Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take kallonta fuskata a hade ba tareda nayi magana ba.

“Ina wuni Anty” ta fada tana wata dariya kamar kwarkwar, seda sake tsuke fuksa kafin na amsa da “Lafiya” a taqaice.

“Tun jiya naso na shigo wallahi na gaishe ki kuma se gajiyar hanya ta hanani ga gidan nazo na tarar dashi duk ba a kintse ba shine fa nayi yan gyare gyare har yau da safe, yanzu ma fita zamuyi wai twins ne suke son Ice cream zamu je a siyo Ina Farida da Amna ban gansu ba su” Amirah ta sake fada tana bin lungu da saqon palour da kallo duk ina ankare da ita, zanyi magana Farida ta fito daga dakinsu, kallo daya kuwa tayi mata ta zumburi baki ta juya ciki ma ta fasa fitowar ita kuwa Amirah se wani murmushi takeyi na ala dole ita ta iya bariki.

Jin bata sake cewa komai ba yasa nace mata
“Zaki iya tafiya tunda mun gaisa ko, amma mu nan bamu saba da shige shigen maqota ba. Kowacce mace a gidanta take zama dan haka karki sake shigowa mana mun gode” nayi maganar raina a sake kai ba kace mun hada wani abu nida ita ba.

Na sani gulma da munafunci ne ya shigo da ita dan ta nuna mun tazo, sannan taga yaya na zama tunda Autan Maza ya sake ni ko? To gani dai garas a cikin hayyacina, sema fari da kyau danayi saboda ni idan na rame ido na da hanci qara fitowa sukeyi ga kuma hutun dana samu kusan kwana nawa ina zaune a cikin Ac sannan da wani hadin ridi da Madara da Anty takeyi mun duk yamushewar da nayi a kwanaki biyun nan na warware fatata ta nuna jin dadi.

“Uhm toh shikenan bari naje nasan Yaya yana ta jira, se mun dawo” ta fada tana miqewa, har ta kusa fita ta waiwayo tace
“Anty gurin nan yayi kyau har yafi can gidan ma wallahi”.

“Allah ko, se ki gayawa Bashir ya zuba miki irin kayan idan kuma nan din kike so se mu baki” na fada ba tareda na daga kai na kalleta ba, itama bata ja maganar ba ta fice tareda ja mana qofa.

Naga qoqarin ya kwarai da tsantsar rashin kunya da har ta iya dakko qafa ta shigo mun gida ko kuwa tana nufin tace mun bata san bana tareda Bashir bane, koma dai yaya yau daya dai na danne zuciyata duk irin abinda ta ringa ayyano mun da nayi mata na daure amma tabbas duk randa ta sake gigin shigowa ban san abinda zanyi mata ba, su kuma dan uban su zasu dawo su tarar dani se sun gaya mun me suka rasa a gurina da suka tafi yawon roqo gurin Bashir.

AMIRAH
Ganin da tayiwa Asma’u lokacin data fito daga gidan Anty sam be gamsheta ba. Bata zata cewa a dan tsakanin abinda be ko kai sati daya ba Ma’un zata iya dangana da abinda ya sameta har ta ganta tana yawo akan qafafun ta kamar babu abinda ya faru.
Mantuwa Bashir yace yayi ya koma cikin gida, yana shiga itama tayi saurin fita daga motar tabi bayan Ma’u.

Ba qaramin girgiza tayi da ganin tsaruwar sabon gidan Ma’un ba tunda dai tasan babu silan Bashir a ciki wato ita wata sabuwar duniya ma ta bude ta qawata gida kamar ba wadda aka saka ba tana walwalarta, ta kuma yi zaton ganinta ze batawa Ma’u rai har tayi fada ko wani abu daga nan ta samu damar da zata sake qunsa mata takaici dan sosai su Addah da Sa’adah sukayi mata hudubobin tsiya tunda suka ji Ma’u tana kusa da gidan.

Sun karanta mata yanda duk zatayi ta uzzura mata ta yanda ita da kanta zata bar kusada Bashir idan taga bazata iya daukar abubuwan da Amiran take yi mata ba amma se gashi ko a kwalar rigarta bata ga alamar ganin ta ya daga mata hankali ba, kai ita se take ganin kamar ma qarya ne babu wani sakin ta da yayi dan daga ita har shi din bata tsammaci ganinsu a hayyacin su ba har gara Bashir ya rame amma Ma’u fa kyau ma taga ta qara abunta.

Haka ta ringa cizon yatsa a mota ga Bala’in da yakeyi mata akan wane dalili ta shiga gidan, ta qudurce a ranta tabbas seta gallabi Ma’u ta bar unguwar nan dan bazata juri haduwarsu da Bashir kullum ba sannan ga wadannan mayun yaran da tun zuwan ta jiya suke zurubtu a gidan, gara suyi can nesa dan in ba haka ba ze zamana an kashe miji ne ba’a sare kansa ba.

Fitar da tayi niyyar warwasawa yau itama gata a gaban motar Bashir a Lagos sun fita shan Ice cream qarshe haka suka dawo kowa yana hada rai yaran ne kadai suke ta jin dadinsu shi kuma ya biye musu har wadanda ba’aje dasu ba seda akayiwo wa tsaraba.

Da suka dawo gidan ma kayan sa yace ta shiga ta gyara masa sukuma suka baje a palour da yaransa suna ciye ciye da buga game baqin ciki kamar ta fashe daga zuwa rana daya za’a fara haka lallai dole a sake sabon lale.

Wayar ta ta dauka ta shiga kiran Sa’adah tunda itace malamar tata, bugu biyu ta daga tana tsokanarta da cewa

“Uwargida Amaryar Engineer, ashe kin kunna waya ai bari nayi ku gurji Amarci kwana biyu tunda an dade ba’a hadu ba daga baya se musha labari”

“Wayake ta zancen wani Amarci yanzu Anty Sa’adah” Amirah ta fada tana jan tsaki, daga dayan bangaren Sa’adah tace

“Bangane me kike nufi ba, kardai ki cemun period din dawowa yayi bana ce miki kisha pills ba ze dauke ko baki sha ba”.

“Duk fa ba wannan bane yanzu, ni kin ganni tunda nazo jiya ma nake aiki kamar jaka. Gida kaca kaca ga gyaran dakina tsabar wulaqanci masu saka gadon a ciki suka bar kwalaye da sauran tarkace, haka ya tasani a daren sena gyara, dan ma na taho da Miya kin gani sefa da na dafa mana taliya mukaci, ga shegun Yayansa sunzo sun tasa mutane a gaba saboda haushi ma nayi bacci na barsu ban san lokacin da suka tafi ba.

To kin ganni yanzu ma dai na taqaita miki tun safe aikin nake, harfa fita mukayi wai ze siyowa Yaran Abu gasu can mun dawo suna palour ni kuma ya saka ni ninkin kaya” ta qarasa maganar cikin tsantsar takaici, badan hudubar da aka mata akan ta kwantar da kai ba da wallahi tun a yau gayyayar zata watse dan ita fa ba aikatau tazo yi ba, zuwa tayi ta mori miji taji dadi a toh.

Dariya Sa’adah ta ringa sheqa mata abinda ya sake qular da Amirah kenan tace

“Wannan ai wulaqanci ne, na gaya miki matsalata kuma kin mayar dani abin dariya shikenan, bari na kashe wayata, barima kiga na gaya masa nifa bazan yi ba dan na gaji wallahi sekace jaka”.

Seda Sa’adah ta tsagaita da dariyar kafin tace “toh ai Amirah dole nayi dariya, nifa bari kiji wallahi na dade banga sakaryar mace irin ki ba amma fa kiyi haquri.

Ce miki akayi a banza kake mallake mijin daman ai se kin zama jakar, a gabansa ki zama kamar baiwa se yanda yayi dake ko takaki yayi kar kice komai shine zaku zauna shiru bame jin kanku ki zama ta gaban goshi yanda ko wani ne ya kawo aibun ki ze tare miki kuma ki more shi yanda kike so tunda yana juya ki shima, ko bakiga ni har wanki nakeyiwa Yallabai ba, idan kuwa ina gabansa biyayya ko ubana Albarka”

“Tab wallahi bazata sabuba kuwa dan ni bazan iya ba. Haka kawai sena zauna kenan na zuba ido se yanda akayi dani ai kuwa bazan iya ba ni indai wannan shine dabarar gara ma nabi ta Addahn kenan a nemi inda za’a kaishi a mallake mun shi ta qarfi amma indai se na zamar masa jaka babu ni a wannan tsarin” Amirah ta fada.

“Ai kuwa indai kina so ki samu yanda kike so a gurin namiji yanzu dayan biyu ne, kodai ki zama kurma makauniya ki sakar masa ragama duk abinda yayi daidai ne bazaki musa masa ba ko kuma ace ke kike wahalta masa da aljihunki to shine zaku zauna lafiya ba tareda an ji kanku ba.

Dan muddin kika ce in ya bada umarni zaki kawo taki shawarar to kuwa kun ringa samun sabani kenan. A cikin Maza yanzu kadan ne suka fita zakka da zaki ga sun bawa matansu haqqin da ya kamace su,

Idan kuma yawon Malaman kikaga yafi miki seki daura aniya, ki dai sani wata rana zanin da zaki daura ma se ya gagare ki tunda kullum kina kan hanyar kaiwa wasu daga zaune kudin ki kuma shi Asiri ko kinyi se kin hada da kissa wallahi randa kuma ya karye se kin fi kare wulaqanta”.

Shiru Amirah tayi dan gaskiya Sa’adah ta fada, yanzu dai gashi tun yaushe suke yawon rabar da kudin daga can inuwar su tsugunna a waccen amma babu biyan buqata, gashi yanzu cikin lumana komai yana tafiya yanda take so to amma kuma ita ai bata zaci haka zaman ze kasance ba.

Cikin sanyin murya tace “Toh yanzu Anty Sa’adah ya zanyi dan gaskiya akwai matsala”

“Yawwa yanzu kika dawo kan hanya” Sa’adah ta fada kafin ta ci gaba da cewa

“Kina ji ko, batun gyaran gida wannan daman ai aiki ne dukda ban san Kishiyar ki ba amma a yanda kuka bani labarinta mace ce data san kanta dan haka yanzu dole ki dage idan baki zarta ta ba toh kuyi kan kan kan.

Tsafta dole ki dage gyaran gida ko ina yayi qal ki saka turare Allah na tuba ma wane aiki ne a gyaran gidan keda ba wani wawakeken Mansion ne dake ba dan Duplex ne fa, sharar palour, Kitchen da mopping dinsu dai wannan dole kullum kiyi.

Haka dakinsa, da kun tashi bacci ki gyara gado, yana shiryawa ya fita ki share ki wanko bandaki kija qofar shikenan fa se kuma gobe. Naki dakin zaki iya ki ringa tsallaken kwanaki tunda ke kadai ce babu me shigar kiki, kwanuka idan kina girki daga kin bata ki wanke idan anci abinci ma ana gamawa ki wanke, dan girki dai cin mutum biyu da safe ne fa se na dare ba shikenan ba duk meye abin wahala a ciki dan Allah.

Sannan ki ringa wanka dan Allah sau biyu dai a rana meye a ciki kayan kwalliyar nan gasu nan kina dasu kar kije ki ringa zama yanda kike a nan kamar wata me takaba da zani da T shirt dan dole ki dauke masa hankali daga kan kowacce mace ta yanda ze manta da tsohuwar matar sa ya shafeta daga lissafinsa tunda yana da ke sabon jini”.

“Toh ai Anty Sa’adah katangar mu daya fa da gidan data koma ga yaran tun jiya na gaya miki suke zuruftu a gidan nan ko tunawa dani ma bayayi” Amirah ta sake fada, se Sa’adah ta danyi murmushi tace

“Dadina dake komai se an koya miki, yo Allah na tuba ko a cikin gidan ku take idan kinsan yanda zaki riqe shi tsaf ai wallahi bata ishe shi kallo ba, yara kuma da dabara zaki janye su, daman karki basu qofar da zasu ringa shigo miki idan baya nan.

In kuma yana gidan sukazo kar kiji kunya ko a gabansu ne kije jikinsa ko kiyita yin abinda zaki ja hankalin sa dakansa ze ce su tashi su tafi, yana dawowa gida ki saka abinki a daki yanda baze ma samu kansa ba bare ya gayyato miki su a hankali se kiga shi dasu se in ya fita sun hadu ne ma ze ringa tunawa da zaman su, ke dai kiyi komai yanda ya kamata zaki sha mamaki wallahi”.

Haka ta ringa yi mata huduna data tsiya data kirki sukayi sallama. Da yake dai quiya a jininta take kayan dai gasu nan haka ta shirya masa dan ma ya sake kaiwa an goge dan haka zuba su kawai tayi. Tana cikin jera masa Suits ya shigo dakin,

“Har kin gama kenan” ya fada yana kallon ta hannun ta wadda kuma ita ce ta qarshe da zata rataye. Seda tayi fari da ido ta lankwashe murya kafin tace

“Na gama fa, duk na gaji wallahi hannuna ya qage kayanka yawa Yaya kamar na mace”.

“Koh?” Ya fada yana wuceta ya bude bangaren da ake zuba masa manyan kaya, Amirah kuwa kumbura baki tayi, a ranta tace

“Ba sannu ba komai ze ce mun wani Ayya, Aa Ayyo mutum dai besan gwaninta ba.” Baya ida tunanin ba taji shi cikin fada fada yana cewa

“Meye wannan kikayi? Haka ake jera kaya daman ji yanda kika loda su se kace wani motar kasuwa, malama sauke su tas ki gyara komai da kika gani irinsa daban zaki jera.
Shaddoji daban kuma kalolin su zaki duba kiyi su a jere sannan dayaj side din ki saka yadi ka, nan gurin Neck tie ake ajiyewa kin wani cusa mun hula baga inda suke can ba

Mtsw komai ke baki iya ba se kinyi wa mutane shirme, kina tsaye ki fara sauke su yanzu ki gyara” ya qarasa da daka mata tsawa.

Amirah da tayi mutuwar tsaye, yanzu duk wannan uban aikin data sha ze ce basuyi ba seta sake aikuwa bazata iya ba, haka kawai me ya hana shi yayi da kansa tunda ba haka akeyi ba, tsawar daya daka mata ya saka ta fara sauko da kayan ba shiri, haka tana ji tana gani da hawayenta da komai seda ta mayar dasu tsaf yana tsaye akanta sannan ya saka ta share dakin ta goge qal ta kuma wanke toilet kafin ya rabu da ita. Tana gamawa kuwa ta wuce tsohon dakin Ma’u inda ya saka mata sabon Gado ta ringa rusa kuka.

Indai kuwa haka zaman Lagos din yake kuwa wallahi bazata iya ba sedai ya maida ita can Gombe ya zauna shi kadai, ta zata da ta ke kukan ma ze bata haquri amma se gani tayi yaja Laptop ya kunna ma ya shiga aikinsa haka data gama ba godi bare na gode ta wuce tana kuka be tankata ba qarshe ma se jin tashin motar sa tayi alamar fita ma yayi.

ASMA’U

Se bayan La’asar yaran suka shigo da ledoji niqi niqi na kayan da suka siyo. Kallo daya nayi musu gaba daya suka shiga nutsuwarsu, karadin da suka fara na bawa su Faridah labari kowa ya kama kansa.

“Wallahi Jafar na sake ganin qafarka ka jasu kunje gidan can sena saba maka, idan banda shegen kwadayi me zakuci da bamu dashi a nan, ina shekaran jiya da kuka Raka Yaya Airport seda ya fara kaiku kuka siyi kayan kwalamar duk ba gasu can kun cika mun Fridge da tarkace ba ko kuwa wani sabo kuke so da ni baza ku gayamun ba wa ma kuka tambaya da kuka dibi qafa kuka tafi har wani guri” Na fada ina tsare su da ido, duk sukayi shiru Yan Biyu har sun fara yar kwalla ganin ina musu fada kuma na daure fuska, Jafar ne ya marairaice yace

“Mami kiyi haquri dan Allah bazamu sake ba, na zata ai tunda Abbi ne bazakiyi fada ba kuma shi yace muje bamu muka roqe shi ba ko Abdallah?” Se Abdallan ya yi saurin daga kai yana cewa

“Seda ma mukace mu baza muje ba Anty Amirah tace se munje Allah kuwa ki ma tambayi Abbin kiji”

“Naji, karku sake” na fada har sannan fuskata a hade. Ni ba fitarsu da Bashir ce ta bata mun rai ba akan me Amirah zata fitar mun da yara shine haushi na.

Waiwaya wa nayi na gansu har sannan a tsaye nace “me kukeyi kuka kun tsaya mun aka, kuje ku ajiye mana idan kuma ci zakuyi to se ku zauna”.

“Toh Mami ai baki ce kin haqura ba tukunna” Jafar ya sake fada, se nace masa

“Na haqura mana Jafar, ku wuce ciki”
“To Mami ai baki saki fuskar ki ba, kuma gashi har wannan Shawarman da kike so na siyo miki, naje na dumama miki a microwave?” Ya sake fada yana marairaice fuska, nasan nacin Jafar yanzu idan ban saki fuskar ba se ya kai dare anan yana mun magiya dan haka nayi murmushi nace

“Je kayi toh” da sauri suka wuce Kitchen da kayan, haka badan raina yaso ba naci Shawarmar da aka siya da kudin Bashir, tare muka qarasa wunin mu dan sallar Magriba da Isha ma a gida sukayi saboda ruwan sama daya sakko.

Washe gari ma muna gida har yamma se bayan da akayi sallar La’asar suka fita qofar gida suka raba ball. Ina zaune akan kujera ina jin Dramar Amna da Farida akan kwalliya ala dole ita Farida wai tafi Amna sanin Fashion tana zabarwa Amnan kayan da zata saka na prom din su ita kuma tace basuyi mata ba.

Wayar Faridah ta miqo mun tana cewa “Kalli fa Mami dan Allah ai wannan ne zeyi mata kyau ko, itafa Yah Amna bata san me ake yayi ba”

“Aike kin sani naga alama” na fada ina karbar wayar daga hannunta, shigowar da Abdallah yayi da gudu ce ta sakani dagowa daga kallon wayar nace

“Kai kuma menene haka, bana hana ku wannan guje gujen ba se kaje ka fadi ko”. A gaba na ya tsaya yana haki yace

“Mami Abbine, gashi can a qofar gida wai se mun dakko kayan mu mukoma can gidan, ga Baba can ya tsayar dashi suna magana”.

Ina shirin bashi amsa Anty tayi sallama ta shigo daga tsaye take cemun

“Asma’u Bashir ne, gashi can yana rantse rantsen se yara sun koma hannunsa, dan Allah karki tsaya tashin hankali dashi, idan dai ya kafe ki barshi nan da can din ai duk guri daya ne”.

Miqewa nayi nima har ina fatali da wayar Amna ban lura ba nace “Bazan bashi yarana ba Anty, Be auri matar da zan barwa tarbiyyar yarana ba kuma ko mutuwa nayi badai dangin Bashir su riqe mun yara ba wallahi”.

Daga waje nake jiyo maganarsa yana gayawa yaran su shiga su dakko kayansu, zan fita Anty ta ruqoni tana cewa

“Karki fita, kijira idan ya shigo da kansa se kuyi magana kuma ni banga abin tashin hankali ba akan yara dai bayan kuna guri daya a zaune”.

Yaran ne suka shigo Aliyu akan Gaba suka wuce can ciki suka tsatstsaya sega Bashir a bayan su yana jaddada musu dasu hada kayan su su wuce gida.

“Harke zaki hana mun yara shiga gidan ubansu ko, toh dake da itan duk zan nuna muku baku isa ba, zan dauke yarana ita kuma dole ta riqe su tunda gidaj ubansu ne bana uban wani ba” ya fada yana kallona, daman jira nake yi dan haka nima a fusace nace

“Seka gorantawa wanda ubansa bashi da gida, Ÿaya kuma tunda ba wani ya haifar mun su ba banga wanda ze dauke su ba, ita kanta matar taka bata wadatu da tarbiyya balle na a bata kula da wasu”.

“Kar ki zageni Ma’u, Ÿaya kuma nawane halak malak ke din yar karere ce dan haka dole su koma gidan ubansu yanzu kuma ba da bata lokaci ba”.

Zan sake magana Baba ya dakatar dani da cewa
“Wai me kukeyi haka yanzu daga ke harshi kenan baza’ace ku bar abu ku bari ba kunzo gaban yara kuna irin wannan abun me kuke koya musu kenan?

Kai Bashir ka wuce muje, ke kuma Asma’u ku hada musu kayan ku tura masa Ÿayansa tunda yana da mata daman ai haqqin ruqonsu a hannunsa yake”.

Kuka na fashe dashi ina cewa “Akan me ya sake ni sannan yace ze raba ni da yarana wannan ai rashin Adalci ne”.

Wayata na dauka na shiga kiran Alhaji Qarami, kira biyu na masa be dauka ba dan haka na juya akalar kiran zuwa Goggo. Tunda yanzu tana goyon bayana gara na gaya mata ko zan samu wanda ze tsaya mun dan gaskiya bazan bawa Bashir yara ba sedai ayi duk yanda za’ayi.

Tana daga wayar na fasa mata kuka ina gaya mata yanda akayi, seda ta gama jina tsaf kafin tace

“Toh Ma’u Menene a ciki tunda yana da yanda ze riqe yaransa se ki bashi, kin fiya son damun kanki wallahi ke kanki ai sauqi kika samu seki nutsu idan an kwana biyu ki nemi wani mijin kiyi aure dan kinsan zaman ki haka baze yuwu ba tunda yayyenki sun daure miki gindin ki zauna a can to ki bashi yaransa ki raka su da Addu’a, a ko ina suke Allah ya tayaki tarbiyyantar dasu”.

Kashe wayar nayi dan na manta ma Goggo duk abinda ya tashi ai bayansa take bi, ina shawarar kiran Alhajin su Bashir din kiran Alhaji Qarami ya shigo.

“Asma’u ki tattara su daga kan Aliyu har zuwa Tukur ki bashi yaransa, bana son wata doguwar magana ki rabu dashi. Yara ko bangwan duniya ya kaisu dole wata rana se sun nemeki da kansu dan haka dan Allah karki tayar da hankalin ki ki tayar da na wasu, mun gaji da Bashir Bashir kullum babu fashi.

Bafa akanki aka fara sakin Mace ace ta bada yara ba dan haka please Ma’u ki bashi ki kuma sararawa kanki haka haba” Alhaji Qarami ya fada tun kafin nayi masa qorafin, daga jin yanda m yake magana na tabbatar da ransa a bace yake maganar ta ishe shi, daman shine dogarona da ze tsaya mun To gashi shima yabi bayan su dole bani da zabi na bawa Bashir yarana.

Ina Kuka sunayi Baba ya tasa su a gaba har qofar gidan Bashir ya barmu muna hada musu kayansu, tas muka tattara komai wani abun ma a hannu aka dauke shi Anty dacAmna suka kai musu.

Dakina na shiga na ringa riskar kuka wannan rashin Adalcin da akayi mun.

AMIRAH A DAREN JIYA


Assalamualaikum Barkanmu da wannan lokacin AUNTY ZEE TAKU CE ,Ina uwar gida Amarya da yanmata albishir gareku

BONONZA; BONONZA;BONONZA;

Nazo maku da SAHIHIN MAGANIN CIRE TUMBI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI,KINCI GAYU ANA TAMBAYARKI YAUSHE ZAKI HAIHU TUMBI YA HANAKI ADO DA KWALLIYA SHA KURUMINKI NAZO MAKI DA MAGANI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI ZAN DANDANA MAKU SHI AKAN RABIN KUDINSHI DAGA NAN ZUWA SATI DAYA 7K DUK ROBA DAYA KI BIYA 3500 KI MALLAKI NAKI NAN DA SATI DAYA ZAI KOMA 7K


MAGANIN BREAST WANDA ZAICIKO MAKI DA TUWON NONO DAN ALLAH KIJARABA ZAKIZO KINA GODIYA DAN DUK WADDA TA GWADA SAITA DAWO MANYAN MATA SUKE GYARA KAMAR YANDA KUKASANI 8K YAKE ZANKARA TALLATA MAKU SHI KI BIYA 4K KI MALLAKI NAKI
KI BIYA TA WANNAN ACCOUNT DIN KITURA MAN SHAIDAR BIYA
3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
08162859027🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 43

AMIRAH A DAREN JIYA

Se dare Bashir ya koma gida har sannan tana nade tana jiran yazo ya rarrasheta. Bayan sallar Isha ya shiga lokacin ta gaji ta fito palour tana zaune tana kallo ga yunwa tana ji amma ta kasa tashi ta girka abinda zata ci, jira takeyi ya dawo se suje su siyo abinci.

A sake ya shigo gidan tayi masa sannu da zuwa ya amsa kafin ya ajiye ruwan dispenser daya siyo ya dawo palour ya zauna yana cewa
“Kawo mun Abinci yunwa nake ji”.

Seta tsaya tana raba ido, wane abinci kuma yanzu ita da take jira ya dawo su siyo shine ze zo yana wani tambayarta dan haka ta gyara zama a shagwabe tace

“Nima fa Yaya yunwa nakeji, kai nake ta jira tun dazu ka dawo se muje muci abincin”.

“Saboda babu kayan girki a gidan nan ko kuma baki da hannun da zaki dafa ko yaya?” Ya fada cikin muryar bacin rai, zata qara magana ya daka mata tsawa yana cewa

“Ki wuce ki samar mun abinda zanci Yanzu bana son bata lokaci, sannan daga yau ma idan zakiyi girkin dare ki ringayi tareda yara anan zasu ringa cin abinci”.

Harta miqe ta koma ta zauna tana cewa
“Wane Yara zan ringa girki dasu ba a gidan su suke ba sannan kuma ni zan ringa musu abinci gaskiya bazan iya ba”.

“Ba wai shawarar ki na nema akan zakiyi ko bazakiyi ba umarnine tunda gidan ubansu ne dole ki dafa abinci ki ajiye musu ko bazasu ci ba, kuma kitashi ki samar mun abinda zanci yanzu karki bata mun rai”.

Miqewa tayi ta tafi Kitchen din tana mita “haka kawai wallahi babu dan da zan yiwa girki yaran ma suna

Please Login or Register in order to submit comment