Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin gashin qumar da zanyiwa Bashir idan har na koma gidan sa. Shi da sake jin dadin zama dani har abada.

Washe gari Goggo ta koma bayan ta sake yi mun kakkausan gargadi akan idan na sake ta sake jin wani abu se tayi mummunan saba mun, na koma gidana na zauna kuma duk abinda zan gani naje nayi haquri karna kuskura na dauki dabi’ar kai qara ko na ce zan sake yin yaji.

“Asma’u badan bana sonki yasa nayi miki haka ba, nasan ba’a kyauta miki ba amma hakan baze zama silar da zaki bar uban yayanki ba idan kin rabu da Bashir saboda kishiya qarshe dai wata zaki je ki tarar a duk inda zaki fada to menene amfanin haka” Goggo ta fada cikin lallama bayan da ta gama yimun fadan kuma, sena share hawayena tunda yanzu ta sakko se muyi magana ta fahimta nace

“Wallahi Goggo ni ba qarin auran sa ko rashin gayamun da beyi bane ya dame ni amma me yasa ze auri Amirah?”

“Saboda yana sonta kuma ita Allah ya zaba masa kin san dai duk yanda mutum yaso da son kasancewar abu idan Allah be hukunta hakan ba baze faru ba ko, haka duk yanda ka kai ga qin abu idan Allah ya qaddara faruwar sa babu abinda ya isa ya tsayar da hakan to kar kiyi jayayya da hukuncin Allah Asma’u, ki dauka daman tun kafin wanzuwar duniya yanda Ubangiji ya qaddara ke matar Bashir ce haka itama aka rubuto matar sa ce dan haka dole se ya aure ku.

Maganar munafunci ko yaudarar ki da sukayi wannan ki barwa Allah komai kina zaune se kiga ya saka miki a ruwan sanyi kinji ko kiyi haquri kar kuma wannan dalilin yasa kice zaki quntata zamanki da mijinki, a yanzu ne ya kamata kija shi a jiki dakyau ki bashi dukkan kulawa da soyayyar data kamata saboda ba ke kadai bace, duk abinda ya rasa a gurinki ze same shi a wani gurin daga nan kuma se hankalin sa ya fi karkata can saboda zuciya ai tana son me kyautata mata ke kuma daga qarshe se kiga kamar dan ya samu wata ne ya watsar dake bayan ke kika bada damar hakan.

Dan haka bani da damuwa akan ki Ma’uta nasan zaki riqe kanbun nan naki na Uwargida sarautar mata dakyau ina so ki nuna musu cewa ke din fa badai mutum ba se Allah, Allah yayi miki Albarka ya ci gaba da kareki a duk inda kike”.

Kalaman Goggo sunyi tasiri sosai a zuciyata dan gaskiya ta fada da ace wata daban aka auro mun davkuwa tabbas na nuna mata cewa kishi da MA’U ba wasa bane se ta shirya amma a duk sanda na tuna wa Bashir ya aura se naji bazan iya amfani da ko daya daga cikin abinda ta fada din ba.

Haka ta koma Yola washe garin ranar nima yan uwana suka raka ni gidan mu na Gombe bayan da suka hadu suka sake yi mun nasiha da rarrashi, banje na bawa su Dada haquri ba itama kuma Goggon bata tsananta ba tunda na yarda zan koma din ta rabu dani.

Gini yayi kyau sosai kuma an saka komai na amfani sabo daga yanayin kyau da tsaruwar kayan na tabbatar da aikin Yan gidan mu ne sunyi zumunchi sosai suka hada mun gida kamar na wata sabuwar Amarya ko tsohon lokaci nada ba’a saka a gidan ba.

Yanda kowa ya ringa yabawa ni kuwa baqin sa nake gani dan da gidan da mamallakinsa a yanzu basa gabana ko kadan biyayyar iyaye ce ta dawo dani cikinsa.

Bayan kowa ya watse Bashir ya shigo yanda kasan wasu Baqin da basu taba haduwa ba haka muka zama, shi yana kaffa kaffa dani karya yi abinda ze zama laifi ni kuma na baiwa Banza ajiyarsa ina ta sabgogina se shi da yaransa yake ta magana yana tambayarsu abubuwan da suke buqata wanda sarai nasan dani yake naji dadi da suka ce masa babu.

Su kansu yaran daga kan Amna zuwa Farida ba wani sakewa sukayi dashi ba Abdallah da yan biyu ne babu abinda ya sha musu kai suke ta murna sunyi kewar Abbi. Aliyu daman yafi kowa daukar zafi, kuka ya ringayi da gaske lokacin da yaji maganar auran ya kuma dauki fushi da uban ko yau din da muka dawo ina kallon yanda yake cika yana batsewa.

Da daddare gurin qarfe tara muna zaune a palourn qasa muna hira muka ga an bude qofa, da yake irin wadda bata buduwa ta wajen nan ce nasan Bashir ne shine yake da key dan haka ban ko kalli qofar ba na sake hada rai na zubawa TV ido.

Da sallama a bakinsa ya shigo, takun qarar takalmin da naji bayan muryarsa ya saka na waiwaya da mamakin naga shi da waye haka karaf idona ya sauka cikin na Amirah data sha Kwalliya da wani Material Cotton baqi me Pink din flowers dinkin riga da skirt sun kamata dam se wani dan yalolon gyale data yafo a kafada.

Cikin abinda be wuce second biyar ba na qare mata kallo na mayar da kaina zuwa ga TV ina nanata “La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minzzalimin” a zuciyata saboda jin wani abu yana tasomun kamar zanyi aman zuciyata har wata zufa naji tana tsatstsafo mun.

Ta gefen ido nake kallon sanda suka zauna akan kujera, ina jin qamshin turaren data saka ya baza gurin irin turaren da nake amfani dasu ne na Maryam collection ta zauna a kusa da Bashir sosai kamar zata shige jikinsa shi kuma se turata yake yi abin ma se ya bani dariya na dan yi murmushi a raina nace “yaro yaro ne” amma ban ko juya na kalle su ba.

Ina jin yaran suka hada baki suka gaishe shi ya amsa a zatona zasu gaida Amirah se naji dif sun ma mayar da hankali akan film din da muke kallo Bashir da qarfin hali naji yana cewa wai

“Baku ga Antyn ku ba baku gaisheta ba”

“Wacece tana ina ai mu kai kadai muka gani Abbi se Amirah” Aliyu ya fada yana kafe uban da kallo wanda mamaki ne nasan ya hana Bashir din magana. Yanda kasan bana gurin haka nayi musu dayake film din yazo qarshe ana gamawa yaran suka miqe dan daman abinda ya zaunar da mu kenan nima se na shiga qoqarin miqewa Bashir ya dakatar da ni da cewa

“Ma’u ina kuma zaki je gurinki fa muka zo” sena koma na zauna na waiwaya ina kallon sa da murmushi akan fuskata wanda a badini kuka nakeyi cikin zuciyata amma nayi Alqawarin wannan yarinyar bata isa taga gazawata ba, se a yanzu nima na dawo hayyacina tabbas idan na bar mata gidan ta ci galaba akaina dan haka zan zauna kuma ba zaman dadi ba kowa se yaji a jikinsa.

“Amirah baki gaida Antyn ki ba “ ya fada bayan dana zauna, Amirah da ta hada fuska bakin nan kamar ze tabo POP tace “Nima ai yayanta basu gaishe ni ba, kana ji fa wannan marakunyar Aliyun cewa yayi ma be ganni ba kuma baka ce komai ba”.

Dukda qasa qasa tayi maganar amma tsaf naji ta a raina nace “zanci uwarki ne yarinya mu dai ke zuwa”.

Kamar me jira kuwa l Bashir ya hau masifa yana fada mata maganganu, abin haushi abin dariya dramar tasu ganin abin bana qare bane na miqe nace masa

“Ka rufe mana qofar idan kun fita” ban ko saurara ba na haye sama na barsu a gurin. Har na kwanta Bashir ya shigo dakin, da saurin gaske ya nufoni kafin ya qaraso na dire daga gadon ban yi wata wata ba na izge Fitilar gefeb gadona daga soket na daga ta na nuna masa ina cewa

“Wallahi ka kuskura hannunka ya tabani sena yi maka rotse da wannan, badai ka hadani da Goggo ta tilastani dawowa gidan ka ba, ka tabbatar da ka kaiwa tashin hankali katin gayyata da hannunka”.

Yanda nayin ya tabbatar masa dagaske idan ya matsa zan iya kwada masan, daga nesa ya ringa yi mun magiya da nayi haquri na saurare shi amma nayi masa banza haka ya qaraci nacinsa ya fita ya bar mun dakin.

Haka muka ci gaba da rayuwa a gidan tsakanina da Bashir daga kallo se harara shi kuma kullum yana nan a lalace gurin roqona da bani haquri amma nayi kunnen uwar shegu dashi dukda qasan raina na fara hucewa bafa wai dan na manta da abinda yayi mun ba Aa sedai kawai na yarda cewa komai muqaddari ne a rayuwa daman tun a lauhul mahfuz an rubuta faruwar wannan al’amari a rayuwar mu.

Kusan sati biyu ranar ya same ni da batun komawa Lagos saboda hutun daya dauka ya qare, a lokacin bani da zabi kodan aikina da makarantar yara da suke zaune a gida ya kamata na koma sannan hakan ze dada nisan tani da Amirah dukda ko a yanzun ma tun ranar farkon suka shigo bamu sake haduwa ba. Haka muka fara shirye shiryen tafiya, ana i gobe zamu tafi ban san meya shigar da Ahmad bangaren ta ba se kukan sa muka jiyo a waje Amna ta tafi da gudu ta dakko shi ina duba fuskar yaro naga shatin yatsu da alamar marinsa akayi.

Cikin tsananin bacin rai na tambayeshi waya mare shi, yana kuka da maganar sa da bata gama fita ba yace “Anty Amirah ce, da safe Abbi ya nuna masa gurin yace tana ciki shine yaje suyi wasa (Sun saba tana wasa dasu) saboda na zubar da Tea ban sani ba ta mare ni”.

Zan dauki komai amma banda taba mun yara musamman ma ya zamana da cin zali amma tayi kadan dana taka gurinta nayi mata kashe di dan haka zan jira wanda ya ajiyeta yazo shine daidai yina. Da yamma Bashir ya dawo, yana shigowa Ahmad din ya tafi gurinsa da gudu ya fashe da sabon kuka yana gaya masa abinda ya faru.

“Ka ja mata kunne karta kuskura ta sake taba mun yara idan ba haka ba zan dauki mataki” na fada ba tareda na kalle shi ba. Se ya juya da Ahmad din a hannunsa suka fita ban san me yace mata ba dab da magriba dan har nayi alwala naji ana buga qofa.

Farida nacewa taje ta bude, tana budewa kuwa ta turo qofar da qarfi dan qiris ya tage ta buge Faridan, seda ta qaraso tsakiyar Palour ta wani tsaya ta kama qugu tace “Saboda munafunci shine za’a hadani da Mijina dan na daki yaro, ai barna yayi mun kuma ko yanzu wani ya sake zuwa yayi mun wani abu se na daka yaro sedai duk abinda za’ayi ayi, mtsw aikin banza kawai...” ban bari ta kai qarshen rashin kunyar tata ba na kai mata wani bahagon mari cikin sa’a na sameta dakyau na doke bakin fitsarar take kuwa leben ta ya fashe kafin ta gama gane abinda ya faru na sake kai mata wani ta dama ta fasa qara ta dafe kunci dama da hagu tana ihu daidai lokacin Bashir ya shigo.

Ban damu da shigowarsa ba ko ihun da takeyi na nunata nace “wannan gargadi nayi miki duk ranar da kika sake tako qafar ki gurin nan ki qaddara ma gaisuwa ce ta kawoki ba wai kinzo yimun fitsara da rashin kunya ba wallahi se nayi miki dukan da zaki kasa tashi, wawiya mata hankali kawai” na juya na haye sama Bashit yabi bayana muka barta a gurin tana zunduma ihu.

“Ma’u meya faru” ya fada bayan daya tarar dani”
“Kaja mata kunne tafi kowa sanin ni ha sa’arta bace idan tana ji da rashin kunya da fitsararta ni daidai nake da ita zan koya mata hankalin da bata dashi” na juya na tayar da sallah ta na barshi a tsaye.

Washe garin ranar muka koma Lagos, Sanda muka je na tarar Bashir ya sake gyara mana palour an chanza komai na ciki, sannan ga sabuwar mota me kyau model din shekarar a ajiye a inda nake saka mota ta, lambar jikin tsohuwar tawa dana gani a jiki ya tabbatar mun da tawa ce.

Haka ya ringa yi mun abubuwa har makaranta ya chanzawa yara ya mayar da su wata da tun farko naso a saka su yace tayi tsada abubuwa dai kala kala wanda duk na neman shiri ne, daga qarshe dai bayan dogon jan rai da ban haquri dana sha kala kala daga gurin Bashir na haqura na sakko muka dawo zaman mu lafiya badan na manta abinda yayi mun ba sedan ban isa na jada hukuncin Allah ba.

Iya horon da zan yi masa nayi ya kuma sauke kai ya bani haquri da tarin alqawarurruka kala kala Albarkacin son da nake masa da dattijantakar mahaifinsa ga kuma Alfarmar Mahaifiyata daya shiga na cire komai daga zuciyata ta na nemi muqulli na kulle wancan baqin littafin na rayuwar mu muka bude sabon babin rayuwa me cike da qauna da Aminci, haka rayuwa taci gaba da gara mana yau fari gobe baqi har kawo wannan lokacin da me afkuwa ta afku, Bashir ya yanke igiyoyin auran mu a lokacin dana gama ammana da bashi rayuwata.

CiGaBaN LaBaRi

Afuwan Uzuri ya riqeni kuyi manaji da wannan 🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 40
Mau ta kwalla ihu tadauki wuka ta nufi adda tace dan kutumar ubanki uwar bashir da dada yau sekun tafi lahira ta caka ma adda a duwawu tsiii kKeji jini nafita ta wanka ma dada mari tayi tsalle ta naushi bshir ta kwaso amira ta hau ruwan cikanta...tsiiii 😂😂😂😅😅😅🤪🤪🤪🤪sekuma kuyi nice nan shugaban en bati
Har Bashir ya gama kwanakin sa a Delta ba wani magana mukeyi ba, a ranar da ya tafi dai bayan sun sauka ya kirani haka washe gari da safe kafin su fita field munyi waya bayan nan kuwa har suka kwana hudu be sake kirana ba nima kuma ban kirashi ba.

A tunani na ko aiki ne yayi masa yawa, dan daman yawan ci idan yana field bamu cika yin waya ba shine dai idan ya samu lokaci ze kira to wannan karon ma na dauka a hakan ne.

Ranar Lahadin da suka kwana hudu da daddare muna zaune wayar Aliyu dake kusa da ni tayi qara,
"Aliyu wato har ka rarrabawa Jama'a Number ka ni bani da ita koh, waye yake kiranka da daren nan?" Na daga wayar ina dubawa.

"Super hero" naga an saka, na gane Number Bashir ce sena miqa masa ina cewa "uhm uhm su Bat Man ne ko Spider man naga an sa super hero".

Gaba daya suka saka dariya, Aliyu ya daga wayar suka gaisa, ban san meya gaya masa ba nadai ji yace "toh ga Mamin ma ko na bata ka gaya mata?"
"Tam Abbi bye" ya sake fada kafin ya kashe wayar yana kallona.

"Mami, Abbi yace Mr Kunle ze zo yanzu ya kawo saqo, akwai kudi a bedside drawer dinsa ki bashi 20k".

Kamar wata sokuwa haka nake kallon Aliyun harya gama. Abubuwan mamakin da yawa, ashe Bashir yana da lokacin kiran waya nice baze kira ba.

Sannan yaushe muka fara haka da ze fadi abu ni baze kirani da kansa ya gaya mun ba sedai ya kira Aliyu?

Wayata dake kan centre table na janyo na danna power button dan na tabbatar ko a kashe take be sameni ba ya kira Aliyun naga a kunne take. Ga network dina full to meye dalili?

"Hmmmm" na fada a fili kawai na ci gaba da kallon da muke, ba'a jima ba kuwa aka danna Door Bell Jafar yaje ya bude se gashi da Babban Package da alama PS din da aka ishe ni da naci kamar nina ce zan siya aka kawo.

"Mami yana jiran saqon wai" ya fada bayan ya zauna ya fara budewa Abdallah na taya shi.
Se na waiwaya na kalli Aliyu nace

"Kaje ka dakko masa baya gaya maka inda suke ba?"

Seda yai dan jim kafin ya miqe ya shiga dakin nasa, be jima ba ya fito da kudin a hannunsa ya miqo mun yana cewa "Gashi na dakko".

A hasale nace masa "zaka tashin mun akai ne ko yaya, ina kai ya gayawa saqon kuma kazo kana nunamun me zanyi dasu".

Zugui zugui ya fice ya kaiwa Kunle kudin ya dawo. Ina kallon yanda yake satar kallona ganin na dora qafa daya kan daya ina girgizawa duk sanda suka ga ina haka to sun san zuciyata a kusa take, ina iya make su idan suka matsamun.

Hayaniyar da Jafar da Aliyu suka fara suna qoqarin jona PS din da Tv tasa na daka mutsu tsawa ina cewa "ku bace mun a nan, ba gobe Monday ba shine a wannan lokacin kuke shirin dasa wata Game, ku tattara ko yanzu na fasata wallahi".

Kama kansu sukayi sum sum gaba daya suka watse, ina zaune ina sakin tsaki, son na tabbatar da zargina sena janyo wayata na dokawa Bashir kira na kuwa taki sa'a akace call waiting.

A da, indai na kira Bashir ko da wa yake waya se ya dakata ya amsa kirana, ba qaramar waya me muhimmanci bace zan kirashi ya kasa katseta amma yau har ta gama ringing ta yanke be daga ba.
Na sake kira nan ma be daga ba, seda na jera masa kira hudu amma bawan Allahn nan ko a jikinsa kuma har sannan call waiting.

Agogo na kalla, tara harda rabi tayi, nasan babu wani official call da ze ce yana yi yanzu, kuma na tabbata bada Dada yake waya ba dan sanin da na mata da Tayi Isha take kwanciya to da uwar wa yake waya da baze amsa tawa ba?

"Amirah" zuciya ta ta raya mun, se ta yuwu kuwa din. A jiye wayar nayi ina jiran ya biyo baya amma har goma da rabi shiru ba kiran Bashir babu labarinsa, sena miqe jiki a sanyaye na shiga dakina.

Tunani na shigayi ko na masa wani abu a wayar da mukayi qarshe, iya hasashena ban gano komai ba dan lafiya mukayi hira kamar ma be tafi muna fushi da juna ba. Haka na ringa juyi a gado ina tunane tunane to wane sabon shafin ne kuma ze bude mun, koma dai menene Allah ya bamu wuce wa lafiya da haka bacci yayi awon gaba dani.

Daga mamaki mani abun na Bashir tsoro ya koma bani, dan fa washe gari be biyo kirana ba, da yake na koma aiki nima ranar na shiga busy ban wani nutsu ba se da daddare na duba wayar na tabbatar da be kira ba kuma qarin abun mamaki da magriba ma seda ya kira Aliyu ya bawa dukka yaran sukayi waya harda tambayar me ze taho musu dashi.

Nidai ido na kawo na zubawa sarautar Allah, duk tsiya dai ze dawo gidan se inji me ya faru kuma.

Na zata ranar Larabar ze dawo tunda itace cikar sati da tafiyar su daman kwana biyar yace ko sati to gashi har yau Talata dan haka na saddaqar se gobe ze dawo.

Bayan na tashi aiki  na biya na dakko yara, dukda magriba ta kawo kai haka na biya wata yar kasuwa da ake siyar da Dangin su Kaji masu rai, Bashir yana son Danderun Zabi dan haka na siyi manya guda biyu aka yanka su aka fige kamun muka kamo hanyar gida Ba mu muka isa ba se ana shirin shiga sallar Isha saboda holdup.

Jakata kawai na ajiye muka shiga Kitchen tareda Amna, seda na wanke Zabon tsaf yanda nake so kafin na saka a kwando su tsane na bar Amna ta hada kayan hadi dan tana fashin sallah ni kuma na tafi nayi magriba da Isha .

Sanda na dawo ta hada komai na marinate dan tasan yanda nake so, seda na saka wuqa na huda jikinsu sosai yanda kayan hadin zasu shiga na shafe lungu da saqo na ko ina ya juqu sannan na nade a Foil paper ya nadu da kyau, Already ta kunna oven yayi zafi dan haka na dora su akan Baking try da aka zuba ruwa na kunna wuta sama da qasa na rufe.

Ban san sanda ze dawo ba da safe ne koda daddare dan haka A daren nan seda na hada masa zobo irin wanda yake so na saka a fridge, na gyara zogale na yanka Albasar da zanyi masa Dambun shinkafa nice harda dakan gyada kamar aljana na turara tsakin shinkar  na saka komai a fridge yanda gobe kawai sedai na hada.

Na gaji tiqis, haka na koma palour na kwanta ina yi ina duba naman dana saka ina qara ruwan dan karya qone nice har qarfe biyu, jin bacci na neman fin qarfina na kashe kawai tunda nasan zuwa yanzu yafi rabin dahuwa in Allah ya kaimu gobe na ci gaba.

Dakyar na iya tashi sallar asuba dan ji nayi kamar ma ina kwanciya aka tashe ni. Haka ina yin sallah na koma kan aikin, ga shirin yan makaranta da ni kaina. Qarfe bakwai muna breakfast Bashir ya kirani.

Rai a sake na amsa wayar duk da qasan zuciyata akwai haushin qin kirana da yayi amma na daure dan babu qarya nayi kewarsa sosai, rabon da mu kebe tun muna Gombe.

A dake ya amsa gaisuwar da nayi masa, mukayi shiru gaba daya kafin ya nisa yace
"Yau zamu dawo In sha Allah zuwa dare zan shigo gida".

"Masha Allah, Allah ya dawo daku lafiya nayi kewarka da yawa". Na fada cikin shauqin da na kasa dakatar da kaina.

Wani miskilin murmushi yayi kafin yace "Na sani ai"
"Oh ka ma sani kenan" na fada adan shagwabe.
"Zan kiraki anjima" ya fada, ko kafin na bashi amsa ya katsewa wayar, sena ajiye na ci gaba da kurbar Tea na rai fes.

Seda nayi yar murya sannan aka bar yaran suka shiga makaranta saboda mun makara, School Bus nace su biyo idan an tashi kawai dan inaga idan Bashir ya dawo kawai zan masa magana su ringa bin school bus din kamar zefi sauqi.

A office ma ban wani maida hankali ba, qarfe biyu na dauki excuse na tafi gida. Seda na gyare gidan qal na chanza Bedsheet din dakin Bashir na saka turaren wuta.

Kayan harkar dana hada na shanye kafin na dakko wani hadin dilka da Anty ta bani na na mutstsike jikina tsaf na turara sannan na dauraye jikina na koma Kitchen.

Na riga naci qarfin aikin tun jiya, Danderun na duba yayi luguf dan tun shigowata na ci gaba da bashi wuta gaba daya gidan ya dume da qamshinsa ga na turaren da nayi se suka hadu suka bada wani kalar qamshin yan gayu, nan da nan na hada Dambuna sannan na dora tuwon semo da miyar Danyar kubewa taji naman rago dan Bashir yana sonsa.

Kafin Magriba munyi wanka nida yaran munyi kwalliya yanda kasan ranar sallah. Wata Atamfa na saka Batik Maroon da akayiwa dinkin A line me dogon hannu babu ado a jiki se aikin stones da aka mata se walwali takeyi na kashe daurina na baza qamshi duk inda na juya yara se sun ce "kai Mami kinyi kyau wallahi" ni kuwa se jin dadi nakeyi.

Ina tahiyar qarshe a sallah naji waya ta tana qara kafin nayi sallama ta katse. Bayan na idar na janyota dan nasan Bashir ne, ilai kuwa wani kiran nasa ya sake shigowa.

"Ranka ya dade Mijin Ma'u, ka iso nazo na bude maka qofa ne" na fada da yar dariya.
Dariyar shima yayi cikin jin dadin sunan dana kira shi yace

"Mun dawo amma ban qara so gida ba"
"Masha Allah, sannunku da dawowa, muna jiranka nida yara mun shirya maka babbar tarba".

"Dagaske, me kika tanadar mun?" Ya tambaye ni, seda na gyara zama kafin nace
"Duk abinda kake so" na bashi Amsa.

"Ke kadai nake So Ma'una" yayi maganar cikin wani salo da yayi mun dirar mikiya dan har seda naji kamar numfashina ya tsaya na dan lokaci, jikina ya karbi saqon sa dagaske, se na yi qasa da murya kamar me gudun wani yaji abinda zan fada nace

"Na tana dar maka kaina, kai kadai nake jira Farin cikin Ma'u". Na fada sannan muka kashe waya. Cike da zumudi na tashi na mayar da dankali na na sake gyara fuskata sosai na qara turare. Palour na dawo muka zauna motsi kadan mu kalli qofa kowa ya qagara Abbi ya🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na

Please Login or Register in order to submit comment