Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bah daya karanta abubuwan da aka rubuta,

Suna isa gda yaje ya duba maganin da take sha, coat dinshi yasaki ta fadi kasa, tagumi yayi bayan ya zauna saman gado, dukar da kai yayi,

"Hubby yaushe ka dawo" da gudu ta karasa saman gadon tana rungumeshi, kiss ta manna mai a kumatu,
"Cuddly B yau shagwabar ta dawo neh" tayi mai cakulkuli, kasa daurewa yayi ya dago yana kallonta,

"Ya akayi neh, baka jin dadi" damuwa ya bayyana a fuskarta,
Kasa cigaba da kallonta yayi ya dukar da kanshi kasa,

"Hubby" ta duka kasa tana dago da face dinshi,

"Dan Allah ka fadamin abinda ke damunka" ta rude dan tasan lfy lau suka gama waya, amma gashi yanxu idanun shi sunyi ja duk yayi wani yaushi,

"I hate liars neh Husna, na tsani ayi min karya wallahi" shafa fuskarta yayi yana kallonta ido cikin ido,

'Husna baxatayi min karya bah, amma abinda na karanta, ya za'ayi tasha abinda ze iya yi mata illa, Husna baxata iya abu irin wannan bah'
Tunani barkatai sun kewaye mai kwakwalwa,
"Huddy" ta rada mai a kunne kaman fitar iska,

Ajiyar zuciya yayi sannan ya jawota jikinshi yana zuge zip din rigarta, mamaki yasa ta bude baki shi kuma yayi amfani da wannan damar ya fara kissing dinta,
"Hubby da ranan nan" ta fada da kunya tana dukar da kai, beh saurareta bah ya cigaba da cire mata riga,

Tunanin da ke adabar shi kawai yakeso ya daina, beh so yayi zargin matar shi da wani abu,
Matar shi ta cika mace kuma duk sadda ya kusanceta yana samun gamsuwa fiyeda yadda yayi tsammani,
Yana yin wanka yayi sallah, tunanin shi ya karkata ya koma ga maganin daya siyo,
Ranar beh wuni da jin dadi bah, shi kadai ya kebe kanshi yana neman hanyar tabbatar da gsky, daya je masallaci mah beji koh meh ake magana akai bah, shidai yasan yabi jam'i,

Hannuwa cikin aljihu, kai kasa yana tafi a hankali shi kadai,
"Ehsaas" Mom ta fada yana shigowa cikin gda, tafiya kawai ya cigaba da yi,
"Ehsaas" Dad mah ya kira da Mom ta maimaita amma be juyo bah,
Kaman itama ta kirashi amma tayi shiru dan gaban surukai take,

"Ehsaas!"saura kadan ya harde kanshi ya fadi kasa,
"Na'am" yace, daya samu ya mike tsaye beh fadi kasa bah,

Suma kallo suka bishi dashi, babu wanda yace wani abu har saida ya karaso cikin falo din, da sauri ta mike taje ta debo ruwa meh sanyi ta kawo ta ajemai, lokacin sun fara magana,

"Kasha" ta zuba mai a cup tana mika mai,
"No Husna am good" sukuku ta aje ruwan sannan ta tafi dakinsu,

Zaune take saman gado tana jira ya iso,

"Wifey" da fara'a ya shigo yana murmushi,

"Ya akayi naga kina kallo na haka kaman na zaman maki sabo" ya daga mata gira daya,
Saida ta kara kallon shi sosai kafin ta saki fuska
"Bazaka fadamin abinda ke damunka bah" ya girgixa kai, beh mah boye mata cewa wani abu na damun shi bah,

"Bazaka fadamin bah" ya daga kai sau daya,
"Ni wifey dinka, kuma Angel eyes dinka, kuma Cara Mia dinka" ya daga kafadu

"Zan fadamaki abinda ke damuna amma sai nayi maganin matsalar tukunna" ya dagata sama ta kugunta,

"Amma ka samo maganin matsalar koh" ya daga kai sannan ya fara tafiya,
"Toh fadamin" ya sake make kafada
"Toh Allah ya baka sa'a" yace Amin,

Idea dinshi shine ya sata tasha maganin ya gani da idonshi, shi yasa ya direta saman gado yana kokarin rabata da kayanta,

Yayi tsammanin zata nuna ta gaji koh bataso, amma saita tayi matching dinshi a komai, kaman dazu da rana basuyi bah,

"Yau babu aiki neh" Da garin Allah ya waye sai yasa mata ido koh bandaki zata shiga sai ya bita,

"Kin gama shan maganin ki neh?" Ta girgixa kai,
Sannan ta nufi cabinet din ta dauko dan dama tana da niyyan sha,

"Har wani na siyo maki" tace tnk u tana karba,
"Kin san abinda maganin nan yakeyi Husna" ta danyi jim kafin ta daga mai kai,

"Na sani hubby" ta fada tana ballowa

"Husna kafin ki sha, bari in fadamaki wani abu" ta juya gareshi,

"Kinsan abinda yasa na tsani makaryata" ta girgixa kai

"Yayata, Ameera muke kiranta, kaman best friend dina ba yayata bah haka take,mun shaku sosai,

Kafin ta rasu na taba jin rumors din tana abota da drug addicts kuma ana ganinta a parties,
University take ni kuma ina high school lokacin, boarding school neh saboda haka ban samun ganinta kullum,

Ban dade da jin rumors din ba na fadamata, sai tayi dariya tace min it's all a lie, every night in zata fita sai tayi karyar classmates dinta zataje gani,
Bazan manta bah ranar data mutu saida na tambayeta inda zata tayimin karya,
Shi yasa i hate liars, nasan koda ta fadi gsky baze hana ta bar duniya bah tunda lokacinta neh yayi,

A makaranta aka tsinci gawarta, tayi overdose din wani kwaya"
Idanun shi sunyi ja, saida ya gama fadamata kafin ya kyafta idanu dan kar hawaye su zubo mai,

"Kina min karya Husna" kasa ta kalla sannan ta kalleshi,
"Ribar meh zanci in nayi maka karya" Ajiyar zuciya yayi sannan ya daga mata kai, alamun tasha maganin ta,

Saida ta juya baya sannan ta iya shan maganin, data juyo sai taga hawaye sun tsiyayo daga danun shi,

"Karya kikayi min Husna, kin dade kinayi min karya, to my face at that" ya cusa hannu cikin gashin kanshi,

"Hubby meh kake magana akai" tayi yunkurin taba shi,

"Don't touch me" ya fada da karfi, sannan yasa hannuwa yana rufe bakin shi,

"Ehsaas" ta fiddo idanu waje dan har lokacin bata san dalilin bacin ran nashi bah,

"Ki rantse min bakisan maganin meye kike sha bah, kwata kwata baya da alaka da period dinki, koh karya zaki sake yimin" ya damki hannunta yana dora mata maganin bisa tafinta,

"Ki rantse min Husna" dukar da kai tayi kasa tana shesheka,

"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un" ya dafe kai daya ji yana juya mai,

"Bana son inyi tunanin ki a haka Husna, amma gani nakeyi duk abinda kika fadamin karya ne" sa sauri ta dago da kai hawaye na bin kuncinta,

"Hubby pls" da tazo gaban shi ze juya mata baya,

"Ki tafi Husna kwata kwata bana son ganin ki, i want to be alone dan Allah karki nuna min fuskarki" kasa ta duka daf dashi tana son ta taba shi,
"Dan Allah karka koreni ba tareda kaji abinda nakeso in ce bah, pls"
"Bari in tafi ni tunda ke bazaki tafi bah".
Zama tayi tana kallon hawayenta dake diga a kasa, ji take kaman ta rasa zuciyarta gabaki daya,komai na jikinta ya daina aiki,

Haka ta kwana tana bin kofa da kallo tana jira ya shigo, da safe neh take jin muryar shi yana magana da Alfie,

"Ni na hanata tazo dama, ko da can da take zuwa ni nake bata izini" fuskar nan kaman beh taba fara'a bah, har tsoron tunkarar shi taji,

"Tace bazata zo bah sai ka gayyace ta da kanka, dan kar tazo kace family time" yayi tsaki,
"Wai ba ita ke son zuwa bah" Alfie yace Eh,

"Mom tasan zata zo" ya sake cewa Eh
Ajiyar zuciya yayi dan yasan hadin bakinsu neh su biyu,

"Yau zata zo kasar koh" Alfie ya fiddo wayar shi,

"Dama miss Danyah tana kasar nan, gdan nan ne kawai bata shigo bah"


Gabanta neh ya fadi, bataji kishi bah sai tsoro daya mamayeta,

"Ahemmmm" gyaran murya tayi dan Kunyar kiran sunan shi takeyi,

"Kace mah Mom ina daki" ya fara tafiya, da sauri tabi bayan shi tana kuka dan bata sannabinda zatace bah,

"Dan Allah ki bar bina kina min kuka" ya fada ba tareda ya juyo bah, girgixa kai tayi tana cigaba da binshi,

"Ban shirya fuskantar ki bah Asma'u, har yanxu raina a bace yake in mukayi magana zan iya yin abinda bazanji dadin shi ba daga baya, so pls just go away, ki barni in ji da abinda ke damuna manah" bata bishi bah daya cigaba da tafiya, jirata tayi taga in dakinsu ze shiga,

Kayanta ta shiga hadawa,har ta kusan rabi kuma ta sake daga farko, wannan katon kayan data san dashi tazo su tayi packing cikin yar travelling bag,

"Salamu Alaikum" ta shiga dakin Hajia

"Wa'alaikumus salam Asma'u, dan Allah ki jirani a falo yanxu mu gama mgana"
Tace toh bayan ta kalli Mom sannan ta koma falon dakin ta zauna,

"Yanxu meh kika gano umma" daga inda take zaune tana jiyo hirar tasu,

Bata nan suka fara amma ta gano abinda suke magana akai,
Bata san lokacin da tayi tagumi hawaye na bin kuncinta bah,

"Wani abu kikeyi haka" dago kanta tayi bayan ta goge hawayenta,

"Asma'u ya akayi" Hajia ta tambaya,
Bata iya kallonsu ba su biyu, kuma taji dama ta tafi ba tareda ta fada musu bah,

"Wani irin ciwon kai nakeyi kwana biyun nan, sai ya tafi ya dawo" Hajia tazo ta dafa ta,

"Kina shan magani kuma" ta daga mata kai,
"Hmmm kila sai munje asibiti, ina da check up ranar Thursday, sai muje tare"
"Gobe Thursday ai" Mom ta sako baki
"Sai kije kema koh" ta fada da wani irin murmushi a fuskarta,

Hajia tace tana zuwa, ta nufi cikin daki,

"Saidai Hajia taje check up din koh, dan ke banga alamun kina nan har Thursday bah" tsaye ta mike rataye da handbag dinta meh dan girma sosai,

"Eh dama nazo" kuma tayi shiru,
"Ban mah san meh nazoyi bah, amma naji dadi dana zo, BOYAYYEN KUDIRI na ya cika, kema naki ya cika" ta fada kai tsaye, muryata bata fayyace radadin dake cikin ranta bah,

"Okay is that so, pardon me but ban san meye wannan HIDDEN INTENTION din naki bah" bata kawo komai a ranta bah da Mom ta koma magana da turanci, saidai ita bata canza yare bah dan bata da wannan karfin,

"Da nasan KUDIRI nah, ban san abinda nakesi bah yanxu" Mom tace Hmmm
"Karatun , aure na dan lokaci, kiyi kudi, naxata KUDIRIn naki kenan" Mom ta sake magana da turanci,

Daga mata kai tayi,
"Kin tunamin, INTENTION dina kenan dama, dama can ina son in bar nan, ban taba sawa a raina cewa aurena anan na din din din bane bah, kuma kin fada daidai, am glad i didn't get pregnant" Mom tayi wani shu'umin murmushi kuma batace komai bah,

Hakanan kawai taji ranta ya bata ta juya, kaman ita yake jira ta juyo ta kalleshi kafin ya tafi,

"Hukuncin da kika yanke yayi daidai koh" bata iya ba Mom ansa bah sai kai data daga mata.





⚜B.W.AπŸ–Š
[5/14, 20:07] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



Story and editing by NOBLE JUDGE
Writing by KHALEESI.



6⃣2⃣




Wani zeyi tunanin bayan satin ta da dawo wa zata samu karfin guiwwan fadama iyayenta abinda ya dawo da ita gda, saidai ta kasa kullum tana aikin kuka in dare yayi, gashi takira Aminiyartata kuma ta sanar da ita baxata samu daman zuwa bah,

Kullum saidai tayi murmushi in aka sako mijinta cikin zance,
Baxata kira shi da mijinta ba mah, anytime ze iya aiko mata da takardar ta,

Da zaman gdan ya isheta saita shirya zuwa wurin Ma'u,

"Ni zaki tambaya toh" kaman ta fasa ihu da Mamanta tace haka
"Yasani ai" Mama ta kalleta,
"Ke matar aurece Asma'u, yawo up and down ba naki bane bah, kin san nace zamuje kiga yan uwa koh"
Tace Eh can kasan muryarta,

"Abba neh zezo ya kaiki" ta girgixa kai,
Kallonta Mama ta sakeyi kafin tace A dawo lfy,

Tsakanin uwa da Da sai Allah, duk kokarin boye damuwarta da takeyi beh hana Mama sanin akwai wani abu a kasa bah,

Kwana uku yayi beh nemeta bah kuma beh ganta bah, curiosity dinshi na son sanin dalilinta nayi mai karya yasa ya shiga dakinsu a kwana na biyar,

Daya shiga dakin ko ina tsaf kaman ba'a zama a ciki, saman gado ya zauna amma bayan minti 10 sai ya tashi ya shiga bandaki, da beh ganta bah sai ya shiga dakin canza kaya, kitchen yaje nxt canma bata nan,

"Hey!" Ya tsayar da wata meh aiki,

"Asma'u fah?" Ta dan kalleshi idanu waje,

"Nima na daina ganinta"
'Ai kai kace baka san ganinta, kuma sai nace ta sani wahalar nemanta in na shirya ganinta' tsaki yayi yana komawa sama,
Ya dan damu daya duba ko ina beh ganta bah, bacin rai da fushi yasa beh nemeta a waya bah,

"Baba ina wuni" ta duka kasa ta gaishe da mahaifin Ma'u, shigarta gdan kenan suka hadu shi kuma ze fito,
"Asma'u ce" tace Eh da kanta kasa,
"Komai dai lfy koh, naga baki dade da zuwa bah" tayi dan murmushi,

"Lfy lau Baba, naxo registration neh, shine na biyo mah Ma'u" yace toh yana dan jin jina kai,

"Allah ya bada sa'a, amma ni sai inga gwara kije kiyi registration dinki ke kadai,
Ma'u kam baxata samu zuwa wannan makarantar bah" taji gabanta ya fadi,
'Akwai matsala kenan'

"Baba ayi mana afuwa dan Allah" ta karasa kai guiwwowinta kasa,

"Bakiyi komai ba Asma'u,

kar laifinta koh na yayanki ya shafe ki, ke har yanxu na yarda da tarbiyar ki, ke diyace ta kirki kuma saliha,
Kuma naji dadin yadda kika dauki Ma'u a matsayin yar uwarki, saidai bata biyo irin halayar ki bah"
'Na shiga uku ' tace a ranta, tana ayyano wasu abubuwa da take tunanin sune laifin da Ma'u ta aikata,

"Baba dan Allah kayi manah uxuri, Ma'u yar uwa tace kuma ita kadai ce kawata, babu halinta da ban sani bah, kuma indai akwai wani hali marar kyau a tare da ita toh nima ina dashi"
Baba ya katse ta da Kul!

"Karki shafa ma kanki kashin kaji saboda ita, a duk cikin yayana wadanda suka girmeta da kanana, babu wanda ya sani ciwon kai kuma ya hanani bacci sai ita,
Shi yasa na bata zabi in dai karatu takeso ta cigaba toh ba'a kusa dani bah taje can inda baxata dinga kunsamin bakin ciki bah"

Ta hada hannuwa wuri daya,

"Baba ni na yadda da tarbiyar daka bamu, nasan akwai akasi a wani wurin, Ma'u baxatayi abinda ze janyo maku matsala koh ya bata maku suna bah,
Dan Allah ka yadda damu da tarbiyar daka bamu, ni nayi alkawari in sha Allah baza a sake maimaita irin haka bah"
Ma'u golden girl din babanta ce, koh meh takeso shi yakeyi mata, meh yayi zafi haka, meh ya faru, ta karasa tunanin da wadan nan tambayoyin,

"Hmmmmm" ta cigaba da bashi hakuri har ya sauko yace sai ya dawo,

"Namecy" baki bude take kallon kawar tata, duk tayi baki ga kashin wuya kaman rakumin daji,

"Ma'u kece haka" hmmm Ma'u tace tana karkata baki,
"Haka kika koma namecy, lallai aure yayi maki dadi" ta rike haba tana binta da kallo,

"Hmmmm kawai zamuce" ta zauna saman gado,

"Ashe kina under lock down" Ma'u ta tabe baki tana dora pillow zaman cinyoyinta,

"Rayuwa juyi juyi ce Namecy, yau tana goya maka baya gobe ta juya maka" matsowa tayi ta dafa kawartata,

"In kinga na bar gdann nan toh kin fadamin abinda kikayi masu Baba har rai ya baci haka" murmushi tayi tana damkar hannunta,

"Ai ni gaba ta kaini, sai kiyi ta zama anan, dama banda abokin hira" duka ta kaimata bayan ta kwace hannunta,

"Ba abin wasa bane bah wannan" takai minti biyu tana kallonta kafin ta fashe da kuka,

Lallashi ta hauyi tana bAta baki,

"Ai keh kin san yadda muke da yaya abba koh" Asma'u ta daga kai, Ma'u kuma ta girgixa mata kai

"Baki mah sani bane bah" ta dan yatsina fuska,
"Ba soyayya kukeyi bah" Ma'u ta daga mata kai,
"Ke bakya ganin akwai wani abu tsakanin mu daya fi haka"
Dan baya tayi tana hango yanayin data gansu kafin aurenta da Ehsaas, ba tun ranar take ganinsu haka bah, lokacin neh dai idanunta suka bude tasan meh take gani,

Bazata manta bah, in Ma'u tazo gdansu toh ya Abba beh sake zuwa ko ina suna tare koh one sttr ta zauna toh shima wurin ze zauna, yayi ta wasa da hannuta koh hijab dinta, ya jingina da ita har dora kanshi Yake saman kafadarta,

Ita gahuwar bata dauki hakan komai bah, dan duk yan gdansu sun dauki Ma'u a matsayin kanwa,

"Amma gsky Ma'u daga shi harke kun ban kunya" ta fada rai bace

"In shi beh da matsala da haka, ke a matsayin ki na mace sai ki biye mai, i can't believe this"
Ta dafe kai tana kallon kasa, dariya taji ta dago kai,

"Lallai namecy, kin sanni da wayau fah, ai koh da His Excellency GCFR yake yawo bazan bashi jikina bah ba tareda munyi aure bah"
Bata fuska tayi
"Toh meye matsalan"
Ma'u ta kalli kasa,

"Ai cewa nayi bazan bashi jikina bah, amma ban hana shi lips dina bah" ta karasa kaman wata tsohuwar munafuka tana zare idanu da kai kasa,

Tsaki Asma'u tayi sannan ta samu jakarta ta kwala mata,
"Rannan mah fah da nazo bayan second 10 ko 15 da Allah kadai yasan abinda zan iske ku kunayi"
Ma'u ta turo baki tana tirje kafafu daga zaune,

"Ni nasan mah lokacin dana saba dashi har yake tabani, Allah ban iya tunawa, nidai nasan na fara lura da yadda yake tabani neh, bayan nazo gda na shiga kitchen zaan dauko abu sai ya bini yana zuwa ya taba kuguna yana jAna jikinshi, wani irin shock naji everywhere najikina wallahi, kin san ai abinda nake nufi"

Bata yi nasara wurin canza topic din bah, sai bata mata rai data karayi,

"Ke kuma sai kika kyaleshi ya cigaba da tabaki bayan nan, tun lokacin ya kamata ki takamai burki" tayi kasa kasa da murya dan kar a jisu,

"Bakya tunanin nayi kokarin yin haka, kasa fadama nayi na bige da kallon mesmerizing eyes dinshi da wannan killer smile din nashi"

"Ga abinda kika jawo ma kanki nan ai, ya akayi yan gda suka sani"
Ta shafa fuskarta tana kallon kasa,

"Congrats yazo inyi mai lokacin daya siya mota, i was so happy bansan lokacin dana rungumeshi bah, shi kuma ban san yadda ya fassara hakan bah, saidai naji yana kissing dinah" ta fada tana kallon kasa hade da sosa keya,

"Ke kuma baki kwashe shi da mari bah" ta girgixa kai
"No, ina ga kwarin guiwwa mah na bashi, Baba kuma lokacin ya dawo daga wurin aiki shine ya haskemu da fitilar mota"
"Tsarki ya tabbata ga sarkin sarakuna, Baba da idanun shi Ma'u" Ma'u kam ta daga kai,

"Da ana bari na in dan fita mah in dai Baba baya nan, amma yanxu har Mama ta juyan baya, tun ranar da ya Abba ya kawo min admission letter dinnan, Baba cewa yayi hanyace muka bullo da ita na holewa"
Asma'u ma ta jin jina kai, dan koh itace haka zatayi tunani,

"Toh kuyi auren manah koh kowa ze huta" Ma'u tayi hmmm da wani murmushi meh nuna takaici karara,

"Har satar jiki nakeyi in fita dan in fadama bawan Allah n nan ya fito kawai a daura manah aure amma yaki, dana bashi jikina wallahi dana sha poison na mutu, ya koyamin babban darasi wallahi, kiyi hakuri nasan yayanki neh amma koh kallo beh isheni bah balle har in nuna mai naji zafin abinda yayi min"
Ta karasa da hawaye na bin kuncinta,

"Honey!" Ta dora kanta bisa kafadar Asma'u tana Kuka meh cin rai,

"Gsky ya Abba beh kyauta bah, karki damu wallahi zanci mutuncin shi duk da yayana neh" Ma'u ta girgixa kai,

"Ni bana so yasan abinda yayi min ya dameni, gwara in dan rage girma na kar ya ida raina ni"

Bata baro gdan su Ma'u ba sai bayan Maghreb, shima saida Baba ya dawo taje tace mai zata tafi,
A nan ne yace ya yadda suje makaranta tare da Ma'u,
"Amma ki sani yardar danayi dake yasa zan barta ta fita, karki bani kunya Asma'u" hannu bibiyu guiwwa kasa ta duka ta karbi wannan amana,

Saidai wata zuciyar na fadamata, daya san abinda tayi a gdan mijinta da beyi kasadan bata amanar yarshi bah,


"Mama ai harda maganar Makarantar ya maido dani gda" ta zura kafafunta cikin takalmi,
"Ki taimaki kanki ki sanar dashi zaaki fita toh" tace Toh murya kasa kasa,

A nan tsaye tayi dialing number dinshi, an dauka saidai ba'a ce komai bah,



Please Login or Register in order to submit comment