Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shiga gidansu Amirah kota kira ta ita taje suyi hira a haka har ta karanci Amiran ta gane irin zaman da sukeyi da Bashir har ma da kishiyarta.

“Amma kedai anyi mara wayo wallahi, yarinyar ki dake kin maida kanki baya ita me haihuwa biyar itace star a gurin miji kina zaune. Inda kinsan kanki wallahi da tuni sanda ze tattarota ya dawo da ita nan ke ki bishi bama ze sani ba” Sa’ada ta fada ranar da Amiran take mata qorafin Bashir yaqi kaita inda yake aiki.

Kwananta Arba’in da biyar da Haihuwa Sosai kuma taji dadin maganin da Malamin nan ya bata dan duk sauran kunburin nan bata fi sati tana sha ba ta neme su ta rasa jikinta ya dawo dai dai rashin kwarin da takeji ma duk ya ragu daman kuma aikinta tuni ya kame yayi kyau dan haka ta fara shirye shiryen tarbar Bashir.

Tunda ya tafin nan be sake ce mata ze zo ba itama kuma ganin bata gama shirya wa ba ya saka bata ce masa yau she zezo dinba amma yanzu da take jinta garau dole ta nemo shi dan haka ta chanza salon hirar su yanzu, babu ruwanta ko yana offfice ta kirashi seta san yanda tayi ta rikitashi da salo kala kala da ta koya a gurin sabuwar qawarta Sa’ada.

Wayar da sukayi ta qarshe ma wani Text Sa’ada ta rubuta mata tace ta tura masa, duk bala’in taurin kansa se ya sauke ya taho gurinta idan kuwa taga bezo ba to ta sallama kawai Asma’u tasha gabanta har gaban abada Bashir baya Sha’awar wata Mace idanba ita ba ilai kuwa tana tura masan ta kirashi ta sake gigitashi da kalamai masu kashe jiki se ji tayi yace gobe zezo Gombe,

da tayi masa qorafin ba,a share gida bama cewa yayi babu komai ta shirya daya zo se suje Hotel kawai ai kuwa kamar tayi me dan murna tun a Daren ta fara shirya kaya da abubuwan da zatayi amfani dasu ji takeyi kamar ta janyo safiyar tayi.

Bashir ya sauka Gombe lafiya kamar yanda suka tsara da Amirah yana sauka ya kirata dan da Naziru ya dakko shima a hanya ya sauke Nazirun ya karbi motar ya wuce gidan Addah yana zuwa ta fito suka tafi.

Babban Daki me kyau ya kama musu, su Amirah se rawar kai ake itama yau an fita yawan shanawa da miji, dan hoton nan da akeyi mata da miji anje chilling ita sedai ta gani a gurin qawayenta saboda duk sanda zezo gurinta a Gomben seta jangwalo tsiyar da zasuyi in ma an shirya fitar ta rushe shiyasa take shaqar takaici idan taga hotonsu da Ma’u Fitar Asabar da Lahadin nan da sukeyi toh itama wannan karon in sha Allahu zata dage babu abinda ze bata mata wannan lokacin hotuna kuwa sedai zuciyar wasu ta buga dan haushi.

Sosai sukaji dadin zama a hotel din nan an murji Amraci an more, washe gari Asbar da safe yaje gidan su Ya gaida su Dada be dade ba ya koma, sun sha yawon su kuwa Joint joint ta dinga janshi ansha hotuna sosai ya kuma yi mata shopping sosai. A yar Keypad dinta ta tura hotunan saboda me memory ce, ta daure ta cije batayi masa zancen waya ba ta bari ta gani zuwa ya tafi tukunna karta ballo wata tsiyar.

Seta tuna maganar malamin nan daya ce idan ta kwantar da hankali zata ji dadin Bashir Asiri ba wani tasiri zeyi akan sa ba gashi kuwa ta gani dan cikin lumana ya amince ze chanza mata Tv da Set din Tv stand da Centre table harya bada kudin Tv da deposite din su Centre table din duk da dai Tv ba irin ta Asma’u bace amma itama babba aka siya mata 53’ ina laifi?

Randa ze tafi kuwa harda ita suka kaishi Airport tana narke masa kamar karsu rabu suna dawowa gida Naziru ya ajiye ta ba’a rufa awa biyu ba se gashi da sabuwar IPhone 11 pro inji Bashir a kawo mata harda layi me Data.

Murna kamar Amirah tayi me ta ringa kwasar Shoki tana tsalle nan da nan ta kirashi tayi masa godiya

“Indai zaki chanza ki dawo irin haka babu abinda bazanyi miki ba Meerah” Bashir ya fada. Cike da sabon jin dadi sukayi sallama ta kashe wayar nan da nan ta hada ta ta dora layi ta shiga downloading WhatsApp, a wayar Ummi ta saka Memoryn ta ta tura hotunan zuwa sabuwar wayar ta tana cewa “yau akwai fafatawa kenan, dole nawatsa hotuna a Internet kowa ya gani” (An kuma ashe tuban muzuru kikayi toh Allah sa a wanye qalau dai 😂😂)


Biki mukeyi se Monday In Sha Allah zaku ji ni 🙏🙏🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 29

Asma’u
Alhamdulillah shine abinda zance dan yanda komai yake tafiyar mun lafiya lau ba tareda wata matsala ba. Dukda aikina na office ya dan qaru dan yanzu har tafiye tafiye zuwa sauran states na Nigeria nake yi amma saboda goyon baya dana samu daga Bashir se abin yazo mun da sauqi musamman da tafiyar tawa bata wuce kwana daya a mun dade ne mu kwana biyu.

Tuni Amna sun gama sun gama SSCE tana zaune a gida se jiran sakamako kuma abinda ya qara sauqaqamun abubuwa kenan dan kona dade a waje bani da tunanin na dawo gida na tarar da wani aiki.

Baban Ali da Amaryarsa kuwa se sam barka dan naga wani shiri sukeyi yanzu bini bini yana hanya an tafi Gombe, ina yawan kama shi yana waya da daddare dukda yanzu ya denayi a daki sedai ya fita ko kuma naga Text dinta idan ta turo har mamaki da dariya abin ya ke bani na tabbatar wannan ba dabarar ta bace ta samu wani da yake dorata a hanya ne.

Ni kuwa sosai hakan yayi mun dadi ko babu komai hankalin na ya kwanta yanzu ne zamuyi kishi na hankali kowa ta iya Allonta ta wanke dan haka bana wasa babu daga qafa idan ya tafi kafin ya dawo nayiwa kaina Gyara gangariya yanda zan kwance masa kai na shafe duk wani gigi daya taho dashi.

Sannu sannu rayuwa na shudawa kusan wata biyar kenan rabon mu da Gombe, tuni akayiwa Yara register da School Bus zata dauke su ta dawo dasu abinda ya sake sauqaqamun zirga zirga ma kenan tunda idan Bashir ya kaisu ni nake dawo wa dasu toh yanzu kuwa suna rigani dawowa ma tunda daman kullum se sunyi jira bayan an tashi kafin a dauko su.

Jikin Goggon mu ne ya sake tashi da har seda aka kawo ta nan Lagos Asibiti wanda Alhaji Qarami Babban Yayan mu ne ya dauki nauyi dukda yanda muka so ya barmu muyi amma yaqi harya nuna bacin ransa akan mun banbanta tsakani kenan.

Satin ta hudu a Lagos shima dakyar dan kwananta uku a Asibitin aka sallameta amma zata ci gaba da zuwa ganin likita na tsahon sati hudu dakyar da ban baki ta yarda zata zauna a gida na wai ita bazata je godai godai ta zaunawa siriki a gida ba seda Bashir din yasa baki sannan fa ai kuwa ranar zuwanta na qarshe washe gari ta koma Yola tareda Amnah da Faridah zasu yi kwana biyu dan su Faridan sunyi hutun Term.

Tafiyarsu da kwana biyu Bashir ya tsiromun da wani sabon hali, a da duk dadewa baya wuce sallar Magriba a waje shima se ta qure kenan ko da zeje wani guri seya dawo gidan dai ya shirya sannan ya tafi amma a kwanakin nan se ya kai Tara Goma be shigo gida ba.

Ranar farko qarfe Tara ya dawo a gajiye na tare shi, seda yayi wanka na kai masa abinci yana ci nake cewa “yau kayi dare Baban Ali ina ta kiran wayar ka kuma bata shiga ba”.

“Eh aiki ne yayi mun yawa shiyasa na tsaya na dan rage wasu abubuwan” ya fada yana ci gaba da cin abincinsa. Har ga Allah na yarda saboda ya samu qarin girma kwananan dan haka nasan ayyukan zasu fi nada dalilin daya saka washe gari ma daya kai goma ban damu ba da yake ma ina dan fama da ciwon kai ka fin ya shigo nayi bacci seda Asuba Aliyu ya ke cemin jiya se 10 Abbi ya dawo.

Abinda ya fara jan hankalina da dadewar tasa yanda abin ya zamar masa jiki dan seda ya jera kwana hudu kullum kuma a maimakon ya rage lokaci qarawa yakeyi, a ranar na hudun data kama Asabar, tun Daya na rana yayi wanka ya fice wai zeje gurin Musa abokinsa akwai wani aiki da sukeyi tare beyi awa biyu da fita ba nayi baquwa.

Maman Shukra maqociyar muce a Estate din da muka fara zama kafin mu dawo nan rabon da mu hadu har na manta ma ina zaune se gata.

Bayan na gabatar mata da kayan ciye ciye na zauna ina sake yi mata sannu da zuwa. Yanda take kallona tunda ta shigo ya tabbatar mun bakinta akwai magana dan Maman Shukra akwai gulma sedai na tabbatar da bata qarya, duk labarin data fada maka to kodai ba gaba daya bane idan kabi diddigi seka gano gaskiyar.

Kallonta nayi da yar dariya nace “Maman Shukra wace jarida muka samu dan tunda kika shigo naga bakin nan naki yana motsi”.

Seda ta kora ruwa me sanyi kafin ta kalleni tace Maman Farida Engineer yana gida kuwa?”

Ina dan murmushi nace “ai kuwa kunyi sabani danba dadewa ya fita yaje gurin abokin aikinsa suna wani aiki ne”.

“Aiki, lallai aiki kuwa” ta fada tana kama baki. Sena maida hankalina gaba daya kanta na kalleta da son jin qarin bayani.
Qasa tayi da murya kafin ta fara cewa

“Nidai ba zan fada miki dan na hada ki husuma da mijinki ba sedan kawai ki tashi tsaye ki dauki matani tunda wuri kina dai kallon halin da nake ciki kullum cikin fargabar kar kana zaune a zo a shafa maka alaqaqai”.

Wato tunda ta fara magana qirjina ya shiga kidan Mandiri, ko bata fayyace mun komai ba na rigada na gano inda maganar ta ta dosa dan Mijinta ba qaramin dan Akuya bane, saboda tantiranci har gida yake kai mata mata seda tayi da gaske da taimakon Allah sannan ya rage ba wai ya dena dukka ba. Jin da tayi nayi shiru ina kallonta yasa taci gaba da cewa

“Baban Shukra ne yazo mun da soki burutsun sa wai Mijin qawar tawa da kike qara zugani ina masa rashin mutunchi ashe duk kanwar ja ce shi da shi yau sun hade a Jungle ya dakko wata Babe me zafi, banyarda ba tunda nasan halin sa ba sanin me yakeyi bama yake wani lokacin se washe gari wallahi Maman Farida mun fita da daddare za’a siyowa su Hisham Icecream mukayi kicibus da su a gurin,

Saboda Baban Shukra ya tabbatar mun seda muka jira su suka gama abinda zasuyi suka fita yabi bayan su har Hotel din da take mukaje kafin muka tafi gida. Washe gari ma ya sake cemun ya ganshi kamar ma daki ya kamawa yarinyar a gurin yake zuwa yana tafiya in taqaice miki jiya gurin 11 ma video call ya kirani ya nuna mun su a Gurin swimming pool kin ga har hoto ya musu kiga evidence fuskarta ce daibata fito ba”.

Idan da Maman shukrah tasan yanda maganganunta suka jefani da ta dade dayinshiru amma seta miqomun wayarta tana cewa “kin gani karma kice qarya nake”.

Duk yanda naso na hana ido na kalla abin ya gagara, a fili na furta “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” ina dafe qirjina jin kamar zuciya ta zata bullo ta fito, dagaske Bashir ne ga fuskarsa nan yana murmushi ya rungume wadda bansan ko wacece ba ta juya baya dan haka ba’a ganin fuskarta.

Har Maman Shukra ta qaraci surutanta ta tafi ban sake gane komai ba, dakyar nayi sallar Magriba da Isha na nemi guri a palour na zauna ina jiran naga ta inda Bashir ze bullo.

Gaba daya ido na sun soye kaina ya qulle na ma rasa ta ina zan faro tunani kalmar “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” kawai nake maimaitawa wadda ta taimakamun wajen zama cikin hayyacina.

Ina zaune a palour har qarfe sha biyu na dare ina jiransa ga wayarsa na kira yafi sau nawa amma se ace not reachable har Musan na kira shi kuma wayarsa a kashe.

Hankali na a tashe ina ta zagaya Palour ina kuma sake gwada wayar sa cikin Sa’a ta shiga daidai sanda naji tsayuwar motarsa a waje se na kashe na tsaya jiran shigowarsa.

Yanda yaci burki yana kallona ya tabbatar mun be so ya tarar dani ido biyun ba amma saboda iya duniyanci irin na Namiji se ya wani chanza fuska zuwa kalar gajiya ya fara sakin wasu guntayen tsaki yana langwabewa, zuciyata na dukan uku uku na nufe shi, a raina Addu’a nakeyi Allah yasa abinda Maman Shukrah ta fada ba gaskiya bane sedai ina qarasawa dab da shi Qamshin Turaren Humrah da kuma shatin Jambaki daya fito radau a gefen kumatunsa da wuyansa suka yi mun sallama,

Dum naji a kaina kamar wadda aka kwadawa guduma, Ban yarda daidai idona ya gani ba dan haka da saurin gaske na riqo fuskarsa na kunna torch light din wayata na haska da kyau se ya janye yana cewa

“Ma’u lafiyarki kuwa, me kike nema a fuskata kuma?”

“Kai zan tambaya Bashir daga ina kake? Turaren waye a jikinka sannan ga shatin Lips din mace nan a Fuskar ka Bashir daman zaman da kakeyi a waje abinda kake yi kenan to yau Allah ya toni asirinka?” Na fada cikin tashin hankali ina ja da baya, se yayi saurin riqoni ganin ina neman fadawa kan Centre table ta baya na fizge cikin faga murya nace

“karka kuskura ka tabani, daman an gaya mun ana ganinka da mace amma saboda yardar da nayi dakai yasa ban taba kawo wa raina zakaci amanata ba, kana da Mata har biyu dame muka rage ka Bashir zaka fita waje kana zubar mana da mutunchi? Wace yar iska ce ka ajiye a Hotel kake zuwa Gurin ta har mutane suke ganinka ana daukar hotonku?”

A zabure ya kwalalo ido waje yana kallona yace “Hotona Ma’u? Waye ya dauke mu?”

“Oh ta tabbata kenan ka aikata, kana zaton Asirinka ze rufune? Toh Allah ya tona ka na gani kuma mutanen duniya ma sun sani duk me maka kallon mutumij kirki ka zubarwa da kanka mutunchi a gurinsu” na fada wasu hawaye masu zafin gaske suna zubo mun, Se ya sake matsowa yana qoqarin riqe ni yace

“Ya isa Ma’u karki tayar da yara a bacci ki bari muje daki zan gaya miki komai ba abinda kike zargi bane wallahi”.

Wani banzan kallo na watsa masa kafin nace “Dawa zakaje dakin? Idan kaga na dara daga nan toh ka gayamun wace yar iska ka ajiye a hotel yara kuma ai bakayi tunanin su ba kaje kana zubar musu da qima kana raba musu abin gori a gari”.

Duk yanda Bashir yaso dana sassauta na zauna muyi maganar qi nayi, gani nake yama raina mun hankali tunda alama ya nuna maganar Gaskiya ce dan da nace naga hotonsa ai be musa ba abinda ya qara dagamun hankali kenan na shiga rusa kuka ina cewa “Ka cuce ni Bashir ka cuce ni idan har mugun halinka ya shafi yayana bazan taba yafe maka ba”.

“Wallahi Asma’u ba abinda kike tunani bane ta yaya tun da quruciyata ban nemi matan banza ba se yanzu da girma ya fara kamani na tara iyali? Ku biyu fa nake da ku wace ni’ima ce Allah beyi muku ba da zan fita waje na nema?”

“Ita waccen din da ka ajiye qanwar uwarka ce kenan” na fada a mugun fusace nayi kansa dan rainin hankalin nasa kuma ya fara yawa, ganin da yayi na taho gadan gadan se ya matsa yana cewa “ba wata bace Ma’u Amirah ce, wallahi Amirah ce tazo nasan bazaki yarda ki sauketa a gidan nan ba shiyasa na kaita Hotel”.

Wani burki naci tareda qamewa a inda nake ina rarraba ido tsakanin idonsa da bakinsa, so nake na tabbatar da abinda kunnena yaji ko kuwa ba daidai bane, se ya matsoni yana sake cewa “Amirah ce tazo wallahi tun last week Sunday, nima ban sanda zuwanta ba seda ta sauka tace mun gata a Lagos, ban san yanda zaki dauki maganar ba shi yasa na kasa fada miki wallahi amma gobe ma zata tafi”.

“Bashir dakai da ita kuje Allah yayi muku yanda kuke mini” na fada cikin wani irin sanyi kafin na juya na shige dakina kfain ma ya biyoni na sakawa qofar key. Kan gadon na fada na fashe da kukan da ko mutuwar Mahaifina banyi irinsa ba.

Kuka ne na zallar baqin ciki da takaici wannan wane irin abu ne? Anya Bashir yana da hankali da tunani kuwa, yana lissafi kafin ya aikata wani abun?

Idan ya gayamun Amirah zata zo me zanyi, kai ko be fadamun ba ina zaune ta shigo gidan na ya zanyi da ita ai gidan sa ne kuma ko bata auran Bashir ita me iya zuwa gidansa ta zauna ce amma shine ze dauketa ya kaita Hotel ya ringa satar hanya yana zuwa mutane suna ganinsa yanzu Allah kadai yasan mutum nawa suke masa kallon Fasiqi ya ajiye farka a Hotel.

Inajinsa yana buga qofar yana magiya na bude amma nayi banza dashi na tashi nayiwo alwala nayi na tada sallah ina yi ina kuka ban idar ba seda aka fara kiraye kirayen Asuba, ina idar da Sallar Asuba kuwa wani wahalallen bacci ya kwashe ni da ban farka ba se sha biyun rana shima qiqi qiqin da ake da qofa ne yasa na bude ido na.

Ina dafe da kaina dayayimun nauyi na nufi qofar jin surutan mutane kamar ma ballata ake so ayi se na murza key din naja baya ganin yanda Bashir ya fado kamar an cillo shi, a bazata ya rungumoni ban yi wata wata ba kuwa na hankadashi da dukkan qarfina yai baya Allah ya taimake shi bango ya tare shi, ina kallon securities din daya gayya toh suka juya suka tafi.

Be daddara ba ya sake nufo ni yana cewa “Ma’u lafiya kike tun jiya kin kulle qofa babu irin bugun da banyi ba gaba daya kin tayar mana da hankali ga yara can se kuka sukeyi”.

Tsaki nayi na juya na cire Hijabina na shige bandaki na bar shi a tsaye a gurin, sanda na fito baya nan, riga kawai na zura dan banida nutsuwar da zan saka komai a jikina, bakina har wani daci yake mun saboda bacin.

Lokacin da na fito Suna zaune shida Matarsa da ban san sanda tazo ba sunyi tsuru kamar masu jiran Sadaka. Kallo daya nayi musu na wuce Kitchen inajinsa ya taso ya biyo baya na seda muka shiga ciki sannan na waiwaya na kalle shi nace “kasan Allah ko ka fita ko kuma ka kalli nan (na nuna masa bangaren da wuqaqe suke) gasu nan kala kala in ka qureni se nayi maka aika aika na huta da takaici” ai kafin na qarasa fit ya fice daga Kitchen din duk yanayin bacin ran da nake ciki seda nayi dariya sosai dan dagaske ya tsorata.
“Allah ya tsare ni da irin wannan zuciyar” na fada a fili kafin na zuba ruwa a kettle na kunna kafin ya tafasa na hada kayan shayi a babban kofin dan bazan bari baqin cikin Miji da kishiya su naka sani ba.

Shayina me kauri na hado na zubo dambun nama a bowl na dakko ledar biredi, kamar bansan da tsurom mutane ba haka na nemi kujera na hakince sannan na kunna Tv ina shan shayina ina kallo.

“Ma’u ga Amirah kin ganta wallahi ita ce ba wata daban ba na yarda nayi kuskure tun farko da ban sanar miki da zuwanta ba amma kiyi haquri”.

Yanda yai maganar kamar wanda yayi wa babarsa wani qundumemen laifi yazo bata haquri harda wani zamowa qasa saboda tsabar iya sharri ga muryar sa har rawa take yasa na kalle shi, seda na cinye biredin dana tura a bakina na kora shayi sannan cikin dan murmushi nace

“Oh wannan be ishe ka ba kenan seka qulla mun sharri a sake tafiya dani a baki ace na mallake ka har durqusamun kake ba?
Ni tunda nake dakai ma ka taba bani haquri ne amma da yake yau kana so ka qaramun baqin jini shine kake duqawa ai shikenan, ni na gama magana ta tun jiya duk abinda mutum yayi mun na barshi da Allah” daga nan na ci gaba da cin abincina ina jinsa ya qaraci naci da magiyar sa amma tafi ka mutu bance masa ba.

Amirah da ta shaqa tayi tam daman ga takaicin dakko ta dayayi tun da sassafe ya ringa surfa mata ruwan masifa ga abinda ta janyo masa nan ana yawo dashi a gari an ce ya ajiye karuwa ya taso ta a gaba wai tazo su bawa Ma’u haquri tun bakwan safe take zaune se yanzun dana fito ga wannan Dramar da yakeyi kuma har wata kwallar takaici ce ta taru a idonta. Cikin muryar bacin rai tace

“Ni Yaya ka dakko ni tun safe ko wanka banyi ba bare naci abinci gashi yanzu Azahar tayi gaskiya ni yunwa nake ji”.

“Waya hana ki kici abincin ai gaki ka Kitchen nan duk bake kika jawowa mutane ba” ya hayayyaqo mata, seta miqe zata tafi Kitchen din nayi sauri tare ta da cewa “Ji mana, karki shigar mun Kitchen malama ku koma can inda ya aje ki ki nemi abinci ba’a nan ba” ban qarasa cinye biredi na ba na daure ledar kawai na kwankwade shayin na tashi. Seda na kullo qofar Kitchen din da mukulli na zare kafin na shige dakin su Aliyu na bar Bashir da Amirah baki sake suna bina da kallo.

Aliyu da Jafar na zaune da alama duk suna jin abinda yake faruwa se nayi murmushi na zauna ina cewa “me kuka bawa yan biyuna har yanzu basu tashi ba?”

“Game sukayi tayi Mami basu kwanta da wuri ba jiya dakyar suka tashi dazu suka ci abinci ma” Jafar ya fada. Whatsapp na bude a wayata ina shiga message din Maman Shukra ya fado nayi murmushi na bude
“Maman Farida ina fatan dai bada tashin hankali kika tunkare shi ba ko, kinsan fa irin wannan abun se a hankali da Addu’a kuma in ba haka ba a maimakon a samu sauqi se ka qara tunzura mutum” ta rubuta, se na mayar mata da cewa

“Ai baki sani ba, ashe Amaryar sa ce tazo sh ya sauke ta acan kin gansu tun dazu ya dakko ta tana nan”.

“Tab amma se abar Engineer, to ke me kakace yanzu?”

“Me zance kuwa, gasu can na barsu a palour ni ina daki ma bacci zanyi se anjim mayi magana” na fada dan na datse hirar.

Alawiyya yayata na duba naga bata online, fita nayi daga dakin na koma nawa dan ina so na l kirata, sanda na fito palour Bashir kadai na tarar har na wuce na yi kwana na shiga dakinsa. Addu’a nake Allah yasa tana ciki yau na gwada musu danyan kai daga shi har ita se Allah ya temaketa babu kowa har Toilet na duba bata ciki na kullo qofar na fito se ya tare ni yana cewa

“Ta tafi gidan Ghali daga can gobe seta wuce Gombe” (Ghali dan wan Baban su Bashir ne).

Wunin ranar zir haka yayi shi a palour daya ji motsina ze taso yana so yayi mun magana amma naqi bashi fuska sam da daddare ina jinsa suna waya yana ta masifa nidai qala bance masa, daya biyo ni dakina ma abinda tun tsahon zaman mu a gidan nan be taba kwana a ciki ba yana kwanciya na juya mukayi kai da qafa yana fita sallar Asuba kuma na saka Key.

Haka muka cinye satin, har zuciyata na huce kodan irin ban haqurin da ya ringa yi mun amma ban nuna masa ba, yanzu dai ina dafa abinci dashi kuma in yayi mun magana ina amsawa sakin fuska ne dai babu na kuma dena shiga sabgarsa sannan na koma dakina da kwana

Please Login or Register in order to submit comment