Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 41

Addah tana cin abincinta tana sake gayawa Dada da tayi zugudi yanda za'ayi. Da tasan halin da Dadan take ciki a sannan ma da tayi shiru tuntuni. Seda ta kwashe abincinta tas tayi gyasa kafinta dauraye hannunta tana cewa

"Kinga kirashi muji zancen sakin nan da kunnen mu karma qarya shegiyar yarinyar can takeyi kinsan fa daman ta iya ta, qilan dan fada sukayi kar mu gama murna muji sabon labari".

"Nidai Addah da kin tashi kinje gida kawai daga baya mayi magana" Dada ta fada tana waiwayen dakin Alhajin su Bashir daidai lokacin kuwa ya turo kekensa ya fito daga dakin.

Fuskarsa ba yabo ba fallasa suka gaisa da Addah, ba tareda ya ko kalli inda Dada take ba ya kira Naziru daya kafe a guri daya kaman gunki yace ya kaishi waje.

A qofar gidan kuwa bayan Naziru ya ajiye a gurin da yake zama suyi hira da mutanen sa se ya kalli Nazirun yana murmushi yace

"Kaji abinda uwarku da yar uwarta suka aikata ko? Ni sam ba wannan Nafisan na aura ba ban kuma san lokacin data zama me son kanta da son zuciya irin haka ba. Amma shikenan, suma ai sun haifa".

"Kayi haquri Baba" Naziru ya fada,
"Kai zan bawa haquri ai Naziru ku da Allah ya jarraba da uwa mara tunani, kuyita Addu'a Allah ya tsare ku da fadawa hali irin wanda dan uwanku yake ciki dukda shi da kansa ya jefa kansa ba wani ya aike shi ba, idan kuwa harta tabbata Bashir ya rabu da yarinyar nan, hmmm Allah dai ya rufa asiri" Baba ya fada yana zaro kudi a aljihunsa ya miqawa Naziru yace

"Karbomin katin Mtn na kirashi naji, wayata babu kudi".
"Bari na tura maka ta Banki Baba" Naziru ya fada sannan yayi masa transfer katin ya danna wayar Bashir.

BASHIR
Se da gabansa ya fadi da yaga kiran Alhajin su dan muddin ba abu me matuqar muhimmanci ba Alhajin baya kiransa sedai shi Bashir din ya kirashi.

Yasan kiran baze rasa nasaba da maganar sa da Ma'u ba labari yaje musu kuma wannan yarinyar ce zata fada dan se daga baya ma ya shiga dana sanin me yasa ya gaya mata? Dukda ko ba yanzu ba ai dole zasuji amma qila se kafin sannan ya gama daidaita komai.

Be daga ba seda wayar ta katse yabi bayan kiran a ransa yana shirya abinda ze fada masa.

"Barka da Rana Baba" Bashir ya fada bayan da Alhajin ya daga wayar, se ya mayar masa da cewa

"Barka dai Muhammadu ya aikin ya iyali?"
"Duk suna lafiya Baba, muna cikin aiki ne ma yanzu idan ba damuwa zuwa anjima idan muka fita sallah sena kira" Bashir ya fada yana goge zufar da tafin hannunsa yayi a jikin rigarsa, Allah yasa ba wannan maganar Baban ya bugo suyi ba dan besan me zece masa ba

"Ai maganar tawa gajeriya ce tambaya daya ce zan maka seka ci gaba da aikinka, shin dagaske ne ka saki Asma'u?" Maganar Baban tayi masa dirar mikiya nan da nan ya fara in ina kamar wani sabon kurma duk yabi ya rude, dakatar dashi Baban yayi da cewa

"Nutsu mana Malam Bashari tambaya ce fa me amsa da Eh ko Aa amma duk ka rikice kamar wanda Alqali ya titsiye, kaga aiki kakeyi ka amsamin na kashe wayata shikenan".

Yanda yayi maganar a dake ya tabbatar wa da Bashir ba a cikin lokacin wasa yake ba, dan haka dole ya kama kansa kamar qaramin yaro yace

"Eh Amma..."

"Riqe bayaninka ai ka amsamin, yanzu dai ina so naji ka tuna rabar daka zo mun da zancen zaka auri yar gurin Fattu abinda na gaya maka?"

Shiru Bashir yayi ya rasa ma wani abu ne ya dabaibayeshi,

"Dakai nake magana kayi shiru fa Bashir" Baban ya daka masa tsawar data sakashi magana babu shiri yace

"Na tuna Baba"
"Me nace maka?"
"Ka tambayeni dole akayi mun nace maka Aa ra'ayin kaina ne, sannan ka sake tambayata me Asma'u tayi mun nace maka babu komai"
"Daga nan kuma fa?"

"Ka gayamun cewa Asma'u matar rufin Asirice kuma mayafi ce data lullube ni, idan kishiya zan yi mata naje na nemo yar gidan mutunchi wadda tasan qimar kanta na hadasu amma na kafe nace ni Amirah nake so".

"Ba shakka kafiya tayi amfani. Tun ba'aje ko ina ba ta rabaka da uwar gidanka uwar yayanka shida ko, to ka dai bi a sannu Bashir idan bakayi sa'a ba duniya da kanta zata koya maka karatun da ka kasa ganewa, seka zubda hawaye a lokacin da babu amfanin da zasuyi maka, ita matar fari komai mugun halin ta tana cin wannan darajar ta kasancewarta tushiya bare kai da Allah ya datar dakai da samu mace ta gari yar gidan mutunchi shine kaga ta wannan hanyar zaka gode masa ba madallah, gaka ga Fattu nan da yarta sun isheka bada misali a gaba" yana gama fadar haka ya kashe wayarsa.

Sosai yake jin baqin ciki da takaicin abinda Bashir ya aikata, me yasa tun a lokacin da Asma'u ta nuna bazata zauna dashi ba be goya mata baya ta barshi tun a sannan ba? Daya san haka zata faru a gaba da koda qarfin tuwa se Bashir ya bata takardarta a lokacin da ita da kanta ta buqata amma ba'a tara sani da ikon Allah, shi yanzu da wane ido ze kalli yarinyar da Ahalinta.

Wayarsa ya shiga lalubawa ya shiga neman Number Alhaji Qarami dan a yanzu shine matsayin uban Asma'u, cikin Sa'a ya samita kuwa ya dannan masa kira.

Cikin mutun taka suka gaisa kafin suka shiga jimamin abinda ya faru kafin yace ya turo masa da Number Goggo ze kirata da kansa tunda Alhajin yace bata sani ba.

Suna gama wayar kuwa ya tura masa dan shikansa yana ta taraddadin ta yanda ze sanar mata da wannan labari a irin yanda ta daukaki Bashir kamar dan data haifa.

Cikin sa'a Alhaji Amadu yana kiran Goggo ta daga wayar, bata da lambar ya sani dan haka yayi mata bayanin shine nan suka sake gaisawa tana tambayarsa jiki da su Dada ya amsa da duka lafiya kafin suka yi shiru.

"Hajia abu ne mara dadi ya faru amma ina so dukka muyarda da komai muka gani a rayuwa muqaddari ne daga ubangiji ya na yin abinda yaso a kuma sanda yaso" Alhaji Amadu ya fada bayan daya katse masu shirun.

Goggo cikin rashin fahimtar inda zancen sa ya dosa dukda tasan dai baze wuce akan Asma'u ba dan haka tace masa

"Amma Alhaji meya faru ne ban gane maganar da kake yi ba".

"Kiyi haquri Hajia kuma ki fahimceni, magana ce akan Asma'u da Bashir, kinsan da aure da mutuwa da haihuwa lokaci ne dasu kuma idan Allah ya saukar dasu babu wani abu da ya isa ya canza faruwar hakan to a wannan gabar ma Allah ya saukar da ikonsa ya kawo qashen wa'adin zama tsakanin Asma'u da Bashir".

Salati Goggo ta kwaso ta dire, cike da jimami tace "Yanzu yarinyar nan seda ta kashe auran hankalin ta ya kwanta wai me Asma'u take nema ne a rayuwa? Yarinya ace zuciyarta babu salama shekaru kusan uku da yin abun nan na zata ta haqura komai ya wuce ashe ita akwai abinda take qulla kai Jama'a wadannan yara namu Allah dai kayi musu Albarka".

"Sam wallahi Hajia ba laifin Asma'u bane, bama tun yanzu ba tun tuni duk abinda ya faru ita akayiwa laifi kuma aka danneta aka sakata yin biyayyar dole saboda ita an isa da ita.

Shi Bashir din ne dai daman gaban kansa yake yi a komai to yanzu ma ya sake nuna mana ya isa da kansa ya isa yanke hukunci babu shawarar kowa yayi saki ba tareda sanin mu ba be kuma gaya mun ba se matar sa ya gayawa yanzu na tsinci zancen a bakin yar uwar tasa na kirashi kuma a waya ya tabbatar mun da haka akayi,

Dan girman Allah kiyi haquri, munyi magana da Alhaji Tukur yace mun baki sani ba saboda sun rasa ta yanda zasu gaya miki wannan al'amari shiyasa nace ni bari na kiraki da kaina na sanar dake Bashir be kyauta mana ba be kuma kyuatawa kansa ba.

Idan Bashir yana da hankali ko dan irin qaunar da kika nuna masa kika fifita farincikin sa akan na yar da kika haifa wallahi ko zaginsa Asma'u takeyi yaci ace taci wannan darajar ya daga mata qafa ballantana na tabbatar da ko kallon banza bazatayi masa ba".

"Karka yi saurin yanke hukunci cewa laifinsa ne Alhaji ita kanta Ma'u yarinya ce me naci da kafiya, wanda yake zaune da ita ne kadai yake gane halin ta tsakanin mace da mijinta kuma se Allah, Allah kadai yasan irin quntatawa da baqin halin da take masa" Goggo ta katse shi a sanyaye dan abin ya dake ta kwarai, Me Ma'u tayi wa Bashir har haka da yayi zafi ya sake ta.

"Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri" Goggo ta fada bayan dogon ban haquri da Alhajin ya sake yi mata, haka suka ajiye waya jikinta gaba daya ya mutu,

"Allah sarki Ma'u ita kuma tata Jarabawar kenan akan abinda take so".

Alhaji Amadu kuwa bayan ya gama wayar sa yasa wani saurayi Abokin Naziru da ya zo wucewa ya turashi zuwa cikin gida, har sannan suna zaune a tsakar gidan Addah na zuba masifa da besan ko akan me takeyi ba, haka ya gungura kekensa ya shige daki ko a fuska be nuna musu yasan me akayi ba ya kuma qudurce baze taba yiwa Nafi maganar ba koda kuwa ita ta kawo kanta da kanta, ze ci gaba da Addu'a Allah ya raya shi ya kai lokacin da zasu girbi abinda suka shuka, a rabar ne ze silleta tas ya yada mata da maganganun da suka dade suna ci masa zuciya.

BASHIR
Suna ajiye waya da gaba daya ji yayi rasa me yake yi masa dadi a rayuwa. Har a yanzu shi bega abinda yayi ba ya kuma san babu me fahimtarsa adan an tashi kowa bayan Ma'u zebi baza'a duba martabarsa ta matsayin mijinta da ita take takewa ba.

Babu abinda yafi daga masa hankali da a kullum Alhaji yake maimaita masa watarana se yayi kuka da idonsa akan Amirah wannan ai baki yake yi masa kawai kuma ita Amiran nan fa ba irin wadda ya sani a baya bace yanzu ta chanza ta gyara duk wasu halayenta marasa kyau da ake gani a baya ita kuma Ma'un da akewa kallon ta kirki yanzu ita ce take masa abinda baya so.

koma dai menene aikin gama ya gama saki dai ya rigada ya furta dukda yanzu dai yaga yayi zari da yayi mata saki har biyu dan daya ya kamata yayi na gargadi amma dai ba matsala,

ze cigaba da lissafi se ya rage wata daya ta gama Iddah sannan ze ce ya mayar da ita, Dukda yasan tabbas zeji jiki na rashin Ma'u a kusa dashi abinda be taba koda mafarkin faruwarsa a rayuwar su ba amma ita ta janyo musu haka, daga ita har shi dole su shiga gararin rayuwa kafin komai ya daidaita dan ta wannan hanyar ce kadai ze horata ta yanda gaba ko ance ta sake musa masa magana bazatayi ba bare har ya bata unarni taqi bi.

Haka ya ringa saqa da warwara har lokacin tashinsa aiki yayi, yasan yanzu yara sun koma gida, ze barsu daga nan zuwa Jibi Amirah tazo dan ko ya dakko su yanzu baze iya musu hidimar da suke da buqata ba dole se mace dan haka dai ze ci gaba da ja har zuwa sannan dan idan yayi shiru kar ta dauka ze bar mata yaran ne.

ASMA'U
Ganin har magriba tayi Bashir bezo da wani tashin hankali ba yasa hankalin tavya dan kwanta tayi tunanin ko ya haqura ya sakar mata ragamar yaran ne tunda taji sunce ya dawo harma su Ahmad sunje gidan ya basu Chocolate.

Bayan Isha tana zaune wayarta tayi qara, shareta tayi dan ta gaji da amsa waya. kamar wutar daji labarin mutuwar auranta ya karade Gombe se kiranta akeyi ana mata jaje ta rasa ta bakin wa maganar ta fita amma bata raba daya biyu Bashir ya gayawa matarsa, ko yan uwansa su kuma suka kwaza a duniya daman mutane kuma masu jiran qiris nan da nan labari ya zagaya.

Har wayar ta qaraci qararta bata ko duba ba can sega Amna ta fito daga daki da wayarta a hannu ta miqa mata tana cewa
"Goggo ce tace ta kiraki baki dauka ba".
Karbar wayar tayi ta saka a kunnenta kawai dan ta tabbatar labari ya rigada ya isar mata yanzu.

Cikin sanyin daya aureta yanzu ta gaida Goggon kafin tayi shiru tana jira taji ta inda zata rufeta da fada amma ga mamakinta se ji tayi tace

"Ma'u kiyi haquri, shi aure raine dashi Idan lokacin mutuwarsa yayi koda dalili ko babu se an rabu, sannan kowa da kika gani da irin qaddarar sa a rayuwa, mutuwar aure bata da dadi amma kar hakan ya sa ki dauka gazawarki ce ta janyo ko kuma wani ne silar hakan Aa babu wanda ya isa ya qulla aure ko ya kashe shi se Allah dan haka ki dauka cewar wa'adin da Allah ya dibarwa zamanki da Bashir ne ya qare kawai.

Kar kuka ki ce zaki saka kanki a damuwa ko wani abu kinji kiyi Addu'a Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri, saki nawa ne?"

Cikin karyewar murya nace mata "Wallahi Goggo ma Banyi masa komai ba, kawai saboda yace se ba bar aikina saboda Amirah Shikenan abinda ya faru"

"Na sani Suhaima ta gaya mun komai kiyi haquri yanzu dai saki nawa ne?" Ta sake tambayata, seda naja Majina dan ta tuno mun da kukan da na bari nace mata

"Saki biyu ne kuma nayi bari dazu da safe".
"Subhanallahi Bari kuma a garin yaya daman kina da ciki ne" Goggo ta tambaye ni muryarta cike da Alhini, seda na tsagaita kukan nace mata

"Nima ban sani ba se shekaran jiya naje Asibiti na dawo ban ma kai ga sanar masa ba ya sake ni".

"Yanzu be san da maganar cikin bama bare barin kenan, ai kuwa ya kamata tun wuri a gaya masa tunda kinga kenan kin gama Iddah kar yaje yayi ta lissafin Bogi tunda da sauran igiya a tsakanin ku" Goggon ta fada, da mugun mamakin maganar ta nace

"Yanzu Goggo har kina zaton cigaban zama tsakanina da Bashir, ai Goggo ko shine autan Maza na haqura dashi. Sakina fa yayi sakin wulaqanci akan kishiya wallahi sedai ya zauna da ita wadda yake so har qarshen rayuwarsa ko ze mutu dan nagama auransa, dan Allah a wannan karon kar kice zaki tilastani komawa gidan Bashir in dai ba so kike zuciyata ta buga na mutu kowa ya rasa ba" na fada ina qara fashewa da Kuka.

Qarshen abinda Goggo zata sakeyi mun a yanzu ta maida ni gidan Bashir, ba dan na dena son Bashir ba wannan nasan wani abu ne da har na mutu yana raina amma na tsani zama dashi ba kuma na fatan Allah ya kawo dalilin da ze maidani gidan sa.

Duk da yana yin da take ciki seda tayi yar dariya kafin tace
"Ni ban ce ki koma gidan Bashir ba amma idan zama be qare a tsakanin ku ba haka zaku gama duk abinda zakuyi kuma ku koma ku ci gaba da zama dan haka duk abinda zakiyi karki tsananta ko dan Albarkar zuri'ar da take tsakanina ku.

Sannan maganar yara idan har ya matsa ki bashi yayansa kar kice zaki tsaya ja in ja dashi tunda yana da me riqe masa shikenan, ke kuma zamanki a nan baze yuwu ba zuwa safiya zan kira Alhaji Qaramin kodai ki nemi transfer ki koma can Abujan gabansa ko ki aje aikin ki dawo gidan ku ki zauna amma bazaki zauna ke kadai anan ba".

A gaba daya tsarikan na Goggo babu wanda naji yayi mun, bana jin zan iya bawa Bashir yarana maganar Transfer kuma ko barin aiki ta manta aikin akansa aka sake ni sannan na barshi ai kuwa na tashi a tutar babu, amma yanzu bazan musa mata ba zan barta tayi magana da Alhaji Qaramin na tabbatar shi baze bari a rabani da yayana ba ko aikina.

Haka mukayi sallama tana sakeyi mun nasiha na kuwa ji dadin magana da ita sosai muka rabu tana jaddada mun dana sanar da Bashir maganar ciki da kuma Barin da nayi dan gudun abinda kaje ka dawo, haka na kwana da niyyar gobe idan yazo kai yara makaranta zan gaya masa tunda da alama bega takardar dana ajiye masa ba.

BASHIR
Yauma dai a hanya ya siyo abincin sa haka ya dawo gidan na nan a yanda ya barshi sema qarin datti da yayi saboda qurar qasan gado da suka watso masa palour dazu. Haka ya shiga dakinsa yayi wanka gaba daya gurin ya hargitse masa ya rasa ta yanda ze fara mayar da kayansa cikin wardrobe tunda ya saba da an kawo masa guga Ma'u ce take jera komai a inda ya dace.

Haka ya zura jallabiyya ya dawo palour ya kade kujera ya zauna ya bude abincin, loma uku yayi ya ture gaba daya abincin ya fice masa daga rai dan bakinsa ya saba dame dadi, dukda wannan din ma me dadin ne amma dandanok girkin Ma'unsa ya banbanta dana kowa shikadai ne abincin da ko iya qamshinsa yana rage masa yunwa dan shi fa abinci indai ba nata ba ko yaci baya jin ya qoshi sedai kawai cikinsa ya cika maganin yunwa amma ba wai dan ya gamsu da cewa abinci yaci ba.

Yana zaune yana dannan waya su Ahmad suka shiga gidan da gudunsu, Ganin sune ya debe masa kewa har aka kira sallah suka tafi masallaci tare, yana kallon Aliyu ko inda yaje yaron be kalla ba yayi murmushi kawai da suka dawo zaau tafi ya dakko Chocolate ya basu harda ta sauran kafin ya raka su har qofar gidan suka shiga, yana jiyo qamshin abinci da alama girki sukeyi.

Badan kar mutunchinsa ya zube ba babu abinda ze hana ya shiga yaci amma ya qudurce a ransa dole ya koyawa Ma'u hankali ta yanda da kanta zata bishi ta bashi haquri, a qalla se tayi kusan kwana dari da wani abu kafin cikar Iddarta dan watan ta me kwana talatin da shida ne kafin sannan kuwa ta biyu liqis ta yanda ko kara ya ajiye bazata sake tsallakawa ba. Haka yaja jiki ya wucw yana hadiyar yawu, qarshe se se shayi yasha da wani guntun cake da Allah yasa basu dauke ba ya hada da dambun nama shima a irin wanda take masa ne ya ajiye a office ya tuna yana mota ya dakko shi.

Seda yaje kwanciya idonsa ya kai kan farar takardar da tun jiya ya ganta amma be duba ba, daga kwancan ya janyota ya bude yana mamakin ko tasa ce ma ya manta sedai tambarin Asibiti da sunan Ma'u daya gani yasa ya qara hasken fitila dan ya gani da kyau.

"Kai Allah na gode maka, Wallahi Allah yana sona" ya fada a fili cikin farin ciki, wannan wata dama ya samu ya tabbatar se Asma'u ta kawo kanta da kanta musamman da yawancin cikinta suna qara mata buqata yana zaune zata zo har inda yake ta bashi haquri kai wannan abu ya masa dadi.

Hotonsu dashi da ita da yake akan bedside drawer ya dakko yana shafa fuskar ta, ranar Anniversary dinsu na shekara Goma suka duke shi daga shi har ita suna dariya ya manta dariyar me sukeyi a lokacin.

Sumbatar fuskarta yayi kafin yace
"Kiyi haquri Ma'una, nasan sena fiki azabtuwa da rashin ki a kusa dani amma ke kika jawo mana, taurin kanki da kafiya ya saka komai ya faru amma yanzu ga dalilin da ze dawo mun dake cikin ruwan sanyi na samu, Ina son ki Ma'una".🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR πŸ₯°πŸ‘Ή
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 42

Ranar Juma’a Amirah ta tafi Lagos, da yake saukar Yamma tayi seda Bashir ya tashi daga gurin aiki sannan ya biya ya dakkota suka wuto gida.

Ina zaune dakina Jafar ya shigo da gudu yana cemun

β€œMami Abbi ya dawo”.
β€œTo sannun sa Jafar” na fada ina duba wani document da aka turomun daga gurin aikin mu.

β€œAi Mami ba shi kadai bane ma tare suke da Anty Amirah” Jafar ya sake fada, se naji kamar an saka mun stop, na dago na kalli yaron kamar me son tabbatar da abinda ya fada se kuwa ya daga mun kai yana sake cewa

β€œIta ce tazo gasu Ahmad can ma sun tafi gurinta kuma naga da Akwatunan kayanta qila ta dawo gidan kenan ko Mami?”

β€œKaje ka kirawo su magriba tayi” na fada kafin na mayar da kaina kan abinda nake yi amma sam ban gane komai ba. Idan nace zancen zuwan Amirah be dake ni ba nayi qarya ta tabbata kenan dagaske saboda ita Bashir ya sake ni tunda ga ta nan ya kawo ta nan din.

β€œAllah kaine Allah, kayi mana sakayya akan duk wanda ya cutar damu” na fada a fili bayan na ajiye Tab din hannuna dan sam na dena gane abinda nakeyi. Tagumi na rafka, se kuma na janye nace da kaina β€œTagumin fa be ganni ba, tun wuri gara na tattara shirgin Baban Ali a gefe na fuskanci abinda ze tun karo ni a gaba” ina fadar haka na miqe na shiga Bayi nayi wanka.

Ina cikin shafa mai Muhammad ya shigo da leda a hannunsa da ban san ko menene a ciki ba.

β€œMami wai gashi inji Anty Amirah ta kawo miki tsaraba” ya fada yana ajiye ledar a kusa dani, har ya juya ze fita na janyo shi, se da na zare masa ido kafin nace

β€œDauki ka fitar can bola kayar, idan na kuma ganin ka shiga gidan nan idan sena cire maka kunne, wuce kaje ka kirawo Ahmad daman kune masu shegen yawo ai bini bini kun tafi can”.

Haka na cigaba da shiryawa ina mita, seda na sake tara su gaba daya naja musu kunne akan babu su babu zuwa gidan Amirah, idan ma uban suke son gani se su jira ai yana fitowa su ganshi a waje su wuto gida amma ban yarda wani ya sake ya je gurinta ba.

Washe gari da yake Asabar ne bamu tashi da wuri ba se gurin goman safe dan haka kafin muci abinci muyi wanka an fara kiran sallar Azahar.

Aliyu ne ya sa su a gaba suka wuce masallaci da suka tashi dawowa shi kadai ya shigo ba tareda sauran ba.

β€œAa Yaya ya naganka kai kadai ina qannen naka” na tambaye shi ina gyara Hijabin jikina dan zan leqa gidan Anty, bata jin dadi kwana biyu itama.

β€œMun taho a hanya sukaga Abbi shine ya jasu gidansa” Aliyun ya fada yana zama akan kujera, se nayi qwafa nace β€œwato basuji abinda na gaya musu jiya ba ko nasan Jafar ne ze jasu za kuwa su dawo su same ni, Faridah taso ki rakani ke kuma Amna idan kin gama cin abincin in zaki zo toh” na fada ina nufar qofa.

Kallo daya nayiwa gidan Bashir shima bisa kuskure na shige gidan Anty, ban zauna ba ganin Baba yana gida dan a zatona yana gidan uwargidansa ne yau dan haka a tsatstsaye nayi mata sannu yana ta in zauna mana nace Aa anjima na dawo muka fito, ina sako qafata waje nayi kyakyawan gani da Bashir tareda matarsa saboda tsabar sabon salon munafunci ta dauki Ahmad se rinjayarya yake kamar zasu fadi suka shiga mota, inajin Ahmad din yana cewa

β€œMami, Abbi ga Mami nan ba tareda ita zamu je ba” ko iskar su ban waiwaya na kalla ba na shige gida. Ban kai ga cire Hijabi na ba naji an turo qofar an shigo ga kuma qarar takalmi qwas qwas alamar dai macace se na waiwaya naga waye ido na ya sauka akan Amirah.

Fuskarta dauke da Fara’a ta qaraso cikin palour nidai ina tsaye har ta samu kujera ta zaune tana waige waige. A lokacin Allah kadai yasan abinda nake ji a cikin zuciyata amma na rigada nayiwa kaina fada, badai ni na sake yin wani tashin hankali akan Bashir ba tunda dai yanzu babu abinda muka hada dashi dan haka nima sena fasa cire Hijabin na zaune a kujerar da

Please Login or Register in order to submit comment