Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki kufce mun, ki amince dani na miki Alqawarin bazakiyi dana sanin bani amanar kanki ba. Na yarda ko bakya sona wallahi zan zauna dake qaunar da nake miki kadai ta isa ta riqe auran mu nidai kawai ki amince mun dan yardar ki kadai nake nema.

Tunda na rasa ki ban sare ba, a kullum cikin Addu'a nake idan harda Alkahiri a tsakanin mu Allah ya tabbatar dashi gashi yanzu bayan tsahon shekaru da har na sare na cire raina akan ki Allah ya karbi Addu'ata ya dawo min dake cikin rayuwata dan Allah Karki sake jefa zuciyata a cikin quncin da ta rayu dashi tsahon shekaru".

"Yusuf wai ka manta da da yanzu ba daya ba, waccen fa Asma'un daka so budurwace me qarancin shekaru yanzu kuwa kana magana ne da Asma'u da ta zama uwa haihuwa biyar fa Yusuf yaya shida a hakan kake sona?"

"Wallahi ke nake so Asma'u kedin nake so ba wata suffa taki ba. Ba aure daya ba ko haihuwa biyar ba idan mazan duniya dukka kika aura kika haifa musu Yaya zan zauna dake saboda ke nake so ba wani abu naki ba.

Yayanki kuma yayana ne Asma'u ko ban aureki ba ni zan iya riqe miki su idan har buqatar hakan ta taso ballantana ace ina auranki ai basu da wani uba kuma sama da ni. Dan girman Allah ki tausaya mun naci darajar tarin qaunar da nake miki ki bani dama na shiga rayuwarki in Allah ya yarda bazakiyi dana sani ba".

Gaba daya yabi ya daureni da jijiyoyin jikina, magiya yake mun akan na amsa zan aure shi ni kuwa na rasa me zan ce masa a lokacin.
Idan na Amsa Yusuf anya banyi gaggawa ba? Meye tabbacin da nake dashi akan zan samu banbancin rayuwa a gidansa sama da irin wadda nayi tareda Bashir?

Idan na auri wani daban yaya makomar Yayana zata kasance tunda nasan ko dama da qasa zasu hade Bashir baze taba bari dan sa yayi agolanci a wani guri ba sannan na tabbatar shika mijin da zan aura baze yarda da zama na a kusada Bashir ba idan na bar nan to yaya makoma da tarbiyyar yarana zata zama?

Kamar ya shiga zuciyata se ji nayi yace

"Nasan me kike tunanin Idan kika aureni zan dauke ki daga kusada Yaranki da aikin ki tabbas zanso hakan saboda zan buqace ki a kusa dani amma in har kinfi son zama anan din zan iya haqura na lamunce miki in har hakan ze faranta miki rainya baki nutsuwar zuciya".

Sosai ya bude mun wuta, na rasa dalilin daya sakashi ma taso mun da wannan maganar a yanzu, duk yanda naso na zille yaqi bani dama gashi ita kanta zuciyata a yau taqi bani hadin kai gurin furta kalaman da zasu saka Yusuf din ya haqura da qudurinsa akaina daga qarshe a dole muka rabu akan ya bani sati daya nayi tunani na yanke shawara akan makomar tarayyar mu.

Acewarsa mu ba yara bane da zamu zauna muna jan lokaci idan har na yarda na aminta dashi a matsayin abokin rayuwata a shirye yakeย  daya zamemin bangon jingina.

Wannan maganar ta mantar dani batun Bashir na shiga Sabon lissafi da komonton hukuncin da zan yanke akan Maganar Yusuf.

Harga Allah idan har son zuciyata ne zan zabi na koma dakina na zauna da Bashir amma ina tuna cin zarafi da wulaqancin da yayi mun ya sake ni akan yar uwata mace se naji sam koda na koma gidan sa bani da sauran wata qima ko mutunchi a idanunsa. Idan har ze iya tsinka igiyoyi biyu na auran shekara goma sha bakwai akan macen daya aura shekara uku bayana to tabbas qarasa dayar bazata yi masa wahala ba.

Amma zan miqa komai ga Allah zan nemi zabinsa duk kuma abinda yafi kwanta mun a rai zan karbe shi a matsayin zabin da Allah yayi mun wannan na qudurce a raina babu kuma bata lokaci na tashi da kaina na shiga Kitchen, ina da tukunya babba da nake girkin Sadaka a ciki nan da nan na dora Jalof din shinkafa me kyau ban dauki lokaci ba na gama na zuba a robobin take away masu murfi.

A qatuwar roba muka jera su, dakaina na dauka a mota muka fita can kan wata hanya inda daman muke kai abincin na ringa rabawa mutane Musulmao harda wadanda ba musulman ba duk wanda na bawa zance kayi mun Addu'a Allah yayi mun zabin Alkahiri a cikin rayuwata nayi hakan kuma da kyakykyawan yaqinin amsuwar Addu'ata.

BASHIR

A wani gidan abinci ya karya, rashintakamaiman gurin zuwa ya saka yayi zamansa a gurin kawai yana kallon masu shigowa suna fita.

Kusan awa daya yana zaune shidai baze ma iya cewa ga abinda yakeyi ba can dai ya miqe ya fita yana qoqarin bude motarsa yaji anyi masa sallama daga bayansa.

Waiwayawa yayi, Macece budurwa a qallah zatayi shekara Ashirin da biyar zuwa sama ba fara bace amma fatarta bata da duhu kuma ba wata shahararriyar kyakykyawa bace sedai yawan Fara'arta ya taimaka gurin fito mata da kyau me sanyi.

Sallama ta sake maimaita masa fuskar ta dauke da murmushi seya dakata daga bude motar yana qare daure tasa fuskar ya amsa ciki ciki yana kallonta.

"Sunana Zulaiha, kayi haquri fa na tsayar dakai, tun dazu naga shigowarka. Alamun ka sun nuna kana tareda damuwa qarara. Idan kana da maganin damuwarka kayiwa kanka idan kuma baka da shi to koma menene yake damunka ka fawwalawa Allah yin tagumi da zama shiru bazeyi maka magani ba" ta fada cikin murmushi tana kaiwa qarshe kuwa ta juya ta barshi a tsaye kamar ta dasa shi.

Jiki a sabule ya shiga motar, harya kunna ta kuma seya kashe cikin dakiya da jarumta ya danna kiran lambar Abubakar dan har seda ya kulle ido kafin ya kira ringin daya biyu uku aka daga Abubakar yayi sallama daga bangarensa.

Cikin faduwar gaba Bashir ya amsa sukayi shiru gaba dayansu kafin can Abubakar yace

"Wayake magana ban gane lambar ba"
"AB goge lambata kayi? Bashir ne fa" Bashir ya bashi amsa a sanyaye dan jij ko lambarsa ma bashi da ita.

"Ayya Yi haquri kasan mutanen da yawa wanne Bashir kenan? Kayi mun bayani yanda zan gane".

Seda yaja fasali a ransa ya maimaita La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin kafin yace

"Nasan ko baka da lambata ai muryata bazata bace maka ba, Bashir ne dai naka kuma Mijin qanwar ka Ma'u".

"Eh to nawa Bashir din dai ko banga lambarsa ba na haddaceta akai (sunada qani Bashir) sannan cikin qannena babu wadda take auran Miji me suna Bashir gaskiya.
Okย  kace Ma'u ko? To Ma'un dana sani a gidan mu ma bazawara ce bata da miji sedai ko idan tsohon mijinta kake nufi sunansa Bashir" Abubakar ya fada cikin irin lafazin nan na ko a jikina.

Shi kuwa Bashir har wata zufa ce ta shiga keto masa. Toh ta ina ma ze fara masa magana jin irin wannan amso shi da yake bashi yana nuna masa cewar babu sauran wani abu tsakanin su kenan yama manta dashi a babin rayuwarsa.

Daurewa yayi muryarsa har tana rawa rawa yace
"Am Abubakar na sani abubuwa da yawa sun faru a baya da sedai nace kayi haquri laifi na ne kuma na karbi kuskurena in sha Allahu zan gyara dalilin ma daya saka na kiraka yanzu kenan na baka haquri akan komai aya faru sannan na nemi shawarar ka akan yanda ya kamata na gyara sauran kura kuraina".

"Toh a taqaice dai ni abinda zan iya ce maka shine kasan hausawa sun ce yanda aka dama haka za'a sha, to nima sedai na maimaita maka hakan nace maka ka koma gefe kawai ka nade hannu ka karbi duk wani sakamako a yanda yazo maka Malam Bashir, batun laifi kuma ni bakayi mun komai ba.

Idan zan tuna ka gaya mun babu ruwana da sabgar gidanka ko dan kana auran qanwata bashi ya bani damar gaya maka abinda zakayi da wanda zaka bari ba, tundaga sannan na sake tsoka bakina a cikin sabgar gidan ka?
To na menene yabzu zaka sako ni kuma?

Ita abotar ka yanke ta tuntuni, auratayyar ma ka sakar mun qanwa to me yayi saura a tsakanin mu yanzu babu dan haka dan Allah karka sake kirana akan wani shirme naka can idan ba haka ba kaga yau na amsa ka a mutunce ko, ka tabbata idan ka sake a ranar zaka gane kuskuren ka zan sauke maka fushin shekara da shekaru dana shanye ban nuna maka ba" yana gama fadar haka ya kashe wayar sa.

Ajiyar zuciya Bashir ya sauke dan ya tsammaci fiye da hakan ai to tunda ma aka tsaya anan ai ya gode Allah har ya samu kwarin guiwar sake tun karar sa kuwa idan aka kwana biyu.

Hanyar Asibiti ya dauka ko ba komai Ya kamata ya je ya duba yanda ta kwana gashi har rana ta kwale yanzu. Yana isa tun daga farkon ward din yake jiyo tashin muryar Addah cikin masifa ga wata muryar da be tantance ta waye baita kuma ana yarbanci da alama itama masifar takeyi, kansa ya sara masa yaji kamar ma yayi kwana ya fasa shiga.

Ya akayi tazo da wuri bayan ya gayawa Samuel se yamma zeje ya daukota sannan ita dawa take fada a Asibiti kuma? Badan kar taje ta jajibo masa wata fitinar ba da juyawa zeyi ya barsu su qarata amma dole ya qarasa cikin dakin daidai sanda matar da suke fadan ta jefowa Addah irin qaramin flask din shayi na silver akayi rashin sa'a ta goce ya fadi tim akan qafar Bashir daya shiga dakin tsautsayi ashe be rufu da kyau ba kuwa ruwan zafin ya kele masa a qafa ga zafin buguwar da yayi ga azabar ruwan zafi besan sanda ya fasa qara yana sakin wayarsa da muqullin da suke hannunsa ba suka fadi qasa.๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ


WATA KISHIYAR ๐Ÿฅฐ๐Ÿ‘น
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 56

โ€œInnalillahi Addah ta qona shiโ€ Amirah dake zaune akan gado ta dora hannaye biyu akai tana fada.

โ€œKan balaโ€™i kika qona shi To wallahi kin taro ruwan dafa kanki daman ni kika so ki laโ€™anta kenanAllah ya kareni tsiyarki ta fada akan Dana ai kuwa bazamu yarda ba daganan har kotun qoliโ€ Addah ta sake hayayyaqowa matar dake tsaye tana numfarfashi.

Irin shinqimemiyar nance ta gaske, itama cikin masifa da yarbanci ta hayayyaqowa Addahn, wato da gani fadan a duhu akeyinsa dan babu me gane yaran wani a cikin su gefe kuma ga Nurses biyu da suna ta faman bada baki amma ko wacce ta kafe taqi haqura.

Cikin radadin Azaba Bashir ya juya ya fita daga dakin dan har seda ya cire takalmin qafar da ruwan ya zuba. Kai tsaye dakin likitan da yake duba Amirah ya nufa yana dingisa qafa suka ci karo dashi a hanya

โ€œYawwa Engineer wannan wace irin mata ce ka kawo mana gaba daya tazo ta tayar wa da mutane hankali kamar ta manta Asibiti tazo? Muji ka fita da ita kuma karta sake dawo mana. Kai itama matar taka bari kawai a rubuta muku sallama idan yaso ta ringa zuwa daga gida ana dubata kawaiโ€ Likita ya tare Bashir tun kafin shi yayi masa magana.

โ€œKa taimaka ka fara dubamun qafata farko ruwan zafi suka watsa munโ€ Bashir ya fada yana zama a kan kujerar dake gaban Office din likita, se likitan yayi saurin durqusawa ya kama qafar yana haskawa, Dakin wanke ciwo suka tafi Allah ya so shi qunar iya sama ce dan haka magani kawai aka saka mishi ya rubuta masa wanda ze siya yasha sannan ya gaya masa ya dan dakata da saka takalmi saboda karya takura fatar ta kwaye.

Saboda baqin ciki ko dakin be sake komawa ba yayi tafiyarsa gida a ransa yana ayyana irin abinda zeyi musu daga Addan har Amiran idan suka dawo masa gida.

Hajia Addah kuwa abinda ya faru Bayan ta dawo daga gidan Maโ€™u ranta a jagule da irin tarbar da Maโ€™un tayi mata. Sam bata taba tsammatar haka daga gareta ba saboda yanda tasan Maโ€™u da haba haba da lamarinsu ada idan suka je gidanta kamar zata goyasu saboda kirki amma yau ita tayiwa wannan korar kai tsaye ba tareda wata shakka ko shayi ba koda yake ada Suruka take a wajenta a yanzu kuwa babu sauran alaqa sedai ta kara kawai ai.

Babu abinda ya qara tayar mata da hankali irin nutsuwa da kyan da taga Maโ€™un ta qara ga uwar daula data zuba a gidan ta dan yafi na Bashir din sau biyar wallahi jifa wasu kujeru tana zama akai taji ta ta lume qa qamshi ta ko ina duk se taji ta raina gidan Bashir yanzu data dawo ba kamar zuwanta dazu ba da ta ga gidan kamar wadda taje wata Villa yanzu kuwa se taga duk ya zamar mata wani qauye dama ga rashin gyara gaba daya dai abin ya zama se a hankali.

Tana zaune ta zabga tagumi Aliyu nata buga Game dinsa dan be nuna alamar ma yaji shigowar mutum ba sega sallamar Jafar da kwandon Abinci. Bata jira ya qaraso ba ta taro shi dan dagaske yunwa takeji, badan bazata gane ta inda suka shigo unguwar bama da fita zatayi tunda da yan kudinta a jaka ta nemi abinci to Lagos kuma abinci ai se kalar wanda ta zaba zataci.

Haka ta zauna tana ci tana zubawa Maโ€™u Albarka seda ta cinye kwan nan tas da sinqin biredi ga qaton kofin data zuba shayi tayi gyatsa kafin ta dakko wayarta tana kallon Jafar tace

โ€œKai Allah dai yawa uwarku Albarka yasa kuma kuji qanta, ungo nan ka duba zakaga wata lamba da aka kira qarshe ta wani qedari ce da ubanku yace ze zo ya kaini Asibiti na duba Antyn ku kirashi maza kace na shirya idan kuma zaka rakani to se mu tafi tareโ€.

Lambar Samuel Jafar ya nemo ya kira ya gaya masa saqon Addah, yana qunquni ya amsa gashi nan zuwa dan dazu daya dakkota har suka Zo tana zabga masa masifa dukda bajin abinda take fada yake ba amma yasan zaginsa takeyi.

โ€œKai nima dai Jafaru zaka fara koyamun turancin nan tunda naga garin gaba daya kowa shi yakeyi karna fita wata rana na manta hanyar gida na rasa waze dawo daniโ€ Ta fada tana dariya bayan daya miqa mata wayar yace Samuel din yana zuwa.

โ€œAllah yasa na ki fitan ki bata daman yan yankan kai na garin nan sunfi son irin ki masifaffun tsofaffi aiโ€ Aliyu dake gaban Tv ya fada ba tareda ya juyo ya kalle ta ba, nan kuwa ta hau sababi tana fadar sedai a sace uban sa badai ita ba shege me baqin hali. Dake dangado ne kuwa ya manna mata hauka tayi tayi ba ita ta haqura ba seda Jafar ya gaya mata ga Samuel ya dawo sannan ta fita, tayi tayi su tafi tare yaqi dan yana Tsoron Maminsa haka ta kama hanya tana ci gaba da mitar ta.

Har bakin dakin da Amirah take Samuel ya rakata ta tura qofar tareda doka uwar sallama kamar me magana da yan sama dai dai nan abokiyar zaman Amiran da aka kawo jiya da daddare tana fama da matsanan cin ciwon kai dakyar aka samu tayi bacci a sannan Mahaifiyarta dake jinyarta na zaune suna hira jefi jefi da Amirah cikin harshen turanci sega sallamar Addah.

Cikin sauri tayiwa Addah data shigo tana sake jaddada sallama da qarin ko bacci sukeyi ne alamar tayi shiru da hannu tana nuna mata yarinyar da har ta fara mutsu mutsu alamar tana son farkawa.

โ€œJi wata masifa Allah ya tsaga mun baki a ringa mun alama wai nayi shiru in ke bakya amsa sallama ai ita Amiran yar musulmai ce balle kice duk kune aikin banza kaiโ€ Addah ta fada cikin daga murya tana kaiwa zaune kan kujrar dake gaban gadon Amirah kafin taci gaba da cewa

โ€œHaka kika qanjale Amirah sannu ko da yake iya jarabar Bashir kadai ta isa ta ramar dake kai wannan Bashir dai ko azababbe daga zuwana fa harya...โ€

โ€œDan Allah Addah kiyi shiru dakyar aka samu tayi bacci wallahi kanta ne yake ciwo sosaiโ€ Amirah ta katse ta kamar zatayi kuka ganin yarinyar ta fara riqe kanta da alamar ta farka daga baccin kenan. Cikin masifa Addah ta waiwaya ta kalleta tace

โ€œTo ni ina ruwana? Ni na dora mata ciwon da zaโ€™a hanani magana ko yaya ina da akwai dakin masu kudi da mutum ze zauna shi kadai me yasa basu kama can ba se kuma ni a takurani ke dallah karki qaramun bacin rai akan wanda nake cikiโ€

Kuka yarinyar ta fara dan ba ita da take ciwon kai ba ko me lafiya dole kansa ya buga irin yanda Addah take taqarqarewa yana daga murya kamar me magana da yan sama. Masifa ta shigayi ita dai matar tana ta qoqarin kama yarta dake fizge fizge ganin abin ya fara yawa yasa ta fita da gudu se gata ta dawo da Nurses guda biyu suka rufu akan yarinyar qarshe se fita da ita dga dakin sukayi saboda yanda Addah ta qiyin shiru gashi anyi anyi ta fita daga dakin taqi se zabga salallami take wai wannan wane kalar sharri ne daga zuwanta se kace wata mayya yarinya zata fara fizge fizge to Allah ya isanta.

Tana cikin sababin matar data bi bayan yarta ta tabbatar da lafiyarta ta dawo dakin ba tareda Addah ta ankare ba tayi kanta tana zazzaga mata masifa cikin yarbanci bakinta ne mutu ba itama ta shiga zaginta da Hausa Amirah dai ka tsakiya tana basu haquri amma babu meji data ga suna neman bawa hammata iska seta koma kan gado ta zabga tagumi kawai tana kallonsu da abin yayi tsamari shine matar ta jefawa Addah flask dai dai sanda Bashir ya shigo tsautsayin ya fada akan sa.

Shiru sukayi gaba daya suna kallon Bashir din daya juya ya fice daga dakin, matar ta dora hannu tana yan tsalle tsalle irin nasu tana kiran Jesus Addah ko harara ta maka mata tace

โ€œAi wallahi se mun daure ki, badai kin qona mun Da ba wato da kasheni kikayi niyya ko? To ki shirya yanzu zaโ€™a turo miki sammaci wallahiโ€ A fusace ta juya kan Amirah da duk ta rikice tace

โ€œKe kuma kukan uwar me kikeyi dallah taso muje mu ga halin da qafar take ciki idan ta sale Aradu sena qonata itama haka kawai zata nakasa mun dan Yar uwa bazan kyaleta ba.

Suna fitowa daga dakin Nurse ta taresu ta miqawa Amiran Farar takadda ta sallama dole suka koma suka hau tattare kaya.

Haka suka fito harabar Asibiti neman duniya babu motar da Aka kawo Addah balle kuma ta Bashir da daman basu saka ran ganinsa ba. A wayar Addah Amirah ta shiga kiransa dan ta gaya masa an sallame su ya turo Samuel ya kaisu gida, kiran Farko harta qaraci ringin be daga ba ana biyu kuwa aka ce mata wayar ma a kashe take.

Lambar Samuel din da Addah ta nuna mata ta kira ya daga suka gaisa kafin ma tace sake magana ya gaya mata Oga ya aikeshi Abeokuta ze kai wani saqo kamar zata rusa kuka haka ta kashe wayar suka samu qasan wata bishiya suka zauna gashiba wani gama jin qwarin jikinta tayi ba dan cikin nata bana me zafin laulayi ne ga Addah da taqi yin shiru se masifa take wai an musu wulaqanci yanzu ta ina zasu koma gida.

Dabarar sake kiran Samuel tayi akan ya gaya mata kwatancen unguwar tasu idan yaso ko Taxi ne se su hau ta kaisu, hakan akayi sukayi shahada suka hau Taxi dan Addah tana shiga ta tuna da fatan da Aliyu yayi mata dazu nan da nan ta jawo jarbi ta hau ja baki ya mutu basu suka saki ransu ba seda suka gansu a qofar Estate din kafin kowacce ta saki ajiyar zuciya.

Har qofar gida ya ajiye su, suka sauke kaya Addah ta zuge jaka ta ciro dari biyar ta bawo me Taxi ta qyafe tana jiran ya miqo mata chanji. Kallonta yayi ya kalli kudin kafin ya juya kan Amirah ya fara tambayarta kudinsa tunda ita ce mejin Turanci.

Tambayarsa tayi nawa yace mata dubu goma zasu bayar tunda Drop suka dauka ta waiwaya ta kalli Addah tace

โ€œAddah dubu goma ne kudin motar, ki bashi dan Allah idan mun shiga ciki se mu warware na gaji ni jiri nake jiโ€ ta juya zata shige cikin gida Addah ta fizgota tana cewa

โ€œDan fashi ne ya dakko mu ko yaya? Wannan tafiyar Asibitin da bata fi nayita a qafa ba inda nasan hanya ita ce zakice a bashi dubu goma saboda ubanki ne ya bani ajiyar kudin?

To banda su, dari uku nayi niyyar bayarwa shima saboda an shigo damu ciki ne amma da a bakin get ya ajiye mu dari dari zan bayar seki nemi dubu taran ki cika masaโ€ ta mayar da dari biyar din cikin jaka ta harhado yan hamsin da dari na dari uku ta watsa masa tayi gaba abinta.

Kamar Amirah zatayi kuka ta shiga roqon ta data bayar zata biyata dan ita sisi bata magani a hannunta ko a cikin gidan gashi babu motar Bashir ballantana tace yana gida zata shiga karbo ita kuwa Addah fafur taqi qara ko sile sema masifa da take zazzagawa me Taxi daya juya P cap baya yana jira yaga zasu bashi kudinsa ne ko se ya dauki mataki.

Ganin suna neman bata masa lokaci gashi wadda yaga kamar kudin a hannunta suke na neman shigewa gida yasa ya fizge jakar Addah, babu bata lokaci ya zazzage komai a qasa sega kudi kuwa suka zubo ya irigi dubu gomansa cif ya shige mota ko kula ihun barawa da Addah take zundumaqa beyi ba ya qara wuta abinsa to masu wucewa ma babu wanda ya kulasu dakyar Amirah ta turata suka shige gida se dafe kanta take daya dauki ciwo saboda balaโ€™in Addah.

A cikin gidan ma Sabon tashin hankali ta dasa mata akan kudinta ganin babu sarki se Allah yasa ta shige daki ta kullo kanta, wayarta ta shiga dubawa dan ta kira Bashir ko ze zo ya kashe wannan wutar ta ganta amma babu chaji seta jona ta shiga wanka saboda jikinta sam babu dadi.

Lokacin data fito wayar tadan caju, lambarsa ta shiga kira yanzu a kunne take amma kiran na shiga zaโ€™a katse shi ta kira yafi sau biyar qarshe dan kanta ta haqura ga yunwa tana ji amma tsoron karonsu da Addah idan ta fita palour yasa ta gwammace ta sha ruwa da wani Biscuit da yake a dakin ta kwanta ledar magungunanta kansu suna palour haka ta haqura bata sha ba.

BASHIR
Daga Asibiti kai tsaye gidan Musa ya wuce dan yanzu can kadai yake iya zuwa ya rage zafi tunda Musan shi kadai ne bashi da mata.

Cikin jimamin abinda ya sami qafarsa ya tare shi, ya ringa masa sannu kuwa qasan ransa kuwa dariya ce fal musamman dayaji wai da surukarsa ake fada tsautsayi ya fada kansa suka qonashi shi kuwa Bashir wace irin sirika yake da ita me fada da mutane a Asibiti?

A gidan ya wuni zir, duk dai hirar da sukayi akan yanda ze gyarota da Maโ€™u ne dan ya gayawa Musan yanda sukayi da Abubakar, shi ya qara bashi kwarin guiwa akan ya ci gaba da binsa yana bashi haquri wata rana ze dace sannan kar ya daga qafa a Gurin Maโ€™u duk irin wulaqanci da cin kashin da zata masa ya daure daman ance ai ramuwar gayya tafi ta gayya zafi amma idan yayi haqurin buqata ta biya shikenan shi yaci riba.

Shi ya sake bashi shawara ya ringa tura mata text na ban haquri akai akai. Gyara zama Musa yayi yaci gaba da ce masa

โ€œKaifa matsalar ka Bashir na fuskanci gaba dayanka se a hankali yar soyayyar nan naga alamar baka iyata ba se tsare gida da hade fuska kawai. Sufa mata da ka gani suna son tattali da kulawa ko baka da sisi indai mace na samun nutsuwa da Farin ciki a gurinka zata Yi haquri ta zauna dakai amma ko kafi qaruna kudi indai ta rasa wannan ba ko wacce bace dukiya take a gabanta zata iya rabuwa dakai ta tafi inda aka san darajarta

Please Login or Register in order to submit comment