Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakomai

"Babu abinda kayimin na bada hakuri, zanje in ga Mamana, in sanar dasu zuwan hajia"

Zata kashe ya tsayar da ita

"Na gayama Baba, yasan zata zo, kuma nayi mai bayanin abinda ze kawota,

Na manta sunan data kira abin

Amma tace hanayr gaya ma iyayenki cewa ina son in aureki ne,

In nayi sa'a daga nan asa manah rana, na roki baba kar ya wuce 2 weeks, haka ma Granny ma nayi pleading da ita karta dawo sai ansa manah rana"

Katse shi tayi da yayi haka nan

"Sorry in ina cikin farin ciki maganan fitowa kawai yakeyi,

Meh kikeso kice? yauwwa na tuna kafin in manta
Granny ma tace in baki Kudi saboda preparation din bikin mu,

Nawa zaki bukata, koh kawai in turo maki, and ki fadamin in kina son kari, bari dai ki fadamin____"

Katse kiran tayi sannan ta kashe wayan, komawa daki tayi ta zuba uban tagumi da hannu biyu,


'Ni kuma haka zan kare, na farko beh ganin darajar iyayena,

Na biyu yana girmama su, amma beh san irin alakar dake tsakanin su bah,

Wake ce mah surukan shi yana so a sa rana gatse gatse,
Mtsewwwww,

Allah yaso mah Baba yasan ba anan ya tashi bah, duk beh san yadda ake komai bah'

Wani tsakin ta karayi, sannan ta mike saman gado,
Zumbur ta mike kuma

'Barin gdannnan zanyi kafin kakarshi ta iso'

Tana so ta kunna wayarta kuma ta tuno dashi, fasawa tayi ta shiga wanka,

Cikin shiri ta nufi bangaren da iyayenta suke, zata shiga dakin mamarsu taji kamshi na tashi

"Mama meh yasa baki tasheni bah nayi wannan aiki"
Ta amshi suyan da mamanta keyi

"Naga akwai gajiyan tafiya a tare dake" ta dan bata fuska

"Kwana biyar fah da dawowata, gajiya ai tabi lfy"
Mantawa tayi da batun tafiya ta zauna sukayi aikin tare,

Kammalawar su kenan suka tsinkayi sallamar Hajia,

Duk sukayi cirko cirko, babu meh cewa komai

"Sai gashi mun sake haduwa" ta fada da fara'a tana cire glass dinta medicated

"Maraba Hajia" mamanta tayi mata iso har cikin falo

Ita ma kuma ta duka har kasa ta gaishe

"Lfy lau Asma'u, shine tunda kika gudo koh dan kira babu, watau kinga Mamanki koh". Ta dukar da kai ta dan murmushi

" sannu da zuwa Hajia, ya hanya?" Mamanta ta mike ta nufi kitchen

Tana amsawa itama tayi kitchen

"Kai mata wadan nan" ta dauki ruwa da juice sannan ta kai mata parlor.

Daki ta koma ta zauna, sannan ta kunna wayarta,

Messages dinshi ta gani birjik, duk magiya yakeyi yana bata hakuri, a text din mah shagawaba yake zubawa, ko wanne da emoji iri iri yake karewa,

Ajiyar zuciya tayi sannan ta mike ta sake kimtsa kanta, dan zuwa gdan su Ma'u,

Ta kofar kitchen tayi niyyan fita, dan karta ratsa su a falo,

"Duk a rana daya koh" taji muryar Hajia tana fada da yar raha

"Bazanyi maku karya bah, ba karamin fargaba nayi bah dana tuno ni kadai zan iya shige mah Ehsaas gaba a maganan auren nan,

Bugu da kari mutunci na dana zubar a farkon haduwar mu"
Muryar babanta taji yana katse Hajia

"Ai komai ya wuce Hajia, mu gode Allah daya sa muka sasanta kafin rai yayi halinshi"

Mamanta mah tace komai ya wuce Ai,

"Dama nasan nan gdan karamci ne da Mutunci,

Shi yasa zan fada maku tsakani da Allah,

Nasan kuma kunyi mamaki da na zo da bukatar neman hannun diyar ku, ni da kaina ba wasu daga cikin dangi bah"

Ta dan jingina da bango, tana sauraren su

"Shekarun baya mun dan samu sabani da Yan uwana, Ban taba sa Ehsaas bah sai shekaran nan tunda aka haifeshi, saboda kasan gaba daya diyata ta bari dama kuma babanshi ba dan nan bane bah,

Saidai ina rokon ku kada wannan yasa ku ki bukatata,

Kun san Ehsaas kun ganshi ba sau daya bah,

Ku yanke hukunci da kanku, nasan in Allahbya yarda baze cutar da Asma'u bah"

Kaman ta leka taga fuskokin su da shirun yayi yawa,
Ji tayi gabanta na faduwa, ta tsinci kanta da fargaban ban kwana da Ehsaas,


"Tabbas jikan ki ya gwada mana hallarci,

Sabanin dake tsakanin ki da yan uwanku kuma wannan rubutaccen abu, Allah yayi dama ze faru,

Ina fatan zaku warware komai, A kowani family dama akwai irin nasu matsalan, saidai ni'ima ne babba ya kasance kanada dangin mah"

Hajia tace hakane
"Ni kokari nakeyi inga mun sasanta"

"Allah yasa hakannya faru" bayan wani shirun kuma ya biyo baya sai taji gyaran murya

"Dan tani Yaron wurinku yayi min, amma bada ni ze zauna bah" taji sun danyi dariya kasa kasa

"Sai munji daga bakin ita Asma'u tukunna, in ta amince kuma sai muyi magana da na gaba damu, koh ba haka bah"

Hajia tace haka abin yake,

"Bana tunanin za'a samu matsala ma ta fannin Asma'u, dan naga tana sakewa sosai"
Ta dan zaro ido data ji zancen mahaifiyar ta

"Bari in kirata____ ". Tana jin haka ta kara ma bujenta iska.



"Arghhhhh, meye hakan?" Tasa hannu tana rufe idanu

"Sai yau kika zo ganina Namecy" tana tunkarota ta matsa baya

"Little sis har bakinmu sun tafi ne" bude ido tayi da kyau tana kallon su

"Ku biyun nan koh" ya abbah ya fashe da dariya, sannan ya rike hannun Ma'u yana cewa sai anjima,

Baki bude take kallon aminiyar tata,

"Ma'u?"
Itama tace
"Asma'u"
"Mu shiga ciki" ta jata zuwa dakin su

"Meye wai har yanxu kika wani zaro idanu"
Ita dai sai kara hango yanayin data gansu tayi,

Jikin bango taga Ma'u ta makure yayan nata, fuskokin su daf da daf kaman zasu hada bakinsu wuri daya,

Ko isowarta basu ji bah, da alamu Ya Abbah ya harzuka Ma'u ne ita kuma marar hakurin ta biye mai,

'Amma abinda na gani yafi haka' ta fada ma kanta

"Tun yaushe kuke tare baki fadamin bah" taga kaman Kunya ya kama Ma'u

"Ni ban mah san yaushe muka fara bah, amma nace sai ya tambayi izini kafin in amince dashi"

Tayi tayi miginawa saman gado tana bata labari, mamaki mah ya hana ta saurareta da kyau.


"Ki dauka manah" tun dazu call dinshi ke shigowa tana bari ya tsinke,

"Wallahi ki bari babu kyau wulakanci"
Ta kalli Ma'u
"Ba wulakanci bane bah, takuran shi yayi yawa"

Ma'u ta hankada ta gefe

"Sai mutum ya damu dakai ze takura ka ai koh, ki dauka kiji abinda zece"

Yana sake kira ta mike ta fita,

"Am not happy" abinda ya fara fada kenan,

"Sorry"
"Sorry bazeyi bah Asma'u, har fushi naso inyi ban san abinda yasa na cigaba da kiran ki bah"
Ta sake bashi hakuri

"Dama ina so in san in komai lfy"
Tace mai Alhamdulillah,

"Uhmm hmmm" sai ya katse kiran,
Ba karamin mamaki hakan ya bata bah, da har ta kasa boyewa mah Ma'u

"Kaman da gaske yayi fushi" ta kwada mata pillow

"Kinga abinda nake ce maki koh,idiot kawai"

Ta kwace pillow din da taga zata sake kwada mata

"Namecy, am not blind, abubuwa da dama sun faru dake, nasan kuma ke sarkin zurfin ciki ce,

Amma aure zakiyi kuma nasan kina fata ya daure har karshen rayuwar ku koh"

A hankali ta daga mata kai

"Abinda nakeson ji kenan Ai, kinsan Allah tunda kikayi aure na fara maida hankali kan koyan zamantakewa da kuma koyan abubuwan da zasu amfane ni anan da gdan mijina,

Aurenki na farko ban samu munyi chat dinnan bah, saboda nima kaina beh waye bah sosai, amma banda wannan in shaa Allah sai munyi duk abinda bamu samu yi bah a wancan"

Itama ta maida mata murmushi,

"Bashi hakuri dai yanxu, sai kizo muyi magana" mikewa tayi tana goge zufan da hannunta yayi daga tunanin yin magana dashi,


"Ba laifin ki bane bah Husna"
Bayan ta gama kame kame ta samu ta bashi hakuri

"Na kasa ganewa ne Husna, da ina ganin kaman everything is good tsakanin mu, amma yanxu kin jefani cikin rudani"

Kasa ta zauna tana jiran ya cigaba

"Babu abinda zakice"
Ajiyar zuciya kawai tayi

"Kina mah sona Husna, koh takuraki nakeyi, in bakya sona meh yasa kika amince zaki aureni,

Am really confused wallahi"
Tsintar kanta tayi cikin wani yanayi, kaman itama an sam mata radadin da tasan yananji

"Am really sorry, pls"
Yayi ajiyar zuciya

"Manta kawai Husna, granny mah ta taho ne?" Ya karasa da tambaya

"Ina so in aureka Ehsaas" ta rufe idanu gam tana gama fadan haka

"Nima haka Husna" taji murna cikun muryar shi

"Yaushe ne auren toh my wife" tace ita bata sani bah

Cikin kan kanin lokaci ya koma Ehsaas din data sani, meh fara'a, shagawaba da san wasa,

"Zamuyi magana anjima koh" tace mai In Shaa Allah.




⚜B.W.AπŸ–Š
[3/26, 06:18] β€ͺ+227 99 95 15 93‬: ⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š




πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Mun sadaukar da page dinnan gareku Masoyan littafin nan,

KHALEESI
&
NOBLE JUDGE

Na miko gaisuwar ban girma, Allah ya barmu tare ya karo dimbin kauna,

Mun gode da kulawa, Allah ya hada fuskokin mu a Aljannatul Firdausi.



4⃣5⃣.


Duban shi ya maida kan hanyar shigowa falo din,

Saura sati daya a daura auren su da Asma'u, basu kara samun sabani bah saida tace bata son ya bata kudi,

Bayan Granny ma tacemai itama tanada nata hidiman,

Nuna mata yayi ranshi ya baci, dan yason bata san haka,
Hakuri ta fara bashi sannan tace mai Tagode,

Jiya babanshi ya iso garin, ya kuma da safe ya fita, bashi ya dawo bah sai bayan dhur,
Daya tunkareshi kuma yace mai bari yayi magana da Mom da Granny Ma,

Sun kusan Minti 30 acikin dakin,shi kuma sai aikin duba agogo yakeyi,


"Ehsaas" da gudu ya amsa kiran yana shiga dakin,

"Gani Granny Ma" ya hau har saman gado

"Tnk u tnk u tnk u" ta jashi jikinta tana hawayen farin ciki

"Zuwan ka kasar nan Alkhairi ne Jikana,

Kalla" ta mika mai wani envelope yana fiddowa yaga I.V ne amma ba wanda sukayi bah


"Babanka ya kai musu I.V din bikin ka, ina ta fargaban abinda ze biyo baya,

Sai gashi sun amshi gayyatar harda nasu hidiman,

Wannan zasu rabama sauran King Family, sannan sunce mu bar Kayan Lefe"

Yayi searching brain dinshi ma inda ya taba jin 'lefe'

"Oh! Kayan da kika ce zaki zaba da kanki"
Ta daga mai kai sau biyu

"WoW! Abin yayi kyau, so generous"
Ta kara katse shi da wani good news

"Ba wannan kadai bah, a compound dinsu za'a daura auren ka"

Ya fiddo idanu
"Kina nufin zanje in gansu" shi da kakar tashi sai aikin washe hakora sukeyi
Har Mahaifiyar shi na tsammani kumantu na musu zafi,

"Tnk u Dad" ya tashi da I.V din a hannu ya rungume babanshi,

Sai lokacin yaga yadda Mamanshi ta hade girar up da down

"Ni dai nace Allah yasa ba wani salon wulakanci bane bah wannan"
Ta harde hannuwa a kirji
'Akwai daurewa a gdan yau kenan, tunda Dad beh fadamata bah ya tafi can'

Kallon baban nashi yayi yaga beh damu bah,

Fatan Allah yasa komai lfy tsakanin su yayi,

Dan zaman su ba irin na kowani ma'aurata bane bah,

"In suka wulakanta mu ai kansu suka wulakanta, tunda duk jini daya muke,

Kuma nasan zasu zo kawo manah kayan lefe mu gani kafin su tafi,
Safiyya zaki tarbesu da hannu bibbiyu"

Juyawa yayi ya bar dakin, daga yadda Granny ma keyi ma mamanshi magana duk da da hausa ne yasan fada takeyi mata,


"Tnk u Dad" ya kara fada a fili bayan ya gama karanta katin

Da manyan Baki Aka kara mai Malik a karshen sunanan shi

Mubarak Mas'ud Malik,
Sama kuma aka sa KING family na gayyatar daurin auren dansu,

"Bari in fadama Husna" ya jawo wayarshi.



Daren daurin auren nasu kasa bacci yayi, itama Amaryar ya hanata bacci,

Tun tana yin katuwar hamma dan yaji ya kyaleta,
Har ta tashi zaune dan baccin ya wartsake mata,

Bada san ranta bah ta cigaba da amsa mai in yayi magana, dan bacci ze iya awonngaba da ita,

Kasa fadamai tayi cewa zasu zo Abuja gobe din, dan tasan wani rigima zeyi, kila mah ya hanata komawa gda,

Yana cikin baccin shi meh dadi harda mafarki, sai murmushi yakeyi, yaji ana tada shi

"Uhm uhmmm" ya sake mirginawa

"Ehsaas kana so ka makara ne ranar daurin auren ka"
Ba sai an sake fada bah, dan zaumbur ya mike da idanu waje

"Yau ne, inna lillahi yau ne!!!"
Ya tashi tsaye yana tsalle saman gado
Babanshi mah ya tayashi ta hanyar yin dariya,

Shigowar Mom ne ta katse su,

"Baka shirya bah" ya wuntsilo kasa

"Good morning" ya hadesu wuri daya ya rungume

"Morning" suka amsa suma suna kara kankame dan nasu,

Kallon kanshi yayi a madubi, yana aje ranar a cikin kanshi,

Yau ya fara sa manyan kaya, babbar riga, yar ciki da hula, babbar rigar wani creamy Golden color ce, meh aiki baki,
Yar ciki da wando kuma bakake ne, sai hular shi baki da akayi mah kwalliya da zare Golden,

Kara tausaya mah kakarshi yayi da sukaje King Mansion, yaga gdan makil da mutane duk mutanen data taso tare da su,
Kowa yasan kowa, hira kawai akeyi,
Sai zuwa gaishe dasu akeyi ana mai congratulations, saidai babu wanda ya tambayi Hajia koh Mahaifiyar shi,

Haka ma kawunshi, kuma walliyin shi, har aka daura aure kan sadakin Dubu dari, kuma aka gama duk abinda ya dace,
Har suka taho kawun shi beh tambayi Halin da mahaifiyar shi da kuma kanwar shi suke ciki bah,

"Dama kasan manyan kaya basa yi maka kyau shi yasa baka sawa"
Dariyar da bata kai ciki bah yayi,

"Kanwata baiwar Allah nasan baxata ce bakayi kyau bah,
Kuma saboda ita zan daukeka hoto"
Dariya sukayi su duka, dan ya saba da tsokanar ya Abbah.


Sai cikin dare suka dawo, suda ya kamata su riga wadanda sukaje daurin aure dawowa,

Aikan sun sha fada, ba a gdansu bah har da sukaje gdansu Ma'u,

"Zaki sanar dashi kin fita koh" ta bata fuska

"Ai dana fita ba'ayi komai bah lokacin" Ma'u ta mata kallon tamabaya

"Da zamu dawo kuma fah" tuno ranar daya sata fadan hakkokin shi dake kanta tayi,

"Ni duk neman izinin nan ne banah so" saida ta dawo masu da abinci sannan ta yi magana

"Ai baki da tacewa kuma yanxu, koh Azumin nafilan nan da kikeson yi saida izinin shi"
Ranar mah saida tayi, a kan hanya tasha ruwa,

"Allah yaso aunty karima bata fada musu inda kika sa mukaje bah"
Tana kai spoon baki kiranshi ya shigo

Gabanta ne ya fadi
"Yanxu a matsayin matar shi nake koh"
Ma'u ta fashe da dariya

"Namecy wani shirman mah sai ke wallahi, in tafi koh zakiyi blowing mai hot kisses ne" ta dan harareta

"Waze san lokacin da zakiyi kike wani bata rai, gwara ki mah bari"

Kiran ya katse, yana sake kira ta dauka

"yanxu ke mata tace koh, mallaki na" shima wani ____ din ya fada

"Ina wuni?" Ma'u ta dan tsinkuleta

" ki kashe murya" ta fada a hankali

Ta make kafada ita kuma
"Useless human being, wa zaki kashe ma murya in bashi bah toh, kiyi abinda nace" harda zare mata idanu,
Abin mah ya bata dariya


"Kina jina kuwa" tace uhmm

"Duk yau dinnan sukuku na yini Matata" ta kalli Ma'u sannan ta danyi gyaran murya

"Wani abune ya faru" Ma'u tayi ajiyar zuciya tana da karkiyi
Tayi mata gwalo

"Duk abubuwan farin ciki ne, amma da nafi jin dadi in kina nan"
Ta dan sunkuyar da kai kasa,
"Dazu nace zanzo in daukoki" ta fara girgixa kai kaman yana ganinta

"Haider yayi min dariya, wai ba haka akeyi bah"
Ba haka bane bah kam, ta dan saki ranta,

"Meh kikeyi ne love" tace bakomai
"Nima haka, tuntuni nake kwance, birgima kawai nakeyi na kasa bacci, kin san meh yasa"
Tace uhm uhmmm

"Ina kewarki, i miss you so much, wata daya da kwana uku kenan rabon da in saki a idona"
Tayi lamo tana jinshi

"Yaushe zaki dawo wifey ,ina bukatar ki a kusa dani" tayi ajiyar zuciya.
"Kice wani abu manah" ta dan yi kasa da murya

"Ni bansan abinda zance bah" yayi yar karamar dariya

"Ki ban labari toh, koh kuma bari in baki tatsuniyar da granny ma ta taba yimin"
"Tatsuniya kuma?" Ya sake yin wannan karamar dariyar meh hmmmm

"Yap story story my love, gwara ki saurara da kyau
Kila ke zaki bah yāyā da jikokin mu wata rana"

Yana cewa yaya, yan han jinta suka daure, hankalinta ya tashi haka zuciyarta ta fara bugawa da sauri kaman zata balla kirjinta ta fito, kyarman da hannunta ya fara yasa ta yarda wayan,
Ma'u na ganin haka tayo kanta,

"Asma'u" ta daga idanun da suka firgito tana kallonta,
"Yi mai sallama tukunna" ta kanga mata wayan a kunne

"Na'am" tace dataji yana kiran sunan ta

"Ya akayi" ta rufe ido dan karta sake hango abinda kwakwalwarta ta hasko mata dazu da yace Yaya da Jikoki,

Uxuri ta nemah ta fadamai
"Am so sorry love, Mom mah nata complain din ciwon kai,
Ya kamata ace nasan kema ze dame ki, am so sorry" tace uhmm

"Karki sha ko wani magani, hutu kawai kike bukata,
Ki sha ruwa sosai sannan ki kwanta bacci, kice kar kowa ya dameki"
Tace mai Toh ta gode

"Allah ya kara sauki Love" da Amin ta matsar da kanta, Ma'u ta kashe wayan,

"Ya akayi namecy" hannu tasa tana matse cikinta

"Ji nayi cikina ya daure lokaci daya"
Ma'u ta tashi tana girgixa kai,
"Duk rashin cin abincin nan ne"
Tace uhmm

Babu wanda ta taba fadama abinda yafi bata tsoro a duk fadin duniyar nan,

Bata taba fadama kowa abinda ya faru bah,

Raees mah ya sani neh dan shi ya taimaka mata,

Cikin zullumi ta kwana, washegari kuma Asma'u ta cikata da kayan gyaran jiki, dana kara ni'ima, abinda ke kara tada mata hankali,


"Namecy focus manah, kila yau za'a kai ki, gwara ki tsaya inyi maki bayani sosai"
Dan karamin smile ta bata sannan tayi kokarin fidda damuwa daga cikin ranta,


"Salamu Alaikum"
Ya amsa mata da fara'a

"Na ga missed calls dinka, kuma tun dazu nake trying"
Awwwwww yace da wasa

"Kinyi missing dina neh" ya cigaba da bata bashi ansa bah,

"Ki canki in da nake yanxu" ta fiddo idanu

"Kana gda" yace uhmm uhmm
"Kana wurin aiki"
"Uhmmm ina wirin aiki amma ba'a gda bah"

"Ina Australia, Granny ma tace sai karshen satin nan zaku zo, shi yasa naga gwara in yi ayyuka na yanxu, dan in samu yin honeymoon dina hankali kwance"
Ta dafe kai, aure na canza mutane ta fada a ranta,

"Okay toh Allah ya bada sa'a" yace Amin

Sannan sukayi sallama, Ma'u taji dadin lokacin da suka kara samu, dan ita da gaske so take ta gyara Asma'u kuma ta wayar mata da kai,

Haka sukayi satin nan kuwa Ma'u na koyar da ita kuma tana dada gyarata,

"Am a pro, baki ga koh Mama ta kyale ni bah dan tasan nasan aiki nah"

Ta girgixa kai kawai,

Baking soda da ruwa sai, Vinegar (ruwan Khal) ta kwaba har ya zama kaman wani cream,

Kullum saita yishi sanman ta shafa mata a tafin kafa,ta tayata wankewa da dutsen goge kaushi,

tace mata yana sa shi yin smooth kuma ya cire ma mutum kaushi,

"Na kaina kuma fah?" Ta tambaya a hankali
"Lokacin wanke wa beyi bah" Ma'u ta sake rada mata, dan basa san kowa ya san abinda sukayi,

"Wai ke a ina mah kika samu giyan" Ma'u ta zaro mata ido

"Toh jawo min mutane" sai tayi tsit,
Saida ta gyara mata farcen hannu

Please Login or Register in order to submit comment