Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Amma yanxu zanje bayan na gama hada maki ruwan wanka" tana gamawa ta nufi dakin da dan fargaba,


Da sallama ta shiga dakin, sannan ta sakeyi dataji shiru ba'a ansa bah,

Har zata fita kuma taga wasu abubuwan na bukatar a kimtsa su, saita fara tattarawa ,

Zata zuba wasu abu cikin kwandon shara taga kwalin turaren data siyo, ta zata kwalin ne kawai sai da taga spray din mah a ciki,

Fiddo su tayi tana dorawa saman side table,

"Ni na yarda su, basuyi min bah"
Da en eena ta duka ta gaishe da mahaifiyar shi

"Lfy lau, ya mah sunanki" ta tambaya bayan tayi kaman tana naxari

"Asma'u " Mom ta maimaita bayan ta fada,

"Kanshin su beyi min bah, shi Ehsaas din ai yasan irin abinda nakeso, da har ya amshi wannan a matsayin wani tsaraba"

Ta dukar da kai tana neman abin fada

"Zoki ga" ta mata alama data biyota

"Kin gani" tace Eh,
Turaruka ne designer ko wanne da irin nashi kanshin

"Baki taba ganin irin su ba koh" tace Eh

"Banyi mamaki bah, ai bana common people bane bah, ballantana talaka"
Ita kuma sai aikin maimaita sunayen su cikin kanta takeyi,
'Black opium, j'adore, coco Chanel, hypnotic poison, black orchid, Allah mai iko ni Asma'u'

"Muje muci abinci, dama ina ta son magana dake ba tareda My Dearest Son a wurin bah"

Suna kaiwa bakin kofa sai gashi a tsaye a wurin

"Mom, yanxun nazo kiran ku dama" tana ganin wannan daman ta tsere dakinta,

"Har yanxu baka fadamin abinda nasan kana so ka fada bah"
Maimakon ya jata zuwa dining area sai ya maidata daki,


"Mom, nasan bazan iya boye maki komai bah"
"Kasan da haka jiya ka zauna kana min karya" kasa yayi da kanshi yana dan jan hanci kaman zeyi mums

"Mom kiyi hakuri dan Allah, duk abinda nayi dan tayi maki ne"

Ta sake katse shi
"Karka lakamin ni ban saka kayi karya bah, kuma baka daukeni bakin komai bah,

Da kana girmama ni da bakayi komai gameh da rayuwar su bah, sai ka sanar dani,

Yanxu ne mah na fara jin bacin ran"

Ta juya zata tafi, da sauri ya duka kasa ya rike kafafunta yana kuka

Bataji dadin kukan shi bah, amma taji dadin cin nasarar da tayi na sashi nadama,
Yanxu zata iya sashi yayi duk abinda takeso,


"Ni ka barni kaje wurinta, tunda tafiye maka ni" wani kukan ya fashe dashi

I
"Pls Mom ina sonta, amma sai kin yarda zan iya yin wani abu akai"

Tasan horon yayi haka amma, saita cigaba da nuna fushinta, shi kuma sai sharba kuka yakeyi yana bata hakuri,

"Safiya" ta shagala tana dariya ciki ciki, bataji shigowan babanshi bah,

Daga yadda yake kallonta tasan beh aminta da abinda takeyi bah,

"Okay Ehsaas yayi haka nan" ta dagoshi tana janshi jikinta harda dan bubugamai baya, kaman karamin yaro shima kuma ya shige jikinta,


"Tnk u mommy, am sorry" babanshi ya girgixa kai yana karsawa cikin dakin

"Kin gama koh, yanxu zaki barshi ya auri matar da yakeso koh" tayi kaman bataji abinda babanshi yace bah,

Saida ya tsareta da idanu sannan ta dan, janye shi daga jikinta

"Da alamu babanka ya yaba da Matar daka zaba" ya danyi kasa da kai yana goge hawayen shi,

"Na zabe ta, amma ita bata zabeni bah"
Mamanshi tayi wani stylish tsaki

"Ta kam ganka, san kowa kin wanda ya rasa" yayi dariya yana zama saman gado

"Barni da ita, zanji dalilin ta na kin Fine Boy dinah, In shaa Allah labari meh dadi zan fada maka bayan mun zanta da ita"

Yace ya gode sannan, yayi niyyan barin dakin

"Kaje ka huta kaji Son, kafin lokacin tafiya ta yayi"
Ya ce Toh,


Tana kwance dakinta tana buga subway surfers a wayarta, akayi mata sallama,

"Gani Hajia ance kina kirana"
Ta fada bayan tayi sallama ta ansa

"Shigo manah in-law dita"
Bata san dalili bah, amma tunda tazo gdan da ta ganta sai taji faduwar gaba,

"Ina wuni" ta durkusa ta gaisheta,

"Daga abinda na gani, akwai ki da diri" ta kankame jikinta ta cikin hijab

"Umma tacemin dama kullum cikin hijab kike, koh ta yaya yaga jikin ki harya kwadaitu"

Ta fara neman tsari cikin ranta,


"Koh kullum in yaje dakin ki da dare wani abu na shiga tsakanin ku"
Fashewa tayi da kuka

"Safiya nace maki karki saurari zancen yan aikin nan,
Ni nayi sakaci dana bari suna kawo min gulma ban kwabe su bah"

Safiya ta juya ga mahaifiyar ta

"Da ban gani bah bazan tambaya bah Umma, na gaya maki ranar da muka zo da ido na na ganshi ya nufi dakinta,

Bashi ya fito bah sai gab da Asubah,

Jiya mah dana je dakinshi da tsakar dare baya ciki,
Da babanshi na nan ne sai ince sun je yawon daren su da suka saba, amma baya nan,

Tambayan ni meh na iske shi yana yi da asubah danaa shiga dakinshi, daga wanka ya fito"

Kara fashewa tayi da kuka,

"Karki damu nasan dana ba dan iska bane bah, amma duniyan nan koh zanin jikin ka baka shaida dan baze fada maka bah in ze yage"

Sa hijab din tayi ta rufe bakinta kar kukanta ya fito,


"Fadamin tsakani da Allah, meh kukeyi? "
Kasa magana tayi sai aikin girgixa kai da takeyi

"Shikenan na yadda, gwara azo ayi auren nan koh ze kashe kishin ruwan dake damun shi,

Dan nason infatuation ke damun shi yake ganin kaman sanki yakeyi"


Dukawa kasa tayi bakinta na rawa

"Dan Allah ku barni in tafi gda, ni bana son in aureshi"

"Privilege ne dana ya kula, karki cika min kunne tashi ki tafi"
Batayi motsi bah tana nan tsugunne

"Bakiji meh nace bah"

"Allah ni bana sonshi kuma bana so in aureshi, bashi kadai bah ni bana son inyi aure, dan Allah ku barni in tafi, bazan sake koh ambaton sunan ku bah"

Matsowa tayi daf da ita sannan ta mikar da ita tsaye

"Dana nason aurenki kuma abinda ze faru kenan, kinji ni koh,

Kuma in kika ce bah haka bah, toh zaki ga wani bangare na da bazaki so bah,

Gwara ki rufa ma kanki asiri ki aureshi, kafin in kai ga taba na kusa dake,

Dan abinda dana keso shi yake samu"

Kallon Mom tayi sannan hajia

"Ban taba shiga hakkin wani bah, ban taba zaluntar kowa bah a rayuwata

Meh yasa kuke yimin haka nida yan uwana, meh yasa kuke amfani da dukiyar ku akan abinda baze amfane ku a lahira bah"

Da kuka take wannan maganar tana kallon kasa

"Asma'u jeki abinki"Mom tace mah hajia Aa

"Kinji na rantse maki koh kiyi abinda nace koh kiyi dana sani,

Bana sassauta wa kaman mahaifiyata, ni in zanyi da karfi nakeyi yadda zaka dade da raunin"

Da gudu ta juya tayi dakinta tana kuka, kayanta dama a hade suke, kadan kawai ta karasa shiryawa,

Ta dade nan zaune tana tausayawa kanta har dare yayi sosai,

Karar bude kofar falon dakin taji,
Da sauri ta mikar da akwatin sannan ta hau saman gado tayi lamo,


'Da gaske ne' haka tayi ta fada a ranta,

Bata iya bacci bah daren, data rufe idonta sai taga kaman ze cutar da ita,

Shi kuma baccin shi kawai yakeyi hankali kwance,

Gab da Asubah ya farka, bayan yayi mika da addu'a kuma ya zagaya gefenta,

Shafa fuskarta yayi sannan ya manna mata kiss a gashi, ya rada mata i love you a kunne,


Yana fita ta kara karfafa zancen ta na barin gdan, tun kafin abubuwa suyi nisa.


Karfe 7:00 daidai na safe ta fita nemanshi, ta rasa wani abu zata fara fada,


"Ina son kunyar nan taki, abin na biyu dana gani a tare dake dayasa na kudirci wani abu a raina"
A hankali ya takowa izuwa gareta

"Na farko jikin ki da kika rufe, na lura kuma haka kike, kunya da Hijab dinki basu sa na kamu da sanki bah saida naga eyes dinki,

i was hooked dana ga eyes dinki, kal kal gasu so expressive, ina iya ayyana abinda kike son fada in dai ina kallin idanun ki yayin da muke magana"


"Na rasa ta yadda akayi na kamu da sanki,

BOYAYYEN KUDIRI na shine in rabaki da mijinki in aureki Husna, wannan kadai ne niyyan babu wani kuma"


Saidai taga sun hada ido, bata ma san ta dago kanta bah

"Kar in cika ki da surutu, meh yasa kike nema nah? "

Ya matsa baya dan da ya shagala da fada mata abinda ke ranshi ya kureta har jikin bango,


"Tsoro nakeji Ehsaas " ya nuna damuwa ta hanyar bata fuskarshi,

"Kar komai ya baki tsoro My love, ina tare dake, zan kareki daga duk abinda zeso cutar dake"

Ya fada ba wasa a muryarshi, alamun da gaske yake

'Meye abin gudu a tare dashi Asma'u ' ta kara kallon shi da kyau

Ya hadu iya kar haduwa, yana da tsawo daidai shi, haka jikinshi mah kaman na dan kwallo, komai fit,

Ga shi ba girman kai, hakuri, tausayi, rikon amana da fadin gsky, meh kuma zata nema a wurin da namiji,

Kila shagwaban ne kadai ya kamata ya bar yi, amma tanayi mai kyau

Ta tsinci kanta da yin murmushi,

"Will you marry me" sai bayan yan seconds kafin kwanyar shi ta gama tantance abinda tace


"Bama irin wasan nan Husna, ina son ki amma bazan jure bah in zaki dinga jamin rai"

Ya bata fuska


"Da gaske nake, in da gaske zaka aureni, kuma kana sona, ni ma zan aure ka"

Taga lokacin daya nufota, bata san lokacin daya karaso inda take bah har ya dagata sama yana juyi da ita,


"Ka saukeni" duk abinda take fada baya ji, murna da farin ciki sun toshe kunnen nashi,

Dan kanshi ya gaji ya sauketa kasa sannan ta juya zata tafi, jawota yayi ya rungumeta ta baya,

Kyarma jikinta ya hauyi, bari kawai take kaman kankara ne jikinshi,
Kokawan sha kan iska takeyi, ji take kaman ana fizgo iskan daga cikin makoshinta,

Tana jin yasa fuskarshi jikin nata yana bata pecks a kumatu ta sike, ta kasa ko wani motsi,
Ihu kawai takeji bata san daga ina yake fitowa bah,
sai da taji makoshinta na zafi kafin ta gane itace ke wannan ihun,

"I swear Mom babu abinda nayi mata, granny Ma? " duk ya tsure daya ga Masoyiyar tashi kwance kasa tana fidda numfashin wahala,


"Asma'u kina jina" ta daga masu kai tana kokarin tashi zaune

Yana kai hannu ze tayata tashi tayi saurin matsawa baya,

"Ehsaas " mamanshi ta fada da babban murya

"Allah babu abinda nayi Mom,

May be i got over excited and hugged her,

But shikenan mom, Allah banyi komai bah"

Tayi ma Mamanshi murmushi da hajia


"Lfy ta lau hajia karku damu, ji nayi numfashi na na neman daukewa"

Mamanshi ta bata fuska, sannan ta daure fuska

"Kai Allah ya sauwake, daga tabaki shine kika wani hargitse haka,

Dama ance masu shiru shiru dasa dogon hijab dinnan duk sune basa iya controlling kansu, mtsewwwwww"

Ta fada da hausa sannan ta bar wurin

"Cewa tayi ka kara yimin laifi in fada mata, zatayi maganin ka da kanta"
Yayi dariya yana cewa ,zata iya

Tunda suka fita ya zauna kasa yana naxari, tasan abinda Mamanshi ta fada yakeson sani,

"Dan Allah ka maida ni gda"
Ya jin jina kai bayan dan guntun tunani da yayi,

"Gobe toh in Allah ya kaimu, amma yau ni dake zamu yini tare"

ya bar dakin, ita kuma ta kalli hanyar daya bi da kallo.






⚜B.W.AπŸ–Š
[3/26, 06:12] β€ͺ+234 706 870 0853‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Story & writing Noble judge.
Editing khaleesi.

Dedicated to Raheema & Meemah,

Allah ya baku sa'an exams din da zaku rubuta, da kuma wadan da zakuyi nan gaba,
Ku da yan uwa musulmai gabaki daya masu facing exams.
🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭

Marubuciyar quruciyar Jummai tazo maku da wani sabon littafi meh suna RIKICIN AURENA,
KADA KU BARI A BAKU LABARI,

SIS LEEMA, ja muje.

LAIFIN ABBA NA NEH,
Shin koh meh Abban Yayi?
Ku kasance da Marubuciyar Uwar Miji, wato Sis Rahama dan samun wannan Ansa.

πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘





4⃣1⃣.


IPad dinshi ya bata da hotunan irin abincin da Mamanshi ke so, bayan traditional data dafa,

Tsaf ta shirya komai, sannan ta gyara ma Mamanshi dakin da zata sauka,

Shiryawa tayi cikin wani lace marar nauyi, kuma marar tsada amma akwai daukan ido,
Purple color meh kwalliya silver, hijab ta sa batare da ta daura dankwali bah,

"No Husna banda Hijab din yau, pls" ta bata rai

"Dan Allah manah" ya biyota bayan ta wuce shi bata ce komai bah

"Mamanka ce zata zo fah, kuma kace min kai da ita are close"
Yayi ajiyar zuciya

"Baxaki gane bah husna"
Sannan yace ta bar hijab dinta,

Cikin suit yake meh laushi, jikinshi kaman na eskimo, maroon color ne sai yasa black T-shirt πŸ‘” da farin bow tie, wando shi mah fari da takalma bakake,

"Ina zuwa" tace tana komawa dakin ta,
Ita tafi sakewa in tana sanye da hijab, duk a takure zata zama in ta tafi haka,

Karan Doorbell taji, da kuma yar karamar kara,

"Surprise Husna harda Dad akazo"
Tace inna lillahi a ranta

Duk ya maida hankalin kowa kanta, gashi ta cire hijab din, babban dankwalin kayan kawai ta yafa

"And wannan kyakyawar fah? " ☺☺☺☺ Da kunya ta duka ta gaishe da iyayen shi,

Tana kallon mutumin data dago ta kasa dauke ido daga kanshi

"Nafi shi kyau koh"harda kanne mata ido daya

"Dad! " Ehsaas yace da yar shagwaba,

Banda kama harda tsokana da raha, duk wurin baban shi ya gadΓ², banbancin su kawai shekaru,

" husna yana ga kin rameh, koh duk kewata ne" ita sai lokacin taga hajia, wacce keta fara'a, itama tayi mata fara'a hade da gaisheta

"Na gaji fah" mamanshi ta fada hade dayin gaba,

"Ni ma haka Ehsaas" inji baban shi, sannan suka barsu su biyu


"Uhmhmmmm, ya kika ga iyayen nawa" harda sa kafadarshi ya tabata

"Kaman ka" yayi yar dariya,
Sannan ya wuce, itama tayi dakinta.


"Lokacin cin abinci yayi" ya leko yana fada mata

"Okay " ta mike tana binshi a baya,

Zazzaune ta gansu a dinning table, kara gaishe su tayi da yi musu ya gajiya,

Dan shiru sukayi, babu meh yin komai,

"Mom, Husna ta iya dafa abinci, exquisite i tell u, sai kin dan dana"

"Kayi gsky Ehsaas har missing girkinta nayi" inji Hajia, dake zaro 🍴daga cikin napkin dinsu,

"Bari in zuba maki" dama tasan warmers masu abincin hajia a ciki,

Tuwon alkama da egusi soup

"Oh My God, abinda nake tunani kenan" ya kara shakan kanshin

"Egusi soup, my God baxan manta da miyan nan bah"
Nan Baban Ehsaas yayi serving kanshi, shima tuwo da egusi din,

Bowl din ruwa ta kawo mai ya wanke hannu,

"Dad ka iya ci" ya daga kai kawai yana kai loma

"Uhmmm this is good, sannu da kokari Husna" kowa a wurin santin girkinta yakeyi amma banda Mom,
Da tayi kaman bata san da wata ajiya bah wai Husna,

"Mom dinka ta koya min cin African food, tun ina gudu har na daure na dan dana, and it was amazing, har san zuwa Nigeria nake ko dan Mom dinka tayi min girki"

Abinda babanshi beh fada bah shine yanxu ta daina, da wuya mah Mom dinshi tayi girki,

Mom dai ta tabe baki, shi ita kadai yake kallo yana son ya gano koh ta yaba da matar daya zaba,

"Asma'u koh" kowa yayi tsit da Mamanshi ta bude baki

"Meh kikeyi anan kuma meh ya kawo ki?" tana bude baki zata ansa ya rigata

"Karatu tazo yi, wasu abubuwa suka sa muka hadu da ita"

Babanshi yace good, meh kike karantawa

"Ahmmmm, Maths, teacher take son zama" ya sake amsawa

"Naxata mutane sai basu da yadda zasuyi suke yin teaching " kafin yayi magana Babanshi ya riga

"Nooo, honey, teaching good profession ne, da bama nan ai da bah teachers" yaji dadi da babanshi ya taimaka mai wajen bada ansa

"Kina da siblings ne? " tace Eh a hankali

"Baban yayanta nada aure kuma dan kasuwa ne, sai meh aiki a nan abuja financial Assistant ne, sannan meh studying sai Husna, itace last born"
Suna hada ido da ita yaga, idanunta sunyi jaa

"Wow! Yada sanin komai akanta kodai kodai" babanshi ya tsokana

Mamanshi kuma tayi guntun tsaki,


"Meh babanki keyi? " koda ya fara magana bata barshi ya karasa bah

"Wai kai ne Asma'u , koh bata da baki ne"
Tun anan yace akwai matsala,

Babu wani abu daya burgeta gameh da Husna da family dinta, da yanxu ta fara janta da hira kuma ta fara mata fara'a, saidai har yanxu tambayoyi kawai takeyi mata,


"Mom, Husna ta siyo maku gifts da taji zaku zo" mamanshi tace yayi shiru Asma'u ta gama

"Tana da register da asibiti amma, bata zuwa karban haihuwa can, a cikin unguwar mu takeyi" ta gama bayani akan Mamanta

"Haka nada kyau, Allah ya bata lada, dan tana taimakon Al'umma" ta amsa mah babanshi da Amin.

Gab da maghrib suka gama cin abinci, ita ta taya masu aiki tattara komai,

"Gashi Asma'u " mamanshi ta mika ta cup din data sha ruwa, bayan sun gama kwashe komai,

Tana jiyo hirar su sama sama daga kitchen inda take wanke wanke,

Bata sake fitowa bah sai can cikin dare, azatonta kowa yayi bacci
Shima kuma fitowarshi kenan da niyyan zarcewa dakinta, sai ya bita waje


"Sweet caramel" ajiyar zuciya tayi

"Kabar kirana da sunayen nan banaso" tayi gaba abinta,

"Ya akayi cara mia" ta juya dan tasan cigaba da bin ta zeyi,

😊😊😊😊
Murmushi taga yanayi

"Har kayi wani abun da zakayi farin ciki ne, bakin ciki ya kamata kayi" ya daure fuska yana harde hannu a kirji,

"Da raina, ina zaune kusa da kai amma ka dinga yimin karya" sai ya dan tausasa fuskar sa

"Husna___"
"Karya na daya daga cikin manyan zunubai, bakaji ance ka fadi alkhairi bah koh kayi shiru,

Kasan irin bala'in da yar karamar karya ze iya janyowa,
Kuma iyayenka kayi ma wa"

"Meh na fada aciki da yaje karya Husna, komai dana fada gsky ne, Akan babanki yan uwanki, duk gsky ne,

Kilan basu fadamaki bah, amma saida na tabbar komai nasu na tafiya normal kafin na fadi wani abu akansu"

Harde hannuwa tayi a kirji

"Naji labarin abinda kayi, tnk u but ina so in na bar nan,

Please Login or Register in order to submit comment