Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne ko kuma tana tare da kai ta ringa kula wasu cana waje da suke bata kulawa suna yabonta.

Da yawa maza mu muke bada qofar da matan mu suke aikata wasu abubuwa da basu kamata ba a bayan idon mu. Yanzu misali kaine kullum cikin hade rai a gidanka, kaida matarka idan taga haqoranka to magana kakeyi babu dariya babu lafazi me dadi balle ace tayi kwalliya ka yaba ko ka zauna kayi wasa da raha da ita tsakanin ku se bada umarni kamar wata yar aiki da ubangidanta dan Allah ta yaya kake tunanin idan ta hadu da wanda ze bata duk irin wadannan kulawar data rasa a gurinka ba bazata kulashi ba?

Ba kowacce mace ce take da qarfin zuciyar daure wasu abubuwan ba, wata koda ba ta sigar fasiqanci ba, wata da sunan aboki zakaga ta hadu da wani namiji da zasu zama kamar wasu Qawaye ko Aminai duk wani sirri nata daya kamata ta yi shi tare dakai shi ze maye mata gurbi ya zama abokin shawararta se kaga matar aure wai tana da wani Besty duk waya ja Mijinta kuma ka tabbatar duk dakon zunubin da zatayo tare za’a kasafta muku dan kai ka yanka mata tikitin da har zata kula wani banza can da auranka.

Ka duba yanzu ko a gurin aikin mu yanda mata suka lalace matan aure kaga suna qazamar rayuwa suna mu’amala da wasu mazan a waje da bana auransu ba a kaso goma idan ka tarasu bakwai wallahi mazansu nada sa hannu cikin fadawarsu wannan halakar saboda basu da ma lokacin su ballantana su san damuwarsu har su maganta musu ita da yawan maza muna dauka kudi shine maganin ko wacce matsala idan ka wadata mace shikenan ka gama mata komai wanda sam abin ba haka yake ba dole ka kula da matarka ta kowanne bangare ka tabbatar da cewa ka toshe mata duk wata buqata idan kayi haka kuma kaga wata matsala ta faru seka qaddara cewa jarabawa ce kuma daga ubangiji amma ba wai dan kai ka bayar da qofar faruwar hakan ba.

Dan haka nidai shawarata Bashir ka canja takunka, ba Asma’u ba ko wacce mace zaka zauna da ita dole ne kasan qima da martabarta. Ka sani cewar ba Alfarma kayi musu daka auresu ba ballantana ka dauka dole suyi haqurin zama dakai da halinka Aa zamane na ibadah da Allah ya hadaku kowa yana da haqqi akan dan uwansa”

“Haka ne kuma zanyi qoqari na gyara kuskurena Musa dan ina buqatar Ma’u a rayuwa ta wallahi” Bashir ya fada bayan daya sauke tagumin da yayi.

“Au saboda ka dawo da Asma’u zaka chanja hili kenan? Bashir bari fa na gaya maka gaskiya Halinka cikin goma bakwai basu da kyau ta fannin zaman takewa. Kai bafa matanka ba kadai mu kanmu haquri muke dakai wani lokacin saboda shi hali zanen dutseaka ce ba’a chanza wa mutum shi amma a wannan karon in har kana so lamuranka su daidaita dole fa seka daidaita sahu a to.

Kai in banda ma halinka Bashir a zamanin nan ka samu mace kamar Asma’u bafa ajinka bace wallahi in ma gaya maka gaskiya Allah ne kawai ya kashe ya baka ka samu tana sonka take hidimta maka da jikinta da Aljihunta, matar nan fa ko daure fuska kayi se hankalinta ya tashi. Ka tashi ka tafka mata kishiya ta wulaqanci koni Namiji naji zafin abinda kayi ballantana ita sannan ka qara mata da tukwuicin saki kai ni idan ta haqura da wuri ta dawo maka gaskiya bata mun daidai ba”.

Daure fuska Bashir yayi tamau yana kallonsa yace
“Karka kuskura kace mun kaima kana son matata dan shine mafi girman kuskuren da zaka aikata, mu kadai ne a gidan nan yanzu zan murqusheka ka mutu Ba wanda yasan meya faru”.

Dariya Musa yayi harda fadowa daga kan kujera kafin yace

“Maida wuqar Malam ashe daba ka fara ban sani ba. Ai ni idan zan so Ma’u bazaka sani ba, qila se kaji nayi aure kawai kazo gidana ka ganta a matsayin matata amma ni sam ba haka nake ba, babu kuma haka a tsakanin mu kawai dai ina nuna maka irin girman asarar daka tafka ne a rayuwarka kuma idan baka hanzarta ba kana ji kana kallo sedai ka mutu kana cizon yatsa da daka sani ka mayar da yayanka marayun dole ka rabasu da uwar su haka kawai”.

Ganin da yayi daga shawara kuma abin na Musa na neman ya koma wulaqanci yasa yayi masa sallama ya kamo hanyar gida, a hanya ya tsaya wani guri da suke siyan Shawarma da wani Gas meat da Ma’u take bala’in so ya siya da yawa ya hado da Madarar ruwa da kwali itama kalar wadda take sha kafin ya kamo hanyar gida.

A qofar gidanta ya ci burki, a waya ya kira Amnah yace tazo ba tareda ya fito ba ya ce ta bude bayan motar ta kwashe ledojin ciki.

Ya dade a mota kafin ya fito qafa daya da takalmi daya babu ya dauki tasa ledar Naman da Madarar ya shige gida, Hajia Addah na zaune a palour ta tasa Amirah data gama zaman dakin ta fito a gaba har sannan dai zancen dubu goma yaqi ci yaqi qarewa.

Kallo daya ya musu sanda Amirah ta masa sannu da zuwa ya wuce daki tabi bayansa, tun dazu take jira ya dawo ita dai ya taimaketa ya biya Addah kudinta kota samu ta shaqi iska a gidan yana shiga dakin kan ya rufo tayi wuf itama ta fada ya kuwa balla mata harara ta sunkuyar da kai se ya wuce ya ajiye ledar hannunsa ya shiga bandaki.

Tana zaune se hadiyar yawu take saboda qamshin naman da duk ya cika dakin ya fito, kamar munafuka tayi qasa dakai tana gaishe shi ya amsa a taqaice yana cire rigar jikinsa ganin taqi fita yace mata

“Lafiya?”
“Am daman Yaya an sallamo mune na kiraka da wayar Addah lokacin baka dauka ba na kira Samuel shima yace mun...”

“Na sani na aike shi ba gashi kun dawo ba se akayi yaya to?” Ya katseta murya a cunkushe, qasan ransa har yana tunanin wane hankali ne yazo mata da har tayi tunanin zuwa ta duba shi kodai Addah ce ta sakata dan yasan a kalar nata tunanin dai bazatayi ba, maganar tace ta katse shi da take cewa

“Daman Taxi muka hawo ta dawo damu, shine seda muka zo yace wai kudin motar dubu Ashirin tunda drop muka dauka to Addah ce ta biya tun safen take ta mun masifa akan na biyata kudinta kuma ni ko sisi bani dashi nayi ta kiranka ma dazun kana rejecting gata can wallahi ko abincin kirki ta hanani naci da masifarta”

Wani mugun kallo me nuna zallar bacin rai yake aika mata, wato kudi take da buqata tun dazun dalilin kiran da ta ringa masa kenan, qonewar da uwarta taja masa ma bata dameta balle taji ya qafarsa kawai kudi ze bata a mugun fusace ya nuna mata qofa ba tareda yayi magana ba.

Amirah dake ta Addu’a a ranta Allah yasa ya bata goman ta ajiye dan tunda tazo sile biyar bata hadasu ba kai ko katin waya bashi ne kusan dubu biyar taci na Mtn saboda ya dena saka mata, da tana Gombe kuwa duk satin Allah yar dubu dayar nan dai seya saka mata wani lokacin ma biyu ga yar cuwa cuwar da takeyi ta karbi kudi a hannun Naziru na cefane anan kuwa shi yake siyo komai kuma se abinda ta gani kawai dan waca wacar nan data san anayi a gidan bata san me yasa yanzu kusan komai a qididdige yake ba ba yanda ta saba ganin sanda Anty tana nan komai na danqare a Freezer ba sedai su bude su diba.

Ita da yake ya raina mata hankali se abinda yaga dama yake siya ya ajiye kuma idan ya qare abinda yake ci ze siyo da wuri, daman nama ne yafi damuwa dashi, tana son kifi amma tunda tayi masa wani farfesun kifi ita kanta dai ranar data ci haka qarnin yayi ta taso mata be sake siyowa ba tayi nacin harta gaji to tunda ta samu ciki ma ya dena cin abincinta, daman yaran ba ci suke ba sedai su dafa abinda suke so ko su shigo dashi daga can gidan sedai tayi ta qara qararta ita kadai ga cikin me dan banzan kwadayi haka zata yita hadiyar yawu idan ta jiyo qamshin abincin makwafta.

Tsawat daya daka mata ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi dan ashe yana ta mata magana ma bata ji ba, da sauri ta tattari qafarta tayi waje tana fita suka kusa karo da Addah dake labe a bakin qofa cikin matuqar takaici Amirah ta kalleta kafin ta wuce dakinta wata kwalla na sakko mata.

Bashir kuwa sallah kawai ya tayar dan idan ya tsaya takaicin Amirah yana iya shaqe shi kawai aga ya fadi, so kuma yake yayi isha ya zauna ya tsarawa Ma’u Saqo ya tura mata dan ya qudurce indai soyayya ce matsalar to kuwa ko Sharukan se dai yazo ya kwashi kos a gurinsa a wanna karon.

ASMA’U
Bayan dana dawo daga rabon abinci sallah kawai nayi na kwanta dan na gaji sosai bani na farka ba se dab da magriba. Kiran Yaya Abubakar na gani guda biyu na shiga bandaki na wanko fuskata da bakina kafin na dawo na zauna na danna kiran lambar sa.

Bayan mun gaisa yake cemun
“Dazu Bashir ya kirani a waya wai yana bani haquri, ban san rashin kunyarsa harta kai haka ba se yau tukunna nadai ja masa kunne akan karya kuskura ya sake kirana in ba haka ba yasan sauran”

“Lallai Baban Ali shi har yana da qarfin guiwar kiran ka kenan, haka fa jiya yazo qofar gidan nan wai yana bani haquri harda durqusawarsa” na cikin mamakin tsaurin idon Bashir.

“Asma’u” ya kira sunana da sautin da yake nuna muhimmancin abinda ze gaya mun sena gyara zama dakyau na amsa ina sauraronsa yaci gaba da cewa

“Kafin ki auri Bashir kin taba tambayata abinda yasa bana farin ciki da auran ku ko to yau zan baki amsa. Bashir Abokina ne kin sani tun na yarinta dan haka nasan halinsa ciki da bai, halayyata da tashi sunyi kamanceveniya ta wani bangaren saboda dani dashi murdaddun mutane ne da ake shan wahalar gane gaban mu.

A bangaren auratayya muna da buqatar samun tsayayyar mace me taurin zuciya da ra’ayin riqau ta yanda dole sedai ko mu zubda makaman mu mu bita ko kuma ya zamana anyi 50 50 ma’ana kowa ya riqe bangare daya bawai wadda zamu taka yanda muka ga dama ba kuma ta biyu.

Baki dace da Bashir ba saboda ke mace ce me sanyin hali da saurin yarda tareda sadaukarwa inda ace Aliyu marigayi ne ya nemi auranki dukda yaso hakan amma Bashir yayi masa shigar sauri, a lokacin da na zamo kan gaba a komai saboda nasan bazaki taba nadamar zabarsa ba saboda halayyat ku kusan daya ce, dake dashi zaku ringa rige rigen kyautatawa junan ku amma Allah be hukunta faruwar Al’amarin a haka ba ya qaddara cewar Bashir din dai shine Mijinki harda rabon zuri’a a tsakanin ku.

Banaqin Bashir saboda shima mutumin kirki ne kuskurensa kuma ajizanci ne irin na ko wanne dan Adam kuma na tabbatar da nima da ace irin ki nake aure da ko ba dukka ba se an samu kwatankwacin halayyar Bashir a cikin gidana saboda nasan duk abinda na dakko zata yarda kuma ya zauna.

Bance Bashir baya son ki ba amma ki sani son da kike masa ko nace kina bayyana soyayyarki sama da tasa shi kansa wannan babban dalili ne da Namiji ze riqe ya kuka juyaki duk ta yanda yaso saboda yasan kina sonsa zakuma ki zauna dashi a duk yanda yake.

Abinda nake so na gaya miki Ma’u, Bazan hanaki ba idan har zuciyarki ta aminta da ki koma gidan Bashir amma ki riqe abu guda daya shine ke din dai kece ba wata sabuwa ta daban ba haka Bashir yana nan a Bashir din da kika sani babu abinda ze chanza daga halayyarsa ta ainihi duk wani chanji da ze zo miki dashi na dan lokacine dole wata rana se an koma gidan jiya.

Karki duba kowa ko wani abu ki duba makomar rayuwar ki, Kin cancanci samun rayuwa me cike da Farin ciki Ma’u kiyiwa kanki gata, idan har farin cikin ki yana tareda Bashir ki koma gidansa ku zauna zamu ci gaba da binki da fatan Alkhairi kamar yanda muke miki a koda Yaushe idan kuma kina da zabin daya fishi Allah ya tabbatar miki da Alkahiri yasa kiyi farin ciki dashi na har abada”.

Shiru nayi kamar wadda aka zarewa laka har Yaya Abubakar ya gama mun magana dakyar na iya cewa

“Nagode Yaya, nima a yanzu banida wani zabi se abinda Allah ya zaba mun, in sha Allahu yau zan fara istikara ina kuma fatan Allah ya saka mun duk abinda yafi Alkahiri a zuciyata Nagode kwarai Yaya Allah ya saka da Alkahiri”

“Babu komai Allah ya jishshemu Alkhairi, Ina Yaran ina fatan dai babu wata matsala ko?”

“Babu komai Yaya, ai yanzu ma kusan anan suke dan bacci ne kawai yake mayar dasu can gidan shima wani lokacin anan suke kwana kuma baya magana dan Farida daman ta dawo nan gaba daya”

“Toh haka ake so, kin gani ko tashin hankalin daman bashi da amfani yanzu gashi a ruwan sanyi ai kusan sun dawo hannunki, Allah ya wuce mana gaba”

“Amin yah rabb Nagode yaya a gaida su Anty Nasiba” daga haka mukayi sallama ina ta juya maganganunsa a raina, matsaya daya dai na zauna akai itace ta neman zabin Allah tunda shine dahir

Bayan sallar Isha ina zaune ina lazumi sega Amnah da leda niqi niqi tun kafin ta ajiye qamshin abinda yake ciki ya doki hancina nan take kuma na gano na ina ne.

Kallonta nayi da alamun tambaya ta ajiye su kusada ni tana cewa
“Abbi ne ya kirani a waya yace na kawo miki”

“Zaki tattara ki wuce mun dasu daga nan ko yaya, me yasa daya kiraki baki zo kin gaya mun kafin ki fita ba” na fada ina rufeta da fada. Setayi rau rau kamar zatayi kuka tace

“Mami Abbi ne fa ba wani ba, kuma ai...”
“Amnah ni kike gayawa Abbi ne ba wani ba Abbin ubanki ne ko yaya? Ki shiga hankalinki Amnah kuma ki kwashe kayan nan ki fita dasu kafin na bata miki rai”.

Kayan ta diba seda ta kai bakin qofa kafin ta waiwayo ta kalleni tace
“To mu zamu ci Mami idan ke ba zaki ci ba”
“Amnah se naci ubanki idan na taso wallahi ki tattara ki mayar masa idan ba haka ba zamu gamu”

Da sauri ta fice ta barni ina mita ni kadai, qamshin naman kuma seya tado mun da tsohon kwadayi dan ina bala’in son Gashin gurin. Seda nayi Shafa’i da wutri na nayi Addu’oi kafin na fito palour ina jin badan dare yayi ba da tabbas sena fita na siyo naman nan dan dai bazanci na hannun Bashir ba.

Turus nayi daga bakin qofa ina kallonsu yanda sukayi face face da naman sunaci wasu nacin shawarma.

“Yanzu Amnah me na gaya miki?” Na fada ina kallonta, se tayi saurin ajiye Naman hannunta tana zare ido tace

“Wallahi Mami shiya ce mu cinye kuma ma seda Addah da Anty Amirah suka diba da gaba daya ma suka qwace seda Abbi yayi ta masifa kafin suka bamu kuma Addah ta sake biyo mu ta dibar musu”

“Shikenan ai kun kyauta, idan kin gama ki dafa mun Indomie ki kawo mun” na fada ina komawa ciki.

Wayata na dauka, Ina so na kira Yusuf wata zuciyar kuma tana hanani. Saqo ne ya shigo wayata, Bashir ne na bude na fara karantawa bansan sanda na bushe da dariya ba saboda ganin irin abubuwan da ya rubuto wato kalaman soyayyane kala da kala a ciki gaba daya se naga abin wani banbarakwai.

Ina gama karantawa na goge shi ina tuno da wani saqo da Yusuf ya turo mun dazu da yamma se kawai na danna kiran lambar sa.

“Allah yasa muga Annabi” ya fada yana daga wayar, senayi murmushi me sauti nace

“Amin”.
“Amma Asmy batan lamba kikayi ko?”
“Me ka gani?”
“Babu komai, kawai dai nasan kina sane bazaki kirani a waya ba sedai tuntuben lamba kikayi”
“To shikenan bari na kashe tunda haka kace” na fada kamar zan kashe din se yayi saurin tare ni da cewa

“Aa bafa haka nake nufi ba, Allah ya taimaki Amaryar Yusufa barka da dare toh ya kike?”

“Barka dai Excellency ya aiki ya Jama’a?”
“Aiki Alhamdulillah kinsan kuwa yau wunin Site nayi na dawo duk na gaji wallahi Asmy, ya gida ya yara ya kuma kewata?”

“Ni na rasa irin son kudinka dai Yusuf, idan ba haka ba dan Allah ina kai ina Wani supervision na aiki? Dan Allah ka barwa sauran Jama’a suma su samu mana”

Dariya yayi yace
“Asmy kenan, nifa ko Inyamuri baze nunamun neman kudi ba, dazu naje wani qauye zamu siyo gyada muna zuwa suka lullube motata nace kai ku matsamun ni ba wannan ya kawo ni ba neman Halal na fito yau”.

Dariya sosai nayi, daga nan muka shiga hira har Amnah ta kawo mun Indomin, Allah Alah nake mu gama magana ba tareda ya taso mun da zancen dazu ba, seda zamuyi sallama kuwa yace

“Saura kwana shida, ina Addu’a Allah yasa naji Alkhairi”

“Amin Allah ya sa muga Alkahiri” nima na fada daga nan mukayi sallama.

Ban kwanta bacci ba se gurin uku da rabi na dare, sosai nayi sallolina da Addu’oi na rufe da sallar Istikara tareda kyakykyawan yaqinin samun haske a cikin al’amarina na kuma bude zuciyata ko Bashir, ko Yusuf ko ma wani ne daban Allah ya zaba mun zan karbe shi nayi fatan ya zame min siradin zuwa Aljannah.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 57

BASHIR
Iya bakin qoqarinsa yakeyi gurin aiwatar da abinda Musa ya gaya masa, duk yanda yasan ze shawo kan Ma’u yi yake amma kamar wadda yake qarawa wuta fetur daman baya samun ta a waya duk ubannin saqonnin da yake tura mata kuwa bata taba maido masa da ko guda daya ba.

Ya rasata ina ze sameta suyi maganata fahimta, baya son zuwa gidan ta tunda tace masa bata so amma dole ya zama me gadin qarfi da yaji, da wuri yanzu yake baro office yazo kanlayi ya kasa ya tsare amma ko sun hadu ma wani shashasha take mayar dashi dan daga gaisuwa bata ma bashi damar magana zata wuce abinta.

Abun na bala’in ci masa tuwo a qwarya, ga azumi yana gaba towa baya so suyi azumi a wannan yanayin. Gidansa daman tuni yafi qarfin sa in har yana son nutsuwa to fa sedaiya fita waje dan karadi da surutun Addah kadai ya ishe shi. Shi bata barshi ba ita Amiran da take fama da kanta itama bata tsira ba ga jaye jayen magana da take dakko masa haka kawai seta wanke qafa ta shiga gidan maqota kuma in dai taje seta takalo wani abun haka za’ayi ta tararsa ana kawo qararta sedai yai ta aikin bada haquri.

Kusan sati ana wannan yanayi ranar yana zaune da daddare a dakinsa haka kawai zuciyarsa ta ayyana masa kiran Goggon su Ma’u.

“Nasan tana sona da Ma’u kuma ita kadai ce zata fahimceni a yanzu in Allah ya taimaka seta shawo mun kanta a sanyi komai ya daidaita” ya fada a fili yana janyo waya cike da kwarin guiwa ya shiga kiran Goggo.

Seda ta dan jima tana ringin kafin ta daga da sallamarta suka gaisa yanda suka saba yana tambayarta jikin Baffa tace da sauqi kafin itama ta tambayeshi su Amirah da yara yace duk suna lafiya se sukayi shiru gaba daya.

“Lafiya dai ko Bashir naji kayi shiru” Goggon ta katse masa shiru, seda ya hadiyi wani yawu kafin ya gyara zaman sa ya sunkuyar da kai kamar yana gabanta yace

“Daman Goggo kira nayi in bada haquri, wallahi nauyi da kunyarki ta saka tun lokacin da abin ya faru na kasa kiranki se yanzu dai na daure nace bari na kira”.

“In banda abinka Bashir meye abin bada haquri kuma kamar wanda ya aikata wani laifi, shi zaman aure ai raine dashi idan lokacin mutuwar sa yayi kuma ba yanda aka iya ko da dalili ko babu haka ana so ba’a so za’a rabu, karka ji komai wallahi Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri a gare mu baki daya” Goggo ta fada a sake babu damuwar komai tattare da ita.

Cike da qarfin guiwa Bashir ya shafa kai yace
“Hakane wallahi duk abinda ma ya faru Goggo laifi na ne kuma dai sharrin shaidan ne amma yanzu na gane kuskurena kuma in Allah ya yarda haka bazata sake faruwa ba”

“Ai ita rayuwa daman haquri akeyi amma babu komai ai koma dai laifin waye a cikin ku Ai abubya wuce Allah yayi wa kowa zabin Alkahiri a gaba”

“Ai Goggo Alkahiri dai yana nan tare damu dan in sha Allah zamu koma kuma babu abinda ze sake faruwa a gaba se Alkahiri, badan ma wancan tsautsayin daya faru ba ai da yanzu ma ta dawo dakinta qila tana shirin haihuwa koma ta haihu amma yanzun ma muna saka rai in Allah ya yarda kafin Azumi komai ze daidaita.” Bashir ya sake fada da qarfin guiwa.

“Toh haka da sauri har kun daidaita kenan?” Goggo ta tambaya cikin mamaki, se ya shafa kai kamar yana gabanta yace

“Aa dai tukunna, kinsan mutuniyar ne akwai rikici itama wani lokacin to har yanzu dai inata ban baki ne amma taqi ta bani dama amma nasan dai in aka ci gaba zata haqura shi yasa ma na kira yanzu ko za’a dan taimaka a saka baki tunda tana jin maganar ku qila tafi saurin sakkowa”.

Seda Goggo taja ajiyar zuciya tana jinjina qarfin halin Bashir kafin ta iya ce masa

“Eh to ai duk da na gari da yake so yaga daidai dole yaji maganar iyayensa. Zancen mu saka baki kuma ai bata taso ba Bashir dan a yanzu Addini da kansa ya bata damar zabar abinda take so dan ta wuce Budurwa bare ace za’a fada mata yanda zatayi.

Idan taga tana da sha’awar zama dakai mu masu yi muku Addu’ane idan kuma tace Aa shikenan se muce Allah zabawa kowa rabon Alkahiri”

Yanda kasanta saka guduma ta kwade masa guiwoyi haka yaji duk ya rikice har wata zufa ce ta tashin hankalo ta shiga zubo masa. Cikintawar murya yace

“Goggo a haqura kuma dan Allah a dai duba ko dan darajar yaran nan Goggo be kamata mu rabu ba”

“Yo Bashir mantawa kayi dasu sanda ka saketa ne? Kuma ina duk cikinsu babu me shan Nono. Daidai da Biyu sun isa su riqe kansu su zauna ba tareda uwarsu ba shekara Bakwai ai da yawa idan ma kuma kana ganin bazaka iya riqe su bane seka kawo mana daman kai ka damu da abaka yayanka amma mu muna so zamu riqe su Allah ya raya har zuwa sanda zasu mallaki hankulan kansu.

Sannan daman ina so na kiraka akan zancen Farida, kaga ita mace ce to na nemi alfarma ka barwa uwarta ta riqeta samarin kuma su zauna dakai shikenan. A gaida matar gidan Da yaran se anjima” tana gama fadar haka ta kashe wayar bata ma bashi damar sake wata magana ba.

Kamar wanda akawa mutuwa haka ya zabga tagumi tunda Goggo bata goyon bayansa toh ina ze kama??

ASMA’U
Sosaina dage da kai kukana da neman zabi zuwa ga sarkin sarakai. A wannan taqin tsakanin Yusuf din da Bashir har na rasa wanda yafi uzzurawa rayuwata dan yanzu Bashir ya dage saqon ban haquri da kalaman soyayya karo da karo seya turo mun Ashirin a rana haka kiran waya sedai nayi ta ganin missed calls dinsa tunda nayi blocking layin se kawai nayi murmushi na share.

Sauqin dana samu da Yusuf tafiyar gaggawa data same shi zuwa qasar Turkiyya zeyi wata daya dan se cikin azumi sannan ze dawo.
Yanzun kam Wasai nake jin zuciyata duk wannan qunci da takura da nake ji da wata makauniyar soyayya yanzu ya yaye, ina matsayin da zan iya karbar ko wanne irin al’amari hannu biyu bani da wata matsala tartibiya, rayuwata kawai nake a kullum kuma ina nanata Addu’ar neman zabin

Please Login or Register in order to submit comment