Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya saka a Silent ya ciro daga Aljihunsa jin tanaVibrating. Ya gane Lambar da ta kira dukda babu suna, Bala ne, da mamaki ya ringa kallon wayar rabon da suyi magana tun waccen ranar kusan wata nawa yanzu, lokaci daya wani bacin rai ya taso masa na tunawa da furucin Balan akan Ma'u se kawai ya ajiye wayar ya shiga cire rigar sa yana ayyana dalilin da ze sa Bala ya kirashi a yanzu bayan abinda ya faru har yana tunanin ze sake hada wata hulda dashi ne?

Alwala ya shiga ya dauro dan an kira sallar Magriba, seda ya saka jallabiyya a jikinsa kafin ya dauki wayar har ze zura a Aljihu yaga saqo akai daga lambar Balan, tsaki yaja ya fita daga dakin yana qoqarin goge saqon dan idan ma haquri yake bashi yayi ta banza dan shi dashi dai har Abada, har ya iya kallon fuskarsa yace idan da matar daya rabu da ita zata yarda daya aureta a matsayinsa na Amininsa ai wallahi in ba muqullin Aljanna bane a hannun Bala baya sake kula shi ba shima sedai idan shi kadai yake rabawa sannan.

Iqamar da yaji an tayar ta saka shi jefa wayar a Aljihu ba tareda ya goge saqon ba ya qara saurin tafiyarsa, a masallacin suka hadu dasu Aliyu, kallo daya yayi masa ya sunkuyar da kai shima be tsawwalla ba yana kallo suka fice daga masallacin dukda yana son magana da Aliyun, dole su chanza wani plan din tunda wannan ya rushe dan baze fa zuba ido yana ji yana gani ya rasa Ma'u ba.

Seda yayi sallar Isha kafin ya kamo hanyar gida, kiran sa akayi daga gidan abincinda yayo musu order ya daga ya qara yi musu kwantance  yana kashewa saqon Bala daya bude dazu be kai ga gogewa ba ya dawo kan wayar.

"Ina tayaka baqin cikin yin wuf da tsohuwar matarka da akayi, gaskiya Bashir ka cika mara sa'a tunda har ka rasa mace Irin Asma'u"
Abinda aka rubuta a saqon kenan.

Wani tsaki yaja kamar ze tsinka harshensa ya goge saqon, ransa a bala'in ya shiga magana kamar wani sabon kamu yana cewa
"Wallahi Bala gamo na da kai baze yi kyau ba, saboda bala'i bazaka fita daga sabga ta ba ko shikenan Allah ya hadamu zaka maimaita abinda ka rubuta yanzu, nida Ma'u kuwa mutu ka raba sedai baqin ciki ya kashe duk me yinsa"

Ko gani dakyau baya yi ya haye kan step din qofar gidan sam be lura da Anty dake tsaye kamar wadda aka bawa aiki ba seda ta kira sunansa.

A dan firgice ya juya ya kalleta, fuskar ta a washe tana Murmushi me kama da dariya babu wannan hararar da take masa duk sanda suka hadu kamar zata rufe shi da duka tace

"Ai daga ciki nake ai aka ce baka nan ka tafi masallaci shiyasa nace bari na jira a nan karka dawo banga wucewarka ba".

Tsayuwarsa ya gyara ba tareda yayi magana ba yana jiran jin dame tazo kuma dan wannan murmushin nata toh Allah yasa dai ya zama Alkahiri

"Se mukaji Abin Arziqi a bazata, koda yake be zama lallai ya iso maka ba tunda muma duk yanzu saqon ya same mu kaga abin Allah daga zuwa tambayar auran Ma'u se kawai iyaye sukace a daura ayi duk wasu shiri daga baya, To me za'a jira abu ba auran budurwa ba Allah na tuba an daura aure dai akan sadaki me daraja bana tunanin ko auranta na fari ma tayi tsadar haka, kai gaskiya Ma'u tayi Goshi".

Yanda take maganar seka rantse da Allah wata qawarsu take bawa labari ko irin shaqiqin Ma'u da ze yi matuqar farin ciki da jin labarin, ta gama tsaf ta juya tana cewa

"Bari naje nima nayi sallar, kaini farin ciki yau ban ma san inda zan nufa ba wallahi Allah kenan wani ya qika da wuni wani da shekaru ze soka, gashi ta fito daga inda ba'a san darajarta ba ta shiga inda suke mararin samunta sema kaga yanda akace yan uwansa nata murna wallahi".

"Hasbunallahu wani'imal wakeel, La'ilaha'iah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" Bashir ya fada yana kaiwa qasa saboda yanda yaji qafafunsa sun gaza daukar sa gaba daya, kamar me ciwon Asthma haka numfashinsa ya shiga sarqe wa, qoqari yake ya bude baki ya dakatar da ita amma ya kasa harta bude gidan ta ta shige tana ci gaba da dariyarta.

"Ina tayaka baqin cikin Wuf da akayi da tsohuwar matar ka" saqon Bala ya dawo masa a qwaqwalwa. Dagaske Ma'u ta daura aure da wani ko kuwa da Bala da Anty wasa suke so suyi masa da hankali amma ai babu wanda yasan wani a cikin su ballantana su shirya yi masa yawo da tunani ai.

Hannunsa daya masa nauyi ya daga yana so ya zaro wayarsa amma ya kasa. To wama ze kira ya tabbatar da gaskiya ko qaryar maganar a yanzu?
Amma ai yafi kusa da Ma'un, a gurinta ya kamata ya samu tabbaci na koma menene.

Cikin azama ya yunqura ya miqe kamar bashi ne ya fadi qasa yanzu ya gaza tashi ba se gashi a kan qafafunsa cikin sassarfa ya isa qofar gidan Ma'u ya shiga bugawa kamar wanda yazo karbar Bashi.

Abdallah ne yazo ya bude masa, kafin yayi magana ya shige ciki ya fara kwada kiran Ma'u yana wulga ido cikin gidan yaga ta inda zata bullo.

ASMA'U

Suman wucin gadi nayi a zaune har Anty ta fice ta barni bana tsammanin ko numfashi ina shaqa a lokacin. Qarar wayata ce tasa na gane a raye nake amma sam bani da qarfin da zan dauketa dan kwayar idona kadai na iya juyawa na kalli wayar na sake maida ita na zurawa qofa ina jiran naga wani yazo ya tasheni daga baccin da nakeyi.

"Mami ga Abbi nan yazo, kizo ki ganshi kamar wani abun ne ya faru gaba daya a hargitse yake" Farida data shigo da gudu ta fada amma na gaza buda baki nayi mata magana se ido kawai dana zuba mata ido kamar wadda ta hadu da cutar mantau.

"Mami, Mami ki taso kinyi shiru ko kema baki da lafiya" ta fada bayan data maso kusa dani ta hau girgizani, ajiyar zuciya me qarfi na sauke nace

"Bacci nake kika tashe ni ko Farida?"
"Bacci a zaune kuma, idonki ma a bude yake fa Mami" ta fada da mamaki tana kallona. Zan sake magana kiran da Bashir yake kwalamun ya shiga kunnena kamar ma a qofar dakin yake seta miqe da sauri tana cewa

"Dan Allah ki taso ki gani Mami gaba daya ba'a hayyacin sa yake ba bamu san meyake damun sa ba daman jiya be kwana a gida ba se yanzu ya dawo" ta juya da sauri ta fice ina qoqarin tsayar da ita.

Yanda yake kwala kiran kamar wanda yake gayyar yaqin duniya na uku yasa na tattara dan qarfin daya rage mun a jikina na miqe, ina kaiwa qofar na jiyo shi cikin qaraji yana cewa

"Zaku gaya mun ko kuwa, dagaske ne Ma'u ta daura aure da wani daban bani ba? Da gaskene wani banza ze rabi gonar da take mallakina?"

Saurin bude qofar nayi na fita jin yanda ya qarasa maganar cikin tsawa dan ni kaina seda na razana, a dari naja da baya na riqe qofa ganin yanda ya juyo ya kalleni da idanunsa da suka rine kamar zeyi aman wuta gaba daya kamannin fuskarsa sun chanza zuwa wani daban da ban taba ganin sa a irin yanayin ba.

"Yawwa Ma'u ki gaya mun waccen matar qarya takeyi ba gaskiya ta fada ba, ki fada mub da bakinki babu wani Namiji daya isa ya mallake ki a duniya bayan ni" ya fada yana nufo ni, da saurin gaske na koma dakin na turo qofa dan Na tabbatar idan har ya riqe ni to qila ni kuma a haka nawa ajalin zezo, gaga labarin daya sakani gajeran suma se Bashir ya qarasa aikin ya murqushe ni na mutu.

Yanda yake buga qofar dakin yana kiran na bude idan ya balla ta ya shigo bazan ji dadin abinda zeyi mun ba. Na fito na gaya masa qaryane kawai shi abinda yake so yaji kenan to ni me zance masa bayan ni kaina ban gama tantance sahihancin labarin baki nima a cikin rudanin nake kamar sa ai an gara shi ba abinda ya shafe shi bane ni kuwa fa, taya ma za'a ce wai an daura mun aure daga zuwa tambaya sekace wata yar tsana.

Wayata da aka kira na janyo da sauri ban ko tsaya duba waye ba dan neman wanda ze kawo mana dauki daga buyagin Bashir kawai nake

"Hello Asmy inata buga qofa ba'a bude ba ko baku nan ne?" Aka fada da muryar da rudun da nake ciki be barni na gane waye ba.

"Ka shigo a bude take dan Allah kayi sauri Bashir ze illata mu dani da yara" na fada ina tsalle kamar wata yarinya tunda dau naji ance ana waje ai magana ta qare dauki yazo kawai.

YUSUF
Duka daya yayiwa qofar da qafa ta bude idan ma a kulle take oho shidai ya bude ya fada gidan cikin azama jin abinda ta fada. Ido hudu sukayi da Bashir dake aikin biga qofar dakinta yayi biji biji kamar wani sabon hauka ya waiwayo a fusace jin an shigo gidan karaf suka hada ido da Yusuf suka shiga muzurai kamar wasu sababin zakaru.

"Me ya kawo ka gidan nan? Bana gaya maka ka fita daga harkarta ba karna sake ganika a kudada mata ta shine ka dawo to kuwa yau senayi maganinka, idan ma dakai ake hada baki saboda a baqantamun rai duk senayi maganin ku zan nuna muku Ma'u tawace ni kadai" Bashir ya fada a zabure yana nufar inda Yusuf yake a tsaye ya harde hannaye a qirji seda yakai dab dashi ya tsaya yana huci kamar ze kai masa duka.

Murmushi Yusuf yayi yana kallonsa yace
"Yaka tsaya? Ka qaraso mana kayi maganin nawa ko ko ba haka kace ba?"

Muzurai kawai Bashir yake yana sake kallon Majiya qarfin da suke tsaye a bakin qofar daga bayan Yusuf jikinau kamar wadanda aka gina da Bulo ko karan hauka ya cije shi baze yarda fada ya hadashi da daya daga cikin su bama balle harsu biyu yanda suka zubo masa ido jira kawai suke a basu umarni su far masa yasan.

"Ya ka tsaya ne Malam Bashir kai nake jira fa" Yusuf ya sake fada, ganin Bashir na kallon bayansa yasa ya waiwaya shima seya saki murmushi me kama da dariya yayi musu alamar daua fita, suka rusuna masa a tare suka juya waje se ya maida kallonsa kan Bashir cikin qasa da murya yanda yaraj da suka zura musu ido bazasujiyo abinda yake fada ba yace

"Ashe ma duk kurarin banza kakeyi yan wadannan qananun kwarin sun tsorata ka duk fiffiqar da kakeyi ta tashi a banza. Bari kaji abu daya ze hana na wulaqanta ka saboda wadannan yaran, bana so mutunchi na ya zube a gaban su dan bazasu taba girmamani ba idan har na wulaqanta ka a gabansu amma hakan bashi yake nufin idan muka hadu a inda babu ido zan saka karnukana su yagalgala ka ba.

Karka dauki shirun da nake maka a baya a matsayin tsoro ko bazan iya mayar maka da martani bane Aa saboda a lokacin daga ni har kai laluben allura muke a duhu ba'a san hannun da ze dauka ba, amma yanzu da na tabbatar da Allura tazo hannuna ta zama halalina mallakina yanzu zan baka amsa daidai da duk abubuwan daka fada a baya.

Kace ina shiga gidan matan aure zaka bata mun suna ka gayawa duniya ni manemin matan aure ne ko? To bari kaji daga yanzu idan  na sake jin labarin anga koda sahun tayar motar ka ne a qofar gidan nan sena batar dakai"

Yanda ya fadi batarwar seda Bashir ya bude ido dakayu ya kalle shi, gani yayi ya juye masa kai bazakace wannan mutumin me yawan murmushi da fara'a bane.

"Kwarai ni ba suna zan bata maka ba dan baka da sunan da zan bata ba kuma kashe ka zanyi ba amma zan batar dakai, babu wanda ze sake ganinka gaba daya za'a shafe labarinka Bashir.

Babu kai babu MATATA, duk abinda ya shafi Yayanka nine wakili tsakanin ku idan bazaka iya tunkarata kai tsaye ba ka nemi wani cikin yan uwanta ka ringa magan dashi amma banyarda ba koda wasa magana ta sake hadaka da MATATA, ina da kishin abinda nake so na kuma san qima da darajar sa idan kana musu ka gwadani Bashir indai shirya mayar da yayanka marayun qarfi da yaji matarka tayi takabar dole Bashir ka sake Shigowa gidan nan ko ka tare MATATA a hanya"

A nutse yayi maganar amma tamkar saukar aradu haka Bashir ya ringa jinsu a tsakiyar kansa. Kalmar MATATA da yake fada tafi komai juya masa kwakwalwa dagaske kenan Ma'u tayi aure kuma wannan mutumin ta aura?

Qarar bude qofar dakin Ma'u da sukaji ta saka su waiwayawa gaba dayan su a tare kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.

ASMA'U

Sadaf sadaf na bude qofar dakina na fito yanda kasan barawo ya shigo sata tunda na dena jiyo hargagin Bashir na tabbatar da mun samu an kawo mana dauki kenan.

Gaba daya suka waiwayo suna kallona cikin wata irin Azama Yusuf ta iso gabana ba zato se jina nayi gaba daya a jikinsa ya rufe ni ruf seka rantse Farida ya rungume ko Amnah saboda yanda na zama wata yar firit a jikinsa.

Wani irin shokin naji ya taho mun tun daga tsakiyar kaina ya dire kan qafafuna, ban farfado ba naji sautin muryarsa tareda dumin numfashinsa da yake fitar da qamshin Na'ana'a daidai kunnena yana cewa

"Karki bari linzamin kishina ya kwace Asmy, meyasa zaki fito gaban wani namiji a haka ya kallo abinda yake mallakina".

Innalillahi, yanda kasan wadda wuta taja haka naji jikina ya dauki rawa nan da nan na shiga qoqarin janyewa daga jikinsa amma yaqi bani damar hakan sema qara qarfin ruqon da yayi mun yayi ta hanyar dora hannayensa biyu ya sake damqe quguna ya dora habarsa akan gashin kaina da se a sannan na lura ashe daga ni se wata doguwar rigar shifom me hannun Bes na fito kaina ko arziqin dankwali be samu ba.

"Yusuf ka bari meye haka dan Allah? Yara fa suna kallonka" na fada a rikice jikina yana rawa jin yanda yake qara danqe quguna yana qoqarin daidaita fuskarmu.

"Wadanne yaran? Tun kafin ki fito suka shige daki, ai kinyi qoqari sosai Asmy gurin basu tarbiyyar barin guri idan manya suna magana" ya qarasa tareda hade bakinmu guri daya ba tareda ya bani damar cewa komai ba, sumbatata yakeyi seka rantse da Allah babu wani abu daya iya a duniya sama da wannan ni kuwa ina tsaye kamar Bishiya yar shekara Dari bidirinsa kawai yake cikin wani irin sauqi yanda kasan dagani se shi muka rage a cikin duniya".

Qarar fashewar abu ta saka shi sakina dakyar yana mayar da numfashi muka daga kai a tare muka kalli inda Bashir yake tsaye, yawun dake barazanar sarqeni na hadiye ina raba ido kamar an jijjiga bera a jarka se na bude baki taread dora hannu akai ganin yanda hannun Bashir yake digar da jini gefe guda kuma mudubin Console dina ne a rugurguje da alama shi ya nausa da hannunsa.

"Kash ya zaka huce akan mudubi beji ba be gani ba, wai daman kana tsaye baka yarda da abinda na fada maka ba kenan? Ka tabbata wannan shine karo na qarshe da zaka sake ganin abinda yake haramiyarka ka kuma fita idan ba haka ba inada tsageru daidai da kai biyu kawai ka gani anan idan kuma kana musu ka jira minti biyar tayi yawa sena saka sun zagaye gidan ka.

Wani irin kallon da na gagara fassarawa Bashir ya bimu dashi dagani har Yusuf din kafin ya tsayar da idonsa akaina se kuma ya juya cikin rangaji ya fice daga gidan har sannan hannunsa yana zubar da Jini.

Ya bata mun farin cikina, gaba daya ya rusamun tsarin dana zo dashi na tarbar Amaryata" Yusuf ya fada yana kallona har sannan hannayensa na saqale da quguna wani irin abu nake yana shiga jikina duk yanda naso na bude baki nayi masa magana kona fizge jikina na kasa yanda kasan wadda ya saka waya ya daddaure haka nake jina.

BASHIR🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 63

BASHIR

Ikon Allah ne ya shigar dashi gidan sa, yana shiga falon ya zube a qasa kamar qaramin yaro hawaye suka fara masa sintiri a fuska, be damu da ciwon hannunsa da har sannan jini na diqa ba ya ringa buga kansa yana cewa
“Na rasata Na rasata, na rasa farin cikina”.

Addah data fito daga Kitchen hannunta dauke da Flask data damawa Amirah kunu tayi saurin ajiye shi ta nufi Bashir cikin tashin hankali tace

“Waka rasa Bashir? Nafi ce ta mutu ko Amadu?” Addah ta fada tana tafa hannaye. Amirah da fitowarta kenan daga wanka ta jiyo maganar su itama se gata, da sauri ta qarasa kusa dashi ta tsugunna,

“Yaya Jini hannunka, dame kaji ciwo?” Ta fada tana qoqarin kama hannun. Seya riqo kafadunta yana cewa

“Na rasa Ma’una dagaske Ma’u ta auri wani ta zama matar wani daban bani ba rayuwata tazo qarshe” ya qarasa yana sakin wani kuka me tafe da sheshsheqa.

A tare Amirah da Addah suka saki wani dogon tsaki Addah na dire nata ta dora da cewa
“Amma Bashir ka isa asararrare, yanzu dan ubanka saboda mace kazo zaka saka zuciya ta ta buga na zata yar uwata ce ta mutu ashe kai tsabar lalacewa akan matar daka saka kake Kuka? To kaida Allah faduwar gaban da ka sakani ban yafe ba kuma nayi matuqar farin ciki da wannan al’amari Mun yada kwallon magwaro mun huta da quda.

Yo in banda ma lalacewa da kana sonta ka saketa ko kuwa wani sabon salon dinar Albarka ne da zaka zo kana mana dirama a nan? Wai da uwar mema ka yanke hannunka ko dambe kaje kukayi da Sabon Mijin ya yanke ka haka? Se ka tashi kasan nayi kafin jinin ka kuma ya tsiyaye ka shiga uku Aikin banza kawai” ta juya ta dauki Flask din kununta tayi dakin Amirah tana ce mata

“Dallah taso ki saka kaya duk ya wani gigita mutane da danyan jego kin fito kai a bude ke ai wannan abin ki hada walima ne ma wallahi yanzu ai se hankalin sa ya dawo kanki tunda mayyar tayi aure”.

A sanyaye Amirah ta miqe itama tabi bayan Addah tana waigensa. har ga Allah tayi bala’in jin dadin labarin ko banza yanzu dole duk wani tunanin dawo da Ma’u da yake ya janye gida ya tabbata nata ita kadai taci karanta babu babbaka.

Har suka rufo qofa Bashir na kallonsu kalaman Addah kuwa ji yai kamar ya shaqota ya huce duk haushin sa a kanta. Hannu yasa ya share hawayen fuskarsa kafin ya yunqura be sani ba ya dafa hannun daya yanke da sauri ya daga saboda zagin dayaji har tsakiyar kansa ya riqe hannun yana dubawa.

Sosai Mudubin ya yanke shi dan gashi nan naman gurin ya fito,
“Abbi ka tashi muje clinic a duba maka hannun kaga fa jini yana ci gaba da zuba” Aliyu daya shiga gidanya fada yana kallon Bashir.

“Me yasa bakagaya munba Aliyu? Me yasa baka sanar dani da wuri ba na dakatar da ita yanzu ya kake so nayi? Shikenan na rasa Ma’u, Mamin ku fa ta auri wani bazata sake dawowa gidannan ba”.

Kasa hada ido dashi Aliyu yayi, kamar shim hawayen yake kansa a qasa yace
“Abbi nima ban sani ba. Ita kanta Mamin nasan bata sani ba seda Anty taje ta gaya mata daka tsaya kunyi magana zata fada maka”
“Qaryane ta sani ita ta shirya komai saboda ta qarasa kassaramun zuciyata, daman ai jiya a gaban ka ta fada masa yaje ya tura a daura musu aure Ranar Juma’a shine daga baya ta sake canzawa meyasa? Meyasa Ma’u zatayi mun haka? Nace na gane kuskurena kuma a shirye nake dana chanza me yasa ita bata yafiya?” Ya qarasa maganar a tsawace.

Duk yanda Aliyu yayi dashi akan ya tashi suje Clinic din Estate din qi yayi qarshe se gidan wani Babatunde Aliyun yaje ya kirashi, Nurse ne matarsa ce suke aiki tareda Bashir shi ya taho da Kayan aiki yazo har gidan ya gyara masa ciwon da har dinki seda akayi a wajen.

Aliyun ne ya dumama masa abincin da aka kawo tun dazu wanda yayi order yaci yasha magungunan sa ya kwanta, yana zaune a dakin gaba daya sunyi shiru kowa da irin tunanin da yake a ransa lokaci lokaci Bashir yana sakin nishi saboda azabar fili data zuciya da yake ji.

Hoton Ma’u da Yusuf ya tsaya masa daram a zuciya yanda ya riqeta yake mata abinda shi kadai yake da wannan damar ada yanzu gashi da ransa be mutu ba ta auri wani, harta sakar masa kanta yana yanda yaga dama da ita.

“Aliyu kaje ka kwanta dare yayi” ya fada yana tashi zaune bayan daya dafe qirjinsa da yake suya, Aliyu da har ya fara gyangyadi yayi fitgigit yace

“Abbi bakayi bacci ba? Na zata a magungunan akwai me saka bacci ai ya kamata ka huta saboda yanayin jikinka”.

Murmushi me ciwo Bashir yayi yana kallonsa yace
“Daga randa na rabu da Ma’u bansake samun nutsatstseb bacci ba Aliyu a lokacin da nake da yaqinin zata dawo cikin rayuwata ma kenan taya kake tunanin yanzu dana tabbatar da na rasata zan sake runtsawa ai nida kwanciyar hankali munyi bankwana Aliyu, na rasa Ma’u na rasa farin cikina. Ta tafi da dukkan wata walwala da jin dadi na”.

“Abbi haquri zakayi mu dauka haka Allah ya qaddaro a tsakanin ku dan na tabbatar da Mami tana sonka amma babu wanda ze iya ja da ikon Allah. Gara kai kana da wata matar da kake so daman mu kuwa fa ita kadai ce Mamin mu yanzu shikenan bamu da maraba da Marayu haka zamuyi rayuwa ba tareda Mahaifiyarmu tana tare da mu” Aliyun ya fada qasan ransa yanajin wani irin zafi da tsanar Amirah.

Ya rigada ya saka ma ransa ita ce silar faruwar komai a gidan su. Ita ta wargaza musu farin ciki ta raba iyayensu kuma yayi alqawarin badai itama taji dadi a cikin gidan su ba. Yanda zasu qare rayuwa cikin quncin rashin uwa tabbas itama haka zatayita cikin uqubar da zasu ringa gana mata a ruwan sanyi setayi dana sanin shiga hurumin da banata ba.

“Laifi nane Aliyu ni na biyewa rudin shedan da zafin zuciya na aikata duk abinda ya faru, a zamana da Ma’u bata taba cutar dani tana sane ba. Tayi haquri dani da duk wasu halayya ta amma a qarshe ni na kasa yi mata uzuri akan bijirewa son raina gashi yanzu ni zan qare rayuwata a cikin dana sanin rabuwa da ita, kaico na dana zama me son kai a rayuwa, kaico na dana zama me rama Alkahiri da sharri.

Ina fatan abinda ya sameni ya zama izina a kanka da sauran qannenka, kada ku kuskura ku dauki soyayyar Mace a matsayin rauni ko gazawa kar kuma hakan ya zama abinda zaku riqe wurin juya rayuwarta yanda kuka ga dama. Tabbas duk wanda be godewa ni’imar ubangiji ba toh ze godewa Azabar sa” ya fada kamar ze fashe da kuka. Se Aliyun ya kama hannunsa yana cewa

“Abbi haka Allah yaso kuma in sha Allahu ze zama Alkahiri. Kayi bacci bari naje na duba su Jafar naga ko sun shigo se na kulle qofa na dawo” ya saki hannun Uban ya miqe

“Kaima ka kwanta ka huta Aliyu gobe kuna da makaranta fa”

“Na sani a nan zan kwana saboda ko zaka buqaci wani abun cikin dare” Aliyun ya bashi amsa kafin ya qarasa fita daga dakin.

Lumahw idonsa yayi yanajin wani qarin yayyafin qaunar Yaron yana shiga zuciyarsa. Ko iya wannan abin da Ma’u tayi masa na kula da tarbiyyar yayansa ta cusawa musu halaye da dabi’u na kwarai ta cancanci duk wata girmamawar duniya daga gare shi, ko kaffara baze ba idan shine a matsayin Aliyu wadannan abubuwan suka ringa faruwa akan idonsa baya tunanin wani abu bayan gaisuwa ze sake shiga tsakaninaa da Mahaifinsa shima saboda sauke haqqine kawai.

Daren ranar be iya runtsawa ba, Nadama yake yi mara amfani dan se a

Please Login or Register in order to submit comment