Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lura batama san abinda ke faruwa bah,

"Sir, sun iso"
"Toh meh aka jira su karaso manah"

"Akwai dan matsala ne" lukman na fadamai ya tashi tsaye yana dubanta har ya fita, da gudu ya karasa bakin gate


"Shi kadai ne Likitan dana sani a unguwar nan" inji Haider

"Ban san meye matsalan bah, amma ina hada ka da Allah ka dubata, kai likita ne ya kamata ace kana da tausayi"

Dr din rannan dake kokarin tafiya ya tsaya sauraron shi,

"Shahid koh" ya fada dan beh manta sunan bah

"Pls, kar abin ya shafe tah"🙏🏻🙏🏻🙏🏻

"Ina marar lafiyar" da sauri ya nuna mai hanya,


"Ina so ku dan bamu wuri" ya girgixa kai

"No way"🙅🏽‍♂
"Ehsaas mu basu wuri manah"
Haider ya fada yana janshi waje,
Fixgewa yayi daya ga Dr din na cire mata hijab

Tsaye yayi a bakin kofa yana kallon abubuwan da likitan keyi


Yana fita Ehsaas ya koma ciki, har a lokacin bata san wake kusa da ita bah,

"Am sorry" kiss ya manna mata a goshi sannan yasa hannayenta acikin nashi yana murza mata,

Wani ajiyar zuciya tayi, kafin ta fara furzar da iska meh zafi,

"Sannu Husna, likitan na nan zuwa" ya jata jikinshi ya dora kanta saman kirjinshi,
A hankali yake rirrigata,yana mata sannu,

"Ehsaas" na'am yace da farin cikin jin muryarta,

"You'll be okay" ya sumbaci goshinta da hanci, a hankali ya dora bakinshi saman nata,

"Da nine kai zan hakura da lip lock din, kodan lafia ta"
Yaga yana fiddo abubuwa daga cikin jakarshi,


"Meh ke damunta" ya tambayi Dr din

Bayan ya lissafo mai abubuwa,
Yace Oh God a ranshi,

"Ba'a nan bah" ya mike yana ciccibarta, ya jita shawal ba wani nauyi,

"Muje cikin gda" yayi gaba Likitan na binshi a baya,

Saman gado ya ajeta, sannan yaba likitan daman daura mata karin ruwa,
Sannan yayi mai bayanin magungunan daze bata hade da allurori,

"Idan wannan ya kare za'a jona mata wani" ya jin jina kai

"Tnk u" ya mika mai hannu
"Hmmm"😒😒😒 Dr din yace kawai ya tafi basuyi musabaha bah

"Karka damu dashi" cewar Haider dake gefe tuntuni bece komai bah,

Wata nurse Dr din ya turo tayi mata duk abinda ya kamata, allurai da sauran su,

Sallah kawai ke fidda shi daga cikin dakin, daya dawo kuma ze zauna kasa ya dora kai saman gado yana lura da ita,


"Bismillah" shi dama ba meh nauyin bacci bane bah, tun tana juye juye ya farka

"Cara mia, u okay" ya zagaya gefenta
"Zafi" ya taya ta yaye bargon,

"Ga ruwa ki sha" ya zuba a cup yana mika mata

"Tnk u" beh ansa ta bah ya taba goshinta

"Alhamdulillah, zazzabin ya sauka" zaune ta tashi tana kokarin sauka

"Sallah zanyi" tace bayan ya tambayi in da zata


"In taimaka maki" ta girgixa kai,

Bata dade a makewayi bah ta fito, bayan ya aje mata Hijab saman sallaya,

Wani green tea yaje ya hado mata, wanda ya samu tasha da kyar bayan ta rama salloli,

"Ki kwanta manah" yana tsaye daga gefenta

"Ka tafi" ajiyar zuciya yayi sannan ya fita dan yasan zaman shi ze takura ta,

Bayan minti 40 daidai ya koma dakin, ya zauna kasa da kanshi saman gado har bacci ya daukeshi,

Kullum haka yake yi, ya fita in tayi bacci ya dawo,
Bayan sallar Asubah kuma a dakinta ze dira sallah kawai ke fidda shi,

Wurin cin abinci da shan magani kawai yake samun matsala da ita, dan tama fi san allura da magani,

Akwai ranar data fashe mai da kukan shagwaba tana turo baki, abin ya bashi dariya dan beh san ta iya shagwaba bah,


Cikin kwana uku ta zamu sauki, duk da jikinta beyi kwari bah kuma tana da sauran maganin da take sha,

"Cokali 9 kawai kikayi fah" tayi kaman zatayi kuka

"18 ne wallahi, kuma ni na koshi" ta juya zata kwanta

"Nasan babu dadi, daurewa zakiyi kici haka nan" tace uhm uhm

Kyalewa yayi ya bata maganinta,

Cikin dare ya dawo dakinta, ya zauna a inda ya saba,

Tunda ta fara rashin lfy ta aje hijab gefe, sai in zatayi sallah,


Abinda ya dade yana imagining a ranshi,
Idanunshi suka kwadaitu da san su gani
Abinda hijab dinta ke hana shi gani,

Yes yaji dadin abinda ya gani, amma rama da bushewar da tayi su sukafi daukan mai hankali,

Lips dinta, bakaman na kasan da yake smooth, full gashi deep pink, yanxu duk ya bushe, ya tsage,

Kyallin da yaga tanayi lokacin da tana P. A dinshi duk ya tafi,

Tabbas ya gaza wajen rike amanar da aka bashi, ya barta tana aikin gda, tana dafa abincin da beh taba ganin taci bah,

Kwana a inda beh inganta bah, tunda har ta kamu da malaria, sannan ulsa, ga Karancin jini da akace mai tana da shi,

'Dama zaki iya fadamin damuwar ki dana saman manah mafita, jin dadin ki da rashin shi nawa ne nimah'

" I love you Husna"

" احبك " .


Ranar ya makara beh tashi da wuri bah har saida Alarm dinta ya buga, kasa ya kwanta flat, saida ta shiga bathroom sannan ya bar dakin,


"Husna, Mommy is coming " harda tsalle up and down,

"But granny Ma zata fara dawowa, tace harta gaji da Australia, kuma tunda ta warke dawowa zatayi"

Saidai ta tsinci kanta da murmushi saboda farin cikin da yakeyi, abin mah ya daina bata haushi yanxu kyau take gani, sangartar nayi mai,


"Kwanakin nan abubuwan farin ciki kawai keta samu na"

"Haider zeyi aure nan bada dadewa bah, kuma nakusan cimma BOYAYYEN KUDIRI na akan Asma'ul Husna"

Baya tayi tana dan cije laben ta na kasa

"Ni kam bana son kana kiran HIDDEN INTENTION akaina, sai in ga kaman wani mugun abu zakayi min"

Tsit bece komai bah, har saida ta dago ta kalleshi sannan ya babbake da daria harda share kwalla, 🤣🤣🤣🤣🤣

"Oh! My! God! Husna, kin iya sa mutum Nishadi koda ranshi bace yake"
Tace hmmmm

"Kin shirya haduwa da Mom dina" sai taji gabanta ya fadi,

"Allah ya kawo su lfy" yace Amin

Zuwa yayi ya zauna saman gado yana kallonta

"Zan gaya maki wani abu dake damuna, kodan ke ma ki aminta dani ki fadamin abinda ke damunki"

Tayi saurin cewa babu abinda ke damunta

"Duk da haka bari in fadamaki kiji"

Yayi gyaran murya

"Dana fadama iyayena abinda yasa hawan jinin Granny mah ya tashi"
Ta zaro idanu tana inna lillahi a ranta

"Irin fushin da Mom tayi ban taba ganinshi bah, Dad kuma damuwa ya nuna, dan danan kuma Mom tace zasu zo Nigeria, a yaran ku wanda bana ganewa kuma, naji Mom nata ambatan sunnan Hannah"

Ita dai ta cigaba da inna lillahi a ranta.

"Ina ganin Hannah ce dalilin da yasa, Mom da Granny Ma suka nisanta kansu da danginmu na nan kasar"

Ta rasa abinda zatace mai daya kai aya,

"Nayi alkawarin bazanyi bincike bah, amma na tabbata zuwan mom kasar nan, zan samu amsoshi dayawa"

Suka kalli juna na dan lokacin kafin yayi murmushi ta maida mai.




⚜B.W.A🖊
[3/19, 10:08 AM] 🎭KHALEESI.🎭:
💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
BOYAYYEN KUDIRI.

💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐

śťőŕŷ, ŵŕĩťĩńğ ßŶ ŃŐßĹĔ ĴÚĎĞĔ,
ĕďĩťĩńğ ĶĤÁĹĔĔŚĨ.


ŚÁĎÁÚĶÁŔŴÁ

Ga gwanaye brilliant writers, Love U all,
❤🧡💛💚💙💜🖤💝💖💗💓💞💕❣😘😍😻
Allah ya bar kauna ya amsa maku du'ain ku, ya kuma kare ku daga sharrin envious ones,
AMIN.


3⃣9⃣.


Cikin office yake zaune yana duban mutumin dake gaban shi yana naxarin wasu papers na jari daya basu,

"Da kyau, komai dai dai, Mun gode Mr Mas'ud"

Da murmushi yace bakomai sannan ya mike yasa buttons din suit dinshi,

"Sai naji daga gareku"

Yana shiga motan ya gaya ma lukman inda suka nufa,

Gyaran murya lukman yayi

"Ahem Ahem, Sir baza mu wuce gda ba haka nan, sai zarya muke daga can zuwa can bah wani hutu, baka gaji bah"

😁😁😁
"Banga ta zama bah tukunna Luk, har sai komai ya daidaita"

Lukman yayi ajiyar zuciya

"Allah ya biya maka bukatun ka na Alkhairi" ya amsa da Amin,

Tunda Asma'u taji sauke yake ta up down, har zaria yaje ganin iyayenta dan ya gaishe su yaga yadda komai ke tafiya a makarantar da babanta ke aiki, da kuma saban gdansu,

Yana dawowa kuma ya cusa kai cikin harkar bada taimako,
Ya ziyarci kungiyoyi da dama dan ganin irin bukatun su da yadda ze taimaka masu,
Duk inda yabi sadaqa yake bayyarwa, da niyyar Allah ya bashi Asma'u a matsayin mata,

Kullum yan uwa da abokan arziki yake mah addu'a , saboda malaiku, su amsa da. 'Amin , harda kai, kuma Allah ya baka fiye da haka', fatan sh kawai Allah ya bashi Asma'u,

Yanzu mah daga wani office yake, in da Alfie yace mai Ya Abbah yazo Interview kwanakin baya,

Yaje bada request din su daukeshi aiki ne, harda kamasho ya bada dan su daukeshi aikin da wuri,

"Mun iso,Sir" ya fidda wani raunan nan numfashi, saboda abinda ze aikata nan bada dadewa bah,

"Ka kwana lfy" mutumin ya dago ya kalleshi, sannan ya dukar da kai,

Luk ne ya shigo cikin dakin hade da rufe kofa,

"Baya hannu na sarkan, police din da suka kamani a lagos sun karba" kara kallon mijin nata yayi yana tausaya mai,

Koda yayi mai driving beh sanshi bah, amma daka kalleshi kasan yasha wahala,

"Taya kayi satan" inji luk,
Shi ba wannan ne gabanshi,
Takardar Asma'u kawai yakeso ya karba, istigifari yakeyi aranshi saboda auren da yake niyyan rabawa,


"Ranar dana daukoshi daga Airport ya barshi a mota"
'Halin da har yanxu na kasa canzawa' ya fada a ranshi

"Saida ina wanke motan na gani, dana bude naga koh menene sai na ajeshi a wuri na, ya dade baka nema bah alamun beh dame ka bah, shi yasa nayi gaba dashi"

Bata fuska yayi, saboda girman kan da salisu yayi magana dashi, kenan beh saduda bah duk wahalar daya sha

"Naga kaman ka shirya komawa prison din, so no problem "

Beh san lokacin daya tashi daga zaune bah yazo gabanshi a durkushe,

"Kamin rai, dan Allah karka maida ni gdan yari"

Ehsaas ya dan matsa baya,

'Haka shine daidai, dama tun can Allah yayi bashi ne mijinta bah, kai ne'

Paper da 🖊, ya mika mai bayan ya gama tunani,

"Hanyar ka ta tsira daga jail kenan"
Salisu ya bishi da idanu

"Rubuta sakin Asma'u " salisu ya wurgar da paper din

"Never, ina san Asama'u tah" 😭😭😭,

Kishi da bacin rai suka ziyarci zuciyarshi,

"Okay, Luk call the police " yana jin salisu nacewa ya fasa ze saketa amma beh koma baya bah,

Baki kawai yake gani saboda bacin rai,

Gammm!!! Ya rufe kofar mota, yana cusa hannu cikin gashin kanshi,


Neman tsari ya farayi daga shaidan har yaji radadin ya rage a zuciyar shi,

"Gashi ya rubuta Sir" ya mika hannu a hankali ya karba,

"Amma yace Dan Allah ka barshi yaga Asma'u suyi bankwana kuma ya nemi yafiyarta"

Saida sukayi nisa kafin ya iya magana

"Kasa a kawoshi gda, kuma a tambaye shi aikin daya iya, karmu barshi haka nan ya koma halin shiu na da, sannan kasa a kaishi wurin yan uwan sa"

Sukuku ya shiga cikin gda, ruf da ciki yayi saman gado yana jan pillow,


"Asama'u" ta fiddo idanu, baxata taba manta muryar nan bah

"Kin canza" ta bishi da idanu, har ya karaso kusa da ita

"Nayi babban rashi yau dinnan, amma haka shine daidai" Lukman ta gani can gefe yana kallonsu

"Inna lillahi" ta yi mai alama daya biyota dan kar a ganshi a kamashi,


"Neman ka sukeyi, kaka baxata ji dadi bah in ta samu labarin sun kaika police station "
Muryarta na rawa, da tsoro fal a fuskarta,

"Kwantar da hankalin ki, daga nan in shaa Allah gda nayi" goge hawayen da suka tsiyayo mata tayi

"Ka yafemin" tace data tuno fitar datayi bada izinin shi bah,

"Ni zaki yafe mawa Asama'u,abubuwan danayi maki a da" ya girgixa kai yana kallon kasa

"Allah ya yafe manah gabaki daya" yace Amin

"Bari inzo mu tafi toh" har tayi gaba ya riko mata hannu,

Take yanayinta ya canza tsoro ya bayyana a fuskarta, har abu ya tokare mata a wuya,

"Dan Allah ka__" kafin ta karasa rokon ya saketa taji muryar shi kaman tashin aradu

"Let her go, kaji dadi na barka ka ganta, but how dare u touch her"

Taga salisu yayi baya yana bashi hakuri,

"Bata ka tafi" ta maida dubanta ga salisu, da yayi mata murmushi yana fiddo abu daga aljihu

"Allah ya baki meh sanki tsakani da Allah, ina tayaki farin ciki, sai mun hadu kuma"
Sannan yayi mata sallama ya tafi, kuka ne makale a makoshinta, neman dalilin yinshi kawai takeyi, kuma ta samu tana bude takardar daya bata,

Zuciyar shi kasa hakura tayi, tana ayyano mai wasu abubuwa da yake rumtsa ido dan ya daina gani, kaman murnar ganin mijinta, tayi mai wannan murmushin da shi kadai yakeso ta dinga yi mawa, koh ta rungumeshi mah saboda murna

'No' yace yana sukuwa daga saman gado zuwa kasa


Dama yanata son yaga yanayin da zata shiga in taga takardar, beji dadi bah daya ga hawaye na tseren fitowa daga eyes dinta,

"Husna!!?? "

" Husna bakiyi bacci bah" ya dan saurara har yaji mostin tahowarta

"Hey" 🖐🏻
Tace mai sannu

"Bakiyi bacci bah" ta daga mai kai kawai

"Akan abin dazu ne" kaman tana jira ta fashe da kuka

"Husna, naxata farin ciki hakan ze saki" ta dago ta kalleshi da red eyes

"Farin ciki?, tun kafin mah rayuwar auren ta fara, an sakeni, taya ma zan gaya ma iyayena"
Kaman ya jata jikinshi, yace mata komai will be okay

"Na gaya masu, Ya Abbah har Alhamdulillah naji ya fada" ya karasa da dariya

Kallon da takeyi mai yasa ya bari

"Waya saka? " ta fada da karfi harda buga kafa a kasa

"Ba ni ya kamata in fada masu bah!!!" 😭😭😭😭ta fashe da sabon kuka

"Am sorry " ta girgixa mai kai alamum bakomai


"Dan Allah kiyi hakuri, Ágapi moú, baki san yadda na matsu da ki zama free bah, ba igiyan kowa akanki, kinyi hakuri Habibty, pls Jaanu"

Ta kafe shi da eyes

"Meh kace daya fara da H" shima nashi eyes din suka fito waje, shi yasa baya sa larabci cikin sunayen da yake kiranta, yasan ganewa zatayi


"Husnaty nace, koh sunan beyi dadi bah"

Ta share zancen
'Allah ya soka daka barota yau yau daga zamanta free'

"Goodnight " yace night, har ya kai kofar dakinshi ya jita tana kiran sunan shi kaman bataso yaji

"Yaya dai Husna? "

"Sarkan? Ya dawo dashi" ya daga kai

"Sai naje police station an tabbatar nawa ne kafin a bani"

🤩🤩
"Dadin meh kike ji"dan daga idanunta ya gane murna takeyi

"Zan iya tafiya gda, babu abinda ze ajeni anan, Alhamdulillah, Allah na gode maka" ta dora hannuwa saman face tana Hamdala

"Meh kikace Husna " dan da hausa tayi magana

"Zan iya tafiya gda yanxu" da sauri har tana dan tuntube ta koma dakinta, tana shiga tayi alwalla tana mika godiya ga Rabbi,

Data gama saida tayi tsalle saman gado, bata da aure, kuma ba yin aiki , murna kaman wacce akayi mah albishir da Aljannah,


Cikin dare ya bude kofar a hankali, ya sulala ciki, sannan ya kulle, bakin gado yaje ya zauna kasa da kai saman gado, dan harya saba tashin tsakar dare dan yazo dakinta,


'Dana sa mijinki ya sakeki banyi tunanin abinda ze biyo baya bah,
Bazan iya rasaki bah husna, ki gafarce ni in ban baki lokacin jinya bah, kafin in furta bukatata a wurinki'

Sai gab da Asubah ya farka, kaman kullum yayi dakinshi,

"Lfy Husna? " da hanxari ta iso in da yake

"Yau zan koma gda" dariyar dole yayi saboda ya rasa abinda zece mata,

Wayarshi datayi ringing ta ceceshi


"Am sowie husna, sai dai kiyi hakuri, kinga tafiya zanyi"

Tace bakomai tasan hanya ai,

"Ba nufina kenan bah, kinga amana aka damka min ke, sai kiyi hakuri in na dawo in maida Amanar"

Ta turo baki,
"Ka barshi kawai, ni zan koma da kaina"

"Kiyi hakuri kinji Ma cherie, ba dadewa zamuyi bah".

Ta xata tafiyan kwana biyu ne, amma saida yayi sati kafin ya dawo, meanwhile tana ta waya da yan gdansu.




⚜B.W.A🖊
⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊




💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
BOYAYYEN KUDIRI

💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐

$TôRý, ëÐíTíÑg ßý Ñôßしë JúÐgë ,
wRíTíÑg kHâしëë$í.


🏳❤🏳❤🏳❤🏳❤🏳❤🏳❤

wâñÑâÑ þâgë $âÐâúkâRwâ Ñë Ðâ kúmâ âÐÐú'â gâ bayin AししâH mâRâ$â しFý, Ñâ gÐâ ÐâÑâ â$íßíTí
AししâH ýâ ßâ$ú しFý ýâ$â kâFFâRâ çë,

Ðâ kúmâ ÐúkkâÑ ýâÑ úwâ mú$úしmâí, kâR mú çí Râí Ðâ $âmúÑ Ñâ$âRâ â Ðúk íÑÐâ múkë,
AししâH ýâ ßíýâ mâkú ßúkâTúÑ kú Ñâ âしkHâíRí.

Amíñ.


4⃣0⃣.


"Salamu Alaikum, Amore Mio" ya hada da washe hakora😁

Sallaman kawai ta amsa ta cigaba da harkar gabanta,

"Red wine ne wannan? " 🍷
Ya dauki glass din yana juya drink din da yayi sanyi, ga kanshin strawberry flavor na tashi, da kanshin splash shima strawberry, hade da cucumber

"Da wine din ne sha zakayi" yayi yar dariya yana aje cup din

"My dear Husna, ina zaki ga red wine har ki kawo cikin gda, koh da yake Luk yacemin kin fita"

"Luk?" Ta tambaya
"Duk abinda nayi sai ya fadamaka kenan" ya girgixa kai yana cewa noooo, kuma yace yesss

"Amma dan safety dinki ne kawai, shi yasa nake tambaya"

Ya dauki glass din
"Pls? " ta bude fridge tana dauko jug din sobon data hada,

"Naje kasuwa siyo mah iyayena tsaraba neh, acan na siyo kayan sobon nan"
Ya tsaya da sha

"Sobo sunan drink din" tace Eh
"Baka taba sha bane bah" yace Eh

"Amma akwai dadi" ya cigaba

"Akwai homemade drinks dayawa, da ina nan danayi wata rana, but gobe gda zan tafi"😌😌

Yaso boye dariyar amma ta kufce mai🤭🤭🤭
"A kaikaice kin fadamin gda kike son tafiya kenan koh"

Ta dukar da kai

"Ni na gaya ma Baba na, gobe zan taho"

Ya fara laluben wayar shi a aljihu beh gani bah

"Bani wayar ki" tace ina naka
"Na manta inda na ajeshi, bani naki in kira Baba dashi"

Beh duba contacts dinta bah, kawai sa number din yayi saboda ya haddace


"Amma wayan ka kake kira koh" yayi murmushi

"Hello, salamu Alaikum Baba" ya kalleta harda daga mata gira daya bayan daya

"Aa, dama akan Asma'u ne" ta matsa kusa dashi kadan dan taji abinda ake cewa sai yasa a handsfree,


"Da sun zo zan tafi toh" ta karbi wayanta bayan ya gama wayan, kuma babanta ya yadda ta kara kwana biyu,

"Toh muje ki rakani inyi mah su granny ma tsaraba" ta tambaya in sake komawa zeyi

"Aa, su zasu zo manah"

Tana tsaye jikin mota tana jira, sai gashi ya fito sanye da suit kuma,

"Zakaje wurin aiki ne" yace Aa
"Kuma suit?" Tayi shiru bata karasa bah

"Ina san looking formal and smart duk inda naje". Tace Ayyah

"Kaji dadi bah lokacin zafi bane bah" ta fada da hausa, da taga ya kafeta da eyes sai tayi saurin kauda kai,

Purple motar shi Rolls Royce, meh kyau irin na da dinnan classic yasa aka fiddo mai,

Boutique sukaje inda yace ita zata zabi komai, shi yasa ya zo da ita,

Turare ta zaban mah Mom dinshi da Granny Ma, Al haramain da kuma set

Please Login or Register in order to submit comment