Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin girgixa kai, muryar hajia ta katse ta

"Sai abincin yayi sanyi tukunna,
Nasan ba wani cin abinci kikayi sosai bah"
Tace toh, zata tafi Mom ta dawo da ita baya

"Sha tukunna" ta dukar da kai tace basai tasha bah

"Wasa nakeyi kenan" ta sake girgixa kai

"Banda dalilin yin karya" sannan ta kyaleta

"Morning" yana bakin kofa ta bi ta gefenshi ta wuce, duk da yana ce mata Hey

"Yarinyar nan zata jamin magana, yanxu sai yace wani abu nayi mata" inji Mom da suka fita

"Husna!" Ya biyo bayanta,

Yadda take tafiya kaman jinita ya daskare, har wani bari takeyi

"Meh Mom ta baki" ya sha gabanta

Yar kara tayi tana cewa NO,

"Am hungry, bari in aje sai mu tafi" yace toh yana bata hanya

Cikin bag din da take aje littafin da maida diary ta saka,

Yini tayi a cikin daki, tana sake sake a ranta,

'Gani sukeyi in kai talaka ne ka auri meh kudi, baka da wani abu da zaka karo masu saidai ka rage masu'

Maganin da ta bata beh wani sha mata kai bah, dan bataga amfanin shi na zuwa bah,

Gskyr Ma'u ne, zama haka nan bege kowa bah,

In ba karatun a rungumi sana'a, ba wanda ze maka kallon banza in ka dogara da kanka,

Tana so ta cigaba da karatun ta , amma ba a gdan nan bah,
Karta jawo ma kanta wani surutun,

Mikewa tayi ta jawo wayarta dan sanin komai gameh da Maganin da aka bata,

Ella Control pill, ta rubuta, saiga abubuwa dayawa akai,

Emergency taga ana rubutawa a kowani article,

Sai ta zabi wani ta shiga,

Na shane bayan saduwa ba tareda kariya bah, koh baki koma mah allurar ki na tazarar haibuwa bah, koh maganin ki na tazarar haihuwa ya kare kuma kinyi having sex,

Ko wani hanya dai na taxarar haihuwa, Ella pill emergency ne, bana sha yau da kullum bah,
Ba'a yadda mah a dinga shan shi, a matsayin hanyar family planning bah,

Dafe kanta tayi tana tambayar kanta, meh yasa ta bata in tasan ba wanda aka yarje ayi Tazara dashi bane,

Illolin maganin ta karanta, abubuwan da zasu iya samunta, in ta sha,

Searching din abinda ze sameta in ta cigaba da sha a matsayin family planning,

Ko ina dai nuna wa sukayi, ba'a son ayi haka,

Screenshot din maganin tayi, tana shirin mikewa ta dauko wanda aka taji sallamar shi,

Tun dazu yake zuwa akai akai, yana dubata,
Abincin rana dana dare duk shi ya kawo mata daki, kuma da an kira sallah ze zo ya fadamata,

"Bakiyi bacci bah" tace Eh,
"Surfing net nakeyi" ya hau saman gadon, amma ya bar fili a tsakanin su,

"Meh da meh kikeyi" fita tayi daga Google ta shiga NeWS,

Tare suka cigaba da karanta kanun labarai, saida tayi hamma sau biyu sannan ya mike yana mata sai da safe,



Yasan ba bacci zatayi bah, in dai yana daki,

Cusa hannuwa yayi cikin kanshi, yana
"How is this possible" harda watsar da pillow da bargo kasa,

Ipad dinshi ya dauka yayi waje dan ya sha iska,

Saman kujeru dake waje ya zauna shima yana surfing net,
Yana cikin latse latsen shi ya tuno, doctor din da suka taba magana tare dashi, ga meh da rasuwar yayar shi,

Email dinshi ya shiga sannan ya sender mah Dr din message,

Take Yayi replying dinshi, da akwai condition haka, ' Sexual Aversion'

Idanu ya fiddo waje, sai lokacin yake ganin seriousness din matsalar su,

Tambayan likitan yayi in ya kirashi a lokacin,
Sai yace mai Aa, yana da conference cikin minti 3,ajiyar zuciya yai,
At least yanxu tasan wani abu akai

Tashi yayi yana
Zagaye compound din nasu, har ya kai bakin gate,

Wani inuwa ya gani ta karkashin gate,

Tafiya akayi kuma aka sake dawowa, amma ba knocking,

Kasada yayi yace waye a wurin,

"Meh ze hana ka bude ka gani"
Juya idanu yayi yana girgixa kai,

CCTV din wurin gate din ya kalla, sannan yayi mah securities dake, camera room, alaman su bude gate din,
Tunda Automated ne , gate din na fara sliding yasa kai ze fita shima yasa kai ze shigo,
Karo sukayi, har ya saki iPad din,

"Ouch" Amyr kam be nuna yasan sunyi karo da juna bah,

"Bina kakeyi koh meh, cikin dare haka"
Amyr ya daga mai gira daya

"Kai din ba wani daukan hankali gareka bah,
A nan unguwan nake nima" ya nuna mai wani gda acan farkon layi,

"Shi yasa nine emergency doctor dinku ai"
Kallon juna sukayi na dan lokaci kafin kowa ya kauda kai

"Meh ya fiddo ango cikin daren nan haka" ya fada da dan dariya

"Oh ashe kasan nayi aure"Amyr ya dan sosa keya

"Bana gari akayi, amma naji labarin, congratulations"
Yace tnx

"Kana cikin cousins dina neh"
Dariya meh kyau Amyr yayi

"Ni nafi karfin cousin dinka"
Ya daga gira shima yana da gaske

"Sosai kam"
"Ya sunan mahaifiyar ka" murmushin Amyr ya dauke,

"Ya sunan taka gyatumar" yace Safiya
Sai bayan dan lokaci Amyr yace
"Hannah" yana dudduba IPad din hannun shi,

Shi kuma ya jin jina kai,

"In ta samu matsa ka kawo in sake maka" latsa tsakiyan yayi, take ta kawo haske,
"Oh!" Yace yana karanta email chat din da sukayi

"Mind your own business" yana fizgan ipad din ta sake faduwa

"Sorry wannan duk fault dina ne" Amyr din ne ya rigashi dauka kuma

"Ni dai ince Ango cikin daren nan, da walaki goro cikin miya"

Ehsaas ya karbi pad din amma yaki bari su hada ido

"Meye dalilin ta na shiga wannan halin?"

kana kallon shi kasan yasan abinda yake magana akai,

Bece mai komai bah, dan baze fadi sirrin shi da matar shi ga dan uwan da beh sani bah, dama Haider ne toh da sauki,

"In ta samu matsala, ka kirani ta nan"
Ya bashi wani complementary card, meh dauke da
Shahid Muh'd Kawai aka rubuta a jiki, sai number dinshi,

"Heads up" yana daga kai ya wurgo mai wani dan karamin kwali,

"Kings kawai keda diamond irinshi"
Azurfa ne meh wani katon diamond amma baki,
"Kuma kings kawai ke sawa,
Happy married lfy"

Ya bige da kallon zoben beh san Amyr har ya tafi bah,

Washe gari bayan ya shirya ya dauki zoben zesa,
M.M.M yaga an rubuta ta cikin zoben,
Hmmmm yace hade da murmushi,

Yauma jallabiya tasa, saidai na yau yana dan budewa, gashi kuma baki da kwalliya Maroon, gyalen data yafa ma maroon,

"Kinyi kyau" tace tnx sannan ta duka ta gaishe shi

"Stop that Husna, sai kisa inga kaman na tsufa"
Hmmm tace tana barin dakin, shima kuma ya biyota a baya yana fara'a

Suna zuwa falo ta duka ta gaishe da Mom da Hajia,
Shima sai yayi haka sabanin da da yake gaishe su da hugs da pecks,

Hajia yar dariya tayi, mamanshi kuma ta daure tana watsa ma Asma'u harara,
Tare suka garzaya dinning table




"Mubarak?" Kowa saida ya razana ballantana shi da sunan shi aka kira,

"Meye wannan a hannun ka" ta fada idanu waje kaman taga ajalinta,

"Ahmmmm"
Kafin yayi bayani tace ya cire da katuwar murya

"But why"
Tace meh garin ku da wai,

Dunkule hannun shi yayi, yana maidawa karkashin table,

"A ina ka samu wannan zoben"
Nan yace Amyr ya bashi jiya

"Ya akayi ban san ya zo bah"
Ya sake fada musu haduwar su

"Ya ilahi Ehsaas zaka kashe da shirmen nan naka,
Meh yasa mah ka karba, abinda ya kamata ka wurga musu a fuska"
Asma'u taji ina ma kasa ta hadiye ta,

"Meh ze hana ya ajiye zoben" Hajia ta fada,
Kafin wani yayi magana ta silale ta nufi dakinta,

"Waya san tsibbu da siddabarun da akayi mah zoben kafin a kawo"

"Lfy ina ta sallama baku ansa bah" ya bada briefcase din daya shigo dashi aka wuce dashi sama


"Stupidity din danka manah"
Ta bashi labarin komai,

"Ehsaas, ya zaka fita tsakar dare" mamanshi tayi tsaki

Sorry yace a hankali
"Sorry won't do, am so mad, ya za'a yi kasa ba tareda ka nunamin bah"

"Ya bar zoben manah in yana so, ba wani abu bane bah"
Inji babanshi,

"Yes, nasan Yarima ne zesa a kawo"
"Nama fi tsanar zoben nan yanxu,
Tunda daga hannun butulun nan ya fito"

Hajia tashi tayi suku ku ta bar wurin

"Safiya ki bar maida abin nan babba, kodan mamanki, kin san halin da take ciki"

Laifin waye toh, ta fada danidanun da suka ciko da hawaye,

"Plan dinsu kenan ai, kuma sunci nasara tunda sun sa kun juya min baya"
Ita tayi sama fuuuu,

Cire zoben yayi ya aje saman table,

"Sannu da zuwa dad" ya hada da dan rungumeshi kafin ya wuce sama,

Ya saba sai ya ba mamanshi hakuri in abu irin haka ya faru,

Ranar sai yaji, wani lallashi na daban yakeso, wanda ya fito daga wurin matar shi,




⚜B.W.A🖊

⚜B.W.A🖊




💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
BOYAYYEN KUDIRI.

💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐


Story, Editing by,
ⓝⓞⓑⓛⓔ ⓙⓤⓓⓖⓔ.
Writing,
ⓚⓗⓐⓛⓔⓔⓢⓘ.


⒟⒠⒟⒤⒞⒜⒯⒤⒪⒩ ⒯⒪

Wannan page sadaukarwa ne ga victims din abuse, bayin Allah da suka fada hannun mugayen mutane,
Wadanda akayi ma fyade,
Wadanda suka rayu karkashin azzalumai,
Koh suka dan dani azabar kishiya koh matar uba,

Allah maji kan bawa ne kuma baya bacci,
Sakayya tana wurin shi, shi kadai,

Allah ya tsare kuma ya kare mu gabaki daya.
Amin.




4⃣8⃣.


Yana bude ido yaji wani kanshi ya daki hancin shi,
Kara shaka yayi sannan yayi murmushi daya ga tray a saman drawer din dake kusa dashi,

Yana tashi zaune ya jawo tea din ya sha, sannan ya jawo tray din saman gado,

Pancakes ne da fresh banana da strawberry, sai caramel da aka tsiyaya a gefe,

Saida ya lashe lips dinshi kafin ya kai first bite,

Duk wani bacin rai da takaicin dazu ya washe,

Yana shigowa dakin ya sameta tana rubutu, tana ganinshi ta aje, sannan ta matsa mai ya hau saman gadon ya kwanta ruf da ciki,

Basu ce komai har ya gama hawayen shi,
Cikin bacci yaji tana shafa mai baya da kanshi,
Sannan ta ce komai ze daidaita in shaa Allah,


Yana gama cin abinci yaga wani paper a saman pillow,

'Granny ma da Mom sunzo kana bacci'
Ajiyar zuciya yayi, dama yasan abin beh kare bah,


Saida yaje yayi sallar dhur kafin ya nufi dakin iyayenshi,

A parlor yayi sallama sannan ya shiga, yar karamar dariya yaji na tashi, yana tunkarar kofar kuma yagan su suna 💏😚,

Sha tale tale yayi yana farin ciki,

Ba sabon abu bane bah fadan iyayen nashi,

Amma tun rasuwar yayarshi suka daina, sai kuma yan shekarun nan da suka wuce shine abin ya dawo,

Amma kanar kullum basa dadewa suke shiryawa,
Ba alfahari yakeyi bah,amma yasan babanshi ke neman sulhu, dan Mom dinshi akwai daukan zafi


"Shigo Ehsaas" sake sallama yayi kafin ya shiga

"Bata baka bah har yanxu" ta fada tana duba yatsun shi

Dan murmushi da hakora basu fito bah kawai yayi

"Naji tana neman ka ta baka"
Yace mata yayi bacci ne

"Bata bah Asma'u ta ajemin bah"

Hajia tace hmmmm
'Taba Asma'u ta aje maka kace, so take ai ka nuna mata farin cikin ka,
In ta ba Asma'u kuma, ai ita zaka nuna mawa'

A fili kuma tace kasan waye Amyr cikin yan uwanka,

Kasa fada mata yayi, dan duk lokacin data tuna baya ,Hanna yake jin tana ambato,


"Na fada maka dama a family dinmu auren cikin gda akeyi, ba'a nemah a waje,

Haka ni da kakan ka, mu muka sasanta kanmu ba hadamu akayi bah"
Fuskarta kaman ta fadan cikin tunanin da yasata annashuwa,

" Saida mukayi shekara 7 bamu samu haihuwa bah, ta ko ina ana cewa ya kara aure amma yaki,

Cikin ikon Allah muka samu Yarima,
Bazan taba manta irin murnar da yayi bah, saida muka kara wani 7years din sannan aka haifi Mom dinka,

Oh Allah! Kaman lokacin ya samu haihuwa,
Tun daga sanda ya dauketa yake mata duk abinda takeso, harta girma data ce Eh toh Eh ne, Aa kuma toh Aa ne,

Dama tun can bata wani jin maganata, nasha yi mai korafi amma sai ya basar, yace yarinya ce,

In kaga Mamanka tana kokarin jawo hankalin babanta toh ya tsundumma cikin taimaka ma al-umma ne,
A lokacin ne baya jin kira,

Tana shekaru 13, ta shiga js1 dan canza mata school yakeyi datace wanda take ciki beyi mata bah,

Safiya akwai san kashe kudi, kyan kyami da Almubazzaranci,

Har abinci na daina bata in zata makaranta, dan zubarwa takeyi, koh ta yar harda cooler din mah,

Lokaci daya kuma ta fara cewa in cika mata food flask in zata makaranta,

Kuma in ta dawo zakaga alaman ci akayi ba zubarwa bah,
Change din ya bani mamaki, sai na shirya naje makarantan dan sanin dalili"

Ta dan jin kirta tana girgixa kai

"Abinda Allah yayi ze faru toh ba makawa sai ya faru,

Nayi mamakin yadda duk kyan kyami , da san nuna abu nata ne amma ta iya guduwa daga school dan ta dinga taimakon wata yarinya,

Bazan manta irin gutters da bola iri iri da muka wuce kafin ta kaini gdan da take zuwa bah,

Gdan so dirty, ba fence, ko meh kakeyi ana gani,
Muna zuwa yarinyar ta fito da gudu tana kiran sunan safiya,

Ga ciwuka jikinta, kaman bata taba wanka bah, kayanta duk sun yage, bakinta a kumbure,
Kasa magana nayi dana ganta, ashe akwai masu rayuwa haka,

Safiya tacemin ranar da suka fara haduwa, taje zubar da abincinta a gutter sai taganta tana jira,

Har muka tafi ban bar zubar da hawaye bah,

But of course da ita na tafi, ban barta anan bah,

Kodan farin cikin da safiya tayi, da farko babansu beh yadda bah, yace a taimaka mata kawai su tafi
Safiya na sa baki ya amince, tunda abinda takeso kenan"

Hajia ta dan share kwallan daya zubo mata

"Kansu daya, haka shekarun su, daka gansu kaman wasu twins gwanin ban sha'awa,

Da farko komai lfy, saida safiya ta fara kokawa mah attention din babanta, abinda da nata ita kadai ne ya zama na su biyu ne,

Bataji dadin haka bah, but tayi shiru,

With time kuma bad habits din Hannah suka fara bayyana,
Karya, sata, rashin jin magana,
Nayi kokarin rabasu da safiya, but sun rigada sun taso tare,
Koh sun bi hanya daban daban zasu dawo su jameh,

Wata rana, around 2 na dare police suka zo gdan mu,
News din da mukaji yayi shocking kowa,
Wai an kama karuwan wasu area and suna ciki, Mom dinka da Hannah,

Na kusan haukacewa akan su fadamin abinda ya kaisu but sukayi shiru,
Abinda yasa ba'a kaisu police station bah shine Zoben dake hannun Safiya, kowa yasan na king family ne, shi yasa aka kawosu gda,

Hannah bata wani ji tsoro koh bada hakuri bah, but safiya tasan babanta he's lenient amma baya daukan nonsense,
Sai yace aure zeyi musu, sai a lokacin nasan Tana haduwa da babanka bada sanin kowa bah sai Hannah,

In ta rakata wurin babanku, ita kuma ta rakata Gdan karuwai"

Hajia ta girgixa kai tana cewa so stupid ita dinnan,

"Dana tunkari Hanna da maganan cewa tayi ' nibba diyarki bace bah ai, da badan safiya bah da ina jail yanxu babu wanda ze saurare n saboda banda'

Ta nuna min yatsan ta, nayi kokarin yi mata bayani amma bata saurara bah ta tafi,

Ashe abin ya dade yana ci mata tuwo a kwarya,
Zuwa family meetings banda ita, family dinmu nada fund inda every month kowani uba yake zuba kudi saboda school din yara, koh ka rasu toh yayanka zasu zamu good education,kuma a wannan accounts din yaran mu ke karatu, amma banda Hannah
Saidai babansu ya biya mata,

Tunda dama sun girma, an fara zuwa wurin Mom dinka daga cikin family dinmu, amma banda Hannah,

Na tausaya mata a lokacin, saboda babu dadi a dinga wareka,

Mom dinka duk ta kori masu nemanta, tace ita babanka takeso, babanta beyi maraba bah, but yasan Mas'ud tunda sun fara business tare, sai yace zeyi kokarin canza masu ra'ayi shi kanshi ya fada ne amma, abinda akayi shekaru aru aru anayi,
Baze canzu dare daya bah,


Hanna kuma, ta canza gaba daya, abinda takeso kawai takeyi,

A haka har aka sa ranar Mom dinka da Wani, amma da ranar daurin aure yazo sai aka daura da kakan ka da Hannah "

Gabanshi ne ya fadi
'Ni nafi karfin cousin dinka' maganar Amyr ta fado mai a rai

'Kawun shine kenan"

"Naxata yayi hakane dan ya bude mah Safiya hanya, but No,

Mutumin daya dawo bayan daurin aure, beh dawo da halin dana san mijina bah,

Tun daga ranar Hannah ke calling shots a gdan, kuma koh safiya bata ragamawa bah,

And ta samu abinda takeso, an sata a jerin family dinmu,
Kuma aka bata nata zoben,

Ba abinda yafi bani mamaki ba kenan sai yadda manyan gdan gaba daya sukayi shiru, babu wanda yayi magana akan auren,

Abin mah ya koma sankai, tunda suka hana Safiya auren wanda takeso, amma sukayi shiru dana Hannah,

Zaman gdan ya zaman kaman cikin garwashi muke, at anytime ze iya wulakanta nashi yayan akan ta, koh ni mah beh ragamin bah,
Ga komai muna dashi amma kwanciyar hankali ya gagaremu,

Cikin halin nan ne na gano ashe Mamanta nada rai kuma harda yaya take dashi,

Mamanta karuwa ce, kuma ita take zuwa gani a gdan karuwa, yayanta kuma sai yaje ya shawo ya dawo gda da abokan shi,
Suke dukanta sannan suyi amfani da ita"

Yace Oh God! Yana rufe idanu


"Na tausaya mata danaji, kuma banyi kasa a guiwwa bah, na tun kareta dan in sanar da ita hakan baze canza komai bah,

Instead ta mareni, dan nace mamanta karuwa ce,
Kuma da ya dawo ni ya dora mah laifi, harda duka, Ya Ilahi,

Banji zan iya dauka ma kuma, sai nace zan tafi kuma a sauwake min a take,
Safiya mah tace zata bini,

Yace in ta tafi ta tashi daga diyar shi,

Yarin yar nan kunnen kashi gareta" ta fada da dan dariya

"Tace ai ta dade da tashi daga diyar shi, shima kuma ya tashi daga mahaifinta,
Har yanxu ina jin karar slap din da Hanna ta bata,

Wai bata da taribiya ya korwta kawai,

Har tsine mata yasoyi, bansan abinda yasa Hannah ta rufe mai baki bah yayi shiru,

Da zamu tafi yarima yace tare zamu tafi,

'Bita toh, kaima sokake ka nuna min ka girma, kwashe naka iyalin kayi gaba, kuma in tsine maka kai da zuri'ar ka,

Koh haduwa kayi dasu Allah ya isa ban yafe bah, yara matasa godiyar Allah'

Beyi mamaki bah data karanto kaman yadda ya faru, koh shine baze manta bah,

" Mom dinka na ganin butulci yayi da beh biyo mu bah,

Nasha yi mata bayani, amma abinda takeso ta gani shi kawai take gani"


Ta murza hannuwanta
"Rings dinmu, wasu accounts dinmu, duk aka karbe, inaga da kayan jikin mu kawai muka tsira,

Family mah suka juya manah baya dan tace zata auri babanka,

there was no stopping her bayan wannan, tare muka tafi kuma bamu juya baya bah tin daga wannan lokacin,


Duk abinda

Please Login or Register in order to submit comment