Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shima Bashir daya dawo yaganta a yanda ya fita ya barta kwafa kawai yayi ya sake wanka ya fice be kuma dawo gidan ba se bayan data kwanta.

ASMA'U
Da safe ganin harna shirya yara basu shigo yasa nayi tunanin sun koma cin abinci a gidan su kenan, toh itama Amna ta huta, a tsatstsaye na karya dan ina sauri mukayi sallama da Amnah ina fitowa na gansu cirko cirko a qofar gidansu fuskar Aliyu dana kalla ta tabbatar mun wani abu ya faru.

A gabansu na tsaya da mota na sauke glass, dukkan su suka gaishe ni na tambaye su lafiya Jafar na shirin magana Aliyu ya galla masa harara yace mun babu komai. Sena tabe baki nace "toh yayi, ina Abbin naku kuke tsaye anan kun kusa makara fa" ina rufe baki na hango an bude qofar, nasan Bashir ne dan haka nayi musu sallama kawai na wuce haka nan bana son haduwa dashi kuma.

Gurin qarfe goma ina zaune a office wayata tayi qara, ta true caller naga sunan me kiran YUSUF IBRAHIM WUNTI ina gani na gane Yusuf ne dan haka na daga wayar na kara a kunnena tareda yin sallama.

"Barka da rana Hajia" Yusuf ya fada daga daya bangaren sena amsa da cewa

"Barka dai Excellency"
"Ashe baki manta sunan ba" ya fada yana dariya sena mayar masa da amsa da cewa
"Haba dai ya za'ayi na manta, waya sani ma ko sunan ya tabbata yanzu dan Majalissar Jaha ne kai ko na taraiyya?"

"Haba Hajjaju ai tuni muka tsallake nan, sanata nake meci a yanzu kuma Gomna me jiran gado in Allah ya yarda" Yusuf ya fada, sena bude ido da mamaki kamar yana kallona nace

"Dagaske amma babu labari ko a gurin Alaqiyya ban taba jiba ita da take yar garinku, toh Allah ya tabbatar da Alkahiri kace na kusa zama qanwar Gomna".

"Toh ai baki taba neman koda labari na kinga bazaki sani ba, duk kuma sanda zanje gida se muyi sabani ace kinso kin tafi shiyasa amma yanzu da Allah yayi zamu sake haduwa kinga a arha na ganki a hanya, ya gida ya yarana na shigo Lagos ya kamata nazo na gansu ki sanarwa da Oga kar nazo yayi mun rotse"

Yanda ya fadi rotsen seda nayi dariya nace "ba abinda zeyi maka ai yasan kai Yayana ne ko, ba damuwa toh yaushe zaka shigo?"

"Injiwa ta ya za'ayi ya yarda da wannan nima bazan fara shigar masa gida ba a waje zan tsaya ki turo mun yarana na gansu kar naje mun sha haduwa ma ban san su bane ko da yake bayanda za'ayi naga jininki na kasa ganewa, ina jin ko a taron Arfa naga wanda ya shafeki sena gane shi wallahi

Zan zo gobe da yamma, idan babu damuwa zan sa a kawo takwarar ki anjima kafin nazo kin san an kawota gurin Hajia to ban samu na shiga Bauchi ba ita kuma ta saka rigima se an kawota gurina, inaga na saka a kawota nan din dan idan aka kaita Abuja ma bani da lokaci acan saboda aiki"

"Ok ba damuwa a kawota, ba tare zasu zo da mamanta ba?" Na tambayeshi, a maimakon ya amsa mun se yace

"Shikenan se goben In Allah ya kaimu kiyi saving Number ta nasan yanzu ma qila sa'a naci kika daga tunda baki da ita"

"Ai naga sunan a true caller na gane kaine, Allah ya kaimu goben a gaida Madam" daga haka mukayi sallama.

Dana tashi a hanya naga wani boutique da suke siyarda rigunan yara masu kyau, na tuna gobe ne fa Graduation partyn su Amna jibi kuma suyi prom kuma Faridah bata da kayan da zata saka goben dan haka na tsaya a gurin na siya mata riga me kyau, har na gama na tuno da za'a kawo mun wata yarinyar dukda bani da tabbacin ze bar mana ita ne ta kwana a nan nace bari na siya mata.

A hoto dana ganta dai nasan bazata wuce tsahon Abdallah ba amma dan na tabbatar sena kira wayar Yusuf amma line busy

Text yayi mun cewar yana busy akwai wani abune?
Sena mayar masa da cewa menene tsahon Takwara da size din takalminta ba'a dauki lokaci ba ya turomun kuwa na siya mata kalar ta Faridan da takalmi harda su Ribbon dan naga tana da gashi kafin na wuce gida.

Ina zuwa na tarar dasu sunyi kaca kaca da gidan na kuwa hausu da Fada akan su gyara na wuce dakina ina shiga Jafar ya biyo ni a baya tas ya kwashe abinda ya faru dazu ya gaya mun.

Sosai raina ya baci akan abin, wane irin rashin hankali ne ze saka Aliyu ya daki Matar Babansa da ko bata aure shi ba matsayin uwa take a gurinsa cikin bacin rai nace ya kiramin shi na hadasu su biyun tunda sune manya nayi musu tatas nace kuma idan ya koma ya bata haquri sannan na kira sauran na tara su gaba daya na sake ja musu kunne akan duk wanda na sake jin ya mata ko kallon Banza ne se ransa yayi bala'in baci, haka na wuce daki na barsu Aliyu ya cika kamar ze fashe har na tafi na koma na sake masa warning akan karya kuskura ya taba Jafar dan nasan qarshe se ya huce haushin gayamun da yayi akansa.

Ina Wanka najiyo wayata na qara, da yaje na kammala sena dauro towel na fito kafin na daga ta katse sega wani kiran ya sake shigowa.

Yusuf ne, ina dagawa muka gaisa yace
"Gata can a waje sunzo amma taqi fitowa daga mota, dan Allah ko zakije ki lallaba ta idan kuma taqi su wuto da ita kawai nan bansan ya zanyi da ita bane meeting mukeyi nasan zan iya kai qarfe biyu ma kafin na gama".

"Zama ta yarda in sha Allah bari naje na gani" na fada kafin na kashe wayar. Dogon Hijab har qasa na zura na saka takalmi na fito har sannan yaran suna zaune suna kallo, Abdallah na ganin na fita ya biyoni, a qofar gida naga motoci guda biyu masu numfashi da wasu qarti su biyu a gaban daya daga cikin motar.

Number Yusuf na sake dialing tana shiga ya katse se naga wayar daya daga cikin qattin tayi qara ya daga da sauri kafin ya juyo inda muke se gashi da dan gudunsa ya taho gurin.

Cikin girmamawa kamar ze durqusamun ya gaisheni cikin harshen turanci kafin ya nunamun motar da take a rufe yace tana ciki.

Gaban motar na qarasa na kwankwasa super tint windown motar, kusan minti daya aka sauke shi wani ni'imtaccen qamshin yan gayu ya daki hancina har seda na lumshe ido kafin na bude fuskata dauke da murmushi na kalli cikin motar mukayi arba da wata farar mata irin fara fat din nan dan duk farina se na ganni na zama wata kala a gabanta siririya me dogon gashi da ta barshi a bude, a yanayinta ma zan iya kiranta da bauturiya ko kuma dai ruwa biyu amma ba hausa ko Fulani bace wannan.

Qara fadada fara'ata nayi, dan naga yanayin yarinyar Yusuf a fuskar ta dan haka na tsammaci itace matarsa, cikin harshen turanci na miqa mata gaisuwa dan bana tunanin wanann zataji hausa, ta amsamun a wani yatsine har seda abin ya sosamun rai nan da nan kuwa nima na datse fara'ar dan ban son wulaqanci a rayuwata.

Cikin yauqi da iyayi tace mun "kece Asma'u?"
Sena daga mata kai kawai ina kallonta ta waiwaya daya bangaren da bana hango wanda yake zaune tace
"Sweetheart kije ga Namesake dinki nan zaki zauna a gurinta, ki zama yarinyar kirki kinji"

Cikin muryar yara da kanaji kasan yaron ma sangartacce ne Yarinyar ta fara mana tana cewa
"Ni bazan je ba gurin Dady na zanje"

"Dadynki bashi da lokacin ki na gaya miki kece kike ganin yana sonki amma baya sonki sam, idan ba haka ba ya za'ayi ki taho tundaga United State amma ya kasa zuwa ya tare ki sema yace a kaiki gurin wata stranger ki zauna hmm" Matar ta fadawa yarinyar seka rantse da wata babba Sa'arta takeyi ni kuwa ina daga gefe ina kallon ikon Allah.

Wannan wace irin uwa ce me qoqarin turawa yarta wata aqida da zata sa ta tsani mahaifinta?
Ganin dramar bazat qare ba ya saka na zagaya daya barin da take, badan kar Yusuf yaga rashin kirki na bama qyale ta zanyi su tafi amma bansan dalilin sa na cewa a kawota ba tunda ga uwarta amma yanzun ma sau daya zan lallabata idan bata yarda ba su sauka lafiya.

Qofar na bude da murmushi na na miqa mata hannu seta dakata daga bubbuga qafar da takeyi ta zuba mun ido

"Muje ko kinga dare yayi Momy tana so ta tafi gobe da safe se na kaiki gurin Dady da kaina" na fada cikin lallashi, seta kalleni ta kalli uwarta data wani tabe baki ta dauke kai gefe, kai na gyada mata alamar tabbatar wa se kuwa gashi ta zuri qafafunta sena dagata na fito da ita daga motar ashe ma afili batafi girman Yan biyu ba.

Qato daya ne ya bude boot ya ciro mata akwatinta ta yangayu me shegen kyau ga wata qatuwar Teddy da tayi girmanta ma ya wuce da kayan bakin qofa ya ajiye, a taqaice nayiwa matar sallama na juya seta dakatar dani, ta bude jakarta ta zaro wata farar takarda ta miqo mun, da rashin fahimta na kalleta se tace

"List na abubuwan da Sweetheart take ci ne"
"Ikon Allah" na fada a fili na sa hannu na karbi takardar na shige gida ina jujjuyata a hannuna, muna shiga muka tarar suna kallon wani cartoon na Bluey ne sunan sa kome ta kuwa dage ta kwala sunan a kunnenan babu shiri na ajiye ta ta wuce da gudu cikin palour, ganin sun cikia ko ina kan kujerun bata tsaya ba ta dane Cinyar Aliyu da yake kujerar data fi saiti da Tv tayi zamanta.

Se kawai muka tsaya muna kallonta, ita kuwa ba abinda ya shafeta dariyarta takeyi da alamar tana son abinda take kallon.

"Mami wacece wanna" Aliyu ya fada yana sauke ta daga jikinsa amma taqi saukar, se nayi murmushi nace "sabuwar qanwa kuka samu tazo mana weekend, gobe Babanta zezo zaku ganshi" na wuce ciki na barsu.

Akan Mirror na ajiye takardar ina mamakin wannan wace irin mata Yusuf shi kuwa ya aura ko a ina ya samota se Allah.

Seda na gama shiryawa tsaf na kalli agogo nasan lokacin sun fara shirin tafiya dan haka na fito, ina sako qafata ido na ya sauka akan Yar Amana tana zaune tayi daidai tana cin wainar fulawa da Manja da alama yanzu sukayita farar rigar jikinta tayi kaca kaca ta canza kala.

"Na bani ni Asma'u me kuka bata haka" na fada ina qarasawa gurin da sauri, seta dago tana yar dariyar yarinta cikin turancinta da kana ji kasan rainon America ce tace

"Mami da dadi amma akwai yaji"
"Waya ce ku bata Amna me yasa baku tambayebi ba kafin ku bata" na fada ina janye farantin se kawai naga yarinya ta fara birgima kamar me hawa bori, Amna na dariya tace

"Wallahi Mami ban san ma sanda suka shirya ba Jafar ne yayi musu gashi can ma yana soya sauran a Kitchen"
"Kun kyauta, idan cikin yar mutane ya baci se kusan yanda zakuyi da ita ai" na fada ina akiye mata kwanon na koma na dauko wayata na shiga kiran Babanta.

To a takardar fa wasu lissafin abincinsu can na turawa yan gayu aka rubuta sunzo sun hadata da fulawa da manja, saurin fa da nayi kenan na fita ko oat ne na saka su hada mata tasha dan banida tarkacen dana ga an rubuta a takardar.

Nayi Sa'a kira daya ta shiga ya daga yana cewa
"Badai yar rigimar taqi zama ba"

"Wa ai gata can muan shigowa ma ta shiga sabgarta, Mamanta ce ta bani list na abincin da take ci, todai in gaya maka ina daki kafin na fito su Jafar suka dura mata wainar fulawa da yaji na dauke na hanata ci ta farayi mun bori shiyasa na kiraka kar muje cikinta ya birkice ga dare yayi" na fada masa.

Dariya sosai yayi yana cewa "Ma'u kenan sarkin ci ai indai taga abinci setaci ko wanne iri ne, ki manta da wata takadda na rasa me yake damun Intee Allah yasa dai batayi miki halin nata na wulaqanci ba"

"Aa ba komai gaisawa kawai mukayi ta tafi, to shikenan ba matsala kenan mu bata duk abinda muke ci" na sake tambayarsa

"Ki bata komai, dambu fura tuwan dawa ba abinda Hajia bata dura mata a Bauchi tun bata kai haka ba me kuma ya sameta tsabar matsala irin ta uwarta ce kawai" ya sake fada, se nace masa

"Allah ya rufa Asiri, goben da wuri zaka shigo dan zamu fita, zamuje Graduation din su Amna qarfe goma"

"Kai masha Allah har Amna ta gama secondary school dagaske dai tsufa ya fara kama mu, ba damuwa a wacce makaranta ne idan na samu dama sena shigo nima"

Sunan makarantar na gaya masa mukayi sallama, ina jiyo ihun Ma'u takwara na fita naga meya faru na tarar wai su Faridah ne zasu tafi ta kama qafar Jafar ta riqe da gani dai dashi aka qulla abota se tsalle take tana ihun bazasu tafi ko kuma seta bisu, kamo ta nayi ina rarrashi amma ina qara zillewa take yi, qarshe dakyar na samu ta haqura shima seda nace Faridah ta zauna ta kwana suka zille sauran suka tafi na saka Amna tayi mata wanka suka kwanta a raina ina Addu'ar Allah sa kar Bashir yace zeyi tashin hankali a daren nan cikin Sa'a kuwa har muka kwanta shiru.

WASHE GARI

M&Z FASHION DESINGNERS
INA MATA YAN KWALISA
KU GARZAYO M&Z
FASHION DESNGNERS DAN SAMUN IN GANTATTUN KAYA MASU AMINCI.
IRINSU
ZANNIWAN GADO
TROW PILLOWS NA ZAMANI
TUM TUM
BABY SET
TOILET SET
KITCHEN SET
LABULAYE DA SAURAN KAYAN KWALLIYAR GIDA.
HARMA DA ATAMFOFI DA KAYAN KITCHEN AKAN FARASHII ME RAHUSA
KU NEMEMU AKAN LAMBAR WAYA 07064870087.08127423783.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR πŸ₯°πŸ‘Ή
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 48



WASHE GARI


Washe garin ranar da wuri muka shirya saboda su basayin African time irin namu na yan Arewa. Sosai nayi kwalliya da Doguwar rigar Lace baqi me Golden din zare na yafa mayafina a kafada na saka coge nida kaina na yaba kwalliyata dan na fito cas dani.

Da muka fito zamu tafi Anty se tsokanata take wai taga alamar fa Zawarcin nan me lasisi nakeΒ  zuba to dai nayi a hankali kar na sa maza suringa karo a hanya a garin kallo na.

Bashir ne ya tafi da yara mazan a motar sa harda Amirah suka tafi, daman bamu hadu ba a bakin Amnah naji cewar da Amiran aka tafi nayi murmushi kawai a raina ni kadai nasan tsiyar da zan qulla mata tunda nidai ban gayyaceta ba ai, A motata muka tafi tareda Anty da yammatan harda sabuwar yata da tasha kwalliya dan tun dare na gyara musu gashin su ita da Farida sunyi kyau sosai cikin rigar jiya kamar wasu Yaya da qanwa haka muka rankaya muka tafi.

Sanda muka isa lokacin an fara shiga dakin taron, sallama Amnah ta mana ta wuce gurin Yan ajinsu ni kuma na tsaya dakko Get pass dan suna motata tun ranar da aka kai mana ban cire su ba nasan su Bashir ma basu shiga tunda dole su jira pass din, murmushi nayi sanda na fito dasu na qirga.

Guda goma ne cif, daman guda hudu suke bawa ko wanne dalibi idan kana son qari seka siya dan haka na qara guda shida ya zama teburi daya muka kama kenan, nida yarana banda Amnah mu bakwai se Anty ta takwas ga Bashir tara ragowar daya kuma daman na siyane kawai dan teburin me Goma ne to yanzu ga sabuwar yar da nayi shi kenan mun cike shi.

Haka kawai naji dariya ta kama ni sanda na hango Amirah yanda taci uwar kwalliya kai ka rantse wata dinner auren qawarta zata tafi se wani karairaya take a gefen Bashir hannunta cikin nasa, wani ikon Allah se banji komai a raina ba illah ma dariya data bani kawai dan a yanda take abun kana gani kasan irin da gayyar nan take dan ta bata mun bata san ko a kwalar rigata ba.
Mijin nata ma da da na dauka na dora akai yanzu na sauke nima na huta.

Seda na qara gyara fuskata tsaf kafin na kulle motar na fito ina gyara zaman gyalena a kafada daya, cikin takun yauqi da yanga na qarasa inda su Bashir suke ina jin yanda idon mutane yayi mun caa a raina na shiga karanta 'A'uthubikalimatillahi tammat min kulli shaydanin wa hammatin wa min kulli aynin lammati' saboda mugun ido haka na qarasa inda suke kallo daya nayiwa Bashir daya watso mun idanunsa da suka fara rinewa da bacin rai nan take na dauke kaina ina murmushin qeta.

A saitinsa na tsaya fuskata dauke da murmushi na gaishe shi, be amsa ba se matsowa da yayi bayan ya saki hannun Amirah da tunda ta ganni ta shaqa tayi fam se wani harare harare takeyi kuma dai baze wuce tsabar hassada da baqin cikin gani na bane ya saka. A daidai kunnena ya tsaya idonsa akan fuskata yace

"Meye kike yi haka Ma'u baki kalli kanki a mudubi ba da zaki fito a haka cikin wannan kwalliyar? Jifa yanda maza suke kallonki dan Allah ki koma nasan bazaki rasa Hijab ko Abaya a mota ba ki saka".

Wata siririyar dariya nayi kafin nayi qasa nima da murya yanda shi kadai ze ji abinda na fada nace masa

"Ai daman saboda mazan su kalleni nayi, ko ka manta a kasuwa nake yanzu ne?"
Ina fadar haka na janye daga kusa dashi ina ji ya na kira sunana amma nayi kamar ma banji ba, katinan hannuna na fara bawa yaran da akwai table Number dan haka sukayi gaba, na miqawa Anty nata na miqawa Bashir daya sannan na juya ina cewa Anty

"Muje toh, Baban Ali seka shigo koh" nayi gaba abuna dan ban nuna nasan da wanzuwar wata halitta ma a kusa dashi ba, hannuna ya riqo da sauri na waiwaya na watsa masa wani mugun kallo da ni kaina bansan na iya shi ba, se yayi saurin sakina yana cewa

"Yi haquri amma dan Allah kije ki.."
"Karka sake mun haka, da mutunchi na kazo kana kamani a gaban mutane bana so, sannan baka da hurumin da zaka gaya mun abinda zanyi yanzu ko wanda zan bari ka gane" na fada ina qara daure fuska.

Ina kallo ya hadiye wani abu qut kafin ya marairaice fuska ya sake cewa

"Nace kiyi haquri ai, naga kati daya kika bani ina na Amirah?"

Juyawa nayi na kalli Amiran da ya ce se numfarfashi takeyi kamar wadda zata haihu na maida idona kansa nace masa

"Na iya wadanda aka gayyata kenan, bama buqatar qarin gayyar sodi" ina gama fada na bi bayan Anty da ta dade dayin gaba daman.

Bansan yanda suka qare ba, munfi kusan minti sha biyar da shiga kafin na hango su sun shigo Amirah na bayansa fuskar nan kamar ka tsira mata Tsinke ta fashe tsabar yanda ta kumbura, acan kejerun yan regular naga ya sama mata sit ta zauna, ya dan duqa da alama magana yake gaya mata kafin a fusace naga ya taho inda muke zaune.

Na zata masifa ze zo yayi na qara tamke fuska ta tsaf se naga yana zuwa yaja kujerar da tayi saura ya zauna ya gaida Anty ta amsa masa sama sama nidai na mayar da hankali kan cultural dance da akeyi ina jin yanda idon Bashir yake kaina amma naqi kallon barin da yake.

Wayata dake ajiye akan teburin ce ta dauki qara, yanda kasan shi aka kira ya bi wayar da kallo na kai hannu na dauka, Yusuf ne da nayiwa saving da Abban Takwara, saboda qarar kida banajinsa dan haka na tashi nayi tacan baya gurin inda kujerun su Amirah yake, ta kusa da ita na wuce ina giftawa naji ta saki tsaki ban kulata ba na wuce na amsa wayata.

Gaya mun yayi yana waje nace ya jirani gani nan zuwa, na sake zuwa na wuceta dan banida lokacin da zan tsaya ina kula wannan yarinyar. Seda na koma sit dina, jakata na bude na ciro ragowar kati daya dan Ma'u Jafar ne ya dagata da yake ta sangarta ta lankwashe a jikinsa yanda kasan wata yar Yaye dan haka basu karbi katin taba muna shiga ya bani na saka a jaka.

Ina kallon yanda Bashir ya bini da kallo ganin na ciro wani katin daga jaka, se na juya na cewa Anty ina zuwa na wuce ta saitin Bashir ya shaqi qamshij da nakeyi kuwa kafin ya ajiye numfashi na wuce shi ina juya mazaunan da Allah ya hore mun shi kuwa Ya bini da kallo da baki a sake har na qulewa ganinsa.

A qofar gurin naci karo da Yusuf, wani dace shaddar jikinsa yanda kasan tare muka siya da kayan jikina sunyi bala'in dacewa.

Cikin mutuntaka muka gaisa da wani dana gansu tare babban mutum ne sosai wai shima Sanata ne akwai yaransa biyu a yan Graduation din, ba'a ma karbi katinan mu ba muka shiga tareda Yusuf din kai tsaye teburin da muke zaune na wuce gaba yana bina a baya.

BASHIR
Tunda yaga Asma'u a gurin gaba daya ta sake kwance masa notin kai. Kwalliyar ta tayi bala'in tafiya da imaninsa ga wani kishinta daya taso masa Ganin yanda maza suke binta da kallo.

Tana bashi katin nan da ta juya haka ya rakata da ido gani yake kamar qara mata quruciya akayi dirin jikinta ya sake fitowa, yana can aikin kallonta tsakin da Amirah tayi ne ya dawo dashi hayyacinsa se ya kalleta sanda take cewa

"Yanzu kana kallo ta tafi bayan kaji abinda tace wato nice ma gayyar sodi ko kuma kayi shiru baka ce komai ba"

"To so kikeyi na kamata da kokawa nace seta baki ko kuma nawa zan baki? Daman ai ba gayyatarki ki akayi ba gayyar sodin kika zo.

Kinga ki kama kanki wallahi karki sake kice zakiyi mun shirme a gurin nan zan bata miki rai" Bashir ya fada cikin bacin rai, wallahi da a Gombe nema tafiyarsa zeyi ya barta idan yaso ta koma gida dan dai kawai nan bata san hanyaΒ  bane.

Amirah data shaqa iya wuya, dakyar ta danne bacin ranta tace
"To yanzu a waje zaka barni ka shiga ciki kenan" ta fada kamar zatayi kuka

"Seki koma mota ki zauna dan dai ni ban san a inda zan samo miki kati ba kuma nan ba irin taron da kika saba zuwa bane ko ba'a gayyace kuba ku shiga su komai a tsare sukeyinsa" Bashir ya fada yana hararar ta, se kawai ta saka masa kuka tana cewa

"Da kasan wulaqanci zaka mun idan nazo tun a gida se kace bazaka dani ba amma yanzu kace na tafi mota bayan ga katuna can a hannunta harda wasu daban ta gayyato se nice baza'a bani ba"

Tsaki Bashir yayi ganin tana neman tara masa Jama'a dan har an fara kallon su yace mata yana zuwa ya tafi Gurin securities din bakin gate.

Seda yaci wuya dakyar ya samo mata regular card shi kansa dubu goma aka siyar masa, daya bata a maimakon ta gode seta hau sabon qorafi wai ba irin nasu bane dan ko a kala katin ya banbanta.

Banza ya mata suka shiga ya rakata kujerarta se raba ido take ganin Jama'a kala kala yanzu da wannan shagalin za'a mata buqulun zuwa tab, Allah ya kaimu Na Aliyu wannan ai dan mijinta ne itama dole tana teburin gaba tunda yanzu ance mata gayyar sodi.

Hakata zauna wani mugun kishi ga kyashi da hassadar Ma'u na dukanta. Duk abinda ta gani a jikinta ji takeyi dama itace, simple lace me Azabar kyau ga zobuna da awarwaron gwal suma qira mara hayaniya sun qara fito da kwalliyar ta sosai qarin baqin cikinta yanda Bashir ya kasa dena kallon Ma'un ba daban ba da se tace su tafi kawai amma ina setaga kwal uwar daka sannan idan sun koma gida se ayi uwar da za'ayi.

BASHIR
Kwarewa yayi da ruwan da yake sha a daidai sanda Ma'u da Yusuf suka ratso dakin taron kamar wasu shaqiqan masoya fuskokinsu dauke da murmushi. Ba Bashir kadai ba, da yawa mutane seda suka bisu da kallo haka suka qarasa har teburin Yusuf ya daga Ma'u qarama data fasa

Please Login or Register in order to submit comment