Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayan ciki a qasa.

Kayane kala hudu, Atamfa biyu se Lace daya da Brocade material shima daya duk an yi musu dinkuna masu kyau. Seda ta ware ko wanne dukda a goge suke tas ta hargitsa kafin ta watsar qasa tana cewa

"Ina nawa naga duk wasu riguna fici fici babu wadda zatamun a ciki"

"To daman an ce miki da naki a ciki ne kayan Matata ne kema ki siya da kudinki mana ai kina dasu ko ni aka ce na miki kayan sallah?" Ya fada kansa tsaye.

Amirah kanta da take murna tana daddaga kayan dan babu wanda beyi kyai ba kana kallo kuma kasan masu tsada ne seta tsaya tana kallonsa jin abinda ya fada tace

"Yaya Addah ce fa kake gaya mata haka"
Harara ya maka mata yana cewa
"Gobe Solomon zezo ya kaiki ki siya takalmi da mayafi zan tura miki kudin sannan na manta ban tambayeki ba ko zakije sallah Gombe ne dan ni bazan je ba"

"Uwarka Nafi ita kake wulaqantawa Bashir bani ba shege wanda be gaji Arziqi ba. Ni zaka kalla kayiwa gori to wallahi bazanyi da kai ba da uwarka zanyi dan ita ce daidai dani se inji idan ma ita ta baka damar ka ringa wulaqanta ni. Idan ma banda lalacewa Bashir in haifar maka matar ka aura amma baka da wadda ka raina a duniya sama dani ko? Nagode.

Ke kuma kina zaune yana qarewa uwarki tana di ai Shikenan gaki gashi nan kuci kanku" Addah ta fada tana miqewa, har tayi gaba kuma ta dawo tana cewa

"Babu Gomben da zamuje uwar me muka manto acan da zamu koma dakkowa?"

Shidai be kulata ba ya kalli Amirah yana jiran tata amsar itama a sanyaye tace
"Anan zamuyi sallah"
"Shikenan, goben da wuri zezo daganan se ku biya kuyi cefanen abincin sallah"

Ya dauki wayarsa yayi danne danne kafin ya miqe ya shige daki yana cewa "gashi nan idan kunje ze kaiki inda ake siyar da Ready made ki dauki 50k ki siya mata kala biyu ai zasu isa".

Wayarta da take gefen ta ce tayi qara alamar shigowar saqo ta janyo ta duba, dubu dari da Hamsin ya tura mata tayi ihun murna daidai sanda Addah ta fito daga dakin da take da waya a kunne tana cewa

"To qarya zan miki Nafi? Zagina yayi ta uwa ta uba ko ince zagin mu nida ke tunda iyayen mu daya har yana cewa idan na isa na danne shi ma kwata mana" se tayi shitu ta zauna a kujera kafin tace gaba da cewa

"Oho dai Idan ma ke kike karanta masa cewar ya wulaqanta ni to dani dake dukka ya wulaqanta aikin banza mana, daman nasan ai ba son zuwana nan kike ba kina baqin ciki nazo naci arziqi ke kina can to wallahi naga guri idan ma zaki barshi ya sake hannu ya ringa yin wadaqar da yakeyi da a gidan sa gara ki bati dan ba dawowa zanyi ba nida Gombe seda ziyara muzo a jirgi mu dawo abin mu".

"Haba Addah, a yaushe ya zageki dan Allah yanzu kin hadashi da Dada so kike ta kira tayi masa fada bayan ga kudi fa ya turamun yace na siya miki kayan"

"To qarya nayi kenan dan ubanki nawa ya turo?" Addah ta zaburo mata, seda ta kalli qofar dakin kafin tayi qasa da murya tace

"Dubu hamsin ce yace na dauki talatin kudin mayafi da takalmi naki Ashirin".

"Hamsin din banza da wofi uwar me za'a siya da dubu hamsin a zamanin nan, su desina takalmi da mayafin da mata suke sawa duk a ciki zaki siya" Addah ta fada cikin daga murya.

Alamar tayi shiru karya jiyo Amirah take mata amma ina qara daga muryarta take yi abinta se Amirah ta narke fuska kamar zatayi kuka tace

"To ke Addah Ina ruwan ki ni hakan daya bani ma na gode dan ba abinda zan suya duk ina da mayafai kalar da zata shiga da kayan gobense muje a siyo miki naki in be isa bama sena cika miki a nawa" ta fada qasa qasa danbata so Bashir ya jiyo su ballantana asirin cuwa cuwar da take shirin yi ya to nu.

Bashir kuwa yana shiga bandaki ya shiga yayi uzurin sa da shirin kwanciya bacci yana fitowa ya tarar da Missed calls din Dada biyu dan haka ya dauki wayar yabi bayan kiran.

"Bashir me yasa akullum baka da aiki sena son tayar mun da hankali ne ace kullum ta Allah seka takali Addah se kace wata sa'arka bayan kasan qarshe duk akaina abin ze qare" Dada ta fada bayan daya gaishe ta. Dafa kansa yayi ya zauna akan gado yace

"To yanzu kuma me tace na mata? Maganar kayan sallah cefa mukayi kuma ni tsokanarta nayi da nace bazan mata ba amma gashi can ai na bada kudin a siya mata"

"Saboda tsarar wasanka ce dole ka ringa tsokanarta ai, kuma zanin sallah ai ba yau ka fara mata ba balle kace mantawa kayi karkuma ka manta yanzu fa matsayi biyu take dashi a gurinka ko baka mata a komai ba ka mata na surukuta ai sannan saboda wulaqanci se ana jini sallah zaka bada kudin a siya waye ze dinka mata toh?"

"Nifa Dada ba dan tana sirikata nake mata dinki ba kawai ra'ayi nayi dan in haka ne Goggon Ma'u ko qualle ban taba siya na kai mata ba kuma baki taba cemun nayi mata dan tana sirikata ba, nidai na bada kudin duk ma yanda zasuyi suyi ni ba damuwata bace tun farko ma waya gayyato ta tazo duk gashi nan ita ba taimakon mutane take da komai ba se qara hura musu matsaloli"

"Allah ya rufa asiri toh, nidai dan Allah ka dena biye mata kuna sa'insa kodan darajar yarta in ma baka dubi ni yayata bace, naji ku shiru da alama dai bana bazaku zo ba kenan?"

"Eh se zuwa bayan sallah in sha Allah ni zanzo, yaran dai zasu taho tareda Mamansu nasan zasu zo muku nan da sallah" ya bata amsa,

"Uhm, ni wai ya kuke ciki ne haryanzu Bashir ba'a samu daidaito bane? Ni wallahi gaba daya ma nauyi yasa na kasa tunkarar kowa nayi maganar nan dashi. Jiya mun hadu da Hajiya Anjin a gidan wata mutuwa haka ta ringa sakar mun habaici mutane na tayata nidai qarshe kasa zama nayi na taho wallahi gaba daya gari kowa laifin mu ake gani wai mun aura maka yar uwarmu mun saka ka saki uwar Yayanka haka kawai bayan ni baka yi shawara dani sanda ka aikata abinka ba.

Dan Allah Bashir ka maida yarinyar nan dakinta dandai kasan bazaka taba maida kamarta ba, idan ma wani surkullen aka muku na saka anata yi maka sauka da addu'oi Allah ya karya shi ya daidaita tsakanin ku" Dadata fada cikin jimami.

"Toh Amin ina ta qoqarin haka amma Ma'un yanzu ba irin wadda kika sani ada bace, gaba daya ta canza kamar wadda aka zuga akaina. Na ina ta addu'a Allah ya shawo mun kanta"

"Toh Allah ya amince, ai ka gani bana ka ja mana, zanin sallar da ake mana bamu samu ba Allah dai ya rufa asiri"

Tsabar takaici sallama kawai ya mata ya kashe wayar, ba Addah ce kadai me matsala ba ita kanta Dadan se a hankali kawai na Addah ne ya fito fili idan ba haka ba ana maganaryanda za'ayi a daidaita ita damuwarta ma ta zanin sallah da bata samu bane Toh Allah ya rufa asiri.

Shi duk meyasa da be gane Baba kadai yake son sa da Alkahiri ba shi kadai yake hango masa illar da rashin Ma'u a tareda shi zata haifar masa duk sauran abin da suke samu ta dalilin ta kawai shine a gabansu ai shikenan yanzu da ta barsu kowa seya ji a jikinsa ai daga shi har su kowa ze gane amfaninta da rashin amfanin ta.

Washe gari tun goma yayi wanka ya shirya dukda jirgin qarfe daya zasu bi, sha daya da rabi ya fito daga dakinsa, gidan shiru dan Amirah sun tafi kasuwaga ko ina kaca kaca yanda yake tun jiya ko arziqin shara be samu ba daidai da bawon gyadar da taci jiya yana gurin basu kwashe ba.

Tsaki yaja ya leqa dakin yaran sun tattare komai hatta Bedsheets dinsu da pillow case sun cire se tsurar katifu akan gadajen na su ya janyo qofar ya fito, bashi a tabbacin ta fita da muqulli dan haka daya kulle gidan ya nemi wani dan guri ya ajiye muqullin ya zaro wayarsa ya shiga kiran wayar Amiraj dan ya gaya mata daidai sanda wata shegiyar Sienna ta shigo layin kai tsaya ta wuce qofar gidan Ma'u ta faka.

Irin masu baqin kayan nan da yake gani da wannan mutumin ne daya ya fito yaje ya kwankwasa qofar gidan, yana tsayen dai se gani yayi suna fito da akwatunan su ana sakawa a mota, a fusace ya qarasa qofar gidan.

Yana zuwa Suna fitowa dan an gama zuba kaya, yaran suka gaishe shi gaba daya be amsa ba ya matsa kusa da qofa inda yake jiyo sallamar Ma'u da Baba Harira alamar suna fitowa seya matsa yana sake hade fuska tareda ayyano abinda ze gaya mata idan ta fito din.

ASMA'U

Da wuri muka gama shiryawa dan kafin goma mun hade komai munyi wanka se dan abinda baza'a rasa ba. Tun sassafe daman mukayi magana da Yusuf ya gaya mun zuwa sha daya ze turo wanda ze kai mu Airport dan haka shadaya da mintina ina jin an buga qofa nasan ya iso, a shirye muke dan haka nace su fara fita da kayan na qarasa sallamar Baba Harira sannan na kira mata Taxi da zata kaita gida dan Anty bata nan itama bana a Zamfara tayi Azumi.

Muna fitowa na kalli yaran da sukayi cirko cirko a tsaye bayan gashi nan an bude musu qofar motar nace

"Me kuke jira kuka tsaya kamar wasu sojojine ku shiga mota in ba so kuke mu makara ba" fada ina kallon su se a sannan na lura da Bashir daya hade girar sama data qasa yana gadin qofa, da yar fara'a na kalle shinace

"Aa Baban Ali ina kwana? Ai da baka wahalar da kanka ka fito ba nasan dai kunyi sallama ai kafin su fito ko??"

"Motar waye wannan zaku shiga" ya fada cikin dakiya kamar me magana da wata yar sa, ko a jikina, jakata na miqawa Amnah ina Cewa

"Mun tafi se Allah ya dawo damu" na kama qofa zan shige ina sake cewa
"Kwa taho mudai munyi gaba" dan har sannan Aliyu da Abdallah suna qasa su basu shiga motar ba.

"Magana fa nake miki Ma'u zaki shige mota ki barni, kai dallah ku fito waje"

"Aa to meye matsalarka da sanin motar waye kuma? Ku kuma malamai idan bazaku jeba ku cire kayan ku tsabar iskanci ana muku magana kun tsaya kuna kallon mutane"

"Yayana bazasu shiga motar ko wanne dan iska ba ku sakko" ya fada a harzuqe yana janyo Farida datafi kusa dashi.

"Bana son abinda kake mun ka ringa takalata a gaban yara muna abinda be kamata ba, ka rabu dasu mu tafi koda yake shikenan" na juya ina kallonsu nace

"Ku sauka, malam bude boot za'a cire kaya" na fada cikin hade rai. Baba Harira da har me Taci dinta ya iso ta saka kayanta ta dawo da sauri tana cewa

"Aa mene haka kuma, Alhaji Bashir ba girman ka bane. Kayi haquri kaga motar ka qarama ce idanma kace zaka kaisu bazata kwashe ku ba a takure zaku tafi wannan kuma tana da yalwa sosai ai. Be kamata ku ringa irin wannan abun a gaban yara ba dan Allah ga mutane duk ana kallon ku"

"Shikenan kinci darajar ta wallahi kuje amma wannan ya zama na qarshe da zaki sake daukar mun yara a motar wani banza" yaja kwafa ya juya. Ko kallon iskar daya kwashe shi ban sakeyi ba wayata ma na ciro ina danne danne na.

Ina jin Baba Harira na magana itama naqi kulata suna gama shiga Driver yaja mukayi gaba abin mu, ta gefen ido na hango yanda yake zabga wa motar harara se nayi tsaki a fili nace

"Iska na wahalar da me kayan kara".

Mun sauka Gombe lafiya lau, daga gidan mu aka zo daukar mu. A cikin dakunan mu na yammatanci da yanzu babu kowa guda dayane Yaya Suwaiba da Mijinta ya mutu ta dawo gida take ciki nan aka gyaramun daya nima na shiga na zauna.

Wani iri na ringaji a zuciyata, ada kai tsaye gidan mijina nake sauka idan munzo se munkwana mun huta kafin nake zuwa gida mu gaisa amma yanzu wai har daki na samu na zawarci Allah kenan.

Saboda rashin ganin wata a daren ranar dole washe gari aka tashi da cikon Azumi na talatin kenan. Har gida aka samo mana me lalle da kitso tazo akayi mana ga yan sannu da zuwa qannena da yayyena suna ta zuwa abin dariya wai duk wadda tazo barka take mun na barin gidan Bashir kamar wadda aka sako daga kurkuku a maimakon su tayani jimami Yah Fati ce kadai ta nuna Alhini da rashin jin dadinta.

Nidai nasan banyi rayuwar qunci a gidan Bashir da har za'a ringa murna haka da rabuwar mu ba.
A daren aka kawo kayan su Jafar na gurin Yusuf, shadda ce yar ubansu kala biyu daya doguwa daya me babbar riga ko wanne da hula da takalmi qafa daya harda Agogo se dogayen riguna Abaya masu kyau na Amnah da Farida.

A daren na kira wayarsa amma a kashe, se na tura masa da saqo kawai nasan in yagani ko zuwa safiya ze kirani.

Washe gari aka sallace, munje sallar Idi mun dawo gurin qarfe sha biyu na saka Aliyu ya hada kan qannensa suka tafi gidan su Bashir suka gaishe su, se bayan Azahar suka dawo tareda Naziru da Yaran Amiru dukkansu da yake suka sunzo sallah harda Dan gidan Fainusa da alama shima bana an kawo mata shi kenan.

Har cikin gida Naziru ya shigo muka gaisa ina tayi masa tsiyar ko a waya ya dena nemana yanzu laifin me mukayi masa.

"Wallahi Anty bansan me zan ce Idan na kiraki ba, Yaya Bashir ya bata komai gaba daya ya saka kunyarki mukeji ko yanzu abinda Yaya Amiru ya gama fada kenan yake Lagos kwanaki amma ya kasa zuwa ku gaisa dan besan da wanne ido ze kalle ki ba"

"Haba Naziru, dan Bashir ya hada mu se kum ace dalilinsa zamu rabu, ni ban qullaci kowa a cikin ku ba wallahi in ma banda abinka shi daya aikata muka ci gaba da gaisawa muna zaune guri daya se ku da bakusan sanda akayi bane zaku ringa ji masa nauyi ai ba'a haka sedai idan kuma daman neman hanya kuke kaga ae ku yanke alaqa dani bawai dan abinda ya faru tsakanina da Bashir ba"

"Haba dai Anty alaqa kuma ai yanzu ma muka qullata kin taba ganin da ya sake uwa ai baze yuwuba, ni yanzu tsoron da nake ma kar ace za'a hanani Yayana ya jawo mun dan dai nasan baki manta alqawarin mu ba" ya fada yana sosa kai.

Dariya nayi sosai ina cewa
"Oh ni Baba Naziru wai kai dagaske kakeyi me zakayi da wannan kwailar ga manyan yammata nan a gari? Nida har ina maka kamun wata ma ashe kai kana nan dagaske kake ashe"

Kallon Amnah data tura baki gaba yayi yace
"Haba Anty wane irin wasa wallahi dagaske nake ni sedai idan kuma baza'abani ba in cire rai amma duk wani lissafina ai kena kinsani Anty tsokana ta kawai kikeyi"

"Babu wanda ze hanaka Naziru indai yarinya ta amince mu kam yan shan biki ne ko Amnah" Zainab data shigo ta tsokaneta ai kuwa ta kwasa da sauri ta bar gurin tana boye fuska.

"Yawwa Anty Zainab inaga qafarki zan kama ki tayani campain tunda naga Anty wasa ta dauki abun, nida ina can na saki baki wai ina da uwa a bakin murhu ashe ita sagegeduwa zatayi mun gara da Allah yasa na sani da wuri" Dariya mukayi gaba daya muka ci gaba da hira shidai jaddadamun yake fa wallahi Yana son Amnah kuma tun tana yarinya damanya gayamun bashida mata se ita nace toh Allahya tabbatar mana da Alkahiri.

Seda aka kira La'asar yayi mana sallama bayan ya rabawa yaran barka da sallah dubu daddaya ina ta masa maganar yayi yawa yayi gana yana cewa

"Bamu samu zama bafa Anty akwai labarai inaga da daddare zan dawo tuna dai an yafe mana laifi"

"Allah ya shiryaka Baba Naziru, ka gaida su Baba zuwa gobe zan shigo nima mu gaisa" munayi sallama ya wuce.

Seda aka kwana uku da sallah kafin ranar da yamma na shirya zuwa gaida Alhajin su Bashir. Ko babu komai darajar qaunar da yake nunamun ya cancanci naje, da La’asar na kwashi Khadija da Alawiyya muka tafi dan ranar gidan mu a cike yake maqil da Jama’a ranar ake zuwa wunin sallah wasu ma sunzo kenan tunda saura kwana uku a fara bikin su Bilal.

Da qafa muka tafi muna zuwa kan kwana daidai gidan su Ibbah na kalli gidan ina cewa
“Oh Allah sarki rayuwa ko ina Ibbah yake oho dan nafi shekara goma sha rabona dana ganshi”

“Wato yanzu har tuno da tsofaffin samarinki kikeyi saboda kin samu yanci, yana nan kamar ma acikin gidan yake zama da yayi aure kin san Mamansu ta rasu da dadewa da ya koma Ingila daga baya ya sake dawowa nan” Alawiyya ta bani amsa.

Seda na harareta ina gyara zaman Gyalen kaina daya zame nace “ke se ana zancen arziqi se ki sako na tsiya meye kuma wasu tsofaffin samari mtsw” haka muka qarasa gidan su Bashir tun daga waje muke jiyo hayaniyar Jama’ar gidan da alama suma yau suka zo ga yaransu nan nata wasa a Gareji muna shiga suka hau gaishe mu.

A tare muka rangada sallama kafin muka cire takalman mu muka shiga Palour Dada inda suke zaune gaba daya suna hirar tun daga kan Anty Amina har zuwa Sadiya autarsu a mata suna ganin mu sukayi shiru kamar ruwa ya cinye su.

Afiya ce tayi qarfin halin farayi mana maraba se Samirah da Sadiya da suke kan Three sitter suka miqe suna ce mana ga guri mu zauna muka samu kujera kuwa muka harde aka shiga gaisawa ina lura da yanda suke qaremun kallo kamar masu neman wani abu a jikina sena sake gyara zamana ta yanda zasuga dinkin doguwar rigar Lashin dana saka ga qafata tasha qunshi haka hannaye na zobuna harda na aro duk na hada na saka.

“Yanzu fa muke cewa zamu shigo gidan ai mu gaisa se gaku kunzo” Anty Amina ta fada tana dariyar yaqe, ban tanka ta ba nayi murmushi ina duba wayata da saqo ya shigo, Yusuf ne yana gayamun sun sauka a Abuja yanzu nayi masa sannu da zuwa da bangajiya.

“Su Asma’u ne lale maraba sannunku da zuwa” Muryar Dada ta katseni se na dago na kalleta yanda take bude mana haqora haka kawai na saki murmushi wanda na zallar takaici ne. Daga inda nake na dan zamo kadan na gaisheta, yanda kasan zata goyani haka ta ringa amsawa ta juya ta koma Kitchen ta kwalawa Fainusa kira se gata ta fito da qaron Try an shaqe shi da kayan lemo ga Kwanon Dambun nama dana Alkaki duka aka hado mana.

“Baba yana ciki ne naga bamu ganshi a qofar gida ba” na fada ina kallon Sadiyah, se Dada daketa faman musha ruwa tayi saurin Amsawa da cewa

“Yana nan, yau din beji dadi bane shiyasa ya zauna a ciki kinsan iskar maraice yanzu seta tado masa da zazzabi. Kusha ruwa bari nayi masa magana” ta juya ta fita.

Juyawa nayi na kalli Alawa da Khadija da suketa muzurai karma Khadija taji labari nace
“Kusha ruwa mana Khadija”

“Alhamdulillahi seda muka qoshi kafin muka fito daga gida” Alawiyyan ta fada tana miqewa, se Khadija ta tashi itama tana cewa

“Muje Anty ku gaisa tunda gurinsa muka zo lokaci yana tafiya”

“Au gurinsa kukazo to ai shikenan, ina namu yayan suke se a turo mana su suzo gurin iyayansu” Samirah da tun asali daman suna yar tsama tsakaninta da Khadija saboda sun taba hada saurayi qarshe kuma ba wadda ta aure shi a cikinsu ta fada, se kuwa ta waiwaya ta galla mata harara kafin tayi magana nayi saurin moqewa ina cewa

“Muje, Anty Amina se anjiman ku Allah bamu Alkahiri”

“Toh Ma’u ku gaida gida se mun shigo daman wallahi bari mukayi mu hadu tare gaba dayan mu se muzo miki jaje kiyi haquri” Anty Amina ta fada tana taka mana.

Alawiyya da har takai qofa ta juyo tace
“Ku mata jaje kuma meya sameki Ma’u da za’azo miki jaje? Indai zancen rabuwarta da Bashir ce kuyi zamanku wallahi ba se kunzo ba abu wata da watanni ai tuni muka gama karbar yan taya murnar base kunzo bama mu yafe muku wallahi”

Gaba daya suka raka mu da ido ina jiyo Fainusa tana cewa
“Kema Anty meye haka dan Allah kina kallon yanda suka shigo suna kallon mutane kamar wasu kashi ai gashi nan kinja sun gayawa mutane magana mtsw”

“Dallah gafara can an jawo din seki dakeni ai nasan kinji haushi” Amina ta fada tana harararta.

“Gaskiya dai Yaya Bashir ya luza ji yanda mata tayi luwai abinta zawarci ya karbeta ba irin wasu ba” Suwaiba data fi kowa iskanci ta fada nan da nan suka fara rigima da Fainusa dan dai ita kadai ce Bazawara a gurin kuma kowa yasan da ita take tunda daman sun ba mudai muka shige Palour Alhajin Su Bashir inda Dada harda qara shimfida mana qatuwar Dadduma akan Carpet din dayake gurin.

Cikin girmamawa muka gaishe shi gaba daya.
“Ki gafarce ni Asma’u wallahi nauyi da kunya ta saka na kasa kiran ki, Bashir be kyautawa kansa ba amma babu komai Allah yasa hakan shiya fiye muku Alkahiri” Baban ya fada daga kwance da alama jikin ya takura masa da gaske.

“Babu komai Baba, nima ai nayi laifi da ban kiraka na gaishe ka ba kayi haquri”

“Aa karki kuma ai ke kika cancanci ban haquri,ki ci gaba da haqurin dai in sha Allahu zaki dauke shi a gaba. Ina Alhaji Abdu? Dazu da safe yazo ai ya kawo mun magani kin gansu can wai shi likita ne saboda jiya na gaya masa ina ciwon kai da daddare da zasu tafi” ya fada yana nuna mun paracetamol din da yake gefensa.

“Au wai daman kai ze kawo wa? Yazo yana ta tambayata wai maganin ciwon kai na zatama shi ze sha na bashi a she nan yayiwo”

“Nan yazo ai ya jima ma, amma fa nayi nayi yaci abinci yaqi wai Mami ta hana su kwadayi banda abin Abdullahi nan ai gidan su ubansa ne ko yana inda yafi nan ne ko da yake qila ba’a fayyace masa ba” Dada ta fada da yar dariyarta, sena daga kai na kalleta kawai nayi murmushi

“Yaushe zaku wuce saboda aiki? Koda yake akwai bikin Su Bilalu na manta se an qare zaku koma kenan” Baba ya sake fada ba tareda yabi takan zancen Dadan ba.

“Eh se an gama biki Baba, daman sati biyu zamuyi gaba daya”
“Toh Allah ya taimaka yasa ayi a sa’a. Kema Allah ubangiji ya fito miki da Miji na gari kiyi auranki kinji”

“Amin Baba, Ai Allah ma ya kawo mata sedai ayi Addu’ar fatan Alkahiri kuma” Alawiyya tayi caraf ta amsa.

“Kai madallah amma naji dadi ubangiji ya tabbatar da Alkahiri yasa zamu gani kai nayi murna sosai, Nafi kinji abin Allah ko Baba ya fada har yana miqewa zaune.Dada da tun fara maganar Alawiyya tayi kasaqe tana kallon ta tace

“Uhm” tareda yaqen dole,har muka gama hirar da zamuyi Baba nata sa mana Albarka muka miqe. Jakata na zuge na ciro bandir din yan dari biyu sababbi dana tanada na ajiye a gabansa ina cewa

“Gashi Baba babu yawa a siyi Goro, an jima na turo su su duba jikin naka”
“Kai kai Haba Asma’u dauke kudinki kinji ai gaisuwar da kika zo mukayi ma tafi komai Nagode Allah yayi miki albarka” ya fada yana turomun kudin se na nufi qofa ina cewa

“Dada se anjiman ku toh”. Seda Alawiyya da Khadija ko wacce ta qara aje masa dubu biyar biyar kafin muka kama hanyar gida. Har Get Dada da duk jikinta yayi sanyi ta rakamu kafin ta juya,

Please Login or Register in order to submit comment