Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abdallan.

Washe gari Litinin Bashir yayi sammakon komawa aiki bayan yabar komai da zaa buqata hannun Naziru, ranar ma bata wuni gida ba, gidan Yaya Bilkisu taje da suke ciki daya kuma ita kadaice yanzu a Gombe Babbar Yayarsu Anty Suhaima tana America da mijinta se Junaidiyya da take Abuja sauran uku mazane biyun qannenta yan biyu Bilal da Nasir suna karatun masters a China se yayanta daya Muslim yayi aure tuni yana zaune a Rivers da matarsa da yaransu biyu da A Lagos yake shima akayi masa transfer.

Sosai suka sha hira da Yayar tata har dare kamar karsu rabu, sun yi sallama akan Nan da kwana 7 zasu tafi Yola tare gurin maman su dukda ita Asma’u taso nan da kwana biyu ta wuce amma Yaya Bilki tace ta bari se anyi radin sunan yar Amirah idan yaso ko bata samu taron sunan ba babu matsala amma yanzu in ta tafi ze iya zama abin magana ai a kan hakan suka rabu.

Haka taci gaba da zaga yan uwanta har ana i gobesunan Amirah bayan la’asar tana zaune ta jiyo hayaniya an bude get. Ta window palour ta ta leqa da mamaki take kallon su Addah dake fitowa daga mota da Amira tana takawa dakyar bata ga jaririyar ba tana asibitin ita har yanzu.

Bangaren Amiran suka nufa seda suka shige sannan ta koma ta zauna tana mamaki tasan dai yau za’a sallameta dan ya gaya mata da tun Jiya daya dawo amma batayi zaton nan zata dawo ba kodan yanayin jikinta amma ita meye nata. Seda tayi sallar isha da dogon hijabin ta a jikinta ta nufi part din Amiran da kulolin da ta zuba tuwo da miyar kukar da ta saka Amna tayi.

Seda tayi sallama uku sannan suka jiyota ta tura qofar ta shiga duk sukayi wani tsilli tsilli alamar basu da gaskiya da gulmarta sukeyi a lokacin ta shiga. Bayan sun gaisa ta sakeyi mata ya jiki yau dai ta amsa bata zauna ba tayi musu sallama ta koma gurinta.

Washe gari suna da Asuba a masallacin unguwarsu aka radawa yarinya suna taci sunan Addah Fatu, Asma’u na daki Farida take gaya mata Amma Anty Ummi tace Iman zasu ringa kiranta, setayi Murmushi kawai ta tuna sunan Farida da tace nan ma ya saka mata Maryam sunan mamanta tunda yace ba sunan Dada ze saka ba ce mata yayi shi bashi da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu daya saka raayin kansa ne badan Aliyu Abokinsa ba kamar yanda ake zato.

Ana Abdallah kuwa cewa yayi ta siyi rago haka kuwa ta siya, haka aka yanka wa Baby Iman ragunanta biyu ba’ayi wani taro ba ranar tunda tana Asibiti har sannan sun dai qudurce a ransu fa se sunyi daga baya, dalilin ma daya sa suka dawo da ita gidanta kenan saboda duk abunda za’ayi ayi akan idon Asma’u dan Amirah tace shagali zatayi na kece raini.

Washe gari Suka soye naman su ko hanji basu Aikawa Asma’u da bama su san asubancin barin garin tayi ba ita da yara zuwa yola, suka rabe abinsu tas dan Bashir ma ya tafi tun safe kuma har nasa rabon suka cinye.

Toh maji ma gani dai.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 15

YOLA
Su Asma’u sun isa yola lafiya sun kuma samu tarba me kyau daga mamansu da suke kira da Goggo da bakinta yaqi rufuwa ganin yayan nata da kuma jikokinta a gabanta ba qaramin faranta mata yayi ba. Se sannu da zuwa take musu tama rasa wanne zata kama ciki idan ta janyo wannan yaron se saki ta kamo wancan su Asma’u har seda sukayi kwallar kewar Mahaifiyar tasu.

Seda suka nutsu sukayi sallolinsu sukaci abincin da Abokiyar zaman Goggon Innawuro ta kawo musu ga fura me sanyi da gardi sannan Goggo tayi musu jagora zuwa bangaren megidan su gaishe shi.

Fari kyakykyawan bafulatanin me kamilalliyar fuska dake cike da haiba da hasken salati yana nan a yanda Asma’u ta sanshi tunda tayi wayo sedai a kwantar a tayar tun zamanin da suke zuwa Tareda Baffan su dubashi wanda kuma tun kafin a haife ta yake wannan ciwon kimanin shekarun sa Arba’in kenan a kwance yana wannan jinyar da har yau Allah ne yanke masa ba sedai fatan ta zamo masa kankarar zunubi.

Seda sukayi dagaske gurin danne kukan tausayin bawan Allahn dake musu maraba daga kwancen ya miqa hannu ya kamo Abdallah yana cewa “Zo nan Abdullahi bawan Allah madallah da Amini na kwarai, Rahmar ubangiji ta dawwa ma tare da takwaranka a makwancinsa”.

Akan shimfidar sa da take a gyare ya zaunar da Abdallah sannan ya janyo Arif din Yaya Bilki yana cewa “wannan kuma me idon yan Chinese dinfa wanene” seda sukayi dariya gaba daya Innawuro tace “Toh takwaranka ne Isma’il dan wajen Bilkisu”

“Toh toh yi haquri ta kwara gajiyar hanya ce ta rufe idon ko nasan anjima zasu bude irin nawa”.
Cikin mutuntaka suka gaisa ya tambayesu sauran Yan uwansu da kowa da kowa duk suka amsa lafiya daga nan ya shiga saka musu Albarkar da bakinsa baya gajiya da ita a kullum suka hadu ko suka gaisa a waya. Sun dan zauna kafin yace suje su huta haka suda suka sha hanya, a nan suka bar yaran suka koma Dakin Goggo jikinsu dukka a sanyaye.

“Allah sarki Baffan Yola wannan jinya dai taqi ci taqi cinyewa Allah yasa kankarar zunubi ce” Asma’u ta fada tana kwanciya akan gado Goggo da Bilkisu suka Amsa da “Amin”. Basu ja wata hira ba suka kwanta aka barwa gobe dan sun gaji gaskiya.

Washe gari bayan sun je sun gaisa da Innawuro da Baffa suna zaune a palour Goggo suna cin Wainar Gero da Kunu me kyau da Innawuron tayi musu dan tasan suna son sa sosai. Goggo dake zaune daga gefe ta kalli Asma’u tace “Ma’u ya Abokiyar zaman ki kuwa kuna dai zaune lafiya koh”

Seda ta tsame hannunta kafin tace “Muna lafiya Goggo to ina muke ganin juna bare wani abu ya hada mu ina Lagos tana Gombe”

“Haka ake so ai dama wani sa’in raba gidan yana da amfani idan har akwai wasu matsaloli amma dai ko zuwa gaba idan ta fara tara iyali itama dole ya hade ku saboda a samu daidaiton kawuna tsakanin su dan dai nasan baki tashi kinga ana yan ubanci a gidan ku ba kuma zaki kaishi gidan wani ba”.

“Haka ne Goggo ai tama haihu fa shekaran jiya akayi suna” Yaya Bilkisu ta fada jin Asma’u tayi shiru bata ce komai ba.

“Kai Masha Allah me aka samu? Kuma cikin satin da aka fita fa Bashir din ya kirani Allah yasa kuwa beji babu dadi ba banyi masa barka ba ban sani ba ai da har ita Dadan tasu da Fatu na kira na musu barka, miqo min wayata nan Bilki ki gani karma na sha’afa da batun”.

Wayar Yaya Bilkisu ta bata ta kuwa shiga kiran Bashir sedai be Amsa ba saboda lokacin aiki ne seta maida kiran kan Dada ita ma seda ta kusa katsewa sannan ta daga. Cikin mutuntaka suka gaisa Dada ta tambayeta ya me jiki tace jiki gashinan se fatan Afuwa.

“Ashe kuma an samu qaruwa wallahi ban sani ba se yanzu muke zancen dasu Asma’u nake ji”

“Asma’u? Sunzo yola ne?” Dada ta tambaya dan bata sani ba Bashir din be gaya mata ba daman kuma tasan Ma’u ba Sallama zata mata ba yanzu.

“Eh wallahi sunzo tun jiya ita da Bilki, Allah ya raya yayi Albarka, haduwa tayi wuya amma Insha Allahu ina sa ran zuwa Bikin Hashim (Qanin su Ma’u da suke uba daya) anyi abubuwa da yawa Gombe ban samu leqowa ba”Goggo ta fada, da haka sukayi sallama ta kashe wayar bata ajiye ba ta dannawa Addah Fatu kira.

Itama lafiya lau suka gaisa tayi mata barka harta bawa Amirah waya suka gaisa da Goggo tayi mata sannu sannan ta kashe wayar ta maida hankalin ta kan Asma’u da tayi kinini da fuska dan tasan seta mata maganar qin gayawa Dada tafiyarta.

“Wato Ma’u bazaki chanza ashe, wai ni shin Nafi ce tayi miki kishiya ko Bashir da zaki bi ki qullaci baiwar Allah ki ringa gaba da ita. Sehi wanda ya miki laifi kina zaune qalau dashi amma kina raina uwarsa”

“Ni wallahi Goggo ban rainata ba me nake mata? Duk wani girma da ya kamata in bata ai ina bata to me ake so kuma nayi”

“Oh kina ma da bakin mayar min kenan, yanzu ina bata masan kin taho nan ba kin kwaso mata jikoki har shida kin biyo wannan hanyar bata sani ba, ba fata ba idan wani mugun abu ya faru kuma fa sedai kawai suji sama”.

“Toh ni yanzu Goggo ai ba haqqi na bane na gaya mata Danta ne ya kamata ya sanar da ita tunda ai ya sani da izininsa muka taho ai”

“Haka ma zakice, to maza ki kirata yanzu a waya ki bata haquri kuma kodan gaba ki kiyaye kar irin haka ta sake faruwa” Goggon ta fada.

“Dan Allah Goggo karki tilastani yin wani abun kuma dan kinsan bazan bijirewa umarninki ba, wane kalar haquri ne banayi, tunda Bashir yai aure sau daya na taba daga waya na kawo miki qarar sa akan yayi mun wani abu ai badan baya yimun din bane dan kince mun naje na shanye komai nayi haquri ne.
Bazan iya ci gaba da alaqa dasu ba abinda ya zama dole zanyi amma wallahi na yanke duk wata alaqa ta baya da kika sani tsanina dasu ga yar uwarsu nan se tayi musu abinda suke ganin ni bazan iya ba”. Ta qarasa maganar hawaye na sakko mata

Ta rasa me Goggo take so ta zama, a zatonta kowa irinta ne me tsananin hakuri, yakana da dauke kai akan komai? Ko kuwa duka maza kalar Mazajen data zauna dasu ne masu Adalci da sani ya kamata? Sannan kowane yayi dacen kishiyoyi na qwarai da dangin miji na gari. Sun fa qare tuni irinsu amma ita Goggo bazata gane wannan baudadden zamanin da muke ciki da ko cikin yayan da mutum ya haifa yake nuna banbanci dan daya yafi daya wadata, Namiji yake fifita buqatar wata mace akan wata saboda alaqar jini, sannan surukai suke zabar jinsu akan sauran surukai da suke baren su.

Ita Dadan ai da bakinta tace mata Dama sun dade suna son dorar da zumunchinsu kuma ta hanyar hada auratayya ne kadai haka ze yiwu ko to gashinan sun hada ta kuma janye ta basu guri suyi yanda suke so se kuma ace seta cusa kanta cikinsu ina sam fa bame yuwuwa bane.

“Toh yanzu menene na hawaye kuma daga magana” Goggo da jikinta yayi sanyi ta fada ai kamar Asma’u na jira kuwa ta fashe da kukan gaske harda sheshsheqa. Haka sukayi zukudi duk suna kallonta ranau babu dadi musamman Goggo, seta janyo Asma’un jikinta tana cewa

“Kiyi Haquri nasani ba’a kyauta miki ba, ba’a miki daidai ba kuma badan nafi son su nake cewa kiyi haqurin ba Aa sedai ina so ki rabauta da ladan da Allah ya tanadarwa masu yinsa. Idan kika jure kikayi haqurin idan ma sun zalince ki ko anan ko acan se Allah ya saka miki amma kiyi shiru ki dena kuka dan Allah”.

Dakyar ta tsagaita kukan tana ci gaba da share hawayen dai dai Innawuro ta shigo dakin.
“Ashsha Maryam me yasa kike haka duk sanda yarinyar nan tazo se kin saka ta kuka dan Allah menee haka” Innawuro ta fada tana janye Ma’un gareta kafin taci gaba da cewa

“Nasan zancen daya ne akan mijinki da danginsa, Duk abinda suka miki na cutuwa kar kiyi shiru Asma’u kiyi magana ki kwaci yan cinki, ki tsarkake zuciyarki kar ki nufi kowa da sharri kar kumaki bari su raina ki da sunan wai kina da haquri ko ita da take gaya miki hakan saboda Allah be jarabceta da irin wadannan fitintunun na zamani bane shiyasa take ganin kamar kowa irin zaman ta yake yi.
Share hawayenki dan Allah karki ragawa duk wanda yace ze taka ki ki rama kinji Ma’u”.

Dadi kalam Innawuro suka mata ai kuwa ta share hawayenta aka dauko wata hirar daban. Suna zaune Sauda da Maimuna Yaran Innawuro sukayi sallama sunzo wa su Ma’u sannu da zuwa nan suka shiga hirar yaushe gamo dan dama Saudah qawarta ce sosai.

Se yamma suka fita tare dasu Saudah sukaje gidan Hamma Isah Babban Dan Innawuro matarsa ta haihu suna gidan a ka kira waya aka fada. Washe gari kuma suka fara zaga dangin Goggonsu ta ko ina sune har Mambila daman haka sukeyi, basu fiya samun damar zuwa ko yaushe ba amma duk sanda suka zo se sun zaga ko ina sun gaisa da dangi tareda kai musu abun arziqi hakan kuwa ba qaramin dadi yake yiwa yan uwan Goggon dadi dan ko basu kai musu komai ba zuwa a gaisa din kadai ya wadatar.

Mu dawo Gombe 😂😂
Amirah na ci gaba da jinyar jikinta da kuma shirye shiryen shagalin sunan data rantse seta yi dukda haryanzu basuyi maganar da ogan ba amma jira takeyi da an sallamo baby Iman, ita kanta Addah wannan karon tace mata ta haqura gaba inda rabo se tayi kudin da ze bata se suyi wata hidimar dasu amma Amirah ta qeqashe qasa Allan fir se tayi. A cewarta haka kawai duk qawayenta tana gani in sun haihu yanda ake raqashewa kamar biki sannan ita ace kartayi wallahi ita ma se sunci uwar sabada kowa yazo ayi bushasha asan itama fa me kudinnan take aure se kuma Addah tace haka ne fa toh suyi kodan ma a maido musu da bikin gudummawar da sukayi.

Ranar Talata da daddare lokacin data tabbatar yana gida ta danna masa waya dan tana so ya bata kudaden da zata siyi kaya ta bada dinki ga kuma shirye shiryen suna. Bashir na zaune a palour yana shan Tea da cake gaba daya dauriya yakeyi amma zaman kadaicin ya isheshi gidan ya masa wani wawakeke saboda babu Ma’u a ciki ji yakeyi kamar ya kirata yace ta dawo.

Abinci kansa se kame kame yake in yunwa ta ci shine dole yake zuwa Restaurant yaci gaba daya besan me yasa wannan karon dan girke girken data saba masa ta saka a frizzer idan zatayi tafiya irin haka batayi ba, ya saba da sedai ya bude ya dauko yayi microwaving yaci to yanzu ko miya ce kadai itama ta qare dan Ma yayi dabarar sakawa a kunna wutar gidan bayan sun tafi wancan ranar daya tuna da abubuwan zasu baci gidan yayi wari dan haka ya saka aka karbo spare key na gidan a Estate Management Anty ta shiga ta qarasa kashe musu duk wani abu da ze iya kawo matsala aka bar frizzer.

Yana cikin tura Cake din Wayar Amirah ta shigo ya harari wayar sannan ya daga a dake dan ya san labarin gizo baya wuce na qoqi, indai Amirah ta kira shi to ko tambayar kudi ko qorafi in yana son jin yanda suke sedai shi ya kirata.

Bayan sun gaisa se duk sukayi shiru, yanayin dataji miryarsa ba walwala tasan dakyar in zata samu yanda take so amma haka ta daure taja numfashinta tace

“Abban Iman dama naji shiru ne baka ce komai ba akan siyayyar kayan Iman da nawa kasan wancan da ka bani unisex muka siya na amfanin farko farko”.

Seda ya mula sannan cikin dakewa dan karta kawo masa wani wargi yace “ke yanzu kayan me kuma kike magana kina fama da kanki?”

“Kayan barka mana” ta fada itama tana dakewa.

“Ni babu kudin wasu kayan barka da zan baki abinda nake dashi na bawa su Dada zasu hada da na gurinsu a siya wannan kayan Al’adar data ce na zata ma sun kawo muku”

“Basu kawo ba inaga se gobe” ta fada a cukule dan ba haka taso ba yanzu ma sune zasu siyo kayan aka san irin wanda take so? Sannan itama nata duk se sun gama gane wa kenan kafin tayi kwalliyar gaskiya bazata yarda ba sedai ya bata ko kudin Lace daya ne da zatayi kwalliyar Suna dashi dan haka ta gyara zama tace

“Toh shikenan amma dai se ka bani na siyi wanda zanyi fitar suna dashi danne kamata kowa ya gani ba sena saka”.

“Suna wane sunan kuma” ya tambayeta da mamaki dan dai yasan ai shekaran jiya akayi radin suna ko?

“Taron suna mana, idan an sallami Iman dole zamuyi tunda ai na farko ne kaga”.

“Karki kuskura wallahi idan bakiji tausayin kanki da jikinki ba to kiyi ke kadai amma ko da wasa karki sako mun ya a ciki ke ko yan barka ki ka ringa bawa yata aka jagwalgwalata se ranki yayi mummunan baci wallahi bare har ki tara mata hayani ya akai. Ke yanzu ko lafiyarta qalau ma ai kya dagamun qafa kodan kashe kudin da nayi a Asibiti kice ba se kinyi wani taro ba bare yarinyar har yanzu kina ganin yanda take”.

Seda ta tunzura baki kamar yana gaban ta tace “ to kowa ya haihu ana suna se ni ace baza’ayi nawa ba nidai se nayi gaskiya”

“Allah ya baki sa’a” ya fada tareda kashe wayar, ya fuskanci so take ta qure shi seya saita mata kwakwalwar ta sannan zata dawo kan hanya. Allah ya bata ikon yin taron sunan tabbas seta gane waye Bashir kuwa.

Amirah

Hararar wayar tayi harda murguda baki tace “Dan rainin hankali wallahi se nayi kuma seka bada kudin, naga matar ka duk haihuwa ai setayi suna na Alfarma sanda ma baka dashi bare ni yanzu dole ma ka nemo su ka bani. Labarta wa Addah komai tayi tace ta rabu dashi ze bayar bari dai a sallamo yarinyar ai taji Likitan yace Alhamis ko Juma’a zasu iya sallamar su ko, haka sukaci gabada tsare tsaren su.

Washe gari gurin goma na safe Suna zaune a palour tareda yan gidansu da suka sake zuwa dubata harda kishiyoyin Addah dukka biyun da matan yayyenta kamar aike sega Sallamr Dada ta shigo Naziru da Fainusa da Ihsan na biye da ita da akwatuna guda biyu ga kuka saitin baho da Qaramin gado me net.

Nan suka shiga musu maraba suka zauna aka gaisa kafin Dada ta kalli Addah tana cewa “Addah ga kayan barka nan nace dai ya kamata a kawo tunda al’adace gashi munyi sa’a ma yan gidan nasu suna nan.

Addah baki har kunne nan aka shiga zuge jakun kuna ga kaya nan tabarakallah komai yaji Babbar kayan jaririyane tsala tsalan riguna da sauran tarkacen kayan baby na yan gayu seta tsakiya kuma kayan Amirah Atamfofi guda biyu Madam Getzner daya se Laces masu kyau suma biyu kayan da gani kaf kasanba qanana bane harda mayafi kalar lace daya da jaka da takalminsa.

Amirah na nade akan kujera Lace din da aka hadowa da takalmi da jaka ya tafi da ita amma kuma batajin zata saka tunda mutane sun gani.

“Gasunan dana gurin Bashir da gudummawar yan uwansa dukka aka hada mukayo siyayyar” cewar Dada.
“Kaya sunyi sosai Allah ya qara arziqi yasa lafiya ta kashe, Se ki fito da na gurin ku kema su gani ko Fatu” Inna Gaji dake faman daga kaya ta fada.

“Fatu ai se ku fito dana ku ko tunda gasu su gani” ai Addah ji tayi kaman ta kwadawa Inna Gaji mari wannan tonon silili da take neman yi mata a gaban kishiyoyi sun kuwa zuba ido da kunnuwa suna jira suji me za’a ce dan Al’adar gidan su haka akeyi da an kawo kayan gidan miji suma zasu fito da masu a hada amma ita ko pant bata siya ba.

Rasa ta cewa tayi dan haka ta shiga kame kame tana yaqe Dada ta taimaka ta kwaceta da cewa “kai se kace wani abun bare ai bamu raba daya biyu ba duk gasunan ai na dangin uwa dana miji kune dai zaku fito da naku yanzu dangin uba” tayi maganar cikin sigar wasa akabat Addah da sauke ajiyar zuciya da yaqen dole.

Dada bata jima ba tayi musu sallama ta fita Addah tabi bayanta.
“Kai Nafi kin ceceni wannan shegiyar Gajin dason qure mutum haihuwar data zo lokacin ta beyi ba ina naga ta siyan wasu kaya ga wannan lalura”
“Hakane” Dada ta bata amsa.

“Yauwa dama yau nake so nazo muyi maganar taron suna da za’ayi idan an sallamo yar, kin san yanzu se ya zama abin magana idanba’ayi ba fa”

“Wace irin magana kuma Addah bayan kowa yasan halin da uwar da yar suke ciki, dan Allah kibar wannan magana Allah ya kaimu gaba ai ba gamawa tayi ba se ayi”. Cewar Dada

“Kiji ki Nafi da wata magana to in kin manta bari na tuna miki Binta ba bakwainin kika haifeta ba(Babbar yarta) kuma haka muka shirya taron suna akayi”.

“Amma Addah bazaki hada zamanin Binta dana wannan yarinyar ba, Binta a sannan ba ma waye da zuwa Asibiti ba qarewarta a gida na haifeta yanzu kuwa abu ko da anyi shi babu matsala tunda zamani yashiga cikin abubuwa koya kika kuskure se kiga an samu akasi azo ana dana sani nidai a shawara ku haqura nasan kuma shina Bashir din baze bari ayi ba”. Dada ta sake fada ranta fal takaicin Addah.

“Wallahi se Anyi jikar tawa ta fari kuma takwarata kice bazanyi suna ma baqin ciki ma kikemun kenan ko”

“Wane irin baqin ciki kuma Addah nima ai jikata ce ko ban haifi Bashir ba”

“Toh in ma dai hada baki kukayi kedashi yace baza’ayi ba tun wuri ki gaya masa wallahi suna ba fashi ya lalo kudade ya bata da zatayi hidima in ba haka ba rai ya baci” tana gama fadar haka ta juya fuuu tayi ciki.

“Dan Allah Dada muje wallahi ko Yaya ya yarda bazasuyi sunan ba ai dai ni zece nabada kudin ko zamu gani” Naziru ya fada yana huci, haka suka shiga motar suna tafe shida Fainusa suna debewa Addah albarka Dada dai bata iya ce musu komai ba gaba daya ta tafi tunanin meke damun Addah a rayuwa ne. Su yanzu inda hankali ko cewa akayi suyi ai sace Aa amma har tana rantsuwar ae sunyi, to wannan karon zata ja itama bazata takurawa Bashir ba kuma ko sunyi galaba akan sa ya yarda seta hana, zata nuna mata bafa tsoro yasa take mata biyayya ba.

Allah dai ya mana maganin abinda yafi qarfin mu.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 16

Ranar Juma’a Bashir ya dawo Gombe kuma ranar aka sallamo baby Iman, Bashir da kansa ya dakkota bayan da ya dawo dan daman shi ya hana likitan sallamar su akan se yadawo saboda matsawar da Addah tai masa akan zancen shagalin suna.

Amiran bata daddara ba washe garin randa sukayi maganar seda ta sake kira ya kuwa yi mata tatas dan dama sunyi waya da Dada ta gaya masa yanda suka kwashe da Addahn dan haka ya qara tabbatar mata da wallahi ko sisin sa baze bayar ayi wani suna ba idan bata gode rai da lafiyar da Allah ya basu ita da yar ba ta godewa Azabarsa. Ai kuwa itama Addah batayi sanya ba ta karbe waya ta masa wankan tsaf ta kuma sake tabbatar masa fa taron sun ba fashi.

Shekara da shekaru tana rabar da kudin Barka da biki, haka auran Amiran kaman na munafukai basu barta tayi shagali ba yanzu ma a haifar mata jika suce Aa, to kuwa bazata sabu ba shidai ya mata shiru harta qaraci kumfar bakinta ta kashe ya kuwa rangadawa Amirah text din gargadi tunda ga ranar ma be sake kiranta ba idan ma ta kirashi baya dauka se yau Juma’a daya dawo garin suka hadu.

Yaso ma da ya tafi ya karbo yarinyar shi kadai sedai kuma ya tuna Amiran na buqatar a karanta mata yanda zata kula da yarinyar yasa yace ta shirya su tafi se gata ita da Hajia Addah aka shige mota.

Sau goma suka hada ido da Addah se sun jefi juna da harara ita da Bashir can dai da abin ya isheta tace “Bani kake harara ba Bashir Uwarka Nafi da Amadu su kake harara mara mutunchin kawai, kuma duk baqin cikinka suna ne se munyi se dai kayi bindiga ka mutu”.

Kici kanki be ce mata ba har suka je Asibitin, sosai likita yaja kunnensu akan kula

Please Login or Register in order to submit comment