Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Kakata ta dauke aiki, nasan zata bukaci jawabi daga gareke lokaci lokaci"

Lukman ya danyi murmushi yana girgixa

"Ita ta bani aiki amma kai nakeyi mah aiki,dan haka loyalty dina na wurinka"

Ajiyar zuciya yayi

"okay ka dauki alkawarin bazaka dinga fadama wani abinda nakeyi bah, koda mahaifiyata ce"

"Alkawari kayana Sir,in shaa Allah zan rike amana, bazan bari taci ni bah"

"Fadamin menene?"


"Sir akan hanyar mu na maida yan uwan Asma'u gda ne naji suna magana"

Nan ya bashi dan takaitaccen labarin abinda yaji da wanda ya binciko,


Zama yayi yana tariyo abinda aka fadamai,,,,,,,,,

'Sun san abinda ya kaishe zaria har ya hadu dasu'

'Bayan sun dawo gda kuma Granny Ma dinshi tayi nata ziyarar, harta so sa su a prison'
Dan sosa kanshi yayi ta hanyar wargaza gashin kanshi,

A ranshi yana fata a iya nan hannun kakarshi ya tsaya,

'Stupid you, ya za'ayi ka zargi Granny Ma' harda dan dukan kanshi a goshi

'Meh ze hadata da accident dinsu wanda yin Allah ne, qaddara ne ai'

"Kuma maganar gdansu da meh abinnan meh taya uku ke so ta karba" ya koma magana a fili

"Abu ne da zamu iya gyarawa"
Ya karasa da murmushi,

"Okaaayyy, akan satan da aka laka mah babban yayan su fah"

Yanayin yadda Lukman yayi maganar kaman yana kokwantan shi

"Shima abinda zan iya fixing ne"
Kafin yace wani abu lukman ya cigaba da fadamai sauran abubuwan daya faru,


"Amma kasan shaidar sata ba meh goguwa bane bah koh,Kuma a wurin aikin shi ne, saboda haka yana bukatar sabon job,

Koh babansu beh samun respect din daya cancan ta saboda wannan kazafin, and her brothers_____"
πŸ‘¬,

"Dude" ya katse shi da babban murya

"Nasan abinda zanyi, kawai ka kalleni kuma kayi duk abinda nace, in kana goyon baya na har yanxu kenan"

Lukman ya daga mai kai ba wani dogon tunani

"Nagode sosai lukman"
Yace bakomai

"Amma aikin ka beh kare bah,yanxu zamu fara"

Lura da yayi lukman yaji dadin haka.

Shima aranshi yace ai ni dan Mommy dina ne, nasan yadda zan bullo ma matsala😏😏😏

Sosai take kula da hajia ba kaman data san matsalolinta da abubuwan dake damunta,

Tana da ciwon suga da kuma hawan jini gata da ciwon kafa , Allah yaso hajia mace ce da bata da kiba bata tara maiko bah,
Hakan yasa ta rage risk din heart attack koh stroke,

A yanxu mah ta gama dafa mah hajia lafiyayyen abinci dake da sina darin vitamins dan su take bukata, ganye da kayan lambu duk sune abubuwan da take tabbatarwa ta hada mata cikin abincinta na koda yaushe,


Kula take da hajia kaman yadda zata kula da mahaifiyar ta, zama tayi ta koyi yadda zata bata kulawa daga wurin wata nurse data taba zuwa duba hajia,

"Lokacin shan maganin ki yayi hajia"
Ta ballo ta bata, sannan ta hau yi mata tausa da man kifi saboda ciwon da take fama dashi a guiwwa

"Kin san bana san kina zuwan min da karnin nan"
Hakuri ta ba hajia

"Dana gama zan wanke maki shi tas,bazaki san mah na shigo dashi dakin nan bah"

Tana gamawa kuma ta hau daga mata kafa tana lankwasawa daya bayan daya,

"Yau dai zamuyi kokari mu dan zagaye ko nan dakin ne koh"

Ta fadama hajia dake kallonta tsaf, wani lokacin takan ji tausayinta, kuma sai wani bangare na zuciyarta yace da haka suke farawa ai,kafin su nuna maka asalin kalar su,

"Koh na minti biyar ne, haka nurse dinki tace mu dinga yi"

Shigowa dakin yayi da sallama, yana ganinta yaji farin ciki ya ziyarce shi, koh kwatan kulawar da take bah kakarshi baze iya bah

Shima kanshi yana bukatar a dinga yimai abubuwa ballantana yayi mah wani,

'Hakan ya kusan canzawa,in shaa Allah ' ya fadama kanshi

"Salamu Alaikum"
Sallama kawai in yayi zata ansa

"Allah ya biya ki Husna, dan ni ban san irin godiyar da zanyi maki bah"


Asma'u bata ansa bah sai wanke mah hajia kafa da tayi sannan ta goge da towel,


Hajia na kallon su ta gefen ido, duk abinda takeyi akan idanshi sai murmushi yakeyi da beh nuna alamun yana cikin farin ciki, kaman na dole ne murmushin


"Ehsaas, komai lfy naga kadan rameh ne" yayi mah kakarshi murmushi

"Am fine Granny Ma,gobe mah aiki zanje, in fact daga gobe mah zan zama busy sosai"

Tana fita yabi bayanta saidai beh samu kwarin guiwwar yi mata magana bah,


"Ki cika aikin abinda nace dazu, da zan tausaya mata amma na fasa, ji yadda ta maida min jikah,ba kuzari kaman an zare mai lakka"
Ta karasa da tsaki

"Bazaki sanar da Mahaifiyar shi abinda ake ciki bah"

"Zan gamu da safiyan itama,wannan duk laifinta ne,ya za'ayi ta koya ma yaro kwallafawa rai abu, ni gani nakeyi kaman asirce shi mah tayi,
Yi maza ki aika masu da sako, bayan abinda ifiritun yarinyar nan tayimin bazan tausayawa talaka bah"

Numfashi ta fara yi sama sama,

"Sannu hajia,kwantar da hankalin ki yanxu zan aiwatar da abinda kikeso"

Ta fita da sauri ta bar hajia ita kadai da tunaninta,

Gwiwowinta ta taba tana tausaya ma kanta, a cikin halin data tsinci kanta,

"Sai Allah zeyi min hisabi dake Hannah"
Hawaye ya tsiyayo mata a fuska.


Ehsaas dagewa yayi wurin taimaka mah iyayen Asma'u da yan uwanta, ganinshi abinda yasa take shareshi kenan

Bayan ita kuma bata mah san abinda ke wakana bah,


Bayan ya gama duk shirin shi ya shirya zuwa Zaria,


"So ya maganan karatun ka, har na yi kokari tsaya maka,sai na tuno ban sani jami'ar da kake so ka shiga bah"

Hannun shi rike dana ya Abbah 🀝daya fito raka su,

"Karka damu,ka barshi kawai ba krtun mah na sa gaba bah a yanxu"
Ehsaas yace Oh,
Gani yakeyi kaman basu yi maraba dashi bah

"Toh duk lokacin daka shirya ka fadamin,nasan Husna zata ji dadin hakan"

Hannun shi ya cire yana son ya isa cikin mota, ba wani farin ciki tareda shi
Ya sa ran cin nasara a wannan ziyarar,hakan beh samu bah

"Ehsaas"
Ya juyo ya kalleshi da murmushi

"Nagode da kulawan da kake bah Asma'u"

Baya ya dan dawo ya kalli yayan nata da kyau

"Abinda yafi haka mah zan iya yi akan Husna, ni a ganina kun rigada kun zama yan uwa na"

Bece wani abu bah sai ya juya ya koma mota inda lukman ke jiran shi,


Ehsaas na cikin mota komai ya dagule mai, a yadda yaga rashin karbuwa a idan babanta haka yake hango rabuwar shi da ita


"Kaman nayi babban kuskure dana boye masu dalilin daya sa na shigo cikin rayuwar su"

Kafin lukman ya samu abin cewa ya cigaba

"Kila dana fadi gsky da batayi aure bah, itama data fadamin da ban barta tayi aure bah"

"Kila nimah nayi gaggawa wajen fayyace masu bukata ta, dama ban zo da kaina bah nabi ta wata hanyar, dukkan su babu wanda ya karbi taimako na"

Yayi dan tunani

"Amma mutumin daka biya zeyi aikin shi da kyau koh,kuma daya gama za'a sakeshi"

Lukman ya tabbatar mai da mutumin ze ce shi yayi satan,sannan ya biya kudi kuma na tara,


Jingina da kujera yayi,bah karamin gajiya ke tare dashi bah, aikin office cinma BOYAYYEN KUDIRI n shi,yawo up and down ga wannan tafiyar...








⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š





πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Story, Writing Noble Judge.
Editing Khaleesi.


Dedicated to B.W.A writers Allah ya kara basira, books dinku na daban ne, sai wanda ya karanta ze san Allah ya baku baiwar Fasaha Da zakin hannu.🀝🏼😘😘

Karku ce na cika Mouth dayawa😏😏😜😜😜,har sai kun nema kun karanta,

Ku kasance da B.w.A, dan samun Ilimantarwa da Fadakarwa ba Nishadi bah kawai😘😍😘😍😘😍😘😍😘😍😘😍




3⃣5⃣.





"Ba ruwan arziki da mugun gashi,Baban Asma'u, haka wanda Allah ya bah hakuri yafi a zageshi"

Muhawarar daya shiga ya iske iyayen shi nayi kenan

"Naji batun ki, amma ki sani barewa ba tayi gudu danta ya rarrafa bah, kuma wannan yaron tsatson wannan Matar ne,kuma the Apple doesn't fall far from the tree"

Ta tabe baki

"To wannan tufa din dai ya fadi nesa da bishiyar sa, ka duba fah tataki yayi yazo neman afuwa akan laifin da kakar shi ta aikata manah"

Maman Asma'u, Fatima Bintu ta fada da sanyin murya kaman ba fada takeyi bah,

"Daga jin abinda tayi manah yazo bada hakuri, ai ya cancanci mu yi mai uxuri"

Ya mika mata wata paper

"Wanda ya sani kenan wanda beh sani bah fah, duk wannan abin da ya faru damu itace sila,kin san wannan dan bata boye manah bah"

Ya dan tsagaita kafin ya cigaba

"baxata barmu bah sai ta gama aiwatar da KUDIRInta akan mu, "

Shiru yayi duk da yana so yasa baki acikin zancen iyayen nasu

"Ban san dalilin wannan Alkhairin da yake yi manah bah"

Ba tareda yayi tunani bah yace Asma'u

"Saboda Asma'u yakeyi, tun kafin ta bar nan ya nuna yana da ra'ayi" Ya Abbah ya gyara ansar tashi


"Kuma saboda shine hankali na ya dan kwanta, na yadda baze bari a cutar da ita bah"

Basuce komai bah na dan lokaci

Har Ya Kabir babban yayan su ya shigo

"Kun san abinda ya faru" harda bari jikinshi yakeyi yana tuntube

Koh sallama mah beyi bah

"Yanxu na dawo daga police station, in da wani ya amsa laifin yin satan harda bayani yayi,sannan suka bani wannan wai tarar da aka ci shine"

Farin ciki da annashuwa kawai yakeyi,suma kuma sun taya shi murna saidai Baba da yayi shiru


"Kakar shi ta bata shi kuma ya gyara"
Sukayi shiru

"Ni nasan aikin shi ne wannan din mah, abinda zeje ya dawo nake gudu, na tabbata saita bullo manah ta wata hanya in tasan abinda yakeyi manah"

Paper din da ya mika mah Mama ya karba,ya karanta,

An bashi aiki a matsayin shugaban wata makaranta dake nan cikin zaria, harda takardun gda, wai cewar su duk malamai ana basu gdan


Dan murmushi yayi daya gama karantawa,

"A gaban ku kawai zan iya nuna rauni na da gazawa, saboda ku iyali nane, babu meh agaza manah sai mu kanmu, dan haka bazan yanke shawara bah sai naji naku ra'ayin"

Jin jina kai yayi bayan ya gama sauraron family dinshi πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘¦β€πŸ‘¦πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘¦β€πŸ‘¦.

Bayan kwana biyu yana zaune a jikin fountain β›² muryar Husna yakeji,amma yaki yadda da magana takeyi mai,


"Sir!" Ta daga murya, koh gezau kaman beh san akwai mutum bah

"Ehsaas" ta fada , azatanta abin nashi ne ya taso, sai taga beh yi koh motsi bah

Juya baya tayi ta shiga cikin gda,sai lokacin ya kalli bayanshi sannan ya cigaba da jin wakar shi da earpiece,

"Husna kalla"
Ya mika mata wani βœ‰

"Bude ke aka aiko mawah"

Cire wayanta tayi daga cikin hijab tana katse kiran,

"Ya dade da aka aiko manah da shi"

'Abinda nayi kokarin baka kenan ka shareni shi yasa na kaima daki ai'
Ta fada a ranta

Ta bude taga Khadija ke gayyatanta zuwa bude sabon shop dinta

"Bazan samu daman zuwa bah"
Abinda kawai tace kenan ta wuce abinta,

Dakin kakarshi ya wuce

"Granny Ma abin karuwa yakeyi" ya fada saman gado yana tura kai cikin pillow

"Har muryarta nakeji a cikin kaina, nan gaba mah fuskarta zan dinga gani a ko ina"

Da kyar ta lallaba shi ya wuce daki bayan tayi alkawarin yima Asma'u magana,


"Wai wani shirmen ya daukeki kika sangarta yaro haka, namiji mah"

Hajia ta fada cikin waya, gani tayi gwara ta sanar da Mahaifiyar shi halin da ake ciki

"Kin koya mah yaro samun duk abinda yaso,koda ze iya samu basai ki nuna mai a rayuwa baka samun duk abinda kakeso bah"

Sai lokacin Maman shi ta samu tayi gaisuwa

"Allah safiya kin kwari kanki, kinga yadda yaron nan ya koma saboda ya kwallafa mah ranshi abu"

Daga canzawar muryarta ta gane ta san abinda take magana akai


"Nayi iya kar bakin kokarina dan ganin ya cireta a ransa, amma sai abin ya karu___"

Katse ta Mamanshi tayi

"Aa ki barsu kawai, ni nasan halin Ehsaas, in ta cigaba da shareshi zefi dora ma kanshi kasancewa da ita,

yasan baza tayimin bah shi yasa beh fadamin na neman mai mafita bah, amma ni nasan yadda zanyi"


"Gwara kam kisan abinyi,dan diyar malamai ce,Allah kadai yasan koh ta bashi wani abu yasha"

Ta katse kiran tana sawa a kira mata Asma'u

"Hankalin ki ya kwanta koh, kin samu abinda kikeso sai ki zuba ruwa a kasa ki sha"

Kanta kasa, fuskarta dauke da mamaki

"Ban fahimta bah hajia"

Ta fada kasan muryarta

"Ga ki gashi, ki cigaba da kanaina yeshi kinji koh, bana son inji yana cika min kunne da complain akan ki, kuma ki sani ke matar aure ce Akwai amana akanki,

Meh mah yasa nake tuna maki,tunda kinfi ni sani, ai niyyar bakar zuciyar ki kenan kinga dan masu gda,

Ni banga abinda ya gani ya nace maki bah, yan mata dayawa ya rasa wacce ze so sai ke"

Bata sake jin komai bah sai kwalalo ido da tayi😳

'Kila Hajia ta saurari gulman yan sa ido neh'
Ta kwantar ma kanta da hankali

A gabanta ta ganshi tsaye dauke da murmushi,

"Bazan samu zuwa bah Ehsaas dare ne,kuma ni irin abubuwan nan ba nawa bane bah"

Ya maida hannun daya miko mata βœ‰ dashi,

Ya bata fuska πŸ˜”, sannan yazo wuce wa ta gefenta

"Ehsaas" ta tsayar dashi,ta tabbata wurin Hajia zeje ya kara ja mata magana

"Zanje toh" bata jira cewar shi bah ta bar wurin,

'Nooo baxata sa irin wannan dinner gowns din bah' yayi ma kanshi murmushi harda cije lips,

Gani yake kaman wani date πŸ’• zasu

Ya kwadaitu daya ganta,harda Makeup ya hangota, yana kokarin suffanta surarta a kanshi,


Da hijab ta fito wanda ya tsaya a saman hannunta, riga da skirt din atamfa ne jikinta, fuskarta babu kwalliya koh kadan,

'A haka mah tafi kyau da burgewa'
Ya fada bayan yayi ajiyar zuciya

Ya bude mata kofa ta shiga cikin motar.



"Yi tafiya a hankali" driver dinsu watau lukman yace toh, sannan ya daga wani bakin glass daya raba tsakanin su da driver.

"Kin daina fushi dani yanxu"
"Dama wa yace fushi nakeyi" Amsarta yasa shi murmusawa


"Naji toh, nagode sosai da kulawar da kike bah granny mah dinah"

Ta amsa da bakomai, cigaba da kallonta mah ze wadatar,saidai muryarta har cikin heart dinshi take tasiri,

"Ya maganan karatun mu" kaman ya sake maimaita tambayar da tayi shiru,


"Zan so in cigaba amma zefi in ka samu wani malamin"
Saida ta daina wasa da yatsunta kafin ya maida hankali kanta


β€œThe best amongst you is he who learns the Qurβ€˜an and teaches it.β€œ
"Wanda ya koya koh wanda ya koyar da al-qur'ani, ladan daya ne" ta cigaba mai

"Kin gani, nima ina so in koyar bayan na koya" kafin tace wani abu ya katse ta

"Ina so in zama malami na farko da yaranmu zasu sani"
Dagowa tayi ta kalleshi

"Yaran mu????"
🀨
"Ina nufin da yarana zasu sani, yarana bah namuh bah, ni da ke" ya nuna ita da shi,

"Kin san da muka daina karatu ban tsaya bah na cigaba da research, kila yanxu ni zan dinga koya maki"☺ murmushinta ya sashi😊

"Ina fata daga in da malaman suka dauko anan ka koyo, ba daga ra'ayin wasu bah"
Ya daga kai
"Yap daga sunnan manzon tsira, Alihi da sahabban sa"

Tace yayi kyau
"Har kin koma malamata kenan" bata sake cewa komai bah koda ya cigaba da magana.





⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSO✍🏻





πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Story writing Noble judge
Editing khaleesi.


Dedicated to our beloved readers, mungode da kulawa,

Tnx to Noble J 3pages yau, coz gobe bazamu samu daman posting bah,

Karku manta comments dinku na kara manah kaimi da kuzari wurin typing😍😍😍😍

Love u all, wanda muka sani masu comments publicly da privately, da wadanda bamu sani bah,

Dan yi manah gyara koh korafi, a tuntube mu ta πŸ‘‰ 09033325153.


Kisses😘😘😘😘😘😍



3⃣6⃣.




"Ya akayi,kinyi shiru dayawa" dan murmushi tayi batace komai

So kawai take ta ganta a gda ita kadai ta kira Ma'u,

"Ke da Raees, kun san juna ne" ta amsa tana daga kai

"Naga kun dade kuna magana ne"
'Har na fara jin haushi' ya karasa a cikin ransa

'Duk da munyi magana kuma yayi min alkawarin nemo wannan da aka aura maki'
Yaji ranshi ya baci daga yin wannan tunanin


"Dan Allah muyi sauri"
'Kafin hawayen su fito ban shirya bah' ta dora kai saman guiwwa

😞 'mata mah are very complicated wallahi' ya sake kallonta bayan tayi magana

Aranshi ya sake magana. 'Da alamu wani abu taji a wurin bude sabon Stores din can'
Kaman yayi tsaki,

"Sai bacci kuma" ta daga kai tana shiga kitchen, sannan tabi kofar daze kaita ban garen da take

Waya ta fiddo tayi ma Ma'u pls call me, ba bata lokaci kuma ta kirata,

Koh gaisawa basuyi bah ta fadi abinda ya tokare mata a wuya,

"Da gaske ne?" Ta tambaya tana kokarin maida hawayenta

Ajiyar zuciya Ma'u tayi kafin tayi magana

"Ya Abbah yace kar in fadamaki namecy, abubuwan ne duk so bizarre, kaman a mafarki, am so sorry, but na sanki da damuwa abu kalilan sai ya tada maki hankali"

"Wannan yayi kaman da abu karami koh wanda beh kamata in sani bah, shima ya Abbah zan gamu dashi ai"

"Namecy!" Kashe wayan tayi kafin Ma'u tace wani abu,


Saida ta goge hawayenta sannan ta debi ruwan cucumberπŸ₯’tasa a kopi, kullum da safe take yankawa cikin jug din ruwa wanda take bah hajia, daya kwana kuma ta zubar ta sake wani, yana taimaka ma masu diabetes ciwon suga, kuma yana gyaran jiki,
Wata rana kuma lemon tsami take sawa cikin ruwa meh dan dumi,dan yana warware yan hanji kuma ya taimaka wajen fidda toxins dake cikin ciki,

Hadawa tayi da ordinary ruwa ta dora saman tray, sannan ta nufi dakin hajia,

Dora wa tayi saman table din dake kusa da gadonta, sannan ta gaisheta,
Kallonta takeyi tana so tayi mata magana akan abinda taji,



"Lafia kikayi min tsaye da daren nan"
Zuwa tayi ta duka gabanta,sannan ta hadu hannuπŸ™πŸ»

"Dama akan yan uwana ne"
Dariya hajia tayi
"Dama inata jiran ranar nan"
Ta latsa inter com tana kiran secretary dinta,

"Karki fara bari tazo,ina so tayi min recording rokon da zakiyi ne, farawa kenan suma sauran yan uwan naki sun kusan farawa"
😁😁😁😁


Shiru tayi tana mamakin abinda tayi mata da take cin zalin su haka

Ranar taji wani zafi a ranta, abinda bata taba tunanin yi bah a rayuwarta ranar shi ta shirya yi, har kyarma takeyi saboda bacin rai,

Dukar da kai tayi tana istighifari, tana gode mah Allah daya bata ikon tausasa zuciyarta bata furta mummunan kalma bah,


"Start" sukace dan ta san sun fara dauka, secretary din nightie ne mah jikinta,

hade hannuwa tayi kaman dazu


"Allah baya yafe hakkin wani akan wani, bani na miki bah haka ba iyayena sukayi maki bah, amma su kike tauye ma hakki dan kin fisu"

Hawaye ya fara bin fuskarta😭😭

"Karki manta ba sanki Allah yafi bah daya baki wannan matsayin, jarabawa ce a gareki,

Allah ba azzalumin

Please Login or Register in order to submit comment