Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ringa bani kunya yanzu da girma na haka kawai aka zo aka shelanta nayi wani aure koma wane me shegen surutun ne oho.

Dab da zan tashi MD ya aiko kirana, da taraddadin dalilin kiran na tafi, bakinsa har kunne yake tayani murna sannan yake tambayata na rubuta takardar daukar hutu dukda naci sati biyu a cikin hutuna na wannan shekarar wai sun bani hutun wata biyu duk sanda na shirya sena fara.

Nidai haka na fito na baro shi a raina ina cewa hutum me zan dauka se kace wani auren fari dan Allah ji yanda suke ta wani digimi.

Bayan sallar magriba ina zaune sega kiran Yusuf, kamar bazan daga ba se kuma na dauka a taqaice muka gaisa ya tambayeni yara da aiki nace lafiya se ji nayi yana mun sallama wai se da safe kawai nabi waya sororo da kallo na ma rasa abin cewa.
Mutumin nan fa dagaske yake, ai kuwa mu zuba mu gani waye ze gaji da wasan.

Washe gari Alhamis da daddare ina zaune a falo badan ina gane abinda suke kallo ba se don kawai na ragewa kaina rayuwar quncin data aure ni tunda dai me afkuwa ta afku.

Aliyu ne ya shigo gidan da sallama dan tunda suka taso makaranta yana gida gurin Babansa da a bakinsu naji sunce jikinsa yayi sauqi sosai ba kamar kwana biyun ba, zama yayi kusa dani ya gaishe ni se yake gaya mun wai Abbin su yace ya tambayeni zasu zauna a gidan na sati daya ze tafi Gombe, wani iri naji, dagaske har Bashir ya sare da wurwuri haka koda yake me nake so to yayi? Ci gaba da kulani zeyi ya take dokar Allah ga wannan Yusuf din shima da ba gama sanin zuciyar sa mukayi ba ban sanme ze iya aikata wa ba dan haka nace masa ya gaya masa babu matsala Allah ya kaisu lafiya.

Bluetooth ya ciro daga aljihunsa ya saka a kunne yayi yan danne dannensa a waya can se ji nayi yace

“Mami, Abbi yace in roqa masa ke ki yafe masa, Uncle Yusuf yayi muku iyaka badan haka ba da kansa ze zo ya baki haquri ya nemi yafiyarki” Aliyu ya qarasa a hankali, ba tareda na kalle shi ba nace

“Ka gayawa Abbin ku na yafe masa ni daman be yi mun komai ba duk abinda ya faru qaddara ce da bamu isa mu kauce mata ba”.

“Mami yace na gaya miki wallahi yana sonki, kuka be taba yi miki wani abu saboda ya wulaqanta ki ko kuma dan baya sonki ba, rashin sanin yanda ze bayyana abinda yake zuciyarsa ne yasa ya ringayin duk abubuwan da suka faru” Aliyun ya sake fada kansa a qasa ba tareda ya kalleni ba.

sena kama hannunsa ina murmushin qarfin hali nace
“Nagode, kace ina masa fatan Alkahiri ina kuma yi masa Addu’ar Allah ya bashi wadda ta fini”.

“Amin, seda safe bari naje na hada masa kayan da ze tafi dasu toh saboda hannunsa” ya fada yana miqewa. Kamar nace masa ina matarsa da bazata hada masa kayan ba amma se naga ina ruwana ma. Alhamdulillah, ko babu komai yanzu rabin hankali na ya kwanta, Bashir ya dawo cikin nutsuwarsa, Aliyu ya dangana ya dauki girman da yake akan sa nasan in Allah ya yarda ko bana tare dasu Yarana bazasu shiga damuwar da nake hasashe ba.

BAYAN WATA UKU🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 64

BAYAN WATA UKU

“Wallahi nagaji, ka gayamun kawai SH idan so kake na mutu kawai ka huta amma wannan jan ran ya isa” na fada dakyar saboda yanda nake jina kamar wadda take yawo a gajimare.

“Ki mutu fa kika ce ni kuma in zauna dawa?” Ya fada da saurin sa,

“Ka zauna da baqin halin ka irin na yan Bauchi mana ai naga alamar abinda kake jira kenan safiya tayi ace maka Asma’u ta mutu”

Wata muguwar dariya ya sheqe da ita dukda nasan shi kansa qarfin hali kawai yake dakiyar zuciya ce kawai irin ta yan maza amma nasan ya fini a zabtuwa da kewa yace

“Da wuri haka haba Asmy karki bawa mata kunya mana, wata uku fa kacal kike cewa kin gaji dame kika gaji toh?” Ya yi tambayar cikin sigar zolaya yana dage mun gira daya.

Baki na zumbura gaba kamar yarinya na kwabe fuska ina harar screen din wayar nace
“Wallahi nasan Asiri kawai kayi mun amma ta yaya yaushe ma ni na fara sonka haka da har nake jin kamar zan zauce saboda ban ganka ba”

Wannan karon ina kallonsa tsabar dariya seda ya fado daga kan kujerar da yake zaune wayar ta kife a qasa, iya quluwa na qulu banyi aune ba sejin hawaye kawai nayi suna diga daga idona dan wallahi kamar wadda aka kunnawa wuta a zuciya haka nakeyin wani irin so da kewar Yusuf suna qonani. Idan za’a saka mun bindiga bazance ga sanda hakan ya fara ba abu daya kawai dana sani A cikin watanni ukun nan Yusuf yayi nasarar yin rugu rugu daduk wani qashi da tsoka da suke a cikin jikina.

“Haba mana Asmy kuka kuma ki bari dan Allah bana so” ya fada a rikice kamar ze fito daga cikin wayar. Sena qarawa kukan shagwabar tawa qaimi ina cewa

“To ba kaine ba saboda kaga na damu dakai shine na zama abin tsokanar ka kake mun dariya, ai Allah yana kallonka wallahi kuma nima duk ranar muka hadu sena rama duk irin abinda kayi mun”.

“Me zaki rama bayan duk wanda kikayi mun Asmy, wata na uku ba da zama ango amma nida qaton gwauro bamu da maraba saboda tsabar mugunta fa korata kikayi kika ce karba sake zuwa inda kike ya kike so nayi? Ina son ki da yawan da zan iya miki duk abinda kike so koda ace ni bazan ji dadi ba indai ke zakiyi farin ciki burina ya cika” ya fada cikin sanyi da taushin muryar da ya yaqi duk wani burnishin taurin kai daya rage mun”

“Nace kayi haquri lokacin ina cikin jin haushin an mun auran dole ne kamar wata wadda ba’a so daga zuwa tambaya kawai aka daura mun aure” na fada cikin shagwaba yanda kasan wata Sweet sixteen, koda yake idan ina tareda Yusuf, yanda yake shagwabani yana riritani jina nake kamar jaririyar da aka haifa yanzu baje kolina nake ina barje shagwaba yanda raina yake so.

“Ni daman baki mun laifi ba, kuma haryanzu kece baki so dana zo inda kike ba tunda baki bani dama ba”

“Ni wallahi naqi jinin wannan halin ayiwa mutum abu yace ba’a masa ba amma kuma yabi ta qarqashin qasa yayiya gallazawa mutane, indai da gaske banyi maka laifi ba ko ka haqura kusan wata yara kenan fa ina baka haqurin nan amma kaqi kazo kullum kuma kace kai banyi maka komai ba” na fada cikin shashsheqa kamar wadda take kukan gaske.

Seda ya dauke wuta na dan lokacin, yana yin kallon da yakeyi mun kansa ya canza kafin qasa qasa yace mun

“Ki bari karki jawo mun kuma ki rasa yanda zakiyi dani, kuma yaushe kikayi wata goma kina bani haquri banda qarya fa Asmy”

“Mugu aini ka iya saka ni a ukun ka barni da jiyi akan gado ai” na ayyana a zuciyata a fili kuwa nace

“Toh ai ni duk wata daya ba tareda kai ba a matsayin wata uku yake, kasan kuwa yanda nake rayuwa a nan? Ikon Allah ne kawai yake riqe dani amma qila da tuni an dade dayinsadakar arba’in dina”

“Asmyyyyy” yaja sunan seda tsigar jikina gaba daya suka miqe kafin yaci gaba da cewa
“Asmy baki so ki ganni ba, kawai fada kike amma ba dagaske kike ba”

Haka kawai naji hawayen gaske suna neman balle mun wai wannan mutumin me yake so nayi masa da ze tabbatar da ina son sa ina son ganinsa? Tun fa waccen ranar daya tafi be sake dawowa ba. Sedai ya kirani a waya yayita zalintata yana kassaramun zuciya sannan yanzu yace mun wani wai fada kawai nake bana son na ganshi bayan badan kar nayi abin kunya ba da tuni ni na bishi duk inda yake.

“Kinga, daga nan ina ga China kawai zan wuce akwai kayan da nayi order zasu taso zan je na dubasu tunda idan na dawo Nigeria ma bani da abinda zanyi, kai Allah ka bani me sona na qara aure kawai na huta da wannan shakulatun bangaron da ake mun ta ko ina” ya fada yana wani shan kunu kamar gaske.

A harzuqe nace “daga can ka wuce bangon duniya ma kawai karka dawo dan ma kaga ana sonka an damu dakai shine zaka ringa yiwa mutane haka, ka tafi din kaida Allah tunda dai kasan ina da haqqi akan ka kuma se naga dama zan yafe”.

Dage kafadu biyu yayi yace
“Toh ai gara na tafi sabgar neman kudina da in zauna ana garani kamar kwallo, kuma da kike maganar haqqi Asmy kefa kika koreni kikace karna sake zuwar miki gida, to tunda bani na siya miki ba kinga dole na kama mutunchi na ai ko”

“Yusuf dan girman Allah kayi haquri wallahi kuskuren harshe ne nayi a lokacin ba abinda nake nufi ba kenan” na fada ina fashewa da kuka, seda yayi qoqari gurin danne dariyar sa kafin yace

“Na haqura, dan Allah ki dena kuka ke se ana maganr wasa kawai ki ringa kuka ki dena mana”

“Toh ni ya kake so nayi? Na baka haquri kaceka haqura amma banga Alama ba. Wallahi dagaske Yusuf INA SONKA, I love you more than anything you could imagine in this world ya kake so nayi da zan tabbatar maka ina sonka?”

“Na yarda Asmy base kin rantse mun ba”
“To kazo” na fada kawai dan na rasa me kuma zan sake ce masa

“Ki tsammaci zuwana a koda yaushe Asmy tunda kin gayyace ni da kanki” ya fada cikin wani irin farin dana kasa tantance dalilinsa.

“Kullum roqona kike kawai nayi haquri baki taba buda baki da kanki kince nazo ba, daman na gaya miki, bazaki sake gani na ba sedai in har ke da kanki kika gayyato ni” ya sake fada.

“Yanzu daman tuntuni kawai abinda kake jira na fada kenan? Duk magiyar dana ringa maka ba abinda nake nufi ba kenan?” Na fada

“Baki fito kince Yusuf kazo ba, amma Yanzu da kika fada zaki ganni, kuma duk ranar dana zo ranar zaki tare ki tabbata Ango nake babu maganar daga qafa sena kwashe gara yanda....”

“Kai dai baka da kunya wallahi” nayi saurin katse shi jin yana neman ya saki layi kuma.

“Ai bazaki tabbatar da bani da kunya ba se rabda kika zo hannuna Asmy, kedai ki shirya mun ki kuma nemi Tissue dozen dozen saboda wannan kukan sangarta da shagwabar da kike yi ina tabbatar miki ranar zakiyi me dalili”.

“Seda safe, na fada ina rufe fuska ta da Pillow”
“Kiyi bacci cikin Amince Wife, I love you”
“Love you more” na fada tare da aika masa da Kiss me qara irin me tara tsigar jikin nan kafin nayi saurin yanke wayar.

Ina kallo ya sake kira amma naqi dagawa daga qarshe ya rubuto saqon yana cewa
“Kinci Bashi Asmy ki shirya biyan sa”

Dariya nayi bayan dana karanta nayi juyi ina sake ruqunqume pillow da yake jikina. Idan aka ce mun a rayuwata zan sake son wani Namiji bayan Bashir tabbas zance qaryane amma se gashi cikin dan taqin lokaci komai ya canza.

Wata irin sanyayyar soyaya ya ringa gwada mun da ban ankare ba seda na kai tsakiya ruwa yasha kaina kafin na fahimci na kusa nitsewa a cikin kogon sonsa. Zuwa yanzu nayi amanna da Yusuf shine cikon rayuwata, duk wani mafarki da burina na gudanarda rayuwar aure me cike da farin ciki da walwala ina hasko ta a tareda Yusuf fatana ya kasance har gidan auran mu, wannan qaunar dana ke gani a gurin sa ta zamo ta gaskiya har qarshen rayuwar mu dan na tabbatar idan har na samu akasin haka daga gurin Yusuf, a irin yanda ya rigada ya gama illata zuciyata tabbas bazan sake moruwa ba.

Washe gari ta kama Asabar babu aiki, tun sassafe nake aikin mulke mulken Dilka da kurkum da Anty ta hadamun nakeyinsa sau uku a sati, cikin abinda befi wata daya da farawata ba ni da kaina idan ina zuba ruwa a jikina bana so na dena saboda yanda fatata take wani sulbi da sheqi kamar jikin tarwada.
Inagamawa nayi wanka na zura doguwar riga harda safa na tafi gidan Anty na dubata bata da lafiya.

Allah me yanda yaso bayan tsahon shekaru da suka kwashe suna neman haihuwa se gashi Allah ya kawo musu dukka su su biyun a lokacin da basuyi tsammani ba daga ita har Abokiyar zamanta suka samu ciki bayan da suka gwada wani maganin sanyi da ANTY ZEE MAMAN MUJAHID take siyarwa.

Tabbas na yaba da kyan maganin ni kaina saboda daga sanda na fara shansa Al’adar da nayi ta farko nasha mamakin abubuwan daya wanko mun dan seda nayi zato ko har sannan akwai ragowar barin da nayi da be gama fita ba tunda ba’ayi mun wankin ciki ba seda na kirata take gaya mun babu komai datti ne kawai banyarda ba seda naje Asibiti suka sake tabbatar mun da mataccen jini ne ya fita babu wata matsala.
Tabbas magani yayi ina kuma ina shawartar duk wata me matsalar sanyi ko abinda ya shafi Al’ada ta gwada, masu matsalar haihuwa kuma ba’a barku a abaya ba, shi magani dace ne idan Allah ya amince se a samu.(Ga masu buqata suna iya tuntubar Anty Zee Maman Mujahid akan 08162859027 Allah yasa a dace).

Ina shiga ta fara dibana wai Amarya.
“Kinga yanda kike wani sheqi da walwali kuwa Ma’u, ki daga qafa haka dan Allah karki saka Bawan Allah ya zauce fa idan ya ganki” dariya na sheqe da ita bayan da na zauna ina cewa

“Kai Anty kin fiya zolaya wallahi, ya jikin na ganki ma da sauqi ba kamar jiya ba”.

“Kinsan abin seda haka se kanayi kana dan qara wa abun gishiri bakiga yanda Yallabai duk yabi ya kidime ba har tausayi yake dan bani wallahi amma gara ya gane ba’a samun Da da sauqi ai” ta fada tana murmushi

“Kai Anty kema fa kin iya mugunta, karna manta ina wannan dakan na gama da wadancan duka” na fada dan karna tuna abinda ya kaini.

“Kai Ma’u, kai Ma’u nidai babu ruwana wallahi karkije ki kashe musu Da ana zaune qalau tam”

“Anty gara ka kankaro mutunchi baka san ya matarsa take ba kinsan dai halin mazan nan namu” na fada ina duba wayata da naji saqo ya shigo,
“Ki duba whatsapp dinki na tura miki saqo” na gani daga Yusuf.

“Banga laifinki ba qanwata gara ka kankarowa kanka mutunchi wadannan mazan zamanin masu ido a tsakiyar kai. Jira nake kawai ku tsaida ranar tariya ai sannan ne zamu fara shiri na gaske, badai mace a gaban ki ba wallahi sedai su biyo baya” hannu ta bani muka tafa ina cewa “se Anty na”.

Whatsapp na shiga ina bude chat dinsa naga wata yar banzar sticker daya turomun ni kunya ma ya bani har seda na rufe ido na, Wani Pdf document na gani na bude, catalog ne na wani Kamfanin siyar da kayan daki na qasar Turkey sena danna masa Audio call ya katse ya turo mun da cewar na masa chat.

“Wannan fa na menene?” Nayi tagging document din.

“Ki duba ki zaba, Four bedroom duplex ne da falo biyu, ragowan abubuwan dole se kinje kinga gurin, ki tayani zabar Gadaje guda biyu nawa da Set din kujera, bana son Royal” ya maido mun da amsa. Sena bude kayan na fara dubawa.

Ajiye wayar nayi a gefe dan ban gane abinda yake nufi ba, siya mun zeyi ko kuwa yana gaya mun irin kayan da yake so a saka masa a gidan sa ne tunda naga yanzu saboda rashin kunya irin ta maza qiri qiri suke fadar irin gadon da suke so ko siya musu.

Na dan jima muna hira da Anty kafin nayi mata sallama na tafi bayan ta bani Dakan da naje karba da wata zuma data ce na ajiye amfaninta ba yanzu ba wai ita Scorpion. Ina fitowa daga gidan muka yi kicibus da Bashir ya fito daga gidansa, Kallo daya yayi mun yayi qasa da kansa harga Allah seda naji wani iri, murmushi na qirqiro harya gota ni nace masa

“Baban Ali barka da rana?”
“Barka dai Ma’u ya gida ya aiki?” Ya bani amsa kamar yana jira na gaishe shi. Se na amsa masa da lafiya kafin naci gaba da tafiyata a jikina ina jin yanda ya bini da kallo har na shige gida na kullo qofa, Allah kenan meyin yanda yaso a sanda yaso.

BASHIR

A cikin watanni ukun nan ya samu canji sosai a rayuwarsa dujda seda yayi da gakse gurin jinyar zuciyarsa kafin komai ya daidaitar masa sakamakon Addu’a da irin nasiha da a kullum Ahajinsu yake kan yi masa akan muhimmancin yarda da qaddara musamman irin tasa da shine silar komai.

Kusan duk wani abu na yaransa ya dawo hannunsa yanzu a gidan suke komai, tsakaninau da gidan Ma’u sedai suje suyi wasan su dare yana yi Aliyu ze hado kansu su dawo.

Zaman sa da Amirah dai ba dadi babu wuya akace lahirar kare, bayan zaman wata daya da ya barta tayi a Gombe ta dawo dole ya kafa mata sharuddan da in har tana son zaman lafiya dashi dole ta bi to anyi dace ta dauka musamman saboda a Gomben ma da sukaje kwananta daya a gidan Dada babanta ya samu labari yace ta tafi gidan su can tayi zaman jegon dan baze sake sakin wani abu daya shafi Yayan sa a hannun Fattu ba.

Zaman da tayi da matan Baban nata sam ba me dadi bane dukda ita ta quntata kanta dan a gurinsu su basu da wata matslaa sam. da fari ta farayi musu rashin kunyar da suka saba sanda Addah tana nan suka taka mata birki se duk tabi ta tsangwami kanta bata sakewa da kowa haka duka tayi zaman ba dadi gashi babu inda take zuwa babu kuma me zuwa gurinta, Anty Binta Amaryar Alhajinsu ce ta dauki ragamar gyarata dayi mata wanka har na wata dayan kafin babu Arziqi ta tattara ta koma Lagos bayan dogayen sharuddan da Bashir ya gindaya mata akan zamansu dan ko Addah da take gidan Anty Talatu ana ta dibar tsiya bata san da komawarta ba se bayan ta tafi dan duk a shirinta tare zasu koma ai kuwa tasha zagi ta kuma tabbatar mata tana tafe dan ma yanzu tana shirye shiryen yin auran kisan wuta ne kamar yanda wani sabon Malami da Tatu ta kaita wajen sa ya gaya mata tayi kafin a gama aikin da zaa karkato da hankalin Alhaji Murtala kanta ta koma dakinta.

Tasha matuqar wahala sosai da irin sabon salon zaman nasu dan yanzu duk wani abu da cikakkiyar matar aure zatayi a gidan ta shi takeyi, girki sau ukun nan seta dora kuma ba irin na ganin dama da takeyi a da ba, shiyake gaya mata abinda yake so ayi ko yaran daya fuskanci bata iya wasu abubuwan bama makarantar koyon girki ya kaita, gyaran gida kuwa haka take wuni ta dauke wannan ta gyara wannan a haka ma dan yaran sam ba masu bata guri bane.

Badan ma ta kasa sakin zuciyarta ta jasu a jiki ba da ko su sun isa su ringa taya ta aikin gidan idan suna nan tunda duk abinda suka saba yiwa uwar su ne. Sauqin ta daya Bashir ya rage wannan fada da hargagin da yake mata da tayi kuskure ada, dukda yanzu shiru shirun sa ya dada qaruwa ne ko da yaushe ya zauna shi kadai zaka lura yayi zurfi a cikin tunanin amma ko laifi tayi masa cikin lumana yake fahimtar da ita kuma babu laifi a yanzu yana kyautata mata daidai da yanda itama take kyautata masa shida Yaran data fuskanci yanzu sune komai nasa dan yawan ci idan suka samu sabani to akan abinda ya shafi yara ne.

ASMA’U

Sati daya tsakani Yusuf ya gaya sanar mun a ko wanne lokaci yana iya dawowa sannan kafin lokacin yana so aje a duba gida dukda har sannan ban rigada na zabi kayan dayace shi ze siya ba, ina jira zanje Gombe na zauna da yan uwana naji shawararsu akan na barshi ya siya din ko mu zamu siya da kanmu.

Daya matsamun akan zancen aje a ga gida Anty Ladi na kira na gaya mata suka hadu ita da Junaidiyya da Anty Nasiban Yaya Abubakar se Zahra suka je ganin gidan. Na Bauchi kuma daga Gombe su Yah Fati suka tafi suka hade da Hajia Alawa qirjin biki suka gano gidan.

Wayyo Allah ranar kam nasha surutu harna gode Allah na santin gidan da suka ringayi ga Videos da suka dauko suka ringa turawa dangi.

A bakin su Anty Ladi nake jin gida daya zamu zauna tareda matarsa a Abujan dan na Bauchi kowa da gidanta na sani amma a Abujan bangaren kowacce daban dan a cewarsu ma tazarar dake tsakani ta isa a gina wani gidan a gurin filin wasanni ne ne da Garden harda swimming pool yayi a tsakiya se a bangaren ko wacce mace yanada dakuna biyu da palour banda wani qaramin flat da yayi a farkon gidan inda ze ringa sauke Jama’ar su yan siyasa se kuma Boys quarters a bayan gida.

Wannna zuwa ganin gida da akayi ya taso da guguwar zancen tariya kuma dan daman sunce duk ido kawai suka saka mun, yanda kasan auran budurwa haka yan uwana suka hau shirye shirye, Yusuf ya kafe akan zuba mun kaya a gidansa na Abuja kamar yanda ya rigada ya sakawa Intee haka kuwa akayi, kamfani sukaje suka tsara yan uwana kuma suka shirya mun na Baushi dan kwandala ta bata shiga ciki ba gudummawarsu suka hada data abokanan arziqi suka mun kaya na yar gata har kuka seda nayi da naga Video gidan bansan da me zan saka musu da irin qaunar da suke nuna mun ba sedai Muyi Addu’ar Allah yaci gaba da hada kanmu har mutuwa.

Dagaske dai Yusuf yaqi dawowa Nigeria har aka tsayar da ranar tariyata sati biyu masu zuwa ya kuma qi bari muyi magana balle na tuntube shi naji makomar aiki na ko kuwa dai an zuba kaya ne kawai a Bauchi da Abuja saboda idan zuwa ya kama mu.

Ranar Juma’ar daya rage saura sati daya tariyata kuma a ranar nake son daukar hutu tunda zamu tafi Gombe gaba daya zuwa Lititin dan yara sunyi hutun Aliyu ne kawai zamu bari saboda ze rubuta Jamb.

Bayan dana karbi takardar hutuna da suka bani har wata uku aka sake qaramun da wata da ban san kota mecece ba. Da wuri nayi sallama da abokanan aikina na kama hanyar gida dan ina so na tsaya na bada wasu kaya a Tasha da za’ayi mun gaba dasu.

Se yamma na shiga gida, ina cin abinci muna waya da Yusuf, ni yanzu na haqura da tambayar sa yaushe ze dawo ma tunda abin nasa ya zama wulaqanci, zancen hutun da aka bani daya mun dazu yasa takardar da aka bani ta fado mun a rai. Farida nacewa ta dakko mun su a cikin jakata, ina budewa na zaro ido ganin takarar transfer ce zuwa Headquarter mu ta Lagos harda qarin girma.

“Yusuf kai ne ko?” Na fada kamar zanyi kuka.
“Oh ni dai naga takaina me kuma nayi Asmy duk wani laifi ace nine, nine me?” Ya fada

“Transfer akayi mun zuwa Abuja nasan wallahi kaine bayan ba haka mukayi da kai ba kai kace zaka barni na zauna a Lagos”

“Ni babu ruwana su sukace miki da saka hannuna a ciki? Qila sun duba miki ne inda mijinki yake amma ni babu ruwana a ciki” ya fada yana yar dariya.

Duk se naji raina ya baci, yanzu kenan dagaske zan bar yarana na tafi wata rayuwa daban ba tare da su ba? Me yasa tun farko yayi mun qarya yace ze barni na zauna tare dasu

“Kinyi shiru Asmy, dagaske nake miki bani na saka ba amma idan kina so se na je na nemi alfarma idan ze yuwu su barki a inda kike, amma bakya ganin hakan da sukayi kamar yafi hankali na ze rabu da yawa ni Ina Abuja Intee tana US

Please Login or Register in order to submit comment