Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tana bi ta gaban Mama ta sake tsala mata wayar hannunta, har kasa ta fadi saboda tsananin rikicewa,
Tsoron kar a kara dukan ta ya hanata shirya kayan da sauri,
"Wallahi suka jira ki sai na lahira ya fiki jin dadi" Ya Mukhtar neh ya shiga tsakanin su kafin ta iya shirya kayan da sauri,

"Ki zauna nan ki jira su, saura in kin koma ki tarkan ma kanki wata tabi'ar da ban sanki da ita bah" in da aka nuna mata ta zauna tana kankame jikinta da yayi ja saboda bulala,

Sai bayan Mama ta fita kafin yazo ya zauna kusa da ita, beh ma tambayi abinda ya faru bah ta fashe mai da sabon kuka, lallashi yayi ya samu ta danyi shiru kafin ya fita,

Babu abinda ke tadata daga inda aka ce ta zauna sai Sallah shima da tayi zata zo ta zauna a wurin, amma har duhu ya fara har dare yayi, har yan gdan suka kashe fitilu basu zo bah,

Washegari mah tanayin sallar asuba tayi wanka, sannan ta zauna zaman jira, da gari ya waye sosai kuma taje ta gaishe da iyayenta, dukan su kaman an sasu dole haka suka amsa mata,

Tana cikin yin kukanta a daki sai ga Mama da abincin ta, saura kadan a sake zaneta da tace ta koshi,
Ranar mah zaman jira tayi, haka daya after saidai har bayan sati babu su babu alamun su,
Ba karamin damuwa Mama ta shiga bah, wanda hakan yasa itama ta damu, gashi koh kallonta Mama batayi, in aiki taje tayata sai tace bata so, in ta matsa saita tashi ta bar mata wuri,

Kullum Addu'arta da fatan ta Allah yasa suzo koda bazasu tafi da ita bah, tasan hakan ne kawai zesa Mama ta sassauta mata.





⚜B.W.AπŸ–Š
[5/14, 20:08] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Story and Writing by
NOBLE JUDGE,
editing by KHALEESI.



6⃣3⃣.



A bangaren su Ehsaas kuma Ciwon Hajia ne ya tashi, rudun da sukaji a muryar Mom yasa basu bi ta ko ina bah suka tafi gda,

"Umma ina zaki je" Hajia ta cigaba da tafiya bata tsaya sauraran ta bah,

Da sallama ta bude kofar dakinsu kafin ta shiga, zaune ya tashi yana niyyan sauka kasa,

"Basai ka tashi bah ni zaman zanyi" ta fada da murmushi,

"Granny Ma hutu aka ce ki dinga yi" ta yatsina fuska tana turo baki,

"Abinda kace ya kara tuno min da dalilin daya sa na taso,
Da Asma'u na nan da tasan ina bukatar hutu, at d same time kuma tasan ya kamata in dan dinga motsa jikina" Mom ta hade rai tana kallon gefe, shi kuma ya dukar da kai kasa,

"Naxata da yar Albarkan nan zaka dawo" da dan mitsitsin murmushi ya daga mata kai,

"Umma ita ta tafi da kanta fah, meye na sai ya dawo da ita, daga can tayita karawa gaba" Mom ta fada da hausa,

"Basai na fada maka bah, amma kasan Asma'u akwai baiwar hakuri da sanin ya kamata, kuma duk dan adam tara yake beh cika goma bah,
Babu wanda yafi karfin mistakes, kayi naxari kaga in laifin meh yafuwa neh ka dawo da ita, kai kanka zakafi samun kwanciyar hankali"
Tun Hajia na magana Mom ta koma ta dayan gefen shi,

"Sai munji in laifin wanda za'a iya yafewa ne ai tukunna koh" Hajia ta watsa mata harara,

"Sai in ta fadamin gsky kenan koh" ya fada kanshi kasa,
Mom dafa shi tayi tana girgixa kai,

"My poor child ka manta da sabgarta, duk mutumin da baze daga ka sama ba saidai ya jaka kasa meye amfanin zama dashi, ga kifaye nan dayawa a teku, sai wacce kake so ka zaba,

Duk kabi ka hana kanka sukuni saboda wata can da ba ajinka bah, haba Ehsaas aikin ka daina zuwa koh murmushi mah ka daina yi,
Gsky zan yi fada da mutanen nan in wani abu ta saman min kai"

Murya ba karfi yace mata ya daina damuwa,
"In shaa Allah kullum zaki dinga gani nah cikin farin ciki" sai ya tashi tsaye bayan ya kakalo wani katon Murmushi,

"Australia zan zo in koma, in manta da nan gabaki daya" harda tafawa Mom tayi sannan ta mike ta bashi pecks guda biyu a duka kumatun shi,

"Ehsaas ka sameni a dakina kaji" Hajia ta mike tsaye tana tafiya sukuku, Mom tayi kaman bataga rashin amincewa da shawarar jikin nata a fuskar Mahaifiyar ta bah,

"Abinda ka zaba kenan" ya zauna a gajiya kaman wanda ya yini yana wankau,

"Granny Ma koh Asma'u ta dawo gdan nan, bana ganin zan iya yarda da ita kaman da, bana ganin zan iya manta abubuwan data furta min da sukayi tasiri a zuciyata bayan karya ta fada,

I can't Granny Ma, gwara in koma can kila in manta da duka abubuwan nan"
Ya mike tsaye yana dafe kirjin shi dake yimai radadi,

"Tunda bazaka iya yadda da maganarta ba meh ze hana kaji abinda bata furta bah, abinda take tunani"

A hankali ya juya yaga tana mikomai littafin daya taba ganin Husna dashi, Meh cover leather da igiyan daurewa,

"Ina jin kunya in na tuno dalilin daya sa na bata littafin, dana karanta abin ciki kuma sai naji dan sanyi, dan tayi amfani dashi ta hanyar daya amfaneta"

Karban littafin yayi ya bude, 'Dear Diary' yaga ansa daya bude wasu pages, saidai daga nan da hausa ta cigaba da rubutu,

Ko daya kalli kakar tashi sai yaga ta kwanta hade da lumshe idanunta, daki ya koma ya yini yana jujjuya littafin, koh sallah ya idar sai yaga idanun shi sun sauka akan littafin,

Dictionary din hausa yayi downloading cikin wayar shi, kafin ya zauna fassara abinda ta rubuta, saiya gama duba layi daya kafin ya ji abin yayi making sense,

Kwana yayi yana wannan aikin, ta rubuta dalilinta na shan magani,
Kuma tace itama taji a ranta tana son shan maganin, saidai da Mamanshi ba ta bata bah da bata san da akwai shi bah
abinda yasa ta aureshi kuma mahaifiyarshi ta tilasta, ita kuma sai bayan sunyi aure ta kamu da san shi, farin ciki da kwanciyar hankalin iyayenta da yan uwa yasa ta yadda, dan kar Mom tayi musu abinda tayi barazanar yi,

da kuma wahalar da tayi ta sha a gaban shi amma beh ganeh bah,
'Baka san irin wahalar da so called taimokon da kake ganin kanayimin ya jawomin bah' abinda ta fadamai kenan a hotel dinnan,

Wani irin haushi da bacin rai ya ziyarce shi lokaci daya, watsa komai na saman study desk din yayi, har monitor da keyboard duk ya watso su kasa, beh gama haukan bah sai ga Dad ya shigo da sauri,

Guiwowin shi ya dire a kasa yana kuka, Kakarshi ta fara sannan Mamanshi ta dora, duk saboda basa san talaka, duk dan suna tsoron kar su rasa shi kaman yadda Mom ta rasa mahaifinta ga wata ita kuma Granny Ma ta rasa mijinta ga wacce ta dauka a matsayin diyarta,

Laifin wata ya shafi yar baiwar Allah r da tunda ya santa koh kallon banza bata tabayi ma wani bah,
Shine sillan duk wahalan da ita da kowa nata ya sha, kawai da ya dauki san duniya ya dora ma wacce Mamanshi bata so,

Kuka meh sunan kuka ya zauna yana yi, beh mah san abinda Dad ke cewa ba, haka Mom data shigo daga baya,
Hango ta kawai yakeyi kullum da safe tana aikace aikacen gda, da dafa abinci da biyayyan da takeyi mai dan ba'a so ta bata mai rai, da wulakancin da akayi ma iyayenta da kazafi harda accident din yayyanta,

Ranar datace zata aureshi ya tuno,harda marin shi tayi dan yace yana son ta da aure, ba dadewa kuma tazo tace ya aureta, bayan anyi mata barazana da zaman lafiyar iyayenta,

Tutturesu yayi ya hau saman gado yana zubda zafafan hawaye, duk sai yaji ya tsani kanshi gabaki daya, komai na duniya ya daina yi mai dadi

Dad tafiya yayi ya bar Mom, shi kuma ita yakeso ta tafi, koh taban shi da takeyi baya so, a haka har baccin wahala ya kwashe shi,

Da Alwalla ya hada bayan ya fito daga wanka, sallah ya fara kafin ya hau shiri dan ya makara,

"Good Morning everyone" ya bisu gabaki daya da kiss a kumatu, su kuma sai kallonshi suke kaman yanada tabin hankali,

"Meh zamuyi breakfast dashi yau" take Mom ta fara serving dinshi abubuwan da yakeso,

Tnk u yace mata kafin ya dauki fork, yana kallon abincin da fadomai a rai, pancakes neh da strawberry syrup, saidai ita bata hadamai dashi wai ya cika shan zaki, saidai ta yanka mai strawberries da banana tace yaci dasu,
Ji yayi abincin ya fitan mai a rai, amma saboda duk shi suke kallo sai ya faraci kaman beh taba ci bah,

"Zanje in ga Granny Ma" ya mike bayan ya gama cin abincin,
Zuwa yayi ya mata ya jiki kafin ya nufi dakinshi in da yaga Dad zaune yana jira,

"Dad" ya fada da kai kasa dan yasan maganar baxata wuce na abinda ya faru jiya da dare bah,

"Shirye shirye naga kanayi" ya dago yaga Dad na nuni da kayanshi dake saman gado da trolley din dake kasa,

"Eh, na tafiya Australia neh" ya taka a hankali zuwa inda babanshi yake saman gado,

Jin jina kai Dad yayi kafin yayi magana,

"Meh yasa zaka koma can, naxata duk duniya kafin jin dadin zama anan " yayi dan karamin murmushi,

'Lokacin matata na nan bah' shima Dad abinda ya hango kenan,
"Zanje can in danyi clearing min dina ne Dad, dana ji komai ya dawo min daidai, zan dawo nan din"
Dad ya tashi tsaye yana tafiya,

"Zaka koma can, amma da sharadi" bin bayan babanshi yayi dan ya zata sharadin nashi neh,

"Yace yana son komawa can" Mom ta tashi zaune da fara'a,
"Gwara yaje can ya manta da ciwon da nan ya ji mai"
Girgixa kai yayi daya ga da gske jin dadin komawar dan nasu Australia takeyi,

"Ya za'ayi kice haka safiya, bayan kin san dalilin shi na shiga halin da yake ciki,
Kuka tabbas kinsan komawar shi can baze rage komai bah sai karawa da zeyi,

Natsu da kwanciyar hankalin da yake bukata duk suna nan, farin cikin shi duk suna nan, meh zeyi acan din shi kadai"
Mom ta budr idanu da mamaki,
"Meye na tada jijiyoyin wuya, ai nima can din zan koma koh" yatsa ya daga mata alaman tayi shiru,

"Dama da shardi na zo maki" yayi shiru yana kallonta ido cikin ido, itama shi take jira ya cigaba,

"In dai Ehsaas ya bini muka koma dashi Australia yau, toh ki tabbata kinyi bankwana damu, dan bazaki sake ganin mu, kuma zan tabbata koh hanya baku hada dashi bah, dan bah farin cikin shi kike so bah naki kikeso"

Ba shi kadai bah har Mom mah she's speechless, mamaki ne kawai kwance a fuskarta,

"Tun yaushe kake neman dalilin daze sa ka rabu dani" ta fada da murya kaman meh shirin yin kuka,

"Basai na nemi dalili bah Safiya, kusan kullum sai kin bani dalili" shima kaman wanda ke rada haka yayi magana,

"Kin san ina sanki safiya" ta girgixa kai tana daga kai sama dan kar hawayen su fito,

"Kin san ina sanki" ya sake maimaitawa,
"I have and will always love you safiya,
Nayi hakuri dan koma menene nine sila, ni na barki kika koma haka,
Maybe ina ganin laifina cikin rabuwar ki da yan uwanki, shi yasa na barki kiyi duk abinda kikeso koda ze cutar dani, koda ze batamin rai indai abi da kike so neh i let you have your way,

Zanyi iya daukan koma menene, in dai ze tsaya akai na ni kadai, amma in ya tsallake ya taba dana i won't let pass me by, harda Asma'u abinnan ya shafa Safiya"

Ya matsa yana so ya tabata, ita kuma ta matsa baya tana kallon gefe, kara yunkurin tabata yayi

"Don't touch me" maganar tata ko fitowa batayi
Beh saurareta bah ya fizgota ta tsaya a gabanshi,

"Na tsani bata maki rai dan ni zanfi jin zafin abin, amma sai kiyi ta sani inyi abinda bana so" yasa hannu yana share mata hawayenta,

"Zan wuce Australia yau in Umma taji sauki Dan Allah ki biyoni" make kafada tayi sannan tabi ta gefen shi ta wuce,
Yasan ranta neh ya baci shi yasa taki yadda data sauko kuma zata biyo shi,

Tana barin wurin tayi dakin mahaifiyar ta inda ta cigaba da kuka,

Yana zaune cikin daki yaji alamun ana jan akwati, a guje ya fito yana neman baban nashi,

"Dad tafiya zakayi" ya fada kaman zeyi kuka, dan shi gani yake in ya tafi toh sun rabu kenan,

"Eh Ehsaas" da sauri ya karasa inda yake tsaye yana rungumeshi,

"Dan Allah Dad karka tafi" dago fuskar dan nashi yayi yaga hawaye,

"Haba Ehsaas, ka girma fah naxata duk ka daina wannan shagwaban, kana da mata fa" hawayen suka cigaba da fitowa,

"Zan barka anan ka kula da mamanka, karka bari komai ya sameta kaji koh" ya daga kai yana goge hawayen,

"Muje ka rakani Airport" yace toh yana rike da hannun baban nashi,

Dama in aka kure masu hakuri abin ba kyau, sun kai Asma'u geji, ga babanshi nan mah sunsa ya furta abinda beh so bah,


"Babanka fah" ya tashi daga tagumin da yayi

"Ya wuce Mom, amma yace ze dawo nan bada dadewa bah" Mom tayi murmushi
"Zanje in ga Haider ne Mom" tace toh itama tana komawa sama,

"Ba zaki bishi bah?" Hajia ta fada daga kwance,

"Barshi ya tafi Umma, in na bishi yanxu zefi jin dadin yimin san ranshi" Da kyar Hajia ta tashi zaune tana tari,

"Sannu Umma" ta debo ruwa a cup sannan ta bata,
"Umma dan Allah ki cire dmuwa a cikin ranki, ki bar Yaya, yasan yadda ze kula da kanshi"
Hajia batayi mamaki bah da taji diyar tata ta san dalilinta na zuwa family house dinsu,

"Abar wannan maganar, Safiya kinsan irin rayuwar da nayi bayan babanku ya auri Hannah, duk da abinda yakeyi min beh hana in bishi sau da kafa bah,

Nasan laifina neh wannan canjin dabi'a da kikayi, ni na koya maki ganin talaka a matsayin Makiyi ba masoyi bah,
A wurina kika koyi yin abinda kika gadama, ba wanda ze amfani wadanda ke kusa dake bah,

Dan Allah safiya tun lokaci beh kure bah ki canza hali, ki nemi yafiyar wadanda kika batama wa tun kafin lokaci ya kure maki"
Kallonta tayi na dan lokaci kafin tayi magana,

"Umma meh yasa kike magana irin haka" Murmushi tayi kafin ta girgixa mata kai,

"Bari in kwanta in huta" tace toh, amma har ta juya bata bar kallon mahaifiyar tata bah,

"Da kai din meh zuwa neh da sai ince kadaina zuwa saika sanar dani"
Dariya yayi yana kokarin karban diyar abokin nashi,

"Wai kai kayi aure shine koh leke" Haider ya hanashi daukanta,

"Saidai kayi hakuri, nima sai ya zama dole ake bani ita" Suka gaisa da Safwana matar Haider,

"Seriously Haider ka ban ita" Ya sake yunkurin daukan Malika,

"Komai lafia naga ka daina wannan kyallin da kakeyi, gashi kuma kazo wurina, yaya dai?"

Murmushin fuskar shi ya dauke, sannan ya samu wuri ya zauna, Haider kuma ya sauke Malika kasa dan ta iya zama tana rigimar rarrafe,

"Abubuwa dayawa sun faru, matata ta koma gdansu Granny ma bata da lfy" ya girgixa kai

"Yaushe duk abubuwan nan suka faru" Haider ya dora hannuwa saman guiwwa,

Da yake ya yadda da abokin nashi sai ya bashi labarin komai, saidai beh fada mai harda sa hannun Mamanshi bah,

"Na kasa hakura da ita Haider, so nake kawai inji ance min it's okay in dawo da ita,
Duk yadda raina ya baci na kasa hakura"

Haider dai jin jina kai yayi, fuskar shi bata fayyace abinda ke ranshi bah,

"Bazan ce komai bah Ehsaas, kila hukuncin da zan dauka, kai ba irin shi zaka dauka bah" saida Haider ya kalleshi kafin yayi magana,

"Meh za kayi?" Malaika ya kalla tana ta kokarin tura abubuwa cikin bakinta,

"Ehsaas da ni neh bana tunanin zan iya hakuri har in yafe mata" ya sake kallon diyar tashi,

"Bazan iya yafewa bah Ehsaas da ace kwayoyin da take sha yayi silar sani rasa Angel dinah,
But situations dinmu daban daban neh"
Yasan da wani dalili na daukan wannan hukuncin,

"Kamar kullum nine idiot din dake fadama matsalata, kai kuma kamar kullum ban kai matsayin sanin matsalar ka bah"

Ya mike tsaye kaman ranshi ya baci,

"Seat down Ehsaas, ba abinda na taba fadamawa kowa bane bah" Ya sake duban tilon diyar shi,

"Safwana kawai ta sani, amma kila har in gama rayuwata Angel kawai zatayi amfani da sunana"
Ehsaas ya zauna ya zuba ma abokin nashi idanu,

"Kafin ka faramin shagwabar nan taka bari in fadama daga kai sai Safwana kuka sani,
Shi yasa nace karka bi ta abinda zanyi"
Hango abubuwa ya fara a kanshi, duk wadanda suke nuna illar maganin data sha,

"Tun yaushe" yayi kokarin canza tunanin da yakeyi,
"I don't know, amma shaye shaye neh ya kara rage chances dina na samun haihuwa"
Sauka kasa yayi ya dauki yar baby girl din
" No wonder babanki ya dauki san duniya ya dora maki" Haider yayi dariya yana kallonta,

"Hmmmm, but Ehsaas har yanxu bana ganin Sweet innocent matar nan taka zata iya shan maganin nan ba tare da sanin ka bah" tsayawa yayi na yan seconds kafin ya cigaba da wasa da Angel,

"Kaman cusa mata idea din akayi" Haider ya cigaba da fada,

Wayar shi da tayi ringing ta hana su cigaba da magana,

"Hello Mom" ya tsaya jin abinda ake fada ta dayan bangaren,
Tsaye yayi a kasake da idanu waje, sai innalillahi wa inna ilaihi raji',un da yake maimaitawa,


"Cewa tayi in barta zatayi bacci, koh minti biyu ba'ayi bah sai ga Yarima, koda muka je munata magana ba'a ansa bah"
Tama kasa kuka kaman har lokacin bata yadda da Mahaifiyar ta rigamu gdan gsky bah,

"Mom, dan Allah ki kwantar da hankalin ki" hannun shi daya dora saman kafadarta ta rike

"Toh ka cemin ba gsky bane bah, My mother is okay, she's just sleeping" ta hau shi da fada, idanunta sukayi ja,

"Mom kiyi hakuri dan Allah" ta mike tsaye tana yawo up and down,
Haka ta yini tana fada da duk wanda yace mata ya hakuri, da Amyr yazo shi korarshi ma tayi tana cewa karya kara zo mata gda,

Wani flight Dad ya canza daya dawo dashi Nigeria, saida yazo sannan tayi kukan da tayi ta rikewa,

Da dare ya kwanta yanata juye juye, bacci ya kaurace mah idanun shi, ji yayi dama matar shi na kusa ya samu wanda ze bashi hakuri ya lallashe shi,

'I Miss you' ya fada a ranshi,

Tana zaune cikin dakin ta gama karatu, dan Ma'u na kawo mata handouts in tazo weekend, da zaman kadai ci taga gwara ta dan dinga duba littafi,

Koh bakin kofa ba'a bari taje, bacci kawai takeyi sai cin abinci, amma duk tabi ta rameh kaman ba hutu take kullum bah, tayi wani haske,

"Ina kwana Mama" mama ta amsa mata da lfy,amma bata ba ta fuskar cewa wani abu bah,

Gdan taji tsit babu kowa sai tayi kasadan tambaya,

"Har sun wuce aiki neh" Mama ta kalleta sai tayi saurin yin kasa da kai,

"Sun na Abuja" Gabanta ya fadi, har idanu ta fiddo waje,

"Yau Arba'in din Hajia Laila, Kakar mijin ki" Hannu ta dora saman bakin data bude, bayan tace inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,

"Allah yaji kanta" Mama ta amsa da Amin,
Tana shiga daki ta fara neman number dinshi a contacts dinta, dan ya dade da fita daga speed dial,

Da ba'a dauka bah har call din ya tsinke sai tayi mai Text, duk da da baki taso ta fada,

Zama tayi tana tunanin Hajia tare da yi mata Addu'a,

" meh kakeyi anan?" Dan duka ta kaimai kafin ta wuce shi ta karasa cikin falon,

"Haka na koya maka tarban baki" Amyr da Haider suka gaishe da Mom data zauna tasa aka kawo masu ruwa,

"Mom tace muzo mu rakaka dauko matarka taga kaman tsoron zuwa kakeji" harara ya aika ma Haider dan ya saba cemai tsoron mata yakeyi,

"Mom?" Ya kira sunanta da tambaya,

"Naga baka da niyyan dawo min da diyata neh"



Please Login or Register in order to submit comment