Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din ammi aka wuce daita bisa ga umarnin dady da ammi, tundaga lokacin da su'ad ta fito daga asibiti take baya baya dashi batason ke'bewarsu guri daya amman kuma ta wani fanni tana tausaya masa saboda yanayinsa tana jin tsoro kar ya jefa kansa cikin wani hali .


a wani yammaci tana kwance akan 3seater cikin parlour'n ammi sanye cikin doguwar rigar baka, tuni ta rigada tayi nisa cikin kogon tunani halin da mijinta zai tsinci kansa na nisanta junansu dasuka samu, yashigo falon yayi tsaye ya tsura mata idanuwa yana kallonta sannan ya zauna daidai saitin fuskarta yana kiran "hrt beat "

ahankali ta d'ago fararen idanunta suka dubi juna su'ad ta saki wata yar ajiyar zuciya ,ta dawo daga duniyar tunanin data dade da lulawa ya dafa kafafarta "meyasa kika cika yawon tunani bayan kinsa yanayin da kike ciki ,ba a son me juna biyu tana yawon zurfafa tunani ples ki daina bana bukatar hk.

ta kalleshi tana murmushi "taso mu koma part dinmu wallahi bana jin dadin zamana ni kad'ai batare da kina kusa dani ba, yakai hannunsa ya d'agota ta fad'a kirjinsa tana murmushi jin takun tawowa yasa tayi saurin barin jikinsa tsayuwar minti biyu suna jiran suka ko waye, gani babu wanda yayi kokarin shigowa yasoma tafiya daita yana rungume daita ajikinsa yana rad'a mata zantuttukansa masu sanyi kicibis sukayi da ammi dake kokarin shigowa parlour'n suka ja baya cike da matsanancin kunya su'ad ta boye abayansa.
ammi ta wurgawa ak wata harara hade da cewa "ina zuwa kuma?


ak yasanya hannusa yana tsotsa keyarsa alamun rashin gsky atare dashi "ammi gyara min shimfid'a zatayi "ammi ta sake watsa masa wata hararar "banason rainin hankalinka daka saba yiwa mutane gyara shimfid'ar ne bazaka iya da kanka ba.

"wai me yasa abdul baka da tausayi ne hk ?

yayi murmushin yake dan ya lura kmr ammi bata fuskanci inda maganarsa ya dosa ba ,dan hk ya kamo hannun su'ad cikin nasa "zo muje kinji hrt dina kyale ammi batason ki dinga aiki byn wannan aikin zai sa ki dinga jinki garass .

ammi tace "maza ki zauna muddin bazakaje Kayi gyaran da kanka ba ko kasa wani daga cikin ma'aikatan gidan nan su maka sai dai ka hakura" ina dalilin wannan jaraba hk mace da ciki baxa'a barta ta huta ba..

"sai kajawo mana yawon zuwa asibiti ,wallahi ni dai babu ruwana idan kayi sanadin rasa abinda ke cikinta, wata irin kunya ce takama su'ad kmr kasa ta tsage tashige ciki ak yayi murmushi yace "shikenan ammi tunda kin hanata amman fa ba abinda kike tunani bane.. ya fice daga parlour'n ammi da su'ad suka koma cikin parlour suka zauna nan ammi take nunawa su'ad had'arin abinda suke kokarin aikatawa..

duk tsawon wunin ranar ak sai wani shashshare su'ad yakeyi yana wani d'aure mata fuska wai shi a dole fushi yake daita domin aganinsa itama din batason kasancewa dashi shi yasa take baya baya dahi.

tashigo parlour'n yana zaune rike da remut a hannunsa yana sauya tashoshi dake cikin receiver ya d'an saci kallonta yana ganin zasu had'a ido yayi saurin yanye idanunsa hkn ya bala'in bata dry.

sautin dariyarta ya tsinkayo acikin kwalkwaluwarsa yasanyashi yayi saurin dubanta ba shiri ya sauke numfashi yana kallonta "dry me kike min?

cikin yanayi na d'aure fuska yake mata mgn hkn yakara bata dry, amman sai tayi saurin sanya hannunta ta toshe bakinta ya taso daga gurin dayake ya nufota tare da riko hannunta ya matse da karfi yace "me kika gani ajikina kike dry?


su'ad taji radadin matse mata yatsu dayayi ta saki wata siririyar k'ara mara sauti tace"wash Allah kayi hakuri bazan kuma ba "sai kin fada min sannan zan kyaleki .

"wayyo Allah ammi zai karya mini hannu ki kawo agaji..
ya sakar mata hannu yana hararata ta fad'a kan kujera tana rike da hannuta.

"nima zan rama ne "

yace "hb yarinya ai sai dai ki rame tashi ki kawo min driks in sha "bazan iya d'akowa ba.

ya kalleta yana dry hade da cewa "ke dai raguwa ce wallahi cikinki bawani girma yayi ba amman sai shegen son jiki tashi plz ki d'auko min ..

ta marairaice murya "da gaske nake bazan iya tashi ba hannuna ciwo yake min.

"da gaske kike ko wasa ?

ta d'aga masa kanta batare da tace masa komai ba. ai bai san sanda ya taso daga gurin dayake zaune ba yayi durkuso agaban kujerar datake kwance ya rungume hannunwansa game da xuba mata mayatattu idanunsa "tashi muje hospital.

suad ta ware idanuwa tana dubansa tace "ai sun daina ya langwabe kai "ban yarda ba ki tashi muje kawai, tayi murmushi "daman fa tsokana ne.

"ki daina min irin wannan tsokanar ta hanyar wasa da lfyarki domin kina daga min hankali, kin ko san irin son da nake miki acikin zuciyata? da ina da halin ko k'uda bazan bari ya sauka akanki ba i love you so much hrt itama ta mayar masa da matani "me too"

tana fad'ar hk ta yunkura ta tashi ta nufi kitchen ,yabi bayanta da kallo shi kam akowani lokaci ya kan tmbyi kansa wai wani irin so yake mata.

cikin wannan lokacin zangaga ya meida hankali akan sabon ginin gidansa dake sun shine estate domin nan yake bukatar suci gaba da rayuwa da sanyi idanunsa tunda taki na green hill.

*******
bangaren zeey kuwa tana barin gida gurin boka na kan dutse ta nufa inda ta isa tsirara haihuwar uwarta aguje tayi samansa yana ganinta ya haukace da wata irin mahaukaciya dry daya sa gbdy ilahiri gurin amsawa "hhhhhhh lananiya ga karshen irinku nan marasa imani irinmu, ya tashi daga zaunen dayake ya kamo hannuta zuwa bayan dutse inda yake ajiyar mahaukata irinta, domin had'awa manyan attajirai asirin neman duniya..
akwai musamman manya yan tsiyasa da kusoshin gwanati da manya attajiran dayake masu aiki, wani aikin kuma dole yana bukatar mahaukatan irin su zeey da zasu dinga saduwa dasu domin neman duniyarsu .

wasu ma daga cikinsu basu mahaukatan akeyi su samu d'aki daya acikin gidansu su ajiyeta kawai su dinga luwadi daita ko saduwa daita ya danganta da yanayin tsarin da boka yabawa mutun, mahaukata agurin sunfi guda dari biyu kowace na yawo tsirara haihuwar iyayensu .. ...

yayinda har wannan lokacin akil na tsare agurin ma'aika ya rame sosai Duk zuwan da yan'uwansa sukayi akan lamarin basu bada belling sa ba sai da musty yaxo yace kotu zasu amman ak ya hanashi"yace barshi kawai yaji da cutar jikinsa "akan wani dalili zasuyi shari'a dashi byn ga katuwar me laifi can tabi duniya itama na yafe mata darajar allah .

akil ya fito daga gidan yari sai dai ya fito ne da burin sai shima ya yad'awa matan duniya cutar jikinsa a cewarsa bazai mutu shi kad'ai ba sannan da ba nemanta mata yayi ba, yanzu zai nemi mata da tushe.sati biyu da fitowarsa yasoma neman mata idan ya kwanta da mace byn yayi realize sai yaki tashi ajikinta har sai ya d'auki lokaci sannan yatashi, wanda wannan kwanciyar kebawa cututuka dayawa damar shiga cikin jikin dan'adam..

haka ya dinga yaran mutane da manya mata yana kwana dasu wasu ya biyasu wasu ya hana idan kikayi mgn ya fito da miki da tsirancinki ya nuna miki dole kiyi shiru..

a wata rana asabar ya fito daga gidansu da niyyar yaje yasha sigari daga nan ya wuce yawon iskanshi, yakarasa wata majalisa dake gaba da gidansu kad'an yace "abashi sigari me sigari ya miko masa kwali London ya amsa ya zari guda daya ya kunna yasoma zuka yana busar da hayaki, suka ji sautin harbe harbe a she plice ne suka biyo barayi.

kowa yasoma gudun ceton rai shima garin gudu bisa sautsayi wani police yayi harbe yasameshi agefen cik take ko shurawa bai yi ba agurin, yace "ga garinku.

hk aka tattara gawarsa byn police sunbi barayin akayi gida dashi.



washegari wuraren karfe takwas aka kaishi makwancinsa.....


mmn sudais ce


💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH



YA HALIM

THE CLEMENT


page 88

......zaune ak yake akan kujerar kushin me zaman mutun 3, system ce akan cinyarsa yana operating dinta cikin iyawa da k'warewa, sanye yake cikin wasu hadd'aun fararen kaya, riga da wando ne na bacci me budadd'en gaba wanda ya bayyana halitar kirjinsa tare kwantace gashin dake kwance a kirjinsa.
wayarsa ta d'auki karar sauti yana jin wayar tana kara ammam yayi buris daita har wayar tagaji da ring ta katse baiyi yunkurin d'aukar kiran ba .

aka sake kiran wayar a karo na biyar kenan yaja dogon tsaki yana me furzar da iska ta bakinsa sannan ya d'auki wayar yana duba screen din wayar sunan wanda yagani yana yawo a screen din wayar yasanyashi sake jan tsaki ,akaro na biyu sannan ya d'auka "ya'akayi ne malik kana kiran mutane adaidai wannan lokacin saboda bakasan darajar iyali ba?

malik yayi murmushi sannan yace " yi hakuri masu iyali ,muma dai Inshaallahu muna kan hanya "daman nakira ne na gaya maka zance rasuwar akil ,amman bansan cewar na wuce limit ba.

"aiki banza kawai malam ai bazaka san ka wuce k'aida ba ,tunda har yanzu kana nan kana yawon tazubar atiti, kowa yayi hankalin da natsuwar daya ajiye iyali ,amman kai har yau shashanci kasanya gaba sannan dan zaka gaya min rasuwar wannan tantirin shine kake min irin wannan kiran?

"to be your first &last dazaka sake min irin wannan kiran adaidai wannan lokacin , "for God sake ma ina ruwana da mutuwar akil ,ai irin wannan mutuwar wulakacin da yayi shine daidai da me rayuwa irin nashi .

"a yadda ak yake maganar cikin zafin rai yasa malik ya fuskanci kmr yasan da zance rasuwar, amman saboda wulakancin dayayi masa a yanzu ,yasa yayi decide ya k'ara masa wani haushi dan hk yace" ok da ala'mun ma kaji zance rasuwar yanzu zuwa yaushe zamuje gaisuwa kenan ?

ak yayi shiru kawai yana tunani ,gbdy yarasa amsar da zai bashi wace zatayi daidai da tamyar da yayi masa ,jin Shirun yayi yawa yasa malik sake cewa ko zamu je gobe ne?

"Malik.......ak yakira sunansa a harzuke, malik ya amsa da" uhm ina jinka yana kunshe dry , dan yasan zuwa wannan lokacin yagama kaisa karshe ,ak ya sake kiran sunansa har sau uku sannan yace
"meye damuwarka dani ne malik da har zaka nemi shiga rayuwata akan rasuwar akil?

"idan fa ka matsamin dayawa zan iya cewa zanci kutumar ubanka........ yana gama fad'ar hk ya katse kiran yakira musty ,musty na d'auka ya hau shi da bala'i kmr shine malik har da cewa "wallahi kagaya wancan jakin abokin naka idan ya kuma kirana akan zance akil zan sa a d'aure min shi ,"
banda hakuri babu abinda musty ke bashi da kyar yasamu ya shawo kansa ya hakura.

su'ad wace ta dade da shigo cikin parlour'n da turtsetsen cikinta daya soma girma, ta tsaya abakin kofar tun soma wayarsa tana dubansa ahankali , kmr ance ya waigo inda take tsaye idanunsa suka sauka akanta ta mugun tsaresa da fararen idanunta tana kallonsa.

ganinta yasa gbdy ya nemi bacin ransa ya rasa , ajiye system dinsa yayi akan kujera ya mike tsaye ya nufi gurinta yayi tsuguno agabanta tare da riko tafukan hannayenta yana murza yan yatsun hannunta ahankali muryarsa a kasalance yace "love you bbynah ya fad'i hk yana me shafo cikinta yana jin tsantsar farinciki "ya bby nah yake?
ta kirkiro murmushin dole tare da yi masa fari da idanu take yaji tamkar ya sume agurin ya mike tsaye yana dubanta ita din ma shi take kallo ahankali ta kai d'an yatsanta tana shafa lab'bansa kusan minti goma tana shafa lip's dinsa batare da tace masa komai ba duk da mgn take son yi masa akan wayar dataji yagama a yanzu ,amman tana jin tsoro abinda zai mata.

" tarasa wani irin halintar mutun ne abdul dinta, ya fiyye zafin zuciya da saurin fushi akan komai kwanakin baya taji ya furta ya yafewa akil abinda yayi masa. atunaninta mutuwarsa a yanzu zaiji babu dadi aransa ,matsawar yafiyar dayayi masa da gaske ne yakamata ace yaje gaisuwar mutuwarsa.

ahankali tasanyawa jikinta jarumta tare da karfin halin soma mgn ta hanyar somawa da kiran sunansa "abdul...
" rungumeta tsam yayi ajikinsa amadadin ya amsa mata.

"da hankalinka da tunaninka kana muslimi ka rinka biyewa sharrin zuciya dana sheid'an ," haba mijina ka daina wannan akidar d'aukar zafi irin hk abinda yarigada ya wuce abar shi a ya wuce,bafa zaka taba kankare faruwa hkn ba acikin kaddararka..

"ya abdul... yayi saurin d'agowa tare da waigowa bayansa yaga ko eiman ce takirasa da hakan ,sai dai bai ga kowa ba hkn ya tabbatar masa da ita din ce takirasa da hkn "ya abdul meye matsayina agurinka?

ak ya rausayar da k'ansa sannan yasoma mgn ahankali "bazan iya misalta matsayinki ba agurina, sai dai nasan kin zarta komai azuciyata" kece komai na, kece duniyar abdulkabir kece rayuwarsa, "rayuwar da babu ke acikinta is nothing "kin taka matsayi iri iri acikin zuciyata har bansa abinda, zance ba..

" to ina son dan Allah da girman matsayina gareka kayi hakuri komai ya wuce acikin zuciyarka ,ka shirya kuje ta'aziyar akil idan kayi hkn zanji dadi sosai .

ak yayi murmushi yana dubanta ita da cikin jikinta " angama uwar gidana a duniya da lahira zanyi yadda kikace .
Allah ya jikan muslimai gbdy yasa idan tamu mutuwar tazo mucika da kyau da imani ..
"ameen nagode sosai mijina Allah yabarni da kai muddin rai "yace ameen tare da kissing din cikinta .
hannunsa ta riko zuwa bedroom dinsu taja shi suka lula wata duniyar me cike da gardi da sikarin dadi.
rungume take ajikinsa tana aikin sarrafa shi ta yadda zaiji dadi sosai, a zuciyarsa yana me k'ara sakankancewa su'ad dinsa ta bance acikin tarin mata ,su'ad ita ce kalar macen data dace dashi, ya sake sakin sanyayiyar ajiyar xuciya ya kai hannunsa yana shafa tsakiyar bayanta .

washegari su'ad na tashi daga bacci brush kad'ai tasamu tayi ta nufi kitchen dan tasamar musu abinda zasuci ak kuma ya nufi bathroom yayi wanka yayi sallah yana gama sallah shima kitchen yabiyota dan ya taimaka mata dan tunda cikinta ya tsufa dashi akeyin komai agidan, tunda ta hana a d'aukar mata me aiki acewarta bazata d'auki me aiki ba tun yanzu sai nan gaba.

tana cikin fere dankali yakaraso ya tsaya abayanta ya riko hannuta dake rike da wuka ta waigo ahankali tana masa murmushi "no karbashi na kusan gamawa "ya girgiza kai "aikin me nakeyi da zan zauna ina kallo kina aiki?

tayi tsadadden murmushinta dake kara mata kyau tare da kai bakinta kan lip's dinsa ta tsotsa sannan suka cigaba da aikin, har datagama, sai data kammala table sannan ta nufi bathroom tayo wanka ta shirya tsaf cikin kananan kaya riga da wando, dan cikinta baya hanata sanya duk kayan dataga dama ,tayi kyau sosai sai baza kamshi take tana isa dining ak dake zaune zaman jiranta ya tsura mata mayatattun idanunsa yana kallon yadda take tafiya komai nata a natse takeyinsa sam bata da rawar Kai, ahankali taja kujera xata zauna "no no kin mata ga gurin zamanki yayi mata nuni da kan cinyarsa?

tayi murmushi ta zauna kan cinyarsa tana shafa fuskarsa sai da suka gama lashe lashe da tande tande sannan fa suka fara cin abinci tana bashi yana bata har suka koshi .

ak yakarasa sabon gidansa dake sun shine estate har ma sun tare mutane nata zuwa tayasu murna.

mahaifan su'ad sun zo dubata lokacin da umman su'ad taganta zubawa su'ad ido tayi tana kallon yadda tasauya dan tunda ta dawo basu zo gidan ba sai da ammi ta matsa musu tukun .
ahankali ta dinga kallon irin dukiyar da ak ya kashewa diyarta, su'ad kuwa sai murna take bata kitchen bata parlour, tana kokarin had'o musu ababen motsa baki.
ko nauyin cikin jikinta bataji ak ya fito ya gaisa dasu a dakile yace "shi zai fita dan har lokacin bai daina jin haushinsu ba.
ko Allah yasanya alkhairi da suke masa bai tsaya amsawa ba yayi gaba.
"shi gbdy yarasa meyasa baya sonsu hatta d'an burbushin son dayakewa sir mahbub ya kau a yanzu dayasan shine asalin uncle dinsa ne kuma uban da yayi silar zuwan Matarsa duniya ..

yana fita umman su'ad tace "su'ad ki zauna ki huta mufa akoshenmu muke ,mu xo muga inda kike da tabbatar da lafiyarki. su'ad tayi murmushi "haba umma meye nayi doctor ma yace na dinga motsa jikina sosai, can tayi k!asa da muryarta sosai ta yadda babanta baxai ji abinda zata fada ba "ummanah Allah Allah nake na haifi cikin jikina nabaku kusamu masu debe muku kewa a gida ..

umma ta jinjina kai tare da duban inda mahaifinta yake zaune dan shima burinsa kenan ta haifa masa ya'ya, bata sawa ranta samun kyautar daga garesu ba saboda tasan yadda AK yake bazai ta'ba yarda da hkn ba ,dan hk ma bazata wahalar da ranta gurin sanyawa ranta ba.

da zasu tafi taji kmr karsu tafi su barta dan taji dadin kasancewa tare da iyayenta sosai, kwana biyu tsakani ammi taxo ta iske ak yana zaune a parlour tayi sallama yana ganinta yayi saurin tashi ya tarota hkn yayi daidai da shigowar su'ad cikin parlour'n ta nufi ammi ta rungumeta tana murna ganinta "wayyo Allah amminah nifa yar gata ce gaba da baya shekaranjiya su abba da umma sukaxo yau kuma ga ammina ..
"ammi ki zauna ta nufi hanyar kitchen da d'an saurinta ammi tabita da kallo ganin yadda tayi bala'in kyau tamkr ata'bata jini ya fito ga cikin jikinta yayi mata dass kmr an kife kwarya tazama wata abar sha'awa ,ak ya gaishe da ammi ta amsa cikin sakin fuska su'ad ta karrama ammi da abun mots baki har sai da ammi tace abarta hk ya isa ba xama taxoyi ba taxo ne ta dubasu .

ammi bata wani jima ba tace zata wuce suka rakota har harabar gidan inda take cewa ak "kai yakamata fa su'ad ta dawo gida haihuwa hkn saboda haihuwar fari ce i think cikinta yashiga wata takwas da doriya?

ak najin hk take yayi kicin kicin da rai sannan yace "eh lisafinki hk ne sai dai babu inda zata ammi nifa bana ra'ayin zuwa wanka jegon nan da'ake wani zuwa kwata kwata baya cikin tsarina..

ran ammi yasoma 'bace ta dubi su'ad dake tsaye tana dubansu tace "ke karki soma yarda da wannan tsarin nasa cutarki zai yi, ki hadva kayanki wani sati zanzo na tafi dake ..

su'ad tayi saurin cewa 'to ammi ko ma nabiki ne yanzu mu wuce, AK ya watsa mata harara tare da cewa "babu fa inda zaki malama dakike wani saurin amsawa ," ammi muje na sauke ki dan Allah , nifa yanzu abun a tausayamin ne zamanta kusadani shine kwanciyar hankalina idan kuma kin matsa lallai sai takoma gida sai dai mu tattaro mu dawo gabadaya .
"da wannan dabarar yasamu yaje ya kai ammi ya dawo ya iske su'ad zaune tana shan Fruit , bayanta ya zagayo tare da d'aura kansa a kafafarta yana goga mata sumar kanshi "sannu da zuwa har ka dawo?

yace "uhm "yanzu ni ba abun tausayi bane da kike kokarin barina 'yar kulawar ma danake samu tayi rauni ko ,"to abarmin ke ko kallon fuskarki na dingayi.
su'ad tayi murmushi tace "abdul kenan babu hakuri "amman ai kasan ina iyakar kokarina akanka ko ?
"yanzu me kake so ka fad'a min ko goyo ne zan goyaka i promise you .

yayi dry yace "dawani karfi zaki goyani?

"da karfina mana ya kwashe da wata dry yace" ai ko ina hawa bayanki zaki fara nakudar dole "kija min maseefa ina zaman zamana, ta lagwabe ajikinsa yana wasa da jelar kitson kanta.


lokacin da cikin su'ad yacika wata tara yayi wani irin girma na ban mamaki kowa yaganta sai yayi mata sannu zama da kyar tashi da kyar ,shi kansa AK daya hanata komawa gidan ammi a takure yake dan yayi bala'i tausaya mata gani Yadda ta kunbura dan EDD dinta ya cika har ya wuce,amman haihuwa shiru ammi ta sake yiwa ak zance "abdul ka kawo yarinyar na ta haihu a gida saboda kai daita duk baku da exprence akan haihuwa ,kar haihuwar tazo mata cikin dare kurasa yadda zakuyi dan komai zai iya faruwa azo ana da'ansani zantukkan ammi suka sanyaya masa jiki ,gashi baya son rasa matarsa wannan tunanin yasa yaji hankalinsa ya tashi matuka dan hk ya tattarata yayi gidan ammi daita tunda ta koma gidan ammi kullun yana gidan safe da yamma har ammi tace "ya tattaro kayansa kawai ya dawo shima hb wani irin jaraba ne da tsohon ciki baza'a bar yarinya ya huta ba a dinga na nukurkusanta kenan .

yana jin zantuttuka ammi kuma yasan sarai abinda take nufi, amman ya make tunda shi yasan bawani abu yake mata ba daya wuce kulawa, shi kansa tausayi take bashi a halin datake ciki gbdy ma jiyayi sha'awarsa ta tsaya cak, hkn ya tabbatar masa da ita din yake so bawani abu nata ba.

ranar wata al'hamis su'ad ta tashi da ciwon nakuda kafin akaita hospital har ta haihu agida ,ta haifi 'yan'biyu mace da nmj ,santalelen yaronta kamar ubansa sak tmkr yayi kaki, da santaleliyar yarinyarta kamarta sak ,kuma duk suna cikin koshin lfy ita da bby's," fad'ar murna gun ak da ammi da umman su'ad har ma da dagin tmkr bata baki baki ne.

bakin ak yaki rufuwa saboda tsananin murna da farinciki rana suna bby's sukaci sunan dady da ammi baraka da Adam ake kiran nmj da farhan macen kuma da ihsan, bakaramin 'barnar kudi ak yayi ba a wannan haihuwar da aka masa. dan hatta ma'aikatansa sai da suka san me gidansu yana cikin farinciki dan har karin albashi yayi musu, hk ma umman su'ad da danginta sunyi kokari matuka ,madam ma shemah ba'a barta abaya wajen nuna bajinta, yan biyu sun sha Kyauta agurin jamar gari .

su'ad tacigaba da zama wankan jego tare da ammi, tana samun kulawa sosai dan wani lokacin idan yaran sun tashi cikin dare su'ad na tashi ,itama ammi ke tashi su'ad nabawa daya nono ita kuma ammi zata had'awa daya madara dan nono uwar bazai ishesu ba.

su'ad na tare da ammi har byn arbain, sai da sukayi wata uku sannan suka fara shirin komawa, ammi tasamar mata mai aiki domin kula da yaran.

********


yau tsayin wata uku kenan da rasa zeey dakayi ,mafi yawa daga cikin yan'uwa sun taya mama jimamin abinda ya faru wasu kuma Allah ya kara suke mata ,acewarsu kyakyayi koma kan mashekiya ne ya faru da zeey ,ita dai mama a kowani lokaci ta tuna da tilon diyarta sai ta zubda hawaye hkn yasa duk idanunta sun gama kod'ewa tarasa wazata tunkara da matsalarta, domin a nemo mata diyarta ko babu komai takasance tare daita, yafi batasan inda take ba.
yanxu hk duk abun duniya yabi ya dameta kallo daya zakayiwa mama kasan tana cikin tashin hankali .

shekaran twins daya da rabi su'ad ta sake haihuwa tasu d'a namiji aka sanya masa emran ko wannan haihuwar bakaramin murna ak yayi ba.

*bayan shekara hudu*

duk inda mutun ya kai ga tunanin su'ad zatakasance ta wuce gurin ,ta had'u takoina zuciyarta na tsaye kyam akan kaunar mijinta da yaranta guda uku da allah ya albarkace da samu.
tabangaren ak ma sosai yake jin dadin zama daita saboda yadda take

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment