Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cinye.

Ganin fa babu mafita ga yunwa ga lokaci na sake qure masa yasa ya kunna Fanfon Kitchen din ya tari ruwan zafi, Madara da Milo ya zuba sosai ya dagawa daya ya kwankwade ya sake hada wani yasha rabi ya hango bread ya dauka ya hada, seda yaji cikin sa ya dan farfado sannan ya haqura yaja kafafuwansa ya tafi daki.

Wayar s ya fara sakawa a chaji dan tun a hanya da dare ta mutu, Yau daya se be ji haushin abinda Ma’u ta masa ba, idan da haka kawai ne tayi masa wannan wulaqancin yasan me raba su se Allah amma yau daya tuna girman nasa laifin se yaga ai ba komai tayi masa ba.

Kamar me maye haka yana layi yayi wo wanka ya fito, badan ba kwanciya zeyi ya dan rage bacci amma yasan tabbas ya kuskura ya kwanta a yanda yake jin baccin nan qila sedai ya farka yaga magriba tayi.

Bayan ya saka kayan sa ya tattara abinda ze buqata kafin ya kunna wayarsa yayi order Bolt, se ya fito qofar gidan ya zauna kamar wani Almajiri, yunwa yake ji dan ba wai ya qoshi bene kawai haqura yayi idan ya fita se yaci abincin sannnan ga bacci har ji yake kamar zazzabi ze rufe shi, haka ya hau motar suka kama hanya.

A cafeteria office din su yaci abinci, Patrick abokin aikin sa da suka shiga tare ya ringa kallonsa da mamaki ganin yanda yake lodar abinci kamar wanda ya shekara be ci ba, kasa daurewa yayi yace masa

“Bash lafiya kuwa ji yanda kake cin abinci?”

“Bazaka gane ba, rabo na da abinci tun shekaran jiya”.

Dakyar ya iya kaiwa qarshen meeting din, suna gamawa suka fita sallar Juma’a. Bayan sun dawo Office din sa ya koma ya kwanta ya ringa bacci ba shi ya farka ba se qarfe bakwai shima Security da suke bi office office ne bayan an tashi suka ga fitilar sa a kunne dan haka sukaje su duba ko lafiya tunda be saba kaiwa dare a gurin ba.

Haka ya tattara a gida ya wuce gida, da murnar sa ya shiga dan tun daga waje ya jiyo qanshin tuwo da miyar kuka harda man shanu abinka da me jin yunwa.

Ya bude qofar ya shiga, fuska a sake Ma’u tayi masa sannu da zuwa harda tambayar ya akayi yau ya dade yace bacci ne ya kwashe shi.

Da zumudinsa yai sallar magriba da Isha ya sako jallabiyya ya dawo palour aka kame akan kujera yana jira ayi masa tayij abinci ya kwashi gara amma har kusan minti goma da zaman sa yaji shiru sema harkar gaban su kawai suke.

Gyaran murya yayi yana kallon Ma’u dake dannan waya yace “Akwai abinci ne yunwa nake ji”

Seta dakata ta dago ta kalleshi da murmushi tace “ai kuwa babu dan ban san zaka dawo ba”.

“Kamar ya baki san zan dawo ba ce miki nayi zan tafi wani gurin ko yaya, sannan nida gida na ayi abinci ace baza’a a jiye mun ba saboda me? Haka fa dazu da safe kika ce mun akwai abinci na duba ko ruwan zafi baku ajiye ba” ya fada a hasale, dan ya rigada ya gama saka rai da Tuwon.

“Ko ajikina na sake gyara zama nace “Aa abin bana zafi bane bafa Baban Ali, gani nayi yanzu ai Idan zakayi tafiya baka fada seka isa inda zakaje toh gudun kar mu ringa asarar abincin yasa mukeyi dai dai cikin mu, idan kace zaka ci se a dafa dakai”.



Abubuwa sun sha kaina, idan na samu sarari zaku jini gobe idan kuma ban samu dama ba se Monday In Sha Allah 🙏🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 28


Washe Gari Asabar tunda nayi sallar Asuba na koma bacci ban farka ba se goma na safe. Ko yaya Bashir ya qare jiya oho dan tunda na gaya masa babu abinci naji ya fara jan kwafa da tsaki na kwashi qafafuna na bar musu gurin, dan karma a biyo ni a dameni seda na murzawa qofata key sannan na kwanta.

Tsaf na shirya cikin wani Material baqi doguwar riga bayan nayi wanka, tundaga dakin nake jiyo kaya kaya alamar Game suke ko ana musu akan wani abun ina bude qofata Yan biyu na suka taso da gudu suka riqe ni.

“Kai ni yunwa nake ji karku kadani me kuka ci ne” na fada ina kama hannayensu, se Ahmad yace “Indomie Yah Amna tayi mana da Tea Abbi kuma gashi can yanzu aka soya masa Irish”.

Kallon inda yake nuna mun nayi muka hada ido da Bashir daya watso mun wata harara kamar idonsa ze fado, duk yanda naso na basar seda dariya ta kufce mun dan haka na wayance ina nufar inda yake nace “Baban Ali barka da safiya, kace kaima yanzu ka tashi? Bari nazo muci dan Allah yunwa nake ji idan bamu qoshi ba se a qaro wani” nayi maganar ina jan kujerar da take kallonsa na zauna.

Ban damu da shirun daya mun ba na fara hada Tea na ina masa surutun da na tabbatar sake qular dashi nakeyi, na gama naja kwanon dankalin, sena bude baki ina kallonsa nace

“Kai Duk wannan da kai kadai zaka cinye shi?”
Can qasa kaman an fuzgo maganar daga bakinsa naji yace “Banci abinci da daddare ba jiya da yunwa na tashi”.

Kallonsa nayi, naji tausayinsa kadan dan nasan Bashir da abinci ci ne dashi kamar dan kwallo, cikin jimamai nace “Ayya meyasa ka kwanta da yunwa da ka saka Amna ko Spaghetti ce ta dafa maka ai”.

Shiru ya sake yi mun, nima ban sake magana ba na fara cin abinci na, ya rigani gamawa, seya miqe ya shiga dakinsa ba dadewa ya fito ya chanza kaya ya saka Caftan na Yadi kansa babu hula. Key din motarsa ya dauka, be mun magana ba ya fice yara suna masa a dawo lafiya.

Harya tada motar se gashi ya shigo, ko me ya tuna oho se ji nayi yana cewa “zan fita amma ba jimawa zanyi ba saura yauma karku ajiye mun lunch”.

“Wa ya isa yaqi ajiye maka, jiyan ma aka si aka samu baka ce zaka dawo ba, amma yanzu tunda munsan kana nan ai zamu girka da kai” na fada ina dan murmushi. A raina nace “da bakayi magana ba wallahi yau ma dakaga Akuya sedai ka siyo ko kayi wunin yunwa.

Jellop rice nayi da pepper soup din tarwada, sena yiwa Bashir pepper meat dan baya cin Tarwada shi se gasashshiya.

Muna cikin yin lunch Amna ta kalleni tace “Mami idan mun gama muje gidan Baba?”

“Za kuje ku dame su ko kunsan dai yau Weekend Baba yana nan zaku hana shi hutawa”.

Bashir ne yace “Baya nan Ya tafi Zamfara tun jiya, idan kun gama kuje dama yau baza mu fita ba sedai ko gobe”.

Muna gama cin abincin kuwa bayan sun tattare kwanukan suka tafi ita da Farida dasu Ahmad, Aliyu da sauran kuwa Ball suka dauka suka tafi Filin da suke bugawa gidan ya rage daga ni se Bashir.

Qin zama nayi na shiga qaqale qaqalen ayyuka dukda na fahimci nufin Bashir, ganin da yayi bani da niyyar saurar sa, ina tsaye ina goge show glass din farantai a Gurin Dining kawai naji anyi sama dani, duk yanda naso nayi tawaye a dole fushi nake amma yaqi bani dama, daman abin be kai zuci ba kuma nima nayi kewar sa nan da nan nima na bada kai bori ya hau sosai kuwa na gigita Bashir.

Ina zaune a gaban mirrow ina Busar da kaina bayan nayi wanka ya shigo dakin yana waya, ta cikin mudubin muka kalli juna murmushi me kyau da narkar da zuciya ya sakar mun kafin ya qaraso ta bayana yana taba Gashina yaci gaba da maganar sa be jima ba ya kammala seya ajiye wayar akan mirrow ya karbi Dryer yana cewa “Dama baki wahalar da kanki ba dan ba’a gama ba”

“Wasa kenan” na fada ina zaro ido, saman da yai dani yasa sauran maganar suka maqale ban samu kaina a hannun sa ba seda aka kira Magriba.

Ranar haka mukayi kwanan farin ciki duk fushin nan seda Bashir ya bi ya kore mun shi. Se wani nan nan yake dani ranar ba’ayi wata doguwar hira ba kowa ya tafi ya kwanta. Muna kwance a dakin sa nayi pillow da dantsen hannunsa yace

“Dan Allah Ma’u karki sake horani da yunwa kinji”
Dariya na sheqe kafin nace “wannan din ma bada gayya nayi ba, aka si kawai aka samu”.

Lafiya qalau muka cinye Weekend din mu ranar Monday Amnah suka fara WAEC, da yake practical suka farayi sha biyu zasu fito dan haka nace mata ta taho gida kawai idan ta gama sauran idan sun tashi Zan dakko su yanda muka saba.

Dawowar da Amnah takeyi da wuri ya sake ragemun abubuwa da yawa dan kafin mu dawo ta ci qarfin girki wani lokacin ma zata dafa musu nasu idan nazo sedai nayi wa Bashir kawai. ne da wuri.

Har aka ci sati uku banji Bashir yayi zancen zuwa Gombe ba kuma da alama ko waya basayi da Amirah ban dai sani ba ko a cikin gidan ne bayayi se ya fita waje yake kiranta.

Ranar wata Alhamis daya kama Sati hudu da dawowarsa da daddare muna kwance Text ya shigo wayarsa, Number Amirah ce dan da sunanta yayi saving, na fishi kusa da ita dan haka na miqa masa yana daga kwance se naga ya tashi zaune.

Kamar wani mara gaskiya ya kalli wayar ya kalleni muka hada ido sena basar na gyara kwanciyata daidai sanda wayar ta shiga qara alamar kira se ya tashi daga kan Gadon ya fita waje.

Tashi nayi nima na zauna, Kusan Awa daya yana wayar sa har sannan kuma bacci yaqi daukata, bawai na damu bane da kiran Aa harga Allah ina tsoron abinda ze iya zuwa ne kuma dan a duk sanda muke zaman lafiya kamar tauraruwa me wutsiya yarinyar nan seta wargazashi.

yana bude qofa nayi luf kamar me bacci, ina jinsa ya tsaya akaina yana haskani da wayar dan fitilar dakin a kashe take kafin ya zagaya ya kwanta shima.

Da Asuba yake ce mun daga Office Gombe ze wuce.
“Ai ka kwana biyu daman baka je ba, ka gaishe mana su idan zaka dawo Dan Allah zata taho mun da saqo a gurin Maman Ayman (Bilkisu) saura kace ka manta” na fada ba tareda damuwar komai ba.

Ni na hada masa dan abinda ze tafi dashi dan baya daukar kaya muka rabu salin Alin kowa ya tafi aikinsa, sanda jirginsu ze tashi ma seda ya kirani ya gayamun yanzu zasu tafi nayi masa fatan sauka lafiya mukayi sallama.

Gombe
A ranar da Bashir ya tafi itama ta koma gidan Addah cikin dacin rai. Naziru ne ya kaita bisa umarnin Dada, suna zuwa suka ci karo da Addah a qofar gida da alama fita zatayi.

“Yawwa shiga da kayan ki fito muje” Addah ta fada tana kallon Amirah, seta wuce ciki ta ajiye jakarta ta fito, Nazirun ne ya rage musu hanya har zuwa gidan wata tsohuwar qawar Addan da tace wai mijin matar ne ya rasu zata je mata gaisuwa.

Suna shiga basu zauna ba dan a shirye suka sameta itama tace su tafi. Amirah dai ranta fal mamaki toh ina zasuje haka dai ta bisu su ka hau Napep ya kaisu Tasha suka hau motar Dukku.

Bayan sun isa can ma ashe ba iya tafiyar kenan ba, Babura suka hau daga tasha suka dauki hanyar wani surququn Jeji kafin su isa kuwa jikin su ya gaya musu da iska gashi lokacin sanyi da Hazo musamman Amira dan daman doguwar rigar Abaya ce a jikinta tayi rolling da mayafin rigar har wani kadawa taji haqoranta nayi tsabar sanyi.

A wani dan qauye suka sauka da gaba daya bukkokin garin basufi shida ba, Masu Baburan suka tsayar kafin Hajia Maliya tayi musu jagora zuwa bukkar data fi kowacce girma. Sanda suka shiga ciki seda Amirah ta dawo da baya da son tabbatar da daidai take gani ko kuwa gizo idonta yake yi mata.

Wato daga waje bukkace ta kara irin ta fulani amma abin mamaki idan ka shiga tamkar ka shiga dakin wani hanshaqin me kudi. Ciki da palour ce, palour Gaba daya a malale yake da Carfet Ja me shegen laushi har wani lumewa qafarsu take a ciki ga kujeru royal an zagaye gurin dasu, yanda gurin yai dumi ya tabbatar mata harda Room heater aka kunna.

Zama sukayi ita da Addah se qarewa gurin kallo suke, Hajia Maliya kuwa da alama ta saba zuwa babu mamaki a fuskarta. Zubgurar ta Addah tayi tana cewa “Maliya ina kika kawo mu karfa muje gurin yankan kai ne”.

Dariya Hajia Maliya tayi tace “ke fa Fatu shegen tsoro ne dake” daidai nan wani dan fari dogo siririn Bafulatani ya bude qofar uwar dakin ya fito.

“Aa Hajia kune ashe tun dazu nake tsammanin zuwanku naji shiru saura kadan ma muyi sabani” ya fada yana zama a qasa inda aka qara shimfida wata darduma ga tarkacen kayan aikinsa akai.

“Mune fa Malam kasan tafiyar mutane da yawa basu shiryo da wuri bane” Hajia Maliya ta fada. Gaisawa sukayi yana tambayar ta bayan rabuwa nan suka dan taba hirar aikin da yayi mata da irin yanda taji dadinsa su Addah dai anyi tsuru.

“Wannan itace Fatu yar uwata da nayi maka baya ni wannan kuma Yarinyar tace Amirah” Hajia Maliya ta gabatar masa dasu Addah, seya gyara zama yana cewa toh toh bismillan a gurguje dan sauri nakeyi zan shiga garin ne nima zanje gidan Gomna.

Matsawa Addah tayi gabansa tace “Allah gafarta yanzu dai matsalar wannan yarinyar itace a gabana dan tawa me sauqi ce”

“Ki fadi taki kawai Hajia itama ai tana da baki zata fadi tata ko” malamin ya katseta. Se Addah ta gyara zama tace

“Malam abubuwan da yawa gaskiya amma kadan daga ciki dai kaga Kishiyoyina uku nice ta fari. Da gaba daya gidan a hannuna yake daga Alhajin har su matan ni nake juya su ko kara na ajiye wa mutumin nan be isa ya tsallake ba amma yanzu Malam karka so kaga yanda yake mun wulaqanci a gaban kowa ci mun mutunchi yakeyi yanzu duk kishiyoyi sun rainani,

gashi yayan su duk sunyi aure sun samu gidan hutu ni kuma biyu ne dani fa kacal na samu daya ta daga to gidan me mata ta fada dayar kuma yanda kasan wadda aka watsawa jinin baqar jaka ko tsayayyen an gagara samu se tarin matsiyata dake sintirin zuwa gurinta”.

“Ya sunan me gidan naki da kishiyoyin?” ya tambayeta se tayi sauri tace
“Alhaji Murtala, su kuma matsiyatan akwai Binta da Nasiba se Memuna”.

Shiru malam yayi yana ta jan carbinsa daya shafe da turare Addah se zura ido take yana kallon bakinsa da yake motsi kamar tasan abinda yakeyi, minti biyu ya dago yana kallonta yace

“Se haquri dai Hajia banajin wani aikin ki ze sake tasiri akan Mijin nan naki dan yanzu ya farka shima a tsaye yake da Addu’a da neman tsari, kishiyoyi kuma ai ke kike shiga harkar su kuma ni cikinsu banga wata da take jifanki ko wani abu ba”.

Raurau tayi kamar yarinya tace “yanzu malam babu yanda za’ayi wallahi yanzu ko dan abinda nake samu a hannun Alhaji ya dena, kwanan nan da rigima ta hadani da wata mata akan kudi, gida na da na saka yan haya ya siye ya biyata kudin ni da so nake inda yanda za’ayi ma a dawo mun da gidan”.

Dariya malam yayi yace “Hajia sama da shekara Arba’in fa kina yanda kika ga dama da bawan Allahn nan yanzu kuma Allah ya taimake shi ya kwace shi daga hannunki ki qyale shi mana.

Ki godewa Allah ma daya ci gaba da zama dake dan yana sonki idan da zaki ajiye komai ki bishi zakiji dadin zama dashi sosai Allah na tuba kwana nawa ya rage muku gaba daya ma da kike tashin hankalinki? Gida kuma inda rabonki idan ya mutu se ki samu wanda ya fishi. Bismillah matso ke” ya qarasa maganar yana nuna Amirah.

Addah zata sake magana Hajia Maliya ta riqe mata hannu tana girgiza mata kai, se tayi shiru kawai ranta gaba daya a dagule. Wannan wane irin abu ne? Yanda Maliyan ta zuzuta mata shi ta zata da tazo buqatarta ta gama biya amma tazo se wasu maganganu marasa kai aka gaya mata.

Jiki a sanyaye Amirah ta matsa gabansa, ya dago ya kalleta yana murmushi yace Hajia ya akayi?”

“Ni malam bani da wata matsala kawai so nake ya ringa so na yanda yake son matar sa”
“Kunji Asararriya ba” Addah ta katseta kamar zata kai mata duka kafin taci gaba da cewa
“Shiyasa nace ka barni nayi maka bayani malam dan wannan sallamammiya ce bata san ciwon kanta ba”.

Seda Malam yayi dariya sannan yace “toh Hajia ina jinki”. Gyara zama Addah tayi ta shiga koro bayani

“Kanaji malam, shi mijin nata Bashir Dan yar uwata ne. Da dabara muka samu har ya fara sonta ya aure ta. Toh munyi haka dan zumunchi sannan kuma ko ba komai dan na samu me taimakamun tunda ni kaga bani da Da namiji toh Amma yana da Mata.

Ita Matar Asma’u sunanta ta riga tasha kansa gaba daya abinda ya mallaka akanta yake qararwa daga ita se yayanta, shekara biyu da auran nan amma ba uwar daya tsinana mana se rashin mutunchi salo salo daga wannan se wannan kuma ita matar tasa na can kusa dashi a Lagos ita kuma wannan ya barmun ita anan se sanda yaga dama yake leqo ta nayi nayi ya maida ita can amma abin yaci tura”.

“Toh ita matar shekarar su nawa a tare kuma yayan su nawa” Malam ya tambayi Addah yana murmushi dan matar dariya ma take Bashi, se Addah ta karkace tace

“Inaga ta sha bakwai suke yanzu, haihuwar ta biyar harda tagwaye da anyi magana se ace ai ita tare suka sha talauci”. Seda Malam yayi dariyar qarfin halin Addah kafin yaja qasarsa ya baza yana cewa

“Toh yanzu Hajia in banda qin Allah irin naki ta yaya kike so ya fifita matar daya aura shekara biyu akan wadda suka shafe shekara goma sha bakwai tare Ai koda Arziqinsa ya aure su dukka su biyun bazaki taba hada shaquwar shekaru goma sha data kwananna ba sannan ga zuri’a har shida a tsakani”.

“Toh nidai malam ko ma menene dai ina so Amirah ta zama mowa a gidan sannan ya ringa sakar mata hannu yana mana bushasha idan so samu ne ma ni banqi Ma’u tabar gidan ba dan indai tana nan be zama kallai mu samu yanda muke so ba”. Addah ta fada tana hura hanci, se Malam ya dago ya kalle ta yace

“Hajia ribar musulmi ya mutu ya shiga Aljanna ni bana kashe aure sedai na qulla qilan Hajia bata gaya miki ba kinganni nan bana aiki in cutar da wani sedai nayi maka kai ka samu mafita sauran zunubai na ma sun ishe ni bazanyi dakon haqqi ba”.

Seda ya gama irga carbinsa kafin ya mayar da hankalin sa kan Amirah yace

“Ita uwar gidan naki ma tana dab da fita, sannan mijinki duk kalar asirin da zakiyi masa tasirinsa qalilan ne akan sa baze dade ba ze karye. Ko ita da kuke ganin ta mallakeshi bada Asiri bane kawai ta iya zama dashi ne amma bawai dan tana jin dadi yanda kuke zato ba.

Shawarar da zan baki itace kije ki gyara kanki ki gyara zaman ki kawai shi me son kyalekyale ne tun farko abinda ya ribace shi harya aure ki kenan kuma itama matar sa da abinda take galaba akan sa kenan amma batun ya so ki sama da ita babu shi, dan ko mutuwa tayi ba na jin akwai wadda zata iya maye masa gurbin son da yake yi mata”.

“Toh malam na gode, se kuma matsalata malam haihuwa biyu kenan nayi ta farkon bezo da raina ba ta biyun kuma sati uku da haihuwar ta koma daman bakwaini ce” Amirah ta fada a sanyaye,

“Wannan Kuma daga Allah ne itama mahaifiyarki ai haka tayi ko, randa yaso se ya baki rayayyen” ya fada yana miqewa.

Kamar anyiwa Addah Bushara da aljanna baki har kunne tace “Malam kace zata fita yaushe kenan amma bazata dawo ba ko?”

Banza yayi mata ya shiga dakin daya fito minti kadan ya dawo da daurin wata saiwa da kuma garin magani a leda ya miqawa Amirah yace “ki tafasa ki ringa sha ze gyara miki jiki wannan kumburin ya sabe tunda bakiyi wanka ba wannan kuma kisha da madara ko Kunu Allah ya qara rufa asiri amma a shawarce dai da kin nutsu dan kalar mijinki ko kinyi asiri idan baki san yanda zaki tafiyar dashi ba wahalar banza zakiyi”.

Godiya tayi masa ta miqe, Addah ta kalleta tace ina zaki je kuma?”

“Shikenan ai ko Hajia na sallame ku koda wata magana” ya fada yana kallon Hajia Maliya se Addah tayi caraftace “malam baka ce komai akan daya yar uwar tata ba batun aure babu tsayayye”.

“Shidai malamin Primary da kika qi shine mijin idan kuma kika daga za’ayi dayan biyu ko ki mutu ayi ko kuma a haife miki shege a gida” ya fada ba tareda ya kalle ta ba, se Addah ta dage qirji tace “na shiga uku Malam na mutu fa kace?”

“Hajia Da wani abu ne ko shikenan” ya sake fada yana kallon Hajia Maliya, seta miqe tana cewa “Aa babu komai malam daman yau rakiya nayo ni ai al’amura se godiya kawai, Fatu bada abin sadaka mu tafi”.

Kallonta Addah tayi da niyyar Magana Malamin ya rigata da cewa “Kuje tayi mun sadaka da kudin Allah ya yafe mun zunubaina” daga haka sukayi masa sallama suka tafi.

Seda masu babur suka sauke su a Tashar Dukku har sun shiga mota Hajia Maliya ta kalli Addah tace “Fatu bakiyi sadakar bafa ko se munje cikin gari?”

“Ke dallah rabani da dan rainin wayo, aikin me yayi mun da zanyi masa sadaka wani Allah ya yafe masa ashe yasan abinda yake babu kyau kenan” Addah ta fada a fusace dan sam ita ba abinda taso ba kenan, dukda wani sashe na ranta yayi fari da aka ce Ma’u zata fita amma ita so tayi ayi mata abinda idan ta fitan bazata dawo ba.

“Ai aikin gama ya gama tunda har kika taka kikaje gurinsa kema kin debo naki kason zunubin kuma dole ki bada kudin nan kinsan dai ba’acin kudin malamai a zauna lafiya” itama Hajia Maliya ta hayayyaqo mata.

“Gashinan nidai Allah ya saka mun” Addah ta gada tana cilla mata yan dubu dubu guda biyar, se Hajia Maliya ta cafe ta fita daga motar tana cewa “Ya saka mun dai nida na kawo ki ke da ba’a miki abun arziqi, Yara Almajirai ta samu ta bawa kudin kafin ta koma motar mintina kadan ta cika suka dauko hanya.


Da suka sauka a tasha ma sama sama sukayi sallama kowa ta kama gabanta, suna zuwa gida kuwa Amirah ta tafasa saiwar nan ta fara sha dan tafi mata magungunan da Addah ta karbo kwana ki tana ji Addan nata bala’i waya sani ko shima hadin bakine da Maliya irin nasu Wizy ita dai bata kula ba harta gaji tayi shiru dan kanta.

Suna dan yin waya da Bashir lokaci zuwa lokaci badai kamar da ba kuma yawanci da rana ne idan yana gurin aiki da ya shiga gida kota kira baya dagawa ta rasa abinda yasa. Randa ta yi masa qorafi ma seda suka samu sabani har yayi mata yaji kusan kwana hudu be kirata ba toh da yake neman shir takeyi tana so ta karbi kudi a hannunsa ta danyi wasu abubuwan shi yasa ta kira ta bashi haquri.

Kwananta uku da dawowa sukayi baquwa, Amaryace da aka kawo gidan da yake kallon nasu daman matar gidan ta rasu tun tuni se yanzu mijin ya sake aure.

Amarya Sa’ada da kadan ta girmi Amirah amma bazawarace auranta daya tana da yaya biyu ma suka rabu da mijinta cikin dan lokaci sabo sosai ya shiga tsakaninsu da Amiran da yake mijinta ba mazauni bane kusan kullum in ta gama ayyukanta se

Please Login or Register in order to submit comment