Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bude idanunsa amman sam baya gani ji yayi tmkr numfashinsa zai dauke amman yana jin ance ammi ta farfado har tayi mgn yasa
ya mike cikin zafin nama yayi hanyar dakin minister ya sanya hannu ya janyo shi yana kallonsa cikin tausayawa.
" yace ka hakura.
ba wannan lokaci yakamata kaganta ba da karfi ya fixge hannunsa daga rikon da minister yayi masa ya nufi cikin dakin da ammi take kwance, yana shigowa yayi daidai da har lokacin idanunta a bude suke . yakaraso gareta yana yi mata sannu tare da kamo hannuta cikin nashi ya matse "ammi dan Allah karki tafi ki barni wallahi nayi nadamar kinbi umarninki danake kokarin yi.
"amince zanyi duk abinda kika so. ta bude bakinta zatayi mgn kenan tari ya tsarketa, nan tashiga tari babu kaukautawa ,
"ak ya sake gigicewa ya matso gareta hankalisa a matukar tashe ya kamo ammi jikinsa "kiyi hkr ammina dan Allah ki yafemin wallahi nabi Allah da manzonsa nabiki zanyi duk abinda kike so, ganin tarin yaki tsayawa yasa murtarsa na rawa yace bari naje na kira likita "kabarni abdulkabir yaji sautin muryarta ta fito ahankali ..."kai ..kaine kake son zama silar daura min cuta ,zuwa gurin likitan me km zakayi?
"likita bazai taba min mgnin abinda ke damun zuciyata ba ni dai kabarni, kama bar dakin nan gbdy bana son ganinka wani irin kuka ya rushe dashi wanda bakaramin tausayi yabawa ammi ba amman ta daure ta sake cewa kabar dakin nan idan km kafinson ganin mutuwata ne kacigaba da zama. ?

mikewa yayi jikinsa na wani irin rawa rawa yabaro dakin karo sukayi da dady dake kokarin shigowa dakin dady yakamo hannunsa yana shafa kafadarsa yana cewa kayi hakuri abdul in Allah ya yarda amminka zata samu sauki .
"kai dai kayi kokari kayi abinda zai kwantar mata da hankali, mahaifiyarka tana bukatar taimakonka ita din abar tausayi ce bata da kowa byn ku 2 da Allah ya mallaka mata sai danginta.

wallahi dady zanyi duk abinda ammi take so zan aure su'ad matukar shine farincikinta shikenan ka kwantar da hankalinka .

kwanaki 2 ammi tayi asibiti km cikin ikon Allah ta samu sauki amman kallo daya zaka mata kasan ta sha wuya ba yar kadan ba ,duk ta firgice ta fita haiyacinta, hk ma dangi dady hankalinsu ya rabu gida biyu wasu na asibiti tare da zeey wasu na gurin ammi .

bangare su'ad kuwa rana da suka koma gida kasa runtsawa tayi gbdy ta kasa samun natsuwa hk ta dinga juyi agado sbd yadda soyayar abdulkabir ya dinga mata yawo a gbdy sansar jikinta sai zabure zabure take tana kuka jikinta yayi wani irin zafi kmr gawarshi, ummanta ma bata samu runtsawa ba ,sbd duk motsin su'ad din akan idanunta ne dan hk takoma kan gado inda su'ad ke kwance ta dagota tana share mata hawaye sannan ta rungumota zuwa jikinta tana shafa bayanta har sai da tayi shiru daga bisani ta saketa tare da zuba mata idanu tace "nasan har yanzu kina son abdulkabir ko su'adullahi ?
su'ad tayi saurin girgiza mata kai ala'mun a'a.

"karki ce min a'a nifa mahaifiyarki ce nasan kina son shi sosai , amman kmr yadda kika gaya masa kin rabudashi har abada ,ina son hkn ya zauna acikin zuciyarki domin kare mutuncinki .

"karki dauki mgnr dana fada agaban iyayensa da wani tasiri sbd bazan taba miki auren dole ba duk runtsi duk wuya wanda kika kawo kika ce kina so shi zanbaki matsawar na yaba da nagartarsa zan barki ki aureshi? dan hk ki kwantar da hankali ki cire wannan damuwar. umma ta kamota suka kwanta kowane zuciyarsa cike da matsanancin tunani.

a asibiti ammi ta nemi ganin minister akan tana son ya kara mata haske akan saleema bai boye mata komai ba ya tabbarta mata saleemar taufeek ce km su'ad diyarsa ce ai jin hk yasa ammi sake samun lfy da natsuwar zuciya wanda duk ya ganta ya san tana cikin farinciki .

ammi zaune akan gadon hospital AK zaune daga gefen hangunta ,eiman akan kujera agabanta tana bata abinci abaki yayinda sauran mutane na zaune har da zeey wace ta fito byn kwana biyu da wuce suna hira kadan kadan.
dady ne yashigo dakin bakinsa dauke da sallama gbdy suka hada baki gurin amsawa zeey cikin rawar jiki ta mike daga kan kujerar datake zaune ta mika masa ya zauna tare da cewa "abdul kunna TV can.
ahankali ak ya mike yaje ya kunna tv ya dawo ya zauna yana mikowa ammi ruwa tare da maganinta, kunna TV ke da wuya wani malami islama ya bayyana yana magana akan cututtukan zamani kama daga hawan jini ciwon suga koda ciwon zuciya ciwon hakori asma har zuwa kan farfadiya.. ai jin hk ke da wuya ammi dake kokarin watsa koyoyin magani abakinta ta fasa ta ajiye take km jikinta ya dauki rawa, cikin rawar murya "tace eiman abdul ku daukar number wayarsa cikin sauri suka soma daukar number wayarsa har zeey wace batasan abinda za'a yi da number wayar ba yayinda me maganin rahmaniyya yacigaba da bayanin magunguna da yadda illolin ciwon ke nakkasa jikin dan adam.

satin ammi daya aka sallamota daga hospital .


mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH

*Allah messenger saw said the best amongst you is the one who learns the Quran and teaches*

page 53

"kwance AK yake a saman makeken gadonsa kusan raba dare yayi batare yayi bacci ba, yana faman tunani akan auren su'ad da'ake neman kakaba masa, alhalin shi baya jin ko digon sonta ne cikin zuciyarsa .
cike da sanyi jiki ya yunkura ya mike tsaye yashiga zariya a cikin dakin yana sake zurfafa tunaninsa akan yuwar lamarin, sosai yake tunanin yadda abubuwa suke neman kwabemasa .

ahankali idanunsa ya sauka akan wayar zeey da ammi tabashi tun ranar da'aka nemeta akarasa , ya kai hannunsa gefen wardrobe ya dauka ya kunna yaga wayar nayi masa waining ala'mun battery low ,dan hk ya ajiyeta akan dresss mirrow dinsa yacigaba da zagaye dakin, gargadin amminsa ne ke dawo masa daki daki cikin kunnuwansa suna masa kuwa akan yarinyar kafin daga baya bacci ya fara fixgarsa ya tattara tunanin komai ya ajiye a gefe ,ya janyo pillow ya matse a kirjinsa ya koma kan gadon ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya.

bangaren zeey itama duk kwanakin nan tana cikin tashin hankali da fargaba iri iri kawai mazewa take dan kada mutane su gane halin datake cikin.
tunaninta kullun akan ta ina akil zai sake bullo mata take dan tunda tashiga wannan hargitsin bai nemata ba "to idan ma ya nemeni yaza'ayi nasani tunda yanzu banida waya?
tayiwa kanta tmbyr tana sake gyara kwanciyarta har dare yayi raba bacci yaki kawo mata ziyara.

washegari tunda sanyi safiya zeey ta tashi kasancewar basamu isheshen bacci, cike da matsanancin faduwar gaba tayi sallahr asuba byn ta idar ne ta dauko cleasing wanda take goge fuskarta dashi ,ta zauna gaban mirrow tasoma goge fuskarta sosai sbd tabbunan dake fuskarta wadan su ore suka mata, sannan ta sake komawa ta kwanta lamo nufi zuciyarta na cigaba da bugawa .

misalin karfe goma ta nufi dakin ak ciki sa'a tana shiga idanunta sukaci karo da wayarta kan mirrow ajiye ,tayi shr kirjinta na bugawa da matsanancin karfi jin saukar ruwa abayi ya tabbatar da wanka AK yake .
dan hk da sauri takarasa ta dauki wayar ta bar dakin cikin sanda,tun a kan hanya ta kunna wayar taga alamun babu charge , kai tsaye hanyar dakinsu ta nufa tana adduar Allah yasa ak bai bincika wayar ba.

tana shiga dakin ta jona wayar charge ta tsaya zuwa 3 minti sannan ta kunna wayar sakoni ne birjik suke ta shigowa dole ta dan dakata har suka gama shigowa sannan ta shiga gallary bata tsaya duba komai ba tayi formatting komai dake cikin wayar sannan tasoma neman layin akil kira daya ya dauka yana kwashe mata da wata uwar dry hhhhhhhhhh "amarya kenan ya akaji da jagaliya?
jagwab tayi zaune rike da waya wani irin matsanancin tsoro da firgici ne yayiwa zuciyarta diran makiya wanda yasa gefen kanta ya sara da karfi .

wata dryr ce ta sake jin ta doki dodon kunneta "amaryar AK yaya akaji da su ore ?
wannan karon mgnrsa ya mugun firgita tare da tsorata zuciyarta "kenan yasan komai daya faru daita.

"kina mamakin yadda nasan komai ko?
"sanin halin da kike ciki yasa na daga miki kafa sugama dake, amman yanxu zamu daura daga inda muka tsaya.
" kafin nan meyye makomana agurunki?

"bakinta na rawa tace akil na rokeka karka ruguza min farincikina yanxu hk wayar nan tun ranar da abun nan ya faru na nemeta na rasa sai yanzu naganta a dakin yaya, bansani ba ko yaga komai daka turo takarasa mgnr tana kukan zuci.

"bai gani ba..nasan dayagani da yanxu kin ci uwarki, ni km zanso naga da wani ido zai kalleni, shirt ya furta da karfi sannan yace"gsky naji haushin da bai gani ba wlh.
"yanzu abinda zakace kenan ?

"uhm idan ba hk zance ba yakike son nace ?

numfasawa yayi tare da cewa "karki bata min lokaci ke nake jira a ina mgnrmu ta kwana ?

"to yanxu me kake son ayi?

"abinda nake son ayi idan kinbi zaki huta, km zan barki kiyi harakokin bikinki salin alin babu wata damuwa .

"ok ina jinka kayi sauri pls sbd tsaro tayi mgnr muryarta ahankli sai dai kausashe take . wanda hkn yasa akil jin haushi tare cewa
"dan Allah mlm karki dameni ni kikewa ihu .

"no pls ..ta fada tare da kwantar da murya, "zaki kasance matar aure me miji biyu ,a gida matar AK a waje km matata, idan kin yarda da sharadina fine kije kiyi bikinki lfy.

"hb dan wannan karka damu ai me sauki ne wlh ni ai takace da tun farko ma ka gaya Min hk da yanxu ance gurin .

"very gud ayi biki lfy idan km kikagama bikinki kika nemi ki kawo min rainin hankali wallahi azim zan baki mamakin da baki taba expecting dinsa ba, yana gama fadar hk ya katse kiran .naunuyen ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana me juyo bakinta na furta wahall.....ai da sauri ta datse harshenta sbd 4eyes din datayi da AK tsaye abakin kofa yana kallonta, take gabanta ya ya hau dukan uku uku zuciyarta tashiga tsalle yana dukan tara tara jikinta ya kama rawa rawa kallo daya zaka mata kagane alamun rashin gsky atattare daita.
a wayance tayi saurin goge number aikil sai dai takasa tashi daga inda take zaune .

ahnkli taga yasakar mata murmurshi wanda kadan ya rage bai tarwatse xuciyarta ba, sannan yasoma takowa ahankli ya tsaya gabanta "keda wa kike waya ?muryarta
cike da in.. ina tace "uhn uhn nida wata kawata ne, ya amshi wayar a hannuta yana dubawa.
" ya'akayi wayar tazo hannunki?

" daman dazu ne nashigo dakinka nagani shine na dauka ,naga kmr babu charge shine nace bari nazo na jona .

"eh wlh babu charge kinsa tun randa wace yarinyar tasa aka saceki ammi tabani ita, ba km bin takanta ba sai jiya dana ganta na kunna naga babu charge wayyohhly Allah dadi kasheni ta furta hkn cikin ranta tana bayyana tsantsar farincikinta azahirance .
shi kuwa AK mgn yake son yi mata akan zance aurensa da su'ad amman ya rasa ta ina zai soma dan hk ya bar dakin gbdy.

zaune suke gbdy ahalin dady daga mahaifiyarsa da yar'uwarsa, ak zeey da eiman sai wasu tsirarru daga cikin yan'uwa . tunda AK yaga an hada wannan taron yasan ana son gayawa zeey abinda ke faruwa ne, dan hk ya sunkuyar da kanshi kasa sbd hk kawai yaji bazai iya hada ido daita ba yayinda kallo daya zaka masa ka tabbatar da cewar ba acikin natsuwa walwala da kwanciyar hankali yake ba . ahankali dady ya fuskanci zeey yasoma mata bayanin abinda ke faruwa tunda daga farko, inda dady ya kara da yabonta "yace nasan kina da hankali da tunani zainab bazaki taba yin abinda zai haifar da matsala ba.
dan hk abinda nake so dake ki natsu kiji abinda zan gaya miki zeey ta dago kanta ta kalli dady batare datace komai ba sbd tun labarin dayaga mata akan su'ad ya daure mata jijiyoyin jiki.

dady ya numfasa tare da dan yin shr na wasu yan dakiku daga bisa yacigaba da cewa yanzu atakaice munzartar da hukuncin abdulkabir zai aureta amatsayin matarsa ta biyu.
zeey taji gabanta yayi wani irin mugun faduwa gbdy ta meida fahimtarta da hnklita akan mgnr dady .
"idan zata fahimci abinda dady yake nufin da kyar yana nufin abdulkabir dinta zai auri yaininyar amatsayin matarsa ta biyu?

"muryata na rawa tace idan har zan fahimci mgnrka dady wannan yar jagaliyar yar iska mara kamun kai abdulkabir zai hadata dani daita matsayin kishiyata?
kwarai kuwa itace zata zama abokiyar zanmaki.
ita kuwa ammi danne zuciyarta kawai tayi akan furucin zeey ,hk ma eiman sam bataji dadi abinda ta fada ba.

shiru ne ya ratsa parlour 'n batare da ta sake cewa komai ba kmr yadda dady bai sake cewa daita komai ba, kusan minti goma sannan yacigaba mgn "nan da dan wani lokaci da zarar an kammala da matsalolin da suka kunno kai za'a daura aukanku tare rana daya .

zeey taji wani tuttukin bakinciki take km matsananci kishinta akan ak ya motsa, wani irin mahaukacin kishinsa ne ya taso mata ya makure mata makoshi tmkr zata mutu amman ya ta iya an rigada an cuceta ?
"dole tai kokarin saita tunaninta ta dawo haiyacinta tace "babu komai dady dan wannan allah yabamu zaman lfy dady yace yauwa ke kanki kinsa addinin muslinci yabawa namiji damar auran mace fiyye da daya muddin yasan zai iya yin adalci a tsakanin matansa.

tun dady bai ida zancesa ba ta mike zumbur tmkr wata mahaukaciya sabuwar kamu ta bar parlour'n cikin yanayi na jan kafa, ji take tmkr ta dora hannuta a ka tace wayyohhly Allah..

arayuwa babu abinda ta tsana irin kishiya wasu hawaye ne masu zafi gaske suka rinka silalo mata daga idanunta.

ta nufi daki tana me xubar da hawayen bakinciki wayarta ta dauka ta fara rubuta text tana gamawa ta tura ma AK wanda ke tare dasu dady har lokacin alamar shigowar sako yaji ya ciro wayarsa daga gaban aljihun rigarsa jikinsa a matukar sanyaye ya duba ,sakon ya fito ne daga bbynsa.
da sauri ya bude yana me cike da fargaba sai dai abinda yayi tunani shi din ne yaga ta rubuto masa gabansa yayi wani mummunar faduwa ga abinda ta rubuto masa.

_na fasa aurenka kaje nabarwa yar jagaliya kai_
a matukar kidime ya mike tsaye da hanzarinsa yasoma daga kafafunsa kai tsaye dakin zeey ya nufa ya murda kofar dakin ya shigo tana zaune bakin gado tana kuka ya tsaya yana kallonta domin yana son fahimatar abinda ta turo masa gaske ne ko kodai bacin rai ne yasa ta aiko masa da hkn ,sai dai gbdy ya kasa fahimtar komai dan hk ya jingina da bangon dakin tare da hade hannuwansa duka akirjinsa ya tsura mata idanu cikin wani yanayi kiran sunanta.
"sweet bby me yasa zaki min hk?
"me yasa kan wannan mgnr zaki zartar da hukuncin me tsauri akaina har da ikirarin kin fasa aurena ?

"ni kaina hukuncin bai min dadi ba amman babu yadda zanyi da rayuwata dole na amince kodan farincikin ammina.

tana jinsa yana mgn tayi masa banza "sweet baby dake fa nake mgn amman kin yi banza dani?
zeey ta dago idanunta dake fitar da ruwan hawaye ta kalleshi tare da antaya masa uwar harara .

"ki tayani yiwa mahaifiyata biyaya dan Allah ki janye mgnr fasa aurena, ta mike a fusace ta fara mgn domin tana ganin shima yana son auren "bazan aureka ba, abdulkabir na fasa aurenka na km fada.
AK ya sanya hannuwansa ya dafe kirjinsa gami da zaro ido idanunsa sukayo waje yace "akan dan zan auri su'ad zaki ce kin fasa aurena, kenan ba soyayyar tsakani da Allah kike min ba?

"ina sonka feyye da tunanika ina tabbatar maka da soyayyarka zan mutu amman wallahi akan nayi sharing dinka da wata yar jagaliya gara na hakura da auranka... " nabarka kaje ka aureta dan bazan zauna da wata kishiya agidanka ba.

ganin abun nata kmr tana son haukace masa yasanshi matsota da hanzarinsa ya kai hannunsa ya rikota yana fadar "baki isa ba wallahi baki isa ba ai tun farko kece kika fara nuna kaunarki gareni tun bansan so ba nazo na kamu da matsanancin soyayyarki dan hk ki canza wani zance wanda zan fahimta amman ba zance fasa aurena ba.

" ni kaina bana son yarinyar ke nake so gidana dan ke kadai na gidanashi sbd me zaki nemi tayar min da hankali?
"nagaya miki babu yadda zanyi dole ko ina son yarinyar ko bana sonta dole na aureta sbd bin umarnin iyayena ko kina son iyayena su tsine min akan rashin aurenta ?

ta sake jifansa da wata muguwar harara, ai dole ka fakaice da fadar hk man byn ni nasan kana sonta kana son aurenta amman kazo kana yaudarata.
"nidai nace na fasa aurenka na bar mata kai idan ma cinyeka zatayi karewar so taje tayi ta kaya ni kam gara mutuwa ta akan na zauna da kishiya ..

ya fahimci zallar kishi ne ke dawainiya daita dan hk ya rikota zuwa jikinsa yana rarrashita tare da fada mata wasu sanyayyun kalamai amman a maimakon taji dadin kalamain sai ma taji tmkr yana watsa mata garwashin wuta ne ajikinta tayi kokarin kwacewa daga jikinsa amman takasa domin yayi mata kwakkwarar rikon da bata isa ta iya kwatar kanta daga gareshi ba.

kuka me sauti ta sakar masa, kan kace me zeey ta haukace masa dukansa take da yakushi amman yaki sakinta "karabu dani mana , ak ya girgaza mata kansa tare da cewa bazan iya rabuwa dake ba, kema kinsani dan hk kiyi hkr wallahi tun iya tsawon rayuwata banta furtawa wata mace ina sonta ba ko son aurenta sai ke.

kiyi hkr ki dauki kaddara domin babu yadda banyi dasu dady ba akan a fasa auren tun kafin mgnr tazo gurinki amman sun tsaya tsayin daka dole na hadaku tare.

"bazai yiwu ba na hakura da kai na bar mata Allah bazan iya sharing dinka ba dan hk na bar mata kai.

kada muyi hk dake mana ta zabga masa harara cikin kankanin lokaci ta rikita masa kwalkwaluwa jinsa yake tmkr ya rutsa ihu.

ita kanta tasha mamaki yadda ya sukurkuce mata yana rarrashi, amman ba abin mamaki bane tunda tasan har lokacin akwai miyagun ayyuka akansa wanda tasirinsu ya wuce yadda take tunani, amman banci hk abdulkabir zata dinga wannan salon iskanci bai mata dukan mutuwa ba, ko yace shima ya fasa auren.
"amman ji yadda ya wani rude ya gigice akanta yana fama bata hkr gsky ta jinjinawa aikin boka na kan dutse.

rungumeta yayi tsam ajikinsa sannan ya lalubo kunnenta yana rada mata wasu sirri kalamai game da yi mata alkwarin zai riketa amana km bazai taba hada gado da su'ad da sunan auratayya ba dan hk itama ta taimaka masa yayiwa iyayensa biyayya ya auri su'ad ba dan yana sonta ba.

da irin wadan kalaman AK yasamu ya shawo kan zeey ta amince da bukatarsa duk da tasan ko ya kusanci su'ad hkn bazai taba karya asirin data masa ba domin daita da su'ad din duk sammakar ne babu cikakkiyar budurwa acikinsu.
"muryata ahankali tace na amince ,sbd murnar abinda tayi masa AK yayi mata alkwarin zai mallaka mata zukekiyar motarsa dayasa aka turo masa daga span domin yin angonci daita .
tayi matukar yin murna da wannan kyauta .
*********
ammi tashirya taje gurin islamic malamin dake bada maganin farfadiya, byn ammi tagama koro masa bayani yanayin ciwon su'ad da yadda akayi ciwon ya dawo kanta mlmin yace azo su'ad.


jiniyace ta cika gbdy ilahiri unguwarsu su'ad har zuwa kofar tafkeken bakin get din gidansu inda tarin motocin minister lafiya suka ja birki suka tsaya ,aka bude masa bayan mota ya fito ammi dake zaune cikin daya daga cikin motocinsa ta fito suka nufin cikin gidan.
shigarsu yayi daidai da fitowar umman su'ad a firgice tana ganinsu tayi mugun bata rai sannan ta juya zuwa cikin daki inda ta bar su'ad zaune gabanta na dukan tara.

bakinsu dauke da sallama suka sanya kansu cikin parlour gidan jin sautin muryar yasa su'ad saurin dagowa da kanta idanunta ya sauka akansu ta mike da sauri gabanta na cigaba da faduwa yayinda ummanta takoma ta jingina bayanta da jikin bango tare da daura hannuta kan TV tana dan bubbugawa ahankali .
idanunta na sama tana kallon ceiling din dakin batare da tace dasu komai ba .
ammi da minister sukayi kansu gurin zama dan ganin ko kallon kirki basu samu daga umman su'ad ba balle su samu arxikin gurin zama.

"muryar ammi a sanyaye tace diyata zo gareni na sake jin duminki ajikina, ko naji sanyi tare da rage radadin dake cin zuciyata.
" yau tsawon shekaru shirin da yan kai ina bulayin nemanki cikin duniya.
"diyata da... a matukar hassale umman su'ad ta katse ammi ta hanyar cewa " wace diyarki anan ina ganin kmr kina cikin rudu amman anan babu wata datayi kama da diyarki.

"wannan "ya"tace ni kadai....

"karki yi hk salema karki yi yunkurin sake raba yarinyar nan da danginta alhalin suna tsananin sonta?

"karka gaya min hk doctor ince agabanka komai ya faru.. dan haka babu wani zance "ya" anan su'ad diyatace dana haifa cikin ganiyar kunci rayuwa da rashin wadataccen soyayyar dangi .

"bari nagaya maka ko taufeek ne zai dawo duniya bazan taba mika su'ad ga danginsa ba balle babu shi araye takarasa mgnr tana goge hawayen daya zo mata.

"kenan kin yar da kice salemar taufeek ?

" tabbas nice salemar da kasani, kmr yadda nida kai mukasan su'ad diyar taufeek ce sai dai duk duniya babu wanda ya isa ya rabani daita.

duk maganganunsu suna shiga cikin kunnen su'ad daya byn daya idan zata fahimci inda zantattukansu ya dosa kenan zarginta ya tabbata ,har yana shirin zamowa gsky ,wadan nan bayin Allah suna da halaka me karfi daita ..
"to su din su waye gareta ?
tayi kanta tmby.

a matukar tsorace take bin umman da mutanen dake zaune a parlour 'n.


sautin muryar mutumin ta sake ji cikin kunnuwanta "tun wancen lokacin naso na bayyana komai amman kika hana wanda sanadiyar hk akayi rashin hjy ,dangi suka shiga halin ha'ulai amman a wannan karon wallahi wallahi baki isa ki rabamu da jinin taufeek ba.

"na isa Doctor sbd nice nan na kawota duniya ko lokacin danake shan wahalar nakudar haihuwarta akwai daya daga cikinku daya tayani?

"tmbyrku nake kun tayani shan zafin nakuda haihuwarta ne?

"bamu tayaki nakuda ba amman ke kinsa ba diyarki bace ke kadai tunda bake kikawa kanki cikin ba.

"har wani abun takoho ne akan cikin da aka nunawa duniya ba'a so sai dai a haifa byn rai "kasani doctor ina mugun jin kunyarka wallahi if not da idan nagaya muku wata mgnr har ku mutu ba zaku mantani ba.

zaiyi mgn ammi ta dakatar dashi mubarak bawannan long talk din ya kawo mu ba yanxu saleema kin zauna muyi mgn ta fahimtar juna.

umman su'ad ta zauna tana jiran jin abinda ammi zata ce "atsanake ammi tasoma mgn saleema bamunzo gurinki dan murabaki da diyarki bane, nan tayi mata bayani me maganin da sukaje gurinsa ne , wanda ya tabbatar musu da dole sai an zo masa su'ad yaganta.

umman su'ad bata amince ba alokaci daya sai da aka kai ruwa rana sanan ta amince .

cikin sanyi murya ammi tacigaba da mgn atsanake kmr farko kiyi hakuri saleema ki sake rungumar kaddararki kmr yadda kika fada a

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment