Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ihun murnar ganinsa ya zauna a gurin suna fuskantar juna da Bashir.

Fuska a sake ya miqawa Bashir da yayi suman zaune hannu dukda can qasan zuciyarsa bazeyi qarya ba daurewa kawai yayi amma sosai yake Adawa da Bashir din daya rabashi da macen da yake so sama da kowace mace a rayuwarsa.

Ya wargaza masa mafarkin shimfida rayuwar aure me ciki da aminci da qauna qarshe ya barshi da gantalewa da zama macen da bata dauki aure a bakin komai ba.

Malam Bashir kuwa bin hannun Yusuf yayi dake daure da wani shegen Agogon diamond a tsintiyar hannunsa, kai Cufflinks dinsa kadai abin kallo ne wani irin tuquqin baqij ciki da kishi suka taso suka shaqe masa wuya kawai ya mayar da kai gefe ba tareda ya karbi musabahar ba, ko a jikin Yusuf ya maida hannun gurin su Aliyu duk suka gaisa yana tambayar su sunayensu dan ko shine Bashir din akan Mace kamar Ma'u zeyi abinda yafi haka shi yama ga qoqarin sa daya zauna teburi daya dashi ai

Gaisuwa me kyau sukayi da Anty Halima nan da nan suka shiga hira kamar sun san juna dan shima akwai faran faran da mutane halinsu yazo daya dukda da ita da gayya ta qara sakewa suke hirar saboda ta turawa Bashir takaici se gashi kuwa Hira ta barke tsakanin Yusuf da sauran Yaran Ma'u qarama na qara maimaita masa sunayen su se dariya suke mata dan bata iya fada ba ya kalli Asma'u yace

"Gaskiya kin iya bida yara kiga yanda yarinyar nan ta sake lokaci daya anya bazan bar miki ita ba kuwa"

"Ai na yara kadai ba har manyan in gaya maka ta iya tafi dasu ta kowacce hanya me sauqi ko me daci, ka bar mana ita kawai mun samu qarin ya" Anty ta fada tana dariya ta gefe kuma tana hararar Bashir da ya kumbura dan har kamar yafi Amirah kumbura yanzu.

Shigowar yan Graduation ce ta dakatar dasu daga hirar, nan da nan aka shiga gabatar da abinda aka je yi, an raba musu kyututtuka sosai Amna ta samu lambobin Yabo dan ita ta lashe Best Student ta shekarar aka kira Iyayenta, Ma'u na miqewa Bashir shima ya tashi daga kan stage ta hango Amna na tsalle tana nuna mata bayanta tana waiwayawa se ganin Alhaji Qarami tayi tareda Matarsa ta biyu da daya daga cikin Yaransa Abdullahi da suke cewa Baffa.

A tsakiyar Mu nida da Bashir Amnan ta tsaya akayi mana hoto se wani washe baki yake shi ala dole ga Baban Amnah, ganin Alhaji Qarami da Yah Muslim da shima bamu san da zuwan sa ba sun qaraso gurin se Bashir ya dan matsa yana shafa kai amma Alhajin ya sake mayar dashi gefen Amnan su kuma suka tsaya daga gefe da gefen mu aka sake daukar hoton.

Haka sauran yaran dukka suka shiga akayi ta hotuna harda su da Anty. Hoto daya muka dauka tare da Yusuf ya mana sallama ya fita saboda kiransa da akayi.

Amirah tana daga can qarshen tana hangomu baqin ciki kamar tayi bunga dan securities ne ma suka tare hanya kar su yan regular su shiga gurin VIP.

Har kwalla seda tayi saboda baqin ciki, tana gani muka gama hotunanmu cikin farin ciki muka sauka kowa ya koma mazaunin sa kafin taro ya koma na ciye ciye da maqulashe.

Abubuwa ne gasu nan birjik se wanda kake so a ka ringa ajiyewa, ita kanta Amirah ba qaramar gara aka ajiye mata ba amma saboda qalata idonta nakan teburin su Bashir har seda ta kasa daurewa ta zaro wayar tavta rubuta masa text tace

"Yaya naga abincinku ba irin namu bane, ka rage mun zanci nima"

"Ai se kici idan ke mayya ce ko kuma daga yunwa kika fito" Bashir da ransa yayi bala'in baci ya mayar mata da Amsa. Tsabar haushi gaba daya ma ta saka abincin ya fita daga ransa ya ringa zabga tsaki su dai yan gurin ba wanda ya kulashi abincinsu suke loda kawai.

Qarfe sha biyu taro ya tashi, bayan abincin da aka ci a ciki harda wani Take away aka sake binsu dashi, Su Ma'u na tsaye aka kai mata nasu ta bude boot aka zuba Anty ta kama baki tana cewa

"Duk wannan abincin da muka ci a ciki qara raba wani suke yi lallai se a gaishe su"

"Yo ba dole ba wannan uban kudade da suka caji iyaye banda contribution da suka samu daga sauran mutane ai dole kiga sunyi bushasha" shiru nayi lokacin dana hango Amirah na cacar baki da daya daga cikin rabon Abincin da alama hanata yayi se na nunawa Anty gurin yanda kasan da Bashir nake shima ya bita da kallo.

A tsawace ya kira sunanta, se gata ta taho gurin tana qunquni, "haka kawai a komai se an nuna banbanci bayan duk abu daya muka zo kuma"

Mudai gabada ya ma dauke kawunan mu gefe mukayi dariya na cina a zuciya, Allah ya sauwaqawa wasu dai da shegen kwadayi suke.

Qarasowar Alhaji Qarami, Yah Muslim tasa na qara fadada murmushi na,

"Gashi bamu zo da mota ba, taxi muka hawo daga Airport yanzu kuma ina so na leqa gurin Olabode nayi masa ta'aziyyar Matarsa kafin dare mu wuce nasan kema baki je ba ko Asma'u" Yaya Muslim ya fada yana kallona, sena kama baki nace

"Wallahi Yaya na manta, bama wannan ba gidan ne bazan iya kai kaina nikadai ba shiyasa Amma yanzu seka kwatanta mun zan samu lokaci naje kar yace seda kazo mukaje tare".

Motata ya karba shida Alhaji Qarami suka shiga suka tafi dan shima akwai inda zeje, Bashir ma tuni ya kwashi yaransa da Amaryarsa da take ta faman zumbure zumburen hanata karbar take away da yayi ya rage saura Ni da Anty se Anty Hadiza Amaryar Yaya da zamu wuce gidana tare da ita kafin su dawo dasu Amnah.

Guri muka samu muka zauna muna ci gaba da hira dan Amnah har sannan tana can suna hotuna da qawayenta. Yusuf ne ya taho gurin yana cewa

"Aa baku tafi ba Ma'u? Ina sauran Yaran dasu Alhaji Tukur?"

"Sun wuce gida, Alhaji Qarami kuma sun fita da Yah Muslim, muma Amnah muke jira mu tafi, ka ganta nan ma zuwa" na fada ina miqewa tsaye. Wayata na zaro ina cewa

"Bari na kira mana Uber muma mu wuce toh"
"Aa bari na sauke ku mana, nima naje mun gaisa da Family colleague dina na dazun nan da kika gani" Yusuf ya fada, se muka bishi gaba daya zuwa gurin wata Arniyar mota High Lander.

Duk suka shige baya harda su Amnah akan dole ni na shiga gaba muka kama hanyar gida muna tafe Yusuf dasu Anty suna ta hira amma na kasa aka musu baki saboda duk se nake jina a takure ko dan yanda duk sanda zan daga ido se naga yana kallona har tsoro na fara ji kar muje ya zubar damu a haka dai muka qarasa gida lafiya.

Tundaga Nesa na hango Bashir a zaune akan motar sa ya zubawa hanyar shigowa layin namu ido kamar me jiran wani abu, kamar da gayya ma naga Yusuf ya taka motar tayi wata qara da take nuna lafiyar injinta kafin ya fizgeta ya cake a qofar gidana, muna tsayawa wayata ta sulale qasa dan haka na duqa ina nemanta kafin na ganota har su Anty sun fice daga motarya rage daga ni se shi a ciki.

Murfin motar na kama da niyyar budewa ina cewa "mungode, zaka dawo anjima tareda su Yaya ne ko se kazo daukar takwara?"

Shiru yayi mun, sema gyara zamansa da yayi ya juyo gaba daya yana jifana da wani irin sanyayyan kallo daya saka naji tsikar jikina sun fara tashi bashiri na sauke kaina qasa ina ci gaba da kiciniya da qofa amma taqi buduwa.

"Kinyi kyau sosai Asmy, amma kamata yayi ace kwalliyar nan ido na ne kawai ze ganta kuma ni kafai zan shaqi wannan ni'imtaccen wamshin naki. Bazan gaji da kallonki da yiwa ubagijij daya halicceki tasbihi ba Asmy dan yayi miki suffar da a kallo kadan take iya sanyaya zuciyar wanda yayi tozali dake, ina ma zan iya ci gaba da kallon ki har qarshen rayuwata nasan bazan taba gajiya ba".

Jikina ne ya dauki rawa saboda yanda kalaman Yusuf suka shigeni, qara damqe wayata da jakar hannuna nayi yanda kasan wata mara gaskiya nace "Ka bude mun qofar na fita kaga..kaga"

"Mijinki yana kallon mu ko?" Ya fada yana gyara zamansa kafin yayi wata siririyar dariya yaci gaba da cewa
"Idan na samu dama anjiman zan dawo idan kuma banzo ba may be Monday nazo na dauki Ma'u m. Zadai muyi waya kawai" yana gama fada ya sun kuyo ta barin da nake ba shiri na dauke numfashi ya kuwa kwashe da wata dariya ya dannan wani abu a jikin qofar yana cewa

"Ke kika kulle kanki bude mini zanyi amma ji yanda gaba daya kika dauke wuta kamar mara jini" nidai ban kulashi ba na kwashi qafata nayi waje, ina direwa kuwa da sauri nayi baya na jingina da motar ganin Bashir a gabana da yana numfarfashi kamar me cutar Asthma.


Yana shirin bude baki na gewaye shi na wuce ina hada hanya dan fa har sannan jikina rawa yakeyi, daga bakin qofa na tsaya ina daidaita nutsuwa ta, sena waiwaya na kalli inda na bar Bashir a tsaye na hango Yusuf ya sauke glass din wundo da alama magana sukeyi.
na seda naja iska na fesar kafin na tura qofar na shiga dan a bude suka barta.

BASHIR
Har suka isa gida Amirah na zuba masa mita da qorafin an mata wulaqanci amma tafi ki mutu be ce mata ba gaba daya hankali da tunaninsa suna kan Ma'u daya baro acan.

Yana tsayar da motar a qofar gida ya waiwaya yace mata
"Ki dauki nawa a Boot gashi can kici shikenan dai ko?"

"Ai ba shikenan ba, bayan ma duk lefinka ne. Da ka nuna inada daraja da qima a matsayina na matarka ai komai nima zuwa za'ayi ana girmamani ayi mun amma fa ji irin wulaqancin da kayi mun ka kama ka kaini can qarshen bango kamar wata mara galihu ko hoto baka ce nazo ayi dani ba seka..."

"Kinga fita, ki wuce gida sauri nakeyi ni akwai inda zanje" ya fada a hankali can qasan zuciyarsa yana qoqarin danne fushi da bacin ran da suke taso masa. Yaga alamar ita bata gajiya da tashin hankali shi kuma a yanayin da yake ciki yanzu nutsuwa yake da buqata bawai qarin wata damuwa ba.

Fitar tayi tana masa qunquni, shidai yaja motar yayi gaba. Niyya yayi ya koma ya dauko su Ma'u tunda yaga ta bayar da motarta amma se yayi tunanin tazarar gurin kafin ya isa qila sun samu abun hawa sun taho gida.

Yusuf ne ya fado masa arai kar dai ya zama shi ze dawo dasu, nan da nan kuwa yaji kansa na neman yayi ciwo se kuma ya tuna da ai tun suna cikin Hall din Yusuf ya tafi be tsaya an tashi dashi ba wannan tunanin ya dan kwantar masa da hankali dan haka ya yanke shawarar ya nemi guri ya tsaya daga farkon Layin ta yanda zega duk motar da zata shigo ciki dan idan ya koma qofar gidan sa waccen jarababbiyar yarinyar seta dagula masa lissafi har Ma'un ma ta wuce be sani ba.

Yana zaune a gurin kusan Awa guda motar Yusuf ta danno kai, plate number motar da aka saka WUNTI 2 yabi da kallo ya tabbatar bata cikin Estate dinsu bace sedai idan wasu ne sukayi baqi, seda suka matso kusa dashi ya hango Ma'u zaune a gaban motar yanda suka saje ita da Yusuf din seka rantse da Allah wasu Mata da Miji ne sabon aure sukayi anko zasu je unguwa ga wani kallo me nuna so da yaga Yusuf din yana yiwa Ma'u ita kuma ta sunkuyar dakai tana murmushi.

Wani Yum yum yaji akansa lokaci daya kamar an tsikara masa abu a qirjinsa har seda ya dafe saitin zuciyarsa yana sakin numfashi ajere a jere, ya tabbatar idan ya miqe a sannan to kuwa seya fadi idan beyi wasa ba ya hadu da paralyze abinda ya dakatar dashi kenan ya zauna yana kokawa da nutsuwarsa, gashi ya kasa dena kallon motar har ta tsaya mutanen ciki suka fito dukka banda Ma'u abinda ya qara masa hauhawar jini kenan haka ya dafa motar ya sauko yana jin jiri na kwasar sa amma ya daure.

Seda ya kwashi kusan minti biyar a tsaya kafin ya iya daga qafarsa ya fara tafiya yana rangaji, duk takun da yake kusanta shi da motar ji yakeyi kamar anan suka masa wuqa a maqoshi idan ya tuna Ma'u ce a ciki tareda wani qato da besan me yake gaya mata ba.

Ji ya ringayi kamar ya debi duwatsu tundaga nesan ya yita rotsawa gilasan motar har se sun rugurguje amma baze yuwu ba dan yasan irin su ba qaramin duka zasuji ba ace sun balle haka ya qarasa Gurin zuciyarsa kamar zata fashe ya kai hannu ze kwankwasa Ma'u ta bude qofar gabansa ya yanke ya fadi ganin irin yanayin data fito, yanayine irin wanda take shiga lokacin da take cikin maye da shauqin soyayya.

Bude baki yayi ze mata magana ta rabe shi ta wuce gaba daya se hankalin sa ya kasu biyu, ita ze bi ko kuma tsayawa zeyi ya fara cin uban wannan me bibiyar masa matar tukunna?
Maganar da Yusuf yayi ce tasa ya wai waya ya kalle shi

"Yallabai barka da rana ashe gaba kayi dazu bamu samu mun gaisa ba ya aiki ya su Madam?? Yusuf ya fada yana miqo masa hannu fuskar dauke da wani shegen murmushi.

Kallon hannun da yake bashi yayi ya sake kallon fuskarsa, 'qut' ya hadiye yawu kafin ya bude baki dakyar yana nuna Yusuf yace

"Ka fita daga sabgar matata, idan ba haka ba sena koya maka hankali ta yanda ko kallon matar wani bazaka sakeyi ba bare har magana ta hada ka da ita".

Ko a jikin Yusuf se ya janye hannunsa da Bashir yaqi karba yana murmushi yace
"Yallabai ni kuma meya hadani da matarka nida ban ma san tare kuke ba seda zaku tafi na hango ku zaku shiga mota, ai ni ko kalar fuskar ta bansani ba bare wata mu'amula ta hadani da ita".

Wani banzan kallo Bashir ya watsa masa kafin a harzuqe yace
"Karka raina mun hankali, ni kake cewa baka san matata ba, to bari kaji wallahi ko a hanya na sake ganin ka kalli Ma'u se nayi qararka na bata maka career badai taqamarka siyasa ba?
To sena gayawa duniya cewa kai Manemin matan aure ne idan yaso se naga ta yanda zaka tsira da mutunchinka".

Dariya sosai Yusuf yayi harda dukan sutiyari kafin ya kalli Bashir daya shaqa iya wuce ya nuna shi yace
"Oh wai akan Asmy kake magana daman ai cemin zakayi tsohuwar matarka se nafi ganewa.

Toh tunda anyi haka yanzu bari nayi amfani da wannan damar nayi maka jajen wautar daka tafka ka rabu da Mace kamar Asmy bayan ka manta akwai irin mu a waje da duk sallah biyar ta duniya da zamuyi a rana se mun roqi Allah ya bamu mace kamarta.

Nagode maka kwarai daka sako min ita a daidai lokacin da nake tsananin buqatar ta, na kuma yi maka alqawarin zan riqe Asma'u na bata kulawa da soyayyar daka gaza bata, kai amma ka tafka Asara yallabai se in ce maka Allah ya mayar da Alkahiri ko da yake naga ka samo wata me fada akan Abinci a gurin taro ko?

Irin matan nan in gaya maka ba'a zuwa gurin kunya dasu dan se sun zubar maka da mutunchi a ringa kallonka kamar baka yi musu komai Alhalin tsabar rashin godiyar Allah ne kawai. Kayi haquri fa amma dai dole in gaya maka kayi wauta Allah dai ya mayar da Alkahiri" yana gama fada ya dage gilashin motarsa yayi gaba yana cigaba da yiwa Bashir dariya.

Bashir kuwa tsabar yanda ya tafi wata duniya na wucin gadi besan sanda Yusuf ya bar gurin ba se qugin motarsa yaji. Ya juya ya kalli motar ya waiwaya ya kalli Gidan Ma'u wai ma takamaimai laifin wa ze gani anan.

Yanzu har Ma'u ta bawa wani dama ya maye gurbinsa a rayuwarta Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.

YUSUF
Wato rai fes sunan wata Atamfa haka ya ringa tuqinsa yana murmushi shi kadai idan ya tuna yana yin fuskar Bashir sanda yake gaya masa magana.

Tun ranar daya hadu da Ma'u da daddare yana sauketa ya kira Alhaji Tukur ya gaya masa yau ya hadu da Ma'u babu bata lokaci kuma ya sanar masa da zancen mutuwar
Wanda yayi bala'in yi masa dadi ya kuma jin jinawa wauta da hauka irin na Bashir amma daya tuna cewa Allah shi yake qulla aure ya kuma rabashi a sanda yaso se ya gode masa ya kuma tabbatar da Allah ne yake son sa shiyasa be sake hadasu shi da ita ba se a yanzu da take babu igiyar kowa akanta.

Yana sane yake nuna mata kamar besan komai ba dan yafi so ita da kanta ta gaya masa bata da aure a sannan ne ze dakko tsohon littafin soyayyarta ya karkade shi ya fara biya mata shafi shafi dan yayi alqawarin a wannan karon babu gudu babu ja da baya se inda qarfin sa ya qare amma se ya mallaki Asma'u kuma in sha Allahu rabonsa ce.



M&Z FASHION DESINGNERS
INA MATA YAN KWALISA
KU GARZAYO M&Z
FASHION DESNGNERS DAN SAMUN IN GANTATTUN KAYA MASU AMINCI.
IRINSU
ZANNIWAN GADO
TROW PILLOWS NA ZAMANI
TUM TUM
BABY SET
TOILET SET
KITCHEN SET
LABULAYE DA SAURAN KAYAN KWALLIYAR GIDA.
HARMA DA ATAMFOFI DA KAYAN KITCHEN AKAN FARASHII ME RAHUSA
KU NEMEMU AKAN LAMBAR WAYA 07064870087.08127423783.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 49

ASMA'U
Kai tsaye dakina na wuce sanda na shiga gidan ban ko tsaya jin Anty data tareni da tsokana ba na wuce. Seda na cire kayan jikina da naji kamar harda su gurin tare mun numfashi kafin na watsa ruwa na saka doguwar riga mara nauyi na fito har sannan tunanin Yusuf da kalamansa suna mun yawo a qwaqwalwa.

Anya kuwa Yusuf be san aurena ya mutu ba amma idan ya sani me yasa ze tsaya beyi mun maganar ba? Da wannan tunanin na dawo palour na tarar da Anty Hadiza ita kadai tace mun Anty taje gida ta dawo.

Hira muka shigayi da Anty Hadiza, itama ba baya bace wurin zance nan da nan ta shiga kwashewa Bashir Albarka.

"Ni wallahi naga qarfin halinsa irin yanda ya iya tsayawa a gaban mu bayan duk rashin mutunchin daya tatawa mutane, kinsan da Alhaji ya kirashi akan maganar ya bar miki yara me yace masa? Cewa fa yayi shi baze bar Yaransa a hannun Mace ba yana buqatar ya basu tarbiyya kiji dan abu ta kazan uba ko ina tarbiyyar take a gurinsu da yake iqirarin baiwa wasu oho.

Allah ne yaso ki ya rabaki da Shi tun yanzu dan wannan mutumin tantirin mara mutunchi ne wallahi qila da se kin kai shekarun da baki da yanda zakiyi ko yaka ki zeyi dole ki haqura ki zauna sannan zece ze sakeki.

Ni wallahi ma sena raina ajinsa dana ga ita matar so din, me mace kamar ki, da se ya bari idan ya auro wadda ta fiki sannan se yayi duk kadifirin rashin mutunchinsa amma yanzu ai baya yaci wallahi ba kuma ze taba maida kamar ki ba In Allah ya yarda"

Nidai "hmmmm" kawai nake ce mata dan har a sannan tunanina yana kan Yusuf ne, so nake na tambayeta ko sunyiwa Yusuf zancen amma sena dake, kai dole ma yasan da maganar nan qilan wani dalilin ya sakashi qin yi mun zancen dan haka zan saurara na gani zuwa wani lokaci.

Se qarfe bakwai na Magriba Anty Hadiza suka tafi bayan Alhaji qarami sun dawo gidan ya sakeyi mun nasiha tareda jan kunnen na kula da kaina na kuma kare mutunchi na a duk abinda zanyi.

Yusuf be zo ba be kuma kirani a waya ba, nima sena rabu dashi nasan dai baze wuce qila zuwa gobe yazo daukar Ma'u ba tunda litinin akwai makaranta dukda bansan a ina take karatun ba.

A bakin Farida da taje gidan su dakko abu naji Bashir bashida lafiya, ko me ya same shi oho nidai haka na kwanta ba tareda na sake bi takan maganar ba a dalilin haka ma ranar har yan biyu a nan gidan suka kwana.

BASHIR
Yana kallon motar Yusuf har ta bace masa kafin ya dafe kansa daya sara da hannu daya ya daga qafafunsa da sukayi sanyi ya wuce gida, a tsaye ya tarar da Amirah ta riqe qugu tana zazzagawq Su Aliyu da suka hada PS anan palour suna game su kuwa babu wanda ya ko daga kai ya kalleta abinda yake gabansu kawai sukeyi tana jin shigowar Bashir din ta juya cike da masifa tace masa

"Gara daka zo kai tunda Ubansu ne zasuji maganar ka. Idan banda iskanci da wulaqanci gardawa dasu zasu zo su zauna mun a palour harda wani qarin dorin dosano da suka samo sannan ina musu magana sun mayar dani kamar wata mahaukaciya sunqi kulani ai idan uwarsu ce bazasuyi mata haka ba".

"Amirah ki na gaya miki ki dena zagar musu uwa koh? Amma idan baki bari ba in sun rama karki kuskura kice zaki kawo mun qara, ki barsu suyi sabgarsu.

A sati sau nawa suke zama a gidan da har ze zama abin magana dan yau daya sun zauna a palour zaki zo kinawa mutane tashin hankali, dan Allah ki kyakeni na huta" Bashir ya fada kafin ya rabeta ya wuce, dakinsa ya shiga ya bude first aid box dinsa yana neman paracetamol dan sosai kansa yake masa ciwo amma be samu ba.

Palour ya sake komawa ya kwalawa Aliyu kira, Aliyun ya ajiye pad din game din ya tashi yaje ya same shi a zaune bakin gado ya dage kai da hannaye biyu.

"Aliyu idan kuna da paracetamol a dakin ku kawo mun idan kuma babu ga kudi nan ka dauka mota kaje pharmacy din tsallake ka siyo mun maganin ciwon kai" Bashir ya fada dakyar dan idan yayi magana ji yake kamar ana sara masa abu akansa.

Abin Da da uba duk yanda Aliyu yake jin zafinsa ganin yana yin da yake ciki seda ya sanyaya masa jiki, cikeda tausayi ya dauki muqullin motar Bashir din dan basu da paracetamol din suma, be dauki kudin daya nuna masa ba ya juya ya fita.

Baffan Abuja yacewa yazo ya rakashi nan da nan suka tafi, hana da kudi cikin wanda Bashir din yake basu ko Ma'u wani lokacin a ciki ya hado masa magungunan ya tsaya a wani gurin siyar da Abinci ya siyo masa sakwara da miyar Egusi da wani gashin nama da akeyi a kusa da gurin dan ya lura be ci wani abun kirki dazu ba kuma Antyn su batayi girki ba suka hado komai kafin suka dawo gida.

Sosai Bashir yaji dadin Abincin, yana ci yana sakawa Aliyu da yayi tsaye a gurin Albarka. Seda yayi nak yasha maganin ya kwanta kafin Aliyu ya barshi ya fita, yana bude qofa suka ci karo da Amirah zata shiga se yayi saurin tareta da cewa

"Bashi da lafiya ki barshi ya huta"

"Idan naqi fa ubana se ayi yaya?"

"Nidai na gaya miki ki barshi ya huta idan ba haka ba ai baki manta gamon mu sau biyu ba idan aka sake na uku se kin gane kurenki, sena cire miki haqori in yaso naga da bakin da zaki ringa yiwa mutane hayaniya a gida, tunda kika zo kin mayar mana da gida kamar kasuwa mu bamu saba ba" Aliyun ya fada yana sake daure fuska sosai.

Seta ganshi kamar Bashir dan kwabo da kwabo haka yake da Bashir har kuwa halin be baro ba sedai abinda ba'a rasa ba da kuma banbancin kwaba daga gurin uwa da suka samu, kwafa tayi dan tana tsoron Allah tana tsoron yaron nan bashida mutunci, na farko ya fasa mata goshi na biyu kunne tasan idan ta matsa dagasken yana iya sauke mata haqora kuma yaci bulus tunda ubansa babu matakin da ze dauka
Seta juya dakinta tana ci gaba da zage zage shima ya wuce gurin game dinsu ba tareda ya kulata ba.

Maganin nan da Bashir yasha ya sakashi bacci sosai dan

Please Login or Register in order to submit comment