Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaman rirrigani takeyi zuwa kwanciyar hankali, da bacci meh dauke da good dreams"

Kallonta ya tsaya yi yana cije lips dinshi na kasa, tasan in ta fadamai kalamai irin haka gani yake kaman ba ita bace bah,

Itama taba mamakin kanta, da har take iya furta kalamai haka,

"Toh meh yasa kika bar fili tsakanin mu, ki matso manah in baki abinda yafi muryata dadi"

Koh bakinshi beh ida rufewa bah, sai gata lafe a jikinshi, shima kuma beh bata lokaci bah ya dukar da kanshi yana meh hada lips dinsu wuri daya,


Kiss din beh isheshi bah saida ya hada da shafa hannayenta da kuma kafarta zuwa guiwwa, beh tabo cinyarta bah, dan beh san yadda zata dauki abin bah duk da yaga itama tana jin dadin abinda sukeyi,

Itama ta taba karanta wani post na ire iren kisses, dan haka ta dage wajen yimai su, taga aikinsu dan sounds din dake fita daga makoshin shi canzawa sukayi, sannan ya kwantar da ita saman gado yana mata rumfa da jikinshi,


"Ehsaas" tayi kokarin saita fuskarshi gareta
"Ehsaas" muryarta ta kara kankan cewa,

Goshin shi ya dora saman nata suna fidda numfashi daya bayan daya, da sauri da sauri,


"Naga honeymoon dinmu zamuje, naxata mun shirya mah base dinmu na biyun karshe"

Saida ta kara shakan iska sosai kafin tayi magana,


"Bana da matsala, kawai dai banyi tsammanin abinda kayi bane bah"


*"matar dake hana mijinta hakkinshi ballagaza ce Namecy, bata san kima da daraja dake tattare da iya daukan wannan nauyin bah,
Of course zaki iya jan aji, ai mu mata da aji aka sanmu, amma hakan ya zama wani fanni ne na wasanni da kuma motsa sha'awa, koda sallah ne bakya yi ai kin iya saman mah mijinki natsuwa ta wasu hanyoyin"*

Ma'u ke maganan amma ita ke jin kunya, da ta tsaya bata gudu bah,tasan da Ma'u ta koya mata hanyoyin, gashi ita bata san abinda zatayi mai bah,

Shi yasa tace bah matsala su shiga next base din,

'Oh! Ko ina maganan tsare budurcin nawa' ta girgixa kai dan tunanin ya bace,


A sannu ya maida hannun shi inda ya cire data fara kiran sunan shi,

Dama idanunta a rufe suke tana tsimayar touch dinshi, kaman shafar iska haka yasa bayan hannun shi ya shafi dukiyar fulaninta,

Tana bude ido taga face dinta yake kallo,

"Jaanu" tace uhmmm tana kallon kirjinshi dan kunya ta hana ta kalli idanun shi,

"Kin san cewa babu wani meh ikon tabaki intimately sai ni, koh kallon ki babu meh wannan ijazat (izini) din sai ni"

Ta daga mai kai tana lashe lips dinta da suka bushe da harshenta,

"Bana so kiji tsorona shi yasa muke daukan komai step daya a lokaci daya, kin gane ai koh"

Ta sake daga mai kai,

"In yau yayi maki sauri ace mun shiga next step dinmu, toh ba komai kinji,

Communication nada matukar mahimmanci a aure Wifey,
Yana da kyau mu dinga fadama juna komai, ba boye boye, abinda kikeso ki fadamin wanda bakyaso mah, ya dace in sani,

Ta haka zamu karfafa auren mu"

Ta sake daga mai kai

"Zan iya, daga nan zuwa nan kawai" ya shafata daga saman kirjinta zuwa saman cinyoyinta,

"Tabawa kawai wifey" daga mai kai tayi tana wasa da yan yatsunta,

Daga da fuskarta yayi suka kalli juna,

"Tabawa kawai wifey, in kinji bazaki iya dauka bah, don't hesitate kice in bari kinji"

Ta amsa mai da toh,

Kulle idanunta tayi gam tana hango shi a cikin kanta,

Duk inda taji hannunshi a jikinta sai tayi imaging dinshi a wurin,

Ta haka ta kauda wani tsoro koh fargaba dataji daga farko,
Ehsaas ne tace a ranta, kuma ina san shi.





⚜B.W.AπŸ–Š
⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š





πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’




Dedicated to,
This smart, wonderful and Amazing ladies,

Ina taya ku murnar kammala littafin ku, Ξ”SMΣΣΠΔT, MΣΣMΞ”H,RΞ”HΣΣMΞ” and RΣΔL MΞ£H DΞ”MΞ²U ,
Books din kaman kar akai karshen su, haka kowanne da irin darasin da yake koyarwa, Kowa ya karanta yasan BRILLIANT minds ne suka rubuta littatafan

Allah ya karo tarin basira da hazaka,
Amin.




5⃣7⃣.


"Wai mazarin meh kakeyi neh" beh ba Mamanshi ansa bah sai hakora daya cigaba da washewa,

"Ka kula da diyar mutane Ehsaas, kasan amanace a wurin ka koh" yace toh da babban murya,

"Mun gode Hajia,sai mun dawo" tayi masu fatan Alkhairi,

Mom sai kallon su take ta kasan ido, murmushi tayi mata bayan ta gaisheta


"In kunje ka kula da babank kaji" ya amsa da Toh mom

"Kai ku shakata abin ku, ita in baxata iya bin mijin nata ta kula dashi bah, ita ta sani, koh zaman meh kikeyi anan mah, i don't know "
Mom yi tayi kaman bataji abinda Hajia tace bah, dama da hausa tayi magana dan haka Ehsaas beji bah,

"Ke kuma, dan Allah karki ja manah abin kunya, ki tsaya a inda aka ajeki"
Ta daga kai a can kasan muryarta kuma tace in shaa Allah,

"Kaje ka duba Danyah, kuma ka kirata" fuskar shi ta canza, amma beh bari rashin jin dadin abinda tace ya nuna a fuskarshi bah,

"Ka kirata ne" ya girgixa kai

"Kadai san bata da lfy koh" yace in shaa Allah ze kirata,


Suna fita waje ya janyo ta jikinshi,
"Ready wifey" tace yes tana zagaye kugunshi da hannunta,

"Sir" da sauri ta matsa baya tana dafe kirji,

"Sorry love yana san jefo ma mutane daga sama" dan dukar da kai yayi sannan yace sorry,

"Ya akayi ne Alfie"

"Na shirya duk abinda kace Sir, baka bukatar in biku dan in cigaba da tafiyar muku da komai"
Matar shi ya kalla da ta bata rai,

"No, ka barshi kawai, ka karasa abubuwan dana bari ban gama bah"
Yace toh sannan yajawo wani zancen,
Dataji akan Danyah ne sai ta kama madafa,


Ma'u ta kira suna kara sallama, duk wanda ta gayama zasuyi tafiya sai tace yan uwanshi na can zasuje gani,
Su Ma'u aka dage ana bata tips din yadda zatayi mu'amula da yan uwan miji,

"Banda san jiki da kadaita kanki, ki saki rai ayi magana sosai dake"

Da dariya tace Toh aunty tah, matar yayana,

Tsaki Ma'u tayi ta kashe wayarta,
Girgixa kai tayi tana mamakin abinda ya hadasu da har yanxu bata huce bah, Ma'u da bata da rikon abu ga saurin yafiya,

"Kedawa ke dariya wifey"
Ta fadamai tana sa wayarta cikin jaka,

"Kin fadama kowa yau zamu wuce" ta daga mai kai,

"Duk na fada musu yau zamuje in ga dangin ka" hmmm yace

Kusa da ita ya zauna bayan ya shiga motan, A sannu Lukman ke jansu har Airport,

"Dama ka bari sun rakomu, ji yadda ko ina ya cika da mutane"
Yar dariya yayi dan yasan tsoran hawa jirgin takeyi,


"Ina tare dake koh?" Ta daga mai kai,

"Kuma tare zamu hau, zan bari ki makalkaleni in kikaji bazaki iya zama a naki sit din bah"
Sakin shi tayi tana turo baki

"Wayace tsoro nakeji" hmmm yace da murmushi,


Ba bata time akayi masu jagora zuwa wani jirgi, taga sauran duk kayansu ana dubawa amma nasu kawai dauka akayi,

Bata taba ganin jirgi face to face bah, amma tayi zaton zefi haka girma,

"WOW" ta fada baki, ido da hanci bude,

Murmushi yayi yana wani kara cika da batsewa dan yayi abinda ya birgeta,


"In bakomai sir zamu daga nan da minti sha biyar" ya girgixa mata kai sai matar meh kula da passenger din jirgin tace toh tana tafiya,

"Mu kadai zamu tafi?" Yar dariya yayi,

"Abinda ke faruwa kenan ai in kika shiga private plane"

Cire coat dinshi yayi, sannan ya kishingida jikin kujera yana kallonta da murmushi,

Har yanxu bata nemi zama bah, kawai kallon jirgin takeyi tana shafa leather seats din da kuma nutsa kafarta cikin carpet din daya kewaye kasan jirgin,

Daga wata speaker taji ana cewa su zauna su sa seat belt dinsu,

'Badai tayi minti 15 tana kallon jirgin bah kaman wata bakauyiya"

Ta gefen ido ta hango shi yana cije bakinshi dan kar dariyar shi ta fito,


"Lokacin tashi yayi Caramel, ki zauna"

Kujerar dake kallon tashi ya zaunar da ita, sannan ya makala mata seat belt, duk inda hannun shi ya gogi jikinta sai taji wani gashin jikinta ya tashi,


Ta dake iya dakewa,amma jirgin na fara dagawa ta kankame hannun seat sannan ta kulle idanunta gam,
Ji tayi kanta na juyawa,

"Wifey" ya balle nashi seatbelt din yana kokarin cire mata nata, saiga ma'aikaciyar jirgin,

"Sir" beh bari ta karasa bah yace ta barsu,
Duk da dan kariyar sune saita kyale ta koma nasu bangaren,

"Sorry, kauyanci na yayi yawa" girgixa kai yayi yana shafa face dinta,

Yanxu tsoron nata ya lafa, saida suka daidaita a sama sannan ta iya bude ido,


"Yanxu komai lfy" ta daga mai kai, murmushi yayi meh kama dana mugunta,

"Dazu na naxata balle seatbelt din zakiyi ki gudu" kokarin sauka daga jikinshi tayi, amma ya riketa,

Tunda ya fiddo ta daga nata kujerar ya maidata saman cinyar shi ya rungume abinshu gam,


"Karki damu zaki saba, tun ina dan karami nake hawa jirgi"

Stewardess din jirgin ta shigo dauke da tray guda biyu,
Da sauri ta mike tana karban mata,

"Tnk u" tace da murmushi sannan ta jerasu a saman table,

Saida aka gama kawowa sannan tayi serving dinshi,

"No muci wannan tare" ya bata spoon da fork,
"Minti daya" ya dandana komai sannan ya zabi abinci masu gina jiki da masu kara lafiya,

Wacce ta kawo abincin ya kira,
"A kawo manah zuma koh Yoghurt" tace suna da duka biyu, sai ya jin jina kai yace a kawo duka,

"Naga kullum sai kin sha daya daga ciki koh" daga mai kai tayi,

Ana kawowa ya debo ze bata a baki,

"Aa ka bari" yace hah yana bin duk inda tayi da fuskarta da spoon cike da kwai

"Allah wifey ki bari, raina ze baci" tayi mamaki da tunda suke tare sai yau zasuyi irin abinnan, kodan kullum cikin mutane suke cin abinci,

A kunyace ta bude pouty lips dinta yasa mata a baki, ana ukun ne tace ya bari yaci abincin shi,

"Sai kin koshi sannan" sai tace ta koshi,

"Liar liar pants on fire" yace yana yanko Sausage din da akayi da naman shanu, kuma ya gasu yayi laushi,


"Bude wannan kissable lips din" dan lashe lips dinta na kasa tayi tana cijewa

"Wifey akwai ki da kwadaita mah mutum abu ba tareda kin san kinayi bah"
Ta dan bude idanu,

"Meh nayi toh" murmushi yayi aranshi kuma yana bata ansa

'Zaki sani neh ai, baridai muje honeymoon dinnan'

"Toh nima bari in baka, kar abincin ya huce inka tsaya bani"
Murza hannuwan shi yayi wuri daya,yana nuna jin dadin shi,


"Ina so indai zaki bani"
Gyara hannun rigarta tayi sannan ta cire gyalen data yafa a saman kanta,

Yana bata tana bashi a baki har suka kusan cinye komai da aka kawo,

Magazine ta dinga kallo shi kuma ya danyi wasu ayyuka a laptop, da suka gaji kuma suka kwanta a dakin dake cikin jirgin, har Allah ya saukesu lfy.




*PΓΕ”Δ¨Εš*

"Naxata Venice zamuje" ya daga mata kai

"Na canza manah abubuwan, ina da wasu plans mah Venice"
Yayi wani karkataccen murmushi

"Allah ya kaimu can da rai da lfy" yace amin Amore mio

Yana rike da hannunta, sai aikin kallonta yakeyi, ita kuma ta zubama window idanu tana ta kallon gari,

Wasu abubuwan in ta gani sai WOW ya fito daga bakinta,

Ji tayi kawai ya juyo da face dinta zuwa nashi, ya hade lips dinsu yana aika mata da sakonni, itama a sannu take maida mai martani,

Limousine ce suka shiga da jirgin nasu ya sauka, driver na can gaba su suna baya abinsu,

Sai ji sukayi ana bude kofa, Ajiyar zuciya yayi kafin ya rikota suka fita daga cikin motar, aka kwasu kaya sannan aka bisu dashi,
Ma'aikatan wurin na ganinsu, sukayi masu jagora zuwa masaukin su,


"Yau ba zagaye gari koh, na gaji sosai"
Kwanciya yayi yana dora kai saman cinyarta, Addu'a ta idar ta shafa kafin ta kalleshi,

"Kinyi min Addu'a " da murmushi ta daga mai kai,

"Kin san abubuwan da nakeso neh" ta girgixa kai,

"Amma na roki Allah ya amshi ibadun ka, sannan ya amsa maka duk bukatun ka na Alkhairi "

Zaune ya tashi, sannan ya juya yana kallonta,

"Kullum sai nayi maka addu'a, babu mah kyau mace ta idar da sallah batayi mah mijinta Addu'a bah"
Bece komai bah sai kallonta da yakeyi, tashi tsaye tayi tana warware babban gyalenta,

"Love tsaya" tana juyowa ta ganshi a tsaye,

"Abinci zamuci yanxu koh" tsuke bakinta tayi da taga ba wasa a fuskar shi,


"Kina sona Husna" ta danyi ajiyar zuciya,

"Dama abinda zaka fada kenan ka wani ci fuska" damke hannunta yayi,

"Be serious Husna, do you love me"
Idanunta tasa cikin nashi,

"Naxata basai na fada bah, naxata abubuwan da nakeyi sun isa su nuna maka haka Ehsaas "
Ya girgixa kai, fuskar shi bah murmushi,

"Nunawa kawai baxe isa bah Husna, sai kin dinga fadamin,
Kuma banda kiran sunana"
Ta dukar da kai kasa,
"Sorry, naga kana so ne shi yasa nake fada wani lokacin"

"Fadamin toh Husna, say you love me"
Bugun zuciyarta ya linku data dago kai suka hada ido,

"Fada in ji My wife" ya jawota jikinshi suna fuskantar juna,

Dan siririn numfashi ya fita daga bakinta,

"I __"

Knocking ya katse mata abinda zatace

"Monsieur " hannu ya mika ma wanda yayi magana,

"Pascal, mutumina"sukayi gaisuwar su na hada kafadu da dan bugun bayan juna,

"Yi hakuri ban samu tarban ku bah, amma ga hanyata na bada hakuri"
Ya lissafo sunayen wasu abinci da wani wine,

"Pascal, kasan abinda mutum ke bukata, tnk u"

Jawo table din da ake jero abincin tayi,

"Wifey" kafin ya rufe baki ta amsa mai

"Inna lillahi" ta bata fuska data dan dana wani abin da aka kawo
"Wannan tsami tsami"

Zaune yayi yana dariyar mugunta daga gefe, dama koh kallon abincin da aka kawo beyi bah, itace ta bude da niyyan zuba masu,


"Pls ka fadamin wanda zan iya ci" ya make kafada yana zaban wasu abubuwa yana sawa a nashi plate din,

"Meye wannan" dodon kodi yace,.
Harda yar kara tayi kafin ta saki wanda ta dauka,

Aje plate din hannun shi yayi yana dariya iya karfin shi,

Bata san lokacin data koma bangaren da yake bah ta haye jikin shi sannan ta jawo plate dinshi gabanta,

"Kuma cinyewa zanyi" dora habarshi yayi a kafadarta, sannan ya kara janyota jikinshi,

"In kinci kaman naci ne koh" ta girgixa kai
"Toh nafi son kici, lafiyar ki top priority dina ce"
Dan gyara zamanta tayi dan ta iya kallonshi,

"Nima ai haka ne a wuri na, bude bakinka"

Ya bi umarnin data bashi,
"Wine din zaka sha" yace harda ke
Yana zubawa a kofi saita bata rai,

"Wasa nakeyi, Pascal yasan bana shan Alcoholic, fruit juice ne kawai da fancy name"
Ya tsiyaya mata a glass hade da mika mata,

"My All" ya bude idanun daya lumshe ta zata mah bacci yakeyi,

"My wife" ya sumbaci tafin hannunta,

"Dana aure ka nasan ina matukar giramama ka kuma ina ganin mutuncin ka,
A sannu kuma ya canza zuwa wani abu, I love you, yaudarar kaina nakeyi in nace ban tsunduma cikin sanka bah Hubby"
Ta shafi gafen fuskar shi, tana wasa da sajen shi dan bataso ta hada ido dashi,

'Kullum zan fada kuma zan nuna maka irin son da nakeyi maka,
A cikin ko wani irin hali muke, bazan sake mantawa koh inyi sakacin fada maka ina sonka bah, da tsufan mu koh da yarintar mu'

Ta karasa acikin ranta, sannan ta dago idanun nan farare kal da ke kewaye da kwalli,

"I love you mijina, kai ne jagorar rayuwata, a duk duniya bana tunanin akwai wanda yayi sa'an miji kaman ni,
Allah ya baka hakurin zama dani da kuma hakuri da kura kurai ni, dan adam ajixine,
Kaji hubby"

"Zaka dinga hakuri dani koh" sai lokacin ya fidda numfashin daya dade yana rikewa dan kar wani kalami nata ya wuce shi, yayin da yake shakan iska,

"Saidai muyi hakuri da juna matata, kaman yadda kikace, dan adam ajizi ne, babu wanda ya cika goma daidai,
I love you so much da wani lokacin ina tunanin inda babu ke a rayuwata da nayi babban rashi"

Lumsha ido tayi, sai ya dago da fuskarta, bakinta ya shafa da baban yatsan shi,

"Meh ya samu kissable lips din nawa neh, koh an daina kwadayin su"

Hmmm yace da murmushi, turo bakinta tayi bayan ta dan lashe su da harshenta,

Sadakarwa yayi hau kissing dinta, aski yazo gaban goshi shi yasa dauriyar tashi ta ragu sosai, Ajiyar zuciya sukayi a tare,


Rufe idanu tayi tana dagewa wajen yin abinda taga mijinta na so,
A yadda bata ganin kowa sai shi tasan babu abinda baxata iya yimai bah,
Dukanta yayi ya nufi saman gado, ya shimfideta, sannan ya kwanta ta gefenta,




"Hunsa, komai lfy" ta kara shigewa jikinshi

"A jikin ka nakeso inyi bacci yau" ya nuna mata jin dadin shi ta hanyar gyara mata kwanciya a jikinshi,

"I love you"
"I love you more" tayi murmushi daya kasa boye farin cikin shi.


Saboda kaguwa taga gari koh breakfast bata bari sunyi bah,

"Naxata suit zakasa yau mah" jeans yasa baki da wani cashmere sweater, sannan ya dora double breasted coat a sama,

"Bakya san ina sa suit ne" ta girgixa kai
"Koh meh kasa yana maka kyau, dan na saba ganin ka da suit ne kawai"

Yayi wani dan murmushi meh hmmmmm,
Wani bakin leggings da tank top yace tasa, kayan ta tsaya kallo, muma tana tuno lokacin da Danyah tasa riga da wando sukayi mata kyau kuma,


"Yawo zamuyi Husna, karki sa kayan daze takura ki"
Ya fita ya bar mata dakin,

Wani coat ta dora cream color saman kayan sai tayi rolling da bakin gyale, tasa loafers baki,

"Yayi koh in canza"saida ya gama kallonta sannan ya daga kai,

Basu kadai akeyi mah jagora bah, saidai basu da wani yawa,

Wani bus suka hau da ba kujeru, tunda inda zasuje ba nisa daga hotel din kuma zasu ga gari ta haka,

Ita keta kallon gari shi ita yake kallo, sai so yake ya ga irin abinda take gani dake sata tayi ta murmushi ita kadai, mamaki ya nuna a idanunta, bakinta ya dan bude kadan,

Wani dan paper aka basu da list din wuraren da zasuje, da dan karamin tarihin wurin,



Please Login or Register in order to submit comment