Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

na harbawa, koh wani motsi in tayi tuno mata yakeyi da wanda zata aura da kuma gobe ne auren


"Gashi" tana jin muryar wanda yayi maganan ta gane

Duk da batasan abinda ya miko mata bah raruma tayi sai taji ashe hijab dinta ne

"Yaya?" Ta fada tana sheshekar kuka

Kaka ta fito da sauri saboda ihun jikanta dataji tana haskesu da touch

"Sabo da taba abinda ba nashi bah shine yake rudarshi da ze iya taba duk abinda yaso, wannan kashedi ne koda wasa karka sake ka kalli husna" ya fita daga soron gdan

Shi kuma salisu saida yayi kwana biyu yana tafiya da kafa bubbude.



Wani silent kuka ta farayi tana rokon Allah ya aiko mata da mala'ikun sauki,dan zama da mutumin nan ba karamin firgitata tunanin yakeyi bah

Gashi wanda shi kadai yace beh yadda da auren bah bayanan, yanxu ya zatayi, dama Raees ze zo


Tashi tayi ta hau sallah tana kai kukanta ga mahallicci, dan bata da wata dabara sai yadda yayi da ita.


Da gari ya waye ta shiga ban daki ya kai sau talatin, zama kawai takeyi taci kuka sannan ta fito a cigaba da shagulgulan biki


"Naji surutai a waje har an daura ne" sikewa ne kawai batayi a inda take zaune ana daura mata dan kwali


"No,ango beh zo bah shine suketa mahawara, amma kaka ta dage ayi tunda dama yace akwai abinda ze hanashi zuwa daurin auren in dai aka daga,kuma aka daga,kinga kenan baze zo bah amma ya amince ayi auren"

Dukar da kai tayi wasu hawayen na shirin tsiyayowa

"Ni na rasa yadda zanyi dake namecy, koh haka kikeso a barki ba koh dan kwalliya"

Bathroom ta ruga ta shiga ta rusa kukanta san ranta kafin ta fito

"Fuskarki na bukatar serious makeup, kinga yadda ta kumbura ga eyes sunyi ja" wata kawarsu wacce zatayi mata makeup ta fada



Duk daran shima beh samu yayi bacci bah,abinda ya daina tunda yazo ya hadu da Husna dinshi,kwatsam jiya kuma bacci ya kaurace mai


Bayan sun dawo sallar asuba ne gajiyar jiya ya hadu da rashin baccin shi,dan haka yana dora kai a pillow sai minshari 😴😴😴😴


Farkawa yayi da addu'a a bakin sa sannan yayi mika, tashi yayi zaune yana jiran yaji knocking a hankali a kofar shi, amma har bayan minti 30 shiru


Agogo ya kalla dan usually kaman yanxu tana nan, tana kauda abubuwan daya watsar yayi da shi kuma yake watsa ruwa


"Oh! Yau Saturday kila zata dan dauki lokaci kafin tazo" komawa yayi ya kwanta saman gado

Hankalin shi dai duk ya koma kanta, mikewa yayi ya dauko wayar shi


*are u still mad at me* ya tura mata text

Shiru ba reply sai ya kara turawa

Karshe video call ya latsa, sai yaji karan wayar na fitowa daga cikin dakinshi


Tashi yayi ya nemi wayar sannan yaga harda laptop da duk abinda ya siya mata


"She was serious, meh yasa zata bar yin aiki dani" ya sosa kanshi

"It's good mah hakan ai, yanxu tunda ta bar yimin aiki, hakan na nufin it's time to make her mine"


Driver dinshi ya kira yace mai yaje ya dauko Asma'u sannan yace mata akan abubuwan shine datayi handling



Murmushi yayi yana shafa shafa gashin kanshi


"Am really going to do this" ya kira room service aka gyara dakin sannan aka kawo flowers masu kanshi akayi decorating dakin



Abinci kala kala yasa aka kawo aka jera, sannan ya fara neman kayan sawa


Red suit ya dauko meh wando baki sai coat Burberry red da black color


Wanka ya shiga yana yar wakar shi, yana fitowa yaji knocking


Sakin baki yayi yana zare ido,
"She's here" tsalle yayo sannan ya fara sa kaya ba koh goge jiki, gashin kanshi mah jike da ruwa haka ya hanxarta dan bude kofa.





⚜B.W.AπŸ–Š
[3/9, 11:00] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSO πŸ–Š


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



1⃣7⃣.




Jikin gado yaje ya tsugunna ya rakube, baki bude yana kokarin shakan iska, ya kasa believing abinda yaji


Abinda ya manta da anayi shi yayi a lokacin😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭


"Is this a joke zakacemin she's married" ya bata rai har saida face dinshi yayi ja😑


"Wallahi na samu ana raba abubuwa,kuma nayi confirming Asma'u din da muka sani ce aka daura mah aure ranan"

Har yanxu jin kalaman yakeyi a kunnenshi

'It can't be my sweet innocent Husna, it has to be someone else'
Ya dora kai saman guiwwowinshi yana kukan da kawai zuwa yayi,kuma yaki yunkurin tsayar dashi


Dafe zuciyar shi yayi,dan beh taba jin radadi irin wannan bah


Yau ne ranar farko daya rasa abinda ya kwallafawa rai, yau ne rana ta farko a lyf dinshi da ya nemi abu ya rasa


"Why didn't she tell me, this is the utmost betrayal I've ever known,it feels like my hearts been ripped out of my chest,"
Ya fara magana shi kadai

"Why does it hurt so much" ya dafe brokenπŸ’” dinshi

Driver din na daga bakin kofa yana tausaya mai, dan tun kafin ya fara nunawa yasan ogan nashi ya fada tarkon love

"Am really sorry Sir, banso ace daga bakina wannan labari marar dadi ya fito bah"

Mikewa Ehsaas yayi ya nufo shi


"Wani scumbag ya aureta"

Ya nufoshi kaman yana shirin artabu da kowa ye mah

Driver dinshi ya sadda kai kafin yayi magana


"Someone who doesn't deserve her sir, shi din nan da muka biyo, your jewel thief"

Sai lokacin ya tuna da abinda ya kawoshi Zaria, sai lokacin ya tuna da abinda ya kawoshi Nigeria mah gabaki daya


'Truly i won't loose you Husna' ya fada yana goge hawayen shi

"Ya dawo kenan" driver din ya girgixa kai

"Good da ita zamu tafi, kace musu har sai mijinta ya fito sannan zamu basu ita" ya bude drawer dinshi yana fiddo suits dinshi


"But sir, hakanan kawai bazan je ince su bani diyar su bah, kuma ba ita keda laifi bah"
Ya juyo da calmπŸ€” look a fuskar shi


"Ina wannan mutumin, meh kawo manah masu aiki" driver ya fadi sunan shi


"Get him here,if he comes kai dashi zakuje can kuce mijinta ya aikoshi, ai sun sanshi koh"
Driver din yace Eh


"Ya zo nan kafin noon ya wuce, dan yau zamu koma gda" ya koma aikin da sai an sake

"Koh shi kadai ne passenger din jirgin,yace su kawo shi nan,Alfie!" Ya fada da karfi kaman PA din nashi na nan

"Husna!" Ya fada a hankali yana zamewa kasa


Sai daya dan dau lokaci kafin ya fadi abinda yasa shi neman PA's din nashi


"Pls tell them to pack my luggage" ya mike ya nufi gado ya kwanta


Daga cikin mota yake kallon duk abinda ke faruwa, jama'a sai gaisawa akeyi ana dariya


Yasan daidai lokacin da driver dinshi ya fadi sakon daya bashi,dan duk shiru sukayi

Sannan suka fara magana bayan sun dan kalli juna,

"What?" Ya fada rai bace

"Babanta zeso yayi magana da kai"
Kauda kai yayi gefe,

"Pls sir, he's entrusting he's daughter to a complete stranger, dan Allah ka bari ya damka maka ita hannu da hannu"

Zuciyar shi ta fara harbawa da sauri, a hankali ya cire seatbelt dinshi ya bude kofar ya fita


"Pls take care of her"
Ya fada a hankali bayan sun gama gaisawa,

"Duk da wannan ne karo na farko da muke ganin ka,nasan bazaka watsar da amana bah,tunda kai musulmi ne"

Abubuwan kara batamai rai sukeyi,dan shi kadai ke kidanshi da rawar shi,ita ashe koh fadama iyayenta tana mai aiki batayi bah


"We'll take our leave" ya fada bayan sun gama magana,

"Tnk u,and I'll take care of her" ya fada sannan ya koma mota


"Su kawota hakanan manah" ya fada da yaga shiru basu fito bah


"Farewell takeyi da mamanta" ya jingina da mota yana tapping kafa dan ya kagu yaga face dinta


"Wai bazaki bar kuka bah Asma'u, dan Allah kiyi shiru kinji"

Mutumin dayasa aka tattago yayi magana



tana shigowa motar yace su tafi, koh lefenta na akwati daya babba beh bari ansa a mota bah,kaman kwaceta za'ayi haka yake gani


Hijab fari meh tsawo ne jikinta amma ta jashi ta rufe fuskarta, sai aikin goge hawaye da takeyi dashi,


Duk zafin da yakeji a zuciyar shi da abubuwan da yayi niyyan fada mata,neman su yayi ya rasa, so yake kawai ta daina kuka


"Why is she still crying?" Ya tambayi driver dinshi kaman shima yayi kuka


"Abin kaman tradition ne sir, haka amaren sukeyi"
ya bata fuska danshi duk auren da yake zuwa beh taba ganin amarya na kuka bah, koh da yake na coci ne auren

"Dole sai tayi kuka kenan, wannan wani irin tradition ne" bacin rai ya maye gurbin tausayin da yakeji


"Ba dole bane bah,but abu ne da kawai yake faruwa, she's leaving the people she grew up with, the house she's always known"


Sanyi ya ziyarci jikinshi

"It's sad, baxata dinga ganin Mamanta kullum bah, gashi an kaita wani sabon wuri"

Ya jin jina kai,yana kurban sprite dinshi,dan sun tsaya sallar dhur ne kafin su wuce


" Asma'u kizo kici abinci" driver din ya bita mota bayan ta dawo daga masallaci

Girgixa kai tayi sanan ta kai kanta saman guiwwa


'Hw i wish u we're mine da babu abinda zaki zauna kina mah kuka' ya kalli waje ta window sannan ya maida kallonshi gareta


'Kece sillar radadin da mu duka biyu keji a zuciyoyin mu, you caused this pain'

"Karki bata tears dinki Husna, I'll find your husband, i have to find your, bazan samu sukuni bah Husna har sai na gano scumbag dinnan"


Beh san a fili ya fada bah,haka beh san ta tsagaita kukanta bah tana kallonshi da idanunta da suka kumbura

"Badan ya zama mijinki bah saidan wani HIDDEN INTENTIONS dana sa araina"
Ya sake fada a fili


"Meh kake nufi da ka nemo mijina?" Da shakakkar murya ta tambaya


"Ni dama nasani, i knew it d moment i saw you,kuma saida na tambayeka da wani BOYAYYEN KUDIRI kazo"

Yauce rana ta farko dazece ya samu damar ganin kwayar idanta da kyau,

Murmushi kawai yayi mata sannan ya kauda kai, dan itama yana ganin laifinta nakin fadamai aure zatayi,


"Wannan useless human being din beh cancanci mace kaman ki bah, A Real Man is wht u need"

'Kuma wannan real man din ba kowa bane bah sai ni Husna'
Ya fada a ranshi hade da kishingi dawa jikin kujera yana kulle eyes.




⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI
KHALEESI,
NOBLE JUDGE.
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



1⃣8⃣.



Tunda suka shigo garin abuja idanunta ke aikin kallo, ba daga kauye ta fito bah amma unguwar da suka shigo abin kallo ce


Mabushi estate ta ga an rubuta jikin wani katon sign board, inda arrow din yake nunawa nan taga sun shigo


Manyan motoci kawai ke shige da fice a unguwar,bataga mutum koh daya kan titi bah har suka wuce gdaje dayawa sannan suka shiga wani street


Gabanta ne ya fara faduwa da gate din ya bude da kanshi,taga wani katafaren white house unguwa guda


"Finally" yace ya bude kofa ya fita, beh bude baki yace ya gaji bah amma yayi complain ba iyaka,da tsaki styles iri iri


Har yayi gaba ya dawo kaman ze tashi sama da fuska bace

"Fito haka nan manah, baki gaji da zama bane bah" ya bude mata kofa yana jira ta fito


"Bakomai ka shiga ciki kawai, ni zan kirashi in yazo sai mu tafi tare, na gode daka kawoni nan"

"Bata min rai kikeso kiyi?" Bata dago bah ta girgixa kai

"Toh ki fito manah,kuma daga yau kar in sake jin kin kira sunan shi, koh kinyi referring kanki as matar shi"
Ya karasa da fada sannan ya juya ya nufi gdan


Gabanta faduwa kawai yakeyi ta rasa dalili, gashi lokaci daya ta tsorata da shi,


" Husna! " taji kiran kaman daga sama

Shi kuma ya kasa shiga gdan ba tareda ita bah,


Saida tazo har kusa dashi sannan aka bude kofa, addu'a a bakinta ta shiga gdan bayan ya shiga yana jira tasa kafa ta shigo itama


Daga meh "Sannu da zuwa sir" sai meh
"Welcome Sir" cikin masu aikin


Beh ansa ko daya bah, sai nashi order din da yake bayarwa

"Ku kaita dakin da zata dinga zama, kuma ku kula da ita da kyau,kar in ga kunyi wani abu bah daidai bah"


Sama ya haura ya barsu nan tsaye, yana shiga dakinshi ya banko kofar sannan yasa hannu cikin gashin kanshi,


"Dan Allah ina neman wani meh suna salisu" ta tambaya tana biye da su a baya


"Ni ban san wani meh suna haka bah, aikin meh yakeyi anan gdan" ta danyi tunani


"Ban san takamaimai aikin da yakeyi bah,amma wanda muka zo tare yakeyi mah aiki"

Daya daga cikinsu ta girgixa kai,daya kuma ta tabe baki

"Gsky yanxu baya aiki anan dan ya kori wasu maaikatan shi"

Gabanta ya sake yankewa ya fadi, inna lillahi ta fara jerowa a zuciyarta


"Dan Allah ina so inyi magana da shi uban gdan naku"

Babu wacce ta amsata cikinsu, saida suka zo wurin wani kofa suka bude sannan

"Sai ya amince sannan zaki samu daman ganinshi"

Sakin baki tayi dan tsoro komai yake kara bata,


"Ki shiga bayi na hada maki ruwan wanka" dayar kuma ta gyara gadon da dama a gyare yake


"Kayanki na nan zuwa" suka fita daga dakin


"Na shiga uku ni Asma'u, in yasan ya koreshi meh yasa ya kawoni nan"

Firgita tayi kafin kuma ta kwantar da hankalinta, wayar jikinta dake vibration ta fiddo.


My Love ta gani rubuce a jikin wayar, kuka ta fashe dashi kafin ta ansa call din


"Asma'u baki bar kukan har yanxu bah?" Girgixa kai tayi kaman tana ganinta

"Kun kai gdan ne" kuka ne amsarta

"Ni dama ban kira ba kenan" ta girgixa kanta


"Kiyi hakuri manah, ni kam bazan kara kira bah in kuka zaki dinga yimin" fashewa tayi da wani kuka sabo


Ta rasa yadda zatace ma mamanta yanxu hankalinta yafi da tashi,

Koda mamanta ta kashe waya batayi kokarin kira bah


Sai ta mike saman gado ta cigaba da kukanta,


Ehsaas beh sake bi takan Asma'u bah har saida dare yayi,lokacin kishin nashi ya ragu, dan shi gani yakeyi san mijin nata takeyi


"Kira Asma'u tazo muci abinci" meh aikin ta amsa da toh


Zama yayi a dining table din da ake jera ma abinci kala kala, aje plate akayi a gabanshi

"Chicken Alfredo Sir" ya daga kai kawai


An gama serving dinshi abinci, ruwa da drinks, Asma'u kawai yake jira ta sauko suci abinci


"Wai so kukeyi inyi komai da kaina, how hard is it to call her" ya mike daga saman kujerar


Zuwa yayi ya iske su suna knocking kofar a hankali


"Taki budewa ne Sir" cewa yayi su


"Asma'u!" Ya fara knocking a hankali, sannan da karfi yana kiran sunanta


"Ki bude kofar nan, Asma'u meh yasa kikeson bani wahala"

Hannunshi duk yayi ja saboda yadda yake buga kofar


Bude kofar tayi a hankali bayan ta iddar da sallah


"Meh kikeyi a ciki?" Kafin ta bashi ansa ya shiga cikin dakin


Ganin sallaya a shimfide ya hanashi sake tambaya
"Muje muci abinci"

Saida ta bari ya fita tace ta koshi


"Asma'u bazan sake tambaya bah" yayi tsaye yana jira ta fito

"Tnk u" ta rufe kofar

Kaman ya fashe saboda bacin rai😀


"Karki ci toh,kanki kikayi ma wah" ya koma dining table din, sai caccakar abincin yake yi

'Dan taga na damuda ita shi yasa takemin wannan rainin wayon'

Bayan ya gama yagalgala farar spaghetti din sai ya tashi ya koma dakinta


Wannan karon da sassanyar murya yake mata magana, kaman yana lallashi haka yakeyi


"Bacci zanyi" ta leko da kai bayan ta bude kofar

"Ki bari in shigo" ya dafa kofar yana kokarin turawa


"Pls, magana kawai zamuyi"
Ganin nan gdansu ne batada ikon hanashi shiga inda yaso, sai ta bude kofar


"Bakici komai bah through out the day, kuma haka zaki kwanta"

Ta dukar da kanta kasa,matsowa yayi kusa da ita
" Husna " matsawa baya tayi kafin ta ansa


Zafin abinda tayi da kishi suka kara ziyartar zuciyar shi


'Tana da gsky, bana da ikon zuwa kusa da ita ai'

"Husna baki zo da kaya bah" ya dafe kai


"Mantawa nayi wallahi,crap"
Ya nemi wuri ya zauna, ita kuma tana tsaye daga can gefe


"Yanxu ya za'ayi toh" ya jira tace wani abu amma tayi shiru


"Bari in sa a kawo maki PJ's, gobe sai a siyo maki kaya" ya fita daga dakin


Rufe kofar tayi ba tareda tasa key bah,sannan ta zauna gefen gadon


Bayan wani dan lokaci sai taji knocking a hankali


"It's me" bude kofar tayi duka dan tasan shigowa zeyi

"Here, kiyi manaji da wannan" karba tayi tanayi mai godiya


Tsaye yayi yana murmushi ita kuma ta kasa fadamai so take ya tafi


"Nagode sosai da kayan baccin" yace oh! Yana dan sosa kai


"Bakya bukatar komai, sai in sa a kawo maki, abinci, ruwa koh mah menene kawai ki tambaye ni"

Ta dagamai kai, ajiyar zuciya yayi kafin ya juya ze tafi

"Dakina shine na biyu bayan naki, ta hannun dama" ya fada yana fata ta dago ta kalleshi


'pls kice in tsaya' ya fada a ranshi
'Pls ka tafi, kaina ciwo yakeyi' kaman tayi kuka haka takeji


"Good night"
'Zanyi kewarki' ya fadama kanshi

'Dan Allah ki dago in kalleki fuskarki kafin in tafi' ya dan tsaya bayan tace good night itama

"Zaki iya bacci yau kuwa?, ni in naje sabon wuri first night dina bana bacci sosai"
'Inna lillahi kace first night' yayi murmushi

'Dafa yau ita da wannan' ranshi ya baci har a fuska sai da bacin ran ya nuna

" Ba fuskarki kadai bah,har zuciyar ki kin hanani Husna'


"Eh zan iya" ta dan jawo kofar alamun zata rufe


"Okay,amma in kika kasa ki fadamin, akwai wani tea da Mom dina ke hadamin, chamomile tea, zesa kiji bacci yazo"

'Da gaske dai baki damu dani bah Husna, yadda kike nuna halin ko in kula a kaina yana breaking heart dina'


Bazata sai ta dago ta kalleshi

"Sai da safe Ehsaas nagode sosai" take farin ciki ya lullube shi


'Zanyi bacci da sautin muryarki a kunne na' ya fiddo fara'ar shi fili

"Nagode Husna, saida safe"


Yana tafiya ta rufo kofar tana kullewa da key, kafin ta jingina da kofar tana maida numfashi,


Kayan daya kawo mata ta dauko, riga da wando ne masu tsantsi,daga gani kasan kayan shine


Linkewa tayi ta aje saman gadon,sannan ta kwanta baki bakin gadon,kaman wani abu za cijeta a dakin,haka takeji.



Tana zaune saman sallaya tana azkar dinta dan ta makara,taji kwankwasa kofa


"Good morning" ya fada shirye cikin suit meh daukan ido ash da layo sirara red color


"Good morning" ta maida mai

"Ya kikayi bacci jiya" tace Alhamdulillah tana fitowa daga dakin


"Nima haka" ya fada yamna bata wuri dan ya tare kofar dakin



DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment