Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

se ana daf da magriba ya farka ko La'asar beyi ba. Seda ya watsa ruwa saboda yanda jikinsa ya yi masa ba dadi amma yaji sauqin ciwon kan dukda yana farkawa hoton Ma'u da Yusuf ne ya fara gilma masaΒ  a ido yayi saurin rufewa jin yanda zuciyarsa ta buga da qarfi, a dakinsa yayi sallolinsa be ko fita palour ba yana jiyo hayaniyar Amirah da be san ko da wa takeyi ba se ma ya sakawa qofarsa muqulli.

Naman dazu yaci da lemo dukda yayi sanyi amma bayaso ya fita ma balle ya hadu da Amirah ta qara masa ciwon kai, yana yin isha ya sake kora magungunan saboda yanda yaji tunanin dazu na neman tado masa da Sabon ciwon daya fi na dazu, dole ya dauki mataki baze zuba ido ba yana ji yana gani wasu wawaye su ringa kula masa mata har suna gaya masa magana.

Dole ya nemi Ma'u su daidaita dan yasan itama bazata taba bawa wanin sa dama ba koshi wannan shishshige mata yakeyi bawai dan tana so ba (A naka tunanin kenan malam Bashari πŸ˜‚).

WASHE GARI
WAI YA LABARIN MUTANEN GOMBE KUWA???
GIDAN DADA
Tun ranar da labarin sakin Ma'u ya sameta tabi duk ta tsangwami kanta, ko kadan abun beyi mata dadi ba kuma da ace Bashir yayi shawara da ita bazata taba bashi goyon bayan aikata hakan ba to a wanne dalili ma ze saki Ma'u??

Babban tashin hankalin ta irin yanda Alhaji Amadu yayi mirsisi kamar besan abinda ya faru ba bayan lokacin da Naziru yaje yana mata buyagi akan abinda Yayan nasu ya aikata ya tabbatar mata da Alhajin ya kira Bashir din sunyi magana amma ita bece mata komai ba har yanzu da aka kusa dosar wata da maganar.

Tasan Alhaji ta kuma san shirun sa ba Alkahiri bane bata san ta inda ze kamota ba, tsoronta Allah kar wannan abin itama ya zama sanadiyyar igiyar auranta kamar yanda ya taba ambata mata a baya da in har bata zare hannu daga sabgar gidan Bashir ba tabbas ze iya yanke igiyoyin da suke kanta idan yaso se taji dadin yin abinda take so tunda ne isa da ita ba to yanzu ma irin yanda ya dauke mata wuta baya shiga sabgarta sam dan ko abu yake so sedai ya kira Fainusa tayi masa abin yana mugun damunta har ta fara tunanin ko da gaske itama an sake ta ne kawai gaya mata ne beyi ba kuma tana tsoron ta tunkare shi da maganar tajiyo hakan ne dan bata san ina zata dosa ba, aure shekara Hamsin ba kadan a saketa ta kama ina toh??

Da hantsin ranar Tana zaune a dakinta ta rafka uban tagumi abinda duniya ya taru yayi mata yawa, tun shekaran jiya da Addah ta sanar mata da Sabon bala'in da Ummi ta janyo musu ta sake rasa sukuni. Dan shege a zuri'ar su wannan wane kalar tashin hankali Ummi take neman jefa rayuwarsu a ciki? Idan aure take so me yasa tun farko bata fada ba in ma bata da me sonta ne ai ko a tsakanin Naziru da Sa'ad ita me iya tursasa daya ya aureta ne a taru dai a rufawa juna Asiri amma yanzu wannan abu data jawo musu ina zasu saka kansu a garin nan??

Shigowar Fainusa da kukan data fasa ne ya dawo da ita daga tunanin data tafi, a gigice ta ke tambayarta meya faru? fainusan na kuka take cewa

"Dada Umar ne, na gaya miki nafi sati ina kiran wayar sa kota shiga baya dauka shine yanzu ya daga yake cemin wai nayi haquri ya fasa aurena. Ya rasa ta yanda ze gaya mun ne shiyasa idan na kirashi baya dauka na kuma tambaye shi dalili yace mun ba komai, ni yanzu yaya zanyi Dada? Shekara Shida kenan fa ina zaman jira yanzu dakyar Allah ya kawo mun mijin kuma shima ya gudu yanzu ya ake so nayi da rayuwata?"

Kuka sosai takeyi, Dada tayi tsam ta kasa cewa komai. Tunda auranta ya mutu da uban da ta shekara shida kenan an tafi ta bakwai kamar wadda aka watsa wa jinin baqar jaka babu wanda ya sake zuwa yace yana sonta, da kyar da Addu'a Allah ya fitowa Fainusa da Umar din nan har ya turo manyansa anyi magana sukace sati biyu zasu dawo da komai da komai a tsaida ranar daurin aure yanzu kusan wata daya kenan babu su ba labarinsu shine ze bullo da wannan maganar kuma kai su dai suna ganin hawa hawan tashin hankali.

"Kiyi haquri, ni tsoro nakeji nayiwa Alhaji magana yanzu kinga tunda Yayanku ya saki Matarsa Ahaji be ce mun komai ba ina tsoron na jangwalo shi dan kinsan gani yakeyi kamar da saka hannuna a faruwar abun nan.

Ki bari a qara kwana biyu idan yaso ko Amiru ne se na saka ya kira Umar din shi yaji menene matsalar se a magance ta" Dada ta fada da son kwantar mata da hankali, se Fainusa ta fizge daga riqon datayi mata tana cewa

"Nidai kije kiyi masa magana dan idan na rasa Umar mutuwa kawai zanyi duk duniya bayan da Iro ya sako ni babu wanda ya qara ko kallona da sunan so se shi sannan yanzu yace ya fasa wallahi gara kawai na mutu na huta da wannan baqin cikin da nake gani. Duk sakayyar abinda kukeyiwa wasu akaina take qarewa, nayi aure naje Miji da kishiya sun wahalar dani sannan yanzu bayan na gama cin benci na samu wani dakyar shima ya gudu to gara na bar gidan nan na koma wani gurin ko Allah ze dubeni ya cireni daga bala'in da kuka jefa rayuwata a ciki".

Sosai hankalin Dada ya tashi, tasan Fainusa ba hankali ta cika ba itama tsaf tana iya yin abintzata illata kan nata kamar yanda ta fada kota gudu daga gidan dan haka jiki a sanyaye ta miqe zuciyarta na bugawa kamar zata fi to ta nufi dakin Alhaji Amadu.

Yana zaune yana sauraren radio ta shiga ya daga kai ya kalleta sau daya ya mayar da kansa a ransa yayi murmushi yace
"Da wurwuri haka"

"Alhaji barka da hutawa" Dada ta fada tana qasa da kanta kamar wadda taje wani baqon guri, seya rage radio yana kallonta yace

"Barka dai Nafi, halan batan hanya kikayi yau kika shigo dakina ko?"

"Batan hanya kuma Alhaji, zuwa nayi naji ko laifi nayi naga kwana biyu gaba daya ka shareni a cikin gidan nan kamar baka san da zamana ba ko wani abun kake so sedai ka saka su Naziru suyi maka ban sani ba ko wani laifi na aikata maka a cikin kuskure"

"Nidin kuma Nafi? Aa baki mun komai ba gani nayi dai ai daman ba se na kiraki ko na saka ki aiki kikeyi mun ba to bansan ko gajiya kikayi ba kika janye shiyasa nake saka yayana gudun karna takura miki da hidimomina tunda har kin qosa da kanki" Alhaji Amadu ya fada yana murmushi qasan ransa kuwa mamakin Dada kawai yakeyi, ya sani buqatarta ce ta kawota danya jiyo wasu daga maganganunsu ita da Fainusan daya leqa da niyyar kiran Fainusan shiyasaya dawo ya kunna radio a zuwan besan wainar da suke toyawa bama.

"Kayi haquri Alhaji wallahi ba haka bane, gani nayo kamar kayi fushi dani akan abinda yaron nan ya aikata ne shiyasa ni kuma bansan ta yanda zan wanke kaina a gurinka ba nasan laifina kake gani" Dada ta fada tana qara sunkuyar dakai.

"Duk wanda yayi na gari ai kansa Nafi, bari nadan kwanta na huta tunda naga Azahar da saura, idan Sa'adu ya shigo kice masa da yamma ze kaini Gidan Malam Isah na sake dubo jikinsa tunda Naziru yace wuni zeyi a makaranta yau" ya fada yana tura keken sa zuwa bakin gado, Dada ta miqe da niyyar taimaka masa ya dakatar da ita.

Dakansa ya hau gadon ya gyara kwanciyarsa dab daman matsalar baya ce ta saka yake qagara miqewa amma tunda Yan biyun gidan su Ma'u suka kawo masa wani ganyaye na gargajiya daga Chana wancan dawowar da sukayi ake dafa masa shayi dashi duk wani ciwon daya shafi qashi yaji sauqin sa cikin ikon Allah, bama shi kadai ba duk tsofaffin da suka bawa a unguwar tasu kowa se dai sambarka dan yanzu yana kama abu ya miqe akan qafafunsa tafiya cedai wannan ya fawwalawa Allah shi ya bashi qafafun kuma yanzu ya karbe abunsa ransa ma wata rana karbar abinsa zeyi balle wata qafa da da ita da babu duk yana iya gabatar da uzurirrikan rayuwarsa.

Kwanciya yayi ya juya baya jin har sannan Dada na dakin se ya juyo yana cewa

"Nafi akwai wani abun ne kuma naga kin zauna kinyi shiru?"
Seda ta hadiyi yawu kafin ta iya cewa

"Alhaji daman akan maganar yaron nan me neman auran Fainusa ne,dazu ya kirata yace wai ya fasa shine nake so naji ko zaka tuntubi waliyyan nasa muji menene matsalar idan da yanda za'a gyarata"

"To ikon Allah ya fasa kuma yace? To Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri" ya fada ba tareda wata damuwa a fuskarsa ba.

"Alhaji tana can fa tana ta kuka har tana cewa mutuwa zatayi ko ta gudu ta bar gari dan Allah ka kirasu muji ko da akwai abinda za'a iyayi" Dada ta sake fada kamar zatayi kukan itama.

Seya yunqura ya tashi zaune yana cewa
"Me auran shekara Goma sha bakwai ma an saketa babu wanda ya biyo ba'asi ko yace a mayar da ita se ita da ko tsayayyar magana ba'ayi ba?

Idan ta mutu ai shikenan kinga ta huta guduwa daga gida kuma in shi ymta zaba to ta jira zuwa Juma'a zan bada sanarwa a masallaci cewar na yanke alaqa da ita ko an ganta a wani guri kar wanda ya alaqantata dani ba yata bace dan karma taje ta kwaso mun damuwa irin wadda kuka jefa Alhaji Murtala a ciki" ya qarasa maganar yana danna wayar sa.

Da sauri Dada ta daga kai ta kalleshi, ya akayi yasan da maganar cikin Ummi bayan Addah ta tabbatar mata babu wanda ya sani shiyasa suke neman hanyar da Asirinsu ze rufu kafin abu ya fashe kowa ya sani in har kuwa Alhaji yasan zancen to babu shakka labari ya rigada ya gana gari sune suke shirmen su da tunanin babu wanda ya sani kenan.

Muryar mutumin daya kira a waya ce ta katse mata tunani, tana ji suka gaisa kafin Alhajin ya ke ce masa

"Yanzu Me dakina take samuna da maganar cewa Unaru ya janye maganar aure ko? Shine nace bari na kiraka na tabbatar daga bakinka tukunna"

"Wallahi Alhaji nima da safiyar yau dinnan ya same ni yake gaya mun na kuma yi masa fada na gaya masa be isa ya mayar damu qananan mutane ba, yanzu haka ka ganni shiri nake zanje na samu uwarsa na gaya mata halin da ake ciki shiyasa ma ban kiraka ba na bari se mun gama yanke sa rana tukunna sedai kawai ka gammu"Β  mutumin ya fada daga daya bagaren

"Aa Alhaji baza'ayi haka ba, babu wanda fa yayi masa dole akanta shi ya gani yace yana so dan haka yanzu ma bamu san dalilinsa na cew aya janye ba. Ka barshi kawai Allah yasa hakan ne yafi Alkahiri amma batun a tilasta yaro ma be taso ba shine ma'auri ba kuma auran fari ba bare ace za'a bashi shawara rajin kansa yasaka shi tunanin qarawa tunda kuma ya janye a qyale shi kawai" Alhaji Amadu ya fada kai bazakace yar sa ake cewa an fasa aure ba.

Haka sukayi sallama wancan yana ta faman bada haquri da alqawarin idan komai ya daidaita zasu zo, yana kashe wayar ya kalli Dada data saki baki tana kallonsa yace

"To kinji dai abinda ya fada. Idan aure take so anjima zan bada sanarwa a masallaci duk wanda yake sonta yazo zan bashi sadaka har sadakin ma ni zan biya masa idan kuma taqi ai kinji abinda na fada a farko seta zabi abinda ya mata a ciki.

Ni yanzu kin cinye mun ma lokacin baccina bari na tashi nayi ta hailala da istigfari maganin masifa kafin a kira sallar" ya qarasa yana janyo carbinsa.

Haka Dada ta kwashi qaqafunta ta fice, a bakin qofa taci karo da Fainusa da ashe tana labe tana jin komai bata kulata ba ta wuce dakinta can qurya ta shiga kiran Addah a waya.

GIDAN ADDAH

Addah na tsaye akan Ummi dake kwarara amai a bandaki tana zazzage mata ruwan masifa da bala'i kiran wayar Dada ya shiga. Bata daga ba ta ci gaba da sababinta, magani ne ta karbowa Ummin na zubar da ciki tana shi shine ta amayoshi tas kuma wannan shine karo na uku data kashe kudi aka karbo mata magani amma ciki na nan daram ko girgiza beyi ba.

Kiran wayarta da ake tayi babu qaqqautawa ya saka ta fito cikin bala'i ta daga tana cewa
"Wai Nafi wannan wace kalar lukutar masifa ce da zaki ringa kirana kamar naci miki bashi ki barni naji da abu daya mana haba"

"Addah dole na kiraki ai, kika cemun babu wanda yasan da zancen cikin Ummi amma ya akayi har Alhaji ya samu labari anya kuwa magana bata fasu ba Addah?"

"To idan ma magana ta fasu Nafi se akayi wace kutumar uba eye nace se akayi me? Da zaki ce mun Amadu yasan zancen waya sani ko a munafuncinki kika gaya masa tunda kema ai ba sanin zuciyarki nayi ba waya sani ko kina cikin masu farin ciki da abinda ya same ni in ba haka ba shi mijin naki yana kanannade a kujera ta ina ze jiyo wani labari?

Ni karki sake kirana indai ba mafita kika samo mun ba, kuma abin kunya ai ba kanta farau ba kumaba ita zata rufe ba wasu da yawa Allah kadai yasan shegu nawa suka haifa aikin banza kawai" ta kashe wayarta kafin ma Dadan ta sake magana.

Kan Ummi data fito daga bandakin da kyar ta koma tana cewa
"Dan uwar ubanki ba kwanciya zakiyi ba tashi zakiyi mu tafi gidan Balaraba yanzu ai Qanwarta sarai ta taba yin ciki sukaje aka cire muje ta raka ni gurin dan dole se abin nan ya fita ko bangon duniya zancen yaje qarewarta se an cire idan yaso senaga shedar da za'a bayar idanan tashi gulmar".

Kuka Ummi ta saka tana cewa ki qyale ni Addah in dai ba so kike na mutu ba dan Allah ki rabu dani. Qaddarata ce tazo a haka kuma kece sila dan haka ki barni na haife abinda yake cikina ban sani ba ko shine silar kaffarata a gurin ubangiji"

"Wallahi sedai ki mutu dan ubanki dama amfanin me zakiyi mun idan kin rayu bayan abin kunyar da kika janyo mana, ki tashi tun wuri mu tafi kafin nazo na haye kanki na murqusheki daga ke har shegen dan cikin naki ku mutu kowa ya huta".

Haka Ummi tana ji tana gani Addah ta tasata a gaba tana kuka suka tafi. Matan gidan da sukayi cirko cirko suna kallonsu dan duk abinda ta ke fada sunji saboda ba a hankali take magana ba.

Daman sun san da qishin qishin din maganar yanzu gashi sun tabbatar suna fita kuwa Binta da tafi kowa tsugudidi ta shige daki ta dauki wayarta ta kira Alhaji Murtala.

Yana zaune a kasuwa a daidai lokacin wani Amininsa Alhaji Yero ya same shi da maganar cikin Ummi daya ji a bakin Matansa.

Hankalin Alhaji Murtala yayi qololuwar tashi da jij maganar wata irin tsanar Addah yaji tana saukar masa shidai tunda ya auri Fatu bazece ga wani abun Alkahiri daya same shi ta dalilin ta ba a kullum cikin jefa shi a masifu kala kala take.

Kiran wayar Binta na shiga ya daga, ba maganar gaisuwa ta shiga rattaba masa cewa
"Alhaji ka kira Addah duk inda take ta dauki Ummi tana kuka da komai sun tafi tackaita a zubar da ciki kar yarinyar nan ta mutu mu shiga uku ka kirata ka dakatar da ita".

Wata zufa yaji tana sakko masa, kiran wayar Addah ya shigayi tana ringing amma bata dagawa seda ya kirata sau goma a na sha daya ta kashe wayar. Babbar rigarsa ya cire saboda yanda yaji tana neman shaqeshi ya ringa safa da marwa a cikin shagonsa yana ayya na irin wulaqancin da zeyiwa Fattu a wannan karon, tabbas yakai bango kuma dole ya dauki matakin da ze shigar da ita hankalinta.

Wayar Amirah ya shiga kira ringing biyu ta daga tana gaishe shi, be amsa mata ba cikin kakkausar murya yace mata

"Ki kira uwarku ki gaya mata wallahi idan wani abu ya samu Ummi a sanadiyyar zubar da cikin data tafi kaita se na daureta dauri har qarshen rayuwarta sannan ki gaya mata daga inda ta tafi karta dawo mun gidana na saketa saki biyu" yana gama fada matan ya kashe wayar sa.

Sosai zuciyarsa take tafarfasa, Addu'arsa Allah yasa kar wani abu ya samu Ummin dan wallahi bega wanda ze hana shi shari'a da Fattu ba.

Hajia Addah kuwa Napep suka haye se gidan Hajia Balaraba suna tafe a hanya tana surfawa Ummi zagi har suka isa.

Ta tarar da Hajia Balaraba tana wanka dan haka suka zauna a palour suna jiranta ba adauki lokaci ba kuwa se gata ta fito daga dakinta a kallo daya Addah ta hango irin yanda tayi sanyi laqwas kamar ba Balaraban data sani ba mace me izza da taqama.

"Aa Fattu kece yau a gidan namu yaushe rabo" Balaraba ta fada tana zama akan kujera, se Addah ta tabe baki kafin tace

"Zaki fadi haka mana tunda kin samu yanda kike so kij watsar dani bayan da kika kaini gidan dan damfara ya cinye mun kudi ai dole kice yaushe rabo, ni ba wannan ta kawo ni ba ma.

Likitan da ya cirewa Sarai qanwar ki ciki zaki hadani dashi wannan tsinanniyar yarinyar taje ta kwaso mun abun kunya dama yana qare da maqiya ballantana yanzu ta janyo mun abun magana a ringa nunani a gari"

"Kai kai Fattu ki bari dan Allah, irin wadannan mugayen kalaman da muke jifan yaran mu dasu su suke tasiri akan su suke lalatasu.
Ummi a garin yaya me ya kaiki irin wannan abu ke da nake yiwa kallon nutsatstsiya ko yar uwarki da take da rawar kai ta gama yammatancinta lafiya Me ya sa Ummi" Hajia Balaraba ta fada cikin Jimami.

Ummi ta qarawa kukan ta volume tana cewa "Wallai Hajia sharrin shaidan ne kuma da laifi Addah, seda na gaya mata ga wanda nake so tace ko zan mutu bazan aure shi ba"

Duka Addah ta kai mata tana cewa "Na fada din yanzu ma na maimaita ko zaki mutu bazaki aure shi ba shegiya da bata san ciwon kanta ba.

Ke kuma ni ba mayar da zance ne ya kawo ni ba ki bani lambar waya ko Adireshi na tafi dan a yau nake so ayita ta qare kafin maganar taje kunnen ubanta".

"Cikin wata nawa ne?" Balaraba ta fada tana janye tagumin da tayi, se Addah tayi caraf ta ce

"Ko wata tara ne se an cire shi babu ruwanki kawai nidai ki hadani da me aiki badai maganar kudi bace zan bayar ba matsala"

"Dan Allah Hajia karki barta ta kaini cikin fa wata hudu ne wallahi mutuwa zanyi Nasan gara ta barni ko a gurin haihuwarsa na mutu nasan nayi shahada Allah yasa haka ya zamar mun kaffara" Ummi ta fada tana sake rushewa da kuka, se Addah tayi kanta da duka Hajia Balaraba ta shiga tsakani tana bata haquri

"Fattu Yarinyar nan tafiki gaskiya, ko sarai da kikaga a lokacin munje an cire wata biyu ba'a ko busa masa raiba magani kawai ya bata tasha cikin ya fita amma wannan wata hudu fa, kisan rai zakiyi qarshe idan ba'a dace ba itama a rasata gaskiya kiyi haquri ki dauki qaddarar data zo miki a haka tunda ke kika jawowa kanki. Yarinya ta kawo mijin aure kinqi ai dole ki karbi duk sakamakoj daya biyo baya kuwa".

"Tashi mu tafi dan Uwarki ai ba ita kadai tasan likitan zubar da ciki ba ke ni da kaina nan ma sena zubar da shege idan na naushe ki yanzu" Addah ta fada tana finciko Ummin, se Balaraba tayi saurin tareta da cewa

"Ba a nan ba wallahi ku fita can idan ma kin kasheta a daure ki ke kadai baza'a ce a gidana a kayi ba" haka ta taso qeyar Addah har Get Addah na zazzaga rashin mutunchi tuni yan unguwa suka fara taruwa ana kallonta haka dai ta angiza qeyar Ummi har tati tana kuka kafin suka samu Napep kai tsaye tace a kaita wani Sha ka tafin Private Asibiti data taba zuwa duba wata qawarta a can qasan gurin GSU, a yanda taga kalar likitan ta tabbatar ze iyayin komai in dai ze samu kudi.

Ita se yanzu ma ta tuno dashi da meze kaita gurin wata balaraba harta bata lokacin ta a banza.

AMIRAH


M&Z FASHION DESINGNERS
INA MATA YAN KWALISA
KU GARZAYO M&Z
FASHION DESNGNERS DAN SAMUN IN GANTATTUN KAYA MASU AMINCI.
IRINSU
ZANNIWAN GADO
TROW PILLOWS NA ZAMANI
TUM TUM
BABY SET
TOILET SET
KITCHEN SET
LABULAYE DA SAURAN KAYAN KWALLIYAR GIDA.
HARMA DA ATAMFOFI DA KAYAN KITCHEN AKAN FARASHII ME RAHUSA
KU NEMEMU AKAN LAMBAR WAYA 07064870087.08127423783.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR πŸ₯°πŸ‘Ή
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 50


AMIRAH

Wuntsulawa tayi daga kan gadonta zuwa qasa tayi zaman yan bori. Number wayar Addah ta shiga nema cikin tashin hankali ta ringa kira amma a kashe seta mayar da akalar kiran zuwa Ummi itama dai amsa daya aka bata wato a kashen.

Bata san sanda kuka ya kwace mata ba, ita ba sakin da Babansu yayiwa Addan ne ya dameta ba illah zancen zubar da ciki dataji. Bazata taba manta qawarta wata Harira Sani ba lokacin suna Sakandire tayi ciki a gurin zubarwa ta mutu tun daga sannan take bala’in tsoron abinda ze hado ace za’a zubar da ciki. Yanzu idan Ummi ta mutu yaya zatayi bayan duk duniya bata da wata shaqiqiyar yar uwa sama da ita.

Ganin ta kasa samun wayoyinau yasa ta yanke shawarar kiran Sa’adah maqociyarsu, tasan bazata rasa sanin wani abu da yake faruwa ba nan da nan ta danna lambar tayi sa’a tana shiga kuka ta daga.

β€œAnty Sa’adah ki taimaka mana ki kaiwa Addah waya nayi ta kiran layin ta dana Ummi baya shiga” Amirah ta fada bayan da tayi qoqari sosai gurin danne kukan ta.

Sa’adah dake kwance akan gadon ta tayi daidai dan tashinta daga bacci kenan ma ita ta yatsina fuska tareda hararar wayar kafin tace
β€œAyyah ai kuwa anyi rashin sa’a kin ganni ina gidan mu a can na kwana jiya.

Idan ba sauri kike ba anjima kadan zan tafi idan yaso sena kiraki kuyi maganar”

β€œShikenan toh idan ban same ta ba na sake kiranki” Amirah ta fada tana kashe wayar.

Daga can bangaren kuwa Sa’adah tsaki taja kafin a fili tace β€œgayyar tsiya kawai, ni blocking number ki ma zanyi bazaki sake samuna ba tunda ku baku san mutunchi ba haka kawai da na saki baki sedai inji ana in matsa za’a shigo da Amarya ko toh Allah ya toni asirin ku gashi nan kuma yayi mun sakayya ya hada ku da dan shege” ta sake tabe baki tana gyara kwanciya.

(Abinda ya faru mijinta ne ya ringa soyayya da Ummi a boye ba tareda ta sani ba se daga baya shine ta janye alaqa dasu gaba daya)

Amirah kuwa rasa wa zata kira tayi, fuskarta shabe shabe da hawaye, daga ita se yar bingikar rigar baccin ta net data kwana da ita wanda hatta da pant din jikinta ana gani ta fito daga dakinta da tun jiya data shige bata sake fitowa ba kai tsaye ta wuce su Aliyu dake zaune a palour suna karyawa ta nufi kan Dining inda Bashir yake.

Wata muguwar tsawa ya daka mata daidai sanda ta isa kansa ta tsaya. Kallonta yakeyi da idanunsa da suka chanza kala nan take saboda bacin rai dakyar ya bude baki yace mata

β€œKe wace irin dabba mara tunani ce zaki fito a haka ki wuce ta gaban Yara samari? Saboda baki da tarbiyya ko baki kuma san mutunchin kanki ba bace mun daga nan kafin na kifar dake”.

Duk yanda ta tsorata da irin tsawa da hargagin da yake mata bata ko motsa taku daya daga inda take ba, cikin kuka tace masa

β€œTo nima ai dole ce ta fito dani, Baba ya kirani yace ya saki Addah kuma

Please Login or Register in order to submit comment