Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dawo dashi daga tunanin daya tafi, se ya dago yana gyara zamansa. Seda ya saita yanayinsa sannan ya bude qofar ya ziro dogayen qafafunsa yana sake kokawa da dacin ransa kafin ya fito gaba daya.

“Kaga Na Ma’u Angon Amirah uban Aliyu ko dubu ta taru” Bala daya gaji da jiran fitowar Bashir din ya zo ya kwankwasa masa glass ya fada cikin sigar tsokana sedai yana yin fuskar Bashir din tasa ya gintse maganar tasa.

“Lafiya kuwa Engineer kaga idanunka” Balan ya sake fada, se Bashir yaja tsakin da ya aure shi ya bude murfin motar ya koma ciki yana cewa Balan ya zagayo. Cikin zaquwa Bala ya shiga motar dason jin meya faru, dan Bala irin mutanen nan ne masu son bin kwakwkwafin duk wanda suke tare se sun san komai nasa.

Shiru sukayi na kusan minti biyar, Bala da gulma take cinsa har ya gaji ya ceda Bashir din “Engineer wai yane kodai akan climax kake ne kaima ka fara busa eh yane”

Wani mugun kallo Bashir ya jefe shi dashi kafin dakyar ya bude baki yace “Abinda banyi da quruciyata ba shi kake mun fatan yi yanzu insha Allahu har na mutu nida hayaqi sedai na murhu balle na kai ga shan wata kwaya kai dai da ka riga ka illata rayuwarka shikenan amma ka ringa tunawa Yaranka Mata ne kodan su ya kamata ka dena abinda kake yi”.

Hade rai Bala yayi dan yasan dama qarshe seya jefe shi da maganar, tun suna secondary Bala ya fara bin wasu Sa’anninasu a unguwa har suka koya masa dabi’ar shaye shaye, babu yanda basuyi dashi ba akan ya dena amma ina qarshe har yaso koyawa Sadiq da taimakon Allah da jajircewar Iyaye beyi nisa ba ya bari amma shi Bala ya rigada yayi nisa dukda abun nasa harda daurin gindi daya samu gurin Babarsa dan shi kadai ne danta Namiji.

Lokacin da aka ringa ankarar da ita akan ta ringa masa fada seta nuna an takura mata Da ba’a qaunar sa seda yayi nisan da baze ji kira ba sannan tazo tana kuka da idanunta akan dabi’ar tasa dan seda takai kayan maye har a cikin gida sha yake babu abinda baya ta’ammali dashi in banda Giya da Cocaine har kuwa ta mutu da wannan baqin cikin toh yanzu dai yayi sauqi saboda girma da iyali daya tara amma fa ko yanzu ba abin kunya bane a gurinsa ya murza wiwi yasha ko a gaban waye su kansu su Bashir dan dai babu yanda suka iyane suka ci gaba da zumunchi dashi musamman Bashir da Yake ganin Balan na bashi shawarwari daidai da ra’ayinsa.

Shiru suka sakeyi kafin can Bashir ya mula dan yana buqatar abokin tattaunawa, idan so samune Sadiq ya kamata ya gayawa dan yafi Bala hankali amma tun auransa da Amirah alaqarsu taja baya dan a lokacin gani yake Sadiq din ya goyi bayan qanwarsa dan haka ya zage ya masa rashin kyautawa shi kuma da zuciya ya fita sabgarsa sam yanzu babu wata kwakwkwarar mu’amala tsakanin su daman ga banbancin gari yanzu ga aiki yasha kan kowa.

Labarin duk abinda ya faru da hukuncin daya dauka da wanda Baba ya dauka shima ya bawa Balan, Bala dayai zuku di kamar gaske yana sauraronsa ya jinjiga kai yana cewa “kai Engineer kafa debo da zafi wallahi, nifa daman wannan Addan taku kasan yar bala’i ce tun duniya na kwance bazan manta sanda muke zuwa gidanta ba lokacin tana kiwon kajin nan in muka kwamusu daya haka zata biyo mu har layi tana sababi, amma ai ita Amiran tayi fa. Ka jure kawai tunda ka samu yarinya me kyau duk abinda ze zo ai daga baya ne”.

Baki bude Bashir yake kallonsa, wai ma wannan ya gane kan matsalar sa kuwa yake masa wannan soki burutsun koda yake shima da laifin sa wani sa’ilin ina shi ina shawara da dan wiwi? Tsaki ya buga kawai tareda yaiwa motar key yace masa “Malam sauka seda safe”

Bala ya kwashe da dariya yana cewa “ah da wuri haka kodayake gara kaje ka lallashi yar Babynka wallahi baka san wahala suke yanzu ba ko kodan kai Allah ya baka zuqa zuqa har biyu ka ajiye a gida baka san yanda kan gayu yake gwaruwa yanzu kafin su samu wadannan kalolin ba”

“Bala sauka ko na tafi da kai” ya sake fada a fusace, se Bala ya balle murfin motar ya fita yana ci gaba da yi masa dariyar qeta yace “Haba Engineer ai daman ba’a samun abu biyu ka hada kyau da zaman lafiya ai baze yuwu ba mu dai da muka auri munanan ba gashi muna qalau ba wayake jin kanmu...” fizgar motar Bashir yayi Allah yasashi ya matsa gefe ya koma majalisarsu yana ci gaba da dariya a ransa yana cewa “Ai baka ga komai ba wallahi, yanda ban samu abinda nake so ba kai ka samu, a baya dai kaji dadi amma bazaka sake samun kwanciyar hankali ba”.

Bayan Barin Bashir gurin yawo ya ci gaba dayi a mota dan baya so ya koma gida ko waccensu haushinta yake ji, seda sha biyu ta buga sannan ya kama hanyar gida bada ban ba ma Hotel zeje ya kama amma yanda duniyar nan take yanzu abu qalilan seya jefaka a masifa wani ya ganshi be san meya kaishi ba a canza masa manufa, gidan ya dawo masu gadin layinsu na zazzaune suna hira mutum biyu suka taso suka bude masa get bayan ya aje motar ya koma yayi musu dan ihi sani ya koma ciki.

A tsakiyar part biyun ya tsaya ya riqe qugu yana balla musu harara kamar masu dakin ne a gabansa, fitilun palour Amirah a kunne suke, daga inda yake yana hango cikin palour tarwai ta window saboda babu labule kamar ya share sedai tunawa da Maganar chanza key da Asma’u tayi masa ya saka shi dosar gurin dan be san ko an sace din ba da gaske.

Da key din hannunsa yayi amfani ya bude qofar tana kwance akan kujera ta duqubqune ya isa kanta ya tsaya ya, ganin yanda ta bar kwanuka ya sa ya fara kiran sunanta. Amirah kuwa Kamar a mafarki taji muryar Bashir yana kiranta, tana bude ido kuwa ta ganshi akanta ai ba shiri ta buga wani uban tsalle tayi gefe sedai kafin ta kai qasa yai azamar riqota dan shi kansa ya tsorata da yanda ta miqe din ba shiru suka zube qasa, a tare suka saki qara shi ta zafin buguwar rashin tsammani data same shi ita kuma ta azabar da taji cikinta ya dauka danji tayi kamar dinkin ze bare.

Kuka riris ta saka gana tsoron abinda ze mata gana azaba abinda ya hadu ya qara qular da Bashir qoqari yake ta tsaya tabar mutsu mutsun amma ita se qara zillewa take tana ihun yayi haquri a zatonta dukanta zeyi, ganin tana bata masa lokaci yasa ya daka mata wata uwar tsawa yana ce wa “wallahi ko ki rufe mun baki kona make ki a gurin ki tsaya mu gani ko kinjiwa kanki ciwo”.

Tsit tayi se shatato kwalla take hannu ta akan cikinta dayan kuma ta rufe baki, yanda take matsa cikin ya tabbatar masa da tana jin zafi ya saka shi cewa ta tashi ta biyo shi yayi gaba tana binsa a baya a dudduqe, seda ya kashe fitilun ya kulle qofa kafin suka shiga motarsa, wallahi badan yana tsoron kar wani abun ya sameta Allah ya kamashi ba da barinta zeyi jikinta ya gaya mata. Haka ya sake fita daya saura suka nufi Asibiti shi yana jera tsaki ita tana kuka qasa qasa.

Basu bata lokaci ba dan an tabbatar musu babu komai motsawa gurin yayi amma dai ta kiyaye irin hakan, Allurar kashe zugi suka mata kafin suka kamo hanya kamar abokanan gaba har suka zo gida yana tsayawa ta wuce sedai tuna bata da key ya sakata rakubewa tana satar kallonsa. Har ze shige part din Asma’u shima ya tuna da bata dakko key dinba dan haka ya qarasa ya bude mata qofar be amsa Nagode din da take ce masa ba ya wuce abinsa.

Kitchen ya fara tsaya wa ya dauki Yoghurt me sanyi kafin ya hau saman, beyi zaton samun Ma’u a dakin ba amma yana budewa qamshin Airfreshner dana turarukan baccinta suka masa sallama besan sanda ya fara sauke aji yar zuciya ba dan har ga Allah qanshin sun san yaya masa rai.

Akan dan teburin da yake dakin ya ajiye yoghurt din da tarkacen keys dinsa da wayoyi kafin ya cire rigar sa ya shiga toilet. Wanka yayo da alwala, bayan ya fito ya shafa mai sama sama ya zura jallabiyya Ya fesa turare lokacin har biyu ta gota kafin ya kalli Gabas ya tada sallah.

Raka’a biyu yayi a sujjadarsa ta qarshe ya dade yana yiwa Allah kirari kafin ya dora da istigfari tareda neman zabin Allah akan dukkan al’amuransa ya rufe da salatin Annabi kafin yayi tahiya ya sallame. Ya dan jima hana lazimin La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin har seda bacci ya fara fuzgarsa sannan ya tashi yana jin nutsuwa na saukar masa. Seda ya sha yoghurt din dan yunwa yake ji sannan ya kwanta ya juyawa Ma’u da bata san da dawowarsa ba baya.

A kusan tare suka farka da Asuba, ya cuna baki Gabas ta cuna Yamma kafin ya miqe tayi wuf ta shige toilet tayo fitsari tareda chanza pad ta koma ta kwanta kafin ma ya gama shirin Masallaci bacci ya sake kwasheta.

Da safe ma haka suka tashi, ya hada fuska tam yana zaune a palour yana kallon labarai ita kuma tana ta kaimawon hada masa breakfast, bayan ta gama ta masa magana daga “Toh” be sake ce mata komai ba kuma be motsa ba se itama ta share kawai dan dai fushin ai ba nata bane, idan kuma zancen komawa ne ai indai yar gaskiya za’abi batayi laifi ba. Dibar Abincinta tayi ta wuce dakinta taci, bayan ta gama ta fito sukayi kici bus ze shiga zata fito ta rabe masa ya wuce kafin ta fito.

Abincin ta fara dubawa taga yaci da yawa ma tayi dariya a fili tace “na zata shima cikin fushi kake dashi ai” ta shiga tattarewa ta sauka qasa da kayan. Tana cikin dauraye kwanukan taji motsinsa ya bude qofa, ta window ta ga fitarsa tana ganin yanda yai diri diri a tsakanin parts din me kuma ya tuna ya wuce ya kunna motarsa ya bar gidan.

Ragowan Abincin ta juye ta yafa mayafinta ta kaiwa Amirah. Tana zaune a palour tun jiyan a nan ta kwana sallah ma duk anan tayi kuma har lokacin bata kwashe kwanukan jiya ba ga plate din data sake cik tuwo bayan sun dawo shika a bushe.

Ba qaramar kunya ce ta kamata ba ganin Asma’u, duk se taji ta muzanta saboda yanda Asma’un ta sheqa wanka da wata Atamfa doguwar riga se qanshi take ita kuwa tama zaune cikin kwanuka da kayan jiya a jikinta seta hau soshe soshen tana gaida Asma’u da tayi mirsisi kamar ma bata ga komai ba.

Kayan ta dire mata tana cewa ta juye ta bata kwanukan kafin ta duqa ta kwashe na jiyan a ranta tana cewa “Na san darajarsu bari na kwashe abuna” bata ko saurari Amiran dake cewa ta barsu yanzu zata tashi ta wanke ba, ganin haka yasa ta tashi ta shiga kitchen ta juye ta daurayo kwanon da zallar ruwa ta kawo mata. Karba Ma’u tayi tana cewa “se ki nemi abinda zaki ci da rana tunda naga kin warware” tayi waje abinta.

Wannan abincin taci tayi nak sannan ta tashi ta dan tattare gurin ta shiga dakin ta tana qarewa Hadadden Gadonta da aka rushe bedside din kallo. Ita dai yan sunan nan sun cuceta wallahi dan dai bata hango ranar da Yaya ze sake mata wasu kayan ba yanzu ma ta samu ya haqura ya sakko daga fushin nan ma kafin wani zance ya biyo baya.

Wunin ranar zir Bashir a waje yayi shi, itama Ma’u bata zauna ba ta fita harhado sauran kayayyakin da take buqata da ba’a samu acan dan haka se yamma lis ta dawo bayan ta biya ta dakko yara. Koda suka dawo ma basu zauna ba kayansu suka hade tsaf dan gobe Sunday tanason suje su wanke kai da kitso Monday se Lagos.

Sanda Bashir ya dawo yaran sun kwanta Amnah ce kadai idonta biyu tana karatu dan da sun koma sati biyu zasu fara SSCE, da niyya tijara idan basu dawo ba ya shigo gidan se Allah ya ceci Ma’u tana kitchen ta jiyo Amna na gaishe shi yana tambayarta yaushe suka dawo tace dazu. Kitchen din ya leqa suna hada ido ya wani qara shan kunu tayi masa sannu da zuwa ya daga kai ya fice ya haye sama qasan ransa yaji dadin ganinta.

Seda suka zo kwanciya ta gama duk hidimominta taji muryarsa yana cewa “akwai abinda kuke buqata ne?” Seta dakata daga saka hular da takeyi ta kalle shi yana zaune a bakin gadon yanda yayi maganar yana fuskarta wani guri daban, kallo daya zaka masa kasan akwai abinda yake damunsa gaba daya yayi laushi.

Kusa dashi ta koma ta zauna, seda ta shagwabe fuska sosai ta tara kwallar qarya a idonta kafin ta riqo hannunsa, waiwayowa yayi seda ta tabbatar ta saka kwayar idon ta cikin tasa yanda baze iya kaucewa ba sannan tafara magana tana cewa

“Haba Baban Ali Haba Na Ma’u wai fushin ne haryanzu ina kake so na saka kaina naga haske bana ganin Murmushin ka? na tuba nabi Allah kayi haquri indai batun Tafiya a motane na yarda gobe muyi asubanci mu tafi idan kana tare damu nasan babu abinda ze same mu se ikon Allah”.

Duk yanda yaso ya janye ya kasa dan riqon da tayi masa da kaifin idonta yayi tasiri a jikinsa, daman dauriya ce kawai amma yana buqatar ta, yana buqatar me kwantar masa da hankali kuma Ma’u ita kadaice duk damuwar daya shiga a duniya take iya magance masa ita har in yana tare da ita tana saka shi ya manta komai sedai daga baya ya tuna shi yasa duk sanda matsala take tsakaninsa da ita yake ji kamar ya zauce dan babu me masa magani.

Fuzgota yayi jikinsa ya mata ruqo me tsauri tana jin yanda zuciyar sa take bugawa jikinsa har wani rawa rawa yake, cikin dasashshiyar murya yace “Badake bake fushi ba Ma’una, me yasa, meyasa ita bazata ji magana ta ba me yasa koda yaushe take sakani ciwon kai”.

Seda Ma’u ta murguda baki ta harareshi dukda be gani ba a zuciyar ta tace “taya zan sanin maka ba kai ka kwasowa kanka ba” a fili kuwa seta qara riqeshi cikin kwantar da murya tace “Kayi haquri” . Yanda ta fadi haqurin yasa yaji tamkar ta watsa masa ruwan sanyi a zuciyar sa, kissing goshi ta yayi kafin yace “Na haqura Yar Aljanna”.

Cikin tsananin farin ciki ta dago ta kalli kyakykywar fuskarsa tace “To Na kawo maka abinci, yau duk nasan baka ci komai ba ga fuskar ka nan ta nuna”.

“Muje ki bani” ya fada yana daga ta gaba daya, seda suka sauka har qasa sannan ya ajiyeta Amnah da ta gama hada littattafanta zata shiga daki tayi saurin saka littafin a fuska tana tafiya da baya da baya. Rankwashi ya kai mata da wasa cikin harshen turanci wanda dashi yakewa yaran magan yace “gidan ku me kike yi anan baki kwanta ba haryanzu”

Dariya tayi ta dan janye littafin tace “Abbi karatu Saura two Weeks mu fara WAEC fa”

“Ok maza je ki kwanta karki manta kiyi Addu’a” ya fada yana zama akan kujera, seta juya tana cewa “Good night Abbi”
“Good night Amna” ya fada daidai sanda Asma’u ta fito da plate din daya zubo masa dambun couscous se kunun aya a Jug.

“Good nigh Mami” Amna ta sake fada, seda Ma’u ta ajiye kayan akan centre table kafin tace “Good night Amnan Abbi”.

Dariya Bashir yayi yana cewa “fadi ki qara kam Amnan Abbi” murmushi kawai tayi, a ranta tana jin dadi yanda Bashir ya dauki qanwar tata tamkar yar da ya haifa a cikinsa dan gani take kamar yana mantawa ma ba yarsa bace, tunda riqon Amna ya dawo hannunta be taba sauya wa daga yanda ya karbi yarinyar ba ko a fuska, komai ya tashi yiwa yaran itace farko a matsayin first born dinsa. Cikin dadin rai yaci abincinsa ta tattara suka wuce Aza rum.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 23

Ranar litinin kamar yanda muka saba tunda muka yi sallah muka hau wanka da shiri dan jirgin bakwai za mubi ga tazarar zuwa Airport Akko dago Gombe. Shida bata qarasa ba muna bakin Sienna da ake kwasar mu in munzo ko zamu tafi. Yaran sun gama shiga ina tsaye daga qofar ina jiran Bashir da yake qara dudduba cikin gidan kafin ya rufe ina murmushin hirar su Naziru da Ahmad yanda yake biye masa kamar wasu Abokai.

Ba dade wa Bashir din ya fito yasha Suit kalar Dark Blue farar cikin nan har wani daukar ido haskenta yake, seda yayi Addu’a ya tofa kafin yaja qofar ya rufe se ya nufi part din Amirah yana cewa Nazirun “ka kunna motar mana ka tsaya kana surutu” ya shige nida Naziru muka rakashi da ido.

Ashe tana gidan nayi zaton tun jiya ta wuce gida yanda ta saba ana washe gari mu tafi take farayin gaba. Cikin motar nima na shiga na zauna ina duba agogon wayata ganin shidan ta yi harda minti biyar.

Bashir kuwa a daki ya tarar da Amirah hankali kwance tana baccinta, shurin qafarta yayi ta farka a firgice tana zare ido ganinsa yasa tayi saurin nutsuwa ta shiga gaishe shi. Be amsa ba ya cilla mata rafar 200 dubu Ashirin kenan yana cewa

“Zamu tafi Naziru ze kawo miki kayan Abinci, wallahi koda wasa kika saka qafarki a qofar gidan nan ki tabbata kin fita kenan mtsw” ya ja tsaki ya juya dan har yanzu bala’in haushinta yake ji gashi an hanashi hukuntata.

Harya kai qofa ta zaburo ta biyo shi da sauri dan kuma yanzu hankalin ta ya koma kan yarta, ga Nononta da suka dameta da ciwo saboda cika, saurin ce masa tayi “Dan Allah yaya zanje naga Iman” tayi maganan cikin rawar murya kaman kuwa yana jira ya jefa mata wani mugun kallo kafin yace

“Ya zama kuskure na qarshe da zakiyi tunaninyi ki sake dora hannunki a kan yarinyar nan, da kina sonta kika jawo mata ciwo sannan tunda aka fita da ita daga gidan kin tambayi yanda take bare kije ki ganta? Idan ke bakya qaunarta ni inasonta dan haka nayi miki iyaka da ita kota warke bazan dawo miki da ita ba tunda bake kadai bace zan kaiwa wadda zata kular mun da ita” yana gamawa yasa kai ya fice ya barta tana rusa kuka.

Abinda baze ma yiwu ba kenan taya ze raba ta da yarta ce masa akayi bata sonta? Ai tasan tana Asibiti kuma a kwanakin in ma tace zataje ba bari ta zeyi ba shi yasa amma wallahi bazata yarda ba dole ma ya barta ta fita kai ita bama zata iya zama a gidannan ba sedai ta tafi gidansu, ta yarda acan din bazata fita ko ina din ba amma badai a nan ba.

Tana son magana da Addah amma babu hali, ita ba waya Addah ma haka dukda da tana da wayar samun Addah bazeyi wahala ba ko a wayar Ummi ne. Tunda suka rabu a gidan Dada basu sake magana ba bata san yaya Addah ta qare a nata gidan ba tilas kuwa tana buqatar magana da ita, ya dai tafin ko Nazirun in yazo anjima ta roqeshi ya siyo mata ko Key pad ce a cikin kudin da Bashir din ya bar mata.

GIDAN ADDAH
Ranar bayan Addah ta bar gidan su Bashir Napep ta hau ya kaita gidanta. Alhaji Murtala na tsaye a qofar gidan da wasu mutane su biyu Addah ta sallami me Napep zata shige ya dakatar da ita.

“Yawwa ga Hajia Fatun ma ta dawo” ya fada yana nuna musu ita. Se Addah taci burki ta bisu da kallo daya da daya amma bata ga fuskar data sani ba dan haka se ta saka kai ciki kamar bataji maganar da Alhajin yayi ba harta tura get ya dakatar da ita dacewa

“Wallahi kika shiga gidannan se ranki yayi mummunan baci Fatu” Alhajin ya fada cikin kakkausar murya. Se Addah taja da baya jiki a sanyaye, to su waye wadannan kuma? Wane jafa’in ne ya sameta.

Takadda daya daga cikinsu ya miqo mata yana cewa “Hajia gashi sammacine daga kotu ana qararki akan laifin damfara”.

“Damfara?” Addah ta fada da qarfi tana dafe qirji tareda zaro idanu waje

“Ni Fatu wana damfara?” Ta sake tambayarsu hankalinta in yayi dubu ya tashi.

“Akwai bayanin komai a ciki idan kunje kotu zakiji cikakken bayani kafin sannan kina iya neman lauya da ze tsaya miki” dayan mutumin ya fada, sallama sukayiwa Alhaji kafin suka hau mashin din da suka zo suka bar Gurin.

Addah data gama jiqewa da zufar tashin hankali ce ta kalli Alhaji Murtala da yake jifanta da wani irin kallo data fassara dana tsana da takaici yace “Daman na fada miki Fatu tun kina dauko magana kina cin riba wata rana se kin dakko ta wanda yafi qarfin ki.

Se kije ki san yanda zaki kare kanki ko kuma ki fara shirye shiryen tafiya gidan prison tunda halinki yaja miki” yana gama fada ya shige cikin gida Addah ta rufa masa baya tana kuka kamar yarinya.

Bata tsaya ba har cikin uwar dakinsa inda ya shiga, Hajia Binta yar tsakiyarsu na cikin Toilet tana wankewa taji shigowarsu da kukan Addah seta leqo tana cewa “Aa Alhaji lafiya waye yake kuka... Au Addah kece lafiya dai waye ya mutu?”

“Kiga mutuwa akanki munafuka kuma duk sharrin da kuka kitsa masa sedai ya koma kanku” Addah ta fada cikin hargagi, dariya Hajia Binta tayi harda tafawa tana cewa “Ikon Allah se kallo, da alama dai bana an kwaso me zafi”

“Fita ki bamu wuri” Alhaji ya katseta, seta hade fuska tana cewa “kamar yaya Alhaji in baku guri bayan ni nake da aiki ko Alfarma za’a nema ai ba ta haka za a zomun ba” kafin yayi Magana Addah ta tareshi da cewa

“Alhaji muje gurina Dan girman Allah”. Shiru yayi kamar baze amsa ba se kuma ya miqe yayi waje ta bishi a baya yana jin Hajia Binta na fadar maganganun an shiga haqqinta dan ba haka taso ba, dayace ta fita zata fitan in yaso ta labe inda zata ji kan zancen tas gashi yanzu ta jashi dakinta.

Addah kuwa tiryan tiryan ta labartawa Alhajin duk abinda ya faru da basussukan jama’ar data ci da yanda sarqar Hajia me Gwal ta salwanta dama yanda suka rabu yanzu ga zancen sammaci”.

Takaici ya gama qume shi, shidai Fatu qaddarar sa ce amma ba komai lokaci yayi daya kamata yayi maganinta ko yaya me taji a jikinta amma yanzu bari a gama wannan case din tukunna.

“Wanda yaja ruwa ai shi ruwa ze doka, takaddun gidan original suna hannuna gobe se muje gidan matar aje da Dillalai suyi masa kudi a siyar a biya kowa kudinsa, Allah ya tsare gaba idan zaki gyaru” ya tashi ya fice ya barta tana ajiyar zuciya dan bata zaci abubuwan zasu zo da sauqi haka ba. Ita yanzu koma menen ai a siyar a biya wannan jarababbiyar matar, ita da tunda Allah ya halicceta ko Police station bata taba zuwa bare a ganta a gaban Alqali gara komeye a siyar a bata kudin su rabu lafiya. Da wannan ta samu sa’idah har ta iya kwantawa tayi baccin gajiyar da batayi ba.

ASMA’U
Gaba daya sukuku mukayi tafiyar babu wani kuzari har muka sauka Ikko, a Airpot din muka rabu Drivern Bashir ya kwashe mu shi kuma ya dauki Shatar Taxi ya wuce office daga nan. Yanda nayi tsammani gida na nan ya hada kari, bamu ko zauna ba na rabawa ko wa aikin da zeyi, Ahmad da Muhammad da suka fara mun rigimar wai Yunwa

Please Login or Register in order to submit comment