Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shawara me ya kamata nayi?"

Shiru ta mun harna gama magana ina gunsheqara kuka, seda nayi iya yina nayi shiru  kafin tace mun

"To yanzu kira kikayi ki gaya mun zaki koma gidan mijinki ko yaya?"
"Goggo shawarar ki nake nema ban san meya kamata nayi ba" nayi saurin bata amsa. Se da tayi wani murmushi kafin tace

"To Ma'u ai maganar ki ba tayi kama da ta wadda take neman shawara ba. Cewa kikayi bazaki iya tafiya kibar yayanki ba to ai seki koma gidan ubansu kawai ki riqe su daman ba abinda kike so ba kenan duk meye na wani kuka ni kin tayar mun da hankali abinda befi ki tura mana da saqo a waya ba akan zaki mayar da aure muzo mu taya ki murna shikenan fa.

Addu'ata kullum Allah yayi miki zabin Alkahiri, idan so nane bazan so ki koma inda ba'a san darajarki ba tunda har Allah ya fito dake ba kuma wai ke kika nemi sakin nan ba amma tunda kin zabi ki koma Allah yasa hakan ya zamo miki Alkahiri" ta qarasa maganar a sanyaye.

Yanda take magana kadai ya isa ya nunamun bata ji dadin abin ba, qarasa hadiye kukana nayi nace mata

"Goggo ba cewa nayi zan koma gidan Bashir ba wallahi nima na gaji, na yarda bani ce a gabansa amma Goggo makomar Yarana nake dubawa. Dazu suka zo suka sameni suna kuka akan nayi haquri na koma gidan su.

Goggo ba'a basu abinci komai na rayuwar su a nan sukeyinsa idan zasu kai dayan dare babu wanda ze biyo sahub su aga suna ina yanzu da bana nan ya ya zasuyi?"

"Saboda an san suna da inda zasuje shi yasa, saboda yasan zakiyi musu shiyasa ya sake sun da kuma su yake amfani yake karya lagon zuciyarki tunda ya fahimci sune raininki.

Waime kika ce kina tsoro ne ma tarbiyyar su karta lalace ko? To bari kiji Allah shine yake shiryawa ko a gabanki suke idan Allah be taya miki ba baki isa su gyaru yanda kike so ba.
Idan kuma kika mutu kika barsu a hannun nasa da matar tasa yaya zakiyi se hakan ya zama silar lalacewarsu ko yaya?

Na yarda iyaye suna taka muhimmiyar rawa a gurin gyaruwar yayansu amma karki kuskura ki saka tsoro ko tunanin ke zakiyiwa kanki ki yarda da Allah ki bashi amanar Yayanki ki bisu da Addu'a duk bangon duniyar da suke zata iske su.

Yaya nawa suka lalace a tsakanin uwa da uba? Nawa suka zama nagartattu ba tareda uwarsu ko ubansu ba?

A sanda Bashir ya sake ki meyasa be kawo Tarbiyyar yayansa ba ya kwace su yace a bashi abinsa ai saboda yasan ze iya ne ko, to in har shawarata kike nema Asma'u akan zancen auranki da Bashir ni Maryama nace ki haqura dashi ko qaddara iyakar zaman da Allah yayi zaku zauna kenan.

A sanda kika so ki balle auran ni nayita tausarki ina nuna miki kiyi hauwa ki zauna badan bana ganin cutarwar da take ciki ba Aa sedan bana so muyiwa Allah katsalandan. A kullum ina yi miki addu'a Allah ya zaba miki mafi Alkahiri tsakanin zamanki da Bashir se gashi lokaci daya ba tareda tsammani ba shida kansa ya qosa dake ya sallame ki sakin wulaqanci Asma'u ko iya wannan a zatona ya isa ya sa ki hankalta ki cire shi daga zuciyarki.

Karki yiwa kanki abinda zaki dawo daga baya kina dana sani, idan Yaya ne ki cire idonki akansu na tabbatar Miki daga sanda yaga babu ke ko kin dena damuwa da al'amuransu ze mayar da hankalin sa tunda ai kin fi kowa sanin halinsa akan Yaya baze taba barin abinda ze cutar dasu ba.

Ko ba wannan ba ai Addini ya baki damar da zaki karbe su ki riqe su idan kin dage kina iya kai maganar zuwa ga hukuma zata kwatar miki su ta baki amma ki sani zaman dan wani da uban wani abune me matuqar wahala dashi kadai idan bakiyi sa'a ba ya isa ya dagula miki lissafi ya hanaki zaman lafiya da duk mijin da zaki aura.

Duk yanda wani ze nuna miki son yayanki ba lallai ya dore ba Asma'u dan yau da gobe tafi qarfin wasa musamman wadannan yayan naki kinga ko Ali kadai ya isa ya kaso miki aure dan wannan dan Halin ubansa tsaf ya kwashe.

Ki barsu Mazane dama kyansu gidan ubansu munyi magana da Bashir din nace ya baki Farida itama bake zaki riqe ba idan kinyi aure daga ita har Amnah tattaro su zakiyi ko ki mayarwa da Hajiyar ku Gombe koni ki kawo mun su nan dukda Qarami daman ya dade yana zancen dauke Amnah ni na hana nace su bar miki ki qara sa ladanki amma yanzu dole in kika sake aure ki barsu dan baki dan irin zamanda zaki tarar ba duk da muna miki fata da yaqinin na Alkahiri in Allah ya yarda zaki dace da irin rayuwar da kike fata, zakiyi farin ciki da zabinda kikayi".

Har Goggo ta dasa aya kuka nake dan na fahimci bazata goya mun baya akan batun komawa gidan Bashir ba ba kuma ta fahimci abinda nake nufi game da tarbiyyar Yayana ba. Mutane suna daukar Tarbiyyar Namiji a me sauqi ni kuwa a gurina tafi ta Yaya mata wahala saboda su kina iya matse su ku zauna a gida Namiji fa? Duk inda kika kai da taka tsantsan se sun balle sun fita su cudanya da Yara kala kala Allah ne kadai ze kare maka su tareda saka ido da jajircewar ka.

"Kuka baze miki magani ba, duk irin halin da kika shiga kar ki sare da yiwa yayanki da na sauran musulmi Addu'a bari kiji wani sirri a duk sanda kikayi addu'a me kyau ga dN wani mala'iku zasu taya ki da yiwa naki yayan irin wannan Addu'ar to meyafi wannan dadi

Asma'u Addu'a itta ce rigakafin da zaki musu ko da ke ko babu ke.Harshen uwa nada tasiri akan yayanta haka Addu'ar ta tana bibiyar su  koda bayan ranta walau ta Alkahiri ko ta sharri shiyasa yana da kyau mu ringa kyautata kalami ga yayanmu saboda wani abun da wasa zaki furta shi ki manta wani lokaci kiga yayi tasiri akan Yaro ki shiga tashin hankali da tunanin ya akayi yaronki yake abu kaza baki san cewar da bakinki kika jefe shi da wannan abun ba.

Dan haka ki cire tsoron lalacewarsu dan wai bakya tare dasu ki barsu a hannun Allah bi jahi rasulillahi babu abinda ze same su se Alkhairi amma zama da Bashir kuwa kin gama shi Ma'u ki barshi har abada Allah ya sanya wa abinda kukayi a baya albarka. Se da safe ni zan kwanta zuwa an jima na tashi, kema da wannan kukan da Allah kika kaiwa kukan naki yayi miki magani" Goggo ta sake fada kafin ta kashe wayarta.

Bawai dan na sauka akan ra'ayina ba Haka na tashi na dauro Alwalar ina sallah ina kuka, Addu'a nayita ni kaina bansan adadin abinda na roqa ba qarshe bacci ya kwasheni akan sallayar se farkawa nayi na ga gari yayi haske tarwai.

Wunin ranar haka nayi shi babu suku ni sam, a zuciyata ni kaina ban aminta da kome na gidan Bashir ba amma idan na dubi yaran se naji zan iya sadaukar da farin cikina in dai rayuwarsu zata inganta.

Da yake asabar ce ina gida babu inda naje, da yamma lis sega Anty ta shigo cikin farin ciki da mamaki na tarbeta dan ban san da dawowarta ba seda muka zauna take cemun wai tun jiya da yamma ta dawo ta tsaya gyara gyare gyare ne shiyasa bata kira ni ta gaya mun ta dawo ba.

"Amma Anty baki kyauta ba maimakon ki kirani na tayaki gyaran shine se yanzu zaki shigo" na fada

"Kiyi haquri kinsan ba wani datti gurin yayi ba tunda Yallabai yana yawan zagayowa, ni ba wannan ba tashi mu shiga ciki kiga kayan arziqi nan dan hadi nayo miki na musamman naku na Amare gara muzo mu fara abinda ya kamata da wuri"

Shiru nayi tareda sun kuyar da kaina qasa dan bansan taya zan fara gaya mata chanjin shawarar da nayi ba Idan na tuna irin ihun murnar data ringayi randa na gaya mata zance wa Yusuf ya turo maganar auran mu ta ringa saka mun albarka yanda kasan qaninta zan aura yanzu idan nace mata na fasa ai inaga dukana kawai zata yi ta huta.

"Meya faru kuma ina magana kin sunkuyar da kai qasa?" Ta fada tana kallona

"Anty, ni ina ganin aurena da Yusuf baze yuwu ba saboda..." bata bari na fada mata dalili na ba ta kwashi salati tana tafa hannu tace

"Ai na dade ina addu'ar Allah ya tsareni da ganin wannan rana ashe tana tafe ni Halima, ai wallahi na sani, ke din kuma ai Ma'u kinyi asara kedai kuma na rantse da Allah daga yau karki sake nuna ma kin sanni babu ni babu ke. Ke ni inaga tashi ma zanyi daga unguwar nan dan bazan iya kallon abin takaici ba bani da damar gyara wa ke yanzu har akwai abinda Za'a gaya miki akan Bashir ki yarda ki koma gidansa?

Muna zaune gani gaki yallabai ya roqe shi dan darajar zuri'ar dake tsakaninku yayi haquri ya maida ke kafin ma wani yaki abinda ya faru amma ya qeqashe qasa yace ko zaki koma ba yanzu ba se kin gane kuskurenki ki sannan yanzu kin gane shine zaki koma masa ba to Allah ya taimaka ki koma kijr ku qarasa igiya dayar daga nan seki share daki kiyi zaman yayanki kuma tunda ya rigada ya tsafance ki bazaki iya rayuwa babu shi ba se kije kiyita komawa kuma na rantse ko qofar gidana kikazo sena miki rashin mutunchi mara zuciya kawai" fuuu ta kwashi kayan data shigo dasu tayi waje, duk yanda na bita ina tsayar da ita amma taqi saurarona se zagina take tsabar masifa yau Sokkotancin ma ta komayi tana aiko mun da wasu qunduma qunduman ashar da ban san ma'anar su ba.

Haka na cinye Weekend gari yamun zafi dan dai Ashar ta kowacce kwana karbarta nake dan Goggo seda ta kira yan uwana kaf ta gaya musu wai zan koma gidan Bashir ko a yaushe mukayi haka da ita oho?

Alawiyya damab cewa tayi daga randa na koma na qaddar ba uba daya ya haife mu ba se na tafi na nemi yan uwana marasa zuciya ko kuma na maida Dada uwata kawai se su san qauanr da nakewa Bashir da ahalin sa ta kai duk cikin su an rasa wadda ta fahimci dalili na, bayan nasan zasu iya yin fiye da haka suma idan da akan su hakan ta faru amma ni na rasa wanda ze bani goyon baya.

Ranar Litinin aka koma makaranta saboda yanayin da nake ciki babu wani shiri da nayiwa yaran dan ko maganar siyo jaka da takalma ma banje ba tsofin nasu suka saka nace idanna taso aiki zan biya na siyo musu.

A tare muka fito Bashir na qofar gida yana jiransu, yanda ya amsa gaisuwar da nayi masa se naji guiwoyina sunyi sanyi dan a wani basarwa ya amsa yana dannan wayarsa ko dagowa ya kalli inda nake ma beyi ba balle wannan binbini da ban haqurin da yake mun duk sanda muka hadu.

Har naje office zuciyata cike da tunanin chanjin da na gani a tattare dashi, ban dade da shiga ba Yusuf ya kirani wai ze shigo yau da daddare, kai wannan mutum shima akwai dan banzan naci na fada a fili ina jan tsaki bayan dana ajiye wayar. Se a sannan na tuna da ashe fa ni nace masa yazo akwai labari me dadi tan kace akwai cakwakiya kuwa dai.

"Madam Asma'u ki godewa Allah, baki rufa shekara da mutuwar auranki ba har kika samu me sonki da aure bada lalata ba shine kike mita kina cewa yafiya naci? To wallahi kiwa kanki qiyamullaili. Ni nan na isheki ishara shekara ta bakwai kenan da fitowata kina kallo duk wanda zezo wata manufa ce take kawo shi badai aure ba shi kansa tsohon mijin nawa dana zata ze dawo tunda yai bikon farko farko na tsaya jan aji ya tafi yayi auransa ya manta dani" Sahiba sakatariyata ta fada cikin jimami.

Kallonta nayi ina juya maganganunta a raina, maganar tsohon mijinta da ta zata ze dawo tafi tsayamun a rai to kodai nima Bashir ya gaji da bani haqurin ne yayi zuciya a yanzu da ni kuma na sakko nake shirin koma masa idankuwa hakane gaskiya ina tsaka me wuya ko ince ina shirin sakin reshe na kama ganye ai kuwa dole na sake lissafi.

Wunin ranar tsaf harna tashi aiki ko qyallin Saqon daya saba aiko mun ban gabi ba bare naga kiransa har na koma gida bayan dana tsaya nayiwa yara siyayyar da nace zanyi.

BASHIR
Dukda zuciyarsa tana cike da taraddadin yuwuwar shawo kan Ma'u da Aliyu yayi masa alqawari amma haka ya dage yake bawa kansa qwarin guiwa. Saboda gudun ta zargi wani abu yasa ya dauke qafa daga zuwa inda take ko a waya ya dena takura mata tunda tace ya rabu da ita to ze bagarar a haka har zuwa sanda zega yanda abubuwan suka daidaita.

Sanda ya dauki yaran suka kama hanya shida kansa yaji kamar abinda yayi kuma be kyauta ba se yaji kamar ya kirata ya bata haquri amma ya kanne shi a nasa tunanin duk salo ne da zesa karta zargi yana da hannu a gurin tura mata yaran su roqeta. A gurin aiki kansa ya gwada tura mata saqo yafi sau biyar yana fasawa haka ya rarrafa ya dawo yana dai ta addu'ar Allah yasa komai ya tafi daidai dukda Aliyu ya gaya masa akwai alamun nasara a cikin shirin nasu dan yaga gaba daya Mamin tayi sanyi kuma ko waya bega sunayi da Yusuf din ba  a kwana biyun.

Da daddare bayan ya dawo daga aiki ta window dakinsa yana tsaye yaga giftawar motar daya tabbata ta wannan Mayen ce dan shi kadai yake zuwa layin da irinsu. Kaya yake canzawa cikin sauri ya qarasa ya fito dan baze lamunci yana qoqarin gyara wani banza yana zuwa yana warware masa ba. Yana kaiwa Palour yaci karo da Ahmad daya shigo gidan da gudu yana kiran Muhammad.

"Kai meye haka so kake seka fadi kake gudu ko" ya fada yana tare shi.
"Moh nake nema Uncle Yusuf ne yazo yace na kirashi" Ahmad din ya fada yana qoqarin shigewa dakinsu ya kira dan uwansa se Bashir ya fizgoshi yana zare ido yace

"Qanin ubanka ne da kake ce masa wani Uncle, dalla wuce ciki ka zauna idan na sake ganin qafarka a waje ma sena karyata kai ko magana naga kuj sake kula mutumin nan se na bata muku rai gaba daya" ya turashi ciki shi kuma yayi waje, gara yaje gidan a gabanta a gaban Yusuf din yaja masa kunne ya fita daga sabgar Yaransa.

ASMA'U

Bayan sallar Magriba Yusuf ya kirani yana hanya, ruwa da Lemo kawai na sa a tanadar masa, har nace a fita da kujera waje sega Yayyafi ya sauko, dukka yaran suna gidan banda Aliyu da tunda na dawo ya leqo daga qofar gidan su ya mun sannu da zuwa ya koma shikenan.

Ina wutri wayata tayi qara, seda na sallame na duba, Yusuf ne, banja doguwar Addu'a ba na shafa na dan goga hoda a fuskata da man leba na fesa turare kadan kafin na zura takalmi na fito palour da Amnah ta gyara tsaf ta saka turare se qamshi yake babu kowa da alama sun shige daki ko sun tafi gidansu.

Da kaina na leqa na masa iso ciki,

Yana zaune akan bayan motarsa yana waya seda ya qara kafin ya sauko fuskarsa dauke da murmushin nan nasa da baya gajiya dayi yace

"Se yanzu duk ruwa ya gama mun duka ina zaman jira".

"Banda sharri ina ruwan yake daya dake ka? Kuma wayace ma ka fito daga motar da sekayi zamanka a ciki ai in baka so yayyafin ya taba ka. Sallah nakeyi sanda ka kira ni shiyasa ban fito ba".

"Aina hangoki shiyasa na zauna anan na kira su Ma'u yau duk ban smau munyi magana dasu ba"

"Allah sarki" na fada can qasan raina kuma wai naji haushi wai shi me mata. A sanyaye nayi gaba ya biyo ni a baya yana tambayar ina yaran yaji shiru babu wanda yazo masa oyoyo, ban kula shi ba dan tilawar abinda zan gaya masa kawai nake a cikin zuciyata seda muka shiga ya zauna akan kujera na wuce dakinsu Amnah ina qwala mata kira ta fito da Hijab a jikinta alamar ita ma sallah tayi

"Gani Mami, Lah Uncle Yusuf sannu da zuwa, Jafar toga Uncle din ma yazo seka tambaye shi da kanka" ta kwalawa Jafar kira da murnarta ganin Yusuf din.

"Ki kawo masa ruwa" na fada ina jiyawa, sega su Jafar din sun fito ashe duk suna ciki aka fara layin gaishe shi kowa baki a washe na rasa irin sabon daya shiga tsakanin su haka, koda yake gaskiya ya iya tafida yara yanda yake jansu a ajiki dole su sake dashi sosai.

"Yanzu sallah guda saboda rowa ko hoto daya baku turamun na gani ba. Gashi mutuniyarka album guda ta turo a nuna maka amma kai baka tura mata ba ko" ya fada yana kallon Jafar dake ta doka uban murmushi

"Ai ni bani da waya uncle yanzu ma nacewa Yah Amnah ta bani aron tata sena karbi Number ka a gurin Mamy damab nayi hoton fa na ajiye mata Allah" Ya fada yana dariya

"To dakko wayar ka turamun tunda gani nazo yanzu" gaba daya suka tafi dakko wayar, ya juyo yana kallona yace

"Kinsan Allah, jikina har rawa yake na matsu naji abinda kika ce zaki gaya mun, inada tulin ayyuka amma na kasa haqura har wani satin dole na tsallake na taho yau ki samu ki gaya mun koma menene zuciyata ta huta Allah yasa abinda na dade ina tsammanin jine daga gareki" Yusuf ya fada yana kafeni da kallon nan nasa me narka mun zuciya, yawu na hadiye na sake gyara fuskata dan karna bashi damar ganin aka sin abinda nake fada akan fuskata.

"Daman abinda nake so na gaya maka kamar yanda ka fada mu ba yara bane, maganar mu zauna muna jan lokaci akan abu duk be kamata ba shiyasa naga ya kamata na fito na gaya maka Gaskiya ni na yanke shawarar zan....."

"Malam tashi ka fita daga gidannan" maganar Bashir da bansan shigowarsa ba ta katse ni daga fadar abinda nayi niyya"

"Barka da dare yallabai" Yusuf ya miqa masa hannu yana fada fuskarsa dauke da murmushi kamar bega irin kallon da Bashir dinyake masa ba.

"Ka fita daga gidan nan nace tun kafin Ranka ya baci sannan bana gaya maka ka fita a harkar matata ba shine kaci gaba da bibiyarta ko to ka tabbata sena aikata abinda nace maka zanyi, sena bata maka siyarka na gayawa duniya kai mutumin banzane manemin matana aure" Bashir ya fada yana Wani huci kamar Ya taka wuta.

"Meye haka Malam ya zaka shigo mun gida kana zagin baqona wa ma ya baka izinin shigowa kai da har zaka kawo mun tashin hankali gida" na fada ina miqewa tsaye.

"Malama ba dake nake ba, ke ko kunya bakya ji ki ringa shigo da qarti cikin gida kina tara zawarawa Saboda rashin kamun kai tunda ke baki san daidai ba to ni dole na kare martabar yayana dan bazaki lalata musu tunani su dauka abinda kikeyi daidai ne ba, kai kuma tashi ka fita idan ba haka ba se kayi dana sanin zuwan ka gidan nan yau" Bashir ya fada cikin fitar hayyaci da kishin da yake cin zuciyarsa.

"Ni kake kira mara kamun kai Bashir nice mara Tarbiyya?" Na fada ina nuna kaina saboda yanda maganar sa ta dakeni, ban fito daga jimamin ba naji yace

"Na fada, wace mace ce zata ringa shiga da Namiji gidanta a kirata me kamun kai? To bari kiji, idan ma kinayin haka ne danki bata mun tai kinyi a banza saboda na tabbatar miki duk wadanda suke rudar miki da tunaninba auranki zasuyi ba. Ni din dai nine duk ma inda zakije ki dawo ina zaune sekib dawo mun dan na tabbatar har duniya ta nade bazaki taba son wani abu bayan ni ba Ma'u idan kuma nayi qarya to ki fda muji".

"Tab Allah Nagode maka daba ka bani damar aikata aikin dana sani ba" na fada a zuciyata kafin na koma kan kujerar dana tashi na zauna ina qoqarin yaqi da maganganun da Bashir ya yaba mun ni Asma'u ya kalli tsabar ido na ya kirani da mara kamun kai lallai Bashir ya isa tabbataccen mara mutunci.

Yusuf daya harde hannu yana kallonsa ne ya bude baki zeyi magana nayi saurin dakatar dashi da cewa

"Ka zauna, mema nake ce maka ne kafin ya shigo?" Na fada fuskata dauke da murmushi, zama yayi shina yana mayar mun da murmushin yace

"Ina jinki, wannan albishir din da kika ce zaki mun fadi ina jinki".

"Oh ga mahaukaci yana magana shine dukkan ku zaku mun shiru ko? Malam tashi ka fita ke kuma Ma'u zaki san ni kike wulaqantawa akan wani can dan iska da be san darajarki ba" Bashir ya fada a haukace kamar ze rufe mu da duka.

"Ko dai mu bari anjima na gaya maka a waya? Kaga yanzu akwai hayaniya bazata barmu mu tattauna da kyau ba kuma maganar tana da buqatar nutsuwa sosai" na fada ba tareda na mayar da hankali akan shirmen Bashir ba

"Aa muje waje toh ko cikin mota dangaskiya kika ga na tafi ba tareda naji dalilin kiran nna ba toh inaga yau bazan iya bacci ba"

Dariya nayi na miqe ina cewa
"Gaskiya dai muje nasan ko ka ji din ma duk haka take be zama lallai ka iya bacci ba yau" fizgoni da akayi baya yasa nayi shiru ina gama daidaita tsayuwata kuwa na kwashe shida mari a mugun fusace nace

"Rashin kamun kan nawa be kai kowanne gaja ya ringa dora qazamin hannunsa a jikina ba" na waiwaya na kalli Yusuf da yanayin fuskarsa ya chanza zuwa matuqar bacin rai nace

"Yusuf bazan iya magana yanzu ba saboda raina ya baci, kaje kawai ka gayawa Alhaji Qarami sati biyun daya saka sunyi yawa a mayar dashi Juma'ar nan me zuwa"

"Bangane abinda kike nufi ba Asmy? Me za'a dawo dashi wannan juma'ar ko daurin auran mu kike nufi?" Ya shiga jero mun tambayoyin a rikice, wani mugun kallo na jefawa Bashir daya dafe kunci yai mutuwar tsaye nayi kafin nace masa

"Haka nake nufi ko yayi maka wuri da yawa.." kafin na idar da maganata ya kife a gurin yayi sujjada ya dago cikin wata kalar madaukakiyar murna ya riqo Bashir yana cewa

"Nagode Nagode Bashir ka gaya mun dame zan biyaka a rayuwa? A da na dauka a matsayin babban abokin Adawa ashe ban san banida masoyi sama dakai ba tunda gashi kayi silar da zan mallaki muradin zuciyata.

Kai na rantse ka shirya samun double promotion, a ina kake aiki? Koda yake barshi zan binciko da kaina" seya sake shi ya juyo ya kalleni

"Wife! Ina fatan wannan hukuncin ya zama mafi Alkahirin hukunci da kika taba yankewa a rayuwarki bari naje zamuyi waya" ya kwasa da gudu kamar yaro ya fita, seda naga rufe qofar sa kafin na juyo kan Bashir muka hada baki ni ina cewa

"Fitar mun daga gida kafin nayi maka tijarar da baka taba zato ba dan daman saboda shi na daga maka qafa kar nayi abinda zan zubar da mutunchi na a gabansa"

Shi kuma yana cewa
"Aure zaki daura da wani namiji nan da sati daya Ma'u? Dagaske zaki iya rayuwa da wani bayan ni? Nasan kinyi ne dan ki baqantamun rai na yarda amma ki janye dan girman Allah.

Bana nufin duk abinda na fada subutar baki nayi da kishinki da yake damuna amma kema kinsan ba abinda nake nufi ba kenan" ya fada yana durqusawa kamar ze kamo qafafuna.

Juyawa nayi ina cewa
"Karka ja nayi abinda yayanka zasu tsaneni Bashir tunda sauran mutunchin juna a tsakanin mu ka fita, badai ni ka kira mara kamun kai ba? Ka jira na fito daga daki yau zan nuna maka qarshen rashin kamun kai kaji ko" na shige dakina ina tunanin me zan aikatawa Bashir da

Please Login or Register in order to submit comment