Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

se yayi magana ya hana ta barin Bedsheet a gado in bata nan amma taqi ji sedata kunna Ac ta tsaya tana maida numfashi, iya nan tayi amma harta gaji amma tasan idan batayi da kyau ba ma kanta ta jawa.

Har zuciyarta tace tabar dakunanta ta gyara palour kawai da Kitchen wata zuciyar ta ce mata ko sama sama ne tayi tasan yanda yake a kusan nan tsaf ze leqa ko ina.

Dakin baqi ta fara shiga Ba shara ba komai ta hau moping, toilet dinta ruwa ta watsa bata wanke ba taja ta rufe ta shiga Bedroom dinta. Yana nan a hargitsensa yanda ta tafi ta bari, kan gadon kayan gugar da aka kawo mata ne bata shiryasu a wardrobe ba, babu lokaci dan haka ta tattara ta watsasu duk gugar ta hargitse. Bedsheet din shima ta chanza ta hau moping bayan ta kwashe kufunan data sha wani lemo wani fura harda ledar balangun dataci ana gobe zata tafi ta manta bata dauke ba da sauran a ciki ya bushe.

Tana bude toilet dinta kuwa zarni da warin kayan wankin data tara suka bugota dan ita fa a qasa take tsula fitsarinta ga Tiles da kama zarni, kaya kuwa nan take watsar dasu har kuwa da inner wears dinta seta tara ta rasa na sakawa sannan zata wanke.

A farko tsabar wauta da rashin hankali ma harsu take hadawa a wanki se randa Allah yakai idon Bashir ya gani yai mata tatas tareda jan kunne me qarfi sannan ta fara wankewa daga baya kuma ya siyamata washing machine ta ringa wanke qananun abubuwa kayan sawa kuma suna da me wanki duk sati yake zuwa.

Sau daya ya taba bata singlets da Boxers dinsa ta wanke masa a injin ta hadasu a ruwan dattin kayanta qarshe dai se zubar dasu yayi daga nan kuma be sake bama sedai ya wanke da kansa.

Kayan ta tattara ta wanke bayin sama sama ta fito. Palour ma ta nutsu dai ta gyara kitchen kuwa da tasan ba shiga yake ba janyowa tayi ta kulle bayan ta kwashe kwanukan data bari da abinci a ciki duk sun rube kitchen din se doyin abinci yake seta watsasu a shara dan bazata iya wanke wa ba.

Tana tsaka da sharar compound ya shigo hannunsa dauke da ledoji daga gani abinci ne a ciki, seda gabanta ya fadi Allah yasa karya shiga kitchen neman plate dan ruwa da lemo a kwai a fridge din Dining. kallo daya ya mata ya shige palour abinsa.

Yafi babu sunan gyaran nata, centre table yaja ya dora abincin dan ko karyawa beyi ba ya fita dama ya zauna akan kujerun da suka fita hayyacin su kamar wanda suka shekara goma bayan ko cikakkiyar shekara beyi da chanza mata su ba lokacin waccen Haihuwar da tayi ne. Yana dab da kammala cin abincin ta shigo tana jan qafa tayi budu budu da qura dan da gaske ta gaji

Kallonta yayi ya danji tausayinta kodan cikin dake jikinta se ya dan sassauta murya yace “kije kiyi wanka ga abinci kici”.

Dan jim tayi, me ta tuna kuma tace “toh” ta shiga dakinta. Kwaskwarima tayi ta chanza kaya tareda fesa turare ta fito, ya tashi daga palour dan haka ta zauna taja abincin taci. Harta gama ta tattara gurin be fito ba dan haka ta bishi tasan yana dakinsa.

Yana kwance akan gado jikinsa sanye da rigar wanka yana waya da su Jafar da Ma’u ta kira shi bayan sun gaisa ta basu. fuskarsa dauke murmushi saboda maganar da Jafar din yake gaya masa, beji ahigowarta ba se sautin tsakin ta daya ji kafin ta dora da fadin

“Aikin banza saboda rashin Adalci ma baza’a bar mutum ya samu lokaci da mijinsa ba se an tauye shi” dan a zaton ta da Asma’u yake wannan murmushin.

Mamaki ne ya kamashi, seya janye wayar daga kunnensa bayan yayi wa Jafar sallama yana kallonta, bata bari sun hada ido ba ta nufi qofa da niyyar fita ya tsayar da ita

“Wace aikin banzan waye kuma mara Adalcin?” Ya tambayeta muryarsa a kausashe. Dukda a tsorace take amma seta dake dan Tayi amanna aikin su fa ya fara tasiri akan sa, murguda baki tayi gefe sannan tace “to in ba rashin Adalci ba nameye zata wani kiraka yanzu kuma...” bata samu qarasa ba saboda dukan daya kawowa bakinta Allah ya sota ta duge dukda haka ya same ta a goshi ta dafe gurin.

“Fita ki bani guri kafin na illata ki wawuyar yarinya” ya fada cikin tsananin bacin rai ai tuni ta fice dan tasan fushinsa tabbas dukda sau daya ya taba marinta amma bata fata abinda ze sake sakashi sauke hannunsa a jikinta dan bataji da dadi ba.

Tana fita ta kira Addah ta saka mata kuka tana gaya mata yanda sukayi, Addah data rasa abinda zatace ta danna mata Ashar kafin tace “kina zaton badan munje gaban uwarsa ba ze saurare ki da wuri ne? To wallahi in kika janyo mun asara bakiyi aiki da abinda yake jikinki ba ni dake ne” ta kashe wayar dan takaicin Amirah nema yake ya sa mata hawan jini.
Ita komai se ance mata ga yanda zatayi in banda wauta har se an ce mata ta lallabashi ma yau din nan sannan zatayi kai wannan kayan takaici da yawa suke.

Goge hawayen tayi ta shiga tunanin ya zatayi yanzu? A yanda ya fusatan nan tasan tabbas ze iya mata komai amma bazata yi asarar lokacin nan ba dan itama tana biqatar aikin nan yaci kodan ta fara zuba ikonta yanda take so, dole ganin ba mafita ta nufi dakin da taraddadin abinda zata tarar tasan dai baze daketa ba dan ba dabi’arsa bace dukan mace yanzu nema take tunzura shi harya kawo mata mari wani lokacin.

Bashir
Yana zaune a gefen gadon ya dafe kansa da hannu bibbiyu, shidai tunda ya auri yarinyar nan yai bankwana da farin ciki, idan ita bata baqan ta masa ba se taja Asma’u ta baqanta masa ta dalilin ta dama wai haka qarin auran yake ko kuka shine beyi dace data gari ba??

Yana jin sanda ta turo qofar dakin ta shigo, be dago ba dan besan kuma meze mata ba se jin saukar ihun kukanta yaji. Dagowa yayi ya kalleta tana zaune dirshen a qasa tana kuka reras ga hawaye da majina nabin fuskarta. Baqin ciki to uwar me yamata kuma ai shi ya kamata ma yayi kukan abubuwan datake qunsa masa ko.

Yaso ya shareta amma cikin jikinta da gargadin likita suka saka shi fasa yin haka saboda hawan jini ne yai sanadin dan cikin ta ya mutu a wancan lokacin. Amirah nada ciwon hauhawar jini a lokacin da mace take da ciki wanda gado tayi a gurin Addah kuma likita ya tabbatar masa shine silar mutuwar jaririn data haifa dan ita ma Addan haka takeyi.
Haihuwarta goma Amma Amira da Ummi ne kadai suka tsaya wasu tun a ciki suke mutuwa wasu data haifesu.

Dukda haka seda ya barta tayi sannan cikin tsawa ya ce mata “wai kukan na uban menene? Me nayi miki?”

Dan tsagaita kukan tayi tana jan dogayen ajiyar zuciya, seda yaja lokaci sannan ya waiwayo ya kalleta tareda miqa masa hannunsa alamar tazo da sauri kuwa ta miqe ta nufeshi gaba daya ta fada jikinsa seyai saurin dagota jin wani kamar qari qari takeyi kai harda qaurin hayaqi ma yaji,. kofar toilet ya nuna mata yana cewa “muje” ya tasata a gaba suka shiga.

Yana tsaye ya saka ta salle jikinta sau uku har gashin kanta seda ta wanke wanda rashin gyara yake hanashi abin kirki dan itama Amirah tana da gashi sedai bekai na Ma’u ba. Seda ya tabbatar da ya duba duk wani lungu da saqon da datti ze buya yaga ya fita sannan ya sata a gaba tayi brush, shidai ko iya haka aka barshi ai sakayyar da Asma’u tace se Allah ya mata gata nan yana gani.

Indai yana son kasancewa da ita ta kwanciyar hankali tofa se ya tasata tayi wanka a gabansa shi wai dama haka matan suke ne Asma’u ce daban a ciki be sani ba?
Tunda yake be tabajin wani wari daga jikinta ba koda kuwa ta kwana batayi wanka ba. Ma’u me tsafta ce komai nata a tsaftace take yinsa ita kuwa wannan har fargabar cin abincinta yakeyi.

To yarinyar da yanzu zata fito daga wanka amma kajita tana tsami, ashe da daya ke ganinta tsaf dan baya matsar tane daga nesa yake jiyo qanshin turare kawai.

Fitowa sukayi ya nuna mata mai da turare yace ta saka ta shirya ranta a dagule shikenan sunyi asarar komai yanzu amma yata iya dole tayi yanda yake so. Daga nan dai suka shige daga ciki.


Asma’u
Jafar ne ya miqa mata wayar bayan da ya kashe
“Har kun gama maganar shine ka kashe baka bani ba” ta fada tana qoqarin sake dialing dan tana so ta gaya masa zasu fita anjima se maganar Jafar din ta katseta

“Shine ya kashe ai kaman Anty Amirah ce naji tana masa magana”. Kallon yaron tayi kaman shine Bashir din wani abu na sukan zuciyarta, wato ya kashe wayar saboda matar sa tana gurin ko?

“Ai shikenan” ta fada a fili kafin ta tashi ta shige dakinta. Kwanciya tayi ta rufe idonta, tana so ta dena damuwa akan wasu abubuwan amma ta kasa.
Yanzu ne take fahimtar ba rashin tawakkali yake saka mata suyi ta tashin hankali in an musu kishiya ba Aa abinda ake ci gaba da yi maka yau da kullum yafi zafin yin Kishiyar dan shi na lokaci daya ne ya wuce amma banbancin da za’a dawwama ana nuna maka shi yake hasala zuciya har wasu su kasa shanyewa ayita tashin hankali dasu.https://chat.whatsapp.com/DpZYwM6HCjs7WDTCBPkyj0

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 11

Wannan karan dai Amirah ta samu yanda take so dan Har ranar Monday da safe da Bashir ze tafi basu sake samun sabani ba. Tayi iya qoqarinta wurin ganin ta tsaftace ko ina kaman yanda yake so shima ya sake da ita sosai ya mori weekend dinsa dukda dai a wannan bangare fa ya dade da cirewa Asma’u hula dan kuwa tayi zarra amma itama Amirah babu laifi yana samunta yanda yake so.

A bangaren girki ne dai tunda yazo be ci abincinta ba gidan Dada yake tafiya yaci na rana na dare kuma ya siyo idan ze dawo saboda shi tun usuli dama baya cin abincin me ciki gani yake wannan Amai da tofe tofen da sukeyi har cikin abincin yana shiga.

Ko Ma’u dakyar ya fara cin abincin ta lokacin da tana da cikin Aliyu shima seda ya ware lokaci ya tsaya akan ta ya tabbatar da ingancin yanda takeyin sannan ya saki zuciyarsa dukda ita bata fiya yin ciki me Amai ko tofe tofen miyau ba.

To balle wannan da kullum tana tafe da Gwangwani wani Sa’in ma tana magana bakinta cike da yawu yana zubowa seda yai dagaske ta dena yace ta ringa samun wani abun ci tana sawa a bakin ze hana taruwar yawun sannan fa ya samu lafiya se kuma liqe liqen chewing gum din da ta koma ci wani lokacin har kan kujera ko kan carpet yarda shi takeyi ba abinda ya dame ta.

Bashir Tun ranar Asabar dinnan basu sake waya da Asma’u ba, ita bata kira ba shima be kirata ba tadai yi masa text kan zasu fita ran Saturday da Sunday kaman yanda suka saba yace to tareda aika mata da kudi dukda bata tambayeshi ba.

Ranar lahadi da yamma ya dauki Amirah sukaje gidansu, A nan ya barta suka fita da Amiru qaninsa daya zo daga Katsina a ranar can yake aiki yana zaune da iyalansa. Bayan isha ta idar da Sallah tana zaune Dakin Fainusa qanwar Bashir ce da take zawarci, Fainusan bata nan taje bikin qawarta Dada kuma tana dakin Baban su Bashir taje bashi maganin sa na dare.

Bangaren shiru seda ta leqa ta tabbatar babu kowa sannan ta dannawa Addah kira dan kwatakwata bata samu sun tattauna komai ba dan Bashir na gida kusan ko yaushe in ya fita kafin tayi ayyukan ta gudun bala’insa kan ta gama ya dawo ita kuma Addah ba karatu ta iya ba bare suyi chatting Ummi ba shiri suke ba bare ta karantawa Dadan. Seda ta jera mata kira biyar sannan ta daga dan so take suyi shawarar abinda za’ayi kafin subar wurin Dada tunda itace makamin yaqin nasu.

Addahn na dagawa babu gaisuwa ba komai tace“Addah gamu a gidan Dada fa kuma da safe ze tafi haryanzu beyi maganar tafiyar tawa ba”

“Au nida naji ki muqus ai nazata komai ya kammala dama yanzu nake so nakira ki wato tunda kura tayi lafiya har kin manta dani”.

“To dai ba lefi Addah, yanzu dai ya za’ayi kinga da safe fa ze tafi”.
Motsin da ta jiyo ya saka ta saurin cewa Addah “nidai kishiga whatsapp dinki kiyimun voice na abinda zance mata dan wallahi muka bar nan kinsan dai ba iya magana zan masa ba” tayi maza ta kashe wayar.

Fainusan ce ta dawo, gaisawa kawai sukayi ta shiga hidimominta batareda ta sake koda kallon Amira ba dan basa shiri. Ta girmewa Amiran amma tunda ta Auri Bashir ya zamana dan girman da take basu ma ta dena a cewarta yanzu matsayin Yaya take a gurinsu tunda tana auran Wan su dukda dama dai tun usuli ba Kunya ce da ita ba.

Tana zaune tana duba waya kusan minti goma sega voice din Addah tayi maza ta kunna tareda saka wayar a kunne

“Kinajina bude baki zakiyi ki mata magana kice befa ce miki ki shirya ba dan haka tayi masa magana dan gaskiya fa ke kina cutuwa bazaki zauna ba” qasa rayi da murya sosai kafin tayi mata reply tace

“Addah anya kuwa Dada fa yanzu surukata ce nifa wallahi kunya nake ji”

“To dan ubanki se ki zauna ai, kina dai jin abinda Jummai yar Bori ta fada tace indai ba kusa dashi kika koma ba babu aikin mu da zeyi tasiri to tun wuri kafin wannan din da muka dan samu yayi ya sake shi kiyi ta kanki” Addah ta fada cikin masifa.

Shiru Amira tayi tana jimamin abun a ranta anya kuwa zata iya dosar Dadan dan duk wannan abun Addah ce takeyi mata yaqin amma fa yanzun ne kadai damar ta. Bata da burin daya wuce ta Mallaki Bashir ta same shi sama da yanda Anty Asma’u ta same shi.
Ita ma yaringa yawo da ita a gaban mota duk inda ze shiga ya nuna ta a matsayin matarsa ya kuma ringa nuna yana sonta a gaban kowa.

Tana zaune tana wasiqar jaki Dada ta leqo dakin, “Amirah kina zaune shiru ki fito palour kici abinci” Dadan ta fada

Da “toh” ta amsa kafin ta yunqura tabi bayan Dadan Fainusa ta rakata da harara tareda tabe baki dan taji maganar Amiran batasan dai Me Addah ta fada ba ko akan me suke maganar.

A palour kuwa Bayan Amira ta zubo abinci ta zauna tana tsakura Dada kuwa Ta maida hankalin ta kan Tv dan dama ita bame sakewa da mutane bace. Amirah ta dago yafi sau goma da niyyar yi mata magana seta kasa daga qarshe dai tayi qundumbala kamar an fuzgo maganar tace

“Dada kiyiwa Yaya Bashir magana gashi har gobe ze koma beyi zancen tafiya ta ba kuma” ta qarasa tana sunkuyar dakai ganin yanda Dadan take kallonta. Shiru Dada tayi kamar bazata tanka ba se kuma ta sauke numfashi tace

“Munyi magana da Addah na gaya mata ki zauna anan tunda tun farko da ya baku zabin jeka ka dawo ke kika qi kafin ma Asma’u ta fara aiki lokacin dan haka yanzu bana son wata fitina ta sake tasowa ki yi haquri ki zauna a inda ya ajiye ki ko dan lafiyar jikin ki ma yanzu kama ta yayi ki hada hankalin ki guri guda kiyi fatan Allah ya sauke ki lafiya”.

Seda Amirah ta harari Dada qasa qasa wanda sarai tana ankare da ita kafin tace “Toh ai Dada lokacin ma shi yace nace na fi son zama anan din Anty ze bari acan kuma yanzu ma bani nake son komawa ba ai saboda Dan sa ne nake son zama a kusa dashi”. Ido bude Dada take kallonta har ta qarasa, bata iya ce mata komai ba illah
“Allah ya rufa asiri” ta maida kai ga kallon da takeyi dan abin yafi qarfinta kuma.

Amirah jin tayi shiru ta tabbatar da bazata sake cewa wani abu ba, se sannan ta gano wautar da tayi cikin salon son kare kai ta fara cewa “Dada ba abinda kike tunani bane wallahi ni kawai...”

“Idan kin qoshi ki kai abincin kitchen zan koma gurin Alhaji in Bashir sun dawo ina can” Dada ta fada tana miqe wa jin da gaske so take ta baro wata maganar in ba haka ba menene kuma nayin bayani gaskiyar magana Addah ba tayiwa yarinyar nan goyon kirki ba ace yarinya bakinki babu control a gaban kowa ki fadi duk abinda yayi miki, Allah ya sawwaqa toh.

Tana fita Amirah ta shiga kiran Addah a waya tana dagawa ta sakat mata kuka tana cewa “Addah kin gani ko nace miki bazan iya ba kince sena mata magana gashi yanzu na bata komai”

“Dan ubanki me kika ce mata a garin yaya? Rashin hankalin naki kikayi ko ni wallahi na rasa wace Asararriyar yarinya ceke da komai baki iya siyaya da kissa ba se wauta da rashin hankali kika saka a gaba yanzu me kika ce da ita?”

Tsaf ta gaya mata yanda sukayi da Dadan, Ajiyar zuciya Addah ta sauke kafin tace “Ni na zata ma wani babban abu ne rabu da ita na lura Nafi so take ta kware mana baya amma bata isa ba wallahi yanda ta saba tursasashi yayi abu yanzun ma haka za’ayi. Ki kwantar da hankalin ki ki rabu dasu muna zaune se ya dawo ya dauke ki wallahi in sun san wata basu san wata ba kedai yi qoqari ki amshi wani abu a hannunsa a turawa Malam a qarasa aikin nan Idan muka samu yanda muke so ko ita Nafin se mun so zata ganshi” fanfo ta cigaba dayi mata da bata dabarun yanda zata wanki Bashir din kafin sukayi Sallama.

Gajia tayi da zamanta zame takwanta akan kujera bacci ya kwasheta, Bashir kuwa se qarfe goma ya dawo gidan, seda yaje sukayi sallama da iyayensa kafin ya shiga palour ya ganta harta fara bacci. Tashinta yayi suka tafi basu koyi sallama da Dada ba. Da suka isa gida ma kwanciya tayi dan baccin yaci qarfinta.

Washe gari tun Kafin a kira Assalatu ya tashi Amirah, tana qunquni tana komai seda yasa ta gyara ko ina dukda beyi datti ba tunda kwana biyun tana kula da komai. Qarfe 6 suka sauketa a qofar gidan Addah, be shiga ba dan haushin Addan yakeji haryanzu dama basu sake haduwa ba tun waccen ranar dukda har kasuwa yaje ya gaida Baban Amiran kamar yanda yakeyi duk sanda ya shigo gari, duk yanda Amiran taso ya shiga wi yayi yace ta gaisheta kawai sauri yake qarfe 7 jirginsu ze tashi sannan ya kawo 50k ya bata sukayi sallama Naziru ya kaishi Airport ya juyo da motar.

Murna gurin Addaha kaman wanda ya basu 50M. Shi dama bame kyautar kudi bane idan ze tafi dai komai ze ajiye mata na amfani sanda tana zama a gidanta Ummi taje ta tayata zama. Da ta koma tafiya gida ma be fasa ba duk qarshen wata ze sa akai Buhun shinkafa carton din taliya, macaroni da Indomie harda Mai da Maggi ga Kayan Tea sannan in ze tafi ya bata 10k kuma duk sati yana saka musu Katin waya na 1k ita da Asma’u Idan kuma zataje Asibiti Nazir ne ya ke kaita ya dawo da ita.

“Yanzu cire Goma ki riqe a hannunki bari na kirawo Malam ya turo a karba in kuma A Akawun za’a saka masa toh. Nidai Alkahiri ya hada mu da Me Keken nan shekara da shekaru muna yawon rabar da kudin mu a banza babu biyan buqata kinga rana daya mun tsinci dami a akala” Addah ta fada tana qoqarin kiran wayar Malam Wizy, kira Daya biyu ana ce mata Switch off amma bata lura bama se sake kira takeyi, wayar ta miqawa Amirah tana cewa

“Ke jimin me matar nan take cewa be wayar taqi shiga”

“A kashe take Addah” Amirah ta fada bayan ta sake kira.

“To bari mu saurara zuwa anjima na sake kira dan bazanyi wasa ba gara ayi wuta wuta a gama aikin nan bari ma Babanku ya fito inaga yau ze bamu ribar mu duk na hada a tura masa kawai a qarasa”.
Ita dai Amirah neman guri tayi ta kwanta dan bacci ne fal idonta.

Har kusan Magriba Addah na gwada layin wizy baya shiga, seta kalli Amirah dake cin Abinci a gefenta tace “Bari kiga na kira Hajia Balaraba itama tunda muka dawo ba waya da alama ta samu kan gidan se muji idan ta kama gobe mu koma kawai ko da abinda ze qara bamu ma” kai Amirah ta daga mata kawai nan ta maida akalar kiran kan Hajia Balaraba sedai itama kamar Wizy waya a kashe harta gaji ta bari akan Gobe idan Ummi ta dawo zata karbi Number Ruqayya a gurinta (Ummi tana gidan yayarsu da suke uba daya ta haihu).

Gidan Hajia Balaraba

Waccen ranar yanda suka watse suka barta ta dade a zaune a gurin tama rasa tunanin me zatayi, wai itace bata da Sa’a ne ko kuwa aikin Malam ne beyi ba? Tana zaune tana tunanin me zatayi, wannan hukuncin da Alhaji ya dauka yayi mata tsauri da yawa ta yaya ma za’ayi ta zauna bazata fita neman taimako ba? Dole da sake idan dama taqi se a kona hagu ai saqesaqen yanda zata wanke kanta ta farayi a zuciyarta har zuwa sanda taji Alhaji ya sake fitowa daga dakinsa. Cikin qarfafawa kai guiwa ta miqe tana cewa

“Alhaji kayi haquri wallahi sam ba abinda kuke tunani bane, kafin gida ne na karbo mana ba kuma iya dakinta na saka ba wallahi kaga kwana biyu unguwar nan anan fama da sace sace shi....” kallon da yake binta dashi ya sakata hadiye sauran maganar ta. A tare suka juya Gurin Dining da Ruqayya ke qoqarin zuba tuwo abinta dan tana wanka bata ma san wainar da aka toya a gidan ba.

“Mayar da miyar nan Ruqayya ki miqomin harda na shayun” ya fada murya a dake dan dukda be gani ba ya tabbatar ta saka wani abun aci ba kuma ze bar kowa yaci ba dan ba yau ta saba ba ita idan ta tashi abun tana ma ba kansa kadai yake tsaya wa ha kowa da kowa take hadawa na gidan.

Karbar flask din yayi ya shige kitchen dasu Hajia Balaraba naji tana gani ya kwarara miyar a sink din ya bi da ruwan Tea kafin ya dauraye ya kora ruwa. Idon sa ne ya sauka kan wani flask daban a ajiye ya janyo ya bude, murmushin takaici yayi zargin sa ya tabbata duk sanda tayi irin haka seta ware nata daban be bata lokaci ba ya dauka tareda sabon plate da spoon se koma Dining.

Tuwon sa ya diba ya zuba miyar ya miqawa Ruwayya ragowar yai shigewar sa daki ya bar Balaraba a tsaye da baqin ciki goma da ashirin, abincin ne sauran taqamarta taso ta lallashe shi yaci gashi yanzu ya zubar da miyar wadda ta ajiyewa kanta kuma ya kwashe duk wuyar da taci tayi girkin nan me kyau amma bata da rabo sena baqin ciki bata san sanda hawaye ya fara zubo mata ba kamar yarinya.

Dakin ta ta shige tayi kukan ta me isarta ta share, ta kuma quduri niyyar ko bataje da kanta ba se tayi aike daga yanzu ma bazata qara karbar aikin da zatayi dakanta ba gara ta samu wanda ze yi mata komai da kansa bate ma har ta kuskure asake kamata.

Washe gari tana zaune Alhaji ya shigo dakinta, wayar ta na hannunta tana shirin kiran Addah ta gaya mata yanda akayi su kuma yi shawara ya shigan. Hannu ya miqa mata ta bashi wayar cikin mamaki ta miqa masa tana tunanin to me kuma ya fatu yanzu? A gaban ta ya cire layin ya balla, kafin ya kalleta yace
“Wallahi ko da wayar

Please Login or Register in order to submit comment