Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

seya kama ka da haqqina". Tana gama fadar haka ta kashe wayar ta, bugun duniya kuma taqi dagawa.

Gaba daya ji yayi hankalinsa ya tashi, shifa duk abinda za'ayi kar a saka batun Allah ya isa. Ya fito kenan ze taho gida suka hadu da daya daga cikin Directors dinsu shima dan Gombe ne suka gaisa se yake gaya masa Gombe ze tafi yanzu.

"Sir Daman akwai jirgi yau ko a mota zaka tafi" Bashir din ya tambaye shi, se yayi murmushi yace
"Haba Engineer mota kuma a daren nan ai kayi mun fada, a jirgine His excellency yazo wani taro, kasan Abokina ne, toh na samu alfarma za'a rabani Private Jet mu tafi.

"Ai Sir ku manayan mutane ne da zan samu a rabani nima ai dana biku na dana" ya fada yana shafa kai, se Director yace "dagaske kake ko wasa se na kira Protocol naji idan ze samu".

Beyi zaton za'a samu din ba kawai ya amsa, yana kiran protocol din kuwa yace su taho yanzu su akw jira. Babu damar yayi wa Director wasa da hankali dole ya bishi suka tafi dukda shi kansa yasan be aikata daidai ba, amma yasan Asma'u tana da Fahimta, gara ya fara gyarota da Amirah sannan ya dawo kan Ma'un sa dan yasan ita bazata taba yi masa Allah ya isa ba kome zeyi mata.

A Flight mode ya saka wayarsa dan karma ta kirashi besan me zece mata ba, seda ya sauka a Gombe, yana kan hanyar zuwa gidan su ya tura mata da wannan Text din.

Sanda ya isa har sun rufe gida seda ya kira Naziru ya bude masa tukkana. Da mamaki Nazirun yake kallonsa, ya karbar masa Jakar suka shiga ciki kai tsaye ya wuce dakinsu da Jakar shi kuma Bashir ya wuce Dakin Dada dan burinsa yanzu yaga Amirah yaga halin da take ciki.

Palour babu kowa dan har sun kashe fitulu alamar sun kwanta, kai tsaye dakin Fainusa ya nufa inda yasba ze samu Amiran. Har ze tura qofar ya daka saboda tuna ba ita kadai bace a dakin baisan a yana yin da ze tarar dasu ba seya dakata.

A hankali yayi knocking, seda ya buga sau uku sannan Fainusa ta taso ta bude qofar tana hamma a zaton ta ma Dada ce, seta yi saurin saita kanta ta shiga gaishe shi, a ranta tana mamakin daga ina da tsohon daren nan kuma.

Fita tayi daga dakin ta koma palour shi kuma ya shiga. Abin mamaki matar da Tace bata iya bacci da ta kwanta mafarkin Iman takeyi se gata tana shaqar baccinta kashirban se a iya sace ta ma bata sani ba.

Tashinta ya shiga yi amma ko motsi se wasu surutaj banza data ringa masa qarshe ya haqura ya koma dakin Naziru ya kwanta dan already Nazirun ya gyara masa Gadon sa shi kuma ya koma Dakin Sa'ad ya kwanta.

Juyi ya ringa yi kawai ya kasa baccin, tunanin halin da Ma'u take ciki kawai yake. "Allah sarki Ma'una yar Aljanna nasan ke me haquri kuma zaki fahimce ni" ya fada a fili kamar yana gabanta. Dakyar ya samu yayi bacci ya qudurce a ransa dai In sha Allah gobe ko a mota ne seya tafi Lagos.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 27
Amirah
Da Asuba duk tashin da Fainusa ta ringa yiwa Amirah tayi sallah ko motsi batayi ba. Ba wai dan bata jin ta ba, A’a kawai ita ta tsani wannan tashin Asubar da sukeyi tun kafin ayi assalatu.

Tana lafe akan gado ta jiyo Fainusa tana gayawa Dada zuwan Bashir din jiya da daddare, seta miqe zaune. “Kardai ya shigo ya ganni ina sharar bacci” ta fada tana zaro ido.

“Wayyo ya zanyi yanzu” ta sake fada a fili tana tunanin mafita. Tunda akayi rasuwar take masa qaryar bata iya bacci da daddare shi yasa kullum suke raba dare suna waya se yayi dagaske take barinsa ta kwanta.

Jiyan ma abinda yasa bata kirashi ba baccin taji da wuri, seta shirya a ranta da safe in sunyi waya se tace masa ai tasan ya koma gida ne bata so ta kirashi Anty taji haushi toh yanzu gashi qilan ya ganta wai ya ma akayi be gaya mata ze zo a jiyan ba. Yanzu ita wace qaryar zata zabga masa?

Ganin ba mafita ya sakata tashi da niyyar ta yiwo alwala idonta ya sauka akan Maganin tari akan Mudubi. Nan take ta tuno ranar sadakar uku aka siyowa Yaron Anty Amina Babbar Yayar su Bashir da take aure a Bauchi, se akayi rashin sa’a aka karbo na manya dan haka bata bashi ba ta ajiye a dakin.

Da sauri ta dauke shi, seda ta leqa ta jikin qofa ta hango Dada da Fainusa suna Nafila kafin ta bude kofar Toilet a hankali ta shiga ta tuttar da fin rabin maganin a rariya kafin ta koma ta kwanta bayan ta ajiye shi saitin kanta ta bar kwalbar a bude.

Har qarfe shida tana kwance a gurin, Fainusa data gama Azkar dinta ta shiga dakin yin wanka dan zata fita gurin aiki tana koyarwa a makarantar secondary dake kusa dasu ta tarar da Amirah a bararraje tana bacci babu Alamar ta tashi tayi sallah.

“Lallai yarinyar nan, daman baki tashi bama kikayi sallar nidai naga randa zakiyi hankali” ta fada bayan da ta danawa Amirah duka a cinya ta bude ido da sauri dan dukan ya shigeta.

“Akan me zaki zo ki dakeni, Allah ya isana wallahi” ta fada tana sosa inda ta dake tan.

“Ni kike yiwa Allah ya isa mara kunyar banza kawai” Fainusa ta hayayyaqo mata, Dada da tajiyo hayaniyar tasu ta shiga da sauri tana cewa

“Bismillahi safiyar taku tayi zaku fara ba, kamar masu ganin hanjin juna yanzu kuma me akayi?”

“Dada wai fa wannan mara kunyar tunda na tashe ta da Asuba ashe bata tashi tayi sallar ba, shine yanzu fa dana shigo na sake tashinta ta fara zagina tana mun Allah ya isa”.

Bude baki Amirah tayi da niyyar magana ta hango Bashir ya turo qofa, se kawai ta fashe da kukan qarya harda sheshsheqa tana cewa

“Wallahi Dada ba haka akayi ba, ni ban ji sanda ta tashi ni ba ban ma san safiya tayi ba kawai yanzu tana shigowa ta hau dana mun duka wai na kwanta ina bacci kamar wata kafura bayan tasan ko baccin bana iyayi, kuma ni maganin mura nasha shine bacci me nauyi ya kwashe ni” ta fara qoqarin miqewa, tana sane ta ture kwalbar maganin dan sauran na ciki ya zube ita kuma ta koma dabas ta zauna a dole jiri take gani.

Sake yunqurawa tayi ta miqe se ta tafi kamar zata kife Bashir yai saurin tarota yana cewa “yi a hankali mana” nan idonsa ya saka akan kwalbar maganin, seda ya zaunar da ita kafin ya daga kwalbar yana kallonta yace “Amirah kina hauka ne, syrup kika sha saboda kin kasa bacci?”

Kuka haiqan ta saka masa tana cewa “to ni yaya ake so nayi? Bana iya bacci ni kadai nasan damuwar da nake ciki babu wanda ya damu da ni har kai din ai baka zo ba bate kasan halin da nake ciki”.

Seda ya yi qoqari ya hadiye bacin ransa, kafin ya sassauta murya yana cewa “shikenan, yanzu ki daure kiyo alwala kiyi sallah, lokaci yana qara ja” ya juya ya fita jin ana kiran wayar sa.

Seta miqe tabi bango, dab da zata shiga bayin ta waiga tareda ballawa Fainusa harara ganin babu wanda yake kallonta ta shige ciki.

Daga Dada ko har Fainu bude baki sukayi suna kallon wannan Drama, ita Dada mamakin yanda zata ce bata bacci kuma kowa babu me kula da ita, to wanne baccin ne batayi yarinyar da duk dare seta leqo su kuma ta ganta tana baccin ta qalau kai har na rana yi take, gaba daya fa jimamin na kwana biyu tayi ta ware se idan taga idon mutane ne zata wani koma kalar tausayi duk fa tana ankare da ita.

Ita kuwa Fainu Murmushin takaici tayi ta nemi gefen gado ta zauna tana cewa “Allah ya kyauta” lallai Amirah ba qaramar makira bace, kullum tana jin yanda take kalallame shi a waya tana raina masa hankali to Yayan shima ba kirki ne dashi ba bare ka gaya masa gaskiya amma dai jiki magayi.

Sanda ta fito Fainusa kawai ta tarar a dakin, bata so ba dan har wani kwararrabe fuska tayi a zatonta Bashir yana nan ganin Fainusan yasa ta saki tsaki ta dauki Hijabinta tana cewa “aikin banza mutum bashi da aiki se sa ido”.

“Wai Amirah ni sa’ar kice? Ni kike gayawa wannan dan uwarki” Fainusa ta fada tana miqewa tsaye

“Karki sake zagar mun uwa nidai” Amirah ta fada tana murguda baki,

“Idan na zaga me zakiyi?” Cewar Fainusa tana qara matso Amiran,

“Nidai karki sake zagina dai tam” Amiran ta fada kafin ta juya ta tada sallah, idan badan tsoron kar ko Bashir yana kusa ba da ramawa zatayi ai uwa bata fi uwa ba.

Kwafa Fainusa tayi, taso ta fadi wani abun da be mata ba wallahi seta tsinkawa shegiya mari idan yaso duk abinda Yayan ze yi yayi. Ai daman saboda taga tana auranshi ne yasa ta raina uban kowa ko amma zatayi maganin ta wallahi.

“Haka kawai dan mutum yana baqin cikin ana auran dan uwansa baze iya dauke kai yaga ana abin arziqi ba shine ze takurawa mutane, idan anji haushi mutum ya koma gidan mijinsa mana” Amirah ta fada daidai sanda Fainusa ta fito daga wanka.

“Idan gidan uban ki nake zaune se kice an takura miki, sannan aure da kike magana kibi a sannu qaddarar zawarci bata wuce kan uban kowa ba” tana fadar haka ta qarasa gaban mirrow ta hau shiryawa, amma tabbas yau se yar iskar yarinyar nan ta bar mata daki.

Ita Amirah zatayiwa gorin zawarci yarinyar da a shekaru ta girme mata da har shekara shida shine zata tsaya tana gaya mata wadannan maganganun dan kawai taqamarta tana auran yayanta? Tabbas dole tayi maganinta wallahi.

Ita kuwa Amirah sum sum ta fice daga dakin ganin yanda fuskar Fainusan ta chanza tasan tsaf zata iya rufeta a daki ta nada mata mugun duka. Tayi tunanin zata taradda Bashir a Palour seta ga babu kowa, zama ta tayi tana jiyo motsin Dada a Kitchen din amma hankalin ta be bata ya kamata ta shiga ta taya ta aiki ba.

Bayan Bashir ya gama amsa wayar, harya danno Number Asma’u ze kira se ya dakata. Wani nauyinta yake ji besan me ze ce mata ba idan ya kira. Seya karkata kiran zuwa Number Aliyu amma a kashe.

Dadi ma yaji da ya sameta a kashe dan qilan ya zama yana tare da Ma’un hakan kuma ze zama qari akan laifinsa.

Dakin Alhajinsu ya shiga ya same shi a zaune kan sallaya yana lazumi. Bayan sun gaisa da mamaki Baban yake tambayarsa yaushe yazo.

Seya shiga shafa qeya yana cewa “jiya da dare Baba, Engineer Sha’aban na biyo zasu taho tareda His excellency bayan mun dawo daga Delta.

“Kace ko gida ma baka je ba kayi yo nan” Baban Ya fada yana kallon fuskarsa, rasa abin cewa Bashir yayi dan haka yayi shiru kawai.

“Ka kyauta, tashi kaje” Baban ya fada ya maida hankali ya ci gaba da jan carbinsa.

Yana fitowa ya tare Naziru da ya fito daga Palour Dada da Kofin shayi a hannunsa.

“Ji mana” ya dakatar da Nazirun kafin ya fara masa magana wayar sa tayi qara. Team leader sune yake gaya masa ranar Monday suna da presentation, dan haka yau idan sun huta gobe Friday zasu hadu a office dan su tattara reports din hannun kowa” bayan sun yi sallama Bashir ya kalli Naziru yace

“Kayi mun booking morning flight gobe”.

“Ai Yaya babu jirgi fa, an samu yar matsala sun dakatar da jirgin Gombe zuwa lagos till further notice. Sedai ka hau mota kaje Kano tukunna ka tafi ta can”.

Kallon sa Bashir yayi kamar me son ganin gaskiyar maganar a fuskar sa, da hannu yayi masa alama da ya tafi, kafin ya lalubo Number Wani Agent da yake siya masa ticket ya kira.
Irin bayanin da Nazirun yayi masa dai ya maimaita se ma qari daya masa akan Yau jirgin qarfe bakwai da rabi ne se na sha biyun rana, gobe kuma babu jirgin Safe se Shidan yamma.

Godiya ya masa ya kashe wayar kafin ya shiga lissafin yanda zeyi, qarfe 10 na safe ake buqatarsa a office goben, dama babu zancen yau dan jirgin safe ya tafi yanzu kuwa qarfe takwas na safe ta gota, indai ba fiffike zeyi ba baya tunanin akwai ta yanda ze isa Kano kafin sha biyu na rana. Goben da yayi tunanin samu ance sena Magriba shida yake da Meeting qarfe goman safe to yanzu yaya zeyi??

Wai wane tsautsin ma ya saka shi tahowa yanzu gashi ya saka kansa a cakwakiya da hargitsin da yake jiransa a can gida, Mafita daya ce kawai Ya tafi a Mota in sha Allahu dai daga nan zuwa cikin dare ai ya isa. Da wannan shawara yayi Na’am dan haka ya juya ya shiga palour Dada.

Amirah na kwance akan kujera ya shiga seta miqe ta zauna tana gaishe shi, kujerar dake kallonta ya zauna ya amsa dai dai sanda Dada ta fito daga Kitchen din ta try a hannunta. Fainusa ta kwalawa kira ta fito cikin shirin fita, Try din ta bata tace ta kaiwa Alhajin su sannan ta kalli Bashir tace

“Yanzu zaka karya ne ko se an jima?”
“Eh yanzu Dada, dana gama zan kama hanya ne ma”.

Daga ita har Amirah kallonsa sukayi,
“Da wuri haka?” Dadan ta tambayeshi, se ya miqe yana cewa “Wallahi Emergency ne ya taso mun a office, kinsan jiya muka dawo toh kuma ana buqatar wasu bayanai gobe gashi na taho dasu nan kuma babu jirgi dole mota zan bi”.

“Tab amma kaima da ganganci kake, me yasa ka taho kasan kana da ayyuka a gabanka. Yanzu a yanda hanya take zaka bi mota har Lagos, to kana da tabbacin ma zaka isa kafin goben nan ina se dare motocin suke tafiya koh?” Dada ta fada tana riqe baki.

“Addu’a za’a mana Dada In sha Allah zamu je lafiya, yanzu dana shirya zanje Tashar, Idan babu masu tafiya yanzu inaga Zan dauki Shatar mota ne kawai na tafi dan kinsan su office babu ruwan su dole na kai musu takaddun nan gobe qarfe goma”

“Toh Allah ya rufa asiri, se kije ki hada masa abin karyawar ki kai masa tunda sauri yake” Dadan ta fada tana kallon Amirah data daskare a gurin. Dakyar ta yunqura ta tashi, lallai ma. Daga zuwansa jiya da daddare zece yau ze juya, wallahi qarya yake ta tabbata babu wani kiran office kawai Matarsa ce tace ya dawo shine ze fake da wani aiki ai kuwa bazata sabu ba wallahi.

Kayanta hada ta kai masa Dakin Nazirun, sanda ta shiga yana wanka, seta nemi guri ta zauna tana jiran ya fito dan babu yanda za’ayi ta barshi ya tafi wallahi.

Da gudun bala’i ta fada jikinsa tareda fashewa da kuka lokacin daya fito daga wankan, gaba daya yayi baya kamar zasu fadi Allah ya taimaka ya dafe bango dan a bazata ta fado masa se ya tureta daga jikinsa yana cewa “ke mahaukaciyar ina ce zaki fadowa mutum haka idan da na fadi naji ciwo kuma fa, mtsw” yaja tsaki yana hararar ta.

“Yanzu dan Allah ko tausayina bazaka ji ba, daga zuwanka jiya ko zama bamuyi ba kaji damuwata ba yau zaka ce zaka tafi saboda wadda ka baro acan tafi ni, shi kenan kaje, amma sedai ka zaba ko ni ko ita wallahi dan na gaji da yanda kake nuna banbanci a tsakanin mu. Gara ka rabu dani kaje can ka zauna da matar so”.

Kallonta ya ringayi har ta kai aya. Wai ya zaba ko ita ko Ma’u shi abun ma dariya ya bashi a ransa yace “idan zabi za’a bani dole sedai na zauna da daya yarinya aike zan saitawa hanya, na rabu da Ma’u nabi ina naga haske??

A fili kuma se ya saki murmushi ya janyo ta jikinsa yace “Allah ya huci zuciyarki haba Amaryata, yanzu kina kallo ko gida banje ba jiya na taho garin nan ko iya wannan be isa ya nuna miki yanda na damu dake ba.

maganar na zaba a tsakaninku kuma ai bata taso ba kinfi kowa sanin Yanda Nake Son Ma’u, ban kuma ga abinda ze raba ni da ita ba se mutuwa sannan kema saboda ina sonki na aure ki dan haka ki dena kawo maganar rabuwata da daya daga cikin ku.

And official call na samu dole na bar garin nan a yau, idan kuma so kike a kore ni daga aikin na rasa kudin siya muku abinci shikenan”.

Qara lafewa tayi a jikinsa, taji haushin yanda ya wani fadi yana son ma’u amma ai ba qarya bane ita ma ta sani, ganin yana cikin yana yi me dadi yasa ta ce bari ta gwada sa’arta.

Tana jikinsa suka qarasa kan gadon ya zaunar da ita ya dakko mai ya fara shafawa, taya shi ta shiga yi kafin cikin muryar shagwaba tace “Yayahh”

Kallon ta yayi ba tareda ya amsa ba, ganin hankalin sa yana kanta taci gaba da cewa
“Toh naji Yaya ka tafi amma da ka gama abinda zaka yi ina jiranka ka dai san alqawarin da kayi mun ni uku nake so ma ba biyu ba” ta fada tan rufe fuskarta da hannayenta.

Murmushi yayi yace “karki damu, just be ready for me”.
Murmushin ita ma tayi kafin ta ci gaba da cewa

“Se kuma Yaya gaba daya kayan dakina an lalata su kuma...” ganin kallon da yake mata lokaci daya fuskar sa ta chanza ya sakata yin shiru,

“Uhm ina jinki kuma me” ya tambaye ta yana saka rigar sa, seta girgiza kai tace “ babu komai”

“Gara da ya zama babu komai din” ya fada yana zama ya jawo kayan abincin ya fara ci. Seda ya gama tsaf ya zuge jakarsa sannan ya kalleta yace

“Karki sake kawo mun maganar kayan dakin ki ko wani abu, saboda banyi lissafin nawa damage din nace a biya ni ba ko?
Zan tafi yanzu, zuwa gobe ki koma gida”.

Seta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace “Dan Allah yaya gidan yayi mun girma da yawa tsoro nake ji, ka barni na koma gidan Addah kaga in nace zanzauna anan ma kullum fada muke da Anty Fainusa”.

Seda ya kalleta na dan wani lokaci kafin yace “ok ki koma din, shikenan ni zan tafi”.

Ganin bata motsa daga gurin ba sema yan hawaye da take gogewa yasa yace mata

“Come on babu ko goodbye” ya fada yana dagata tsaye, light kiss ya mata kafin ya saketa yayi gaba ta bishi a baya. A qofar dakin Alhajin su taci burki, harya saka qafa jij ta tsaya yasa ya waiwayo ya kalleta

“Shigo mana” ya fada yana qarasawa ciki. Se Alhajin ya dago ya kalleshi yana murmushi yace “Amirah ce ko, ka barta kawai ban san menayi mata da bata iya zuwa mu gaisa ba”.

“Hmmm” kawai ya iya cewa sukayi Sallama da Baban yayi masa fatan sauka lafiya ya fito. Shareta yayi ya shiga dakin Dada itama sukayi sallama kafin ya fito har Naziru ya saka masa jakar sa a mota.

Tana bayansa kamar Jela suka fita, tunda yaji bata zuwa tana gaida Baban ransa ya sake baci, gaba daya dana sanin zuwa ma yake yi dan dai babu biyan buqata se kayan takaici daya kwasa kawai haka ya shige motar Naziru yaja tana tsaye kamar ta kurma ihu, yanda suka faro a dadin rai taso su qarashe haka ko ba komai ta samu kudin kashewa yanzu gashi ya tafi da sabon fushi.

Sanda suka isa ya taki sa’ar samun qaramar mota sharon saura mutum biyu dan haka ya biya kudin mutum biyun kawai ya shiga suka dau hanya. Seda tafiya ta fara miqawa sannan ido ya raina fata.

Rabon daya je Lagos a mota kusan Shekara Goma sha biyu kenan sanda ya taba samun wani aiki har aka kirashi interview daga qarshe aka ce wai ba’a dauke shi ba.

Wannan aikin ko lokacin daya same shi da aka kirashi documentation harda ticket din jirgi Alhaji Qarami ya hada masa na zuwa da dawowa tundaga nan kuwa da Al’amura suka bude masa shida tafiyar mota sedai inda jirgi baya zuwa.

Akace tafiya yankin Azaba tabbas Bashir ya kwashi Azabar tata. Wata irin tafiya yayi da a rayuwarsa ze iya cewa be tabayin me wahalarta ba. Haka suka kwana suna tafiya sau uku kacal suka tsaya shima sallah kawai sukeyi wasu su nemi abinda zasu ci sannan a qara wuta.

Bashir dai Azumin dole yayi in banda ruwa babu abinda ya shiga cikinsa har suka Isa Lagos da Asubar Ranar Juma’a.

Firkai firkai dashi kamar wanda ya qwato daga hannun Yan Kidmashin ya shiga kwankwasa gidan bayan da Shatar Taxi din daya dauko ta sauke shi.

Lokacin Asma’u na kitchen sauran yaran kuma suna zaune a palour suna qarasa saka sport wear dinsu dan yau Juma’a. Da farko duk basu zaci gidan ake kwanwasawa ba tunda waye ze zo musu da sassafen nan shida ma yanzu tayi.

Jin Basu bude ba yasa Bashir neman dutse ya hau buga qofar kamar an aiko shi dan a yanda yake ba shida qarfin da ze fara binciko keys a jakarsa, daga ciki Asma’u ta fito daga Kitchen din tana kallon yaran da sukayi cirko cirko tace

“Waye wannan yake mana bugu kamar mara hankali” seta nufi gurin qofar. Seda ta leqa ta yar bular da ake ganin mutum, da mugun mamaki taja baya. Fuskar Bashir ce, tasan a kowanne yanayi bazata kasa gabe shi ba amma da seta ce wannan me kama da shi ne.

Qofar ta bude da sauri tayi gefe ganin yana neman fado mata ya wuce ciki bayan ya watsar da kayan sa a bakin qofar, seta kwalawa Aliyu kira ya tafi da sauri ta nuna masa kayan tana cewa “shigar masa dasu dakinsa” ta juya ciki tana mamakin daga ina yake.

Bashir kuwa Yana shiga ya zube akan kujera, yunwa, gajiya da bacci sun hadar masa gaba daya. Kallonsa yaran suka shigayi kamar sunga baqo kafin suka gaishe shi ya daga musu kai dan baze iya bude baki ba.

Yanda Asma’u tayi kamar bata san da wanzuwarsa a gurin ba yayi bala’in bashi mamaki, shirinta ta ci gaba daya yi. Yana kallo suka qarasa cinye abin karin su yaran sukayi masa sallama suka fice gurin mota ita kuma ta shiga daki ta dakko jakar ta.

Ina sane nayi tamkar na manta dashi a gurin, yana ganin nayi hanyar qofa yai saurin dakatar da ni da muryarsa a har dashewa tayi saboda yunwa yace “Ma’u baki ganni ba zaki tafi kuma”.

Seta na dakata na kalle shi, da dan guntun murmushi a fuska ta nace “Na ganka Baban Ali ai nayi maka sannu da zuwa tunda ka shigo ko baka ji ba?”

“Hmmm” ya fada kafin ya yunqura yana cewa “Nagaji wallahi a mota na taho, gashi qarfe goma ya kamata inje office ki taimaka mun da abinda zanci bari nayi wanka”.

Se da na saki wata dariyar takaici, ina kada key din hannuna nace “wato ka rantse dai se ka biyo mota toh ai gashi dai kaji abinda ake ji. Abinci kuma akwai komai na buqata a Kitchen se ka nemawa kanka kaga mun makara ma se mun dawo” na juya nayi tafiyata ina jin yanda ya raka ni da kallo har na kulle qofar.

Wato daga dan rainin hankali se Bashir, Allah ya qara. Abinci kuwa babu komai a Freezer mun cinye kwana biyun nan kuwa ban zauna ba bare nayi ko miya ce na ajiye.

Malam Bashir kuwa dakyar ya iya miqewa ya shiga Kitchen din, ya zata ze samu ko ragowar abinda sukaci ne ya tarar da wayam, ya bude Freezer nan ma danyun nama ya tarar babu ko guntun abinci.

Cike da takaici ya bude Fridge din shima babu komai se tarkacen ruwa da lemo se wani guntun nama ya samu a foil paper ya dauka da sanyin sa da komai ya

Please Login or Register in order to submit comment