Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin gidan. gurin qarfe biyu qannen Yusuf mata da maza suka zo suka kawo mun abinci zuwan nasu kuwa yamun dadi nan suka zauna har gurin dab da magriba muna tare kafin suka tafi bayanda yammatan suka tayani muka gyara gidan tsaf na basu kwanukan suka wuce dasu bayan na bisu da kudi nace su sha mai cikin cinikin da mukayi jiya a gurin budar kai. Har sannan gogan fa ko a waya be kirani ba dana kirama kin dauka yayi shi ala dole yayi fushi. Seda akayi sallar Magriba

A gurguje na sake wanka, Ina cikin yin sallah naji an bude Get, a jikina naji cewar Yusuf ne. Har na idar na sake gyara jikina na daura dankwalin Atamfar dana saka dinkin straight gown tunda naga kayan da matarsa take sawa kenan kuma yana so to nida nake da abinda zan nuna ai se na fita qure gayun ma.

Ina shirin fitowa daga dakin jin har sannan be shigo ya turo qofa muka kusa yin karo, hannu biyu ya bude mun ban tsaya bata lokaci ba kuwa na fada jikinsa ya rungumeni yana sauke tagwayen ajiyar zuciya kamar wanda ya kwana yana kuka, a kunnena yake rada mun

"Baki san yanda nake jin ki bane Asmy shiyasa kike jamun aji yanda kikaga dama amma ki tabbata yau duk wani hukunci dana dade ina tarasu akan ki yau se na yi miki"

"To ni kuma yau me nayi maka bayan fa kashe munwaya kayi tun jiya baka neme ni ba" na fada a shagwabe bayandaya sake ni yana kallon fuskata

"Kinyi kyau, juya na gani dan Allah na kine ko ciko kikayi?" Ya fada yana ja da baya yana bina da wani kallo yanda kasan soko, hararar wasa na masa na shiga juyi a hankali ina cewa

"Shafa kaji" ai kuwa kafin na gama ya kawomun wata cafka na durqushe ina dariya ya bini cak ya dagani be ajiye ni ko ina ba se kan Gado.

Kiran sallar Isha da akayi ne ya kwace ni daga hannunsa, tare muka dauro Alwala ya wuce Masallacin da yake kusada gidan ni kuma nayi sallata a gida. Kafin ya dawo na fito na duba kayan daya shigo dasu, na saka komai a inda ya dace Kazar kuma na sake dumamata a Microwave na hado duk abinda zamu buqata na kawo falo ina zama ya shigo bakinsa dauke da sallama.

Kan kujerar dana ke zaune ya zauna bayan ya dagani ya mayar dani kan cinyarsa, yanda Yusuf yake maidani yarinya qarama yana mun dadi,

"Yunwa nake ji" ya fada yana shafa fuskata, sena riqe tasa fuskar ina cewa
"Yi haquri yanzu zan kore maka ita kaji"
"Ba yunwar abinci kadai nake ji ba Asmy, harda taki" ya sake fada yana kashe mun ido daya. Sun kuyar da kaina nayi qasa ina murmushi nace

"Duka gaba daya zan kore maka su, kai dai ka fara cin abincin yanzu sauran magana ba anan zamuyi ta ba" ina gama fada na dire qasa kafin ma yace zemun wani abi.

Tare muka ci Kazar muka sha madara cikin farin ciki, ban cuci kaina ba dan nima Yunwar nake ji, abincin dazu ba wani nutsuwa nayi naci ba saboda duk cikina a cunkushe yake seda na samu dazu na zagaya sannan cikin ya daidaita dan haka na ci Naman sosai na daddaki madara dan nasan yau kam seta Allah.

A nutse Yusuf ya ja mu mukayi sallah raka'a biyu kamar yanda Annabi yayi mana unarni dayi, bayan da muka idar ya dafa kaina yayi mana Addu'a bayan ya gama ya zauna sosai yana kallona yace
"A ina kika tsaya a karatun Addini?" Dago kaina nayi na kalleshi jin tambayar tazo mun a bazata, yo ko aurena na fari daga sallar nan bamu qara komai ba aka wuce karatu na gaba.

"Kinyi shiru kina kallona" ya sake fada yana dab murmushi, cikin sanyin murya nace
"Nayi saukar Alqur'ani me girma kuma inada haddar Izu talatin na qasa, nayi karatun Fiqhu nayi na hadisi na sauke littattafi da yawa kuma har yanzu ina kan neman Ilimi ban dena ba".

"Al-Qur'ani ya miqo mun na karba nayi bismillah na fara karanto fajin da ya bude mun, ina karanta Aya uku ya karba ya sake bude wani tsagin ya bani na karanta masa se ya karba ya ajiye yayi Bismillah cikin sautin karatunsa me dadi ya janyo mun wani tsagi daga qasa na dora daga inda ya tsaya.

Sosai ya ringa yi mun tambayoyin a cikin Fiqhu harda ma tauhidi ina bashi amsa a raina ina mamakin yanda yake kamo hadisai yana tambayata qarin bayani akansu kai Addu'a kawai nake a raina karya qureni dan naga yana neman kai gejin dan Ilimin da nake dashi.

Tabbas ko a wannan gabar na sake godewa Allah, fata nane auran Namiji me cikakken ilimin Addini domin qalubale ya kan zowa mace da sauqi a gidan aure idan har Abokin zaman ta yasan haqqoqin ubangiji a cikin zaman auran se dai nayi fatan ya zaman ya zamana yana aiki da abinda ya sani.

Addu'a mukayi muka shafa kafin ya wuce dakinsa yace idan na gama na same shi a can. Seda na sake sabon wanka bayan dana tuttuli wata zuma da Anty ta sake aiko mun da ita wai ita Emergency, ai kuwa taci sunanta dan ina wanka ina jin kamar fitsari nake yi haka na qarasa shiryawa nabi lungu da saqon jikina da hadin turaren da nake amfani dasu a irin wannan lokacin.

"Allah sarki Bashir" zuciyata ta ayyanamun se nayi saurin yin a'uziyya na dakko zumbulelen hijabi na dora akan Rigar baccin dana saka. Seda na kashe fitila da dukka soket din dakin na saka wayata a silent kafin na ajiyeta naja qofar na fita ina jin yanda zuciyata take bubbugawa na tunkarar sabuwar rayuwa, Allah yasa mu shiga a sa'a.

Yanda Yayi daidai akan gado ya jingina da Allon gadon ya wani watsa hannu ya bala'in bani dariya, kamar wani mara jini haka ya ringa bina da kallo ina ta nuqu nuqun da nima ban san na menene ba, yanzu fa shikenan bayan Bashir wani yana shirin sanin sirrina? Ina tsaye na bashi baya ban ankara ba se ji nayi ya sureni kamar wanda ya dauki kara be ajiyeni a ko ina be se a tsakiyar gadon.

"Ka bari Alwalar kwanciya bacci zanyi sena cire Hijabin na kwanta" na fada  atsorace ganin yanda gaba daya idanunsa suka birkice kamar wani wanda yasha kwaya, be saurare ni sema janyoni da yayi nida Hijabin ya shiga yamutsanu yana cewa

"An yafe miki yau ki bari yanzu zanyi miki alwalar" mutsu mutsu naci gaba dayi dan yanda ya cukuikuyeni da hijabin kamar ma numfashina ze dauke fahimtar hakan da yayi ya sakashi kama wuyan Hijabin cikin abinda befi sakan biyu ba ya ketashi se gani nayi ya sauka daga jikina gaba daya, ya sake kama rigar baccin dana saka, tafiyayyace tun daga America Anty Suhaima tayo mun aiken su amma Yusuf ya tsagata gida biyu yana cewa

"Bata da guri anan dakin, ke kadai nake son gani a shimfidata, nayi miki izinin ki saka Hijabi kawai shima saboda kar Aljanu su gabe mun surar ki" ya saki wani nishi a kunnenan kafin ya kama bakina ya shiga aikamun da wani kalar kiss me gigita kwakwalwa.

"Zan goge miki duk wani tunanin da yake kanki Asmy, daga yau bazaki sake tuna wani namiji ba bayan ni. Zan baki haddar da bazaki taba mantawa ba zaki tabbata kullum cikin bitar karatun" ya ringa sakin maganganun kamar acikin Maye ni kaina bawai ina wani fuskantar sa da kyau bane dan tuni jikina ya fara amsar saqon daya aika masa ta kowanne Angle.

Wani irin Romance yake aika mun dasu masu zafi da tikita tunani, cikin dan lokaci gaba daya muka rikice, jikina har rawa yake kamar wata farin shiga a harkar koda yake a irin makarantar Yusuf dai kam ni Farin shiga ce. Seda ya kwashe kusan mintina talatin yana Juyani son ransa kafin ya mirginoni daga qasa na dawo samansa ya sakar mun kiss akan maqogarona kafin ya kira sunanan da wani kalar sauti

"Asmyyyyyy" ya tallafe fuskata da hannu biyu yana kallon cikin ido na, gaza jure kallon nayi na rufe ido rufa sejin bakinsa nayi akan idon ya sakar mun wani kiss me qara da ya saka na bude idon babu shiri na kalle shi.

"Ki gaya mun yanzu kina sona? ina so ki gaya yanzu da kanki cewar kina sona Asmy, Ina so mu zama abu daya da yardarki, kin Amince kin yarda kin bani kanki?"

Dukda fargabar da nake ciki haka na daure se kawai na hade bakin mu guri daya da kaina na shiga mayar masa da irin martanin karatundana koya a gurinsa harma da qarin nawa Ilimin da ban samu dar bayyana shi a baya ba.

Wani qaramin ihu yayi ya sake juyani daga nan labari yasha banban, ban tashi gano wautata ba seda naji yana karanto Addu'ar saduwa da iyali kafin nayi wani Yunquri tuni ya sama wa kansa hanya me kyau ya shiga jikina, dani dashi muka saki ihu a tare, ni nawa na yanda abin yazomun a bazata ne shi kuwa na qololuwar gejin dadin da yaji ne na jinsa a wata sabuwar Duniya, babu bata lokaci ya shiga aikin lada kamar wanda akace za'a biya.

Ni Ma'u naga ikon Allah na kuma yarda da fadar da ake cewa Maza suna suka tara dagaske cikin jarumai ma akwai Jarmai. Tabbas Bashir Namiji ne na gaske dukda shi kadai na sani a rayuwata amma nasan samun irin sa se an tona se gashi tun ba'aje ko ina ba na gano tarin banbancin dayake tsakaninsa da Yusuf.

Tun ina daurewa ganin abin fa ya fara zarce na islama se na fara neman hanyar ceto dan gaba daya Yusuf ya birkice mun kamar wani mayunwacin zaki wanda ya shekara goma beci nama ba, maganganu kuwa in nace zan tsaya jin me yake fada ma batawa kaina lokaci zanyi dan na tabbata har Ahmad da Muhammad seda ya kama sunan su yayi musu godiya, seda ya kwashe kusan awa daya yana aiki akaina kafin Allah ya kwace ni a hannunsa ya samu nutsuwa bayan da yayi mun wata muguwar runguma kamar ze rabani biyu.

Kwanciya yayi a gefena muka ringa mayar da numfashi kamar wasu yan tsere kusan minti goma se jin mutum nayi yana neman komawa jikina ba shiri kuwa na bude baki na saka masa kuka dan wallahi ko daren farko na Albarka, banbancinau kawai wannan babu budurci amma gurzar dana shi ko rabin ta Bashir be mun ba.

"Kuka Asmy daga yi sau daya karki bani kunya mana, gara ki shirya dan Mijinki jarumi ne" ya fada yana qoqarin hade bakin mu guri daya amma naqi bashi dama cikin kukan nake cewa

"Naji amma yau ka barni haka wallahi ban shirya ba ni ban san haka kake ba".
Miqewa yayi ya shige Toilet, har na fara sauke ajiyar zuciya ina tunanin ya barni ne se gashi ya fito jikinsa da ruwa alamar alwala yayi kafin na sake wani yunquri ya maidamu ruwa haka ina ji ina gani Yusuf ya kusan cinye daren nan tas yana bidirinsa yanda kasan ance masa kafin safiya zan gudu ne.

Ban samu kaina a hannunsa ba seda mukayi Sallar Asuba wanda tsabar yanda qafafuna suka yi sanyi a zaune nayita ina yi ina sharar hawaye. Wai  se a sannan yake wani rawar jiki yana lallabani, ya hado mun shayi me kauri ya bani tareda pain killers da daman ya tanadi abunsa tunda yasan kalar muguntar daya shirya, ya dauke ni ya mayar dani kan gadon daya chanza shimfida kamar yar jaririya haka ya ringa juyani yana bubbuga bayana tareda huramun kunne har bacci yayi nasarar yin gaba dani.

Qarar bugun qofar da akeyi ce ta farkar dani, ina buda ido na na ganshi akwance gefena hannuna cikin nasa ya riqe dakyau yana bacci abinsa. Wani irin kyau da kwarjini naga ya qarayi mun, buga qofar da aka sakeyi da qarfi ta saka ya farka yana zare ido ya kalle ni na daga masa gira alamar nima haka naji se ya miqe ya nufi qofar yana tambayar waye

"Nice sweet ka bude" mukaji an fada daga wajen, mamaki ya kamani, wacece wannan kuma zata shigo mun har cikin gida tana kiran mijina da wani sweet?

Qofar ya bude kafin yayi wani Yunquri ta danno kai ciki tana wannan yatsinar tata tana bin dakin da kallo tace

"Qarfe kusan sha biyu baka tashi ba bayan kasan yau zan tafi kuma" ta fada tana rungume shi.

Kan bala'i lallai ma wannan matar ta cika yar rainin hankali ta qarshen lamba, yunqurawa nayi na tashi zaune kafin nayi magana Yusuf ya rigani ya ce mata

"Haba Intee meya kawo ki gidan nan? Wama ya bude miki qofa kika shigo? Kuma da ba se ki kirani a waya ba kawai se dai ki shigo mana daki kai tsaye"
Key ta zaro daga jakarta ta ta miqa masa tana cewa

"Gashi, jiya ka manta su, ka duba wayarja mana ka duba wayarka mana kaga sau nawa na kiraka, ni kaga kazo ka kaini Airport, kasan dai qarfe uku jirgin mu ze tashi idan na rasa jirgi daga nan zuwa Abuja ya kake so nayi?"

"Ki tafi Driver daya kawo ki ya kaiki mana me yasa dole se ni zan kaiki ba mun rigada munyi sallama tun jiya ba" ya fada cikin alamun bacin rai, seta ta waiwayo ta kalleni ni kuwa na saka musu ido kawai ina kallon ikon Allah ita kuma haka zamuyi da ita?

"Ki ce masa ya kaini" ta fada tana tabe baki kamar wata qaramar yarinya, se na juya na kalle shi kafin ma nayi magana yace mun

"No, babu ruwanki Asmy ki kwanta ina zuwa" yaja hannunta qii sukayi waje. Kwanciya nayi a raina ina sake jinjina wannan Al'amari, yanzu ita sangartar tata har ta kai haka kenan, wannan idan guri dayavzamu zauna ai wahalarta kadai ta ishi mutum dan da alama bata san daidai ba.

Bansan yanda suka qare ba dai se gashi ya dawo, babu alamar wani bacin rai ya dagani sama yana juyi dani kafin ya ajiye ni muka shiga Toilet, shi ya saka mun Toothpaste akan brush bayan danayi fitsari ya kunna mun fanfo na shiga wanke bakina. Tare muka gama muka fito ya sake daukata muka sauka qasa be ajiye ni ba se akan kujerar Dining inda naga an jera abinci.

"Wa yayi girki" na tambaye shi bayan dana karbi shayin daya hadamun.
"Daga gidan Hajiya aka kawo tace tana gaishe ki" ya bani amsa.

"Ina amsawa amma ya kamata a dena kawo wa haka zan ringa dafa mana"
"Kin tabbata?" Ya tambayeni na daga masa kai.

Yinin ranar naga gata me sunan gata a gurin Yusuf dukda naji a jikina nima amma na fuskanci dole indai ina son zaman lafiya dashi sena koyi juriya to wai ma duk tsahon lokacin nan ya yake da wannan matar tasa ne?

Sati daya mukayi muna cin Amarci da tsinke, koda yaushe muna tare sallah kadai take fitar da Yusuf waje dai dai da wayoyinsa ya kashe su komai tare mukeyi, ayyukan gida, wanka bacci koda yaushe ina zaune a jikinta ko muna wasanni kamar wasu qananan yara dan har wasan guje guje muke yi idan mun rasa abinyi sosai  shaquwa ta shiga tsakanin mu da soyayyar da ban taba zata zan sake yiwa wani kalarta ba.

Satin mu biyu da aure muka tafi honeymoon, seda muka shafe wata biyu muna zagaya duniya kafin muka yada zango a America yayi wa matarsa sati daya dan ni a hotel nace ya ajiyeni dukda ma bacci kadai yake mayar dashi gidan kusan kullum da ya dakko Ma'u qarama ze taho da ita gurina se dare zasu koma gida har muka cika kwana bakwai kafin muka dawo Nigeria. Cikin kwana uku muka huta aa duk wani shiri da zamuyi, Naje Gombe nayi kwana daya mukayi sallama dasu muka tattara muka wuce Abuja inda muka kafa sabuwar rayuwar mu me cike da Aminci da yarda da juna.

Watanni uku da suka biyo baya bayan Fitowar sakamakon jarabawar su Aliyu Yusuf ya sama musu Scholarship na gwamnatin tarayya shida Amnah suka tafi America inda ze karanci Fasahar Zane zane (Architecture) Amnah kuma  Pharmacy, ba'a samu wata tangarda daga Bashir ba dan a gurin Anty Suhaima zasu zauna shiyasa ni kaina lokacin da Yusuf din ya kawo mun maganar fitarsu waje ban damu ba.

Babu dadewa Bashir ya samu izinin tafiya qaro qaratu daga gurin aikin su zuwa qasar Faransa, wannan dalilin ya dawo da riqon Faridah da Jafar hannuna wanda da Goggo ta kafe akan itama sedai a barta a gidan ubanta. Suka tafi tareda Abdallah da yan biyu saboda A lokacin Jafar yana Aji biyar ne a sakandire yace baze bisu ba ze zauna ya qarasa karatunsa a nan dukda rabin zaman nasu gidan Alhaji Qarami ne duk tsarin Goggo ne wai bazasu je agolanci ba.

BAYAN SHEKARA GOMa

ALHAMDULILLAH shine abinda a kullum bana gajiya da maimaitawa tabbas na yarda ba komai da kake so a rayuwa yake zamar maka Alkahiri ba kamar dai Soyayya ta da Bashir, haka abinda kaqi a qarshe idan ka bashi dama yakan zamo wannan Alkahiri da kake ta wahalar neman sa baka samu ba.

Rayuwar aurena da Bashir, shigowar Amirah rayuwar har zuwa rabuwar mu da kumaaurena da Yusuf su kadai sun isa su zame mun izina a rayuwa. A cikin shakaru shida da auren mu da Yusuf ko nace His Excellency Governor YUSUF WUNTI mun samu qaruwar Yaya uku, na farko nayi yan biyu mace da Namiji da suka ci sunan Umar da Ruqayya se Autana Sulaiman da muke kira da Junior.

A tsahon shekarun nan a kullum tsakanina da Yusuf se godiya da sam barka dan ya isa Miji kuma uba da duk mace zata bugi qirji ta nuna shi a matsayin mijinta. Bance babu qalubale a zaman auran mu ba amma fahimtar da muke da ita ta taka muhimmiyar rawa gurin kawo daidaito a tsakanin mu dan koda wasa Yusuf be taba kwana da fushina a zuciyar sa ba haka nima.

Tuni nabar aiki ba tareda wani ya bani shawara ba, dan abin shirita ya zamar mun dole na rubuta resigning na tsayar da hankali na akan gidana na qara bunqasa kasuwanci na dan yanzu kasuwa kam se Hamdala, tuni na sake bude qaton shago a cikin Abuja na zuba kayan yara, da aka kwana biyu na sake bude Salon qaton gaske na zuba ma'aikata duk wani gayar da kwalliya na mata munayi a Gurin kuma Alhamdulillahi komai ya samu karbuwa dan Yusuf da kansa yake sake tallata ni duk abinda nake siyarwa da yaji wani yana nema ko ana zancen za'a siyo a wata qasa zece matarsa tana siyarwa, har tsokanar sa abokanan sa suke idan ana son abu ace
"Wunti Madam na siyar da kaza?"

Duk sanda dayan mu ya batawa dan uwansa, ya koya mun dabi'ar fitowa na fadi abinda yake zuciyata. Idan nayi masa laifi ze zaunar dani ya gaya mun, idan na yin fada ne ze yi mun ya nuna mun kuskure na daga nan gurin maganar ta wuce har Abada zamu koma daidai kamar babu abinda ya taba faruwa a tsakanin mu.

Haka tsakanina da Yan uwansa se sambarka, har bayan rasuwar Hajiyar su shekaru biyu da suka gabata sanadiyyar Hadarin mota daya rutsa da ita sun ci gaba da daukata a matsin Yar uwa da suka bani. Suna girmamani a matsayina na matar Yayansu nima kuma naja su a jiki ina tafiyar da kowa a yanda ya kamata.

Hajiya Intee kuwa lokaci da yawa ma ni mantawa nake ina da kishiya dan a rayuwa idan kuna jin ace mutum Zero tension to Intee kenan, ita dai barta da kallon wulaqanci wanda na lura da cewar dabi'arta ce idan aka zo batun Miji ita auro ni da akayi ma qara mata wani Yanci yayi dan ta sakar mun ragamar komai ban fi shakara ba ta tattaro Ma'u qarama aka dawo da ita Nigeria, shi kansa Mijin se ya shekara beje mata ba se randa ta bushi iska ta kirashi ko ita tazo sannan fa badan ma Allah yasaka Adali bane dana tabbata zuwa yanzu idanbe rabu da ita ba toh tabbas ita da babu zasu zama basu da banbanci a gurinsa.

Bazan gaji da buga misali da Rayuwar Yayana ba wadda a koda yaushe na daga hannu na bana sauke shi ba tareda na roqa musu kariya da shiriya a gurin Allah ba wanda Alhamdulillahi dan ubangiji ya dafamun, ya shirya mun su da shiriyar sa da kuma jajircewa irin ta mahaifinsu dan dole na Jinjinawa Bashir ta yanda abubuwan da suka faru suka zamar masa darasi babba da yayi sanadiyyar daidaituwar rayuwar sa.

Amnah tayi aure ta Auri Naziru qanin Bashir tun taba shekara ta uku a karatun ta yanzu haka suna Can American inda shima ya samu aiki harda qaruwar dansu guda daya Ahmad.


Aliyu ya gama karatunsa ya dawo dukda seda ya hada harda Masters yanzu yana ayyukan kwangila wanda Yusuf yake sakar masa sosai yake nemo masa kwangila daga ko ina dan yanzu sun dinke baka jin kansu, wani lokacin ma zezo Bauchi bazan sani ba sedai kawai Na ganshi yace Dady ne ya kirashi zeyi wani aiki.

Jafar nedai na hannun damana kuma sirikina dan fa hadin nan dagaske zamuyi shi da takwarata data zama budurwa itama yanzu saboda tana da girman jiki, shekaru sha shida idan ka ganta zaka dauka tayi Ashirin dan haka ma Babanta yace da Faridah ta qarasa karatunta ze hadasu yayi musu aure idan yaso ita Ma'u ta cigaba a gidanta.

Yan biyu na dai da Babana sun zama yayan Amarya sedai lokaci lokaci idan sun samu hutu suzo mana, Bashir ya qara aure tun banfi shekara uku da yin aure ba auri Sa'idah Bayerabiya ce yar wani babban Malami a garin Lagos macen kirki data rungumi yayana ta riqe da amana tamkar ita ta haife su.

Fadar irin tashin da sukayi da Amirah ma bata lokaci ne dan har seda tayi sanadiyyar mutuwar auranta tayi zaman shekara daya a gida dan daman akayi sa'a ta dawo Nigeria lokacin haihuwar Yarinyar da Bashir yayi mun takwara da ita wadda daga kanta har yanzu bata qara ba, dan haka koda aka fara dauki ba dadi akan zancen auran nasa a yanda na samu labari har cikin gidan su taje ta ambaci sunan uwarsa da ubansa tace idan ya haifu a cikinsu ya sake ta babu bata lokaci kuwa Dada ta kirashi a waya tace ya saketa Alhaji yace a ta fau baza'ayi haka ba.

Qarshe gidansa na Gombe ta cinnawa wuta ya qone qurmus ko tsinke ba'a fitar ba babu Arziqi ya aiko mata da saki biyu ya kuma saka aka kwace yarinyar bayan daura auransa da Amaryar sa ta wuce da ita Faransa suka ci gaba da rayuwarsu.

Seda taji jiki zawarci shekara shida kafin ya mayar da ita ya barta anan Nigeria cikin gidan su ya gyara mata bangaren Alhajinsu bayan ya rasu take zaune ana gara rayuwa babu dadi babu wahala dan taji jiki shiyasa ta yarda da duk yanda yace dan ko banza bazata taba hada zaman da irin zawarcinda tayi a gidan su ba bata da maraba da boyi boyi, kudin da zata siyi omon wanki ma gagarar ta ya ringa yi gashi ita ba wata sana'a ta iya ba babu kuma wanda yazo koda wasan yace yana sonta saboda yanda labarin abinda ta aikata ya karade ko ina harya gama zawarcin.

Addah kanta da take tsaya mata tayi duk abinda taga dama ta kanta take yi dan ta gamu da wanda ya fita iskanci, malamin daya ce tayi auran kisan wuta zeyi mata aikin da Ahaji Murtala ze mayar da ita dashi sukayi auran akan sati biyu zatayi ya saketa se gashi yanzu ana lissafin shekara kusan Tara kenan harma ta haqura rayuwa ta bida ita tana can wani surquqin qauye ya kafeta ga kishiyoyi uku shegun qauye sun tasata a gaba rayuwar ta kam yanzu ta zama abin tausayi mutum dai kawai ya tsoraci Allah a rayuwa.

Ummi qanwar Amirah tana zaune lafiya a gidan mijinta cikin rufin asirin Allah sun rungumi junansu sun zauna tamkar babu wani abu daya taba faruwa a

Please Login or Register in order to submit comment