Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace you need a new phone,
"Zan dinga haduwa da manyan mutane, my PA can't be seen holding that" ta dan ji zafin abinda yace amma ya zatayi

"That reminds me,you have an event to attend tomorrow, your Mom's secretary informed me yesterday"


"Ahhhhhhhhh am here on vacation Mom" kaman tana gaban shi ya fada da shagwaba


"Don't think i didn't hear you, you called me sir twice now say my name 20 times"

Fuskarshi dauke da murmushi ya fada kaman wani game sukeyi wanda shi ke taci

Driver ya katse ta daga fadan sunan shi,ta hanyar cewa sun iso phone galaxy


"Husna choose" ya fada bayan sun zagaya shop din ya dauko wasu guda uku da sukafi yi mai

Kowanne da tag din kudinshi a jiki,kuma babu wanda zata iya affording a ciki

"Sir" ya bata rai
"Can i choose one for myself" bayan dan lokaci ya daga kai

Irin wayar da aka bata kyauta ta dauko,tace ita take so

Karba yayi ya juyata sannan ya aje
"Do you have a Mac book pro?"

Ana kawowa ya hada yace a sama su cikin leda

" Husna this is the part where you pay" ba karamin faduwa gaba tayi anan tsaye bah

'Pay,ita ina taga kudin OH!' Da kudinshi tunda dama komai sai an biya mai


ATM din taciro daga wallet dinshi tana ajiyar zuciya,lokacin shi kuma kallon wasu abubuwa yake yi

"Plus this" ya dora headphone beats wurin biya

"And this" ya dawo da simcard prepaid

Meh karban kudin mah daina cire kudin yayi yana jira dan yasan ze iya kawo wani abu

"This too" ya dora phone pouch da wireless keyboard

"Dan Allah ka cire kudin komai kuma kafin ya dawo" mutumin ya noke kai alamun Aa, tunda suna samun ciniki

Wurinshi taje lokacin yana neman power bank

"Pink one koh" yana dauka sai ta karba

"We have to leave now so i can prep you for tomorrow's event"


⚜B.W.A πŸ–Š
[3/9, 10:59] β€ͺ+234 706 870 0853‬: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



1⃣5⃣.



"That's enough you have to be there tomorrow and that's final" tashi yayi ya shiga dakinshi ya barta nan zaune


Zama tayi tana fadamai abinda za'ayi a wurin event din da kuma irin mutanen da zasu halarci taron

Banda wannan ita zata dinga binshi a baya tana radamai sunayen mutanen daze gaisa dasu sannan ta fadamai aikinsu da kuma sunayen iyalin wanda yake magana dashi

Da farko ta zata PA dinshi Alfie yace tayi haka ne kawai dan baya santa, amma data fadamai sai yace eh haka abin yake


"Pls i can't come here tomorrow, gobe weekend ne fah" ya juyo da murmushi

"You don't have a weekend, whn i work you also have to work"

Zatayi magana ya rigata

"That's why i pay you guys generously, to compensate for any inconvenience i might cause you"

"Kuma sai akace dan kana da kudi sai ka zauna komai sai anyi maka,sunayen mutane mah baka iya rikewa bah" ta fada da hausa tana kallonshi


"What did you just say" tayi kasa da kai kawai tana duba list din mutanen da aka gayyata

"Husna am talking to you" ya fada yana karasowa inda take


"I said how much is my pay, I've been working and i don't even know that" sai da ya dan kare ma face dinta kallo duk da ta dukar da kai kaman beh yadda da abinda ta fassara mai bah

"How much will you charge?" Ya zuba mata idanu yana jira ta dago

"Husna?" Ya dan hada yatsa kusa da face dinta


"I don't know, I'll ask Alfie how much you pay him" ya dan jin jina kai

"You should tell me if you need a rise, okay" kafin ya tashi ze tafi

"I should go home and study this" ta fada tana mikewa dan rike sunayen mutane da brief history dinsu ba Karamin abu bane bah


Dawowa yayi ya zauna saman kujerar dake kallon nata

"Bari a kawo manah abinci muci sai ki cigaba da gayamin abinda ya kamata in sani" ya fada da turanci


Duk da taso tafiya,sai ta zauna dan gwara a gama yanxu da gobe ta dinga binshi a baya tana rada mai abubuwa

"But pls come tomorrow, I'll be a mess at the event without you" ya tambaya murya kasa kasa yana hade hannu wuri daya

'I can't go a day without seeing you Husna' ya fada a ranshi bayan ya rakata har cikin mota sannan ya koma hotel din


A dakin yayyanta ta baje musu abubuwan daya siya mata na aikinta

Rada ma juna abu sukayi sannan yaya Abba ya kalleta

"Kin dai fadamai kin kusa aure koh"
Gefe ta kalla kafin tayi magana a hankali

"Ina ruwa na da wani aure,shi kuma ina ruwanshi da ni" Suka girgixa kai tare

"My naive little sister" inji Mukhtar

Bata kawo komai a ranta bah ta tattara yanata yanata tayi gdansu Ma'u



"Yanxu haka zance babu necktie kenan" ita dai tana tsaye gefe

Jiya da dare PA dinshi ya turo mata email, wai na wani boutique a inda suke dake saida authentic designers,

Aikinta shine taje ta siyo mai kayan da zesa gobe zuwa events din

Daga kan takalmi,suit ,harda underwear saida ya turo mata size dinshi wai ta siyo, sannan silk socks, tie, cufflinks da brooch

"Am sorry ni ban san yanda ake daurawa bah" ta fada da turanci

"Video call Alfie" nan ta kirashi sannan ta daga wayar ana koya mai yadfa ze daura tie din, karshe ita ta aje wayar ta daura mai tunda ba saba yin abubuwa yayi bah,



Kallonta Kawai yakeyi tunda ya shiga motar,yana so ya gano ya akayi daga jiya zuwa yau ta kara kyalli da haske, ( dilkan kwana biyu ya fara aiki)

"We should go in together" ana aje su a harabar hotel din ya fadi haka,

Ita dai iyakar saninta a events dinnan da wuya kaga mutum da hijab,ita gata hijab ne jikinta,kenan data shiga kallonta za'a hau yi


"Can i please stay here,am not dressed for an event" ta fada kaman zatayi kuka

"Here,take this with you" ta bude mai email din da aka turo mata na sunaye da kuma hoton mutanen dake taron

"Okay" ya karba

Koh minti goma ba'ayi bah sai ga call dinshi ta sabon simcard din daya siya mata

"Can you please come,am getting confused" wayar hannunta ta aje sannan ta fita bayan ta ja dogon numfashi

Sanye take cikin dogon hijab har kasa meh hannu da hula, brown color meh dan haske yadin tiyobo,yasha guga neat da ita,takalmin kafanta flat kawai ake gani

Kaman ta san zatayi turning heads in ta shiga hall din da aka kayata da decoration golden da black


A hankali take tafiya koh gabanta bata kallo kanta kasa, har saida ta isa tsakiya sannan ta dan dudduba wurin

"Am here" shi da kanshi ya karaso wurinta yana mika mata wayar data bashi

"Lets go" yayi murmushi sannan yayi gaba, da sun nufi wani dan su gaisa saita fadamai abubuwA kafin ta barshi yayi gaba ita ta tsaya baya


Bayan ya gaisa da kusan duk wanda ya dace sai ta koma gefe ta barshi yana hira da jama'a, tana ganin drinks ana yawo dashi amma tsoro ya hana tace a bata daya,


Hannu ta dan daga ma wani daya zo wucewa da drinks a tray,sai yayi kasa dashi ta dauki colorless drink daya

"Tnk u" ya dan daga kai kafin ya wuce,tana kaiwa baki zata sha aka katse ta

"Kin san meye wannan?" Ya matso kusa da ita

"Water" ta ansa dan kar tayi tsaye haka nan kaman wata sokuwa

"Are you sure" ta kara kallon glass din,taga koh bubbles babu a ciki, shi kuma abin hannunshi dark brown ne ga kankara aciki

"Excuse me" ta fasa sha taba wani usher ya wuce da shi

Sai mutumin ya hau dariya har yana sa mutane suna kallon su
"Ruwa ne" ya fada cikin dariya, ba shiri ta matsa daga wurin mutumin


Tana gaba kuma sai ga wani shi kuma da champagne flute cike da drink meh color lime green

"Meh beautiful girl kaman ki keyi anan, har classless ppl na magana dake"


'Wai meke faruwa ne, whats happening' ya tambayi kanshi daya ga kaman jira ake wani ya tafi ayi magana da ita


Cire kanshi yayi daga hirar da akeyi ya nufeta kai tsaye

"Excuse me,i need to talk to her"
"You know this guy" in ji wanda ke tsaye kusa da ita

Bata bashi ansa bah ta danyi gaba,sai da tajo takunshi a bayanta kafin ta tsaya

"Am going back to the car"
"Better, didn't you tell them you are taken, your husband is very jealous man,tell them that next tym"
Saida ta daga kai ta kalleshi, kenan yasan aure zatayi

"Wait for me in the car,yanxu zan fito mu tafi"


Ya sha ganin mata cikin mini skirt da halter tops,in fact irinsu ya saba gani,dan eligible bachelor kaman shi mata tururuwa sukeyi mai kowa na nuna irin nata zakuwar da zama matarshi,

Babu wacce ta taba sawa yaji kishi kaman yadda yaji yau, abin mamaki ya bashi dan in banda face dinta da yake ganin glimpses sai tafin hannunta dayake gani

Amma ace wai akanta yake ji blood dinshi na boiling,
Gefenshi ya kalla inda take zaune a takure jikin marfin mota,


In yaga kunya a fuskarta har wani nishadi yake ji,dan ado ne da beh saba gani bah

Ganinshi wannan hijab din da take sawa kyauta ne takeyi mai,saboda shi kadai ze iya bude kyautar

'Oh God,am in heaven' ya fada da tsan tsan farin ciki

Sai kuma murnar ta koma ciki, gobe sunday baxe ganta bah,
'No i have to see her' ya fada yana kallonta

"Gobe zanzo in gaishe da grandmother dinki" dan dagowa tayi amma bata kalleshi bah

"She won't be around,we are going out" beh dauketa a matsayin meh karya bah dan haka ya yadda yana ji dama ze iya jawo tym zuwa monday



"You have to open an account" ya kirata office yana fada mata bayan ya so ganin account balance dinta tace bata da account


"I don't need it Sir" ya kalleta ta gefen ido, ya dade yana kallonta ko zata dago,a iya aikinsu tare ze iya kirga lokutan daya ga kwayar idanta

"Hunsa am waiting here" ajiyar zuciya tayi ta tashi tsaye


'Mutum ba abinda ya iya sai san turasasa ma mutane suyi abinda yake so' dan murmushi tayi ba tareda ta kalleshi bah taje ta karbo abinda take bukata


Yau take san yin resigning dan gobe Saturday, har lokacin aikin data daukan ma kanta ya kare,shi yasa zatayi abinda yakeso dan su rabu lfy


"And am going to take out my pay today" ta fadamai

"You see!" Ya fada kaman abin kirki yasata yi
"you need an account to be putting your earnings" ya jawo paper din data kawo


Da yake shi yasa sai gashi an gama komai har ATM card an bugo da name dinta

"Tnk u sir" ya daga kai yana smiling
"Yi fast transfer dinki" ya bata order

BlackBerry din daya bata ta dauko ta farayi dan har ta saba mobile transfer

"It's done"
Yayi shiru na dan lokaci yana jiran yaji ping din alert ya shiga wayarta


"Ba wannan number din na bude account dashi bah" ta kwashe duka abubuwan daya siya mata daga cikin bag dinta tasa cikin leda


"Why are you doing that" ya tambaya

Ita dama tasan yana ganin abinda takeyi,koda kuwa beh dauki hankalin shi bah dan kullum kallonta yake prey da predator


"Take this" ta mika mai resignation din data zauna ta rubuta da hannunta


"Your hand writing is very good" yayi scanning letter din ba tareda ya karanta bah

"Read it then" ya maido mata,ajiyar zuciya tayi dan tayi expecting haka

Daga paper din tayi tana rufe face dinta zata fara karantawa

"Ah ah, take away from your face" ya fada kaman ta hanashi wani abu dayake so


"It was really a pleasure working with you" ya washe hakora 😁

"But it has come to an end" ya bata fuska😟

"This is my resignation letter" ya yi yar dariya

"Are you speaking in that language again, because i don't understand what your saying" shima wannan accent din dataji a farkon haduwar su ya dawo muryar shi


"If your worried that you won't be able to do anything by yourself you can ask your driver he's educated"
Tana juyowa taga kallonta yake rai bace ga baki na hanging open😲

"Did you just say i can't do anything by myself?" Ya fada rai bace

"Ba haka nake nufi bah, but it's true you need ppl to do stuff for you, drive you, pick out clothes for you, buy things for you, answer your calls, you might be paying them buy you need them"

Mikewa tsaye yayi ya kwace phone dinshi

"I'll show you that i don't need any of you" , ya kwace wallet dinashi har yana tsoratata

"Any of you" ya karacewa yana pointing dinta
"Go ahead leave you are already fired" tasan ba bacin rai bane bah matsalar girman kanshi ne, watau taji ma ego dinshi ciwo

" Hmmmm" tace kafin ta fito da ledar dan ba driver, tsaye ta ganshi shima a waje ba mota

Lallai ya dauki abin da girma,ta fada a ranta sannan tayi tsaye dan ta tabbata sai ya dawo yace yana bukatar su.



⚜B.W.AπŸ–Š
[3/9, 11:00] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSO πŸ–Š



πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Godiya ta musamman ga masu san karanta littafin nan, saboda kune nake typing duk lokacin dana samu time, tnk u and happy reading.



1⃣6⃣.



Tafiyar shi ya bata daman zuwa ta cire duka kudin aikin da tayi daga bank, taso barma driver duk abubuwan daya siya mata amma sai ya nuna mata bazeji dadin bah


Garin yawon da yakeyi yazo inda aka tare hanya, dama kuma yasan ya dade da bacewa, kawai sai ya yanki corner din dayaga ana bi


Sallah ya tsaya yayi a inda yaga an jera sahu har gefen titi tunda friday ne kuma suna da prayer mat a bayan mota


Yana komawa cikin motar ya dora kanshi saman sitiyar, ya fara jin yunwa gashi beh taba tukin daya kai awa daya bah,duk hannuwanshi sun gaji


Beh san yana cikin matsala bah saida yazo wurin shan kwana motar shi ta tsaya, abin mamaki ya bashi dan ana kula da motocinsu sosai


"Unbelievable, empty tank" bugun sitiyari yayi da hannunshi sannan ya dafe,


Ya fita daga motar yana murmushi dan yasan sunan hotel din da suke zama


Kasa tare abin hawa yayi dan beh san abinda zeyi bah, Allah ya taimakeshi wani yazo wucewa


Rokon mutumin yayi daya kaishi hotel din ze bashi koh nawa ne


"Money first" inji mutumin dan ya ganshi a hargitse,

"Money" ya fiddo wallet dinshi sai ya duba yaga kudaden waje ne a ciki,amma ga ATM's dinshi nan ai


"How about you take me to the bank first"
Mutumin ya nuna mai wani hanya yace ya bi wurin akwai banki shi yana nan yana jira


Daya bayan daya ya dinga zura ATM's din, saidai ya turomai dan beh san pin dinshi bah, duka ATM's din saida aka kulle su

Komawa yayi wurin motar yaga mutumin ya tafi, kaman ya sake yi ma wasu mutanen magana kuma ya fasa dan ba amfani


Kicking tayar motar ya hauyi saboda haushi, bayan yayi mai isarsho sai saukan zafi, komawa yayi cikin motar ya fiddo wayar shi


"You win, bazan iya yi ma kaina komai bah, i need you so pls come here" ya fada cikin muryar ban tausayi




"Were are you?" Ta mike ta bar inda ake kwaba lallalen da za'a zana mata

"I don't know" sign boards tace ya duba har ya gano address din inda yake


"Namecy naga kina sa takalmi" tace yi hakuri ina zuwa


Dauko jakarta tayi daga daki sannan ta fita ta tare abin hawa


Driver din na nan banki inda ta barshi, nan tayi mai bayanin inda yace mata yake da kuma man daya kare a mota


"Kina nufin bazaki ce komai bah" ya tambaya da turanci dan tunda sukazo cikin napep yake jira tace
'Dama nace you nees us'

"Sauri nakeyi ana jirana a gda" dingishi yayi ya shiga dakinshi

Bowl ta dauko ta debo ruwan zafi daga bathroom ta hado da towel, sannan ta nufi living area

"Am glad kina nan har yanxu" ya taho da kafa daya sama


"Sit here" ta nuna mai wani side stool ya zauna sama


"What will you do?"
Zaka gani ta fada da hausa,sai ta tsoma towel din cikin ruwa sannan ta dan dora saman kafarshi da yake dingisawa


Saurin dauke kafar yayi yana fifitawa

"Ya kike managing kisa hannun ki ciki"

"Sauri nakeyi" dawo da kafan yayi kasa, ita kuma ta cigaba da gasamai a hankali


"Nagode Asma'u, kuma daga yanxu zan zama oga meh kirki" ya fada yana kallon yadda take aikinta


"Dan Allah ki dago in ga eyes dinki" mikewa tayi taje ta zubar da ruwan sannan ta wanke towel din ta shanya


"Zan tafi Sir" ya dan langwabe kai

"Gobe Saturday fah, ya kamata kizo aiki" daga mai kai kawai tayi sannan ta fita tabar jakarta acan.

Sai bayan sunyi isha sannan meh kunshin ta hau zanzara mata a hannu da kafa,

Kafin a fara shafa mata red mah tayi bacci abinta



Rakube take jikin bango kaman tana so ta shige ciki, da yayi magana sai taga kaman kara matso ta yakeyi dan haka ta kara matsa baya tana manne da bango


"Asama'u kaman ba dan uwanki bah, ko dan wannan kin dan saki jiki ki min magana"
Uhm tace can kasan muryarta sannan ta sake matsawa baya


Inna lillahi wa inna ilahir raji'un ya fito daga bakinta ana dauke wauta, ko ina yayi dun dum kuma yayi shiru


Tuno inda take tsaye kuma da wa sai tayi saurin juyawa zata koma cikin gdan kaka


Rikota yayi ya manna da bango

"Zancen yau da armashi yake,tunda har da yar kyauta zan samu yau" ya fada yana kokarin cire mata hijab


Bude baki tayi tana so tayi ihu sai ya daura hannunshi saman bakinta


"Haba Asama'u kar muyi haka dake manah, dan na tabaki ai ba komai, tunda aurenki nakeso nayi"

Ta fashe da kuka tana kiciniya dashi

Har kaka saida ta kira duk da ya toshe mata baki

"Koh kaka baxata hana bah tunda tasan gdana ne ze zama wurin zamanki" ya fada da dariya

Ba karamin kokowa sukayi bah kafin ya rabata da hijab din jikinta,
Lokaci daya kuma ta daina jinshi yana gogar jikinta da nashi

Sai wani ihu da yayi, itama tsoro yasa ta fasa ihu

Haka kuma da ihu ta farka daga bacci, duk ta tsorata wadan da suke tare da ita, watau abokan amarya

"Asma'u" Ma'u ta fada tana nufota da sauri, sannan ta rungumota tana mata addu'a

"Shhhhhh yi shiru hakanan, mafarki ne kawai, kiyi addu'a kinji"

Addu'an takeyi amma kukan yaki tsayawa

Maman Ma'u ce ta shigo dan ihunta ya kai har cikin dakinta

"Ya yah? Komai lfy ?" Ta duko tana dafa Asma'u da idanunta rufe tana kuka


"Zo diyata, a bar kunshin haka nan" ta jata taje aka wanke kunshi sannan tayi alwalla tazo ta fara salloli


Dan hankalin kowa ya kwanta suyi bacci sai ta daina kukan,ta kwanta saman sallaya


Ji tayi an rufa mata bargo sannan an dora kanta saman pillow


"Kiyi ta addu'a har bacci ya dauke ki kinji namecy"
Bata tafi bah saida ta tofeta da addu'oi sannan


Tunda garin Allah ya waye take jin zuciyarta

Please Login or Register in order to submit comment