Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

love gsky ak na dade da kamuwa da soyayyar eiman amman narasa ta inda zan gaya mata sai yau,"uhm sai km yaya daka gayama what the she said?

"batace komai ba ina kokarin tace wani abu ne kazo ka rusa min budget dina gsky banji dadin fitowarka ba da yanzu nasan matsayina a zuciyarta"very good gara ma da batace komai ba sbd bazan baka Sister dina ba..

"kan wani dalili kasani ak ba tun yau ba asalima tare muka taso guri daya ne kawai ba a haifemu ba dan me zakace hk? kmr irin wanda kasani da mugun hali..

"dan Allah karka hanani auren eiman wallahi na maseefar kamuwa da matsanancin kaunarta...

"karka dameni nace bazan baka ba sister dina ba .

"coz of what?

"sbd kai dan shaye shaye ne kasha giya kasha taba kasha wiwi shine zan dauki kanwata na baka dan bansa ciwon kaina ba, duk rana da kasha tai maka karo ka dawo gida ka lakada mata duka, ina ai bama zai yiwu ba ka kaje wani guri ka nemi mata amman ba eiman ba..

"hb ak karkace hk iya abinda nake yi kenan km cikin kaso dari na daina 70 sauran 30 shi ma zan daina wallahi kaji na rantse daga ranar danasamu eiman matsayin matata na daina shan komai "ok har ma sai ka aureta zaka daina wannan ai shirmen banza ne.

"naji na daina daga yau daga rana me kamar ta yau na daina shan komai dan Allah ka taimakeni ka aura min ita yakarasa mgnr cike da marairaicewa ak yayi sororo yana duban musty cike da mamaki .

"ak kasanya ido sosai akaina muddin kaga nayi kuskuren shan wani abu na yarda ka hanani aurenta.

"kaga malam karka dameni da zattukanka na banza da wofi ko ina zan dinga binka yawo ne ,ka make kawai ka nemi wata.

"kaga banson rainin hankali sai wani binka nake kana zamemin ,kai meye bakayi ba?

"da bakayi shaye shaye amman yan'mata nawa kayi mostivetion dasu kafin ka shiryu kayi aure, "ai wallahi garani shaye shaye ne kawai shima bana rashin hankali nake ba, dan duk shaye shaye na ban taba fadawa quater an cironi ba, idan baka yarda ba sai inbi tasa tunda nasa ko burkutu nake sha idan dad dina yasame dad din'ka da zance dole a aura min eiman yana gama fadar hk ya juya fuuuuuu ya shige cikin motarsa.

ak kuwa me zai idan ba dry ba dry yayi sosai har da rike ciki yana nuna musty da yatsansa tare da cewa "wani fa ya haukace akan love..

"musty dake shirin tada motarsa yace "naji amman duk haukata akan lov ban kai ba dan iska kawai yasoma kokarin murza sitiyarin mota.
ak yacigaba da yi masa dry kmr wani zautacce har musty ya bar gidan dry yake..

yau takama tafiyar ak kasar koria yana zaune. tare da ammi yana mata sallama amman gbdy hankalinsa da nutsuwarsa basa cikin gangar jikinsa sbd bai ga ala'mun eiman ta shawo masa kan su'ad ba, duk mgnr da ammi take masa basa shiga cikin kunnuwansa, burinsa kawai yaga fitowar su'ad da niyyar yi masa rakiya airport, addua kawai yake acikin zuciyarsa ya Allah kasa ta amince da rakiya nan ,cikin ikon Allah sai gasu sun fito ita da eiman tunda ta fito ya kafeta da mayatattu idanunsa yana kallonta sanye cikin wasu haddaun bakaken kaya riga da wando sai farar riga me dagon hannu daga cikinta ,ta daura after dress asamanta hannuta daure da agogon fata baki, tai Rolling kanta da mayafin after dress , flat bby shoe ne red sanye da kafafunta tayi wani irin azababben kyau," gsky ban da tafiya zaiyi daita da bazai bari ta fito hk ba, killace abarsa zaiyi kawai km ban da ammi dake gurin cewa zaiyi takoma ta sauya wasu kayan amman yasan yana yin wani abu karsheta ya rusa plain dinsa akanta, dan hk ya mike tsaye yana sake yiwa ammi sallama yayi gaba abinsa.

eiman tasanya kai ta fice tare da cewa "ammi sai mun dawo su'ad ma har takai bakin kofa tana wa ammi sallama ta dawo baya kadan gabanta na faduwa tana jin kmr karta tafi rakiyar "ya'akayi mamana ko akwai matsala ne?

girgiza kai kawai tayi tasoma tafiya kmr kazar da kwai ya fashewa aciki "idan bazaki rakiyar ba kiyi zamanki man. kmr tace to km ta kasa mgn .

can waje kuwa AK ne ke zubawa eiman maseefa ina tabar su'ad .

"wallahi yaya ban san me ta tsaya yi ba amman bari na dubuta ta juya cikin sauri.

can sai gasu sun fito tare hannunta rike cikin na eiman tana tafiya ahankali kmr batason taka kasa, naunaiyen ajiyar zuciya ya sauke yashiga byn mota ya zauna har bakin motar eiman ta kaita ta bude mata kofar motar tashiga ta rufe ta karasa tashiga dayar motar .

daga ita sai shi acikin motan sai direba dake mazauninsa hk kawai ta tsinci kanta cikin yawon jin faduwar gaba idanunta suka cicciko da hawaye ta dinga jan numfashi da kyar tana fitarwa hankali yayi matukar tashi hk kawai taji tana zubda hawaye sanda suke gifta unguwarsu ummanta ce aranta kmr tace a tsaya tashiga amman tasan mgnrtata bazatai wani amfani ba ga mutumin take mahaukacin so.. kawar da kanta tai gefen titi tana kallon motoci dake wucewa tana cigaba da kuka..

"sautin kukanki na dagula min lissafi ,yayinda kwalkwaluwata ke cikin over thinking ,"ki tsagaita kukan nan zuwa gaba ko zai miki amfani kunnuwanta suka jiyo mata sautin muryarsa yana mata mgn cikin sanyi kmr ta juyo garesa ta sake kallon yanayinsa sbd yadda muryarsa ta fito din kmr yana cikin damuwa amman sai ta fasa tacigaba da kallon gefen titi.
ya motsa labbansa zai sake cewa wani abu sai km ya fasa ya ciro wayarsa data dauki karan sauti me dadi yanayin yadda yake amsa mgnr tasan musty ne wayar suka cigaba da yi har suka iso airport wanda dole tasa ya takaika mgnrsa ya katse kiran.

yana gaba suna biye dashi a baya ita da eiman airport din cike yake makil da tarin jama'a wadan yawancinsu duk matafiya ne zuwa kasashen duniya
ahankali ta lura yana rage saurinsa zuwa tafiya ahakalin har takaraso garesa.
ala'mun yayi mata tayi gaba byn ya dakatar da eiman wanda ita bata lura da hkn ba gaban tayi kmr yadda ya umarce sbd idanun mutane da ke kansu tasan halinsa ganin mutane bazai hanashi shuka mata rashin mutuncinsa ba sai dai idan bata kuskure masa ba.

ahankali sukacigaba da tafiya duk takun datai idanunsa na biye daita jikinta kebata idanu na kai kawo akanta hkn yasanya jikinta daukar rawa gabanta yashiga faduwa da sauri sauri kafafunta suka soma rawa rawa batare da ta ankare ba kafafunta suka harde tana yunkurin kaiwa kasa cikin zafin nama ya tarota ta fada kirjinsa rungumeta yayi tsam ajikinsa batare da wani shaka ba sannan ya rada mata sannu cikin kunneta "ki bi ahankali cikin siririyar muryarta ta amsa da to ahankali ya dago idanunsa yaga yadda idanunwa mutane sukai caaaa akansu ciki kuwa har da wani abokin kasuwancinsa kamal wanda gbdy idanunsa da natsuwarsa nakan su'ad .
wani irin tuttukin bakinci ne me tattare da kishin matarsa ya caki tsokar dake makale da kirjinsa kawar da kansa yayi ahankali ya tsuguna har kasa yana duba kafafunta sai daya tabbatar da bataji rauni komai ba ya sake cewa "ki natsu plz naga duk kin rude bawani gurin zan tafi dake ba .
kmr ta tbyeshi eiman kasancewar yanzu dayake tsugunne a gabanta ta juya bata ganta ba, amman tayi sh.

mikewa tsaye yayi tare da cewa " muje ko ta dai kasa hkr sai da tmbyesh.

"abdul wai ina eiman? tayi mgnr muryarta a sanyaye.

mayatattun idanunsa ya watsa mata su cikin wani irin salo na shaukinta kana yace na aiketa yanzu zata dawo tayi mamaki kwarai sbd ita bataji sanda ya aike din ba.
kwata kwata hk kawai takasa yarda dashi zuciyarta takasa samun natsuwa "ok bari najira anan ya watsa mata harara wanda yasa ta gigice tana shan jinin jikinta yayinda still idanu mutane ke kansa tun datake arayuwar har zuwa lokacin datayi zaman tantiranci bata taba zuwa airport ba wannan shine karonta na farko data sanya kafafunta cikin aiport tasan km hkn yana da nasaba da rudewarta .

ahankali taji ya rike hannuta cikin nasa yana massaging ahankali ahankali yana cigaba da tafiya tare da daita.

koda suka karaso reception baifi sauran minti goma jirginsu ya tashi ba ,kallonsa take cikin wani yanayi , shi km yana duba agogon diamond dake daure da tsintsiyar hannunsa can akasoma sanarwa matafiya su shiga jirgi abunda yabawa su'ad mamaki bai wuce hannuta dataji AK ya sake damka cikin nasa ba yasoma tafiya daita agigice take binsa da wani irin kallo ahankali aka gama duba kayansa kadai dan ita ba da komai sai yar jakar rataye data makala itama babu komai ciki sai wayar hannu da yan tarkacenta kai tsaye harabar inda jirgin yake suka nufa "ki natsu ki daina zazzare idanu hk kar mutane su dauka satoki nayi gabansa yasata yana biye daita abaya har cikin jrgin kai tsaye kujerun da'aka tanada na VIP suka nufa yasanya ta gurin window shima ya zauna gefenta ya hade fuska dan ya lura da yanayinta tana iya yin abinda zai saka mutane su gane ba'a son ranta take zaune ba .
cikin mintuna da basu wuce 30 ba jirginsu yasoma shawagi aiko su'ad ta kamkame jikinta dan ji tayi kmr ana ya mutsa mata kayan cikinta ne.
satar kallon yayi kadan ya kawar da kansa sai lokacin yayi tunani may be wannan shine Karonta na farko data shiga jirgi ba ta saki jikinta ba sai da jirgi yai balance a sararin samaniya .

Wani zama ne sukayi cikin jirgi,tunda suka shiga babu wanda yayi wani mgn sai da tafin hannunta na cikin nasa yana massaging ahankali ahankali .

wannan abokin kasuwancinsa ne yayi masa magana wanda tun shigiwarsu aiport din ya lura da yadda yake binsu da kallo, su'ad ta dubi fuskarsa taga ya maseefar tsare gira kmr wanda aka aikowa da mutuwa ,kasancewar yasan halin mutumin mugun mayen mata ne, idanunsa basa ganin mace ya kyale mugu mugun dan harka ne na bugawa ajarida sbd tsabar jarabar neman matansa yasa duka matansa suka kasa zama dashi ,ga dai kudi kmr ya kasheshi amman dukiyarsa na neman mata ne.

km wannan mutumin yasan halin AK ciki da bay hk shima ak kar tasan kar ne tsakaninsu sai duk neman matan ak bai kai kalma ba, kamal karshe ne km hatsabibi ne gurin harka da mata dan ya zarta ak . duk macen da kamal yaji yana sha'awarta ko matar aure ce sai yasan yadda yabi ya nemeta. ko yanzu dayake zaune daga dayan bangaren idanunsa na kan su'ad yana satar kallonta a ranshi ya furta Allah yayi halitta anan tunda yake bai taba cin karo da macen dayaji farat daya tashiga ransa ba kmrta zance zuci kawai yake yana kokarin sake kallonta idanunsa yayi clashing dana AK. da idanunta yayi masa gargadi sannan ya kare matarsa sosai ta yadda babu yadda za'ayi yaganta duk nacinsa.

har wannan lokacin a dan tsorace su'ad take dan jikinta bai bar rawa ba ganin hk yasakashi yasanya tafin hannunshi cikin nata yana sake matsowa kusa daita sosai yana mata magana kasa kasa,duk wanda gansu zai gane suna cikin shaukin soyayyar juna .
ahankali yake mata mgn cikin kwantar da murya
"Banson ki sakawa zuciyarki damuwa ina matukar son kasancewa tare da domin in dawo da soyayyata cikin zuciyarki shiyasa nasatoki tunda mamanki takibani hadin kai, dan hk kibini a hankali" yanzu kina cikin doka da orde ne.
kirjinta ya dinga budewa maganganunsa na masu masauki na musamman yayinda zazzafar soyayyarsa ke sake kawo ma zuciyarta ziraya yana fixgar tsokar dake makale akirjinta .
wani irin sauyin yanayin take ji ajikinta sbd taushin laulausar tafin hannunshi da ke ratsata yana circulating every part of her ,yayinda shima ya tsinci kanshi cikin yanayi datake ciki sai dai shi ba lallai ne a fuskanci hk ba .

ahankali taji ya sauke boyayyar ajiyar zuciya lokacin dayake jin yadda dumi tafin hannunta ke ratsashi yana bin kowacce jijiya dake zagaye da jikinsa.

ganin yadda ta runtse idanunta ala'mun sakon dayake aika mata ta tafin hannunsa yasoma tasiri ajikinta yasa cikin sanyi muryarsa yace
"Kwantar da kanki a saman kafadata idan kina jin bacci ne .

idanunta ta bude ta waigo gareshi tana dubansa sai taga shi din ma ita yake kallo ta kawar da fuskarta, shi km yasoma daddana wayarsa.

,a hankali ta dora kan nata saman kafadarsa kmr yadda yabata umarni ,dumin jikinsu ya soma gauraya atsakaninsu yana kaiwa kowanensu farmaki taja wani irin numfashi da kyar wanda ya shako mata daddande kamshin turaren jikinsa,kana ta sauke numfashinta a hankali tana lumshe fararen idanunta ahankali kamshinsu dake gauraye da juna yashiga bada wani sihirtaccen kamshin na daban sosai take jin dadi kamshin turarensa dake bugar mata hanci.
numfashi take ja sama sama kmr me cutar asma tana fesarwa ahankali shima numfashinta da kamshin turarenta ke kaiwa zuciyarsa farmaki wanda yake neman caza tunanisa, kokarin control din kansa yayi dan ji yake kmr ya kwantar daita ajikinsa ya daura bakinsa kan nata ko zai dan samu natsuwar zuciya .



Jin bai sake yunkurin ce mata komai ba .
yasanya itama taki
bude idanunta ko daga kanta ,tayi lamo akafadarsa tana shakar daddadan kamshinsa,a hakan batasan sanda bacci yayi nasarar daukarta ba .
ya gyara zamansa ya tsura mata idanunsa yana kallonta .
ahankali yake jin yadda zuciyarta ke bugawa a nutse,wanda hakan ya tabbatar masa da baccin take.

ya jingina da kujerarsa shima yana lumshe idanuwansa dan shi kadai yasan yanayin dayake jin kasa akanta.

kwana sukai suna tafiya acikin jirgi sai wuraren asuba suka isa Thailand daga nan suka dan huta na minti goma sannan suka dauki hanya zuwa koria atakaice sai da suka yi kwana da yini suna tafiya acikin jirgi sanan suka isa kasar koria.
Cike da nutsuwa fasinjojin dake cikin VIP suka soma sauka daya bayan daya daga cikin jirgin wanda mafi yawanci yan kasuwa ne da masu fada aji a kasar Nigeria .
ahankali ya waigo inda take tana bacci yana kallonta,bata motsa ba a hankali yasoma busa mata iskar bakinsa har gashin dake kwance a kyakkyawar fuskarsa gogor nata fuskar , ta bude idonta.
fesss idanunta suka sauka cikin mayatattu idanunsa, idanunsu sukar sarke cikin juna batayi yunkurin dauke idanuta ba kmr yadda shima yake kallo cikin kwayar idanunta ahankali ta daga kanta daga jikinshi tana gyara zaman rolling din mayafinta daya dan zame,baice mata komai ba ya dauki jakarta ya riko hannuta cikin nasa yasoma tafiya daita tana biye dashi kmr wata hand bag dinsa.


sir mahbub ne ya turo da manya manya motoci na alfarma dake mallakinsa tare da securities wadan nan
ratsatsun motocin suka tsaya agabansu aka budewa AK byn mota wata hadaddiyar mota daga cikin motocin da suka zo daukarsu .

tunda suka fito harbar inda motoci suke yaga yadda kamal ke bin su'ad da mayataccen kallo kmr zai ciyenta ,hkn yasa zuciya tazo masa wuya ahankali ya sanya hannunsa ya shafa sumar kanshi domin samun natsuwar zuciya yakasa shiga motar yakarasa har inda kamal yake , ya tsaya agabansa tare da zube duka hannuwansa cikin aljihun wandonsa yana kare masa kallo shi din ma kallonsa yake cikin sauri kamal ya mikawa ak hannu amman yaki bashi hannunsa hk jiki a sabule ya kawar da hannusa matso kamal ak yayi sosai yana Huci "ina bukatar ka dauke wad'an nan mayun idanun naka akan iyali if not I will suprise you.... kana ya juya cikin takunsa na isa yakarasa inda ya bar su'ad tana zare idanu.

kamal yabi bynsa da kallo yana jin bugun zuciyarsa na karuwa gsky shifa yarinyar tayi masa ,gashi ta hadu iya haduwa bakaramin tafiya da eimaninsa tayi ba ai idan yasamu irinta bazai yi ganganci sakinta kmr yadda yake sakin sauran matarsa ba .
take zuciyarsa ta buga da matsanacin karfi tuno da mgnr AK "ka dauke wadan nan mayun idanunnaka akan iyalina... kalmar iyali fa na nufin matarsa gsky ban yarda ba wallahi .

badan tare da AK take babu wanda ya isa ya hanashi kusantarta koda kuwa ta karfin tsiya ne lasar lips dinsa yayi km duk AK na lura dashi.

mutane dayawa suka zo tarbansa ciki kuwa har da musty amman bai yarda wani ya budewa matarsa mota ba shi da kansa yasa hannu ya bude mata motar yana tsaye abayanta ta shiga ta zauna daidai lokacin da kamal ya karaso daf dasu yana murmushin yake .

cikin dakiyar zuciya ya shiga tare da rufe murfin motan yana bawa driva umarni yaja suka tafi kallonta yayi a fusace yana zaro ido kmr mayunwacin zaki yayi kasa kasa da muryarsa kmr zai mata mgnr azirki cikin rada yace "kalli dan iskar shigar da kikayi wanda hkn yabawa wani banza kallemeki, "duk tarin siturinki ki rasa kayan dazaki saka sai wadan banzayen kaya yaja tsaki yana kawar da fuakarsa jikinta tabi da kallo dan ta gano illar shigarta , koina ajikinta a lullube yake baya ga fuskasta da tafin hannuwanta idanunta ne suka cicciko da ruwan hawaye tare sa kawar fuskarta gefen hawaye na gangarowa ta gefen idanuta .

Tun daga hanya take karewa garin kallo tare da mutane garin masu fasali da aljanu har suka isa kawataccen hotel din da zasu sauka.
wanda ya amsa sunansa hotel ne wanda manya attajirai, ko kusoshin gwanati wad'anda suka ci suka koshi ne zasu iya zama cikinsa.
hotel ne mai kyau da tsari,duk wanda kaga yakama hotel din to shahararen me hannu da shuni ne ,zamanka cikin hoter din tmkr kana rayuwa ne a muhalinka duk wani abun bukata akwai shi acikin wannan hadadden hotel din, daya amsa sunansa a duniya gbdy babu abinda zaka bukata ka nema ka rasa.

ahankali motarsu ta tsaya cikin farfajiyar hotel din shine yasoma fitowa ya barta zaune cikin mota.

shi da nustymusty ne tsaye suna mgn yayinda babban yaron sir mahbub ke kai kawo amsar musu daki kusan minti goma tsakani komai ya kammala ya budewa su'ad kofa ta fiti tafiya yasoma yi ahankali tana manne a gefensa yana rike da hannuta.
ta kowani bangare ta kalla ma'aikatan hotel din ke kai kawo daga maza har mata sanye da wasu haddadun suit
har suka karaso dakinsu hannuta na rike cikin nashi bai yarda yayi ganganci sakinta ba .


suna shiga dakin sanyi Ac ya ratsa ilahiri jikinta Komai a gyare yake tsab a dakin.

ahankali ya saki tafin hannunta zuciyarsa na harbawa har yanzu ya kasa hakurin iskanci da kamal yayi masa, yane shi da bai taba kusantar kowace mace da suna zina arayuwarsa ba byn matansa na sunnah ,bai taba tsayuwa da wata matar aure wace ba yar uwarsa bace ,shima tsayuwar baya wuce gaisuwa," ta yane wani kato zai dinga kalle masa mata har da lasar lip's wannan abu ya maseefar tsaya masa arai anya kuwa zai iya hakuri wannan iskanci wayoyinsa ya ciro gbdy ya watsar a saman gado .

ma'aikatan hotel din suka biyosu da manya hakunkunansu .

tsaye take har lokacin a gefesa tana dan kalle kalle a dakin kallo daya zaka mata kasan wannan shine Karonta na farko data sanya kafa zuwa wata kasa.

takaicinta bai sa saurareta ba ya matsa kadan daga gefenta yayi tsaye gaban gado yana k'ok'arin sassauta tie din wuyansa,yana son rage daya daga cikin rigunan dake sanye a jikinkinsa .

daya daga cikin wayoyinsa daya watsar a saman gadon ta dauki karar sauti me dadi sai da kiran ya katse bayan ya gama sassauta tie din wuyansa sannan ya dauki wayar yana dubawa,hannunshi daya riqe a kugunshi yana takawa ahankali zuwa bakin window hotel din,ya zuge labuyen yana kallon harabar hotel din , yana mgn atsanake ta dan saci kallon yanayinsa taga har lokacin fuskarsa a hade take kmr wanda aka aikowa da sakon mutuwa duk km sai taji babu dadi zuciyarta tashiga damuwa da halin dayake ciki kmr takarasa gareshi ta runguneshi tabashi hkr sannan tace ya dan saki ransa, ammam fargaba abinda zai mata ya hanata ta manna jikinta da bangon dakin tacigaba da kallonsa tana sauke jiyar zuciya .oh Allah ko ta ya ne zansoma rayuwa dagani sai shi
,ta fada hk cikin zuciyarta tana runtse idanunta Tare da dunkule hannaye.

tsawon lokaci ya dauka yana waya da wanda taji yana kira sunansa da sir mahbub sannan ya katse kiran yashiga wanka cikin sauri sauri ya fito yace tashiga wanka shi km yasoma shirin fita tana tsaye tana kallonsa ya sake kaya zuwa wasu kananun kaya masu matukar kyau da daukar hankali kayan su amshi jikinsa matuka sosai suka sake fito da ainihin surar jikinsa ahankali muryarsa ta fito "ina zuwa zanje mu hadu da sir mahbub bazan dade ba zan dawo ya nufi kofar fita .

"Allah ya tsare ya dawo da kai lfy ....

da sauri ya dan dawo yana zaro idanu waje yana dubanta cike da mamakin jin furucinta ya lumshe mayattun idanunsa tare da furta "woww tun yanzu yarinya karki min hk man plz banason kiyi saurin yin ladaf tun yanzu ba gsky. yakarasa mgnr yana fice daga dakin ya kulleta ta baya.

numfashi taja ta sauke da kyar tare da cewa masefaffe kawai , da ba'a ayi masa gwaninta , idan bakayi ba yace bakayi ba idan kayi ya gwasaleka.


zakaye dakin tashiga yi tana karewa yanayin gurin kallo , dakuna ne guda biyu wannan datake ciki babba ne sosai dauke da makeken gado brow colour wanda aka shimfidesa da laulausar zanin gado fari sol sai bargo daga gefe ,sai doguwa kujera guda daya, can gefe km guda wordrob ne da mirrow bedside duk set ne da gadon dakin .
sai wanda suka baro kafin shigowarsu shima babba ne sosai dan kusan yafi wannan datake tsaye acikinsa girma zagaye yake kujeru masu kama da italy bed da frigde daga gefe .

ahankali ta sake fitowa parlour inda idanunta suka sauka ta gefen damanta tasoma takowa ahankali cike da matsanancin farinciki har takarasa ta yaye labulen datagani wani madaidacin bancoly tagani wani irin tsalle tayi hade juyi tana rungume hannuwanta duka a kirjinta tana shakar iskar garin .

"guri me kyau"

jikin karfen takarasa tana kallon tsirarrun mutane dake kai kawo cikin hotel tare da sake bayyana farincikinta ahankali ta sake furta "gsky gurin nan ya tsaru sosai "gurin abun sha'awa zanji dadina .

ta dauki tsawon lokaci tana tsaye a bancoly har sai data duba taga lokacin sallar azahar tayi sannan ta dawo dakin ta shiga toilet .

bathroom din tsab yake yana bada wani cent din kamshi me dadi tayi wanka tare da dauro alwala ta fito ,sai data kammala sallar sannan hankali ta mike takarasa inda taga jakunkuna guda biyu ta janyo daya tare da zuge zip din ,kayansa tasoma cin karo dashi ajere gwanin sha'awa suna fidda kamshi turarensa me sanyi dadi da taba zuciya haka ta dinga fitar da su tana jerawa a tsanake ta sake janyo dayar jakar abinda yabata mamaki bai wuce ganin kayanta shake

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment