Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanaki ko” daga wannan maganar da banga abin zafi a cikinta ba se Bashir ya hau fada yana cewa

“Ni na gaji naga alama kin mayar dani wani yaronki kina zaune ina miki neman kudi ko? wato kina so na saka ido a Shago dan kar a cuceki amma kika kasa aminta ki damqamin gadonki a hannuna na kula miki dashi. Daga yau na dena zuwa, kinemo wanda ze ci gaba da kular miki da gurin” haka yai ta fadar maganganun sa ni dai na tsaya kawai ina Jin ikon Allah.

Kusan sati baya fitar dan haka na nemi Nasir qani na ya maye gurbinsa a gurin sannan ga Naziru qaninsa da daman yana zuwa na kwashe shi shida duk tsiyatakun da yake ji dasu na watsar dan ni yanzu hidimomin gabana sun ishe ni.

Beci gaba da zuwan ba amma dai ya dawo yana neman shiri dani, nima ban nuna masa komai ba muka ci gaba da sabgogi cikin hukuncin Allah se gashi ya sake samun aiki a Ma’aikatar haraji ta qasa reshen Gombe.

Aikin da Bashir ya sake samu ya tabbatar mun da cewa idan har yana dashi babu abinda baze yi ba, rayuwar mu se sambarka idan ka cire sabanin irin na yau da kullum da a kowanne gidan aure anan samun irinsa bani da wata matsala da Bashir.

Albashin sa nada tsoka dan haka a wannan karon na bashi shawara daya siyi gidan da muke ciki ya zama nasa, kai tsaye ya amince yace ze ringa biyana duk wata na yarda, da na gayawa Yah Abubakar a take ya karbe takaddun yace kuma A ringa tura kudin ta account dinsa har zuwa sanda ze biya sannan a chanza suna ya koma nasa abun nan kuwa ya qona ran Bashir ya ringa mita yana masifa nidai bance masa komai ba cikin qanwanin lokaci kuwa ya biya kudin tsaf aka chanza takaddu aka bashi ni kuma Yayan ya siyar mun da shagunansa guda biyu a wata babar plaza dan ina so na fara siyar da kayan yara Anty Suhaima zata ringa turomun su daga UK.

Bayan Farida na haifi na sakw haihuwar Da Namiji, kai da fata a wannan karon na kafe se Bashir ya sakamun sunan Baffana, dan gaske kuwa ya murzawa idon sa toka yace sedai na siyi ragon suna, dukda naji zafin abun amma haka na siyi manya manyan raguna guda biyu harda Bijimin Sa na qauri aka yankawa Abdallah na.

TUSHEN MATSALATA

Shigar Amirah Ajin Babbar Sakandire yazo mata da wani sabon tashen fitsara da rashin mutunchi. Amirah Kyakykyawar Yarinya ce Fara tas me gabaren girma a shekaru sha hudu qugunta ya bude qirjinta ya cika tazama budurwa sosai da bazaka yarda ba idan aka fada maka shekarunta.

Abinda ya fara hadani da ita shegen rawar kai da kule kulen samarinta dan har ta kai an fara zuwa sallama da ita. Zuwan saurayin na farko da kaina na fita na kora masa jawabin karya sake zuwa, hakan da akayi kuwa saboda rashin kunya har gurin Addah takai qarata wai ka korar mata saurayi. A sannan da Addahn tayi magana na ce mata

“Tunda kika bani ita ta zama yata dan haka zan lura da ita ne a matsayin uwarta idan kuma ba haka ba sedai ta dawo nan se tayi duk yanda take so amma muddin tana gabana Ba yanzu Amirah zata fara kula samari ba, se ta gama makaranta idan bata da burin ci gaba a sannan na yarda zamuyi mata aure”.

Jin da tayi nace ta koma ya sa ta haqura har da yiwa Amiran fadan da be kai zuci ba muka koma gida ashe bata deba ba, idan suka tafi Islamiyya seta tura sauran yara ta tafi warkajamin ta se lokacin tashi yayi su dawo wata rana Allah ya dawo da Bashir da wuri gida ya kamata a can farkon layi a motar saurayi suna zance har yana bata Ice cream a baki, ina Kitchen suka shigo tun daga get yana tamola da ita ashe an dade ana kai masa gulmar a unguwa yau Allah yasa ya gani har da daddare tana satar hanya ta fita hira ban sani ba.

A wannan karon ma dagewa yayi yace seta koma gida taje can kome zatayi a gaban Addahn amma zata lalace a nan ba ace a gidan sa ne, seda nayi ta bashi baki sannan itama naja mata kunne dakyau kafin ta shiga hankalinta.


Gashinan na yau dana gobe 😂😂🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 37

Takun kumi Bashir ya sakawa Amirah na daga gida se makaranta hakan ya taqaita duk wata firirita data fara dan yanzu ba inda take zuwa ba kuma wanda yake zuwa gurinta ban dai sani ba ko idan ta tafi gidansu tana yin hirar a can. wata rana nayi baquwa, maqociyata ce Maman Ahmad ta shigo muna zaune su Amirah suka shigo daga makaranta.

Uniform dinsu irin me guntun skirt din nan me da riga me dogon hannu se doguwar safa da dan qaramin hijabi dan haka sosai kayan suka bayyana qirar jikinta musamman ga wata tafiya data samu a kwanakin nan takeyi tana gantsaro qirji.

“Maman Aliyu wai qanwar kice wannan ma” Ta tambaye ni bayan da suka wuce ciki, se na kalleta ina murmushi nace
“Eh, qanwata ce me kika gani?”

“Qanwarki ciki daya ko kuma ta dangi?” Ta sake tambayata ba tareda ta bani amsa ba,

“”Gaskiya ba qanwata bace,qanwar Baban Ali ce diyar yayar mahaifiyarsa”

“Lallai Maman Aliyu se a barki, yanzu duk yayan danginsu qanana ki rasa wa zaki dakko se wannan qatuwar budurwar zaki ajiye a gida wai cousin din mijinki kina kallon Yarinya wanda be sani ba in ya kalleku ma se yace kishiyoyine wallahi nidai bazan iya ba, kema kuma tun dare ne miki ba kisan abinyi tam” Maman Ahmad din ta fada.

Se nayi murmushi nace “Girman jiki ne fa kawai Maman Ahmad ko sha shida bata cika ba ina ga idan ma Bashir kike tunani nasan babu abinda zeyi da ita ko aure zeyi baze nemi qaramar yarinya ba balle wannan da sam ba tsarar sa bace”

“Ai wallahi ta wuce kice mata yarinya dan duk abinda mace take taqama dashi gashi nan a jikinta dadin da dawa ga quruciya meze dami namiji da qananun shekarunta bayan kina kallo yanzu yayin yan sha shidan sukeyi, shiyasa randa kika aiko su da Amna ko palour ban bari sun shiga ba dan Abban Huzaifa yana nan shi daman ido a farar fata, tun wuri kisan nayi wallahi kafin kiji kidan Janaral a sama”.

A lokacin jin Maman Ahmad kawai nayi bawai na dauki abinda take fada da muhimmanci bane dan na yarda a zuciyata Bashir baze taba kallon Amirah a matsayin mace ba balle har yayi sha’awar auranta.

Yarinyar da banda kyara da tsangwama babu komai tsakaninsa da ita har haushi nakeji idan yayi mata wani abun, barar magi na bawa Amirah idan har na kuskura Bashir ya sani to ranar baze ci abincin ba saboda yanda yayi mata tambarin qazanta balle har takai ace ze aureta na tabbatar wannan ko a mafarki ba abu ne me yuwuwa ba.

Shigarta SS3 yasa ta qaro wani sabon tsagwaron rashin kunya da fitsara. Ganin ta takeyi kai daya dani dan yanzu idan na gaya mata magana ma se ta ga dama zata aikata, fita kuwa ko Bashir ze kasheta idan ta dawo setaje daman tuni ta sallama Islamiyya ta dena zuwa qarin daurin gindin data samu a gurin Addah harma da Dada kanta dan sunce data kammala makaranta aure zasuyi mata dan haka dole a barta ta fara tsayuwa da samari ta samu wanda zasu daidai ta a ciki.

Nima banqi ta tasu ba tunda har aure za’ayi mata ya kamata a barta ta farayin zancen dan haka koda Bashir yace sedai tabar masa gida ko kuma in zatayi zancen ta ta tafi gidan su se nace masa baza’ayi haka ba.

Dakyar na lallashe shi ya yarda sedai ya kafa mata sharadan kar ta kuskura ta mayar masa da gida centre tara samari duk randa ya ga sama da mutum biyu suna zuwa gurinta se ya mugun saba mata daga nan ta fitar da wanda take so a ciki ta sallami daya amma da yake me kunnen qashi ce kullum da wanda zata gayyato yazo gidan.

A cikin samarinta akwai wani Yaro Sadam, irin fitinannun yaran masu kudin nan ne. Tana bala’in sonsa musamman yanda yake mata barin kudi duk sanda zezo haka ze ciko ledoji niqi niqi da kayayyaki ya kawo mata sannan haka zebi su Aliyu da kudi idan sukaje suka gaida shi wani sa’in harni yake shiga ya gaisar,

yana da kirki amma idonsa a bude yake na kuma tabbatar ita kanta Amiran ba dagaske yake son ta ba duk yanda kuma naso na nisar da ita qarshe dukda ba kai tsaye ta fada ba se jin ta nayi tana cewa duk baqin cikin mutane seta auri Sadam da kowa ze ringa wani ce mata ba auranta zeyi ba, daga ranar na cire bakina a sabgar samarinta, Allah Allah nake ma ta qarasa makarantar ayi mata auran kowa ya huta.

Bazan taba manta wata rana da mukaje gidan Dada ba, akwai wani Lace me kyau da tsada da nayi mana nida Amiran da Amna harda Farida da sallah shi muka saka ranar mukaje.

Muna zaune kamar an matsi bakin Addah se cewa tayi “Baku ganku ba wallahi Abin sha’awa kamar wasu Uwar gida da Amarya”.

Ban kawo komai ba a raina nayi murmushi muka yi hirar mu muka gama, har mun tashi zamu tafi Addah take cemun

“Ni kuwa wata shawara nake nema Asma’u, kinga nida Nafi mu kenan shaqiqai da iyayen mu suka haifa, gara ita ma Allah ya bata yaya da yawa ni kuwa kin gansu nan biyu kamar kunnuwa.

Shine nayi wani tunani ina so ko bayan ranmu zumunchin Yarana da nata ya dore kinga ta hanyar Auratayya ne kadai hakan ze tabbata. Toh yanzu ina so na gabatatar mata da maganar cikin yaranta maza daya ya nemi Amirah ko ya kika gani?”

“Kai Amma kuwa kinyi tunani me kyau Addah idan abin ya yiwu kuma zakuji dadi wallahi Allah ya tabbatar da Alkahiri yasa zamu ga lokaci” na fada sak da zuciya daya dan dagaske naga kyan tunanin ta, Auran zumunchi yana da dadi idan yayi kyau.

A lokacin tunanina gaba daya kan Amiru ya tafi dan shine me shirin aure a sannan amma kuma sam basa shan inuwa daya da Amirah saboda rawar kanta.
“Idan Allah ya qulla abun haka zasu shirya su zauna tare” na raya a raina.

A haka muka ci gaba da lallabawa har Amirah ta fara rubuta Jarabawar fita daga sakandire lokacin ina da tsohon cikin yan biyuna.

Daman iya WAEC tayi, dan haka suna gamawa ta tattara kayan ta ta koma gidan Addah haka kawai ba tareda wani abu ba, nima ban takurata ba, nadai tambayeta ko wani abu aka yi mata tace Aa daga nan na barta ta tafi.

Ranar da na haifi yan biyu ranar Bashir ya samu aiki a wani Babban Oil company a Lagos. A tsakanin watanni uku Alhaji Qarami ya tura masa da Advert dinsu yace ya cike, yana rashin mutunchi da fadar maganganun sa dai ya cike din cikin ikon Allah kuma da yake se a sannan rabon sa ya tsaga se gashi suka gayyace shi Interview shine yanzu kwasam muna Asibitin sun aika masa da Email cewa sun dauke shi aiki.

Fadar irin farin ciki da murnar da muka shiga ma bata baki ce, Allah kenan me kyauta da qari a kuma sanda yaso. Lokaci daya ya bashi kyautar yara har biyu sannan ya qara masa da tukuicin Aiki me gwabi irin wanda ya dade yana fatan samu se gashi ya same shi a sanda be taba zato ba.

“Albarkar yan biyu kenan, yanzu Legas din zaka koma kenan? Daman ina so naje legas nima naga yanda take yanzu tunda dana zeje kaga na samu gidan zuwa” Addah ta fada cikin murna kamar ta taka rawa musamman jin yanda su Amiru suke ta zuzuta irin aikin da Bashir din ya samu da kuma Albashin da ze ringa kwasa a wata.

A ranar aka sallamo ni na koma gida, da Daddare Bashir ya shigo dakina, fuskarsa dauke da murmushin da na dade banga irinsa ba. Seda ya dakko yan biyu daga cikin gadonsu kafin ya dawo kusa dani ya zauna yana kallona yace

“Wane suna kike so a saka musu”
Se da na kama baki ina yar dariya nace
“Tofa, yaushe aka fara haka? To bana dai bani da kudin siyan raguna har hudu dan haka ka saka musu duk abinda kaga yayi maka”.

“Kina so ki ringa dawo da abinda ya rigada ya wuce, dagaske nakeyi, ki zabar musu sunan da kike so kin cancanci fiye da haka ai” ya fada yana kallona.

“Toh Daya dai a saka masa sunan Baba dayan kuma na bar maka zabi”

Da daddaya yayi musu huduba, seda ya gama ya miqo mun Hassan yace “Ga Ahmad” sannan ya bani Hussain shima yace “Muhammad Tukur”.

Sosai naji dadin karar da Bashir yayi mun ta saka sunan Alhaji Qarami dan kuwa ya cancanci sama da haka a gurin mu.

Wannan haihuwar dai nayita da qafar dama dan sosai Bashir yayi bajinta ya gwangwaje ni da zadaddun sururu na fitar suna haka yaran ma akwatunan su tsaf aka ciko da kaya, ga kuma kayan takwara da Alhaji Qarami ya jido mana abin dai se sam barka haka shagalin sunan da mukayi kansa bazakace haihuwa ta biyar bace tamkar sunan Aliyu da akayi shi lokacin ina cikin gata na a gidan wannan kuwa ya samu qarin tagomashin cigaban zamani.

Tuni Bashir ya kama aiki a Lagos bayan da ya dauki leave a tsohon gurin aikin sa a matsayin ze tafi qaro karatu saboda baka barin aiki kai tsaye har sekaga kamun ludayin wanda ka samu tukunna. Shi kadai ya tafi Lagos duk qarshen wata yake zuwa Gombe.

A cikin shekara daya da fara aikin Bashir rayuwa ta qara sauya mana sauyi irin na Alkahiri, ba qananun kudi yake karba a Albashin sa ba sannan ga Kasuwancin mu da Allah ya sakawa abin Albarka tuni mun sake bude branches guda biyu bayan na farkon a wasu unguwannin ga kuma harkar siyar da baqin mai daya kafa bayan daya fara sabon aikinsa ya zamana yana supplying daga kamfanin zuwa gombe ya rabawa yan sari abin dai se godiyar Allah kawai.

A shekarar ya biyawa Dada da Alhajin su Aikin Hajji suka tafi tare da shi kansa bayan sun dawo ya sake biyawa Addah da Anty Amina Babbar yayarsu harda Amiru sukaje Unarar Mauludi.

Bayan dawowar su Addah da sati daya sega Amirah ta dawo mun harda jakar kayanta bayan kusan shekara guda da barinta gidan, yanda sanda zata tafi ban hanata ba haka yanzu ma data dawo ban tambayeta dalili ba ban kuma chanza mata ba muka ci gaba da zaman mu kamar baya.

Abun daya fara hadamu bayan ta dawo wasu halayen data tsiro dasu, Duk lokacin da Bashir zezo gari yanda zanyi shiri nayi kitso dasu lalle haka Amirah ma zatayi tamkar matar gidan taci kwalliya itama ranar da ze dawo ta kame a palour.

Sannan a da idan har Bashir yana gida indai bashi ya zaunar dasu ba da daddare daga mun gama cin abinci zasu shige dakinsu tunda ko wanne daki na saka musu Tv idan ma kallo ne zasuyi acan wannan karon kuwa tun dawowar ta idan muna zaune itama zata nemi guri ta zauna ne babu ruwanta.

A ranar farko data fara zaman dakansa ya mata magana ta tashi hakan be hana washe gari ta sake zama ba har tana tsoka baki a cikin hirar da mukeyi nan ma yayi mata kaca kaca kafin aka samu sa’ida har ya tafi basu sake haduwa guri daya ba.

Wani rainin hankali data samu ma se ina waya da Bashir din zata zauna ta tasa ni a gaba tana kallo, idan nayi mata magana se tace mun wai

“Wallahi Anty soyayyar ku da Yaya tana bala’in burgeni shi yasa nake zama nayi kwas, Kai Allah nima ya bani miji irin yaya mu kwashi romon soyayya”.

Wani lokacin kuka tace “Dan Allah Anty ki ringa koyamun yanda zan mallake zuciyar mijin da zan aura nima na zama kamar ke a gurinsa ya ringa riritani irin yanda Yaya yake miki” idan ta fadi haka se nayi dariya nace

“Nidin har wani riritani Baban Ali yakeyi kenan, miji kuma ai banga kin dakko hanyar samun sa bama dan ni rabon da naga kinyi waya da wani a gidan nan ko anzo gurinki har na manta man Amirah anya lafiya?”

“Lafiya lau Anty, kedai ki taya ni da Addu’a kowa se yayi mammakin mijin da zan aura”.


Hutun da Bashir ya sake dawowa ta bullo da sabon salo, wannan karon se dare ya tsala irin 10-12 nan kawai zata sako qananun kaya wando skin tight ko Pencil skirt daze fito mata da surarta ta kai babu dankwali ta saki dogon gashin ta ta bazo turare ta fito tana miqe miqen iskanci irin ala dole daga bacci ta tashi har kuma ta kalle mu tace wani
“Au har yanzu Anty bakuyi bacci ba? Ruwa na tashi zan sha mun manta bamu shiga dashi dakin ba” sannan ta tafi tana rangwada ta bata lokaci a Kitchen kafin ta koma daki.

Na daya na biyu ranar a daren na same ta naci mata mutunchi musamman abinda ya qara tunzurani ganin yanda Bashir ya ringa binta da kallo har yana cemun wai me yasa na dena saka irin kayan nan, ban kuwa yi qasa a guiwa ba na bi bayanta nayi mata tatas tareda kashedin kar na qara ganinta a gaban Bashir ba tareda hijabi ba.

Washe gari da safe yace su shirya ya kaisu gidan Dada gaba daya harda Yan Biyu zasu tafi, muna tsaye a palour suna jiran Amirah se gata ta fito da wata fitted gown ta Atamfa ta kamata tsam kamar zata yage idan tayi numfashi me kyau se dan mayafi data rataya a kafada.

Ina kallon yanda Bashir yakalleta kafin ta qaraso inda muke nace ta juya ta canzo kaya ina jiran naji ya dora nasa fadan se cewa yayi ta wuce su tafi baya son bata lokaci ya tasa su gaba yana baya suka barni tsaye kamar bishiyar da aka dasa.

Haka na kusan wuni ina saka da warwara ni kadai akan sababbin halayen na Amirah da na kasa fassara ma’anarsu, shin da wata manufa takeyinsu ko kuwa haka kawai? Idan ma yin kanta ne kawai shi kuma Bashir fa da baya ganin laifin abinda take aikatawar fa?

Gaskiya bazan zuba ido ba saboda zuciya bata da qashi, kodan gudun afmuwar barna dole na taka mata birki tunda Bashir ba muharramin ta bane shedan yana iya qawata masa ita ya kuma tunzura zuciyarsa ga aikata abinda be kamata dukda na yarda da Bashir ba kuma na masa tunanin wani abu makamancin haka amma fa zuciya bata da qashi.

Allah sarki ni a sannan sam zancen ace wata aba me kama da soyayya tsakanin Bashir da Amirah be taba zuwar mun ba kawai ina daukar abin da takeyi a matsayin tashen fitsarar dake kanta daga irin kalamanta a yanzu kuka nake ganin kamar aure take so dukda ina mamakin dalilin da kwata kwata yanzu samarinta babu me zuwa ko waya ta dena yi dasu se na mayar da hankali na cikin yayyena marasa aure na fara qoqarin samo mata wanda zasu daidaita dashi.

Abinda ya raba mana gari da Amirah kwata kwata na sallama ta ta barmun gida gaba daya a wani zuwa da Bashir yayi mana, a lokacin dama na fara gajiya da hakayenta saboda kullum sabon salon da zata bullo mun dashi. Gaba daya ta gama raina ni dana rasa menene musabbabin rainin dan har takai Amirah ta shiga dakina ta bude cikin kayana ta dauki abinda take so ba tareda ta tambayeni ba sedai kawai na ga abu a jikinta duk fada da masifar da zanyi mata kuwa baze hana gobe ta sakw yi ba dukda haka naci gaba da haquri nake zaune da ita saboda a yanzu idan nayiwa Bashir qorafi baya cewa komai sabanin da da qiris yake jira tayi abu ya samu nayi.

Abinda ya faru da yasa na tilasta mata barin gidan kuwa shine zuwan da Bashir yayi qarshen wata. Fasalin ginin gidan mu corridor ne guda biyu hagu da dama ko wanne da dakuna biyu daya na kallon daya a ciki dan haka na dauki daya nawa dana Bashir dayan kuma ya zama dakin su Amirah, Amna da Farida daya kuma na yara maza.

Bayan da Bashir ya gama weekend dinsa ranar litinin ya koma Lagos a ranar saboda tsabar gajiyar dana kwasa a hannunsa Se Amirah ce ta hadawa yara abin tafiya makaranta suka bi Amiru da ze kai Bashir Airport ya sauke su a makarantar.

Da misalin sha biyu na rana na fito daga dakin Bashir bayan na gama ramuwar bacci gidan shiru se Amirah kadai a zaune a palour tana sana’arta ta kallon Indian series yan biyu suna gidan Dada an kaisu yaye kusan sati biyu kenan ba’a dawo dasu ba. Dagowa tayi da murmushi tana kallona tace

“Sannu Anty se yanzu kika tashi”
“Yawwa Amirah sannu da gida, me kuka rage yunwa nakeji wallahi” na fada ina zama a gefenta.
“Na dai feraye miki dankali bari na soya” ta fada tana miqewa, mintina kadan ta soyo dankalin harda kwai ta kawo mun nasa ta hado mun shayi na zauna na fara ci”.

“Ai dole kisha Baccin Gajiya Anty irin wannan gurza da kika sha a hannun Yaya jiya kai, gaskiya Anty dole ki shirya ni idan zanyi aure yanda nima zan rikita shi ya ringa sambatu irin na Yaya...”

Kwarewar da nayi da shayin dana kurba tsabar kidimar jin magangan ta suka sa tayi shiru ta miqo mun ruwa tana yi mun sannu. Kallonta kawai na ringayi zuciyata tana luguden duka a raina ina ta maimaita “Hasbunallahu wani’imal wakeel”.

“Dagaske Amirah taji mu’amalar mu da Bashir? Tun yaushe hakan ya fara sannan ita kadaice ko har sauran yaran ma duk suna ji?” Tambayoyin da nayiwa kaina kenan dana rasa me bani amsar su, tabbas wannan dalilin shine silar rainin da naga Amirah tayi mun shi a yanzu har ma da Bashir din kansa ashe a banza take kallon mu amma ta ina ko ta yaya taji? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.

Ganin da tayi na dena tarin ba tareda damuwa ko tunanin komai ba taci gaba da magana tana cewa
“Wallahi Anty kum....”

“Rufe mun baki Amirah” na fada cikin tsananin bacin ran da fuskata da muryata suka nuna kafin na ci gaba da cewa

“Ashe baki da hankali ban sani ba? Saboda tsabar rashin mutunchi da rashin kunya har ki iya tsayawa kina maimaita wadannan maganganun a gaba na sa’arki na zama, wallahi se na yi mugun saba miki” na qarasa ina huci bayan dana ture kayan abincin gaba na dan gaba daya komai ya fice daga raina ita kuma sum sum ta tashi daga gurin ta shige dakinsu.

Wannan abun kunya har ina, tabbas Bashir irin mazan da basa iya rufe bakinsu ne a lokacin da yake mu’amalar aure amma ban dauka ihun nasa har yana karade gida da Amirah zata iya jiyo wa ba musamman idan ka duba tazarar da ke tsakanin dakin sa da inda nasu dakin yake dama dai a dakina ne ana jiyo duk motsin da akeyi a dakin Bashir.

Haka na wuni cikin rashin sukunin zuciya dan Amirah tuni ta fice ta tafi gidan Addah ina nan sukuku har yara suka taso daga makaranta su kansu seda suka gane bana jin dadi.

Da magriba muna Kitchen da Amna ina girki tana dan tayani da wasu abubuwan, tun tuni nake saqawa a zuciyata na tuntubeta da dabara naji ko suma suna jin wani abun ina ta fargabar amsar da zan samu tunda dai daki daya suke kwana, me nauyin bacci ma taji bare amma da sam bata da nauyin bacci amma kuma ya zama dole na tambayeta kodan nasan matakin da zan dauka saboda tarbiyyar su, ina ta hiqilo akai kar naje tufka nakeyi ta baya tana warwarewa.

Gundumbala nayi nace “Amnah, ni

Please Login or Register in order to submit comment