Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo da baya da murmushi

Nima murmushin nayi nace "yaya dai?"
"Mantuwa nayi" ya bani Amsa yana zaro wayarsa daga Aljihu ya miqa mun
"Na manta ban karbi numbar Hajiya ba saboda ko akwai wani abu se na kiraki".

"Ai da akwai Number a jikin Letter headed dinmu, idan kana da wani enquiry seka kira" na fada ina zama akan kujerata, se ya ja kujera shima yana cewa

"Ki dai bani da kanki bata kamfani ba lambar wayarki nake so tunda dake muka qulla kasuwanci".

Irin masu tsinannen nacin nan ne, daya tasani gaba seda na bashi lamba sannan ya sarara mun, sema daya gwada kira yaga ta shiga wayata dake ajiye tayi qara sannan ya haqura ya tafi yace mun sunansa Hayatuddin.

Mamaki na ringayi me yasa yanzu Maza suke tunkarata suce na basu lambar waya wai tayaya suke gane banida aure yanzu tunda nidai babu abinda na chanza daga yanayin shigata ko mu'amala amma yanzu ranaku daddaya ne zan fita ba tareda wani ya tare ni ba, baga masu aure ba saboda tsaurin ido harda samari dan akwai ranar da na shiga Shoprite seda nayiwa wani dan banza tatas a gurin wai yazo ze biya mun kudin kayan dana siya.

Kafin na koma gida har Amnah ta shirya abincin da zasu kaiwa Bashir sanda na isa har sunyi wanka suna zaman jirana. Ina shiga suka fara sintirin zuwa tambayar yaushe zamu tafi yaushe zamu tafi dana ga zasu dame ni nace inaka sake tambayata an fasa zuwa shine na samu sa'idah, seda mukayi sallar Isha, ina cikin yafa mayafin Abayar dana saka kalar Maroon data karbi fatata kamar ka sace ni ka gudu Kiraj Yusuf ya shigo wayata.

Haka kawai naji murmushi ya kwace mun, wayar mu ta jiya da daddare na tuna dan duk yau bamuyi magana ba ya dai yi mun wani mugun text da safe dan seda muka fita break din rana ma na gani ina karantawa kuwa na goge dan ji nayi yana neman ya tsaga mun zuciya biyu bayan na rigada na saka zaran kirtani na dinketa tsaf ta yanda babu abinda ze sake hudata ya shiga.

"Ran gimbiya ya dade" ya fada cikin sakakkiyar muryar sa.
"Tareda naka" na bashi amsa ina fesa turare.

"Ki saka kadan dan Allah, bana so wasu su ringa jiye mub qamshin ki baki san irin yanda nake kishinki ba ko?" Ya fada daga cikin wayar,

Seda na janye na duba naga ko video call ne amma naga normal kirane, mamaki ya kamani ya akayi yasan me nakeyi se ji nayi yace

"Mamaki kikeyi ya akayi na sani ko, ruhina da naki a hade suke, duk abinda kike yi ina ji a jikina"

"Hakane" na bashi Amsa se ya fashe da dariya yace

"Gani a qofar gida nazo zance"
"Se dai ka daki gurbi dan bana nan"

"Kina ciki, shiryawa kikeyi zakuje duba Babansu Farida a Asibiti ya fadi jiya bashida lafiya" Yusuf ya fada.

Ko be fada mun ba nasan Ya gamu da Jafar dan shine me shegen surutu kamar ya qone akai.

"Ku fito se mu je tare na duba shi" ya sake fada kafin ya kashe wayar.

Tareda Driver sa yazo, dan hakaMota biyu mukayi tashi da tawa muka tafi.
Su Aliyu ne a motar da Driver yake ja, nida yammatan a motar Yusuf muna tafe se jansu yake da hira ni kuwa duk nabi na takura kaina sedai ya kalleni yayi murmushi har muka qarasa bayan da ya tsaya a wani guri ya siyi fruits harda kaza da ruwa da Lemo kafin muka wuce.

Tundaga qofar dakin kana iya jiyo karadin Amirah, Yaran ne suka farayin gaba nida Yusuf muka shiga a qarshe mun jera kamar wasu Mata da Miji yana rada mun yanda muka dace wai se kallon mu akeyi da murmushi a kan fuskata nayi sallama muka shiga dakin idona akan Bashir daya zabga uban tagumi kamar wanda aka cewa Dada ta mutu.

BASHIR


Please disregard the previous page 52 it was a technical error πŸ™πŸ™



*SODA COMMUNICATIONπŸ“±πŸ’»πŸ“±
*CHEAPEST & RELIABLE DATA SERVICES*πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½ with the validity of 30days at affordable price we are available 24/7 08137145294

*MTN DATA*
1GB@280βœ…
2GB@550βœ…
3GB@850βœ…
4GB@1150βœ…
5GB@ *1400* βœ…
10GB@2800βœ…

*AIRTEL DATA*
1gb@320βœ…
2gb@640βœ…
3gb@950βœ…
5gb@1600βœ…

*Pay throughπŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½*UNION BANK*
*0139814463
Khadija shehu soda*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°we are always there at ur service. WhatsApp/CallπŸ“ž08137145294🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR πŸ₯°πŸ‘Ή
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 53


BASHIR
Se gurin Azahar ya tashi daga baccin dolen da Likita ya saka shi. Jikinsa a matuqar mace yayi wanka ya saka uniform din marasa lafiya da aka bashi kafin yayi sallah ya sake komawa kan gadon ya kwanta.

Abinci Nurse din dazu ta kawo masa, loma daya yayi ya ajiye dan yanda yaji shi salam babu dandano haka yayi ta zare ido ga yunwa yana ji se Fruits ya iya sha da Yoghurt kawai har kusan qarfe uku tun yana tsammanin zuwan wani harya fitar da rai se a sannan ma ya tuna da yau Litinin ashe, be je aiki ba kuma be kira ya bada uzuri ba.

Wayarsa ya dauka ya shiga kiran Engineer Musa abokinsa, bayan sun gaisa musan yaje masa ya jiki yace masa idan sun tashi aiki zasu zo su dubashi dan Oga Abdallah ya sanar cewa yana Asibiti.

Mamaki ya ringayi da har gashi ya kwana ya hantse ana neman awa 24 da barin sa gida amma babu Amirah babu alamarta.

Yanzu ace da lissafi kuwa a Gurin nan mijinki ya fita ya kwana be dawo ba ai ko a waya ta neme shi taji lafiyarsa tunda be saba hakan ba amma ze saka ido ya gani daga nan zuwa anjima ya koma gidan se yaji abinda zata ce masa.

Yana cikin yin sallar la'asar se gata kamar an jefota dakin yana sallamewa kuwa ta dira masa mitar ya za'ayi bashida lafiya har a dauko shi a kawo ahi Asibiti sannan ne za'a gaya mata daga baya saboda bata da muhimmanci a gurinsa.

"Saboda ba'a gaya miki bane ya hanaki zuwa tun jiya kiga halin da nake ciki?" Ya fada yana tsareta da ido, seda ta zumbura baki gaba kafin tace

"To ai gani nayi ba'a buqata ta shiyasa nayi zamana nasan dai duk tsiya in ma mutuwa kayi dole a sanar mun tunda ni ce dai matarka ba wata ba" ta qarasa tana juya ido, se kawai ya girgiza kai ya koma kan gadon ya kwanta tareda rufe ido kamar me bacci.

Yana jin ta tana tambayarsa jikinsa yayi banza da ita, tayi maganar harta gaji amma kamar meyi da dutse ko motsi daga qarshe dan kanta ta miqe tana cewa
"Qila bacci yayi, bari naje waje na wasa qafata kafin ya tash" ta fice abinta.

Tana fita ya bude ido ya raka ta da harara tareda dogon tsaki, haka ya zauna rabi da rabi ido biyu da bacci saboda Allurar har sannan bata gama sakinsa ba dagoya kawai yake ya saka wa qofaΒ  idon yana dakon zuwan yaran idanze fadi gaskiya ma harda jiran Abinci yake dan na safen da yaci ya taso masa da tsohon kwadayin girkin Asma'u.

Har akayi sallar Isha Amirah na zaune tana zuba masa surutun da sam ba fahimtar ta yakeyi ba, ya hade girar sama da qasa qarin haushinsa da likita yace baze sallame shi yau ba se ya sake kwana kuma shi bega amfanin zaman nasa ba dan bazasu iya yi masa maganin abinda yake damunsa a yanzu ba.

Suna haka yaji an turo qofar yaran suka shiga, a jikinsa yaji Asma'u tana kusa dashi be gama tunanin ba kuwa ya daga kai kenan yayi kyakykyawan gani daya saka zuciyarsa ta tsallake bugu.

Har suka shigo cikin dakin idanunsa akansu, yanda take zabga murmushi shi kuma yana mata rada seka rantse da Allah su kadai ne a cikin dakin dan babu alamar wai suyi tunanin wasu na kallonsu.

"Qut" ya hadiye wani abu me tauri, lokaci daya idanun yan maza yayi jajir kaman wanda yasha duka, Fuska a washe Yusuf ya miqa masa hannu yana cewa

"Barka da dare Engineer, ya jiki kuma? Allah yasa kaffara ne"

Kallon Yusuf din yayi ya kalli fuskarsa, gaba daya ma se ya kasa bude baki dan ji yayi kamar an saka masa tsumma a a bakin, Yusuf da ya ga bashida niyyar bashi hannu ya janye yana murmushi ya waiwaya kan Amirah da itama tayi kinini da fuska yace

"Madam yame jiki? Allah ya qara sauqi toh".
"Amin" ta amsa can qasa dan gani tayi ya mata kwarjini kafin ta wurga ido gefen da Ma'u take tsaye kaman anyi mata dole tace

"Anty Ina wuni?"
"Lafiya lau, ya me jiki?" Asma'u ta amsata ba tareda ta kalle ta ba.

"Baban Ali ya qarfin jiki? Allah ya qara afuwa" Ma'u ta fada tana kallon Bashir daya zubawa Yusuf ido ganin yanda shi Yusuf din ya kafe Ma'u da wani mayan kallo kamar ze cinyeta.

Ji yakeyi kamar ya tashi ya shaqe Yusuf din kowa ma ya huta, yanzu da wannan kwalliyar ya dakko ta suka taho yana shaqar qamshin turaren? Abinda yake mallakinsa yanzu suke rabawa tareda Yusuf din.

"Asmy muje ko? Dare yana yi kuma kinga ko zama bamuyi ba muka taho" Yusuf ya fada cikin kwantar da murya kamar me magana da yaro, murmushi Ma'u tayi masa ta fara tafiya tana cewa

"Allah ya qara sauqi, Aliyu ku debo kwanukan safe ku taho dasu" tayi gaba abinta ba tareda ta sake kallonsa ba se yaran suka miqe suna yi masa seda safe suka fice gaba daya banda Aliyu.

"Zoka kwashe wannan abin daya shigo dasu" ya fada yana nuna masa ledar Fruit da kajin da Yusuf ya siyo ko yaya akayi ya gane shi ya siya se Allah.

Juyawa Aliyun yayi ya kalli Uban kafin ya bankawa Amirah harara ya juya ya fice abunaa ba tareda ya dauke ledojin ba.

"Kana kallonsa yana hararata ko? Wallahi sena ci uhan yaron nan zamu koma gida ne. Daman jiya ni kadai suka bari na kwana a gidan ka kirasu ma ka gaya musu..."

"Tashi ki fita" ya fada a tsawace har seda ta zabura ta miqe, har tayi gaba ta koma ta dauki ledar kazar tana cewa
"Idan bazaka ci ba ni na dauka dan daman banyi girki ba dazan fito" tayi gaba abinta tana ci gaba da qunquni.

Samuel da tuntuni yake jiranta a reception ya miqe rai bace ya fita tana binsa a baya, a kusan tare suka isa gida dasu Ma'u, saboda bala'in sa ido a qofar gidan ta tsaya.

Tana hangen Ma'u da Yusuf suna magana kafin sukayi sallama ya shiga motarsa Driver yaja suka wuce.

A kan kujera ta jefar da dankwali da jakarta ta zauna, gaskiya bazata sabu ba, ta yaya za'ayi ace daga rabuwar Ma'u da Bashir har ta samu madadinsa kuma dan gayu me kudi da take ganin kamar yafi Bashir din komai da komai wai me yasa a duk sanda take ganin ta taddo Ma'un seta sake tsere mata ne?

Dole ta tashi tsaye, bazata zuba ido tana kallo Asma'u tayi gaba ba, tunda har ta rabu da Bashir tana fatan ta qare rayuwarta a haka tana kallonta a matsayin da da ita take kai(Fata na gari lamiri Amirah )

ASMA'U
A qofar gida muka tsaya bayan da yara duk suka shige ciki, Kallona kawai Yusuf yake yana murmushi har seda na gaji nace

"Ni zan tafi dare yayi kuma gobe ina da aiki"

"Toh agogo, ni ban gaji da kallonki ba ai" ya fada yana gyara tsayuwa.

"Ai kuwa an kusa rufe gate kaga kwanan mota ya kamaka yau a cikin Estate" na fada ina juyawa kamar zan tafi yayi saurin shan gaba na yana cewa
"Haba hajjaju ki barni mana na kalleki, gobe fa zan tafi se nayi sati daya ban sake ganin fuskar nan taki ba".

Kamar yarinya haka na tura baki ina hararar sa qasa qasa, se ya faramun dariya yana cewa

"Kinga Asmy ta tana dawowa yanda na santa a hankali, shikenan ki shiga ki kwanta kiyi bacci amma fa kiyi mafarki na".

Murmushi nayi masa na kauce ina cewa "seda safe mun gode da zuwar mana dubiya kuma"

"Dole na dubashi dan kinsan yanzu banida masoyi sama dashi, tunda ya iya sako mun ke ai ni ya gama mun komai a rayuwa. Ina ga gobe ma zan koma na sake dubashi kafin na tafi"

"Allah ya yafe maka" na fada ina bude qofa se yayi saurin dakatar dani ya koma gurin motar sa, wata yar qaramar leda ya miqo mun na karba ina mamakin meye wannan a ciki dan qanqantar ta tayi yawa".

Godiya nayi masa na wuce, ina jin yanda yake bina da kallo har na shiga gida na kullo qofar kafin ya shiga motarsa suka tafi.

Ban tsaya ba na wuce dakina dan yaran da alama sun kwanta ma, ian shiga na zare rigar jikina ya rage Doguwar riga ta roba me siririn hannu da na saka a ciki na fada kam gado na zazzage ledar da Yusuf ya bani.

Yan qananan akwatuna ne suka fado guda biyu, na dauki na Farko na bude, wani hadadden zobe ne a ciki tsabar handa ya burgeni ban san sanda na ciro shi na zura a hannuna ba yanda ya zauna seka rantse an gwada ni kafin aka qera shi, juya hannun na ringayi ni kadai ina murmushi.

Kamar ya sani ina son zobe musamman wannan ya tafi dani, dutseb da yake ka sa ma se na ga kamar Diamond wallahi amma ya za'ayi Yusuf ya siya mun Diamond ring.

Dayan akwatin na bude shi kuma yan kunnene qanana sosai maqale dan kamar zallar dutseb nema akayisu dashi, ban bata lokaci ba na cire na kunnena na saka su.

Qanana ne sosai amma idan kaga yanda suka yi kyau a kunnena seka dauka wani babban dankunne na saka. A daren nan na ringa daukar hoton kunnena da zoben, na rasa wa zan nunawa ina shiga whatsapp naga Alawiyya a online ban bata lokaci na kuwa na tura mata da hotunan se gashi ta kirani ina dagawa ta fasamun ihu a kunne tana cewa

"Ma'u Allah ya bamu ya taki, kin shiga zawarci da qafar dama. Ashe ina da rabon ganin Diamond ido da ido a duniya ai kuwa zanzo kallo a cikin satin nan".

Dariya sosai na ringayi, indai tsokana ce ka samu Alawiyya ka gama, ban gama dariyar ba ta sake cewa

"Gobe idan zaki aiki ki saka hannun nan a gaba yanda kowa zega menene a jiki su san fa Yar uwata ta faso gari wallahi"

"Aa cire hannun zanyi nakai Museum kawai kinga afi zuwa kallo dakyau" na fada mata.
"Ke tsaya ma wai waya baki ni inata murna ban tambayeki ba, ko da yake qila nasan Yarabawan Lagos din nan ne ko kin san daman ance sun iya kashewa Mata kudi kamar hauka, nidai dan Allah ina daga gefe ki ringa tunawa da yar uwarki kinji"

"Allah ya yafe miki Alawiyya, ni seda safe wai ina Baban Dija kiketa wannan ihun a daren nan?"

"Ni ki gaya mun dan Allah wa kika samo mana" ta fada tana marairaicewa, kamar an fizgo maganar daga bakina se ji nayi nace mata

"Yusuf Wunti ne"

Ta buga ihu har seda nayi saurin cire wayar daga kunnena ina jiyo yarinyar da take goyo Afifa ta fasa kuka da alama itama ta tsorata.

"Wallahi a satin nan se nazo Lagos wannan maganar bata waya bace kai Allah na gode maka Allah na gode maka, kwanta kiyi bacci yar uwa qila gobe ki ganni kawai dan bazan iya jira ba" Ta fada cikin tsananin murna kamar wadda akayiwa kyauta kafin ma nayi magana ta kashe wayarta, murmushi nayi a fili nace

"Allah ya shirya ki Alawa"
Har na ajiye wayar se kuna na janyota na shiga rubutawa Yusuf saqo

"Nagode kwarai amma da baka wahalar da kanka ba"

"Zan iya kira?" ya dawo mun da amsa, kamar nace Aa se kuma zuciyata ta ce mun baze ji dadi ba dan haka na mayar masa da amsa
"Eh" se gashi kuwa ya kira din.

"Bana so na kira ki fara mun qorafin bacci zakiyi amma da bamuyi magana ba nasan ni yau sedai nayi kwanan zaune kawai" ya fada a hankali.

"To ai yanzu seka kwanta tunda munyi magana"

"Yanzu kuwa ranki ya dade, karki manta kiyi mafarkina zan kiraki da safe ki bani labari".

Haka mukayi sallama na kwanta rigingine ina tunani, yanda Yusuf yake yi mun tamkar wasu saurayi da budurwar da suke kan ganiyar soyayya ganai nakeyi kamar ma ya manta da na taba aure harda tarin Yaya.

Ian daga kwance ina ta faman saqa da warwara, idan naji kamar zuciyata zata karbi tayin Yusuf se kuma dayar ta bijiro mun da Bashir, ganin kaina na neman yayi ciwo yasa na tattara su duka na watsa gefe na gayyato baccin doleΒ  ina ta kallon zoben hannuna da yake qyalli a cikin duhuj dakin.

Zumbur na tashi na zauna na kunna fitilar wayata na haska cikinzoben sosai, tunawa nayi a jikin akwatin naga wani Rubutu kamar Letter A da Y anyi musu wani irin design daya ta shiga cikin daya kuma kamar na hango hakan a cikin dutsen ma ina haskawa kuwa sega wasu qanann rubutu da seka nutsu sosai zaga gansu cikin dutsen
'Yusuf loves Asma'u' aka rubata, kamar yarinya haka na qanqame hannun nan nayi bacci dashi.

BASHIR
Wani irin zafi da ciwo zuciyarsa ta ringayi masa, a da tuna kalmar saurayi da Aliyu ya gaya masa kadai take tayar masa da hankali a yanzu daya GansuΒ  a tare bashi da buqatar qarin bayani fuskokinsu kadai sun isa shaidar alaqar da take a tsakaninsu, yanzu daman Asma'u zata iya son wani namiji a rayuwarta bayan shi??

Yanzu harta manta da rayuwar da suka gina tsahon shekaru a yan kwanaki ta iya mantawa dashi ta karbi tayin wani Namiji bayan shi abinda ko a mafarki be taba tunanin faruwarsa sannan har ta iya zuwa gabansa dan ta nuna masa cewar a yanzu fa baya gabanta ta tigada ta gama da shafin rayuwarsa gaba daya.

Dafe qirjinsa yayi saboda azabar ciwon da yake masa, tun yana zaune har seda ya kwnata saboda yanda wani ciwo ya masa rubdugu lokaci daya ya shiga numfarfashi kamar me shirin mutuwa, hankali tashe Likita da Nurses suka rufu akansa domin ceto rayuwarsa.

Seda sukayi dagaske kafin bacci ya dauke shi dan fizge ruwan da aka daura masa ya ringayi seda Likitan ya sake gayyato wani suka hadu suka danne shi Akayi masa allurar baccin a jiki kafin ya kwanta lakwas yana kiran
"Asma'u karki rabu dani, wallahi ina sonki Ma'u karki zabi wani a kaina"

Cikin dare ya farka cikin ikon Allah jikin ya masa sauqi nauyin da qirjinsa yayi masa dazu ya sauka, kulolin daya gani suka tuna masa da yunwar da yake ji nan da nan ya janyo kwanukan ya bude.

Tuwon shinkafane da Miyar danyar kubewa dataji naman rago da manshanu.
Ba maganar wanke baki ya zuba ya fara ci loma biyu yayi kamar qaramin yaro ya fashe da wnai irin kuka irin wanda yake bayyanar da quncin da zuciya take ciki ya kifa kansa a qasa ya ringayi.

Likita ne ya shiga dakin dan yayi hasashen yanzu ya farka dan yaga jininsa nada qarfi Allurar bata dadewa take sakinsa yana shiga ya tarar dashi yana kuka ya isa gurinsa da sauri ya dagoshi yana cewa

"Subhanallahi meya faru badai jikin bane? Wane guri yana maka ciwo ne?"

Saitin zuciyar sa ya nuna masa, likita ya kamashi ya koma kan gadon kafin ya shiga hada na'urar dake jikin gadon ze sakawa Bashir din sw ya dakata jin Bashir din yana cewa

"Ina sonta Dr, bana so na rasata na rasa yanda zanyi ni na bata komai yanzu kuma bansan ya zan gyara ba".

Zama Likita yayi a kusa da shi ya zare farin gilashin idonsa yana kallon Bashir yace
"Daman Mace ce damuwarka, Wacece ita?"

"Asma'u, mata ta ta farko kuma uwar yayana. Likita banaan ya akayi shedan yayi mun kururuwa ba nabi rudinsa na rabu da ita wallahi ina son matata amma duk duniya kowa ya kasa fahimtata".

Shiru Likita yayi yana kallon Bashir na wani lokaci kafin ya dakko kwanon da ya saka abinci ya miqa masa yana cewa

"Kaci se muyi magana, ina zuwa" ya tashi ya fita ya barshi.

Tura abincin kawai yakeyi, wani bangare kuma yana jin kamar ya sauke nauyi daya furtawa wani cewar yana Son Asma'u. Amma me yasa likita ya tafi ko dai shina be yarda yana son nata ba kamar yanda kowa yaqi yarda dashi?

Haka ya ringa tura abincin har ya gama yasha ruwa sega Likitan ya sake shigowa hannunsa riqe da wata farar roba da gani ta magani ce.

Robar ya bude ya debo kwayoyi qanana guda biyu ya miqawa Bashir yana cewa

"Kasha, ze taimaka maka ka samu sauqin ciwon qirjin".

"Likita kaima baka yarda ina sonta ba ko? Kaima kana ganin bada gaske nakeyi ba" Bashir ya fada ganin Likita na qoqarin sake fita bece masa komai ba, se ya waiwayo yana murmushi yace

"Bani zaka gayawa ba Malam Bashir, shawara daya zan baka In dai kana so kaci gaba da rayuwa me dadi ka sauke duk wani girman kai ka nemi abinda kake so. Ita mace ba'ayi mata gadara ka hanzarta kafin lokaci ya qure maka, gobe da safe zamu sallame ka in Allah ya kaimu tunda na fuskanci ciwon so ne yake damunka mu kuma bamu da maganinsa sedai mu baka shawarar yanda zaka sauqaqawa kanka indai ba kana so ka saka kanka a hatsarin kamuwa da ciwon zuciya ba".

Haka ya kwana yana juya maganganun Likita a ransa, qarfe goma na safe aka bashi sallama, kamar mara galihu haka ya tattara Samuel yazo ya dauke shi ya kaishi gida sanda ya isa yar gasken da alama ko tashi daga bacci ma batayi ba se ya wuce dakin sa shima ya kwanta akan gado yana ci gaba da saqe saqe.

Kiran Bala ne ya shigo wayarsa, kamar ya share sedai ya daga dan haushinsa yakeji tun ranar daya katse masa kira be biyo baya ba se yau.

"Allah ya taimaki Engineer Allahh sa ban katse maka aiki ba" Bala ya fada yana yar dariya.

Shiru ya masa be damu ba yaci gaba da cewa
"Gani a Lagos na shigo yanzu, idan anjima ka tashi aiki se na shigo nan ta gurin ku"

"Banje aiki ba ina gida yau" ya fada a cunkushe

"Oh dan Allah? Ta bari yanzu naje na kama daki idan na ajiye kayana se na shigo gidan, a sanarwa Madam dam ko Karyawa banyi ba na taho" Bala ya fada daga daya bangaren, se Bashir ya ajiye wayar yana cewa

"Seka iso toh".

Wa ze gayawa tayiwa wani girki ko ya manta da wacce take a gidan sa ne yanzu yake wannan maganar. Wanka ya shiga yayi, yaji dadin zuwan Balan dan yana da buqatar wanda zasu tattauna akan lamarin Ma'u, baya so ya sake yanke hukunci ba tareda shawara ba.

Se daya Bala ya iso gidan yaciyo uwar kwalloya kamar me zuwa daurin aure. A palour suka zauna Amirah ta kawo masa ruwa da lemo daga nan ta shige daki basu sake jin duriyarta ba.

"Mutumin wai Ina Ma'u ne banji labarinta a Gombe ba ko kun daidaita ban sani ba?" Bala ya tambaya yana shan Lemo.
Bashir yaja tsaki yace
"Tana gidanda yake kusa da namu, kasan wai har Ma'u ta manta dani ta fara sabuwar rayuwa tareda wani mutum daban bani ba" ya qarasa cikin jin zafin abinda ya ke fadar.

"Dagaske kai amma naji dadi" Bala ya fada cike da murna se kuma daga baya ya gano shirmen da yayi saboda yanda yaga Bashir ya zuba masa ido yana kallonsa se yayi saurin wayancewa yana cewa

"Ina nufin naji dadi da kace tana kusa daku kaga yanda zaku fi samun daidaito da wuri kenan"

"Bazata saurare ni ba Bala, idan ta ganni nunawa take kamar bamu taba hada komai a rayuwa ba Ka bani shawara ya zanyi na dawo da Ma'u rayuwata Bala kai kafi kowa sanin ina son Matata"

"Na sani Bashir amma yanzu yayi wuri da ka nuna karayarka, kafi kowa sanin irin son da Ma'u takeyi maka na tabbata bazata taba iya rayuwa da wani namiji idan ba kai ba. Ko kaganta da wani is sedai tayi dan ka gani rabka ya baci amma na tabbatar badan wai tana son sa ko akwai wani abu a tsakanin su ba.

Ka qara haquri mutumina karka manta fa laifi tayi maka ka hukuntata idan ka karaya yanzu ka bata qofar da a gaba zata taka ka yanda take so".

"Laifin me tayi mun Bala? Nifa nayi mata laifi na

Please Login or Register in order to submit comment