Dad neh yasa tayi saurin ficewa daga wurin,

"Kaga ahinda ka jawo koh cuddly B, yanxu zasu ce banda kunya"
Ta harde hannu a kirji bayan tayi hugging dinshi kuma tayi kissing dinshi,
"Guda biyu nake bin ki" bata ankara bah taji ya jata jikin shi yayi kissing dinta,

"Kuma dama nayi daring dinki neh in ga in zaki iya, am impressed matata na sona sosai"
Tayi mai kallon da wasa neh,

Daya shiga wanka sai ta sauka kasa ta kwaso better din data hada dan shi kawai,

"Hmmmmm" cin abinci kawai yakeyi yana mata santi


"Ya office din yau" ya dan daga kafada yana cewa Alhamdulillah,

Ya saba cewa Alhamdulillah kawai, bayan wani lokacin sai taga kaman beji dadin aiki bah ranan,
Kila yadda take tambayar neh yake sawa bata samun ansa gamsasshiya,
Duk surutun shi amma ya tsaya a Alhamdulillah kawai, dan tunani tayi kafin tayi magana,

"Meh ya faru a wurin aiki yau, wa ka kora" tsayawa yayi da cin abinci bakin shi dan karkace,

"Ka kori wani bawan Allah koh?" Sai yayi yar guntuwar dariya,

"Ban kori kowa bah, amma na kusa" ta bude baki alamun mamaki, nan ya zauna ya bata labari in details har na wasu ranakun da suka wuce, labarin beh wani daukan hankalinta, amma yadda ta tattara duk hankalinta ta bashi sai kace Novel take karantawa,

"Wifey" tace uhmmmm


"Zanje wani wuri da Dad yanxu, amma in na dawo ki tunamin akwai abinda nakeso in fadamaki"

Ji tayi gabanta ya dan fadi, tsari ta nema sannan ta daga mai kai,

Throughout yinin nan bata sake bah, data dan fara sha'anin ta sai ta tuno yace ze fada mata wani abu, gashi basa dawowa sai bayan isha,

Wanka tayi tasa kayan baccinta dataga har dare ya danyi basu dawo bah,

Mai da turare ta shafe jikinta dashi kafin ta jawo collection din lipstick dinta, tana shafawa tana gogewa, harda hada kala biyu koh uku,

Bude kofan dataji neh ya tadata daga abinda takeyi,

"Kinyi kyau" yasa yatsa yana shafa lips dinta,
"Da gaske" yace uhm hmm
"Nagode, yau ya akayi kuka dade" ya dan dafe kai,

"Wurin Haider naje naga Angel dinshi" murmushin yake tayi sannan tayi mai jagora,
"Nima ya kamata in je in ganta" ya daga kai yana cewa haka neh,

"Na manta nace zan fada maka, akwai ranar dana je wani shop na kashe kudi sosai" tayi magana tana dan wasa da yatsun ta,

"Kaman nawa kika kashe" ta dan dora hannu a baki, kafin ta sosa keya,
"Nikam na manta nawa neh" bayan ga amount din tana hangowa baro baro a jikin receipt,

"Ba dayawa bane bah kudin tunda har kika manta, besides ya kamata in dinga baki allowance, monthly kike so kaman salary koh duk sati"
Ahmmmm tace kafin tayi magana,

"Sai ka dinga bani kudi?" Ya daga mata kai,

"Saboda kiyi wasu bukatun ki koh" a sannu ta daga kai,

"Zanyi magana da Alfie dan yayi arranging komai"
Dakin canza kaya ya shiga,

"Hubby kace in tuna maka zaka fadamin wani abu" dan juyowa yayi ya kalleta kafin ya cigaba da sa kayan shi,

"Da har ina murna kin manta, ashe kema abin na ranki kaman yadda yake nawa" ta daga kai duk da beh juyo bah,

"Gashi keh da kawar ki, da kun fara zuwa nima zan koma can da yin aiki"
Yana gama gaya mata abinda sai ta karanta paper din cikin envelope din daya bata zata fahimci zancen shi, sai tunanin shi ya koma ga mahaifiyar shi,

Yasan in ranta yayi dubu sai ya baci in taji ya zabi yabi Asma'u in da takeso daya tsaya a nan Abuja,

Beh ankara bah yaji an kankame shi,

"Tnk uuuuuuuuuuu, ina sonka sosai My All"
Ta koma ta zauna tana sake karanta offer din admission din da aka bata,

"Inna lillahi harda Ma'u" harda tsalle a zaune tana yar kara,

"Na fada maka ina sonka sosai kuwa" ta kara makalkaleshi tana fadin i love you da karfi,

"Bari in kira namecy in bata good news, Mama zan fara fadama wa" ta fara yunkurin mikewa,

"Ke! Slow down dare yayi ki bari sai gobe" yana jin yadda excitement ya hanata zama wuri daya, kaman an dura mata karfi a jikinta sai bari takeyi,

"Farin cikine ya mamaye ni Hubby, tnk uuuuu" ta kara rungumeshi sanna ta lalubi bakin shi dan bashi lafiyayyen kiss,
Jawota yayi ta zauna saman cinyoyin shi, ita kuma ta zagaye wuyanshi tana cusa hannunta cikin gashin kanshi slowly, kafin ta rage wutar kiss din shima tanayi slowly, bata bashi daman taba harshenta da nashi, sai wasa takeyi tana shafa shi a hankali,
Shima daya ji hannayenshi sun fara bin umarnin da ba nashi bah suna kokarin rabata da kayan jikinta sai ya tattaro iya karfin shi ya tureta gefe,

Yana kallo lokacin data bude idanun ta cike da mamaki, batayi magana a take bah sai data bude lips dinta dake sheki ta shaki iska sosai kafin tayi magana,

"Ya akayi?" Ta dan jinkirta kafin ta cigaba,
"Nayi wani abu bah daidai bah, koh na takura ka"
Saurin girgixa kai yayi,

"Bazan taba gajiya dake bah Husna,safe, rana, dare any time, amma"
Ya raunana muryar shi,

"Na lura da lokacin da kike ciwon kai, baya zuwa sai na kusance ki tukunna, ina ga hakan matsala neh kuma beh dace in zama sanadiyar,___ wifey ina zaki je?"

Wayarta dake saman gado ta tsaya dauka kafin ta fada bathroom,
Ranta na gaya mata dalilin ciwon kan nata, bata yadda bah saida ta karanta side effects din maganin da take sha,
Dora hannu tayi saman bakin data bude,
'Meh nakeyi mah kai na ni Asma'u'
Saura kadan ta fashe da kuka,

"Asma'u open d door"
"Husna!"
Goge hawayen da basu zubo bah tayi kafin ta bude kofa,

"Am sorry My All, babu abinda nake yi maka sai matsala da nake jawo maka"
Janta yayi ya rungume,

"Ya za'ayi kice haka wifey, kin san ni bana ja baya, duk matsalar data kunno min kai sai na magance ta da izinin Allah"

Kwantar mata da hankalin daya cigaba dayi shi yasata kuka,
Tana yaudaran bawan Allah dan taga yana mata so matsanaici,

"Angel eyes" a sannu ta bude idanun ta sauke kanshi,

"Akwai hanyoyi da dama da zan iya biya maki bukatar ki" murmushi tayi mai tana girgixa kai,

"Am good" harta rufe idanu kuma ta bude a hankali,
"Ban san kai koh kanada wani agenda bah a ranka" lokacin taga ya dace ta gwada hanyoyin data karanta da take ganin baxata iya bah,

He was speechless data yi maganan nan, data aiwatar kuma he was dumb, kaman beh taba magana ba haka ya koma,


Side effects din maganinta ta karanta kafin ta zauna tana tunani,
Abinda yafi damunta shine ji da takeyi a ranta itama bata son ta dauki ciki lokacin, kuma in ta tuna da fuskar mijinta in yana magana akan baby,da irin hope din da yake dashi sai taji dama tana da ciki,

Banda wannan mah, bata san illar da shan maganin nan kusan kullum ze iya yi mata bah, ance mutum ze iya sha bayan kwana biyar da saduwa, amma yafi aiki in ka sha kafin kwana uku,
Kuma taga wani rubutu, inda ake tambaya in akwai matsalan shan maganin wata daya a tsakani,

In masu sha bayan wata dai daya na ganin akwai matsala toh ita fah,

Gaban madubi taje ta daga rigarta tana kallon cikinta,

'Kar wani buri naki ya kaiki ya baro ki Asma'u, duk san da yake maki, kika kasa bashi yara ze iya sallama maki, koh ya auro wata'
Tsaki neh yazo mata, wata zuciyar na cewa,

'Toh bah abin kenan bah, ya sallame ni, kuma koh na bari cikin ya shiga ai Mom wani aure zatayi mai koh, sannan ta maida mu doormat, ta taka in zata fita kuma in zata shigo ta takamu san ranta,
Gwara salin alin, in koma gdan mu'

Mayar da rigarta tayi yadda take sannan ta shafa lipstick,

Das das take takunta da wani confidence dan ta kara tabbatar da meye KUDIRIn ta,

Chak ta tsaya tana jin hayaniyan mutum biyu,

'Har karshen satin yazo kenan' ta fada ma kanta da taji ana maganar kotu,

"Wai meh yasa kuke kareta neh, zan iya understanding in Amyr ya kare mata,amma kai meh ka hada da ita, ta sanadiyyar ta neh ka rasa mahaifin ka"


Please Login or Register in order to submit comment