Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gurin uwar su ace ni zan basu abinci wannan ma bame yuwu ba bane ai”

Haka ta dora ruwa ta saka kwai guda biyu sannan ta dora wata tukunyar ta hau dafa musu Indomie, a maimakon ta jajjaga attaruhu ta zuba se kawai ta saka dakakken Yaji ko Albasa bata saka haka ta zuba masa a plate da kwai kwalli daya a gefe ta saka fork ta kai masa.

Akan centre table ta ajiye, ta koma ta dakko masa ruwa da lemo sannan ta dakko nata abincin harta fara ci sannan Bashir ya fito daga dakinsa ya chanza kaya da alama wanka yayi.

Seda ya zauna akan kujera kafin ya kalleta yace “Ina abincin nawa?”

“Gashinan tun dazu na gama baka fito ba Allah yasa ma bata huce ba”.

Wani kallon banza yayiwa farantin da abinda yake ciki kafin ya saka hannu ya dauka ya tona Indomin da cokalin ciki yana kallonta yace

“Ni zanci wannan abun? Meye wannan kikayi? Idan ma Indomin zaki dafa haka akeyi duk kayan hadin da suke a cikin Kitchen kika gagara sakawa shine zaki kawo mun abu kamar na yan birsin ga wani kwai guda daya akai”.

“Wallahi Yaya ka fiya qorafi kaci mana kaji ai tayi dadi ba gashi ni har na kusa gama cinye tawa ba kuma wane hadi za’ayiwa Indomie bayan wannan harfa yaji na zuba a ciki dan tayi dandano....”

A mugun zuciya ya wulla mata farantin Indomin Allah ya taimaketa be qarasa kanta ba ya fadi a qasa ya tarwatse abinka da tangaran, a tsorace ta kalle shi, ya miqe yayi yo kanta se kuma meya tuna ya kaiwa Iska naushi kafin ya zari key din motarsa yana cewa
“Allah yasa na dawo na tarar da gurin nan a haka” ya juya ya fita.

Badan tana tsoron abinda kaje ka dawo ba babu abinda ze sakata gyara gurin haka ta dakko tsintiya da mopper ta kwashe fasashshen tangaran da Indomin ta kai shara kafin ta saka ruwa ta goge gurin.

“Haka kawai mutum se baqar zuciya kamar kuturu ina laifina dan Allah dama na dafa, ni da yasan baze ci ba se ya bani na qara dan ban qoshi ba yanzu ya wa mutane Asara aikin banza kawai” haka dai ta gyara gurin tsaf ta wuce dakinta ta fada wanka, tana fitowa ta shiga shiri shafa wancan goga wancan ta gama ta saka wata hadaddiyar Night gown ta gyara gashinta tsaf ta wuce dakin Bashir dan har ga Allah a matse take.

Tana kwance tayi daidai tana chatting ya shigo dakin fuskar nan kamar hadiri, to jiki da jini gashi daman kwana ya dade rabonsa da abin dole ya ajiye fushi suka raya sunnah kafin sukayi baccinsu cikin salama dukda seda a ka kusa sake wani fadan da yace taje tayi wanka tace seda safe, dataga yana neman bata mata farin cikin data samu dole tayi wankan suka koma sukayi bacci.

Washe gari ma lafiya qalau suka tashi, ta cije ta daure tayi duk abinda ya kamata akayi sa’a kuwa harta hada masa abin karyawa suka zauna beyi qorafi ba. Seda ya gama suna zaune a palour yake cewa

“Yaran nan kinji shiru har yanzu babu wanda ya shigo ko basu tashi bane”.

“Eh qilan kasan jiya an sha ruwa gari yayi sanyi may be shi yasa basu fito da wuri ba” ta fada a fili a ranta kuwa zagi take auna musu tana Addu’ar Allah yasa kar su zo.

“Bari naje na karbo katin wuta shaf na manta jiya dana fita ban siya ba naji kuma mitar tana qara” ya fada yana miqewa, seda ya sako jallabiyya ya dauki muqullin motarsa kafin ya fita, yana fita itama ta miqe akan kujera ta kwanta ranta fes a qarshe dai ta samu irin rayuwar da take so ita da Yayanta a gidan su su kadai suna zuba soyayya.

BASHIR
Yana fita qofar gida ya ga yaran suna Ball, gaba daya suka gaishe shi banda Aliyu da tunda suka hada ido ya juya baya yana hada fuska se kawai Bashir din ya girgiza kai tareda yin qwafa ya kama hannun Abdallah yana cewa

“Kun tashi daman me yasa baku shgo gida ba toh?”

“Abbi Mami ta hana tace idan muka sake zuwa gidan seta cire mana kunne ko Yah Abdallah” Ahmad yayi zuruf ya fada dan daman duk cikinsu shine me dan banzan surutu ai kuwa Aliyu ya kai masa duka yana cewa
“Waya tambayeka me shegen surutun tsiya kawai”.

“Idan ka sake dukan sa Aliyu sena saba maka, ita Ma’un ce tace kar ku sake shiga gidan yayi kyau zan nuna mata kuwa na fita iko a kanku” Bashir ya fada kafin fuu ya juya ya koma cikin gidansa.

Amirah da har bacci ya fara daukanta bude qofar sa ya farkar da ita se ta miqe tana goge ido tace
“Wai har ka dawo? daga dan kwanciya ashe bacci ne yayi gaba dani ban sani ba”.

“Wai me Ma’u ta dauki kanta ne har ni zata ce Yarana karsu sake shigowa gidan nan saboda taga na saka mata ido na barta dasu ko? To shikenan ai kuwa a yau zasu bar wajenta idan yaso se naga wanda zata sakw hanawa zuwa wani gurin, ki fitar da kwalayen da kika zuba a can dakin yanzu zan fita za’a kawo sababbin gadaje a saka musu tunda ta kwashe wadancan, Amna da Farida kuma se su zauna a dakin ki kafin zuwa na samu wasu kudin suma a gyara musu dakin su” ya fada a mugun fusace ya wuce dakinsa dakko Atm dan ya manta ma dazun daze fita be dauka ba.

Har yakai bakin qofar Amirah data miqe tsaye tace “cabdi wadanne yaran ne zasu dawo gidan nan ni nace maka zan riqe maka yaya ne ko yaya? Harda ma wasu in basu dakina su zauna wallahi baze yuwu ba babu dan wanda zan riqe ehe”.

“Idan sunzo seki kore su kinji ko tunda baki da hankali ni zan koya miki har in fadi magana ki tsaya a gabana kina cewa ba za’ayi ba to ki jira na fito na tarar da ke anan gurin wawiya kawai” ya shige dakin ransa idan yayi dubu ya baci.

Me matan nan suka dauke shi ma? Ita waccen ta hana masa Yara zuwa gidan sa ita kuma wannan tana cewa baza su zauna a gidan ba, to ze gani idan gidan ubanta ne seta hana su ita kuma Ma’u ze kwace yaransa yaga in akwai abinda zata iya yi akai.

Sanda Ya fito Amirah ta shige dakinta dan haka yaja qwafa ya fita, yaso ya tarar da ita wallahi da se jikinta ya gaya mata tunda yaga alamar ita se an taba lafiyarta sannan take nutsuwa idan banda ma rashin kunya shi a matsayinsa Amirah zata kalla ya fadi abu tace bazatayi ba? Illar auran qaramar yarinyar kenan yarinyar da aka haifa akan idonsa ya raineta a gidansa da auran wuri ma yayi yasan tsaf se haifi kamarta amma yanzu tunda taga makwancinsa shiyasa take iya tsayawa a gabansa tana masa fitsara zeyi maganinta kuwa.

Amirah kuwa Dakin ta ta shiga, a fusace ta danna kiran Addah tana daga wayar kuwa ta saka mata kuka tana gaya mata yanda akayi.

“Kayyasan nan to ke me kika ce masa yanzu” Addah ta bada daga daya bangaren,

“Me zance masa kuwa Addah na gaya masa wallahi babu dan da zan riqe shine wai idan gidan uban wani ne se na hanasu zama ya gani”.

“Kina jina ko, lalabashi kuje a hakan zuwa musan abinyi dan ba mutunchi ne dashi ba kar muje ya sako mun ke kamar yanda ya saki uwarsu. Suzo din kisan mummuqe zaki musu a gabansa ki nuna kina son su a bayan idonsa kici ubansu yanda da kansu zasu gudu kinga qarshe se kefin ya koma kan uwarsu yace ita ce ta kitsa musu mugun abu” haka Addah tayi ta lallaba ta dakyar ta sauka ta yarda zata bashi haquri idan ya dawo ta kuma karbi yaran idan yaso a hankali ta gasa musu aya a hannu yanda zasu gudu da qafarsu su bar mata gidan.

Kafin ya dawo kuwa an kawo gado, haka ta danne baqin cikinta ta tsaya suka saka kayan harda wallpaper aka chanza musu masu suka gama suka tafi ta dawo palour ta zauna tana jiran taga shigowarsa da yaran tana nan zaune kuwa se gasu daya bayan daya suna shigowa kowa fuska jiqe da hawaye.

Muryar Bashir da tajiyo daga waje alamar shima yana dab da shigowa ya saka ta tashi ta taro Yan biyu tana cewa

“Meyasa kuke kuka da nan da gidan Mami ai duk daya ne kuje fa kuga yanda aka gyara muku dakin ku yayi kyau sosai”.

“Karki sakw tabasu kuma babu ruwanki damu a gidan nan kiyi harkar ki muyi tamu in ba haka ba kuma zaki sani” Aliyu ya fada yana fizge su daga hannunta kafin ya wuce dasu dakinsu yana sake balla mata harara Amirah kuwa da kallo ta bisu kawai baki bude, badan Bashir na waje babu abinda ze hana taci uwar yaron nan yau amma ai suna hade, Bashir din zeyi nisane wallahi seta koya masa hankali.

Kowa tayi ta zauna sega Bashir kaman wanda aka wullo, kallo daya yayi mata, yaso ace ta ci gaba da tata fitsarar ya ida saita mata nata hankalin tunda ya gama da Ma’u amma sabanin haka se yaga ta miqe tana murmushi tace

“Yara sun shigo suna kuka, ina ta lallashin su ma suka wuceni suka shige daki. Kaje ka lallabasu dan Allah badadi yaro ya ringa kuka”.

Wuce ta yayi ya shiga dakin nasu, suna nan har sannan sun hada kai suna kuka musamman Faridah da take ita kadai yau Babu Yah Amnah, Aliyu dai yana tsaye yana huci dan a fusace ya waiwaya da aka bude qofar ya zata Amirah ce ganin Bashir se ya mayar da kai gefe yana ci gaba da lissafi a ransa.

Bashir kuwa tsayawa yayi, seda ya irgasu kamar wasu yayan kaji kafin ya sake fita fuu kamar iska ya tafi gidan Ma’u, yayi Sa’a qofar a bude take dan tunda suka fita tana zaune tana kuka Ita da Amnah Anty kuma tana zazzaga mata masifa dan ta gaji da lallashin se ganinsa kawai sukayi ya fado yana cewa

“Ina Amnah? Nace ki tattara mun yarana shine zaki rage wasu akan wane dalili ke wuce mu tafi” ya qarasa yana kama hannun Amnah da tunda ya shigo ta miqe, tundazun taso ta bisu amma kukan da taga Mamin nayi ya sakata tsayawa daman jira takeyi idan tayi shiru se ta tafi daga baya.

ASMA’U

Toshe kunnena nayi naqi jin lallashin da Anty takeyi mun dan kuwa ba abinda zata fada mun tunda taqi hanawa Bashir ya kwashe mun yara, kuka nakeyi haiqan, daman ba wai na gama mantawa da abinda ya faru bane Aa kawai dai na bawa kaina haquri ne na dangana shine yanzu za’a sakeyi mun fami.

Bashir ya rabani da aure na, ya kuma rabani da yarana sannan kuma ace nayi haquri wai na dena kuka ai wannan zance ma be taso ba babu wanda ze fahimci halin da nake ciki se wanda masoyi ya tabayi masa yankan qauna a rayuwa.

Shigowar da Bashir yayi ban ko daga kai na kalle shi ba seda naji yaja maganar Amna tazo su tafi kafin na dago fuskata data jiqe da hawaye tayi jajir na kalle shi nace

“Ina tunanin abinda ka fara sha Bashir yana gaya maka qarya. Yaranka kace na baka kuma na baka, idan ka manta ne kuma bari na tuna maka Amnah ba yarka bace qanwata ce babu kuma abinda ka hada da ita dan zama na takeyi a gidan ka yanzu kuwa bata abinda ta manta a gidan ballantana ta koma su dai da yake gidan Ubansu gasu can an baka itama zata zauna a gidan da aka biya da kudin ubanta”.

Wani kallo ya watso mun da na kasa fassara kona menene idanunsa sunyi fici fice har wata kwallar masifa ce ta taru a acikinsu, nuna ni yayi da hannu yace “bani da lokacin ki yanzu dan ba gurinki nazo ba, idan kuma kin isa seki hanani tafiya da ita mu gani” ya fizgi Hannun Amna zasu fita na jawo ta baya da qarfi har seda ta fizge daga hannunsa kafin na daka mata tsawa nace

“Wuce ciki, kai kuma ka fita idan ba haka ba wallahi se nayi maka abinda harka mutu bazaka taba mantawa dani ba. Maganar lokaci kuma har abada karka tabayin lokaci na Bashir saboda a sanda kake tunanin kayi lokacin nawa kafin nan ni kuma nayi maka nisa tamkar tazarar sama da qasa sedai kallo.

Daga yau ka dauka cewa bamu taba hada komai da kai a rayuwa ba Bashir, aure ne dai ya qare a tsakanin mu yara kuma da suka hada To gasu nan kaje ka kwada su ka cinye duk tsiya dai baka isa ka canza musu wata uwar ba Asma’un nan dai tana nan a matsayin uwarsu”

Na dakata na share hawayen fuskata kafin na cigaba da cewa
“Daga yau idan Anyi duniya dan manzon Allah na gama qunsar takaicinka Bashir kuma ka qaddara cewa naka shafin baqin ciki da zubda hawayen yana dab da budewa a rayuwa” Ina gama fadar haka na wuce daki na barshi a tsaye yana bina da kallo, jiki a sanyaye kamar wanda aka zarewa laka ya juya ya fice daga gidan.

“Allah yasa da gaske kikeyi, dukda da ciwo amma idan kika daure kika mayar da komai ba komai ba Ma’u zakiga ribar hakan a gaba. Bance ki dena son Bashir ba amma Ki share daga zuciyarki, ki gayawa kanki koda Bashir ko babu shi zaki ci gaba da rayuwa ki kuma tsohuwar Asma’un ki wani koke koke duk ba naki bane abinda be faru ba shi ake tara wanda ya faru kuwa sedai a kiyaye maimaita irinsa.

Kina kallonsa yanda yake abubuwan sa tamkar babu abinda ya faru, gidan da kika fita ya dakko wata ya saka dan ya nuna miki dake din da babu ke babu abinda ze chanza masa kuma walwalarsa yakeyi amma ke yana takalarki da duk abinda yasan ze quntata miki kuma ki biye masa ina dalili?

Ai wallahi yanzu shi ya kamata ki nunawa yayi babban Rashin da baze taba maida irinsa ba, ki tattara hankalinki guri daya ki koma aikin ki, ki ci duniyarki da tsinke dama ce yanzu ubangiji ya baki ta ki samu duk abinda kika rasa a baya.

Kin auri Bashir saboda kina mugun son sa yanzu kingani ga damar ki ta se irin mijin da kike so zaki samu kin kuma san kura kuren da kika tafka a zaben baya yanzu zaki kiyaye su shine kuma zaki zauna kina baqin ciki da abinda Allah ne ya so ki ya qwato miki yan cin ki.

Koda ace gaba zaki koma gidan Bashir Ma’u ina so kafin lokacin yasan kima da darajar ki ta yanda koda Allah ya sake qaddara zama a tsakaninku zeyi miki ruqo na gaske da bare sake bari ki kufce masa ba, amma kin zauna abu kadan ya jangwaleki kiyita masifa yana jin dadi haka mana Ma’u ki farka daga wannan magagin da kikeyi” haka Anty ta cigaba da gaya mun maganganu har seda ni kaina na ji haushin kaina kafin ta barni ta koma gida.

BASHIR
Sosai yanayi da kalaman Ma’u suka dake shi, babu abinda yafi tayar masa da hankali irin hawayen daya gani suna zuba daga idonta, me yasa shi a koda yaushe yake zama silar kukanta ne? Wai takamaimai meye dalilin daya saka ya kasa bawa Ma’u irin kulawar data kamaceta tukuicin sadaukarwar ta a gare shi?.

A duk sanda ya kalli cikin idonta yana hango tarin so da qaunar sa a ciki irin wanda yake saka mutum aikata komai domin farin cikin wanda yake yiwa wannan soyayyar amma a yau sam bega hakan ba illah tarin tsanar sa da dana sanin kasancewa dashi daya hango a cikin idanunta da suke zubar da hawayen nadama.

Harga Allah yana son Ma’u, yana kuma tsoron kar wannan abun daya aikata ya saka ta tsane shi domin a duk sanda So ya koma qiyayya yana zamowa me zafin gaske, idan kuwa har ace tarin so da qaunar da Ma’u take yi masa suka rikide zuwa Qiyayya tabbas ya shiga gararin rayuwa dan kuwa babu wani ruwa a duniyar nan da ze ishe shi wanke kansa yayi hasken da zata kuma kallonsa harta maida masa da wannan so da qaunar daya rasa.

Abu daya ne idan ya tuna yake sakashi jin dama dama wato cikin jikinta, a qallah yana da watanni bakwai kwarara da ze taka duk irin rawar da yake so daga qarshe ko taqi ko taso ya mayar da ita dakinta a sannan kuma ko sama da qasa zata hade babu wanda ya isa ya saka shi ya qarashe sauran igiyar datayi musu saura a tsakanin su koda kuwa Ma’u zata ringa yankar naman jikinsa ne saboda qi sedai ya mutu sannan ta samu yanci amma badai ya sake sakinta ba wallahi.

Da wannan tunanin ya koma cikin gida, duk yanda yaso ya rarrashi yaran sunqi sauraren sa haka ya haqura ya qyale su, a cikinsu ma yafi tausayawa Faridah da take mace ita kadai, da Amnah tana nan bashida ko wacce damuwa yasan zata kula dasu tamkar Ma’u tana nan amma yanzu besan yanda zeyi da Faridah yasan bazata sakw da Amirah ba.

“Kodai na mayar da ita gurin Ma’u?” Ya raya a ransa,
“Kai amma ai in nayi hakan kuma na kwafsa na gama buyagin banza tun ba’aje ko ina ba kenan taga gazawata, haka zata haqura har ta sake da Amirah da sauqi ma tunda ba nisa Ma’u tayi ba kullum zasu ringa ganin ta a hankali ma zasu warware su saba da zaman kafin komai ya daidaita mu ci gaba da rayuwar mu cikin farin ciki” Alhaji Malam Bashir ya sakw ayyana hakan a ransa.

Da rana Amirah tayi iya yinta ta musu jalof din shinkafa taji busashshen kifi da nama, ganin Bashir na zaune data gama harda zuwa ta kirawo su suzo suci kai tsaye kuwa Aliyu yace bazasu ci ba.

“Yaya kaje kayiwa yaran nan magana su fito suci abinci mana ni naje sunce sun qoshi” ta fada tana zama a kusa dashi, seya miqe ya shiga dakin, suna nan jugul sun dena kukan dai amma kowa yayi tagumi.

“Oya muje muci abinci se mu fita yawo ko ina kuke so muje?” Ya fada yana tsugunnawa a gaban gadon da yan biyu suke zaune, su daman basu tsawwala ba dan ba wani fahimtar budurin da akeyi sukayi sosai ba kawai duk abinda Aliyu ya fada ne sauran se su mara masa baya shiyasa suka suke zaune a dakin amma tun dazu Ahmad yake zungurin tagwan nasa yana masa radar su fita shi ya gaji sa zama, daman yunwa suke ji dan haka suka miqe da saurin su ya kama hannu su suka nufi qofa.

“Baban Mami fa? Bazaka bi mu ba?” Ya sake fada yana kallon Abdallah daya rabe guri guda, se yaron ya maqe kafada yace

“Aa ni gurin Mami zanje”.
“Toh muje kaci abinci seka tafi Mamin ko?”

“Abbi nima haka” Farida ta fada kamar zatayi kuka. Se ya waiwaya yana mata murmushi yace
“Muje toh kuci abinci me son zuwa gurin Mami ya tafi wanda zamu je yawo mu fita toh” nan da nan suka hau murna suka bi bayansa banda Aliyu da Jafar da suke tsaye nan fuska kamar Hadari, shima be kula suba, ai su ba yara bane kamar sauran idan yunwar cikin su ta ishe su zasu fito su nemi abinci.

Haka suka ci abincinsu da yaran ya biye musu sunata labari, zuciyar Amirah kamar ta fashe tsabar baqin ciki, taso ace sunqi cin abincin in yaso ta huta da sake yi masa wani girkin da daddare seta ajiye abinta amma yanzu shine zasu wani fito suci gashi se wani biye musu yake suna surutu duk sun bata gurin ai kuwa bari su gana sedai su gyara ko kuma shi din yayi dan ta gaji wallahi.

Bashir kuwa suna gamawa yace suje gurin Mamin kafin ya shirya se su tafi, haka suka kwasa da gudu zuwa gidan be ko bi takan Amirah dake mitar an bata guri ba ya shige dakinsa ya shirya tana kallonsa ya ci kwalliya yace mata sun fita da yara kar tayi girkin dare zasu taho da abinci.

ASMA’U
Muna zaune shiru su Faridah suka shigo da gudu suna rige rigen fadawa jikina. Da murnata na tare su wata zuciyar tana cemun
“Badai ya haqura ya dawo mun dasu ba kai amma da kamar wuya”.

“Mami unguwa zamu je da Abbi yanzu Yah Amnah ki chanza mana kaya” Ahmad ya fada.

“Iye yan gatan Abbi to ai kayan naku suna can gidan kuma na jikin ku ma babu abinda sukayi zaku iya zuwa dasu” na fada ina duba rigunan jikinsu na cire musu rigar sanyin da na saka musu dazu saboda garin da dan sanyi sanyi yanzu kuma yanayin ya daidaita.

“Mami nima na bisu” Amna ta fada tana kallona, sena daga mata kai kawai alamar “Eh” da saurinta kuwa ta shiga daki ta hau shiri Faridah ma ta bita dan ita kayan ta ba dukka aka kwashe ba daman. Suna gama shiryawa muka jiyo horn dinsa daga waje sukayi mun sallama gaba daya suka fice.

Ajiyar zuciya na sauke me qarfi bayan fitarsu dan kaso saba’in cikin fargabar rabani da yarana da Bashir yayi ya kau dan a zatona ze rabani dasu ne kwata kwata ya hanamun ganin su amma indai har haka za’a cigaba komai ze zo da sauqi kenan.

Yan gyare gyarena na tashi na shigayi bayan na gama na hau kwaba musu cake na tafiya makaranta tunda basa zuwa da abinci acan suke basu harna rana shiyasa se nayi musu dan abin tabawa su tafi dashi bayan sun karya a gida shima Bashir na zuba masa to yanzu kuwa sedai Can Matar sa tayi masa indan zata iya su dai zan ci gaba da yi musu yanda na saba in zasu tafi na basu.

Ina cikin kwabin cake din Aliyu da Jafar suka shigo, ina kallonsu nace
“Aa ku ban da ku aka tafi yawon kenan?”

“Ban da mu, Mami akwai Abinci?” Jafar ya fada yana nufa yana bude tukunya, Aliyu kuwa kan deep frizzer ya hau ya zauna yana kumbura fuska,

“Ali mazan fama ya akayi ne ko kaima yunwarce ga abinci nan ku diba ku ci to”.

“Wallahi Mami watarana sena sumar da matar can idan ta sake shiga harkata” ya fada yana sake hura baki. Se na ajiye Mixer hannuna na juya dakyau ina kallonsa nace

“Wace mata zaka sumar kuma Aliyu?”
“Amirah mana” ya bani amsa kai tsaye.
“Kana jina ko Aliyu, karku kuskura kuce zaku saka abinda ya faru tsakanina da mahaifinku a rai har hakan ya shafi alaqarku dashi.

Rabuwar mu qaddarah ce daga ya rigada ya tsara iya lokacin da zamu zauna kunga babu abinda ze chanza hakan, sannan tsakanin ku da matarsa babu rashin kunya dan ba ita ta raba mu ba Allah ne ya kashe auran mu.

Koda wasa karna ji dayan ku yayi mata wani abunda ba daidai ba dan idan ma kunyi a maimakon ku ce kun rama abinda akayi mun qaramun laifi zakuyi aringa cewa ni na saka ku dan haka babu ku babu sabgarta. Duk abinda kuke nema a gidan baku samu ba kuzo nan shikenan”.

“Amma ki gaya mata wallahi Mami duk randa ta qara zagar mun uwa ko tace zata dakeni kafin ta fara ni zan doketa tam” Aliyun ya sake fada kafin ya sauka daga kan freezer ya fice daga Kitchen din gaba daya. A yanda yayi maganar hatta da muryarsa se najita kamar ta Bashir idan yana cikin fushi se kawai na bishi da kallo kafin nace
“Allah ya shirya ka ya rage maka wannan zafin zuciyar” se na juya kan Jafar dake kwasar abinci nace

“Meya hadasu da matar Babanku yake cewa ze daketa?”

GIDAN BASHIR BAYAN FITAR SA
Bayana Bashir ya fita seda Amirah ta tabbatar taji tashin motarsa alamar sun tafi ta sake leqawa taga basa nan kafin ta kulle qofar ta ciki ta yanda dole se an buga zata zo ta bude.

Dakin su Aliyu ta wuce kaitsaye, A zaune ta tatar dashi da Jafar suna magana sama sama

Please Login or Register in order to submit comment