Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bata damu bah dan ta kara samun lokaci ne na yin ibada,

Daga masallaci kuma saita dan shiga gari, in taga abinda ya birgeta kuma ta siya koh taci,

Wani shop data sha wucewa ta shiga, shop din cike yake da mata dan kayansu ake sayarwa,

Anan tayi mah yan gda tsaraba, kuma ta siye nighties, abin har bata dariya yakeyi,
Saidai taga tasirin sa sexy kaya, under wears da kuma kayan bacci,

Dataga irin kudin data kashe saida ta cije harshe, kaman ta maida abubuwan data dauka kuma kunya ya hanata tunda har ansa a leda anyi komai,

Tana fita ta sanar dashi banar da tayi, amma har taje gda bah reply, ranar har marmarin dan guntun 'tnx' din tayi,

Wasa wasa saida taje garuruwa dayawa ita da Dad, shi yana business dinshi, ita kuma sai yasa a kaita tayi yawon bude ido,



Ranar da suka koma Australia sai gata harda kuka sannan tabi hotunan shi na cikin wayarta tana kallo, sai murmushi takeyi ita kadai tana shafa hotunan,

Closet ta shiga tana gyara mai suits dinshi, wasu handkerchief ta gani masu Ehsaas a jiki guda biyu, dasu ta goge hawayenta tana maidasu inda ta dauko,

Ringing din wayarta ta jiyo daga daki, bata nufi daki bah sai da kira na biyu ya katse,

Tana dubawa taga missed calls dinshi ne, kaman ta rusa ihu haka taji,

'I love you' ta tura mai bayan tayi ta kira ba'a dauka bah,

Bata sake barin dakin nan bah, har saida Dad ya nemeta, fada yayi mata akan damuwan data sa kanta ciki,

"Am sorry Dad" yayi Ajiyar zuciya dayaga yasa diyar mutane kuka,

"Ya akayi neh, kina ta hutun ki lami lfy,lokaci daya kuma kun canza, why?"
Cikin kuka tace tana kewar gda ne kawai,

Dan jin jina kai yayi dan yasan komin dadin garuruwan data je, gda ne inda zatafi so ta kasance,

"Okay, ina zuwa"
Wayar shi ya fiddo yana latse latse,

dayake shi shine yana kira aka dauki call din,
"Good Afternoon Sir"
Taji kaman tasan muryar dake magana,

"Danyah" bugun zuciyarta ya toshe mata kunne bata jin duk abinda suke fada,

Saidai gani tayi yana miko mata waya


Hawaye ya cika mata idanu da kyarman hannu ta karbi wayan,

"Husna " mantawa tayi da Dad na wurin ta fashe da kuka,

"Love ya akayi" ta rungume kafafunta tana sabon kuka,

Shi kadai ke surutu, ya rude yana san sanin dalilin kukan nata,

"Ni kawai ka dawo"
Ta katse mai magiyan da yakeyi, tana gama fadan abinda takeso taba Dad wayan shi,

"Na gama komai Dad, kaman yadda nayi alkawari, Allah ya bani iko na nemo manah mafita,
Komai is settled"
Ya fada da yaji muryan Dad,

"Banyi tantama bah Ehsaas,

Yaushe zaku dawo, banji dadi bah da ka manta da iyalin ka koh kira bakayi"

Kaman yana gaban baban nashi, kasa ya kalla yana jan kafafun shi,

"Saida na bar umarni in dai ta kirani koh meh nakeyi su bani,
Basu taba fadamin ta neme ni bah, duk da hakan ya bani mamaki, naxata saboda aiki neh yasa bata kira bah"

Dad ya dan yi mai fada na jiran saita kira,

"Yaushe zaku dawo kenan"
Dan sosa keya yayi,

"Ka sansu, hanyar nuna jun dadin su na nasarar da aka samu shine party,
Kuma bazan iya tafiya bah, bayan ni nake wakiltan family dinmu,

Kuma manyan bakin ni na gayyace su,
So i can't leave just yet"

"Barshi kawai Ehsaas zan kula da komai daga nan, ka tabbata kun taho kafin gobe"

Ya kashe wayan, dakin dan nashi ya nufa, har ya dora hannu ze kwan kwasa kuma yaji sautin kuka na fitowa a hankali,

Fasawa yayi ya juya, dan yasan sai tayi kukan kafin zata ji saukin abinda ke damunta.




Gaban window taje tana kallon watan daya fito, ko ina yayi haske kaman ba dare bah,

Haske ne ya dalle mata idanu har saida tasa hannu tana karewa,
Bayan ya lafa ta samu ganin wadanda suka fito daga cikin motocin da suka shigo gdan,
Shine sanye da wani black coat meh dan tsawo har zuwa guiwwa,

Da murmushi ya fito, har tana tunanin dan ze ganta neh, itama sai tayi murmushi,
Da hanzari ta bar dakin dan ta tarbeshi a bakin kofa,
Saidai tana juya baya dalilin murmushin nashi ta fito daga mota,

Maganar su da dariya taji dan haka ta kara gudu, tana ganin su kuma fara'arta ya bace,
Kaman yana jira ta karaso daidai lokacin ya daga kai, suna hada ido ta juya tayi daki,


"Danyah ya kika ga aiki da dana"
Ya hanata bin bayan Ehsaas ta hanyar janta da surutu,

"Very inspiring,mutum ze karu sosai yasan sirrikan kasuwanci,
Nasan bani ce farkon fadan haka bah"

Ya daga mata kai, sai ya tsinci kanshi da kwatanta ta da Asma'u,

Bawai hankali koh natsuwa Asma'u ta fita bah, saidai ya yaba da tarbiyar yarinyar, ta shafa mah danshi halin kirki da hakurin ta,
Dama can salihi ne shi, amma yanxu yafi kama da babban mutum, in ka ganshi bazaka ce yaro ne bah,

"Mr Mas'ud zan wuce" ya daga kai ya kalleta,
Duk ta wani fiddo idanu waje kaman taga fatalwa,
Silalewa tayi ta tafi upstairs da yana tunani, ita tasan abinda ta gano mah kanta,

"Mun gode sosai Danyah, ki gaishe da babanki"
Tacr toh tana rataya jakarta.


"Matata" yasa yatsun shi biyu yana goge mata hawayen dake bin kuncinta,

"Hauka ne kawai banyi bah Husna, saboda kewar ki" wasu sabbin hawayen suka tsiyayo,.
"Na dawo ai, kukan kuma na meye"
Rungume shi tayi kam, har saida ya yaja numfashi sosai,

"Karka kara bari nah ni kadai Dan Allah"
Dan rabata da jikin shi yayi yana bin fuskarta da kallo dan ya gano yanayin da take ciki

Da karfi ya jata jikin shi, habarshi ya dora sama kanta,

"Meh sanki ke san maida ni neh Husna" ya fada da Ajiyar zuciya,

"Duk inda naje in dai babu ke a wurin bana jin dadi, in na jiki a jikina kaman na sha ruwan sanyi neh bayan doguwar tafiya cikin sahara"

Yaji jikinta yana dan kyarma alamun kuka takeyi,

Duban fuskarta yayi, sannan yasa bakinshi yana share mata hawayenta, sumbatar saman idanunta yayi daya gama,

"In kikayi min asarar tsadadden hawayen ki kuma tafiya zanyi" ta turo baki hade da bata fuska kaman zatayi kukan,

"Nayi kewar kissable lips dinnan" cije lips dinta na kasa tayi hade da dan murmushi,

Baxata iya fadami tayi kewar hakan bah, amma alamun da yake gani yasan tana so, matso da ita yayi sannan ya dago fuskarta, yasan tana tsumayar abinda zeyi mata dan har fitar numfashinta ya linku,

Sai ya tsaya ja mata rai, sai yayi kaman ze hada bakin su, har rufe idanu tayi amma ya tsaya musayar numfashi da ita,

Saida ta bude ido yaga yadda suka canza kafin ya fidda su daga kangin su,

Dangana su yayi da gado inda ya samu damar sarrafata san ranshi, dan ranar bata nuna tsoro bah koh tayi yunkurin katse shi,

Tasa a ranta ranar neh komai ze faru,
Da suka kwanta bayan guguwar tasu ta lafa, sai take tunanin dalilin shi na kin saduwa da ita,

"Cara Mia" murmushi tayi dan ya dade rabon daya kirata da wannan sunan,

"Uhmmm"
Dora mata hannuwa yayi a jiki,

"Muje muyi wanka kafin bacci yayi gaba dani"

Da hanzari ta tashi zaune saboda baccin da taji cikin muryar shi,

"Tashi muje toh" dan karkata baki yayi yana dago kai

"Jeki gani nan zuwa" toh tace tana laluben abinda zata rufe tsiraicinta,


Ta saba bata kulle kofa da key in ta shiga wanka,
Tana tsakiya da wankanta taji wani hannun da ba nata bah yana bin jikinta,

A tsorace ta juya bayan ta damke hannu,
Dayan hannun shi yasa yana wasa da kumfan dake jikinta,

"Tsoro na kike ji" ta girgixa kai duk da tasan ba tambaya yayi bah,
"Koh kunyata kike ji" ya sata karkashin shower dan kumfan jikinta ya wanke,

Bata bata second koh guda daya baya wajen kokowar kare jikinta, sakin hannayenta yayi yana matsawa baya,

Saurin kallon sama tayi bayan ta kare jikinta da hannu, dan girman ta beh kai na abinda yake nuna mata bah,

"Da sauran mu dai kaman yadda nayi tunani"

Sai kuma ta dukar da kai kasa,

"Ka taba cemin kunyata na birgeka, yana daya daga cikin abinda yasa na shiga ranka,

Toh meh yasa zakayi mamaki dan naji kunyar tsayawa a gaban ka bayan wani beh taba ganin tsiraici nah bah"

Dan baya yayi yana kallonta ido cikin ido,

"Amma ni mijinki neh koh, beh kamata ki bari kunya ta hanamu sakewa bah koh"

Bakin shi take kallo tana jin kalaman na fitowa daga bakin shi, saidai wata murya na daban take ji tana fada mata mahimmanci kunya ga ya mace, da kuma inda ya kamata a jeta gefe,

"Cire rigar kunya akeyi in kina tare da mijinki, ki bari sai kin sa kayan ki kafin ki dauko rigar kunya ki daura"

Gani tayi har yanxu ita budurwa ce, kaman da matsala ta nuna fetsaran cinta tun yanxu, gwara ta bari in sun tashi daga sabon shiga tukunna,

"Kana da gsky mijina, ni mallakinka ce, beh kamata ina wasa da hakkokin ka dake kaina bah,
Kabar jira saida amincewata pls"
Tace pls din da wata yar karamar murya,


Mannata yayi da jinkin tiles, dumin jikin shi beh bari taji sanyin da tiles din ke dashi bah,
Wani duniyan na daban ya mirginata, ya sanya ta cikin halin da bata san ana shiga bah, ya mantar da ita aikin kwakwalwarta, yasa ta narke mai a jikinshi kaman ba kรขshi a jikinta, duk inda ya taba a jikinta sai taji kaman lokacin wurin ya farka daga bacci, da tafiya tayi tafiya bata san sadda ta fara kiran sunan shi akai akai bah, shi kuma hakan ya kara rudashi ya kusan sashi aikin da beh shirya bah,

Fita yayi daga ban dakin ya barta ta karasa wankanta ta kuma yi wankan tsarki,


"Yaushe hakan ya faru" yana zaune saman gado yana kallon pictures din wayarta,

"Mu gani" ta gyara daurin towel dinta kafin ta isa inda yake,

"Lokacin da mukaje Bangkok ne da Dad,kalli wannan" ta bude mai wanda sukayi data je umarah ita da Dad,
"Yayi kyau" ta dago kai taga ita yake kallo ba fara'a a fuskar shi,

"Wa yace ki fita har kikaje garuruwa dayawa haka, kin san bana son kina zuwa wani wuri ba tare dani bah koh"
Fuskarta ta nuna mamaki, girarta ta hade da kallon shi wani iri,


"Saida na tambayeka fah, kuma kace in je" ya harde hannu a kirji a matsayin alamun tambaya,

"Na kira baka dauka bah, sai na tura maka text kace ba matsala in tafi, kuma nasan bazaka so inje ni kadai bah shi yasa Dad ya kaini da kanshi"

Mikewa yayi ya shiga bathroom beh bata ansa bah,

Itama saita tashi ta zabi daya daga cikin kayab baccin data siyo, koda ya fito daga wanka sai ya sa kaya kawai ya fita,
Mikewa tayi ta sa hijab dogo kafin tabi bayan shi, waya ta ji yana yi,

"Gsky banji dadi bah,da na shirya barin komai ya wuce, amma raina ya baci mah wannan Danyah"

Hadiyan miyau tayi
"Yes ni na baki umarnin amsa kira nah da kuma yin abubuwa a matsayin ni, saidai ban bada izinin ki sa hannu a abinda ya shafi ni da matata bah"

Dan shiru yayi na dan lokaci yana sauraren abinda ake cewa,

"Aikin gama ya rigada ya gama Danyah, sorry baze canza komai bah"

Wani dadi taji data ga yadda suka rabu abu bah dadi tsakanin su,


Koda ya juyo ya ganta tsaye bata wani kama kanta bah, sai shi daya kasa hada ido da ita,

"Tare da Babanta Dad ke yin aiki kafin ya fara rashin lfy,
Da aikin ya dawo hannun na sai babanta ya turota ta wakilce shi shima,
Farkon aikinta kenan sai nace ta fara da matsayin P.A dinah dan tasan abinda ke faruwa,

Bansan kin kira kuma kin turamin texts dayawa bah haka My wife"

Dan murmushi tayi mai kafin ta taka zuwa inda yake,

"Bakayi tunanin na damu da kai bah har zan nemeh ka"
Da beh bata ansa bah sai taji wani iri a ranta, juya mai baya tayi zata tafi,


"Ba haka bane bah Amore Mio, kunya ce nake ji, ban san yadda zanyi in kalleki bah bayan ni ban nemeki bah tunda na tafi"

Ya riko hannunta yana rungumeta ta baya,

"Kinyi hakuri" Ajiyar zuciya tayi tana dora hannu saman nashi dake kugunta.

Zaune take saman wasu kujeru da aka dan zaman masu jiran suga shugaban makaranta,

A takure take dan koh kanta bata dagawa sama, balle ta kalli masu wucewa,

Ana budo kofar office din ta daga kai,
Ba'a sakota cikin maganar tasu bah, amma akanta ake maganar,
Kashe kunne tayi tana saurare,
"Ya kikaga makarantar tamu" ta mike tsaye amma ta kasa cewa komai,
"Bari mu zagaya dake kiga makarantar nasan da kin ganta zaki ce nan kikeso, karka manta ka nuna mata Trophy Room dinmu inda aka muke aje lambar yabon da ake bamu"

Hannu suka mika ma juna kafin shugaban makarantar ya juya ya koma office dinshi,

"Ya kika gani love, school din yayi maki"
Sai tayi rau rau da idanu kaman zatayi kuka,

"Ya akayi?" Ta girgixa kai tana mai kallon kasa,

Ajiyar zuciya yayi kafin ya koma office din shugaban school din, beh fito ya isketa bah sai ya nufi inda sukayi parking mota,


Bece komai bah haka itama har suka isa gda, dataga shariyar tayi yawa sai ta nemi sanin dalili,


"Cuddly Brat dinah" ta tsaya ta gefenshi ,

Uhmmm yace yana aikin gaban shi,

"Na bata maka rai neh" ta karasa shiga jikin shi tana dan narke mai,

"Akwai abinda ban ganeh bah har yanxu"
Ya matsa daga kusa da ita,
Itama baya tayi da taga abinda takeyi beh daukan hankalin shi,

"A Nigeria kikeson kiyi karatu neh?" Ya girgixa kai
"Karki mah ansa wannan, kina da ra'ayin yin karatun neh mah?"
Tsaki yayi yana niyyan tafiya,

Ko kadan bataji dadin tsakin bah, kuma taji kaman ta kyaleshi ya tafi, saidai tasan asararta ce in ya tafi da fushi,

Sauri tayi ta sha gabanshi, fuskarta dauke da yanayin tausayi,

"Am ungrateful na sani, daga dawowa jiya koh hutawa bakayi bah, kuma cigaba da neman min makaranta,

Maimakon in baka hadin kai ina kara maka matsala, am sorry"

Ya harde hannu a kirji yana mata kallo mai nuni da ta cigaba,

Matsawa tayi gabanshi tana warware hannayen daya harde a kirji tana dora su saman kugunta,

"Am not happy My all, ya kamata ace ka gano abinda ke sani inji bansan inje makaranta"
Tanata wasa da yatsan ta saman kirjinshi kaman tana rubutu,

"Ni ban gane bah" ya fada rai hade,

Dora kai tayi saman kirjin shi,

"Tsoro nakeji in na fara makaranta anan kai kuma ka dinga yin aiki a wasu wuraren ka barni ni kadai fah, Allah ni ban san haka"
Ta karasa maganar da yar shagwaba kaman zatayi kuka

"Bana so in sake maimaita irin watan danayi ba tare da kai a kusa dani bah Mijina, na saba da kai wani irin wawan sabo Cuddly Brat, in na yini ban ji dumin jikin ka bah Allah sai inji kaman bana da lfy"
Da ta daga kai sai yaga idanunta sun cika da kwalla,

Taso ta furta kalamai neh kawai da zasu sa ya daina fushi da ita, batayi tunanin asalin abinda takeji a ranta shi ze fito bah,


"Wifey" ya dan lashe lips dinshi,
Bata san abinda yasata kuka bah, kodan da gaske tayi matukar kewan shi neh shi yasa,

Shigewa jikinshi tayi tana zubda hawayen dake jika mai riga,

"Wifey ki bari manah, wai meye haka" baki bude, mamaki dauke da fuskar shi,

Shi da yake ganin kaman har yanxu beh gama sace zuciyarta bah, sai gashi ta nuna mai ya rigada ya mallaki zuciyarta,


Dago da fuskarta yayi yana neman kwayar idanunta,

"Kullum kara bani mamaki kikeyi wifey,
u never seize to surprise me"

Sakala yatsun shi yayi cikin nata, saida ta kalli hannayen su kafin ta juyo ga fuskar shi,

"Dan Allah kayi hakuri in abinda nayi dazu a makaranta ya nuna kaman ban dauki effort dinka na sani a makaranta da mahimmanci bah,

Wallahi ba niyya ta kenan bah, rasa hanyar dazan sanar da kai nayi gashi bana so inyi disappointing dinka"

Ta karasa da yar sheshekar kuka, ga wasu siraran hawaye dake bin kuncinta,

"Kina so ki kasance kullum tare dani, a in da nake" ta daga kai tana jan hanci,

"Tsakani da Allah abinda kikeso kenan" ta bashi ansa ta hanyar makalkaleshi,

"Nima abinda nakeso kenan wifey, ta ko wace irin hanya kika bani kanki bazanyi korafi bah"

Hawaye suka cigaba da bin kuncinta,
Abu daya ke damunta yadda ta koma meh fadin rabin gaskiya dayan barin kuma karya, kara shigewa jikin shi tayi tana kuka,

"Duk saboda kai nake yin abubuwan nan Ehsaas, Allah kada ka kawo ranar da kalamai na zasu daina tasiri a zuciyar mijinah,
Allah kada ka kawo ranar da zeyi min kallon makaryaciya'

Kaman an bude famfo haka ta cigaba da hawaye, shi kuma sai bata baki yakeyi na In Shaa Allah ze neman masu tsayayyen wurin zama, in da baza su dinga nisa da juna bah.







โšœB.W.A๐Ÿ–Š
โšœBRILLIANT WRITERS ASSO๐Ÿ–Š





๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
BOYAYYEN KUDIRI.
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’

Story, writing by โ„•แชโ„ฌโ„’โ„ฐย โ„แ‚ฎโ……โ„Šโ„ฐ,
Editing by โ„ชโ„แ—…โ„’โ„ฐโ„ฐีโ…ˆ.






5โƒฃ9โƒฃ.


Tun ranar da sukayi episode dinsu na fadama juna yadda suke kewar juna in basa tare, komai ya canza, da komai good ne tsakanin su, yanxu sunyi escalating to excellent,

Babu inda suke zuwa kullum suna cikin gda makale da juna,
Kowa na gdan saida ya yaba da irin kaunar da sukeyi mah juna,
Dad mah in suna wuri baya zuwa koda kuwa abu meh mahimmanci koh magana meh mahimmanci zeyi da Dan nashi,

Yanayin yadda sukeyi mah juna kallon love da kasaitattun smiles in suna tare na narkan mai da zuciya, in su kadai ne wurin cin abinci sun dinga tarairayar juna kenan, suna ciyar da juna, sunayi suna satar kisses daga lips din juna,

Tuno mai sukeyi da irin soyayyar da sukayi da matar shi kafin ta tsunduma cikin harkar kasuwanci,
yana fada a ji a gdan shi saidai abinda matar shi tayi niyya shi takeyi, kaman kin biyo shi da tayi ta zauna a gda tana planning fansa akan wadanda suka yi mata ba daidai bah,

Ya matsu ya je inda take, kuma ya gaji da binta at d same time,

"Dadin meh kake ji kai kadai?"
Da fara'a dan nashi ya juyo gareshi,

"Dad ban san kana nan bah" ya karasa saman kujerar yana gaishe da baban shi,

"Yanxu Haider ke turo min hoton little Angel dinshi, sunanta Malaika" ya nuna mah baban shi hoton yarinyar,

Dad yace Masha Allah yana mata addu'a, yar hira suka taba da Dad kafin yayi mai sai da safe ya nufi dakin su,

"Wow wannan cute baby din fah"
Ya rungumeta ta baya yana dora kanshi a kafadarta,

"Ya sunanta" ya fadi sunan yana wasa da karan hancin shi a wuyanta,



Please Login or Register in order to submit comment