Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke kina Lagos bani da hutu kullum ku tausaya mun mana” ya fada kamar zeyi kuka.

“Uhm, shikenan bari naci abinci mayi magana” na fada na kashe wayar.
Goggo na kira, tana dagawa na saka mata kuka ina cewa
“Goggo kin gani ya saka anyi mun Transfer zuwa Abuja bayan shi yamun alqawarin ze barni a Lagos yanzu kuma yazo ya canza gaskiya ni bazan yarda ba ku kirashi kuyi masa magana”.

“Wallahi Wallahi Wallahi sau uku kenan Asma’u kika sake kirana akan wannan shirme da rashin hankalin naki sena ci ubanki. Ke se an fara miki zaton kinyi hankali se ki sake kwanto wani sabon diban Albarkar naki ko? Da dab ubanki idan yace ki zauna se ki zauna ke? Me zakiyi ashe baki cire Bashir daga ranki ba? To Shikenan ki ci gaba dayi keda Allah kiyiwa kanki sanadin da zaki mutu a banza ki tafi wuta da auran wani akan ki zuciyarki tana ga wani shashasha da be san darajar ki ba wawiya kawai” Goggo ta fada cikin bacin rai

“Ni ba haka nake nufi ba ni babu ruwana da wani Bashir kawai saboda yarana nake so na zauna a nan kum....”

“Se kinci kutumar ubaki dake da yaran Asma’u idan baki rufe mun baki ba, ai daman na fadawa Qarami wannan lambon da kikayi mu saka ido na tabbatar indai Ke din dana sani ce sekin nuna halinki, to bari kiji ni na kira Yusuf din na gaya masa yasa ki bar aikin gana daya ma amma yace Aa za dai ayi miki canjin guri dukda kun rigada kunyi yarjejeniyar zaki zauna a inda kike.

Naga alamar so kike ki mayar dashi kamar dan da kika haifa se yanda kika ce za’ayi ko to ni bazan saka ido ina kallonki kina iskancin da kika ga dama ba, ko ki tattara kibi mijinki ko ki bar aikin gaba daya kuma na rantse da Allah babu dan da zaki dauka ki riqe, ita kanta Faridar dana ce an fasa ki hadasu da Amnah zasu koma gurin qarami dan ubanki ki je kiyi zaman aure Idan kinga dama kiyi abinda ba haka ba zan tabbatar miki da shirun da nake yi bawai dan ban iya bane ko kuma kunfi qarfina nima na iya maganin ko wanne dan Banza” Goggo ta fada cikin matuqar fada da hargagin da ban taba jinta tana yi ba.

Bata barni ma na sake magana ba ta kashe wayarta, wannan abun ya sake dugunzuma mun hankali, wayar Yusuf na sake kira yana dagawa na fara magana cikin kuka ina cewa

“Yusuf me yasa munyi Alqawari zaka saba sannan kaje ka hadani da mahaifiyata tun farko ai bani na roqa ba kai da kanka kace zaka barni na zauna kusa da yarana se Yanzu dakaga na rigada nazo hannunka zaka canza magana me yasa”

A dake ya fara magana yana cewa
“Kinaji Asmy bana son ki jawo abinda ze sa mu fara samun sabani tun daga yanzu. Koma me nace miki a da yanzu Goggo ta tayar da wancan hukuncin tayi nata dan haka idan beyi miki ba kina iya zuwa ki gaya mata ni kuma duk abinda tace dashi zanyi amfani. Ki duba na tura miki da saqo saboda hidimar biki idan baze isa ba se ki gaya mun”

“Bana so me zanyi da kudinka kuma ni babu inda zanje in dai kana son auran mu sedai ka biyo ni Lagos idan ba haka ba kowa ya kama gabansa” na bashi amsa

“Tunda ke kike aurena dole na biyo ki ai, kudi kuma ki zubar idan bakya so wannan ba matsala ta bace” ya fada tareda jan tsaki ya kashe wayarsa.

Lallai ma wannan mutumin tun daga yanzu? Ashe daman duk kwantar da kan daya ringayi na qaryane se yanzu ze fara fito mun da halinsa na ainihi kenan shikenan zamu gani.

A dole badan naso ba muka tafi Gombe ranar Lahadi, Nama na kadai ya rage su taru su cinye dan tuni Goggo ta gama yayata musu na rasa yaushe ta koyi wannan halin ita kuma duk abinda nayi seta fada musu bayan tasan daman qiris suke jira dani.

Har ranar Laraba babu abinda nayi daya shafi lalle ko kitso dukda da har walima muka shirya yi ranar Alhamis tunda ran Juma’a za’a kaini can Bauchi amma da me Lallen ma tazo korar ta nayi ina ta baqin rai gashi Gogan tun ran Juma’ar nan be sake kirana ba kuma ya dawo naji labarin a bakin Jafar.

Ina kwance a dakin Hajiya Babba Sumayya babbar Yar Alawiyya ta shigo tana cemun
“Mami wai kije kinyi baqo a waje”
“Wane baqo kuma kin sanshi?” Na tambayeta ina tashi zaune, se tace mun
“Eh Baba ne”
“Baba?” Na fada da sigar tambaya.

“Baba na gidansu Baba Naziru fa” ta bani amsa.
Ikon Allah, me Baba yazo yi gidan mu a daren nan kuma? Na tambayi kaina. Hijabi na na saka har qasa na fito, a can falon baqi na tarar dasu, Baban, Bashir yasha uban baqin gilashi se Yusuf kowannen su ya kama waya yana dannanwa Baba yana binsu da kallo.

Da sallama na shiga suka dago a tare suka zuba mun ido, ina kallon yanda Yusuf ya wani harare ni ban daga ba kuwa nima na maka masa tawa se yayi murmushi ya sunkuyarda kai. Cikin girmamawa na gaida Baba nayi shiru, se kuma kamar an mun dole na hadasu su biyun nace

“Ina wunin ku” babu wanda ya amsa mun a raina nace
“Maganina kenan ai”
“Asma’u se gashi mun hadu da Ango kuma muna zuwa muka tarar dashi shima daman kuma zuwan nawa da niyyar ki kiramun shi a waya na roqi Alfarma se gashi kuma mun hadu” Baba ya fada cikin sakin fuska yaci gaba da cewa

“Masha Allah, Allah ya sada ku da dukkan Alkahirin da yake tare da junanku ya tsare ku da dukkan sharri. Ba tareda bata lokaci abinda ya kawo mu Bashir ne yace na rakoshi yana so ya sake baki haquri akan duk abubuwan da suka faru a baya, sannan mu nemi alfarma akan takunkumin da Me gida ya saka masa kodan Albarkacin yaya”

“Ni Baba babu abinda yayi mun ai kuma ko yayi na gaya masa ai na yafe masa tun tuni, in dan wannan ne ma da be taso ka a daren nan ba ai” na fada kaina a qasa.

“Kina fada ne kawai Ma’u amma nasan nayi miki laifi kuma hankali na ne ya kasa kwanciya ina so naji da kunnena kin furta kin yafe mun ko zan samu nutsuwar zuciya” Bashir ya fad yana zamowa daga kujera kamar ze durqusa.

Seda na kalli Yusuf da fuskarsa ta gama bayyana kishin da yake cinsa kafin nace
“Na yafe maka Baban Ali Nima ka Yafe mun”
“Baki mun komai ba Ma’u” ya fada da sauri

“Shikenan Allah ya yafe mana gaba daya, sannan dan Allah ga amanar yarana nan, ka kula dasu kasan bani da sama dasu a rayuwata” na fada kamar zanyi kuka, kafin yayi magana Yusuf yayi saurin cewa

“Baba wace Alfarma kace zaka tambaye ni”
Baba yayi murmushi yace
“Yaro saboda Bashir ya gaya mun ka yanke duk wata alaqa da take tsakaninsa da Asma’u koda gaisuwa baka yarda da ita ba, shine nace zan roqi alfarmar Yaran lokaci zuwa lokaci zasu ringa zuwa gurin mahaifiyarsu idan ka amince”

Seda ya shafa kansa kafin yace
“Ai wannan Baba daman dole ne, ni idan ma ze yarda ya bamu yaran se mu riqe babu komai ai Da na kowa ne”

“Bazan iya ba, na dai yarda duk hutu zasu ringa zuwa gurinta” Bashir ya fada yana kallona.

“Wanan al’amari daya faru gaba dayan mu ya isa ya zamar mana izina mu kuma qara tsorata da lamarin Allah, a duk sanda Allah ya azurtaka da samun abu kayi qoqari ka riqe shi dakyau saboda ba lallai idan ya kufce maka ka sake mayar da irinsa ba. Ina miki fatan Alkahiri Asma’u tabbas nayi baqin ciki rasa nagartacviyar suruka irinki a cikin ahalina, ina fatan kuma hakan baze sa ki yanke zumunchi dani ba kodan Arziqin abinda Allah ya rigada ya hada” Baba ya fada

Se naji Hawaye na neman zubo mun da maganar da yayi ta idan Allah ya baka abu dukda nasan da Bashir yake amma se naji kamar ni yakewa gugar zana akan matsayin da nake kai da Yusuf a yanzu. Dakyar na bude baki nace

“In sha Allahu Baba ai kai ubana ne babu yanda za’ayi nace na yanke alaqa dakai, Nagode kwarai da irin qaunar daka nuna mun na gode”.

“Allah yayi muku Albarka gaba daya, yaro kai dai ina tayaka murna Allah kuma ya baka ikon riqeta da Amana Amin” yana gama fadar haka ya shiga qoqarin tura kekensa, se Bashir ya miqe ina kallonsa ya dauke kwalla daga idonsa kafin ya mayar da baqin gilashin daya kwamo ya zura hannu a Aljihu ya zaro wata Envelope ya ajiye a gaba yana cewa

“Ina miki fatan Alkahiri” ya tura Baban suka fice, miqewa nayi tsaye ban yi aune ba se ji nayi anyi sama dani

“Ka sauke ni Yusuf”na fada a tsorace dan a bazata abin yazo mun
“Naqi na sauke ki se kin dena fushi dani” ya fada yana mun cakulkuli, duk yanda naso na daure na kasa haka na shiga kyalkyaka dariya kamar wata sabon kamu na tabbatar su Bashir sun jiyo ni dan basuyi nisa ba kuma darene ko ina yayi shiru.

“Wash Allah na matar nan fa nauyi ne dake” ya fada bayan daya direni akan qafafuna. Baki na tura gaba ina harararsa ya miqo hannu kamar ze tsokane mun ido ina ja baya ya biyo ni muka fada kan kujerar baya na ina qasa yana sama na se jinayi kawai ya kama Bakina ya shiga bani wani irin kiss me goge hadda.

Dakyar na iya kwatar kaina na rarumi hijabina da tuni Yusuf yayi fatali dashi ban jira komai ba na ranta a na kare dan naga alamar tabbas in na qara ko sakan daya za’a tafka abin kunya a gidan Jama’a.

Yusuf kuwa dafe kansa yayi ya bini da hargitsatstsuj idanunsa da suka canza kala har na fice daga dakij kafin ya janyo robar ruwan da aka kawo musu ya balle daya ya kwankwade, beji dai dai ba ya sake daukar wani ya shanye yayi cilli da robar har sannnan yana jin wani bala’in son kasancewa tareda Ita yana taso masa.

Wayarsa ya zaro daga aljihu ya shiga kiran layinta yaji qarar wayar nan qasa kusada qafarsa se ya dakkota, Envelope din da Bashirya bani ya gani a gurin ya hada ya dauka, seda ya samu ya daidaita nutsuwarsa kafin ya kama hanya yana sunkuyar da kai dan karma ya hada ido da kowa Allah ya taimake shi harya fice bega idon kunya ba bayan ya bawa daya daga cikin masu gadi wayar da envelop din yace su kai mata.

Daren ranar da ciwon Mara na kwana saboda yanda Yusuf ya yamutsani ga kayan tsumin da nake amfani dasu gaba daya suka rikitamun lissafi se gurin qarfe biyun dare na samu bacci ya dauke ni ina kallon yana ta kirana bayan da aka kawo mun wayar amma naqi daga wa qarshe qarin wata damuwar ce gara koma menene da safe ma hadu.

Washe gari tun Asuba natacciyar me Lallen da Alawiyya ta dakko tun daga Kano ta saka ni a gaba da naci dole na zauna muka fara, ta zana mun hadadden Jan lallae na qasa da qasa dan bana son na Salatif, tana gamawa kamar Aljana ta hau zana mun kitso, ko wahalar kitse doguwar Jelar gashina bataji ta kuma debeshi yiri yiri ni kaina da nake gani a mudubi seda ya burgeni.

Kusan awa biyu lallen yayi ya kama sosai kafin aka cire se mita nake dan gaba daya duwawuna ya qage da zaman shiyasa nafi gane ayi mun baqin lallae idan ma jan ne sedai da Sajam shi kuma se suce wai saurin fita yake amma ai yafi saurin kamawa.

Seda muka gama kitson tsaf mukayi sallar Azahar ta doramun da baqar fulawa sega Ma’u ta fito kamar wata fure, gyaran da fata ta ta samu da hutu ga Kitso da kalle suka sake fito da yarintata babu yanda za’ayi a nuna maka zaratan Yayana ka yarda nina haife su, a qaryar me Lallen ma cewa tayi ta zata ban taba aure ba, ta ringa rantsuwar qaryane da aka ce Jafar Dana ne wai dan ma bataga Aliyu da ya gama zangamewa ba.

Kafin La’asar gidan mu ya dinke da Jama’ar da bansan sanda aka gayyato su ba, dagaske dai yinin biki suka shirya harda masu kidan kwarya, haka nasha kwalliya da wani Arnen leshi cikin dinkunan da nayi Aljanar me Lallen da komai ta iya tayi mun make up, muka sha shagali abinka da hidimar mata zallah kowa tayi rawa ta gyagije an zubda galan galan masu kidan kwarya kuwa sun kwashi kudi dan ganin dangin Yusuf mukayi daga sama qannensa da yayyensa mata, matan yan uwansa harda matar Gwamnan Bauchi data Gombe suka hado kusan mota Goma suka zo.

Aka hadu aka yi harkar Arziqi da zasu tafi bansan daga inda Alawa ta ringa fito da kayayayki tana loda musu musu a mota ba, harka dai akayi ta ta girma da Arziqi se godiya suke haka na rungume Alawiyya dan ta fitar dani kunya ta kuma siyamun qima a idon dangin Miji, ni kuwa me zan saka wa wannan Yar uba tawa me tsananin qaunata? Da ace ko wanne Yan uwa haka suke riqe zumunchi ba tareda saka banbanci uwa a tsakani ba irin na gidan mu da duniya ta zauna lafiya🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 65


Qarfe Hudun ranar Juma'a jerin gwanon motocin da suka dakko mu daga Gombe zuwa Bauchi suka tsaya a qofar gidan Marigayi Malam Suleiman Wunti. Da Bismillah na fito daga mota ina qara gyara zaman Lafayar da na nannade Jikina da ita.

"Yah ubangiji ka saka na shiga cikin su a sa'a, Allah ka wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan aure na. In sha Allahu yanda na saka qafata a cikin gidan aure na babu abinda zan aiwatar se wanda ze saka Mijina farin ciki, na haqura na sallama komai a yabzu bani da kowa bani da komai a Duniyata se Yusuf da yake mijina" na fada a zuciyata ina bin bayan Hajiya Aisha da take riqe da da hannuna Qanwar Baffan Mace tilo a cikin su.

Ina jin yanda mata suka dauki guda ana sanar da na ciki ga Amarya ta iso a haka aka shigar dani inda nake tunanin Dakin Hajiyar su ne. Falo danqam da Mata manya masu aji qamshi kala kala na tashi.

"Sannunku da zuwa maraba lale" wata me zaqin murya take fada har muka zauna a tsakiyar falon kan wani lallausan Kilishi kaina nidai yana qasa ina ta maimaita Hasbunallahu a zuciyata.

Gaisuwa aka shigayi kamar yanda ake tsakanin dangin ko wacce Amarya dana Ango, aka gama bada Amana, ina ji aka kwalawa wata Hauwa kira akan tazo takai Amarya dakin da zata huta kafin lokacin budar kai, Budar kai fa sekace wata budurwa dan Allah. Nidai nabi su su biyu suka sakani a tsakiya har muka shiga wani daki se qamshin turare yake.

"Nidai bari naga Fuskar Matar Yaya bazan iya jira se anje budar kai ba" Hauwan ta fada tana qoqarin bude fuskata se dayar tayi saurin riqewa tana cewa
"Baki isa ba se kin biya"
"Ya haka ku meyasa bakwa girma ne se kun cire mata dankwali dallah ku matsa" wata data shigo dakin ta fada taba matsowa kusa da mu sena dago kaina na kalle su ina murmushi a tare suka hada baki suka ce

"Masha Allah wai zuqi, kai amma Yaya ya iya zabe" murmushi na sake yi musu ina kallon mutum biyun da muka shigo tare dasu kamar su daya kana ganinsu kasan Yan biyu ne irin masu tsananin kama da Juna ma.

"Sannunku" na fada ina kallonsu,
"Yawwa Amarya ke za'ayiwa sannu ai, karbi biyewa shirmen wadan nan yaran, kiyi sallah yanzu lokaci ya rigada ya tafi kuma ba'aso akai magriba ba'a gama Budar kan ba" Babbar cikin su da a qallah zamu iyayin sa'anni ta fada tana murmushi.

Ita ta nuna mun bandaki dan korar qannen nata tayi, na warware Laffayar jikina na shiga, ko ina qal na kama ruwa na dauro alwala na fito a raina ina tunanin ina su Alawa sukayi, jakata tana hannunta kuma zan dan buqaci Powder da lipstick.

Seda na idar da sallah ta sake dawowa dakin hannunta dauke da dan kit na kwalliya se Madarar kwali me sanyi ta miqo mun tana cewa

"Kisha nasan be zama lallai hidima tabarki kinci abinci ba, ni sunana Nusaiba, ni nake bin Yaya Yusuf"
"Nagode Anty Nusaiba" na fada bayan dana karba dan tunda ita take bin Yusuf ta girme ni kenan jikin ne irin namu da baya nuna tsufa.

"Aa fa karki jawo a janye mun tallafi yaji kina kirana Anty, barni dai ni nace miki Antyn, Idan kin gama ko zaki gyara fuskarki ga kayan kwalliya nan" ta fada tana dariya.

Nima dariyar nayi nace "Tam Shikenan, dan Allah akwai wata da zakiga kusan kamar mu daya ko zaki kiramun ita?"

"Ai duk wanda kuka zo kamarku daya kawai dai kin fisu kyau ne"
"Kai banda zolaya fa, toh kice Alawiyya tazo" na fada ina dariya

"Toh shikenan bari naje" ta fita bata dade ba sega Alawiyya da Zahra Aminiyata suka shigo.

"Kai amma kinyi sa'ar dangin Miji Ma'u, suna da kirki kinga yanda ake ta nan nan damu kamar wasu gwal? Allah dai yasa su dore a haka zakiji dadin su" Zahra ta fada tana zama akan gadon da nake.

"Gaskiya dai basu da matsala dukda haka dai saura ki sake musu yanda kikayi da wadancan matsiyatan banzan baya baya, babu shishshigi babu wulaqanci" Alawiyya ta fada

Su suka tayani na qara gyara fuskata Zahra ta daura mun dankwali dan gwanace. Ina cikin qara turaruka masu sanyin qamshin a jikina mukaji ana kwankwasa qofa, a zatona  Nusaiba ce dan haka muka ce a shigo se ganin Yusuf mukayi yaci wata shadda yar ubansu anyi masa irin rawanin nan na malamai harda wani kwagiri ya riqe yana dogarawa.

Rige rigen neman mayafi aka shiga yi tsakanin Alawa da Zahra abin harya bani dariya ma. "Kuyi haquri ban san kuna ciki ba" ya fada yana dauke kai, yanda kasan wani surukin su jiki na rawa suka fice suka barmu Alawa harda waiwayo wa tana qiftamun ido na maka mata harara dan na gane me take nufi.

"Amaryar Yusuf" ya fada yana qarasowa inda nake tsaye ya kamo ni jikinsa se nayi saurin cewa

"Jirana ake dan Allah karka bata mun kwalliya"
"Jiran mu ake dai, kuma kwalliyar daman wa kikayi wa ita idan ma na bata ai tawa ce" ya fada yana shinshina fuskata. Kai wannan jaraba da yawa take, buga qofar da akayi tareda turowa ta taimakamun na zille daga hannunsa wata Mata fara yar gajeriya me jiki ta shigo tana cewa

"Yanzu Excellency ka iya tsallake matan da suke falo ka shigo nan gaskiya ban sanka da rashin kunya ba, to kaje Hajiya tana kiran ka, Amarya taso muje kinji wannan Angon naki rawar kansa tafi qarfinsa".

"Allah ya taimaki Woman Leader" ya fada yana dariya, dukda haka seda yayi mun peack akan lips dina ko kunyar Woman leader data juyar da fuska tana murmushi beji ba yayi waje.


Ita ta sake dawo dani falon dazu da duk mutanen ciki sun fita se yan biyun da alama jiran mu suke, haka suka saka ni a tsakiya muka fita can wani qaton fili da yake daga gefen gidan an gyara gurin da kwalliya irin ta Kamu ga rumfuna an saka da kujeru da tebura ta ko ina yanda kasan za'ayi wani hamshaqin biki ne.

Seda suka kaini har kan wata kujera da aka tanada saboda Ni, kaina na qasa seda na zauna naji mutum ya jani a firgice na dago ashe Yusuf ne shi harya nemi guri ya zauna shi Budar kan tare za'ayi mana kenan.

Seda aka bude taro da Addu'a, manyan mata suka ringa zuwa suna mana ruwan Naira da daloli Alawiyya da Zahra na durawa a jaka yanda kasan basu san darajar kudi ba da wannan ta gama juye nata wata hajjajun zata sake zuwa ta watsa nata seda aka kwashi kusan awa daya ana wasan kudi kafin MC ta kira Qannen Ango akan suzo su bude fuskar Amarya.

"A dakata Yammata, Uwargida sarautar mata tace ita zata bude fuskar qanwarta" naji MC ta sake fada danjar yan biyun nan sun taso suka koma. Ta qasan lafaya ta nake kallon qafafunta da take hardewa tana irin tafiyar Models wato cat walk, straight gown ce a jikinta data kamata ta wani arnan leshi yanda kasan zatayi nishi rigar ta bude dan ma bata da qiba se irin mayafin Chantilly dinnan ta dora a kafada daya ta ruqo jaka a daya hannun tana taunar cingan.

"Oh waifa yanzu gidan wata nazo da ina nawa gidan a matsayin uwargida yanzu wannan figaggiyar za'a kira da uwargida na Allah kenan.

Tana isowa ta bude jakarta ta fara yi mana ruwan yan dala dari dari seda ta zazzage mana rafa biyu dala dubu biyu kenan MC kuwa se kirari take mata yanda kasan tayi tsalle ta kwashi kudin ita ko se wani yatsina take yanda kasan an mata dole.

Da hannu daya taja Lafayar dana rufe fuskata na dago na kalleta ido cikin ido a raina ina karanta 'A'uzubikalimatillahi tammat minkulli shaudanin wa hammatin wa min kullu aynin lammati' ta kalle ni na kalleta kafin ta wani tabe baki tace
"Kinyi kyau" da irin sautin da tayi magana nima na mayar mata nace
"Nagode" se jin Yusuf mukayi ya saki wata siririyar dariya muka kalleshi a tare ashe Video yake mana.

A tsakiyar mu ta zauna aka mana hoto se waniliqe masa take shi kuma yana faman rirriqeta na ja tsaki qasa qasa yo mani ina ruwana, qarewar ta ya haduye ta mana su suka sani.

Haka aka ci gaba da gudanar da shagali nidai murmushi  dole nakeyi dan idan na tuna yanda Intee ta ringa wani kwanta masa ana hoto se naji raina ya bacihar seda Yusuf ya gane ya matsa hannuna da yake cikin nasa yace

"Asmy kishi, ita bata ji haushin kin aure mata miji ba se kece kike kishi da ita" ya fada qasa qasa daidai kunnena.

Harara na maka masa nace
"Saboda bata iya riqe mijin bane shiyasa har aka iya qwace mata shi din zata wani zo tana kwanta maka a jiki se ta nunawa wanda be taba kwanciya a jikin ka ba"

"Wallai kuwa qarewarta ma yau a kan jikin zaki kwana ko?" Ya fada yana mun wannan shegiyar dariyar tasa se nayi sauri sunkuyar da kai dan se yanzu na gane baranbaramar da nayi ya ringa tsunkulina kuwa yana gaya mun maganganun da suka girmi kaina nidai haka na kanne dan kar muzo muna raba hali a gaban Jama'a.

Seda mukayi sallar Isha a gidan su Yusuf kafin muka shiga motoci muka wuce gidana duk a zatona ma anan cikin gidan nasu ne. Gida kam se dai ace Masha Allah dan fadar haduwar sa ma bata baki ne wai a haka fadi suke sema kinga na Abuja ai nan a qauye kike Aljannar duniya na Abuja.

Seda akai dagasken gaske kafin Yusuf ya haqura yabar yan uwana su kwana a gidan dan har seda wata Antyn sa Anty Mami ta kirashi a waya tayi masa tatas lokacin muna tsaye ya tsareni wai se naje nace su tafi su koma can gidan Hajiya su kwana ko subi Alawiyya ai wasu da yawa sun tafi gidan ta me yasa sauran zasu ce se sun kwana.

Haka ya kwashi fushinsa ya tafi harda ce mun kuma gurin Inter ze tafi ya kwana nace a tashi lafiya, to idan ba fitina ba kawai se nacewa mutane su tafi wani guri bayan kuma duk wanda suka zauna din yawanci yan uwan mu na Kumo dana Yola ne yan gidan mu wasu suna can gidan su Yusuf wasu sunbi Alawiyya, su cewa sukayi ma badan dare ba da tuni sun jiya abin su su kuwa wadannan yanzu ince su tafi ai an samu na yawo dani a dangi ko.

Washe gari kuwa kafin sha biyu kowa ya watse ya rage daga ni se halina a

Please Login or Register in order to submit comment