Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Zanje makaranta neh" saida ya dauki sweet time dinshi kafin yayi magana,

"Karki ban dariya manah Husna, it's not like kina ganin girma na neh, da kina gani ai bazaki sa kafarki ki fita daga gdan nan bah"

"Kaifa kace in tafi, that u didn't want to see my face, umarnin ka nake bi har yanxu" ta fada da murya babba,

"Umarni nah?" Yayi wani dariyar takaici

"Umarni na neh shan Contraceptive pills, umarni na neh zuwan ki gda, haka neh koh?

Toh Allah ki sani bada izini na bah kika bar gda, ki ma bar yin wani ibada dan ba karba akeyi bah har sai kinzo kin nemi yafiya na yafe maki" ya kashe wayan shi,

A hankali ta cire wayan daga kunnenta, a sannu kuma hawaye ya tsiyayo mata,

"Asma'u" tace na'am ba tare da ta juya bah,

"Ni zan wuce Mama sai na dawo"

Taji dadi da Mama bata tsaida ta bah, a wajen gate ta tsaya taci kukanta kafin ta bar gda,

"Ya Abba!" Ta zagaya ta shiga motar tashi,

"Shine kike ta wani tafiya ina maki horn" ta bashi hakuri kafin ta cigaba

"Dama ina neman ka fah" ta koma serious
"Gani nan ai say what u want"
Kallonta ta maida gareshi,

"Akan bestie dina neh" yayi tsaki yana juya idanu, tasan da ze iya daya bar mata motar ya tafi,

"Yaya Abba baka san irin matsalan da baiwar Allah n nan ta shiga bah fah" gabanshi yake kallo beh mah nuna yasan tana magana bah,

"Wow, am very surprised, kasan bayan ta fadamin abinda ya faru ban yanke hukunci ba, ban saka a jerin irin mutanen nan bah, Kuma Ma'u fah ya Abba, na dauka matsayi daya ka bamu ni da ita"

"Har kin gama neh, naxata sai kin hada da dukana hankalin ki ze kwanta" tace Allah ya baka hakuri,
tana kallon wajen ta window

"Ina son Ma'u, da da hali dana dade da auren yarinyar nan, naso in bata rayuwa ingantacciya neh irin wanda ta saba dashi, tasha nuna min bata da matsala koh wurin Mama zata zauna, kilA ita da gaske tana son haka kuma hakan ya isheta,
Ni hakan neh beh isheni bah"
Tunda ya fara magana ta koma kallon shi,

"Toh ka aureta yanxu manah" ya washe hakora kawai,

"Kina ganin mahaifinta ze dube ni har ya ban auren yar shi" ta danyi tunani

"Amma dai ai yafi ace bakayi komai bah koh, in yaga da gaske kake ai ze dube ka koh" ya sake girgixa kai alamun bazaki gane bah,

"Ka ajeni nan, bana son Baba yayi fushi dani in yaga munzo tare" tsaki yayi kafin ya samu wurin parking,

"Ya Abba ka tafi abinka, Ma'u ma baxata shiga motarka bah" da bacin rai ya kalleta,

"Wai ke kika sani in kawo ki nan, koh fadamin inda zaki kikayi, ki shiga ki kirata, in baxata je bah fyn, in kuma iskemu zatayi acan toh"

Ya kauda kai daya gama,
"Ahmmm Yaya Abba ze kai mu"
Ma'u ta saki baki,

"First class Ass hole din ze kaimu makaranta" ta bata fuska
"Haba Ma'u, yayana neh fah" hmmm inji Ma'u
"Nikam ba inda zanje" ta dora hannu saman kugu tana shaking, dama gashi tasha kwalliya,

"In kika koma saboda shi ai ze san yana ranki har yanxu, ki share manah kawai ki nuna baki san mah yana wurin bah" ta kara zugata kafin suka fito daga gda,

Ba ita kadai bah har shi beh nuna yasan akwai ta cikin motar bah, duk da ko wani motsi tayi akan idanun shi,

Message din daya shigo wayar Ma'u neh ya yanke tafiyar kuramen da sukeyi,

"Namecy kalla" ta koma bayan kujerarta kafin ta nuna mata wayan,

"A gari kike, sai ki kira kiyi godia" Ma'u sai Fara'a takeyi,
Text ta turama Asma'u,
'Kin san da zan fito mama ta bani kudi tace inyi duk abinda ya dace,banyi zaton Baba ze turomin kudi bah, tnk u namecy'
Juyawa tayi ta kalleta da murmushi kafin tace bakomai,

"In muka dawo da wurin mu biya kasuwa plssss" ta tabota,

"Sai naji abinda zakiyi a kasuwan tukunna" Ma'u ta fara lissafowa

"Ai dama na sani" Ma'u tayi murmushi
"Kiju dadi nayi including dinki a budget dinah, gyale guda uku zan siya maki, as appreciation, ni kuma guda bakwai nakeso"
Dariya sukayi su biyu,

"Da hijab kika siyamin da kin fi birgeni" Ma'u ta turo baki,
"Akwai kalan hijab din da bakya dashi neh, ni dai bazamu dinga yawo tare bah in kullum hijab zakisa, karki ja ayi tunanin nima matar mallam ce" ta karasa tana kallon kanta ta madubi, lipstick ta fiddo daga bag dinta da niyyar shafawa, tana kallon madubi taga idanun shi a kanta, bata fuska tayi amma ba ta fasa abinda tayi niyya bah,

Ba karamin yawo sukaci a kasuwa bah, bayan sunyi wani a makaranta,

"Sai munga yanayin komai kafin mu koma hostel koh" ta amsa mata da Eh,
"Lectures din mah mu bari sai nxt week" Asma'u ta sake cewa toh,
"Namecy ki shigo manah,ki ci abinci ki huta kafin ki tafi" ta girgixa kai tana rufo kofa,
"Gwara inje gda in huta gabaki daya, sai munyi waya koh" tace Eh suna yima juna bye bye,


Suna isa gda Mama ta hauta da fada,
"Akan wani dalili zaki biye ma Ma'u tun safe sai yanxu da yamma kafin ki dawo" saida yaya Abba yasa baki kafin Mama tayi shiru,

"Babanku ya fara tambayan yaushe zaki koma gdanki, mutane sai surutu sukeyi, gashi ke sai yawo kike tayi"

Inna lillahi ta fara jerowa a ranta kafin kwashi kayan da suka siyo tayi dakinta,


"Ji nake kaman kowa ni yake kallo" ta cigaba da kokowa da gyalen data yafa,
"Zasu cigaba da kallonki kam in kika nuna baki iya yafa gyalen bah" sauko dashi tayi daga saman kai ta dora saman kafadu,
"Haka yayi" Ma'u ta rufe baki tana mata dariya
"Ga sarkin surutun nan ya biyoki" da sauri sauri take maganar tana tabota,

"Wucewa zeyi" da taga da gaske su yake tunkarowa sai ta daga kafa,

"Da gyalen zamuje gda" sai lokacin wannan tunanin ya fado mata a rai,
"Da fah" inji Ma'u, ita koh ta girgixa kai,

"Ni dai hijab zan saka da mun samu abin hawa" taki kallon Ma'u dan tasan bakauya zata kirata,

"Tagwaye masu suna iri daya" Ma'u ta gimtse dariyarta, ita koh Asma'u ta bata rai,

"Dazu naga kunata sauri nace kila kunyi latti neh" taki juyawa,

"Haba malama Asma'u" ta kara bata rai kafin ta juya, harara ta baka ma Ma'u dan ita ta tsaya kuma ta riketa,

"Yanxu ma sauri mukeyi mlm muna da wurin zuwa neh" ya daga kai kafin ya kallesu up and down,

"Masha Allah shi yasa naga kun tsatso kyau haka, gsky tsarki ya tabbata ga sarki daya tsaro yan mata kyawawa irin ku" sauran kadan ta buga tsaki, amma saita kauda kai,

Kirjinta ne ya fara bugun konga drum da idanunta suka sauka kan the one and only Ehsaas,

"Ma'u" ta fada kaman zatayi kuka
"Kin gan shi kema" Ma'u ta danyi dube dube kafin ta hangoshi,

"Ba gizo yake maki bah yar uwa shi din neh" suka hada tsaya kallon juna,

"Ma'u muyi gaba kaman bamu ganshi bah" basu tsaya sauraran wanda ya tsayar dasu ba suka fara tafiya,

"Namecy mu yake kallo" ta kara sunna kai kasa

"Ke waya ce ki kalle shi"
"Ke kuma meh yasa bakya so ya ganki, gyalen da kika sa" Ma'u ta tsayar da ita

"Haba namecy ya za ki kauda kai kaman baki ga mijin ki bah"

Beh dauke idanunshi daga kanta bah saida tazo daf dashi, kafin tace wani abu kuma ya bude mata gdan baya,

Abinka da marar gsky,sai ga zufa na tsiyayo mata daga goshi har cikin jiki,

Bece uffan bah sai shades dinshi daya cire yana kallonta, ita kuma hannayenta ta dunkule tsakankanin cinyoyinta,

"Muje Lukman" saida ta rumtse idanu saboda yadda muryar shi ya ratsata yasa zuciyarta harbawa kaman tana tsere,

"Ina mukayi Sir" ya kalleta kafin ya bada ansa,

Da taga cikin gari suke shiga sai ta fiddo wayarta daga cikin jaka,

'Kin taho namecy' ba dadewa sai ga reply din Ma'u
'Na fasa zuwa weekend din ni kadai, tunda ke holewa zakije yi da mijinki' gimtse dariyarta tayi amma saida ya fito,

Wayar ya fige daga hannunta sannan ya duba, Duka text din su ya karanta sannan ya duba messages da contacts dinta,sannan ya mika mata wayar, ita kuma ta jefa cikin jaka,

Bece mata komai bah sai kallonta daya cigaba,

"Yau kazo?" Murya kaman rada haka tayi magana,
Daga kai tayi suka hada ido, da sauri tayi kasa da idanu tana wasa da yatsunta,

Hannu yasa yana kokarin cire gyalen data yafa, duk kunya tabi ta isheta dan beh taba ganinta da gyale bah,
Bata ankara ba taji ya rabata da gyalen sannan ya bude window ya jefar,

"Meye hakan?" Tasa hannu tana kare jikinta,

"Ni banga amfanin shi bane bah ai" ya fada da babbar murya bacin rai karara a ciki,

Shiru tayi dan yana da point, gyalen sharara yake gashi light blue color,

"A haka kike yawo" ta daure fuska tana kallon gabanta

"A haka dai kakeso inyi yawo tunda da gyale na ka yar min dashi" cije hakora yayi dan da bacin rai yaxo, kuma ta sake guma mai daya ganta tsaye da wani ta yafa wannan rag din a jiki,

Yana tunanin yadda ze fito da ita daga cikin mota a haka, gashi kuma sun iso hotel din daze sauka,

Yana cikin tunani sai yaga ta bude jaka ta zaro hijab dinta tasa, sannan ta bude kofa ta fito,
Ganin inda akayi parking saita ja baya tana hade gira,
'Cin mutunci ya za'ayi ya kawoni nan' ta juya tana jiran ya fito daga mota,

"Ni dai bazan shiga nan bah" Shiru yayi mata sannan ya kama hannunta ya jata suka shiga ciki,

Feelings Pyramid, ta karanta sunan hotel din kafin ta kalleshi,

Key yasa ya bude kofar sannan ya matsa baya, alamun ta fara shiga,
Tana shiga yabi bayanta sannan ya kulle da key,

Ji tayi an fizge jakarta an wurgar gefe,
"Hey" beh bata daman magana bah yaja hijab dinta,

"Wai meke damun ka" fizgota yayi jikinshi yana fidda numfashi sama sama, kasa kissing dinta yayi sai lips dinta da yake kallo,
Mannata yayi jikin bango yana kallon yadda ta firgice,

"Tunani nayi akan abinda yasa kika cigaba da zama dani bayan bakya san ki haihu dani" tayi kokarin kwacewa amma yaki kyaleta,

"Nasan dai bakya sona" ta girgixa kai
"Sshhh karki katse ni"
Ya shafa fuskarta zuwa kirjinta ya tsaya a cikinta,

"Bazan ce kina son kudina bah, but kin canza zeyi zama shine dalilin daya sa kika zauna dani"
Abu ga mai saurin kuka sai hawaye shaaa ba wani sauti,

"Hmmmm Husna kenan" akan bakinta ya huce bacin rai da kishin shi,

Fizge fizge ta fara dayayi kokarin rabata da kayanta,
"Bakiyi kewata bane bah" ya fada da small husky voice yana shafata a hankali,

Abinda yace kawai kenan ta biye mai suka rama kwanakin da basuji dumin juna bah,

Suna kwance saman gado yayi rigingine, saita dora kanta saman bayanshi tanayi mai tafiyar tsutsa da yatsanta,

Shi dama yasan baxata hana shi jikinta bah, dan itama meh karfin sha'awa ce,
"Hotel dinku neh nan koh" ya maida hankalin shi kanta,

"Ba'a budeshi ba tukunna" ya tashi zaune yana cire hannun ta daga jikinshi,

Tana nan kwance shi kuma ya shiga bandaki dan yin wanka,
"Husna tashi kiyi wanka" saida ta tashi zaune kafin taja blanket din ya rufe mata kirji,

"Ina zamuje" ya tsaya dasa kaya ya maida duban shi gareta,

"Inda na dauko ki" ta tsaya kallon shi,

"Kin zata na dawo maida ki gda neh" ta zuba mai manyan idanun nan nata,

"Karki ban dariya manah Husna, in nace nazo maidaki gdana neh ai bazaki yadda bah" zura kafafunta tayi zata sauka daga saman gadon,

Kaman an zare mata lakka haka ta shiga bandaki dan yin wankan, kokwanto yasa ta fito dan ta kasa tsaida hankalinta wuri daya, sai tsaki yakeyi yana cewa tana batamai lokaci

'Ka tafi ka barni manah in sauri kakeyi' ta fada a ranta, a fili kuma ta cigaba da bata lokaci,

"Akwai abinda nakeso in fada maka" ta fada kaman zatayi kuka,

"Kar in bata lokaci na wajen saurarenki kuma kizo ki fadamin karya" wayar shi ma yake latsawa,

"Gsky zan fadamaka, akan dalilin daya sa nake shan maganin nan" mikewa tsaye yayi da sauri,

"Sorry na manta nazo maki da shi mah" ya lalubi aljihun shi har ya ga maganin, sannan ya tako zuwa gabanta ya damka mata a hannu,

"Kuma bana son jin abinda zaki fadamin, lokacin dana so ji bakya nan,
Yanxu kuma banso in ji" ta dukar da kai tana kuka a hankali,

"Abinda kunnena ya jiyo min ya isheni, kinji dadi bakiyi ciki bah, kuma kina so ki yanke duk wata alaka damu, koh ba haka kika ce bah"

Ta girgixa kai hawaye na rige rige a fuskarta,
"Bazan sake ki bah, saidai zan dinga zuwa wurin ki duk sadda na so, nasan baki da matsala da hakan koh" ya karasa cikin wani sexy voice, yana dan cije mata kunne

Tureshi tayi daga jikinta, kafin ta mika mai hannunta,

"Ni ka ban takarda ta, akwai maza dayawa dake bibiyata, kuma banda matsala da hakan"
Da sauri ya juya mata baya yana cije hakora, dunkule hannayen shi yayi yana fidda numfashi sama sama,

Hijab dinta ya wurga mata bayan ya sace, sannan ya kama hannunta da niyyan janta,

Kwacewa tayi tana bubbuga kafa a kasa,

"Kaban takarda ta, na gama SADAUKAR da farin cikina da kuma rights dina saboda ku,
Baka san wahalar da so called taimakon da kake ganin kayimin ya jawo min a rayuwa bah,

in dai a kan kun neh wallahi sai inda karfina ya kare, dama nasan rana irin ta yau na zuwa, abin a jinin ku yake, kaje can ku karata da su,ka ban takarda ta kawai koh na samu kwanciyar hankali for once tunda na hadu da kai, kullum mutum na cikin fargaba, gwara in je in auri daidai ni, in da baza'a dinga min barazana da lafiyata koh na yan uwana bah " tama rasa wurin kamawa, surutu kawai take zubawa

Tasa hijab dinta sannan tayi gaba abinta, kaman yasan niyyarta ya biyota da sauri,

" Husna!" Ya bita yana kiranta,

Bata saurareshi bah ta cigaba da tafiya tana fitowa daga hotel din ya cinmata, yana rikota ta fizge,

"Husna get back here" ya tsaya inda akayi parking motar su,
koh hanya bata kallo da kyau haka tasa kai zata tsallaka, kafin ta ankara da horn din da akeyi har mota ta bigeta,
Da kanta ta mike tsaye a firgice, da gudu ya karasa zuwa inda take tsaye, beh san lokacin daya daga hannu ze zuba mata mari bah,

"Ehsaas" muryar wanda yaji yasa ya sauke hannu kasa, ita kuma ta bar wurin da gudu tana tare abin hawa,

"Abinda yasa kace zaka riga mu zuwa kenan" ya kauda kai yana rumtse idanu,

"Ehsaas meh ke faruwa" kanshi kasa beh dago bah sai tafiya daya fara,

Dad ma mota ya shiga amma yace a kaishi gdan su Asma'u,

Hannu bibiyu suka tarbi Dad duk da basu san da zuwan shi bah,
Abinci lafiyayye aka kawo mai,hankalin shi da ba'a kwance bah ya hana shi ci,

"Daughter dina fah? Ya jikinta" suka ce lfy lau,duk da basu ta da rashin lfy bah,

"Bata dai ji ciwo ba koh, kaman daga sama tazo tsallaka titi anyi kokarin taka birki amma dai saida aka bigeta"

Nan Baba ya sanar dashi ai bata gda,tana makaranta ne,
"Zamuyi wani dan taro neh anan, shine Ehsaas ya daukota daga makaranta,ban san abinda ya faru tsakanin su bah, amma dai nasan akwai matsala, kuma Ehsaas yayi shiru bece komai bah,

Gsky am worried in bata nan ina ta shiga" baba ya mike yaje ya kira ya Abba,

Koda ya dawo Dad ya kira dan nashi,

"Ehsaas yace bata tare dashi" Dad ya fada yana mikewa tsaye,

"Yanxu za'a kira abokiyar ta du suke makaranta" suna nan tsaitsaye saiga ya Abba, girgixa kai kawai yayi suka san bata can,

Mama kawai aka bari a gda sauran suka bazama nemanta,

A bakin gate ya iske ta zaune, yana karasowa ta mike tsaye,
"Har yanxu baku ganta bah" yaya Abba yace mata,

Ma'u ta koma ta zauna,

"Bari in je wani wurin toh tunda kina nan" tace toh tana sake dialing number din Asma'u,

"Switched off, da dauka ne ba'ayi, mijinta fah, tare suka bar nan ai" girgixa mata kai kawai yayi beh bata ansa ba,

Ana idar da sallah a masallaci ya fito ya cigaba da nemanta, hanya ta biyo dashi ta gaban hotel din da suka shiga dazu, sai gata tsaye tana fiddo kudi daga cikin jaka zata ba mai Napep,

A birkice ya tsayar da motar ya fito, koh kullewa beyi bah yaje ya juyo da ita ya tabbatar itace kafin ya rungumeta,

"Sau biyu a rana daya kina kusan samin heart attack" fizge jikinta tayi daga nashi kafin ta cigaba da ba meh napep kudi,

"Bazaka maida ni bah"
"Gsky tafiyar ba kadan bace bah" saita ce bakomai tana yi mai godiya,

Hannun data fiddo daga hijab ya gani a gurje, gefen goshinta mah ga jini nan ya bushe,

"Ba karamin fushi nakeyi da ke bah, amma bazan iya kyale ki bah Husna"
Titi kawai take kallo tana rokon hawayenta karsu zubo,

"So kike in roke ki kafin ki shiga motar mu tafi" ta harde hannuwa a kirji bata da niyyan tafiya,

Wayar shi ta katse tunanin shi na sabata a kafada,

"Yeah Dad na ganta" tana ganin wannan daman ta fara tafiya da sauri, tana samun wani adaidaita kuma ta shiga ba tareda ta kalli bayanta bah,

A kan idanshi ta shiga napep din, ranshi ya kai kololuwar baci, amma saboda ya ganta kuma yaga she's okay sai beh bita bah,

Tana shiga makaranta taci karo da Ma'u, saida ta fara dukanta kafin ta rungumeta,

"Allah namecy kin dauki Alhakin mu dayawa" hakuri ta bata kafin tayi mata bayani,

"Wallahi saida na iso makaranta naga ashe ba jakata a tare dani, saida na koma na dauko, kuma wayata ta mutu lokacin"

A hankali suka taka zuwa hostel, tana mata sannu dataji har bigeta mota tayi,

"Gashi Mama ce" koh zama basuyi ba call din ya shigo,

A sanyaye tace hello, taxata fada Mama zatayi mata dan kullum laifinta take gani, amma sai taji tsantsan kulawa da har ya sata kuka,

Karfe takwas na safe a gda yayi mata, clinic sukaje aka karbo mata magani da dan dressing a ciwukanta, bayan taci abinci tasha maganin kuma ta samu isasshen bacci sai Mama ta sata a gaba,

"In da matsala ki fadamin Asma'u, yanxu neh zan iya taimakon ki basai lokaci ya kure bah"
Dora kai tayi saman guiwwa,

"Ni tunda kika dawo nasan akwai matsala, akwai koh babu" kai ta daga mata,

"Fadamin abinda ya faru" murya na rawa a ta fara fadan abinda ya dawo da ita, saidai batace Mom ta bata maganin ba

"Ba tareda amincewar sa kike sha bah" tsoro ya hanata cewa komai, saida Mama ta sake maimaita tambayar da muryar daya fi na da kafin tace Eh,

Kare kanta tayi daga dukan da Mama ta kaimata, kuka take tana bata hakuri amma Mama bata saurara mata ba,

"Shine tunda kika dawo kika tisa mu gaba kina kallo baki iya fadamin abinda ya faru bah, abinda na koya maki kenan"

Tace Aa tana girgixa kai, wani ihu tayi tana neman hanyan tsira da taga Mama na dauko cable,
Tunda take Mama bata taba dukanta bah saidai tace zata duketa, abin sai ya zaman masu sabo su duka,

"Gwara in kashe ki kafin ni ki karasa ni, ace tun zuwanki amma kika shiru, watau ke abin beh ma dameki bah"
Iya karfinta take cewa Aa, dukawa kasa tayi ta rasa ta hanyar kare kanta,

"Mama!" Tana jin muryar Ya Mukthar ta boye bayan shi,

"Matsa ka ban wuri" kankameshi tayi tana dan Allah kiyi hakuri, shima yasa baki yana fadan abinda take cewa,

"Mukhtar stay out of this!" Sai ranar ya taba jin Mamanshi ta daga murya kuma tana fada,

"Zo ki shirya kayan ki, Allah ya rufa maki asiri mah zasu koma da ke, bazaki zo bah" saida tabi umarnin da aka bata duk da dar dar take tafiya,


Please Login or Register in order to submit comment