Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muke dashi yanxu saboda Allah ne yaji kanmu, kuma babanka yayi maraba damu,

Da Allah kadai yasan halin da zamu shiga,

Karka so kaga yadda naki jinin talaka Ehsaas, zakka da sadaqa badai kudina bah,

In naga mabukaci gefe nake kalla,

Sai zuwan Asma'u sannan,

Meh ma tacemin ranar daya tadamin hankali,

Babu fakiri sai wanda yaje lahira a kwashe ladan shi ana raba ma wasu,

Toh ni dana yanke wannan sashin meh dimbin lada fah,
Naji wani abu a zuciyata"

Ta ruko hannun shi duka biyu

"Shi yasa Ehsaas karkayi wasa da Asma'u, bayan duk abubuwan danayi mata bata bini da sharri bah,
Ita ke kula dani, kaman jinin ta, abin har mamaki yake bani,
Nake ganin kaman da biyu takeyi,

But No, haka take, abin a jinita yake,

Pls ka kula da ita"

Yace in shaa Allah,

Ajiyar zuciya hajia tayi

"Bakaramin dadi naji dana fada maka komai bah, i feel relieved"

Yace nima haka, naji dadi da kika fadamin komai,


"Ka tsane shi?" Ya tambayi wa

"Amyr" dukar da kai yayi

"Ni mah ban tsaneshi bah, ina nan lokacin da aka haifeshi, idanun shi irin na babanshi,

Ranar dana ganinshi anan tuno min da abubuwa yayi, shi yasa na daburce,

Amma ban tsaneshi bah, har babanshi mah,

Saidai ina ji dama zan iya ganin dana,

Muna barin gdan naji ance Yarima ya gamu da accident"
Daga mata kai yayi

"Da Kujerar guragu yake amfani koh" ya girgixa mata kai

"Yana da kafar roba, ranar daurin aure naji yana mah Dad complain, cewa ya kagu a gama koh ze cire, dan beh saba dashi bah"

Murmushi tayi amma hawaye ke tsiyayowa

"Am sorry Granny ma" ta girgixa mai kai,

Kwanciya tayi shi kuma ya fito daga dakin,
Card din Amyr ya fiddo sannan ya kirashi,

"Zanzo anjima toh" sukayi sallama sannan ya nufi dakin Asma'u

"Ina bukatar comfort Husna, pls let me hug you"
Tashi tsaye tayi numfashinta na neman daukewa,

Yana ganin haka ya bar dakin,
Sannan ya nufi gdan Amyr din,

"Nace Anjima!" Ya fada da dan karfi

"I have a big problem, banda damar bari sai anjima"
Barin shi yayi ya shiga,

Daka ga gdan kasan na namiji ne kawai,

Takalmi, kaya saman kujera, kwalin takeaway, kwala bai

"Ban cika zama anan bah, kuma ina da meh zuwa kowani sati, ta gyara min"

Idanu ya bude daya ga ya jera bindigogi da wukake kaman zarto, ga abu kaman bombs, da laptops hade da IPads, ga wasu kana nan nau'rori

"Yana yin aiki ne"
Nesa da table din ya zauna

"IPad dinka ne matsalan, koh Mamanka ne Koh wani abu"

"Wani abun dai?" Amyr ya kishin gida

"Naga kaman u r smart, saboda haka kasan abinda ya kawoni"

Dariya Amyr yayi sannan ya mike

"Ba kama bane bah Nephew, am smart"
Ya kawo mai Ruwa da drink

"Banda cups" ya fada yana ajewa

"Akan abinda ke hanaka baccine kenan, hmmmm"
Ya girgixa kai

"Zaka iya taimakawa koh in tafi"
Ajiyar zuciya yai

" na taba jin cases din sau daya koh sau biyu,
Usually wadan da akayi mah fyade, koh wadan da suke ganin bazasu taba iya cinma wani abu bah,
Koh wadan da na kusa dasu yayi masu fyade, kaman wa koh kawu koh kani haka,

Meye na matarka"

Tsohon mijinta yace

"Okay, well anayin therapy, amma zaku dauki lokaci"
Banda time ya katse shi

"Toh Yarda fah, akwai shi tsakanin ka da Matarka,
In akwai yarda toh komai yazo da sauki,

Next dauki pen da paper in zayyano maka"




⚜B.W.AπŸ–Š

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOπŸ–Š



πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Story& Writing by
NOBLE JUDGE,
Editing, KHALEESI.

Dedicated to Maman Sadeeq, Allah ya baki lafia yasa ayi Operation a sa'a,
Da sauran Yan uwa musulmai marasa lfy,
Allah ya kara sauki da karfin jiki,
Amin.
❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀



4⃣9⃣.


"Okay ka bi komai da ki da ki koh, yanxu sai haduwa da ita"
Ya fesa mouth spray sannan yayi wanka da turare,

Girar shi dake cike ya kwantar, sannan yayi styling gashin kanshi,
Harda sa comb ya kwantar da sajen shi,

"Hello Handsome"πŸ˜‰ya kashe ma kanshi ido daya

Dariya yaji daga bayanshi, yana juyawa ya ganta tsaye cikin atamfa riga da skirt, sai katon dan kwalin da tayi rolling dashi,

" karki cemin baki taba kallon kanki a mirror kinyi blowing ma kanki kisses bah"
Ta kara boye dariyar ta ta hanyar rufe baki da hannu


"Nasan i look goood" ya wani jaa good din

Sai bayan sun gama dariyar ta tuno abinda ya kawota,

"Ina kwana?" Shima ya duka kasa yace lfy lau,

"Kin san irin gaisuwar da nakeso" ta girgixa kai

'Daman sanin wasu abubuwa ga meh da tsoronta ya gani'


"Ina son kullum da safe ki gaishe ni da Hug,koh da pecks, in san samu ne mah muah" yayi sautin sumbata,

Yana lura da yadda kalaman shi suka fara takura ta,

'Aciki wanne ne bata so, Allah yasa ba hugs bane bah'

"Fadamin wanne ne bakya so ki dinga yimin" ta girgixa kai

"Zan samu duka kenan" ta fara muraza yan yatsun ta,

"Muje waje in da zamu fi shan iska"
Ya nufi dakin kayan sawa ya dauko wasu sneakers, farare masu blue igiya da zanen Adidas a jiki,

"Bari inyi" zama yayi saman gado yana cewa ta barshi,

"Bakomai ka barshi inyi" ta duka gabanshi tana daure mai igiyan in ta samai takalmin,

"Tnk u My Wife" tayi murmushi

Kalaman Amyr ya tuno,
'Ka bata fili ta sha iska karka cika takurata,
Kuma ku dinga abubuwan nishadi tare, dakesa mutum ya manta damuwar sa, ya saki jiki yayi relaxing'

"Muyi breakfast a garden koh, ga iska meh dadi yana kadawa, ga shiru babu kwaramniya"

"Ga kamshin flowers, bakaman da daddare" ta karasa da yayi shiru

"Awwwww, matata na son in bata flowers ne"
Wani tsadadden murmushi tayi mai daya tafi da Myocardium (ban garen zuciya)dinshi,

Sake tuno wani abu yayi
'Mata nasan magana akan abinda ya shafe su,
Ka saurara sosai dan jin abubuwan da zatace,
Ta haka zaka iya dubara har ka gano abinda bataso daya kunshi saduwa'

Jin jina kai yayi shi kadai,bayan ya gama tuno point din daya haddace a kanshi,

'Lokaci yayi da zan sa matata tayi ta zuba kaman aku'

"Kai Allah ya barmin ke Wifey"
Trays ta jera saman carpet din da sukayi shimfida a waje,
Yaso ya tayata kawo kayan karin kumallo amma taki,

"Nagode sosai, har cikina ya fara kuka daga jin kamshin abincin nan,

Kece ta daya matata"

'Karka gaji da yaba ma matarka,komin kankantar abinda tayi,
Jin dadin haka ze kara mata karfin guiwwa wajen dagewa ta faran ta maka rai'

Kuma gashi sai blushing☺ takeyi,
'10 points Ehsaas, aikin ka na kyau'

"Wifey muci manah, koh sai na ba ki a baki tukunna"

Kallonshi tayi da eyes a waje,

"Toh ni ki bani" ya fada da shagwaba,
Dan nokewa tayi sai ya kyaleta

'Saika rungumi hakuri a irin lokacin nan, banda takura mata,

Ribar da mukeso muci shine ta saki jiki da mu, ina nufin da kai' Amyr ya gyara a lokacin da yake fadama Ehsaas,

"Thank you" tace don't mention
Fork ya dauka yana mika mata daya, saita dauki plate zata zuba nata, rikewa yayi saita dago suka hado,

Alama yayi mata da ta matso,
"Kara matsowa" shima ya dan matsa, space karami ya bari tsakanin su,

"Naji ance cin abinci a plate daya yana kara shakuwa da dankon soyayya, hakane?" Ta dan ga mai kai a hankali

"Dan Allah muci tare, pls wiiifeeeeeey"

Kallon mamaki ta tsaya yimai, banda turo lebenshi na kasa harda ido yake mata shagwaba, gasu kal kal sai dan circle din da yake hazel in color, shi bah brown bah kuma beh kai hasken light brown

"Plsss wiifeeeey?" Kyafta idanu tayi sau biyu sannan ta daga kai, dan batada muryar magana,


Coffee ta hadamai shi kuma ya yanka masu kwai daidai dauka kaci,
French toast din mah bayan ta shafa mai strawberry jam, sannan tayi topping da ice cream da Cherry a samaπŸ’,
Shi ya yanka masu into bite sizes kafin suka faraci,

"Barshi zasu kwashe" ya mike tsaya sannan ya mika mata hannu,

"Taso muje, akwai abinda nakeso in fada maki, kuma mu tattauna akai"

Suna tafe yana tuno abubuwa

'Wannan abu ne daya shafi ku biyu, so zefi in kuka tattauna akan abinda zakuyi wanda ze taimaka maku'

Tun a lokacin ya nemi cire wannan shawarar,

'Yana da mahimmanci ma'aurata su fuskanci ko wani matsala tare,

Koda matsalar na mutum daya ne, kada dayan ya tsangwame shi

kuma su taimaka ma juna wajen magance ta'

A yanxu ma da suke zagaye cikin lambun, ji yake baze iya fadamata bah,

Kar taga kaman jikinta yakeso , shi yasa ya dage kan neman masu mafita,

"Yanayin nan so romantic koh"
Ya sake cewa koh?
Dan ta amsa shi

"Eh, ba rana sosai" yana shirin magana yaga wani motsi

"Husna kalla, yama sunan abin, na dade bangan shi bah"

Ware idanu tayi tana kallon ko ina amma bataga abinda yake nuna mata bah

"Banga komai bah" tana tafiya kaman bataso ta daga kafa

"Ya sage da ciyayi ne ai, kuma kalli yadda yake tafiya a hankali, shi yasa baki ganshi bah" ta sake tsorata tana bude idanu sosai

"OH!MY!GOD! Kallan kayanki yake komawa"

Tana cikin zare idanu ta hango yellow da dan blue

Ihu ta kwada tana neman guduwa, yana bayanta, dan haka tana juyawa ta shige jikinshi,

Kara kankameshi tayi tana fidda sautin kuka,

"Bakya san hawai niya ne" ya tambaya da dariya a muryarshi

"Wake son shi" ta kara shigewa jikinshi

"Ni ina so kuma daukanshi zanyi" kara tayi tana neman sauka daga jikinshi,


"Wasa nakeyi, kin san na taba ganin harshen shi, wani irin dogo, daga can ze iya kawowa har nan inda muke"

Tana jin haka ta sauka,sannan ta dane bayanshi tana boye fuska jikin wuyan shi,

"Aww Husna ni ya tabani kenan"

Tace uhm uhmmm

"Mu tafi toh"
Sa hannu yayi ya goyata da kyau, sannan ya kara shiga cikin garden din,

Saida sukayi dan nisa kafin ta fara kokarin sauka


"In saukeki" ta daga kai,tana rikeshi gam gudun karta fadi,

"In akwai wasu fah" wannan karon saida ya cije lips dinshi, ya rufe idanu hade da dan tsayawa da tafiya,

'Gwara ka sauke diyar mutane kafin ka rasa dan control din da kake dashi'
Ya dan turo ma kanshi baki

'But ina jin dadin yanayin nan'

"Meh yasa muka tsaya" yayi yar dariya

"Mu tafi ne"
"Uhmmm" ta kara zagaye hannayenta a kirjinshi tana boye fuska a jikin wuyanshi,

Ajiyar zuciya ya fidda, phewwwww

"Mun dawo, koh in kaiki cikin gda" tana jin haka ta fara mutsu mutsun saukowa

"Ki daina motsi Husna" ya fada da karfin da beyi niyya bah,

Natsuwa tayi,amma kana ganinta kasan a tsorace take,

"Kin daina jin tsoron koh in fitar dake daga cikin lambun nan" kasa tabi da kallo

"Da mun fita daga nan zaka ajeyi ni koh" ya daga mata kai


'Basai na fada mata bah' yace a ranshi

'Tunda har ta yadda dani haka, nasan zamu gama da wannan shafin na rayuwar mu cikin sa'a'


"Yayi nan manah" kaman zatayi mai kuka,

Saida suka kai gaban kofar shiga yayi niyyan sauketa,

"Meye hakan" suka tsinkayi muryar Mamanshi, da sauri ya sauketa kafin ta fadi ta nakasa kanta,

Babanshi dariya kawai yayi yana girgixa kai,


"Ina kwana Mom Dad"
Ita tayi saurin gaishe dasu tana boye fuskarta,

"Sai yanxu ka tuno kana da Mu"
A ranshi yace yanxu mamanshi nasan yimai fada,

"Am sorry" ya bada hakuri, Asma'u kuma ta karasa cikin gdan da sauri,

Kafin ta tafi ya lura da wani abu, Idan ta kalli babanshi kunya zaka gani a idanunta

Amma in ta kalli mamanshi, tsoro zaka gani rubuce a fuskarta,

Shima din ya fara tsoran Mom din
Shi
"Yayi haka nan, Zo son" ya karasa zuwa inda suke

"Bawai da san raina bane bah, dan ya matsa ne" ta miko mai abu damtse a hannunta

"Bashi toh manah" gefe ta kalla sannan ta bude tafin hannunta

"Mom in bakya so in sa ____"

"Karka sa in canza ra'ayi na, ka dauka koh"
Da sauri ya dauka,tunda dama so yake

Yace Ya gode, yana barin wurin da sauri tayi tsaki

"Ka canki wurin wa zeje"

"Ki barsu manah, yara ne kuma yanxu suka shiga rayuwar auren, sai a hankali"
Babanshi ya fada yana fadaddan murmushi


"Kalla abinda Mom ta bani"
Dan kwalinta ta jawo tana rufe kanta

"Na tayaka murna" yace tnx
Sai lokacin yasa

"Yayi min kyau" tace Eh,

"Muje falo Manah, ya zaki zauna ke kadai a daki"
Girgixa kai tayi

"Kunya kike ji ne" batace komai bah amma yasan dalilin kenan,

"Kaman in muka canza gda zefi"

"Zefi meh" ya girgixa mata kai kawai

"Ba matsala in muka koma wani gda, ina san zama a kasar nan, amma a wani gda inda zakifi sakewa"

Batace komai bah sai gefen dankwalinta da take cukwi kwiyewa

"Ba matsala koh"
A hankali ta dago ta kalleshi

"Duk inda mijina yake ai nan ne mazauni na"

Yayi katon murmushi

"Okay, fara packing" kaman tace tun yanxu amma tayi shiru tace toh

Shima nashi dakin yaje,yana fiddo kaya

"Mom mun shirya" duk suka bishi da kallon tambaya

"Kun shirya Meh"
Nan yayi mata bayanin shirin shi na barin gdan,

"Ehsaas notinan kanka sun kwance koh,

Hakanan kawai sai in barka ka tafi wani wuri dan matarka naso"

Dama bata kaiga fitowa bah, tana jin wannan bayani saita tsaya daga baya,

"Mom ba haka bane bah, akwai dalilan daya sa nakeso mu tafi"

"Oh! Ta kalallame ka kana ganin kaman idea din naka ne"

Dukar da kai tayi kasa,hawayen na bin karan hancinta suna diga kasa

"Mom ni nakeson in tafi"
Dan tsagaita kukan tayi dan taji abinda zasuce

"Suna bukatar nasu space din tunda yanxu sukayi auren "

Bata tsaya karasa jin zancen bah ta koma daki, tasan koh babanshi baze iya canza ma Mom ra'ayi bah,


'Dear Diary' ta rubuta a cikin littafinta

Ta dan dade tana tunani kafin ta cigaba

'Dear Diary ina da BOYAYYEN KUDIRI'
Kafin auren nan na roki Alkhairin sa, in kuma ba Alkhairi bane bah kada ya faru,

Ta cigaba da rubuta duk abinda ke cikin ranta,

"Hey" itama ta cemai Hi

"Meh kikeyi" rufe littafin tayi tace na gama

Kunyar sanar da ita abinda ya faru yakeyi,
Ita kuma hanyar da zata sharemai hawaye take nema,

"Kana bukatar Hug dinne" maganar na fitowa daga bakinta ta zare idanu, tana dora hannu a saman bakinta,

" In zan samu" ajiyar zuciya tayi

'Ya cancanci fiye da haka daga wurin ki'
Mikewa tsaye tayi ta taka a hankali zuwa inda yake zaune,

Shima a hankali ya mike,kaman yana taka tsatsan ne kar ya tsoratata,

"It's okay" tace da murya meh karkarwa

"Kin tabbata" murmushin karfin hali tayi mai

Yana rungumeta gam, taji ya fidda sassanyar ajiyar zuciya

Kokari tayi ta kara sakin jikinta, ta rufe idanu dan kar barin jikinta ya cigaba

'Tare nake da Ehsaas, mijina' haka tayi ta fada har tazo ta daina

Sun dade haka a tsaye,babu meh cewa komai,

"Tnku Husna, u just made my day"
Tayi farin cikin jin kalaman shi, dan bata yi tsammanin su bah


"Ya kamata muyi sallah mu gode mah Allah, jiya bamu samu yi bah, kar yau mah ya wuce mu,

Sallah kawai"

Tace toh,
Da dare yayi sai gashi cikin jallabiya, abinda bata taba gani yasa bah

"Yayi min kyau" ta dago suka hada ido
Ashe ya lura da kallonshi takeyi

"Granny ma tasa na siye su, tace nima inyi maki kwalliya"

Bandaki ta shiga tayo alwalla, sannan ya jasu sallah,

Bayan sun iddar kuma ya dafa kanta ya jero addu'oin da aka tanada,

Kan akwatin da ta shirya kayanta idanun shi suka sauka,

"Na saki kin sha wahalan shirya kayan ki"
Da dan murmushi ta nuna mai bakomai

"In tayaki shirya su koh" tace Aa ya huta abinshi

"Meh yasa kace mu tafi da?" Dan kallon juna sukayi kafin kowa ya dauke idanun shi,

"Ina son ajeki inda zakiyi feeling comfortable,

In da babu wanda ze sa mana ido,

Na tabbata nan bada dadewa bah zasu fara gane ba nan nake kwana bah,

Kuma bana son confrontation, dan ban san abinda zance dasu bah,

Bazan iya fada musu dalili bah, kuma bazan iya karya bah"

"Meh ze hana ka dinga kwana anan"
Ita ma basan jin ansar tayi bah sai ta cigaba

"Zan iya komawa can in haka kakeso"

Girgixa kai yayi

"Nan mah yayi Husna, naji dadi sosai da kika bani wannan dama"

'Allah ka kawo manah sauki cikin wannan rayuwa tamu'
Tace a ranta,

"Husna, ina so kiyi min abu dayan nan pls"
Matsawa baya ta danyi tana rufe kafafunta da hijabi,

"Yau in zaki kwanta bacci, kiyi tunani akaina,
Akan halaye na masu kyau da marasa kyau,

Abin so da kuma abin ki"

Tacemai toh zatayi,

"Muyi bacci koh" ya mike yana kwashe prayer mat,

Bece komai bah data kwanta da hijab,
Pillow ya jera a tsakiyar gadon ,

"Haka yayi" daga mai kai tayi, saida ya kashe fitila ya kwanta sannan ta rufe idanu tana abinda ya nemi tayi.




⚜B.W.AπŸ–Š

⚜B.W.AπŸ–Š
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
BOYAYYEN KUDIRI.

πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Story, Writing By NOBLE JUDGE,
KHALEESI,
EDITING
KHALEESI.


DEDICATED TO,
Surayyahms, marubuciyar Alfah,

Congrats on d completion of your amazing book,

Can't wait to read d nxt one,πŸ€—



5⃣0βƒ£βž•5⃣1⃣




Steps bibiyu take tsalakewa saboda ana jiranta

"A hankali Asma'u, karki ji ciwo"
Da fara'a ta kai step na karshen sannan ta ba Hajia jakarta,

"Nagode Asma'u, kin tabbata bakya so ki bini,
Ehsaas da babanshi can zasu wuce daga masallaci"

Ta ce Aa ta hanyar jijiga kanta

"Ballantana mah basu gayyaceta bah"

Gyale ta mika ma Hajia wacce ta tsaya sa agogo

"Ai family yace beh banbanta bah,

Kema da kikace bazaki je bah, dan kanki kika zabi haka"


Uhmmm inji Mom

"In je in kwaso ma kaina bakin ciki,

Dan in zan gansu nasan sai na tafasa na kone a wurin nan _"

"Gwara ma karki je" Hajia ta hana ta karasawa da nata zancen,

"Ban son ki janyo min hankali mutane kanmu,

Kuma ina son inje ne kawai dan inga dana,

Kuma in gyara zumunci da yan uwana

Tabbas zanji zafi in naga Hannah,

Amma bakaman da bah, dan nasan komai mukaddari ne daga Allah"

Ta zata zancen ze kare a nan,

"Shima dan naki da kike kyarman gani Umma,

Ai beh da kishin kansa,

Da shi din ya cika dan halak, ai da beh barsu bah bayan rasuwa, zeyi waje dasu ne ya korasu inda suka fito,

Amma shi good

Please Login or Register in order to submit comment