Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tambayi mamanta akan hanyar komawar su gda

"Kin girma ai Asma'u, kuma ansa maki rana,babu wani abu da yayi saura yanxu ai" tunda aka tuna mata ansa rana ta fara inna lillahi a cikin ranta,har suka isa gda lokacin ana kiraye kirayen sallar asuba bata ce komai bah

"Maman Husna, ya matar da zata haihu din" mahaifinta dake zaune yana jiran su dawo ya tambaya
"Ta sauka lfy, an samu ta mace" yace Alhamdulillah, Allah ya raya kan tafarkin musulunci ya kuma sa Albarka
"Itama a ranta tace Amin" kafin ta shiga dakinta dake tsakanin na mamanta da babanta,

Kwance take saman sallaya tana kokarin yin azkar amma tunanin abinda ke damunta ya hana

Tun 2 da wani abu na dare ta tashi daga bacci sukaje amsar haihuwa,gashi yanxu har garin Allah ya waye amma bata ji alamun bacci bah a idanunta

"Asma'u" ta amsa da na'am da sauri jin babanta ne ke kira

"Ina kwana Baba" yace lfy lau
"Jiya malamin islamiyya yacemin wai kin daina zuwa,meh yasa?" Ta dukar da kai badan tana da laifi bah sai dan ansar zata tadamai hankali

"Meh yasa baki biya kudin makarantar bah dana baki,gashi yace kun kusa fara jarabawa" ta dan dago da murmushi

"Yo baba gani nayi muna da malamai a gda,kuma zasu iya koyamin batare dana biya kudi bah,shine na bah mama kudin aka siya kayan cefane"


Ta zauna kusa dashi saman tabarmar shi,
"Koh kai ai saika dinga koyamin kafin kaje wurin aiki koh" yayo murmushi

"Jarabawar shiga sabon aji zakuyi fah" wannan karon itace tayi dariya
"Mune ajin katshe fah Baba, kuma ai duk kowa yasan da ina nan za'ayi jaraba war duk saina kadasu" babanta yayi dariya
"Wannan haka yake Asma'u ta akwai hazaka da kokari,babu meh iya kayar dake" tayi murmushi

"Gashi wannan, mamanku naji tana cewa bakiyi ankon graduation dinku bah" tayi kaman dama abun ba damunta yayi bah

"Baba wai kaga ankon ne,wani yellow, so suke duk inda mukayi abimu da kallo koh meh" ta sake sashi dariya

"Gashi abinka baba,ka manta dasu dan ni bazan sa yellow wal wal bah" ta linke mai kudin tasa cikin aljihu

"Duk da haka dai ki dinka wani kayan,graduation dinku ne ya kamata a ganki da sabon kaya,koh ba haka bah"
Karshe dai saida ta karbi kudin kafin ya tafi wurin aikin shi

"Kar a taba kudin nan Asma'u, yanxu da an fasa dubu zaki ga sun kare,ki bari in ya dawo sai a karba a siyo sugan"
Ta mike tsaye ta dauko 2k sannan ta cire k,

"Mama kin san ban damu da siyan wani kaya bah koh,in na siya mah sai an chargi kudin dinki"
"Bari in siyo da kaina,dan Allah in kunun ya huce bazan sha bah" ta zari takalminta dan dama akwai hijab jikinta sannan ta tafi siyowa

"Salam, ga Abba ya dawo"
"Abban ya bari a ansa sallama kafin ya shigo koh" matashin ya karso ciki da murmushi

"Kuma wannan sallamar batayi bah" bece komai bah sanadiyyar ido hudu da sukayi da cup din kunu da Asma'u ta rufe kafin ta fita

"Abba dan Allah ka aje mata kunun nan, koh aikin gdan nan aka barka dashi ya ishe ka balle a hada da wanki". Ya cigaba da sha ba sugar aciki

"Mama, Asma'u fah waliyya ce koh bataci abinci bah bata jin yunwa". Ya cigaba da sha
"Tace maka" saida ya shanye tas sannan ya aje cup yana ma mamansu murmushi

"Ni nasan bazaki bari in shanye bah da shikenan" ya fiddo makullin napep din dake aljihun shi sannan ya gyara zama suna tattaunawa da mahaifiyar shi

"Salamu Alaikum" ta shigo harda tuntube garin sauri
"Mama wallahi har jiri nake gani" Mamanta tayi saurin mikewa dan debo mata wanda yayi saura a kitchen

"Ya abba bah yanxu ka dawo bah" yace yana zuwa sannan ya fita
"Gashi kisha wannan duk da baya da wani zafi sosai, Abba ya shanye dayan"
Ta karba sannan tasa sugar din
"Ina ya shiga kuma?" Mamanta ta tambaya
"Wai yanxu ze dawo"

Kwance take saman cinyar mahaifiyarta Abba ya shigo

"Yanxu koh sallamar babu" ya dafe kai
"Kuyi hakuri mama, ina ta sauri in kawo muku wannan" ya mika musu ledar daketa kanshi

"Meh ya sameki ne Asma'u, naga sai rumtse idanu kikeyi"
"Cikinta ne yake mata zafi,kasan ta da wasa da cin abinci,kila shi yasa cikin ya daure"
"Sorry sis"

"Tashi kici abinda na kawo maki" da sauri ya dagota zaune
"Koh kefa,gashi"

"Nagode yaya"
"Ke good girl ce ai shi yasa" ta cigaba da cin wainar kwai da indomie din daya kawo mata

"Gashi mama" ya fiddo kudin dake aljihun shi
"Zan aje rabi kema gashi" ya mika mata kudin daya samo daya je aikin shi

"Yau kayi ciniki ne haka" da taga naira 3500
"Wannan da nake kaiwa makaranta kullum tayi nata biyan bashin,kuma na dan kai mutane wuri meh nisa
"Allah yasa Albarka toh" ta cire dubu daya ta linke dubu biyu
"Gashi wannan in kinji sauke sai ki dinka hijabi dashi"
Asma'u ta dade tana kallon kudin kafin ta karba
"Yaya zaka saukeni a kasuwa koh in zaka fita yanxu"
"Har cikin ya daina ciwo" tace eh tana cin abincinta
"Kila dama ba kunu yakeso bah sai kwai" tayi dariya.


Ku biyo mu dan jin yadda labarin ze cigaba da tafiya, taku har everyday KHALEESI da NOBLE JUDGE.😘
[3/9, 10:55] β€ͺ+234 706 870 0853‬: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


0⃣4⃣.

Asma'u Musa diya ta karshe ga Fatima bintu da Musa Wada, Yarinyace natsatsiya data gaji muutunci da hakuri daga iyayenta biyu, banda haka akwaita da zurfin ciki,sannan ya kamata da kamun kai,

Allah ya azurta iyayenta da yaya Bakwai, Kabir, Maryam,Abba, Aina'u,Mukhtar, Siyama sai Asma'u,
Acikin mata ita kadai ce keda rai,sauran Allah yayi masu cikawa tun kan su cika shekara a duniya,

Shi yasa da Allah ya azurta iyayenta da ita a lokacin da basa tsammani, suka kula da ita fiyeda yadda sukayi ma duka yayensu, a cikin yan uwanta ita kadai ce keda certificate na gama rigakafi
Sun san cewa duk abinda sukayi baze hana mai badawa ya anshe bah,saidai cikin ikon Allah gata ta girma har ta gama secondary school, gashi cikin ikonshi ya kawota wannan rana na SSCE graduation dinta,

"Da babban murya kuma da farin cike zan kira sunnan nan na gaba, wannan kyauta ba tun yau akayi niyya kuma da tana din bada ta bah, dalibai wannan kyauta tun da makaranta tayi muku jarabawar MOCK aka yanke shawarar bada ta". Dalibai kowa aka sunna kai ana jiran aji wanda za'a kira duk da dayawa sun ayyana koh wacce za'a bah

"Without further a do zan kira Tsohon V principal din makarantar mu dan ya bada wannan kyauta, Mallam Musa Wada, dalibar data ci wannan kyauta Asma'u Musa Wada"
Ko ina ya hautsine ana rafraf rafrafπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»

"Yau in muka koma gda saina zaneki" kafin mamanta ta barta ta tafi

Ba tun yau bah Asma'u ta saba karban kyaututtuka,saidai bata taba karba directly daga babanta bah dan haka hannunta har kyarma yake

"Congratulations daughter, am very proud of you" saida dan tears ya tsiyayo mata,
Wani mutum dake can gefe cikin guests of honor ya taso ya bata kyautar 5k,dan da wuya a bada kyauta biyar a na shida ba'a damka mata bah.

Duka yayyanta suka baje a tsakar gda ana bude presents🎁,

"Ni banga meh kyautar bah" tana jin muryar babanta ta budo dakinta data kulle da πŸ—,sannan tayi gudu taje ta tsaya kusa dashi

"Wannan baze hana in dukeki bah ai"
"Toh fah? Waze duki autata"
"Ina abun duka anan mah" sukayi dariya da yaya Kabir yayi magana

"Koh ka shi ce yau saina zane, kina son sa mutane jin kunya cikin taro". Babanta ya dafo ta

"Meh tayo ne toh"
"Uhm,meh nayi" ta noke jikin Baba tana tambaya

"Wai na aiki yarinyar nan kasuwa ta siyo atamfa,kasan meh taje ta siyo, ji yadda mutane suka taru amma ace baka da suturar kirki"

Ta kalli babanta dataji yayi shiru bece komai bah

"Baba hijabi fah na dinka da duka kudin" sai taga yayi murmushi
"Dogaye har kasa mah" ta kara dan tasan yana son haka

"Yo dan wannan sai a hana diyata sakat, hijabin datasa har kasa ai tafi mutunci fiye da duk wani sabon atamfa da zata sa"

"Hijab zata dinga sawa kenan,yanxu da za tayi aure ya kamata_____"
"Inna lillahi wa inna illahir raji'un" duk suka kalli yaya Abba, duk hankalin su yaso tashi
"Waya ne special kyautar, smartphone πŸ“² kuma kaman galaxy". Ya kankame kwalin a kirji

"Yaya mugani" batama san ta rarrafo zuwa inda yake bah
"Yan makarantar nan ne zasu bada kyautar waya kuma galaxy, kila dai turaren nan ne meh hoton galaxy"
Yaya Abba da Asma'u suka daina kiciniyar wanda ze bude kwalin

"Har na hango kaina ina buga temple run" Mukhtar ya karbi kwalin su kuma suka hau yi mata dariya

"Matsalar ki kenan temple run" inji ya Abbah

"Turaren na zuwa da charger ne" Mukhtar ya daga masu dan su gani

Ihu ta kwada harda tsalle,dama kaman mama na jira saita kwada mata duka data kusa da ita

"Ihu ya kamata kiyi ba"
"Dama dai kince sai kin duketa" in ji baba

"Gsky yan makarantar nan sunyi abin kai" cewar baba, su yaya Kabir kuma aka goya mai baya

"Naji dadi wayana ze huta da hannun ki" ya fada yana kokarin kunna mata
"Yaya Abba,sai bayan awa shida yana chaji kafin a kunna, ina so batteryπŸ”‹ dina yayi karko" ta kwace

"Kenan kin daina wanke min kayan kwallo tunda kinyi waya" sai lokacin ta tuno idan tana son latsa wayar Mukhtar saita wanke mai kayan kwallon shi wata rana harda πŸ‘Ÿ take wankewa


"Hah, nama manta wallahi, nayi wuce nan yanxu"

"Kawo ai ba'a ce zaki iya amfani dashi bah" duk sukayi tsit ita kuma har eyes sun cika da tear
"Baabbaaa" ya mika mata
"Wasa nakeyi maki,sarkin kuka" tayi wani ajiyar zuciya da kowa yaji.


"Mama,wai ina Asma'u, har na yi tafiya meh nisa Kaka tace in dawo in kira mata Asma'u"

"Yaya Mukhtar meh yasa baka kira wayata bah,koh ka manta" tayi show din fiddo wayar

"Kinji sakon koh" mamanta ta fada baya Mukhtar ya tafi makaranta

"Eh Mama yanxu zan tafi dana ida goge maki kayanki" mamanta shiga dakin
"Aa Asma'u zo ki tafi,ni na karasa gugan"

Gdan su be da wani nisa dana kaka, tafiyan baze wuce na 15 minutes bah,
"Aslm" taji ana mata sallama
"Wasalam" ta ansa tana kokarin cigaba da tafiya
"Asama'u dama inta so inyi magana dake"
"Eyyah,kaga yanxu kan hanya ne kuma ana jira na ne" ta cigaba da tafiya
"Toh Asama'u zanzo in sameki" ita dai ta cigana da tafiya

'Wai Asama'u, daga na kawo chaji sai ka wani nacemin,kuma ai bani nace kayimin kyauta bah kai kaki karban kudi, dan haka karma ya zomin da wani shirme'. Ita kadai tana tafe tana zantawa da ranta

"Salamu Alaikum"
"Kaka,gani nan ma iso___" tayi kicibus da tulun wanke wanke a wurin maguji

"Sai yanxu uwar taki ta gadamar turoki" ta cire hijabi dan tasan aikin baze wuce wanke wanken bah

"Baki kikayi ne kaka, naga kwanuka dayawa" ta yi kaman bata lura da kaka ta daure fuskarta bah

"Ki fito kiri kiri ki tambaye ni basai kinyi min wani kwanare bah,

"Yi hakuri kaka, nayi shiru" kaka tayi tsaki

"Duk cikin mata ya rasa wacce ze jajibo sai ke, gashi yanxu an tsaida rana amma baki da kayan daki" jitayi kaman an dora mata kasala a jikinta, wanke wanken mah kaman marar lakka haka takeyin shi

"Cewa nayi ki tafi in kin gama da zaki wani sunna kai kina tafiya, dan rashin tarbiyya koh sai anjima baza ki iya zuwa kice min bah, kina nufin saidai in nemeki in rasa koh meh"
"Yi hakuri kaka hankalina ya koma gda ne" kaka tayi tsaki

"Zakije ki kitsa mata abinda ya faru koh, kiji dadi mah yaro kaman jikana, salisu dina ya nuna sanki"
Duk da ranta bace yake saida tayi tsaki a ranta
'Allah ya kara manah maza irin ka baba a duniya, da kake hakuri da kishiyar uwar nan taka, wani salisu dina, ki rike abinki manah'

"Gashi cewa yayi in baki" ta miko mata waya, ita kuma tayi kasake
"Kin ji yar iskar diya,bazaki sa a kunne bah" ta dan hambareta

"Asma'u ta ya kike" ta juya idanu
"Wa'alaikumus Salam ya riketa, har sai ance Salamu Alaikum kafin ya sakota" taji ya babbake da wani irin dariyar da yasa ta cire wayar daga kunne tana yatsina face

Daga idonta sukayi 4eyes da kaka
"Bari in ansa a waje" ta tashi simi simi tayi waje

"Asma'u kina nan"
"Uhm hmm"
"Kina burgeni Asma'u, wannan jan ajin naki yana sa sanki kara shigata har cikin kashi na"

"Ana jira na a gdanmu,kuma zanyi mah kaka wasu yan ayyuka,ka fadamin abinda yasa ka kira"
"Sai akwai dalili kafin in so jin muryar masoyiyata" ta dafe goshi da hannu daya
"Kuma akwai dalili mah, yau babban ranace gareni, an samin rana kuma na fara aiki a babban gda,karki so kiga gdan"
'Allah ya tsare su daga halin ka toh'

"Yayi kyau toh sai anjima" zata kashe ya hadata da Allah ta saurare shi sai ta tsaya

"Nan da sati daya za'a kawo lefe, next week kuma in an daura aure zan zo in tafi dake ". Cire wayar tayi daga kunnenta tana jan numfashi wani kan wani, hawaye na tsiyaya kaman famfo aka kunna

"Gashi kaka ni zan wuce" ta mika wayan,kafin kaka ta karba ya silbe ya fadi kasa, bin wayan tayi da guiwowi zube a kasa ta hada wayan sannan ta mika mata, dungurinta tayi kaman kanta ze balle daga wuyanta

"Yar bakin ciki" da gudu ta bar gdan, sannan ta share hawayenta da kyau dan karta jawo ma kanta mutane

"Ina masallaci sakon kiranta ya iso, danaje na iske sun kawo goro, dabino duk dai abinda ake sa rana dashi"
Mamanta ta cire tagumi sannan ta mayar kuma

"Baka roki alfarma a bamu lokaci bah, dauren aure nan da sati biyu, koh na shirya komai ai na bukaci lokacin daya fi haka koh"
"Na fadi haka amma kaka tace wai bata bukatar shawarata,kuma tasan menene ya kamata"

Ji tayi kaman muryar mahaifiyar ta ya canza zuwa na meh kuka"

"Gsky ni ban shirya bah,in baza su daga bah toh a fasa"
Dakin mazan daki soro ta shiga taci kukanta harta gode Allah.

"Meh yasa baka zo Airport taro ni bah, ni best friend dinka"
"Am so sorry Ehsaas, Akwai reasons dayawa da ban samu daman zuwa bah"
"Fadamin dukkan su inji toh" yaji tsit

"Welcome to Nigeria Ehsaas" Haider ya kashe mai baki

"Nagode Haider ina fata it won't be long kafin in samu in ganka"

"Ai muna kasa daya yanxu,zanyi kokari in ga Nigeria bata gimshe ka bah"
"Tnx man I'll see you"


Late post sorry,πŸ™‚, sai mun hadu a nxt page.
[3/9, 10:55] β€ͺ+234 706 870 0853‬: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


0⃣5⃣.

Kujera tsugunne dake cikin dakin taja ta zauna, sannan ta dan dubi inda mamant ke zaune

"Mama gani" taga dai kallonta kawai takeyi

"Meh kika tsaya yi a waje da wani bayan kin san ansa maki rana" ta danyi murmushi

"Mama kinsan tun kafin ayi wannan abun ni ba kula maza nakeyi ba koh"
Uhmmm kawai mama tace
"Wai a makaranta ya ganni ranar da akayi graduation, shine ya tambayi address din gdanmu aka kawoshi"
Yadda take maganan kaman abin dariya yake bata

"Ke kuma kika cemai meh" bata bada ansa bah dan bata iya mah cewa ansa mata rana saboda tsananin kin abin da takeyi

"Ya za'ayi gameh da anko, zaki je ki nemi kawarki ne sai kuje ku fiddo"
"Mama ni fa tsakani da Allah " ta fashe da kuka
"Nima ba yadda na iya ne Asma'u, kiyi hakuri kinji,kuma ki cigaba da rokon Allah ya zaba maki mafi alkhairi kinji"

"Mama ni koh kayan daki mah karki wahalar da kanki dashi,tunda su suka matsa ayi sai suyi kayan dakin" dariyar da mamanta tayi itama shi yasata dariya

"Ai koh bashi ne naci in yi maki kayan daki Asma'u, ko da kuwa zasu sawwake manah"
Ta danyi kasake tana kallon mamanta, daga jiya zuwa yau harta rameh kaman wacce tayi ciwo

"Mama dan Allah ki daina damuwa da abin bikin nan kinji, dan Allah ki cire shi daga ranki" a hankali take maganar kaman nasiha takeyi mata

"In ba auren nan aka daura bah koh aka fasa Asma'u hankali baze kwanta bah" tayi murmushi dan tasan duka yan gdan babu wanda keson wannan auren

"Kin tunamin mah Asma'u, ina jira a kawomin kudin adashe in hada da abinda babanku ya kawo jiya in je kasuwa inyi siyayya, koh akwai abinda kike so sai ki fadamin koh in baki kudi ki siyo" girgixa kai kawai tayi

"Karki damu zan tabbatar na siyo duk abinda kika bukata, in na dawo mah ina tunanin zuwa gdan hajiar nan in samo kudi, bayan aure in dinga yi musu aiki dan in biya"
Mama ta tashi ta dauko wani jakarta dake rataye tana fiddo kudi
"Kin san tana da mutunci matar ba ruwanta"

Tashi tayi tana kuka ta bar dakin, bata zauna bah taje tayi alwalla ta dawo tana ta sallah, karshe data kwanta sai wayarta tayi vibrating, tana daukan wayan ta danyi tunani na lokaci kadan kafin ta bude ta cire sim dinta dake ciki

"Sis zaki sani cikin matsala idan Baba yaji" ta girgixa

"Yaya Mukhtar baze sani bah, dan Allah i need to help my parents somehow"
"Kuma wedding dinki ne, ya kamata ki bada contribution" yaya Abba da tun daya ji abinda takeson yi ya koma gefe dan kar a hada dashi in Baba ya sani

"Karki damu Sis, ki aje phone dinki zamuyi aiki twice as hard dan ganin komai ya daidaita"
Ta girgixa kai
"Na rigada na yanke shawarar sayarwa"
Yaya Abba ya matso
"Sis in kinaso ki taimaka, kisa a daga bikin" ta kalleshi confused

"Ni,? Ya zanyi in hana?" Taga suna kallon juna

"Come on sis, sai mun gaya maki plan" ta cigaba da kallon su, yaya Mukhtar yayi murmushi yana jawo pillow
"Wannan good for nothing din zaki sa ya daga, in dai har yace a daga am sure kaka ma zata yadda a daga"

"This is a good plan, too bada bazan iya sawa yace ya fasa bah" ta daga wayar tana mika musu
"But still ina so ku sayar da wayar"
"Hey Asma'u"
Amma ta cigaba da tafiya abinta,

Washegari bayan ta gama duk ayyukanta na gda, koh abinci bata ci bah ta shirya dan zuwa gdan kaka, tun abakin kofa take murmushi tana kwala mata kira

"Kaka, wai ina kika shiga ne" kaka ta fito daga dakinta da asuwaki cikin bakinta
"Wannan zuwan naki bana arziki bane bah, tunda har kikazo ba tareda na aika a kiraki bah toh na tabbata munafurci ya kawoki"

'Kaka kenan' tace a ranta sai ta shiga ta mika mata kullan data kawo

"Wannan jiya aka kawomin daga gdan Aliyah, kan rago ne ta kawomin saboda kokarin danayi lokacin data haihu" ta fada da fara'a tana mikamata

"Allah yasa mah kin iya dafawa bah shirme zakije kina kwaba mah jikalle na bah"

Ta zauna saman tabarma tana budewa
"Kar kije kinayi mai asara bayan ya sha wahalar nemowa" tana mata fada tana sa yatsa ciki tana tsamowa

"Jiya yake cewa ze turo kudi dan ayi lefe" Asma'u ta tabe baki
'Naxata ke ze bari da wahalar komai ai' amma a fili tace

"Yana dai san ya saki wahala ne kawai"
Kaka ta girgixa kai

"Aa gwara ya turo kudin dan in san abubuwan daya dace asa cikin akwatin"

'Koh a ina ze samu kudi, daya zo zaria ba aiki yake dashi bah, haka daya bar nan garin ba aiki yakeyi bah, farat daya kuma ya samu aiki harda aure' ta gyara zama dan jin in halin data sanshi dashi yana nan har yanxu

"Kaka ya fadamaki aikin da

Please Login or Register in order to submit comment