Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dagawa daga baya ma blocking dinsa yayi, haka Naziru ma baya amsa wayarsa to yan uwansa ma kenan kuma shi bashi da sauran wani shaqiqij Abokin da ze tattauna wannan matsalar in banda Balan se Abubakar da ko giyar wake yasha be isa ya tun kare shi a yanzu ba.

Abdulkarimu ne ya fado masa a rai, ba bata lokaci ya danna masa kira kuwa akayi sa’a ta shiga seda ta kusan tsinkewa kafin ya daga wayar

“Alhaji Bashir yaushe rabon da ka nemeni tunda giwa tayi lafiya ka samu kan Madam shikenan ka watsar dani” Abdulkarim ya fada bayan da suka gaisa. Seda Bashir yaja numfashi kafin yace

“Abdulkarim ina cikin Bala’i na rasa yanda zanyi wallahi ka taimaka mun”

“Allah yayi mana maganin abinda ya damemu, lafiya dai Bashir meya sameka haka kake dangana kanka da Bala’i?”

“Abdulkarim hau ce ta hauni, nabi dokin zuciya na saki Ma’u gashi yanzu harta gama iddah ban mayar da ita ba na rasa inda zan kama ji nakeyi kamar zan haukace, yanzu har ta fara kula wasu Mazan sau biyu ina ganin ta a motar Maza Abdul” ya qarasa maganar kamar ze fashe da kuka saboda yanda yakejin zafi a duk sanda ya tuna ganin da yayiwa Ma’u na jiya dana yau din.

Salallami Abdulkarim ya ringayi yana cewa
“Ka saki Ma’u Bashir wace irin hau ce kai kuwa take binka haka ka rasa matar da zaka saka a rayuwa se Asma’u, Asma’u fa Bashir toh wallahi babu ruwana, abu daya zan iya maka inyi maka Addu’ar Allah ya taqaita maka wahala na kuam roqeshi karya maido maka da Asma’u rayuwarka dan baka san darajarta ba”

“Idan Allahn naka ne seka roqeshi karya dawo mun da ita din, na kiraka ka bani mafita shine zaka zageni kayi mun fatan tsiya ko? Daman nasan ba qaunar zama na da ita kake yiba, to dakai da duk sauran masu jin dadin abinda ya faru kuna kallo Ma’u zata dawo mun sedai baqij ciki ya kashe ku ku mutu”.

“Allah ya yafe maka Bashir” Abdulkarim ya fada kafin ya kashe wayarsa.

Bashir kuwa hada kansa yayi da teburin gabansa yana sauke numfashi, babu abinda yake cizon zuciyarsa irin idan ya tuna ganin da yayiwa Ma’u da wasu, Matarsa Ma’u da wasu qartin maza da sunan zawarci.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Allah ka kawo mun dauki, Allah karka barni da iyawata” ya fada a fili yana sake wawurar wayarsa, dole ya ajiye duk wani abu a gefe ya kira Baba, ko ze zageshi kai idan ma ta kama yaje ya tsugunna a samowa Baban bulala ya zane shi duk ya yarda indai ze saka baki Asma’u ta haqura ta dawo masa dan yasan a yanzu dai su biyu ne zasu iya shawo masa kanta babu musu ta yarda daga Baban se Goggonta, shi kuwa dai rashin kunyar tasa bata kai ya tunkari Goggo a yanzu ba dan yaci ace kafin ya saki Ma’u ya tuno da karamcin matar amma duk ya hada ya take to wai shi me tayi masa ne ma??

Sallamar da Baba yake ta faman kodawa ce ta dawo dashi hankalin sa ashe wayar ta shiga tuntuni yana can zurfin tunani be sani ba.

“Barka da rana Baba, ya qarfin jikin?”
“Barka dai Bashari, jiki Ahamdulillah idon ka kenan se yau zaka kirani ko da yake kaida kake da Amarya ai dole ayi maka uzuri” Baban ya fada babu wata damuwa a muryar sa.

“Ayi haquri Baba” Bashir ya fada yana gyara zama, yanda yaji Baban a sake ya qara masa kwarij guiwar fadar abinda yake ransa.

“Ba komai ai nima ban ce kayi laifi ba, ya iyalan naka gaba daya da yaran kuna lafiya dai ko?”

“Lafiya lau Baba sedai Ma’u ce dai..” se kuma yayi shiru ya kasa ci gaba da magana, Alhajin da yaji yayi shiru yace

“Me Ma’un tayi kuma? Lafiya dai ko wata matsalar ce ta sake tashi?”

“Daman Baba naje ne jiya da niyyar mu sasanta na mayar da ita dakibta, shine take gaya mun wai tayi bari bayan mun rabu dan haka iddarta ta cika tuntuni babu kome tsakanin mu”

“Kai masha Allah barka barka abu yayi dadi gaskiya, ai kuwa na kirata da mun gama wayar nan tunda nima laifinka ya shafe ni kwana biyu ta dena kirana” Baba ya fada cikin murna kamar be ji abinda Bashir din ya fada ba.

“Baba kamar baka gane me nake cewa ba” Bashir ya fada a rarrabe, se baban yayi murmushi yace

“Nagane Bashir, kace Ma’u tayi bari ko iddarta ta cika. Murna nake tayata da Allah ya dubi kyakykyawar zuciyarta ya rabata Mijin da besan darajarta ba butulu irinka, wannan kadai ya isheka ishara ka gane cewa Allah yana arawa mutum dama ne a rayuwa idan yayi wasa ta subuce masa shikenan sedai ya mutu yana nadama da dana sani, yanzu daka kirani me kame so nayi maka?”

Kwata kwata kalaman Baba basu dami Bashir ba dan ya tsammaci fiye da haka ma, shidai fatansa Baban yayi iya fadan da zeyi ya haqura tunda dai ai bazece yafi son farin cikin Ma’u akan nasa ba.

Seda ya sake marairaicewa sosai kafin yace
“Na karbi kuskurena Baba duk abinda ka fada gaskiya ne kuma na yarda, zan chanza hali wallahi zan dena duk abinda kasan inayi na rashin kyautawa kasa baki Ma’u tayi haquri ta koma dakin ta”.

“Toh fa da wuri haka Malam Bashir kuma ni wannan lissafin ai bani zaka yiwa ba ita wacce kayiwa laifi can zaka samu ka bawa haquri ka gaya mata ka chanza ko kuwa kayi shawara dani sanda kayi sakin”

“Ko naje Baba bazata saurareni ba tace ta gama aurena dan girman Allah Baba kaji tausayina ka saka baki nasan kai kadai ne zaka saka baki ta haqura ” Bashir ya fada kamar ze fashe da kuka

“Amma Allah yayiwa Asma’u Albarka, in gaya maka gaskiya Bashir indai da shawara ta ne bazan taba barin Asma’u ta koma gidanka ba zan kuma ci gaba dayi mata Addu’ar Allah saka mata ladan haqurin da tayi dakai ya bata mijin da ze yasan mutunchinta, Idan Wannan ya sa ka kirani to se anjima kar kuma ka sake kiran wayata indai akan wannan shirmen ne” kafin Bashir ya sake cewa wani abu Baba ya kashe wayarsa.

Ji yayi zazzabi na neman rufeshi, ya hade kansa da guiwa yana jan Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un a zuciyarsa abinda yake dauka ze zo masa da sauqi gashi se komai yana sake rincabewa, ya zeyi? Waze kama? Ta ina ze fara? Duk be sani ba.

Haka ya qarasa wunin ba tareda ya saka ko ruwa a cikinsa ba ya kamo hanyar gida dan bashida wata nutsuwa, se a sannan ma ya ji daya sani Azumi yayi da wannan wunin yunwar yana shiga ya tarar da Amirah tana masifa Ahmad ya zubar da Lemo akan carpet tanayi masa magana ya gudu waje,

Tun kafin tayi masa magana ya tareta da cewa
“Bana jij dadi, ki barni dan Allah karki qara mun damuwa akan wacce nake ciki, ki hada abinci na ki kawo mun daki” ya shige ciki ya barta.

Yana wanka ta shiga da Try ta zubo doyar dazu da safe a plate se Sauce din Hanta da Albasa da ta dan qarayi saboda doyar tayi Armashi ga Lemo me sanyi na Exotic da ruwa duk ta ajiye masa.

Yana fitowa ana kiran sallah dan haka ya zura jallabiyya ya tafi masallaci seda ya dawo ya tsaya a Kitchen ya fara hada shayi kafin ya wuce dakin dan gaba daya hanjinsa sun qulle, yana bude farantin ya fara kwala mata kira, Amirah na can ta sake wanka tana kwalliya ta jiyo kiran nasa, seta zura hijab ta fito tana mitar

“Haka kawai daga dawowarka shikenan kuma mutum baze huta ba zaka fara kiransa kamar wani saboj makaho” da wannan mitar ta tura qofar ta shiga babu ko sallama.

“Meye wannan kika kawo mun” ya fada yana nuna doyar, seda ta harare shi ta qasan ido kafin tace

“Doya ce, naga da safe baku ci ba kuma kar ayi almubazzarancinta shiyasa na ajiye na dumamata yanzu, gashinan har sauce fa nayi maka dan kaji dadin ci”.

“Tunda kike kin taba ganin an maimaita mun abinci a gidan nan, bama wannan ba ke kike siyan abincin da bazaki dafamun abinda nake so ba ko kuwa” ya fada a nutse dan bama shi da qarfin yin masifar a sannan.

“Ni fa na gaji da wannan abun, duk abinda nayi ban iya ba a gidan nan, ance bana girki idan kuma nayi a qi ci akan me wallahi daga yau idan na dafa in za’a kwana goma ba’a cinye ba shi zanyita maimaita wa ba ruwana ai ni ba yar aiki aka dakko ba balle ace...” bata san tasowarsa ba se saukar tagwayen mari dataji akan fuskarta, kafin ya angizata waje, ya sake komawa ya kwashi try din abincin ya watsa mata sannan ya kullo qofarsa.

Dafe qirjinsa da yayi masa nauyi yayi ya fada kan gado da baya, beyi aune ba sejin wasu hawaye masu dumi yayi suna gangarawa zuwa cikin kennensa a maimakon ya hana kansa se kawai ya bude baki kamar qaramin yaro ya shiga rera kuka irin na wanda duniya tayiwa daurin Goro.


Ayi haquri dab Allah 🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 47

Kuka me sunan kuka Bashir yayi tamkar wanda aka cewa Dada ta mutu, seda yaji wani kaso na damuwarsa ya kafin ya shiga bandaki ya wanko fuskarsa ya dawo ya zauna tareda rafka uban tagumi ga Yunwa se sakadar ciki aa takeyi dan takaici shayin da ya hado ma be sha ba harya huce.

Yana zaune a gurin seda yaji hajijiya na neman kadashi kafin ya miqe da kyar dan dole ya gita ya nemi abinda zeci kafin yunwa ta kashe shi, yana bude qofar ya ga Faridah a tsaye, da Alama kwankwasawa zatayi.

"Abbi kaga Anty Amirah ko, dan kawai na tambayeta kai shine ta zage ni" Faridah ta fada tana hararar Amirah dake zaune can kan kujera tana kada qafa. Komawa ciki yayi Faridah ta bishi ta kwandon Abinci ta ajiye tana cewa

"Abbi ga Abinci, a gurin Mami na karbo maka kaga harda zobo ta ce a kawo maka sadaka".

"Sadaka, Almajiri na zama kenan lallai Ma'u" ya raya a ransa kafin ya hadiye wani tsinkakken yawu sanda qamshin shinkafar ya dake shi, ga Kaza mutuniyarsa.

Faridah na shirin Zuba masa a plate ya karbe kular gaba daya ya saka cokali ya shiga cin abincin kamar wanda ya shekara yana Azumi seta miqe ta koma kan kujerar dake dakin ta zauna tana kallonsa.

Cikin dan lokaci Bashir ya tashi abincin nan tas Ya shanye Zobo Faridah dai se kallonsa takeyi, seda yayi gyatsa tareda hamdala kafin ya kalli Faridan ya miqa mata hannu alamar taje. A jikinsa ya dorata ya sumbaci goshinta kafin yace

"Nagode Faridah ta kamar kin san Abbinki Yana kewar Abincin Mami".

"Abbi yah Amna ce tayi ai, kuma Abbi tunda Anty Amirah bata girki kaima ka ringa zuwa gidan Mami kana ci mana kaga mu a can muke cin abincin mu me dadi" Faridah ta fada tana marairaice masa, murmushi yayi yace

"Ai ba laifina bane Mami ce bazata bari ba, amma ki gaya mata da kanki ki roqeta ta dawo nan gidan ko ni na ringa zuwa can se mu ringa cin abinci tare duka yanda muka saba ko?"

"Toh Abbi amma bakaine ka koreta daga nan gidan ba ai nasan bazata sake dawowa ba sedai kai ka ringa zuwa can, gobe da safe zan gaya mata tunda yanzu dare yayi"

"Shikenan, dauke kwanukan kije ki kwanta Allah ya yi miki Albarka"

"Amin Abbi" ta fada tana hada kayan a kwando ta fice taja masa qofar.

Wani irin sanyi da nutsuwa Bashir yaji a zuciyarsa, to kodai maganar Bala gaskiya ce da yace ya bata guri idan aka kwana biyu zata huce su daidaita tunda gashi kuwa yaga alama.

Idan har Asma'u zata aiko masa da abinci to kuwa in yayi haquri yana zaune zata neme shi su shirya, daman ya sani duk abinda zata fada iya fatar baki ne be kai zuciyarta ba. Ya sani Ma'u tana sonsa kowa kuma ya shaida hakan shima yana sonta amma ya rasa me yasa mutane suke da tantama akan son da yakeyiwa Ma'unsa.

Tashi yayi yaje yayi brush ya dawo kan gadon ya kwanta gaba daya jikinsa ya mutu tunda ciki ya dauka bacci kawai yake da buqata, wayarsa ya jawo ya rubutawa Ma'u text

"Nagode Ma'una, uwargida na har a Aljanna" yana turawa ya saka wayar a silent ya ajiye zuciyarsa qal ya kwanta tareda jan bargo dan gani yake kamar ma har sun shirya da Ma'u ai, hannunsa ya miqa ze kashe makunnin filtila ya jiyo kamar Muryar Faridah tana kuka, se ya miqe ya fita palour yana zuwa kuwa ya tarar da Amirah ta cukumeta kamar me danbe da sa'arta tana cewa

"Ni za'a nunawa Bariki, a zubo abinci daga wani guri a baki ki kawowa mijina ko to wallahi duk abinda aka zuba bazeyi tasiri ba, zama na daram a gidan nan babu yanda aka iya dani ke kuma sena miki dukan tsiya ta yanda gobe bazaki sake karbo abu ki kawo masa ba" Ta kaiwa Faridan Mari ya tareta a fusace ya tunkudeta gefe yana cewa

"Wai ke wace irin shedaniya ce da baki taba so a zauna lafiya, saboda dazu na barki shine yanzu zaki kama mun yarinya kina duka akan me?"

"Akan me ma kake tambayata? Da kasan kana son abincin uwar tata me yasa ka koreta daga gidan ai da seka barta ta zauna tayi ta girka maka kana ci dan haka yanzu wallahi baka isa a ringa shigo maka da abinci daga wani guri kaci ba, kodai kaci wanda na dafa ko kuma ka zauna da yunwa idan ka fita can waje ka siya kaci ehe" Amirah ta fada tana girgiza jiki a gabansa,

Tsabar mamaki Bashir ya gagagara cewa komai, yanzu shi take tsayawa a gabansa tana gaya masa be isa yayi abu ba a cikin gidansa ba bata jin tsoron bare shakkar gaya masa duk abinda taga dama lallai Amirah.

Jan hannun Faridah yayi zuwa dakinsa kafin su qarasa kuwa Amirah ta tare qofa tana cewa "Ai wallahi bazata sake kwana a dakin nan ba idan banda rainin hankali ni ina matar gida ka koreni daga dakinka sannan ka bar yarka ta kwana a ciki baze yuwu ba".

"Amirah ki matsa mun daga hanya bana cikin yanayin da zan biye miki yanzu" ya fada yana kokawa da bacin ransa, Amirah kuwa ko a jikinta sema qara babbake hanya da tayi tana murguda baki tasan dai qarqari yace ze mareta ko to kuwa ta dena tsayawa ya daketa kamar wata jakarsa.

Ganin da yayi ta kafe a qofar bata da alamar matsawa ga shi sauran yaran duk sun fito suna kallo yasa ya sassauta murya yace da Faridah
"Wuce dakin Antyn ku ki kwanta, ke kuma shiga ciki muyi magana"

"Nifa na gaji tun wuri ka nemar mata Gurin ka nemar mata gurin kwana, haka kawai banida sirri nida dakina" Amirah ta fada cikin qunquni tana hararar Farida data tafi dakinta, wucewa Bashir yayi ciki tabi bayansa tun kafin ta zauna ya juyo a mugun fusace yana cewa

"Wannan ya zama karo na qarshe da zaki sake gaya mun magana a gaban yayana, sannan ke kike zamana ko ni nake zamanki dan Saboda baki da tarbiyya zaki kalleni kice ban isa nayi abu ba, so kike ki qure ni ko Amirah? Bazaki ji dadin abinda zan miki ba wallahi ki bar ganin ina daga miki qafa, ranar dana waiwayo kanki bazaki ji da dadi ba"

"To nima a dena yimun abinda bana so indai ana son zaman lafiya" ta fada ba tareda ta kalle shi ba, da mamaki ya ke kallonta, kallon wai daman haka take ko kuwa yanzu ne tazama hakan.

A da dai duk rashin kunyarta bata tsayawa a gabansa ymta gaya masa magana sedai taqi bin umarninsa amma yanzu a gabansa qiri qiri yana fada tana fada bata ko shakkarsa yaushe suka fara haka.

Gani yayi idan ya biye mata qarshe ze iya lakada mata dukan da zata kasa tashi se kawai ya haye gado ya barta a tsaye tana ci gaba da qananun mita, har kansa yaja bargo, yana jinta ta kashe fitilar ta hau kan gadon tana matsawa jikinsa ya tureta yana cewa

"Kika sake tabani sena kwada miki mari wallahi, saboda bakida kunya ki gama zagina sannan kizo kusadani dallah matsa can kafin na make ki"

"Allah dai yana kallo idan kuma aka take mun haqqina ba yafewa zanyi ba ehe" ta fada tana murguda baki kafin ta sauka daga gadon ta koma kan kujera.

Zaune Bashir ya tashi shima ya zuba mata ido kawai yana kallonta amma taqi bari su hada ido, shi tayi wa Allah ya isa? Shi Amirah ta ke zagi harda Allah ya isa

Wani irin tuquqi zuciyarsa ta shiga yi masa idonsa ya kada yayi jajir kamar wuta, cikin kakkausar muryar da seda ta bata tsoro yace mata

"Fita daga dakinan, idan kika bari nazo inda kike sena illataki Amirah, kuma wallahi ko tashin Faridah kikaje kikayi daga bacci yanzu se nayi miki dukan da na lahira seya fiki jin dadi wawuya mara hankali kawai".

Da sauri ta fice, a palour tayi kwanciyarta ko banza dukkan su zasuyi kwanan baqin ciki, yanda ya bata mata itama tayi masa fiye da haka ai su zuba su gani ita da shi za'a ga wanda ze gaji tunda tagane duk abin nasa ma hargagin qarya ne.

Bashir kuwa kasa kwanciya yayi sya shiga safa da marwa a dakin, Allah sarki Ma'u a zaman sa da ita baze taba cewa ga ranar data zageshi ko ta gaya masa maganar da zata sosa masa rai haka kawai ba.

Iya qarshen ladabi da biyayya tayi masa amma ya raina abinda takeyi yake ganin kamar bata girmana shi irin yanda ya kamata qarsheya saketa a dalilin wata, watan da gata nan tun ba'aje ko ina ba ta fara tsayawa a gabansa taba qare masa tanadi tabbas kuwa dole ya dauki mataki akan hakan, ya hukunta wadda batayi masa laifin komai ba balle ita data siya da kudinta dan haka ta shirya karbar sakamako daidai da abinda ta aikata masa.

Washe gari ta kama Juma'a tun asuba ya gayawa Amirah ta hada musu abin karyawa, yanayin yanda yayi magana ya saka bata musa masa ba ta dai bishi da harara daya fita tana idar da sallah ta hau firar dankalin kafin bakwai ta soya tas harda qwai ta dafa ruwan shayi.

Yana zaune a palour dan da wuri ya shirya ya fito tagama jera komai, yaga alamar saken daya bata ya saka raini shiga tsakaninsu a yanzu ne ze tabbatar mata da be chanza ba yana nan a Bashir dinsa data sani.

A daure yace mata taje ta kirawo yaran suzo su karya, suma kuma basu musa ba harda Aliyu duk suka zauna a Dining din kowa ya hada shayi, Aliyu ya turawa yan biyu farantin daya zuba musu dankali Ahmad na taunawa ya watsoshi waje yana cewa

"Kai kai muba haka Mami take yi mana ba".
Ahmad ya fada yana bata fuska, ai kuwa Amirah ta zaburo masa tana cewa

"Aa ba Mami ba uwar Mami ce ba haka takeyi muku ba shege me qaton kai"

"Se dai taki uwar Addah, kuma wallahi kika sake zagar mana uwa se mun hadu mun miki duka a gidan nan" Aliyu yayi wo kan ta kamar ze daketa a lokacin, seda ta ja baya gurin kujerar Bashir daya hada hannu biyu yana kallonsu kafin tace

"Ni zaka daka ashe zaka iya dukan uwarka Asma'u kuwa in dai zaka dake ni"
A mugun zuciye Aliyu yayi kanta kafin Bashir ya miqe har ya kai mata gula da qafa ta sunkuya ya sauke mata qafar a daidai kunne ai kuwa ta fasa qara ta zube a gurin be tsaya ba ya sake yin kanta amma kafin ya kai mata wani dukan Bashir ya tareshi tareda zabga masa mari.

"A gabana Aliyu zaka daki matata?"

"Ai a gaban naka ta zagi uwata kuma baka hanata, wallahi tunda ka saki uwarmu akanta itama bazata taba zama lafiya a gidan nan ba, ku tashi mu tafi" Aliyu ya fada babu ko dar a fuskar sa, ya kada qannensa waje suka fice suka bar Bashir da Amirah a gurin.

Amirah dake durqushe a qasa ta riqe gefen fuska tana kuka ta kalli Bashir tace
"Kana kallo sun tafi bayan ya kurmantar dani, wallahi bazan yarda ba se an bi mun haqqina"

"Dallah ki rufewa mutane baki, duk ba ke kika jawa kanki ba? Sau nawa zan gaya miki ki dena shiga sabgar sa  a kan me zaki zagi uwarsu sa'arki ce? Sannan ai ba qarya Ahmad din yayi ba kin soyawa mutane abu salam babu ko digon gishiri tayaya ze cuwu, se ki tashi kije ki samu ruwan dumi ki gasa gurin idan da man zaitun ki tsiyayaqa kunnen gobe ma ki sake zagin musu uwa su sun san darajar ta" yana gama fada shima ya dauki jakarsa ya fice.

Yauma dai haka ya fita beci abinci ba shidai bashi da maraba da gauro yanzu gauron ma mara galihu.
A bakin motar ya hango su Asma'u tayi parking daidai gurin suna magana kafin ya qarasa taja motar ta ta wuce dan haka ya bude musu motar suka shiga, haka ya kaisu makaranta ya ajiye su sannan ya tafi ya siyo musu breakfast a wani gidan abinci kusa da gurin ya sake kai musu kafin ya wuce office dinsu zuciyarsa kamar zatayi bindiga saboda takaici.

AMIRAH
Suna fita ta tashi dakyar ta dakko wayar ta ta dannawa Addah kira, a speaker ta saka dan da gaske fa kunnenta yaji duka tana dagawa ta saka mata kuka tana cewa

"Wallahi Addah na gaji bazan iya ba, haka kawai na zama kamar jaka shi ya dakeni sannan yanzu takai yayansa su dake ni nidai na gaji tahowa kawai zanyi"

"Ki taho ina? Ni Fattu kashe ni kuke so kuyi ne ko me, nan ga wannan shegiyar ta dibgo mun abun kunya ke kuma kina shirin kaso auranki ki dawo to bazaku kasheni ba koma menene yanzu ki dakata mun na kashe wanann wutar kafin ta fasu idan yaso se na dawo kanki" Addah ta fad cikin tashin hankalin da muryarta ta kasa boyewa.

Cikin rashin fahimtar maganar Addahn Amirah tace
"Addah meya faru? Wane irin abun kunya kuma aka dakko miki badai bashi kika sake ciwo aka zo ana miki cin mutunchi ba?"

"Yo ba gara in ci bashi ba ko birsin ne a kaini da abinda wannan yar iskar yarinyar tajawo mun, ciki fa cikina haihuwa Ummi tayo har wata uku yanzu ina zaune ban sani ba.
To wallahi na gaya mata zubar dashi zamu tafi yanzu ayi dan bazata ja mun abinda za'a ringa zundena a garin Idan na wuce ba shi kuma shegen matsiyacin da yayi mata daga baya inyi qararaa tunda ai na raba shi da yata yaqi barinta seda ya dibga mata ciki tukunna" Addah ta fada cikin masifa se haki takeyi,

Amirah na jiyo kukan Ummi daga gefe tana cewa "ni wallahi baza'a cire ba, haka kawai ance mutuwa akeyi. Ki kyaleni ai Jawad din ya yarda idan na haihu zamuyi aure"

"Sedai ki auri ubanki, na gaya miki indai ina raye bazaki auri wannan matsiyacin ba wallahi" Addah ta zabura tayi kanta, can ta wullar da wayar ma da alama ta manta da cewa waya takeyi.

Zugudi Amirah tayi da waya a hannu cikin tashin hankali, ciki dai cikin shege Ummi ta yi to yaushe hakan ta faru? Zama tayi akan gado ta rafka tagumi radadin da takeji a kunnen ma ya tafi saboda jin sabon tashin hankali yanzu me Alhajin su zece idan yaji wannan maganar ta tabbatar da sedai Allah ya tsare amma da wuya auran Addah be mutu ba a dalilin wannan abun amma.

Ummi ta cuce su koda yake ba Ummi ba Addah zatace ta cuci Ummi tunda babu yanda batayi akan ta barta ta auri wanda take so ba amma ta kafe cewar bazata aureshi ba saboda bashida komai, shegun da take yawan ambatarsu dashi gashi yanzu ya tabbata ai seta shirya goya shegen jika.

Wanann maganar ce ta kashe wutar abinda ya faru da safe, haka ta wuni jiki a sabule batayi musu girki ba daman yaran suna dawowa gidan Ma'u suka wuce

Please Login or Register in order to submit comment