Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gama lfy "daman duk wannan tashin hankali da maseefun bai saka kin zubar da mutuncinki ba kai naji dadi sosai wallahi banyi tunani kin tsira da budrcinki ba ammi takarasa mgnr tare da riko hannun su'ad cikin tana murmushin jin dadi .

yadda maman zeey ke fakaicewa tana dirkawa diyarta magunguna mata a boye hk ma ammi take bawa su'ad maganin mata wanda ita su'ad din har ta soma gundura da shan wadan nan magunguna da'ake banka mata kullum.
kmr wancan lokacin data daukowa zeey me gyaran jiki hk ma wannan karon ma yakasance ta daukowa su'ad sai dai wata mata ce daban sabanin wace tayiwa zeey.

inda me gyaran jiki tashiga aikin daya kawota cikin kwana biyu har fatar su'ad ta sauya tayi wani irin azababben kyau ga wani sihirtaccen kamshin turaren amare na musamman dake tashi ailahirin ajikinta duk inda ta wulga sai tabar kamshin turarenta me matukar kama jiki kana ganinta kaga amarya sak, tayi haske fatar jikinta tayi luwai luwai sai sheki take da daukar hankali kmr ka tabata jini ya fito jikinta yayi wani haske na ban mamaki asalin farinta na ainihi ya sake bayyana idan kaganta sai kaji kmr ka sureta ka gudu.

musamman ammi take ware lokaci sosai ta sake shirya su'ad da kanta tana sake dirka mata maganin mata, dan karta zama baura agurin mijinta sbd lura datayi da maman zeey ta diyarta kadai take musamman zata saka Zeey gaba babu kunya balle tsoron allah tana bata hakin maye.

tun bayanin da ammin tayi masa akan zance mlm , ya dauki tsanar duniya ya daurawa su'ad ko kallonta baya kaunarki yi balle ya daura idanunsa akanta ya sake canzawa tare da jin mugun tsanar su'ad din cikin zuciyarsa, gbdy duk wani salon iskancinsa daya soma ajiyewa ya dawo shi sabo fil..
babu abinda ke shiga tsakaninsu sai mugun kallo da harara wulakacin da musgunawa hade da zagi marasa dadi ,tare da sake jaddada mata kalmar karuwanci .

wani sa'in ma har da gayya yake hadawa gurin yiwa zeey wasu abubuwan da wasu salon iskanci yayinda gefe guda km tunani su'ad na nan makale cikin zuciyarsa.

sosai aka shiga hidamar auren,, umman su'ad batazo ba amman ta wakilta wasu daga cikin mutan unguwarsu wadan take mutunci dasu suzo su wakilceta, sun hallarra domin dasu ake ta duk wani shige da fice acikin gidan .


kuka sosai ta kwana tana yi har waye washegarin daurin aure wanda hkn yasa ta tashi batajin dadin jikinta dan gbdy ko kwakwarar motsin takasa yi sakamakon tuzarcin da cin mutuncin da ak yayi mata a daren jiya agaban zeey .
ita din auren saurayi da buduwar zasuyi ba'a auren saurayi da bazawara ba sweet baby ki daina taba hankalinki akan wannan har kiyi kishi daita, kin zartata a komai sosai su'ad ke kuka lokacin da komai ke dawo mata eiman ce ke rarrashina dan Allah aunty ki share hawayenki ki daina kuka yau ranar farinciki ce gareki ki kwantar da hankalinki wata killa daga yau kinyi bankwana da bakincikin yaya sai dai farinciki akwai lokacin da zaki nemi wannan tsanar tasa ki rasa ina tabbatar miki wata rana sai kinyi alfahari da kasancewarki matarsa .

su'ad ta tsurawa eiman idanunta cikin muryar kuka tace wai me nayiwa abdulkabir da zafi hk yake min wannan zazzafar kiyayyar?
wayyohhhly Allah nashiga uku bani da sa'a aray....eiman tayi saurin rufe mata baki barki ce hk pls babu abinda kika masa zallar iskanci ne darashin tunani ke damunsa amman da sannu zai gane mahimmanciki gareshi da kyar eiman tasamu ta lallabata ta tashi sukayi sallah sannan sukayi wanka.

misalin karfe tara da minti goma jama'a an hallara a kofar gidan ambasodor adam kofar gidan ya cika makil da tarin jama'a kama daga manyan attajirai zuwa kososhin gwanati kanan ma'aikata zuwa talakawa ta fanin ambasodor adam, data bangaren dagin mahaifin Zainab dagin mahaifin su'ad suma sun hallarar ta bangaren ummanta ne dai ba'a samu ko mutun daya ba.

auran Zainab aka soma daurawa , sannan aka daura na su'ad wanda minister dr Mubarak ne yabada aurenta akan sadaki dubu dari biyar kmr yadda aminin dady km mahaifin musty wato alhj jafar ya bada a auren auren zeey .

jin ihun kururuwar an daura auren yasa hankalin su'ad mugun tashi ta dinga jin kmr ana kwara mata ruwan sanyi ne ajiki barin ma dataji haniyar shigowar AK tare abokansa suna biye dashi abaya, sanye yake cikin wata hadaddiyar farar shadda gezner babbar riga me hannun link's da malulun a samun rigar wanda tasha aiki ajikinta sai hula me dauke da kalar aikin dake jikin shaddar sai agogon diamond dake daure da tsintsiyar hannunsa kafafunsa rufe cikin takalmai disigner suna zuba kyalli fuskar nan tasa sai sheki taki zubawa sbd gyaran fuskar da yayi , wani irin azababben kamshi turare ne me gauraye da sanyi dadi da bata zuciya ke tashi a gbdy ilahirin ajikinsa kallo daya zaka masa kaji yayi maseefar shiga zuciyarka tare da birgeka . gurin zeey suka fara zuwa byn an daura aure suka sha hotuna sosai .har zai wuce yayi tunanin matsawar bai xo gurin su'ad ba zai iya haduwa da bacin ran ammi ,shi km abinda bai kaunar faruwarsa kenan acikin wannan dan lokacin albarkata kawai yafi bukata.idan ka kalli fuskar abakan ango cike take da matsanancin farinciki banda fuskar ak wanda ke tattare da bakinciki da tarin damuwa kallo daya zaka masa kasan zuciyarsa dankare take taf da tsagwaron bakinciki

su'ad dake kwance kuryar dakin ammi ta sake kudindine jikinta daya dauki rawa waje daya wani sabon tsoro da fargaba ya suka taru suka kawo mata ziyara lokacin dataji amon sautin muryarsa yana tmbyrta gurin eiman tana jin eiman tace tana kuryar dakin ammi .

yayi jimm tare da yin shr na minti goma sannan yacewa abakansa yana zuwa ya barsu tare da su eiman ahankali ya nufi cikin dakin ammi yana jin zafi cikin ransa gbdy bakinciki da damuwarsa sun addabi zuciyarsa bakincikinsa daya ta yadda bazai fara kusantar zeey ba ,sao wata su'ad banzar karuwa wace tagama rabawa gayyu jikinta atiti ......
yana karasa shigowa dakin idanunsa suka sauka akanta can ya hangota kwance akan gadon ta rufa da bargo ganin yadda take rawar jiki yasa yayi saurin karasawa gurun gadon ya zauna yasanya hannusa ya birkitota tare da daura kanta bisa cinyarsa muryasa a matukar harzuke "yace ke lfyrki kika wani dukunku ne guri daya?

ta bude idanunta da kyar tare da yamutsa fuskarta ala'mun rashin lfy "kaina ke min wani azabben ciwo takarasa mgnr hawaye na biyo gefen idanunta .

"shine km dan iskanci ki kayi shr bazaki sanar ba ? ta runtse idanunta gam kirjinta na bugawa daf daf da sauri..

wani dagon tsaki yaja tare da mikewa tsaye ya fito daga dakin a babban parlour 'n part din ammi yaga ammi cikin mutane ana mata allah yasanya alkhairi ya sanar mata su'ad ba lfy yana gama gayawata ta rude wanda yasa ta rage sautin muryarta gurin amsawa jama'a tare da cewa subuhanallah muje ka kai ta asibiti mana, bari ma dai naje naga halin datake ciki ta juya da sauri ta shiga cikin dakinta inda ta wuce su eiman zaune ta nufi uwar daka AK na biye daita .

lokacin da suka isa dakin abin ban mamaki ammi ta bude bargon da su'ad ke lullube ciki ta sanya hannuwanta duka ta tabata amman sai ji tayi babu wani ala'mun motsi tare daita ammi tace inna ilaihi rajiun..........

mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH

*Allah messenger saw said fasting is a shield against sin's*

page 56

ahankali AK cikin sanyi murya yace, "me ya faru ammi?

yana me karasowa kusa da ammi cike da hanzarinsa hankalinsa a matukar tashe.

ammi tace.
kmr bata da rai fa ".

a matukar harzuke yace, what me kika ce ammi?

yayi wani taga taga yayi baya baya sakamakon wani mahaukacin jiri dayaji yana neman kayar dashi kasa Allah ya takaita , ya samu ya jingina bayansa da bango daki take kansa yayi wani irin mugun sara ..

a matukar tsorace ammi ta waigo taga halin dayake ciki duk da itama cikin matsanancin tsoro da tashin hankali take amman kallo daya tayi masa tasan bazai iya jan mota ba.
dan hk ta fito daga cikin dakin da sauri tana fitowa parlour 'nta su eiman da sauran abonkan AK dake zaman jiran fitowarsa duk suka mike tsaye sbd ganin ammi ta fito cikin sauri sannan km a firgice.

"lfy ammi ? suka hada baki gbdynsu gurin tmbyrta .

"musty taimaka ka tsaita kan motarka su'ad ce babu lfy ko numfashi batayi a kaita asibiti abdul bazai iya tuka motar ba.

take hankalin jama'a dake gurin ya tashi matuka
gbdynsu suka nufi hanyar fita waje cikinsu babu wanda yayi ganganci shiga dakin da su'ad da ak suke sbd tsaro dan basu san halin dazasu tadda su'ad din cikin ba.

ammi wace ta rude ta gigice tarasa takamaiman abinda yakamata tayi ahalin tashin hankali datake ciki madadin ta koma cikin daki gurin su'ad sai tabi bynsu zuwa harbar gidan nan fa hankalin
mutane yayi kanta suka shiga binta da ido sbd ganinta a hargitse.

nan take aka shiga tmbyrta abinda ke faruwa bata tsaya kulasu ba ko amsa tmbayoyinsu ta nufi gurin direbanta tayi masa mgn ya fito da motatar da sauri zasuje hospital sannan ta sake juyawa zuwa cikin part dinta
da wani saurin.

wanda zuwa lokacin AK ya samu karfin halin karasawa inda su'ad take kwance ya tallota zuwa jikinsa ya tsura mata idanunsa da suka gama birkicewa zuwa wani launi na daban yana kare mata kallo, wani irin tiririn zafi ne ke fitowa daga jikinta yana ratsa tafukan hannunwansa kansa ne yacigaba da sarawa ahankali ya gyara mata doguwar rigar dake sanye ajikinta wace ta yaye ta bayyana santala santalar cinyoyinta dake fitar da wani sheki da hasken kyau, kmr wace take amfani da madara ajikinta ,hk kawai ya tsinci kanshi da rungumeta ajikinsa yana shakar kashin turaren jikinta tare da busa mata numfashnsa a hk ammi ta shigo dakin ta samesu yana ganinta yayi saurin waskewa tare da zameta ajikinsa .
ya yunkura tare da su'ad ajikinsa ya sabata a kafarsa suka fito daga dakin ammi na biye dashi abaya cikin matsanancin sauri agigice cewa "kayi sauri abdul kar wani abu yasameta har suka iso parlour inda dandazon mutane ke tsaye cirkocirko.

kai tsaye inda motar musty yake pake ya nufa daita wanda zuwa lokacin har musty bude masa byn motar ya kwantar daita yashiga ya zauna tare da daura kanta bisa cinyarsa musty da malik suka shiga gaban motar suka bar gidan aguje .

yayinda ammi tashiga motarta ita da eiman direbanta yaja suka bi bayan motarsu ak aguje nan sukabar mutane cirkocirko kowa na fadar albarkacin bakinsa tare da Allah ya bata lfy.

cikin kankanin lokaci suka isa hospital, gadon tura marasa lfy aka turo aka daura Su'ad akai ,da gudu gudu sauri sauri aka shiga daita dakin likita domin a samu a ceto rayuwarta likitoci suka dukufa a akanta sai bincike matsalar suke .

ammi da ak kuwa sun kasa zaune sun kasa tsaye ,AK banda zariya babu abinda yake domin shi kadai yasan cikin tashin hankali daya tsinci kansa ciki.

wani likita ya fito daga dakin da'aka kwantar da su'ad.

ammi da ak naganinsa sukayi saurin suka rufa masa baya zuwa cikin office dinsa byn ya zauna yayi musu nuni da su zauna likita ya kalli inda ak ke zaune tare da cewa "kaine mijinta?

da sauri yace eh yaya akayi doctor ta mutu ne?


doctor yace "a'a tana raye bata mutu ba ta samu jijiga ne na zuciya sakamakon jinita da yayi mummaunan hawa .

"ya'akayi kuka bari hkn ya faru daita ?

ammi taja naunauyen ajiyar zuciya tare da numfashi ta sauke atare tana furta alhamdullahi Allah na gode maka da bata mutu ba.

ak ya fuskanci Doctor sosai yace babu wanda ta fadawa bata da lfy.

Doctor ya dan yi rubutu a saman farar takarda sannan ya dago tare cewa "yanxu dai xuwa wani lokaci zata dawo daidai sai dai a dinga kula da yanayinta, a guji abinda zai dinga taba mata zuciyarta, yadda jini ba zai sake hawa ba idan jinita yana hawa dayawa irin hk zai iya mata lahani ko haifar da wata matsala ..

shiru shiru su'ad bata farfado ba doctor suka sake yin tsaye akanta yayinda hankalin ammi da AK ya sake tashi matuka, ga dai su'ad kwance amman babu numfashi attare daita office din likinta ammi da Ak suka sake komawa tayi masa korafi yace" kuyi hakuri zuwa nan da goman dare mugani muna saka rai zata farfado.

ak ya saki wata zazzafar ajiyar zuciya tare da share wani gumi dayaketa faman tsatsafo masa a goshi kai kace wanda ya hadiye kunama .

karfe goma daidai tayi bata farka ba har washegarin ranar bata motsa ba kmr yadda likita yace hankalin ammi ya kai kololuwa gurin tashi ta kasa zaune ta kasa tsaye jikinta sai rawa yake ta juyo ta kalli inda ak ke tsaye rungume da hannuwana duka akirji tare da cewa abdul "ko za'a sanarwa mahaifiyarta ne?

uhm mu dai yi hakuri muga abinda Allah zai yi Inshaallahu zata samu lfy.

ammi jin ak kawai take zuciyarta na bugawa itama daza'a auna bp dinta a wannan lokacin definitely tasan za'a tarar da jininta yayi mugun high, ganin yadda hankalin ammi yayi matukar tashi yasanya ak binta da nasiha da rarrashi dan ganin kusan har tafishi shiga damuwa amman babu abinda ammi take fada Abdul kada yarinyar mutane ta mutu fa idan ta mutu yaya zanyi da tawa rayuwar ina matukar sonta.....

ak ya fara jin haushin wannan mahaukacin son da ammi takewa su'ad acikin zuciyarsa yaja tsaki sanin da yayi idan yayi a zahirance ranshi ne zai baci.

sai dai a dan zafafe "yace ammi ki kwantar da hankali babu wanda ya isa ya hana allah ikonsa idan zata rayu zata rayu idan mutuwar ce allah yabada ikon tafiyar duk kaunar da kike mata bazaki hana allah ikonsa a kanta ba?

idan ya karbi abinsa yaya zamuyi? ai yafi mu sonta dan Allah ki rage wannan son da kikewa yarinyar soyayyar tayi yawa yakarasa ransa a matukar bace sannan cike da takaici .

daddare dady da minister har ma da maman zainab da hjy kakar AK sukazo domin duba jikin su'ad cikin ikon Allah ta farfado ta fara samun sauki xuciyarta ta daina bugawa da sauri sauri kmr lokacin data dawo haiyacinta sai dai har lokacin bata bude idanunta ba, ammi tayi matukar murna har da hawayen dadi su'ad na daga kwance idanunta a runtse amman bakinta sai kwararo addua take da ambaton sunan Allah domin samun saukin abinda take jin yana tokare mata zuciyarta.

maman zeey da dady da minister har ma da ak suka ce su zasu tafi gida.

eiman tace itama a nan zata kwana tare da ammi koda taje gida bazata iya runtsawa ba .

eiman itace takasance me tausar zuciyar ammi kasancewar acikin wannan yanayin babu abinda da zai hana zuciyarta ta bugawa sbd yadda tasaka soyayyar su'ad cikin ranta, dan hk eiman ta dage sosai da rarrashin ammi wanda hkn ya ragewa ammi tarin bakinciki da damuwarta , amfanin diya mace kenan akwai tausayi da jinkai byn shakuwa da kusanci ta musamman dake tsakani ga tsantsar tausayi da jin kai iyayen duk runtse diya mace tana tare da zuciyar uwa tare da jinkan iyaye, sabanin ya'ya maza hawaye ne ya gangarowa ammi amman wannan karon hawayen farincikin ne nasamun diya kmr eiman arayuwarta .
byn kwana biyu su'ad ta samu kanta da kyar ammi ta tmbyeta ko zata sha tea ta daga mata kai cike shagwaba sai kace wata small bby mayar daita ammi tayi ta kwantar sannan ta nufi gurin da aka tanada domin ajiye kayan hada tea ta hado mata mai kauri ta hado mata da biskit acikin plet ta ajiye akan dorowar dake gefen jikin gadonta sannan ta taimaka ta tashita zaune tare da kara mata pillow a bayanta ta dinga bata tea din abaki sai data ga takoshi sannan ta kyaleta.umman su'ad ma tazo dubiya tare da makwantata har da mahaifiyar ore wadan da suka zo da abin arzik.

da daddareshi su ore da ganiya tare da sauran gangan dinsu suka zo dubata.

eiman tagama hada komai acikin basket din da zata taho dashi asibiti ta fito falon ammi inda ta tarar da ak da zeey zaune wanda kadan ya rage basu shigewa junansu ba tsabar jaraba AK sai wani nuna soyayya yake mata ita km sai wani narke masa ajiki take kmr zata koma ciki.

wani irin mugun takaicinsu ne yakamata tun washegarin ranar da aka kai su'ad hospital taredashi bai kara yunkurin zuwa ba yana nan tare da zeey ya manne mata , ita ba mannewar da yayiwa zeey din ne yadame ba ko bata mata rai ba illa kowace na da haki a kansa km yakamata ya sauke hakin koawace amman yazo ya tare gurin mutun dayaz ta gabansu taxo ta wucesu bata sake yunkurin kallon inda suke zaune ba balle tace musu wani abu .

eiman na isa hospital ammi ta tmbyeta ko AK yazo gidan bata tsaya wani boye boye ba ta gaya mata komai tace"yanzu hk yana can tabarosa tare da zeey agida ,ammi ta jinjina kai kawai bata sake cewa komai.

mutane suna ta zuwa duba jikin su'ad amman banda ak da zeai wace taji sakowanta gurin mutane Allah yasa su'ad ta mutu gbdy bakaramin zafi ammi taji ba lokacin da saudat take gaya mata dan hk ammi ta kullacesu cikin ranta jira kawai take a sallamesu daga hospital .

su'ad tasamu sauki har an sallamota daga hospital tana gida tana cigaba da jinyar zuciyarta tare da shan magani.

kusan kwanaki biyu kenan da fitowarsu daga hospital amman AK ko take ko leke bai zo duba yanayin jikin su'ad ba tun ammi na dauriya sbd kar yaga kmr ta matsa masa dayawa, amman ganin iskancinsa sai gaba yake yasa ta buga masa waya byn yazo ta rufeshi da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba mgn yasoma yi mata domin kare kansa ammi ta buga masa tsawa kayi min shiru shashan banza kai yanzu har sai an maka mgn sannan zakazo duba jikin yarinyar nan, tun washegarin randa muka kawota rai hannun Allah da kai baka sake yunkurin neman inda muke ba wallahi idan kayi kuskuren da wani abu yashiga tsakaninka da zeey ba su'ad sai na tsine maka ....
wayyyohly Allah ammi ak ya furta hkn tare da dafe kirjinsa da hannunsa na dama sakamakon matsanancin bugawar da dayake jin zuciyarsa ta yi masa ,sannan ya rarrafa gaban ammi ya riko kafafunta "pls amminah kiyi hkr karki min hk karki tsine min..," kibari nasamu natsuwar zuciya tukun ki taimakamin ammi tace "mgnr natsuwa babu ita matsawar bakabi umarnina ba .

cikin rauni murya da zuciya "shikenan ammi bazan taba kuskuren aikata abinda zai sake bata miki rai ba ,"ta shi kabarmi guri takarasa fadar hk tana barin gurin zuwa dakinta da su'ad take.

********
duk wata tarairaya da nuna kulawa su'ad ammi take bawa hatta umman su'ad tadazo gidan sake dubata ta yaba da kullawar ammi ga diyarta sannan ta sake amincewa da kaunar da ammi kewa mahaifin su'ad ta gsky ce ,duba ga yanayin irin soyayyar da tattalin datake mata .

misalin karfe takwas na dare ranar lahadi wanda yayi daidai da kwanaki goma da daurin aure ak da matansa, aka shirya zainab tsab cikin wasu haddaun doguwar rigar shadda blue black har kasa wace tasha aikin stone work aka lullube mata kanta zuwa jikinta da farin mayafi sai wanka ruwan turare da'aka mata , aka fito daita zuwa part din dady domin yayi mata fada byn mamanta da sauran dagi sun mata sannan aka nufi part din ammi daita nasiha ammi tayi mata me rasa zuciya na tsakani "ya" da uwa kmr yadda tasan zata yiwa eiman ko su'ad sbd zeey itama kmr diyarta ce cikinta koba ak ta aura ba, akwai shakuwa me girma atsakaninsu sosai wace sukayita acan baya, yanxu ne ma tarasa gane kanta da gindinta tun dawowar su'ad gidan ....

byn ammi tagama mata fada kai tsaye farfajiyar gidan akayi daita inda mutane da sauran dangi wadan da basu rigada sun koma baz suke tsaye domin yiwa amarya rakiya dakinta sababbin motoci ak aiko dashi kusan guda goma wanda duk mota daya akwai abakinsa daya cikinta wanda zai ja motar.
aunty bilki da aunty malika sune rike da hannu zeey har zuwa jikin wata haddadiyar mota wace tafi dukkanin motocin gurin kyau da tsada suka bude mata gidan baya tashiga sai kawayen amarya mutun biyu sha'awa tashiga ta zauna kusa da zeey nuratu km tashiga gaban mota aunty bilki da aunty malika suka nufi motar dake bayan ta zeey .
ahankali securities suka bude tafkeken get din gidan motoci suka soma fita daya byn har sai da gbdy motacin suka gama fita wajen gidan suka jeru sannan suka soma kokarin barin unguwar zuwa gidan AK dake Hill Green estate..

ahankali ak yake daga kafafunsa jikinsa sanye cikin wata tsadaddiyar shadda buwa fara sol. me shegen kyan da tsadda sai kyalli shaddar take zubawa kallo daya zakawa shaddar dake sanye a jikinsa ka tabbatar da tsadarta tsinsiyar hannunsa daure da agogon gold kafafunsa sanye cikin wasu tsadadden takalmin Gucci ,yayi matukar kyau na fitina da daukar hankali ga wani azababben kamshi turare disiner dake tashi a ilahirin sansar jikinsa wannan kamshin turaren dake tashi ajikinsa babu yadda za'a yi wata diya mace ta shaka bataji mamallakinsa ya burgeta ba .

kai tsaye dakin amminsa ya nufa ahankali ya daura hannunsa kan handle din kofar ya bude da su'ad idanunsa suka soma cin karo dashi tana kwance rigingine tasanya pillow abayanta suna hira da ammi dake zaune a gefenta yakarasa shigowa dakin bakinsa dauke da sallama batare daya dauke idanunsa akanta ba, sbd wani azabben kyaun dayaga tayi masa duk da tayi maseefar ramewa amman hk bai hana sihirtaccen kyawunta fitowa ba, shi gani ma yayi kmr ciwon datayi kara mata wani kyau yayi ,sosai ya kafeta da mayatattun idanunsa yana kallonta kmr ranar ya fara ganinta.
kwata kwata bai yi yunkurin dauke mayatattun idanunsa akanta ba , ahankali ta dago kanta idanunsu suka tsarke cikin juna ta sauke fararen idanunta cikin nasa atare zuciyoyinsu ya buga da maseefar karfi ,take tayi saurin dauke idanunta acikin kwayar idanunsa zuwa wani gefen daban sbd bazata iya jurar kallonsa ba zuciyarta banda dukan uku uku babu abinda take.

wata karamar stood ya janyo zuwa gaban ammi ya zauna yana fuskantarta sosai daga bisani muryarsa a matukar kasalance yasoma motsa labbansa "ammi mun wuni lfy?

"lfy ta amsa masa atakaice .

su'ad ta yunkura zata tashi daga jinginar datayi domin basu guri ammi ta dakatar daita ta hanyar cewa "ina zaki km ?

su'ad ta langwabar da kai ala'mun shagwaba kana muryarta cike da sanyin dadi" tace zan shiga cikin dakin na kwana ne ... "koma kiyi zamanki idan ma kwanciyar ce kiyi anan ,dole tasa su'ad takomawa ta kwanta tare da juya musu baya dan ba yadda zatayi bazata iya musu da ammi ba. kokuwa tashiga yi da numfashinta dake kokarin barin gangar jikinta "yanzu wannan shirin fa da yayi na zuwa gurin zeey ne?
tayiwa kanta tmbyr a kasan zuciyarta ahankali

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment