Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

" Towet Eiffel"ya fada mata da french,

Makaleshi tayi da suka shiga wurin, sannan akayi sama dasu,

"Inna lillahi, kalli kasa"
Da ya zata bazeji dadin yawon bah tunda duk yasan inda za'aje sai gashi yana Nishadantuwa fiye da yadda yayi zato,

"Château de Versailles"
Suka shiga suka ga painting da sculptures iri iri,

"Louvre museum" kuma abubuwan da ne na French fa Egypt,

"Buttes Chaumont park" duk flower din data taba sai daya siya, kuma daya bata har rungumeshi tayi saboda murna,

"The grand magasins" beh san matar shi ta iya shopping bah sai ranar, gashi wuri cike, kuma beh zo da security dinshi bah, dole shi yayi ta aikin daukan abubuwan data siya,

Koda yake shima ya siya mata wasu abubuwan da beh nuna mata bah,

Dayace saidai su shiga taxi su koma gda daboda kayan data jida kaman tayi kuka, har suka je hotel tana chuno baki,

"Dama wurin suka bari karshe" yace toh
Har suka kai dakinsu tana gunguni,

"Akwai gobe love"
Dama kuma dare ya kusa yi, sallah sukayi abinsu sannan suka ci abinci,

"Gobe in Allah ya kaimu abinda nafi sonyi in nazo garin nan shi zamuyi"
Dan tunani tayi sannan ta kalleshi,

"Gobe ci zamuyi kenan" da wani faddaden murmushi yace
"yes baby yes"

"Kalli fah wuraren da ban gani bah" ta rarrafo zuwa inda yake tana nuna mai paper din hannunta,


Kallon wuraren yayi,

"Wata rana sai muje" ta turo baki tana mai kallon dake kashe jiki,

"Wayace zamu kai gobe ballantana wata rana, nidai muje"

Ts kankame mai kafadu, taba dan jijjigashi

"Baki gaji bane bah Love, Allah kafana ya gaji"

Zama tayi tana mike kafafu

"Nagaji manah, ga loafers din can yasa kafata kuubura"

Ya samu abun fakewa dashi

"Kin gani, gobe din mah ai zamuga gari, hade da ba cikin mu hakkin shi, yau fah sau daya muka ci abinci"

Tayi yar karamar dariya

"Waya manta beh kama manah restaurant bah"
Da sauri yace Alfie ne, girgixa kai tayi tana jan kafafunta hade da dan danna su,

"Mu gani" ya dora kafafunta saman cinyarshi yana matsa mata su,

"Kina son haka" tace Eh tana ajiyar zuciya,


"Zanzo in tura mah Ma'u pics din da mukayi, kuma inyi mata gwalo, sannan in nuna mata kayan dana siyo dan ta haukace"

Ita kadai ke magana tana wani murmushin mugunta,

Tana kokarin mikewa ya janyota,

"Bakiga aiki nakeyi bah"
Tace oh, harda cigaba,

Jin dadi da gajiya ga yunwa yasa ta manta da kunya ta zauna daga ita sai leggings dinta da tank top, sannan ta warware gashin kanta dan yasha iska,

"You look amazing" cikin tunani takejin kaman yayi magana, amma batayi yunkurin tambaya meh yace bah,

Zafi taji yana sauka a kafanta, kafin dan karamin kiss ya biyo baya, dan tashi zaune tayi, sai suka hada ido,

Da sauri ta koma ta kwanta tana rufe idanunta, wai ita sarkin kunya,

"Wifey" a hankali tace Na'am,
"Abinda mukazo yi kenan ai"
Tayi shiru bata ce komai bah,

Cigaba sukayi daga inda suka tsaya, ranar tabata kawai yayi yau kuma ya kara hot kisses a sama, be cire mata kaya bah, shima kuma da kayanshi a jikinshi,


Ware idanu tayi data tuno wani abu data karanta, wai mata nayi mah mazajensu, girgixa kai tayi sannan ta dan bude idanu,

'Haka mah ya ishe shi" ta damtse hannayenta

Saida suka kara kwana biyu a garin Paris, da yamma suke fitowa lokacin anyi baking sabbin abubuwa,
Bayan sun gama tasting a shops, sai kuma su siyo wani su koma dashi masaukin su,



V̰ḚN̰ḬC̰Ḛ.


"My All tnk u very much daka bar Venice ya zama karshe"
Yayi dariya marar sauti,
A garin Venice kusan ko ina zagaye yake da ruwa, gada ba iyaka, kuma ta cikin wannan gini sai ka billa zuwa wani,

Ga yan rumfuna da aka kafa a wajen restaurants ana shan coffee da juice,

Tun da rana suka iso, ta matsu su fita amma yace Aa,
Sai dare sannan suka fito, ko ina haske ga signs iri iri,

Gondola suka shiga, wani dan karamin kwale kwale da ake yawo dashi cikin ruwan garin,

Manyan gidaje ne suka sa ruwan tsakiya, hannu tasa cikin ruwan tana wasa dashi,

"Grand Canal kenan, duk meh ji da kanshi kuma yake ji da kudi anan area din yake zama"
Ta jin jina kai dan basai an fada bah tasan wurin na manya ne,
Wani restaurant aka sauke su inda suka ci abinci kafin suka sake shiga wani kwalekwalen ya maida su hotel dinsu,

"Gobe zamu shiga gari da rana" ta dago daga duba pics din da suka dauka a wayanshi,

"Da dare kuma zamu wuce Australia"
Batayi tambayan a fili bah, saidai yasan tana mamakin saurin da sukeyi

"Akwai wani meeting dana kasa tsere mawa, da naso in barki anan" kafin ya karasa mah ta girgixa kai,

"Nima bazan iya tafiya in kyale ki anan ke kadai bah, kuma irin meetings din nan bah tabbas din zamu gama mah a ranan"

Ta jin jina kai, alamun bakomai ta fahimta,

Gadon ya hau ya jawota jikinshi,

"Yau wa za'ayi mah gwalo" yar dariya tayi tana rufe screen din wayan,

Hotunan suka kalla suna hira kadan kadan, sai call ya shigo wayar shi,

Sai da safe yayi mata sannan ya dauki laptop dinshi ya fita, ba ita ta rumtsa bah sai daya zo ya kwanta shima kusan karfe biyu na dare,

Washegari mah bataji dadin yawon bah, dan rabi da kwatan lokaci wayar shi yake ansawa koh yake dubawa,

Har jitayi kaman ta fizgi wayan ta wurgar,
Bata saba da yana kusa da ita bah,kuma hankalin shi na wani wuri,

Sai turo baki takeyi tana tsaki, tafiyarta mah daka ji zaka san na neman magana ne, gogan da takeyi dan shi beh mah lura bah,

Hotunan ranar mah duk basuyi mata kyau bah, dan ta tuna wuraren data je ne kawai yasa bata goge hotunan bah,


Suna komawa hotel dinsu ta fara hada masu kayan su, sai bubbuga abubuwa takeyi,


"Yi a hankali wifey, bana jin abinda ake cewa" kabbara tayi tana kwaso kaya tana jibgewa saman gado,

"Abinda ka fada duk yinin yau kenan da ba kalma biyu koh uku bah"
Da hausa tayi magana, kuma yasan dashi take,

"Cigaba manah, kar suce ka share su" harfa wani murmushi na dole ta hada mai,

Ta juya baya tana cije hakora,
' Kafin aure suyi ta bibbiyar mutum, da anyi kuma su dinga share shi'

Har da dan guntun hawayenta,

Jitayi an rugumeta ta baya,

"Kina kallo dai koh" ya kashe wayar tashi a gabanta,

"Sauran fah" ta fada da shagwaba
Fiddo su yayi ya kashe gabaki daya,

"U have my attention, meh kikeso?"
Ta harde hannuwa a kirji tana dan tunani

"Tabdi! Haka nan kiketa kwakwata baki da abinda zaki ban, koh zan maki, sai anjima"

Da sauri ta tsaida shi ta hanyar makalkale mai hannaye,

"Ni komai mah ina so, in dai kai zakayi min" Ajiyar zuciya yayi sannan ya nufi kayan data fiddo ta watsa a ko ina, wani shopping bag baki meh kwalliya ja ya dauko sannan ya mika mata,

"Wannan fah" ya harde hannuwa a kirji,

"Amma bani na siyo wadan nan abubuwan ba koh" ya daga mata kai,
Da kanshi ya zabo su a grand magasins lokacin tana ta fama da siyayya,

"Honeymoon mukazo wifey, sexy clothes ake sawa, kuma naga ke baki zo da koh daya bah,
Koh kin boyesu ne?" Tayi saurin girgixa kai,

"Ni dake bamu taba kasancewa tare ba kaya bah koh?"
'Sai na ansa' tayi kasa da kanta,

"Wannan ai yafi babu koh, daga shi sai babban aikin,

Amma in bazaki iya bah" ya daga kafadu
"Ba matsala"
Saida ya zauna saman gado sannan ya kalleta, ta wani daure fuska kaman zata balbaleshi da masifa,

"Ni dai bana so kana cewa in banzan iya abubah in barshi,
Kasan babu abinda bazanyi maka bah koh"

Ya dade yana kallonta kafin yayi magana,

"Ke kuma fah, kina so ne?"

"Meh ze hana in nuna maka" tayi murmushin da beh kai ciki bah, shima ya maida mata irin shi,

Shopping bag din ta dauka sannan ta fita daga dakin ta banka bathroom,

Cika baki sauki gareshi, aikatawa shine meh wuyan,
Harda wanka tayi dan ta bata lokaci sannan ta fesa turaren da Hotels din ke ajewa a bandaki,

Wandon ta fara sawa, meh wani shape din ⬜, ga wani shegen tsantsi da sulbi da kayan ke dashi,
Rigar tasa meh siririn hannu ga wani V neck kaman ze nuna har cibiyarta, wandon kawai rigar ta rufe,
Ta tabbata mazaunanta mah ana gani,

Da tafin hannunta ta rufe fuskarta,
'Kuma wai ace wasu da kansu suke wannan shigar ba tareda an sasu bah, ni dai banga ranar bah'


Data fito ta dade tsaye da kanta duke, ta zata duk ganinta haka ne yasa ya kasa magana, saida ta kalleshi ta kasan idanunta taga ya tusa waya gaba,

Da zafin nama ta isa gareshi ta fizge wayan, ya dan tsorata amma yana ganin itace i kokarin janyota,

"Nayi seizing" bata rufe baki bah ya biyota


Manta dalilin dayasa yake binta yayi, halittun jikinta kawai yake bi yana son tabawa,

Da ya samu ya cafkota, ya manna da bango beh yi wani jinkiri bah ya maida jikinta paper hannun shi kuma biro,

Abinda yake shirin hada ido dashi ne yasa ya sallama mah lips dinta da sukayi ja sannan suka kumbura,

A hankali ya zare hannayen rigar daga kafadunta sannan ya jata zuwa kugunta,

Idanunta rufe tana ta sauke numfashi, tana so ta bude ido ta kalli kwayar idanunshi taga irin kallon da yake mah surarta, saidai ta kasa koh motsa eyelashes dinta,

Da sauri ta bude idanunta, tana jin kafafunta basa manne da kasa,
Saman gado ya azata, tana bude idanu taga shima ya cire rabin kayan shi, kuma yana kokarin rabata da nata gabaki daya,


Allah kadai yasan abinda ya hana shi yin abinda yayi niyya,

Taji wani yanayi da bata taba jinshi a duk sauran lokutan da suke tare bah, shima kuma halin daya shiga ba irin wanda zata iya misaltawa bane bah.




⚜B.W.A🖊
⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊




💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐
BOYAYYEN KUDIRI.
💐💐💐
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐


Story, writing by NOBLE JUDGE.
editing by KHALEESI.


Duk mai rai mamaci ne, kowa jiran nashi ranar yakeyi dan babu wanda keda tabbacin ze kai gobe,

Allah ya kan yan uwa musulmai da suka riga mu gdan gsky, Allah ya kai haske kabarin su yasa Aljanna ce makomar su,

Yasa mu cika da kalma shahadda, da kuma kyau da imani, in lokacin mu yayi,

AMIN.





5⃣8⃣.




A༘U༘S༘TRA༘L༘I༘A༘.



Mika tayi ta hada da addu'ar tashi daga bacci, a daren jiya suka shirya suka kama hanyan gdan su dake Australia.


"Sorry na tashe ki wifey but mun iso" murza idanunta ta tsaya yi,

Bayan ta gama yayi mata jagora suka fita daga jirgin zuwa ga motocin dake jiran isowar su,


Abu daya ya dauki idanunta fiyeda komai data gani a Australia,
Katon hotonshi da ta gani a billboard, da farko data gani ta zata dan bata dade da tashi daga bacci bane bah, amma na biyu baro baro taga hoton shi yana bada wani katon cheque zuwa ga mutane dayawa,

Juyawa tayi ta kalli mutumin dake gefenta zaune sannan ta cigaba da kallo har
yasa ta kara ganin wani hoton nashi,

Da sauri ta juya ta sake kallon na asalin kafin ta koma hoto,

Duk abinnan da takeyi yana kallonta ta gefen ido, magana ne kawai beyi bah ya cigaba da abinda ya sha mai kai,


"Wai kai ne da gaske" yaso ya boye dariyar shi amma saida bakinshi ya nuna ,


Wani katon gda suka shiga meh farin penti, ga wasu kattin windows da kesa a hango abubuwa da akeyi a cikin gdan,

"Barka da yini dadi"
Ya tashi zaune da kyar yana sannu da zuwa diyata,

Fara'ar ta daukewa tayi data lura sosai da yadda yake,

Juyawa tayi ta kalli Mijin nata,ita saida ta karasa bakin gado sannan ta lura, amma shi tun bakin kofa yayi full stop,ya zuba ma mutumin dake saman gado ido,

"Bakacemin baka da lfy bah"
Tari yaci karfin dariyar daya kakalo,

"Naji sauki "
"A hakan" ya katse mahaifin nashi,

Tasan tsoro da fargaban da yake ciki ya ke kokarin boyewa ta hanyar nuna bacin rai,

"Naji sauki sosai Ehsaas" Ehsaas ya mike yana fiddo wayar shi

"Mom zan kira" baban shi ya fara magana da babban murya,

"Ka kyaleta am okay, Ehsaas!"
Ya cigaba da scrolling up and down,

"Shit! Ba number dinta a nan wayan" dukar da kai tayi dan ta tuno dayar wayarshi data saki lokacin da suka shiga wani yanayi,


"Daughter jeki huta abinki kinji koh" ta mike tsaye sukuku ta fito daga dakin,

Tsaye tayi dan bata san inda ta nufa bah, yawo ta dan farayi har ta ganta a kitchen,

After dress dinta ta cire sannan ta gaishe da cook din dake dafa abinci,

Dakyar ta samu ta shawo kan matar ta harta ta dafa mah Dad abincin da zeyi daidai da marar lfy,
Tayi meh yaji, meh gina jiki da kuma wanda zesa appetite dinshi ya dawo,


Da sallama ta shigo cikin dakin, duk suna saman gado ga laptop a gaban su,

"Wifey meh kikeyi?"
Bata bada ansa bah kawai ta nemi wuri ta aje tray din data shigo dashi,

"Daughter!" Shima ya bude, kanshin abincin ya bide dakin,

"Saida nayi kokarin hanata, amma taki" shugaban masu dafa abincin gdan ta fada itama tana ajeyi tray meh jere da plates hade da juice kala kala,

"Bakomai" yace da meh dafa abincin,

"Ni bazan ci bah" bata mah saurareshi bah ta cigaba da zuba mai,

"Gwara ka ci abinci Ehsaas, baka san sanda zaka samu time din cin abinci bah kuma"
Ta dungura mai sannan ta cigaba da zuba sauran abubuwan data dafa,

"Na katse maka hutun ka na saka wannan aikin,
Na yarda da kaine shi yasa, akwai mutane dayawa da zasu iya yimin wannan aikin"
Yace bakomai tun kafin baban nashi ya karasa,

"Naji dadi daka zabeni in shige gaba mah wannan aikin dake da mahimmanci, kuma in shaa Allah zan saman manah mafita"

Babanshi ya jin jina kai,

"Allah yasa a samu mafita Ehsaas, mutanen da muka kulla business dinnan dasu, bazasu rungumi kaddara bah in deal dinnan ya sha ruwa,

Kuma zasuyi pressuring dinka tunda sunga kai din yaro ne"
Dafa baban nashi yayi,

"Karka damu Dad, nasan yadda zanyi mu'amala da irin mutanen nan,

Kuma naga irin kudin da kuka zuba mah wannan harkar Dad, muma zamuji jiki kafin mu farfado"

Babban abinda ke gaban babanshi shine ya kare dukiyoyin sauran jama'a, koda nasu ze salwanta in d process, shi kuma in shaa Allah baze bar hakan ya faru bah.



Tana kwance a Falo da laptop a gabanta, taji gyaran murya,

Da sauri ta duka kasa tana gaishe da Dad,

"Wani abu zanyi maka" ya girgixa kai yana nuna mata kujera bayan ya zauna,

"Wannan gatan da kuke nuna min yakesa naji kaman ban warke bah"
Tasan kam yaji sauki sosai tunda har ya maida kibar shi kuma yana fita, bakaman da bah da kullum yake daki,

"Badai sai yau kike lalubo mijin naki a internet bah" kunya ya kamata,

Kadaici ne ya dameta shine ta fara browsing abubuwa, daga nan tayi searching sunan shi kawai dan taga abinda ze faru,

"Beh san duk wannan tallata shi din da akeyi, amma mamanshi nasan kowa yasan irin achievements din da yayi a karan cin shekarun shi,

Nima kuma ina Alfahari da shi"
Ta jin jina kai dan tasan wannan,

"He's very smart, ya bani mamaki sosai daya cinmma farkon aikin dana sashi bayan ya gama makaranta,
Abune dana rigada na aje a gefe dan naga ze bata time kuma ba lallai ne kwalliya ta biya kudin sabulu bah"

Shima ya taba fadamata, yana wasa amma banda wurin aiki,
Duk da a Nigeria beh wani maida hankali akan aikin da yakeyi bah, yaje late ya riga kowa tashi,

Tabbas wannan serious aiki ne, tun tafiyar shi take neman layin shi bata samu, in ta tura text mah sai dai ya turo mata dan guntun 'Tnx'



"Meh ze hana ki je wasu wuraren, dan nasan ze dade kafin ya dawo" tace toh Zata fadamai,


Tana komawa daki ta fara laluban wayar shi, as expected beh dauki call din bah sai wani guntun message daya turo mata,

'Can't talk now, what's up?'

Sai kallon text din takeyi kaman tana jiran abinda ya turo ya canza zuwa wani abinda zata so karantawa,

Tura mai text din dalilin kiran tayi sannan ta jira reply,
'Sure tnx' ne abinda ta samu,

Kifa wayar tayi a saman gado, ringing ne ya fiddota daga tunanin da takeyi,

"Hello" zaune ta tashi tana jin muryar dake magana,

Tana gaishe da ita tace ta aje abinta,ba dalilin kiranta kenan bah,

"Meh ke faruwa a gdan nan" tace Na'am

"Ya akayi Ehsaas yazo gda yin wasu ayyuka,
Baban shi fah"
Ji tayi abu ya tokare mata makoshi,

"Yana Nigeria?"
"Abinda nake tambayan ki kenan, .ina baban shi yake?"

Dad yace baya san a fada mata beji dadi bah, amma a lokacin bata wani damu bah, hankalinta duk ya karkata zuwa ga inda taji mijinta ya je,

"Baya da lfy ne da muka zo, sai ya cigaba da yin aikin"
Kashe wayarta tayi tana gama fadamata abinda take son ji,

Kila kin biyoshi tayi su dawo nan, shi yasa yace kar a fadamata, taji Hajia mah na maganan kin bin mijinta da tayi,

Gashi ita ta biyo mijin amma yayi nisa da ita,

Tunanin inda zataje tayi sai ta tuno Alfie ne ya shirya masu wuraren da zasu je,

Email ta turamai tana bashi umarnin turo mata holiday plan dinsu, kuma ya sake shirya mata komai ita kadai,



Bayan kwana biyu sai gashi yazo,

"Saidai kibi commercial flight, Oga na yana amfani da jirgin kusan kullum"
Tace ba matsala tana duba abubuwan data ga zata iya,

"Ke kadai zaki je" ta daga kai ta kalleshi kafin tace Eh,

"Baze bari ki tafi wani gari ke kadai bah, kin tabbata ya sani?"
Kallon datayi mai yasa yayi gyaran murya yana kauda kanshi daga kallonta,

"Bari in kirashi in tambaye shi"
Zatayi magana saiga Dad ya shigo,

"Ta wurin zanbi, sai in ajeki a Bangkok in kin dawo daga umrah din koh"
Da Fara'a tace ta gode, sannan ta koma daki tana kyarman fadama yan gda inda zataje,

Sun tayata farin ciki ba kaman ranar da zasu tafi, taga love daga yan uwa da abokan arxiki, data isa kuma ta tsaya tsakani da Allah tayi ibada hade da rokon Allah, daga nan kuma ta fauwala wa Allah komai,


Dad beh samu daman zuwa a ranar da suka shirya bah, saidai yace taje taga gari ta danyi shopping kafin ya samu zuwa,


DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment