Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakeyi ne" dan koh sama da kasa zata hade baxata auri meh hali irin nashi bah

"Bari in kira maki shi sai ya fadamaki aikin da yakeyi a Abujan" dadi taji dan zata samu damar sashi canza ra'ayin shi

"Yanxu da sassafe in beh tashi bah fah" ta dan yi kaman tana jin kunya

"Shi yasa abinda yakeyi ba shirmam meh bane bah kaman yan gdan" Asma'u tayi murmushi ' ban san ranar da zaki canza bah kaka'

"Salamu Alaikum, salele saleleh" taji magana ta dayan bangaren amma ba ta tantance koh meh yake cewa bah

"Karka damu, duk lokacin daka shirya ka turomin kudin, ni zan fara shirye shirye anan"
'Ahaf! Ni dama nasan ke ze bari da duk abinda za'ayi' ta girgixa kai tana tunanin irin lfy din da zatayi da shi

"Gashi,kuma karki dade" tana karba ta fita waje

"Hello"
"Tun da safe haka masoyiya,koh kinyi kewata ne"
'Hakan baze taba faruwa bah'
"Harda tunanin ka"
Kaman tayi amai taji bayan ta fada
"Anya wannan Asma'u ce ba'ayi min chanji bah" tayi yar dariya ihi ihi
"Ita din dice daka sani" tana ganin ze zarce ta fadi abinda ke tafe da ita

"Nace bah,meh ze hana adan daga bikin nan" tayi shiru tana jiran abinda zece

"Asma'u baki kagu ki ganni bane bah,kin san yadda nakeson in ganki kusa dani kuwa" ta duka kasa tana tunanin yadda zatayi dashi

"Toh kazo ka ganni manah, amma kafin nan kasa a daga yadda zan samu time din shiryawa da kyau,kaga koh anko bana dashi,gashi aure saura sati fah" uhmmmm yace

"Ya zama dole inyi mah amaryata duk abinda takeso"
'Phew, ba fasawa akayi bah amma hakan mah da sauki ai'

"Wata nawa za'a kara"
"Wata!?, yan kwanki dai koh,Asama'u"

"Sati hudu koh" ta danyi shagwaba
"Sati daya dai koh kanwata. Amaryata, kuma uwargida tah" ta cire wayar daga kunne na dan lokaci kafin ta maida,

"Koh dan sati uku ba'a kara bah" taji kaka na kwala mata kira
"Toh sati biyu,dan Allah ka yadda" yayi dan murmushi
"Dan buso min sumbatar nan da masoya keyi ma juna manah"
"Kaka na kira" kashe wayar tayi gabaki daya dan tasan baze iya sake kira bah

"Gashi kaka nagode"
Kaman ta zari takalminta tayi gaba,sai kuma ta kasa ta tsaya tana tayata ayyukanta.


Sorry readers, page daya ne ya samu yau 😘😘
[3/9, 10:56] ‪+234 706 870 0853‬: 💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
BOYAYYEN KUDIRI.
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐


0⃣6⃣.

A hankali ya bude ido yana kallon dakin, sannan ya tashi zaune daga jin yadda ko ina yayi tsit yasan gari beh waye bah yau mah ya tashi da wuri, kaman yadda yakeyi tunda yazo Nigeria.

A Australia yanxu rana take faduwa, anan kuma tsakar dare ne, ya jawo wayar shi dan duba tym
"3: 24AM" jefe wayan yayi saman gado sannan ya sauka ya shiga ban daki

"Hello Mom" yace da ta ansa video call din
"Ehsaas my dear, ya akayi ne fuskan ka ya canza sosai, ya dan kumbura, are you okay"

Kaman zata iya taba shi ta cikin wayan sai shafa screen din takeyi tana kara kaishi wurin fuskarta

"Mom komai lfy wallahi, am just restless, naxata in a day or two zan saba but har yanxu, dana danyi bacci sai in farka"


"Meh ke damunka toh?, koh zaka dawo gda ne tunda can din beh karbe ka bah" ya girgixa mata kai

"Chanjin tym da yanayi ne mom,nothing to worry about" ta fara tafiya tana magana

"Honey!"
"Mom basai kin fadamai bah am okay"

"You're not okay son, yanxu tsakar dare ne a inda kake, maimakon bacci video call kakeyi"

Yaji dama beh kira bah,dan yanxu zasu iya zuzuta abin susa ya dawo gda

"Mom gobe grandma zata je dani office, dan in ga gari" ta dan sassauta tafiya

"Ya zamanka da umma na" murmushin da yayi ya fadamata duk abinda take bukatar sani

"Kullum muna tare Mom sai kara sanin juna mukeyi, kuma daga yau zamu fara fita" tayi murmushi meh dauke da farin ciki

"Am glad kana jin dadin zama da umma, kasan da ina Nigeria akwai wuraren da nake san zuwa"
"Da gaske" ta jin jina kai

"Yes, kace umma ta kai ka wuraren zaka nisha dantu kuma kasan culture da traditions dinmu"

Yayi maraba da idea din ganin gari, yana jin dadin spending day din da kakarshi, but soon ze iya gajiya da zaman gda

"Nagode mom ki gaishe da Dad toh"
"Zance ya kira ka in gari ya waye anan"

"Okay mom,bye"
"Bye son" yana rufe laptop din yayi zuru babu wani abinyi,

"Wannan wurin is not as exciting as i thought" mikewa yayi a nufi window din dakin ya yaye labule kafin yayi tsaye nan har aka fara kiraye kirayen sallar asubah

"Good Morning Granny ma" ya fada da murmishi yana tsalle kaman wani yaro

"Barka da safia Ehsaas, ya ka kwana" ya zauna saman hannun kujerar da take

"Lfy lau,ya kike kwana" tayi dan yake
"Da gajiya,amma ina ganinka yanxu gajiyan ya washe" shima yayi murmushi

"Kince yau zamu fita" ta dauki maganinta zata sha taga ba ruwa kusa da ita
"Gsky yan aikin ki are incompetent grandma"
Ya fada bayan yayi ringing bell

"Wannan abu ne da kikeyi koda yaushe, amma kullum sai kin tuna musu su kawo miki ruwa"

"I used to be very strict Ehsaas, but yanxu bana da energy din reprimanding kowa,shi yasa na bar wannan aikin ga head manager dina"
"Itama din she's useless, tun kafin inzo Mom tace ta nemo min PA,but shiru har yanxu bata samo bah, it's like sai an koya masu job dinsu"
Wacce ta kawo ruwan ta shigo sumi sumi tana sadda kai kasa

"Danaji sauki komai ze canza kaji my boy" ta sha ruwan bayan mintuna ta mike

"Argghhh inna lillahi, kafata ta rike kuma" da gaggawa ya tallabota

"Sannu Granny" ya jata zuwa saman kujera

"Basai munje asibiti bah Ehsaas, kafan nayi min haka ai" ta fadamai daya damu suje asibiti

"Gsky da ban yadda kinyi throwing party dinnan bah" take ta mike daga ki shingi dawar datayi

"Banga yan decorations bah" ta fada da bacin rai

"Ina salamatu, badai batayi aikin dana ce bah,dauko min wayata" daga kai tayi taga babu meh aikin ta tafi

Wani bell dake kusa da ita ta fara kadawa har saida ya toshe kunnen shi

"Rashin lafiyata da zuwan jika na yasa bana lura da ku sosai, shine hakan ya baku daman mantawa da aikin da naje biyan ku kunayi"

"Duk ku barmin gda yanxu na sallame ku" take yan aikin suka zube kasa ana neman afuwa

"Koh kowa ze tsaya ban dake salame, leave right now"
"Ke!" Ta nuna wata

"Dauko min wayata ki tabbatar manyan mutanen dana gayyata zasu zo welcome home party din dana shirya mah Ehsaas, sannan ki aje Invitation card na birthday party dina da za'ayi kusa dake"

"Ehsaas" ta juyo gareshi
" Maroon din meh rubutu golden shi aka raba na party dinka koh". Ya jin jina kai

"Granny Ma, dama kin bari sai nxt week ayi party din tareda birthday dinki, kinga bakya jin dadi"
Ta shafa face dinshi da murmushi
"Don't worry, ina jin karfin jikina ciwon kafan nan phases ne,kuma ina zuwa check up"

"Toh jeki huta Granny ma,yau ba zuwa ko ina tunda za'ayi party kuma zaki gaji, bana so in kara maki gajiya " ta shimai Albarka kafin ta dau hanyar dakinta

"Haider it's good to see you again" suka tafa da abokin nashi

"Kaima haka, ya zaman naka anan" ya dan yatsina fuska

"Not as fun as I thought,"
"Yi hakuri Ehsaas, nasan ban kyauta bah,best friend dina yazo amma koh sau daya ban jashi mun fita bah, abin ne akwai complication ta wuri na"
Ehsaas ya dafa shi
"Don't worry guy, ni nasan ba haka nan zaka ki entertaining dina bah"
"Just focus on recovering da aikin ka"

"Muje ka gaishe da granny ma"
"Granny ma?"
"Eh manah" Haider dai dariya yayi ma sunan

"Ina wuni Hajia" ta ansa ba yabo ba fallasa
"Ina ta duban hanya"
"Wallahi wasu abubuwa suka hanani shigowa, in ba haka bah da gdan mu zan saukeshi daya zo" dan dariya tayi

"Kuma Granny mah shima ba lafia gareshi bah" Granny ma tayi mah Haider Allah ya kara sauki sannan suka fata zagawa cikin mutane

Shi dama haka yake baya san shiga cikin mutane dan rasa abinda zece yakeyi, amma in suna tareda Haider to bah matsala, dan Haider smooth talker ne yanxu sai yasa duk mutanen su saki jiki dashi

"Har yanxu dai kai baka canza bah, kana nan da share mutanen" yayi murmushi yana kurban drink dinshi

"Zanso inga yadda zaka dinga zantawa da budurwar da Mom zata zaba maka" ya kalli Haider da alamar tambaya

"Oh! Kana nufin ni bazan iya sama mah kaina girlfriend bane bah koh meh" Haider ya jin jina kai

"Gwara mah ka daina share yan matan da Mom ke cinno maka, dan in a way taimakon ka takeyi"
Ya dan harari Haider yana gyara tie dinshi

"Banga wacce tayimin bane bah shi yasa" ya fada a hankali

"Abinda yasa mom keta kokarin sama min mata bakomai bane bah sai dan cire temptation" Ya kalli Haider dake kallon shi shima

"Sierra ce halan taja suke ganin kaman kana kauce hanya" ya dan dukar da kai

"Sierra, kai" ya dago suka kalli jun.
"Nasan iyayena basu ba ilimin addini mahimmanci sosai bah, amma sun yi kokarin nuna min abinda is halah da haram"

"Kuma sex da drugs ba komai bane bah a Australia koh London, tsoro sukeji tunda u guys are my friend you'll influence me"
Haider ya girgixa kai

"Maganin ka kenan daka zabi friends irin mu,gashi yanxu munja za'ayi maka auren dole"
Ehsaas ya dan bashi naushi na wasa yana dariya

"Nima zanso inyi settling down Haider, am a man not a stone"
Ya kalli Haider dake shan drink dinshi beh da niyyan fadamai komai

In da sabo ya saba da shirun Haider in yazo ga fadan abinda ke damunshi,
Halin daya shiga saboda shaye shayen nashi mah a waje yaji badai daga bakin Haider bah
Gashi shi kuma beh iya boye abinda ke damunshi bah sai ya fadamai

"Ehsaas zan tafi ana jira" ya tashi daga kujerar yana nuna mai inda wacce suka zo tare da ita take tsaye

"Sai mun hadu nxt week koh, birthday din grandma dina ne"
"Okay toh" sukayi shaking da dan hada kafadu kafin ya tafi.



"Ina zan kaishi toh dani na dauka" yarinyar ta hau sabon kuka
"Ni ba kuka na tambayeku bah, kawai simple ansa nakeso"

"Allah ni ban ga wani sarka bah a dakin ka"ta fada da kuka

"Cikin da kwalinshi yake red color, ni nasan nazo dashi nigeria"
Ya tuna ranar daze bar Australia Alfie saida ya tuna mai ya dauki gift din daze bah kakarshi na ranar day dinta, kuma ya shiga private jet dinsu dashi, sannan ya shiga motar da tazo daukan shi dashi a hannu

"Toh a ina kuka ajeshi da kuka dauko daga cikin mota"

Ya saba Alfie ke shirya mai duk abinda zeyi, in lokacin yayi kawai fadamai abubuwan daya kamata ya sani zeyi sannan ya bashi abinda ze bukata

Har ya sauka kasa anata party, ya juya bayanshi dan karban 🎁, daya juya baya dan karba yaga babu wanda ya mikomai abu shine ya tuno babu PA dinshi a nan, alokacin ne ya tuna beh kara ganin sarkar bah tun ranar daya zo

"Ni wallahi koh sau daya ban gani bah da ina gyara daki" itama dayar tace haka

Cemusu yayi su tafi ya zauna saman gado, bayan nan ya tashi ya bude drawer dinshi ya dauko ticket din daze je umarah dashi ya koma downstairs in da ake shakatwa

"Happy birthday Granny ma" ya bata envelope sannan ya sumbaci kumatun ta

"How thoughtful Ehsaas, nagode sosai" itama ta jashi jikinta

Mom will be disappointed in tasan custom made, one of a kinda sarkan datasa ayi ma mamanta ya bata
Kuma duk saboda carelessness dinshi , toh a ina ya yar da wannan box
Yayi shiru yana tunani , dole yayi bincike ba tareda sannin kakarshi bah,Allah yaso shi zata tafi umarah.


Tnk u all for reading, zan cigaba da kokarin nisha dantar daku 😘😘😘
[3/9, 10:56] ‪+234 706 870 0853‬: 💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
BOYAYYEN KUDIRI
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐


0⃣7⃣.


Godiya sosai ga fans din wannan book, ina fata kuna jin dadin karanta book dinnan kaman yadda nake jin dadin rubuta shi,


"Sis kuka kikeyi" bata dago bah ta noke cikin pillow tana kuka kasa kasa

"Come on sis, ya akayi" dagota yayi dan ta zauna, shi ma kuma ya zauna saman katifar yana kokarin share mata hawaye

"Fadamin abinda ya faru manah, nasan kaka ta saba saki kuka"
Girgixa kai tayi

"Bazaki fadamin ba kenan" ta sake girgixa kai
"Toh fadamin in ji, kila yau sai naje nasa tsohuwa ta tada jijiyoyin wuya" dariya yaso sata sai yaga kaman batama san yana wurin bah

"Meh ya faru Asma'u" ya fada all serious
Share hawaye tayi sannan ta kakalo murmushi

"Am fyn yaya Abba, kasan duk abinda kaka zatayi koh a kwalar rigata"
"Fadamin abinda yasa ki kuka toh" ta girgixa kai

"Mutum baya auran matar da bah tashi bah, haka aure lokaci ne in ba lokacin ki bane bah baze faru bah, jst relax and hope for the best, okay"

Wani sabon kukan yazo mata, najin dadin kulawar daya nuna mata, ajiyar zuciya tayi dan yanxu matsalolinta sun karu ne

"Ban san in abinda zan baki ze saki farin ciki bah,tunda wayar da kikeso so much"
Murmushinta ya hana shi karasa maganar

"Ka sayar dashi" ya daga mata kai sannan yasa hannu cikin aljihu

"Phone din beyi kudi sosai bah koh" ta fada data ga yana lalube

"Bari dai ki gani"
"Yauwwa gashi" ya fiddo kudi ba laifi masu dan yawa

"Inna lillahi, it's 63,000" ta dan rufe baki saboda murna

"Mama zatayi murna in tagani" ya tashi tsaye yana dariya
"Bana nan za'ayi wannan transaction din sai lter,or wait ina zuwa"

"Gashi,nasan Baba ze tambaya in yaji ya kira ki beh samu bah" ita hankalinta mah beh kai can bah

"Nagode sosai yaya Abba" yana fita ta koma ta kwanta, tana tunanin abinda ya faru ranar

"Asma'u zoki karbo manah icce dauri biyu da Allah" barin wanke wanken tayi ta mike ta zura hijabi

"Kudin fah Mama"
"Gashi ki biya gdan asabe kiga in tana da sauran kosai"

A hankali take tafiyar kaman ba dauke take da abubuwa masu nauyi bah, tana isa gda mamanta ta karasa wanke kwanu ka
Ita saita nufi murhu ta hura wuta sannan ta dora ruwan dama koko

"Mama barshi in wanke bayin" ta mike tsaye tana cire hijabin ta

"Dama har naji bayana ya rike saboda rashin sabo da dukawa in dade"

Tun kafin tasan ciwon kanta take sawwake ma Mama wasu ayyuka, har ya kai ga kullum ita ke aikin gda sannan ta dafa abincin rana da dare, na safe kuma Mama keyi

"Oh Allah, ashe gasarar mah ta kare, sai na tuna mah mallam ya auno gero kenan"
Tana cikin bandaki tana wankewa, amma hankalinta na kan tunanin yadda zata taimaka ma iyayenta, duk da yayyenta maza na iya bakin kokarin su

"Salamu Alaikum" aka shigo gdan da sallama

Bayan Mama ta ansa sun gaisa da kawar Asma'u wacce itama sunnanta Asma'u amma ana kiranta da ma'u

"Amaryar August, yaya ne" ta fito Tana gyara daurin dan kwalinta

"Namecy, naji ana cewa an daga bikin ki" ta danyi murmushi kawai

"Gwara mah da angon ya dan bamu tym dan gyara ki da kyau da kyau"
Kaman tayi tsuntsuwa ta bar wurin takeji dan ma'u bata da matsala duk abinda yazo mata fada takeyi

"Kina bukatar mu dilke ki sannan, a hada maki turarukan amfani, da abubuwan nan dana ga ana bah su Karimah suna sha da zasuyi aure"

Ji tayi ma'u ta makalota tana janta zuwa tabarmar da aka shimfida a tsakar gda

"Bani lbr kawata, har kin cinye kazar ki, dan na rantse sai na dan dana" Asma'u ta girgixa mata kai

"Toh duk ranar da aka kawo ki sanar dani,dan in ji abinda ake ci" tagumin mama ta kalla wabda tasan bana magan ganun da ma'u ke fada bane bah sai na tunawa

"Ma'u,kiyi shiru manah, bakya ganin Mama ne" ta dan fada kasa kasa

"Mama" ta mike gaba daya ta nufi inda take zaune gaban murhu


"Mama meh ze hana Asma'u ta koma gdan mu da zama har ayi biki, mamana tasan duk inda za'aje nemo mata abubuwan da zata bukata

"Zan fadama babanta idan ya dawo"
"Lokaci ya kure manah mama,saura sati uku fah, ga anko da kayan da amarya zata dinga sawa"

Asma'u ta mike ta shiga cikin daki,sai tayi tagumi

"Namecy bazaki zo ki rakani bah" ajiyar zuciya tayi kafin ta mike ta fita daga dakin

A kan hanya mah kaman tayi ihu, saboda ma'u cigaba da zayyano mata abubuwa tayi

Kaman ta bude baki tace mata 'ke babana fah yayi retire yanxu islamiyyan manya yake koyarwa sai bada maganin addini da yake yi, kin rigada kin san mahaifiya ta bata aiki, amma kike ta jajibo min abubuwa, dama ina son auren ne'

A fili kuma murmushi tayi mata, dan ita bata iya fadan matsalarta bah

"Ma'u ki gaishe da mama kice zanzo in gaisheta, yanxu kinga akwai aiki a gda" sukayi sallama kafin ta koma gda

Yadda ta tafi ta barta haka tazo ta isketa da tagumi

"Mama, sai kin sake zuba wani ruwa ya kone wannan" ta debo ruwan da kanta

"Hankali na ya tafi wani wuri ne wallahi"
Bayan ta zuba ruwan a cikin tukunya saita jawo tabarma zuwa inda murhu yake

"Mama kin san in kina damuwa sosai zance na fasa auren" ta fada da shagwaba tana dan turo baki

"Asma'u kenan" sukayi dariya su biyu

"Da ina da iko Asma'u da koh tunanin sa maki rana baza ayi bah, yadda muka takarkare akan kiyi karatu" mama ta tsaya bata karasa bah tana iza wutar kawai

"Na mah manta in tambayi Asma'u in result din jamb dinsu ya fito" dan ita bata rubuta bah, waec da neco ya cinye yan tsohuwar ajiyar iyayen nata

"Yau tun da safe baba ya fita"
Ta fada dan taji inda yaje

"Kauye yaje dan yaji in zasu yadda a kara daga bikin" labari beyi mata dadi koh ya bata hope bah dan tasan baza a daga bah, da dai Kaka ya samu ta amince toh da tabbas za'a kara dagawa

"Da naso in hanashi zuwa, sai naga gwara ya tafi kila su dan nuna kulawar su akan mu su bada gudunmuwa"

Dariyar takaici Asma'u tayi a ranta, dangin ubanta kam baza su bada wani gudunmuwa bah, dan tunda babanta yayi retire sukaga baya samu kaman da, gashi private school yayi V principal babu wani pension duk sai suka juya musu baya

"Ni Mama guduwa mah zanyi" dariya mama tayi dan tasan ba zata iya bah kawai fada takeyi

Ni dama wani ne bah salisu bah, da mutumin kirki ne bah meh dan hali da damfarar mutane bah da ta iya hakuri ta zauna dashi, amma salisu

"Koh meh yasa kaka bata ganin abinda duk sauran dangi ke gani" sai ranar ta taba magana akan shi da mamanta

"Kuma duk tafi kowa wahala, tunda ita yafi zuga ma karya ya karbi dan abin hannun ta, kuma in ta juya baya ya dauke wanda ta aje"

"Wai auran nan mah ya halasta" ta dago kai taga mamanta na kallonta

"Kila ta sanadiyyar ki ya shiryu" haka baba yace mata da aka ce an ba salisu ita yazo gda ya iske tana kuka

"Kin san babu meh ketare maganar kaka,in dai a dangin babanku ne dan haka kawai ki fawwala mah Allah komai"

"Salamu Alaikum, wai kaka tace a turo Asma'u" mama ce ta fito daga dakinta

"Sai ka shigo har tsakar gda kafin kayi manah sallama" almajirin ya juya ya fita

"Nasan wani aiki zan mata" itama ta fito daga nata dakin

"Gashi kin sha aiki kuma a gda, zo ki kai mata wannan abincin dana aje ma babanku tunda ya kai har la'asar nasan sai dare ya shigo"

"Toh ki ajemai wannan din

Please Login or Register in order to submit comment