Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsawa ya buga mata a fusace meyasa kike bibiyata.

take ta dawo cikin na muryar na craking tace Sbd ina sonka.

kina sona again ?

su'ad ta runtsa fararen idanunta kana tace yes of course .
murmushin takaici yayi yana ciza lips dinsa na kasa ahankali ahankali sannan ya furzar iska me zafi, hakika baki da cikakkiyar lafiya ni din kike so....? yayi mgnr yana tabe bakinsa tare da nuna tsaitin kirjinsa da yatsan hannunsa daya.
zuciyarta adake batare da wani tsoro ko shakku ba tace eh kai din da kake tsaye agabana nake so km so irin na aure .
ya sake yin wani murmurshin me cike da matsanancin mamakinta sannan yace OK kina sona kika ce?
ta girgiza masa kanta ala'mun eh ok idan har kin tabbatar kina sona daura hannuna asaman tsaitin xuciyarki naji ,yau ina son jin wannan sound din soyayyar daga zuciyarki.
gabanta yayi masefar faduwa da jin abinda yace .
cike da dakewar zuciya jikinta na rawa ta kamo hannushi daya ta daura daidai saitin inda zuciyarta ke harbawa da sauri sauri tana me cizan lip's dinta na kasa muryarta a sanyaye cike da tsoro da fargaba nasan yanzu kaji yadda zuciyata ke beating akan matsanancin kaunarka. ya Dan motsa yatsun hannushi , yana son dauke hannunsa daga tsaitin zuciyarta.
tayi saurin sake dafe hannushi sosai ta yadda zai ji bugun da zuciyarta keyi akan tsansar kaunar datake masa.
, wanda takejin duk duniya babu mahalukin daya isa ya rabata dashi .


Tabbas yaji matsanancin bugun da zuciyarta keyi me tattare da rudani .
sai dai shi akaron kanshi baya sonta, ba km zai taba sonta ba...
Waskewa yayi cikin sanyayyir muryarsa me cike sautin dadi yace gskiya kinyi kuskuren afkawa cikin tafkin sona...
sbd kinyi rashin sa'ar ni bana sonki ba km zansoki ba har abada yasoma kokarin fixge hannushi ta dafe da sauri karka min haka abdulkabir adam .......wallahi azim ina sonka .
so km mafi girma da sadaukarwa.... mamakin bai bar gangar jikinsa ba sai da yaji ta ambaci complete name dinsa , kenan ma ta dade dasaninsa wata zuciyar tace bai kamata kayi mamaki ba mutumin dake biyabiyarka duk inda kaje ta yaya samo sunanka zai mata wuya, ya sake kokarin zare hannusa yana jan tsaki ta sake hanzarin dafe hannun ta matso sosai kusa dashi babu wani space dayayi saura atsakaninsu tunda nake ban taba ganin mutumin daya shiga zuciyata at one's ba kamar ka abdulkabir kasace zuciyata da ruhina da rayuwata gbdy Dan Allah ak kabani dama nashigo rayuwarka domin nazama abokiyar rayuwarka, shi dai ak kawai jinta yake ranshi na sake baci ta tagama zubarta bai ce mata kala ba.
abdulkabir nasan kana jina.. dan girman allah kamin mgn kona ji sanyi a zuciyata I love you you abdulkabir..
i love din uwarki ..ya katseta yana buga mata tsawa sannan yacigaba da mgn a zafafe
Nace bana sonki.. bana sonki ko dole ne sai na so ki ,yanakarasa zame hannushi da karfin tsiya daga kirjinta.

Dole ne .....wlh abdulkabir dole kasoni kai wlh *sai ka aureni dole* idan ba hk ba daga ni Har kai sai dai muyi mutuwar kasko ..ko mu mutu bamuyi aure ba .
you are very stupid dakikiya jaka kice Zaki mutu bakiyi aure ba.
Amman ni Gaf nike dayin aure useless kawai look at you plz kalleki ki kalleni kinga alamun mundace da juna?
ya juya fuuuuu a fusace yana taku ahankali cike da izza da zafin rai... tabiyo bayansa da sauri tana kuka wallahi *sai ka aureni dole* ko duk duniya nan gatanka ne baka isa ka tsirewa aurenaba *sai ka aureni dole*

wayarsa ya ciro cikin aljihu wandonsa yasoma kokarin kira number commissioner of police dake yankin sar's wanda yakasance abokin dady ne..... commission na dauka cikin fushi yashiga bashi umarni ya turo masa yaransa yanzu yanzu tare da tura masa full address din inda yake.
tasha gabansa
ak ban taba soyayya ba sai akanka karkamiin hk dan allah zuciyata bugawa zatayi ..
takarasa mgnr cikin sanyin murya da zubda kwalla zuciyarta na tafarfasa da tsalle tana kokarin kamo hannuwansa cikin nata, yayi saurin ja da baya tare da watsa mata wani matsayacin kallo lallai kuwa kin cika mahaukaciya jikina kike kokarin tabawa ai kuwa da kinyi kuskuren aikata hk..

zan miki mugun duka km na ballaki na tattaraki waje, matsawar baki fita cikin rayuwata ba, wawiya sokuwa dakikiya wacce batasan kima da darajarta, ta diya mace ba .
dube ki pls .. yayi mgnr yana nunata wlh ko matan duniya sun kare bazan aureki ba, me zanci da auren mata irinki minti biyu kacal nabaki ki bar gurin kafin na tarwatsa ratuwarki na mikewa police..... kuka take sosai hawayen idanunta na sake gangarowa ta kasa tsaida kukanta yayinda shi km ya juya mata baya byn karasa mgnrs yasoma tafiya yana zariya agurin hannuwansa duka goye abayansa ,kafafunta take dagawa da kyar cike sanyi jiki pls abdulkabir ka taimakeni ka taimaki rayuwata duk abinda zakamin bazai taba dakushe soyayyarka acikin zuciyata ba, ka aureni ko da zaka meidani baiwa agidanka zan zauna dakai.
zan maka biyayya zan maka abinda bakowace macece zata iya maka irinsa ba, zan kasance mafi sanyayyiyar mace gareka , duk abinda kake so shi zanyi bazan taba sabawa umarninka ba.....ohh fuck you !! what the hell is this goat stil doing here? ya fada ahankali yana me juyowa daidai lokacin jininyar police tasoma karade unguwar hkn ya hankaltar da ore dake makure da williams tana zuba masa dundu abaya.
da sauri ta saki wuyansa tana kokarin tsaita kanta.

ak na jin karasowar police yatako zuwa inda take .
kmr wata yar tsana hk ak ya finciko su'ad da karfin tsiya a matukar ,tsorace take kallonsa.
ido cikin ido, take kallon cikin idanunsa hawaye na sake tsiyayowa, take jikinsa ya dauki rawa sosai karamar tantiriyar mara kunya .....karamar karuwa jaka dakikiya tsayuwar me kike sake yi a nan ya fada a zafafe.

karamar tantiriyar mara kunya karamarar karuwa jaka dakikiya, shine sunan daya dace daita agurinsa kenan? tayi mgnr kasa kasa.
gigitaccen , Mari ya dauketa dashi ba dake nake mgn ba still kina tsaye kina karanto min rubbish.. saurin fincike hannunta tayi tana turesa kabarni babu inda zani wlh sai dai ka kasheni amman sai ka tabbatar min da soyayyarka gareni.
hannunsa yasa ya sake dauke da wani mahaukacin mari guda biyu ajere take bakinta da hancinta ya balle da jini... lallai kuwa zaki mutu.. lallai kuwa lokacin mutuwarki tayi.
ya janyota fuuuuu har zuwa waje inda dandazon police suke wagaye da gidan. kowanensu tsaite da bundigarsa ya wurgata gabansu ya kalli babban cikinsu me mukamin asp ku wuce min daita ku hada da wacen monkey din ta bayanku ya nuna inda ore ke makure jikin bango tana kokarin waskewa, sannan ya meida mayatattun idanunsa kan su'ad yana mata kallon rainin hnkl yace karamar karuwa kar na sake ganin wannnan kazamar fuskartaki me razana min zuciyata.


karuwa ?
ta sake maimaita kalmar acikin zuciyarta hawaye na zuba daga idanunta yayinda wayannan police din dake zagayeta da bundugarsu suka shiga bata umarnin shiga cikin mota, duk tunaninsu bai basu yar fashi da makami bace , batare datace musu komai ba ta mike tsaye tasoma nufo zuwa inda ak ke tsaye rungume da hannunwansa duka akirji .
daya daga cikin police din yayi saurin buga mata tsawa yana sake bata umarni tashiga mota karta bata musu lokaci..bata sauraresa ba balle mgn ,sai da takarasa inda ak yake tsaye rungume da hannunsa sannan ta tsaaya cak tana kallon cikin kwayar idanunsa mgn take son yi masa amman tarasa me zata sake fada masa ya gamsu da ita din cikakkiyar masoyiyarsa ce.. wannan police din yakaraso yana ingiza keyarta take zuciyarta tazo wuya, zafi biyu biyu ya hade mata guri daya, ga rashin samun soyayyarsa ga wannan police din na kokarin sake tunzura zuciyarta.
banda zungura mata kan bindiga babu abinda yake , ai batasan sanda tajiyo afusace ta dauke shi da wani maukacin mari ba......



mmn sudais ce

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~



*AYSHA A BAGUDO*



~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH


*qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam innal haya'a mina iman*

*Allah's messenger (s. a. w) said modesty is part of faith*

page 27

ihun ore ne ya karade ilahiri gurin da kururuwarta ,tana daga hannuwanta sama da tsalle tare da yin rawar shaku shaku tmkr dai yadda cikakkun yan iskan lagos kan yi a duk sanda wani abu makamanci hk ya faru.
yauwa.. kawata kin min Dade wallahi shiyasa nake mugun yinki irin karshen nan.
kina maseefar birgeni gurin saurin daukar action akan komai.
,idan ya sake kawo miki rainin hankali, ki kara masa wani marin .
, kiyi masa double din Wanda kika masa nima zan tayaki.naji dadin wannan marin da kika masa .
,allah yayi miki yadda kike so arayuwa , ya mallakamiki zuciyar wannan mugun me taurin zuciyar tsiya,
ta karasa mgnrta tare da kamewa guri daya tana me sarawa police' da hannuwanta duka , shugaban tawaga karka damu ku cigaba kawai , akan duty'nku kuke tana kaiwa nan ta kwashe da wata mahaukaciyar dry tana nunasu da hannu.
,take wajen ya dauki wani sauti mara misaltuwa tare da al'ajabi da ban mamaki. yayinda wannan police din daya sha mari yanzu ya kame guri 1,dafe da kuncinsa yana kallon su'ad dake tsaye tana zabga masa harara.
kallonta yake cike da mamaki da karfin hali tattare da jarumta irin nata.
wannan shine Karo na farko da wani abu makamanci wannan ya faru dashi ,a iya tsawon rayuwarsa.. mari fa.......
, marinsa fa wannan yar karamar yarinyar tayi amatsayinsa na dan sanda me zaman kansa.
bama zai iya tuna when last daya sha mari irin wannan ba.
yarinyar da a girme ya girmeta, kusan ma zai yi kanwa ta kusan 5 daita amman ta iya cire hannu ta dauke shi da mari .
wannan mamaki ba iya kan wannan police din kadai ya tsaya ba.
har uban gayya AK dake tsaye rungume da hannunwasa bisa kirjinsa, ya sha mamakin yarinyar .
hakika lamarinta ya zarta tunaninsa, bai taba tunanin takadirancin yarinyar ya kai hk ba... cikin wannan tunanin da ak da polisawan dake gurin keyi, su'ad tasamu karfin gwiwar karasowa gaban Ak kirjinta na bugawa, shima hkn ce takasance dashi dan wani irin mahaukacin bugu kirjinsa keyi wanda yarasa dalilin jin hk.
cikin daga murya tana zubd hawaye tasoma mgn ka gayamusu su bar gurin nan yanxu yanzu .. suyi tafiyarsu ,su barni da kai .......
,tafiya dani bashi ne solution ko raba zuciyata da kaunarka ba, sai ma tarin damuwa da nadama dazakayi arayuwa....
dan hk nake umartarka daka gaugauta sallamar wayan nan banzayen yan sanda daka kwaso ... ta karasa mgnr tana nuna bayanta da yatsan hannunta inda police's ke tsaye cirkocirko har zuwa lokacin Mamakinta bai bar gangar jikinsu ba.
tacigaba da kallon cikin kwayar idanunsa, kafin daga baya ta sanyaya muryarta cike da ban tausayi why.. why abdulkabir.....
so kake ka kasheni ..... ina sonka ka tausayamin ka daina wulakantar da soyayyata..
wallahi wallahi wallahi ina sonka bilhakki da gsky.
,bancanci wannan gallazawar daga gareka ba.
ka tausayamin abdulkabir ka daina sauraron wacan jakar karuwar .. sannan ka daina abinda kake aikatawa daita, haramun ne abdulkabir ya haramta.
ahankali ta sake matsoshi sosai har suna iya jiyo saukar numfashin junansu. ta shafa kyakkyawar fuskarta data dan soma tasawa sbd marukanka datasha agurinsa. zuwa yanzu kuka take wiwi tana kallon cikin mayatattun idanunsa ,
,sosai tayi kasa da muryarta ta yadda babu me iya jin abinda zatace. wasu sabbin hawaye na sake zubo mata
kana ji ko kayi hakuri masoyina Allah nayi nadamar tafka wannan kuskuren abinda nayi dazu, karka kyamace arayuwata kai ne abu mafi mahimmanci da soyuwa gareni .
idan ka gujeni rayuwata zata tagyyara fiyye da yadda nake ciki yanzu.
kayi hakuri wlh kishinka da soyayyarka ne ya sani aikata hk.
ina da matsanancin kishi akanka abdulkabir..
banason ganinka tare da kowa balle wacan jakar prostitute din taka .
pls and pls ka tuba, Allah ya haramata irin abinda kake aikatawa ..
wayan nan surutan nata yasanya take ranshi ya sake baci ya dugunzuma ya kai kololuwa, dan jin abinda tace..
shi zatawa wa'azi ?yayi mgnr cikin ranshi.
wani irin zafi zuciyarsa ke masa akan zantuttukanta.
bai san sanda yakarasa fincikota gabansa ba kirjinsu ya hade guri daya yanamata wani irin kallo me tattare da tsagwaron tsana, ita ko su'ad bakaramin tashin hankali tashiga ba, ganin yadda kamaninsa ya sake canzawa .
akalla ya kusan minti talatin yana kallon cikin fararen idanunta dake fitar da hawaye, kafin wannan dan sandar data mara yasamu damar takowa zuwa inda suke .
yana gama karasowa gurin rike da bindigarsa ya daga hannunsa sama zai sauke mata bindigar akanta.
, zaraf AK yayi saurin rike tsintsiyar hannunsa gam tare da dago mayattun idanunsa yana dubansa.
a kaskance muryarsa a matukar harzuke yace mekake shirin aikatawa hk..?

kana nufin ta hk zaka hukuntata?
no no yashiga girgiza masa kai, karka soma kuskuren aikata wannan dayen aiki .
kabari idan takasance agurinku ,kana iya mata duk abinda kagamada.
ka hukuntata bisa abinda tayi maka ,dan ko civilians bai kamaci tayiwa irin abinda tayi maka ba.
asp ganiyyu AK yakira babban cikinsu, ku wuce da wacan jakar yarinyar ni zanzo da wannan tantiriyar mara kunyar.
no sir ,sai dai kayi hakuri dole ne mu tafi tare daita acikin motarmu,ak yayi shr yana jan tsaki tare da meida kallonsa kanta, kallonta yake cikin rainin hankali da bakincikinta jin zuciyarsa yake kmr zata fasa kirjinsa ta fito.
, ahankali yaja numfashi ya fesar tare da sauke naunayen ajiyar zuciya, batare da ya sake cewa komai ba, ya runtse mayatattun idanunsa.
asp ganiyu ya kalleta cike da kaskanci da ranin hankali yace bitch we are here for work not for prostitution, wuce muje yanxu tun ban fasa miki kafarki da bullet ba.
da sauri AK ya bude mayattun idanunsa da suka gama rikidewa tsabar tashin hankali dayake ciki,
ya saukesu fesss bisa fuskar asp ganiyu yana dubansa zuciyarsa na wani irin harbawa da sauri sauri.... har sai da ya kai ga dafe daidai tsaitin kirjinsa,da hannunsa 1 ,batare da yasan ya aikata hkn ba.
asp na karashe mgnrsa yabawa sauran polisawan umarnin tafiya take suka juya gabadayansu tare da cakumar wuyan ore suka soma ingizata keyarta.
,haba kubi a sannu man ,bafa kisan kai mukayi ba dazaku dingawa mutane rainin sense, muke rainin sense..? eh man ai bazan ji tsoron fadar hk ba, ok idan muje station zakiyi bayyani dalla dalla ya sake ingiza geyarya .....
asp ganiyu ne ke bawa su'ad umarnin shiga mota ,amman sam taki. sai kuka take tana rokon ak, kar ka bari atafi dani police station abdulkabir ina sonka ni masoyiyarkace ,duk zuciyar datace tana so ta wuce wulakanci, nasan kaima zuwa yanxu kasoma kamuwa da matsanancin kaunata.....hannusa yasa ya buge mata baki yana nunata da yatsan hannunsa nace bana sonki bana sonki ,har saunawa zan gaya miki bana sonki.
dakikiyar ina ce ke da kika kasa fahimta hkn.. kana sona man, yazaka dinga fadar abinda bashine Acikin zuciyarka ba.
,idan har baka sona kmr yadda kake kirari.

meyasa sanda nazo ma'aikatantarka ka hana securities dinka wulakantani da tozarni...?

meyasa sanda mukayi musayar yawu da kai a spankys ka hana abokinka daukar matakin da yayi niyya akaina...?

yanzu na mari police agabanka da hanuna wanda nasan aikata hkn na daidai ayi dispiling din duk mace data aikata hkn, amman ka hanashi ramawa sai ma cewa da kayi kar yayi kuskuren aikata dukana . duk wannan salon ma cikin kiyayya ce..?
uhm tell me...i said tell me kiyayya ce ko soyayya .?
ka fara sona kmr yadda nake matsanancin sonka you are very stupid mahaukaciya ...idan har hk ake soyayya tabbas masu yinta sun tabbata cikakkun mahaukata ... soyayya dake ko asarar rayuwa.
bari kiji koda matan duniya kaf zasu kare....koda ni dake kadai zamu saura aduniya ni abdulkabir bazan taba tunanin aurenki ba.....
karya kake kalmar hauka da dakikancin da kake kirana dashi bai kamaceni ba.
sbd kaine katun mahaukaci km dakiki .. zan sake tabbatar maka muddin muna raye acikin duniyar nan *sai ka aureni dole*
bai tsaya sauraron shirmenta ba illa ya zabga mata mari.
fincikota yayi da iyakacin karfinsa ya watsata byn mota police yana basu umarnin su wuce daita , km idan sun isa station, suyi mata hukunci mafi tsanani....... labbansa dayake motsawa ahankali take bi kallo.
matsowa tayi sosai , ta daidai tsaitin inda yake tsaye yana kallonta, bansan me zan gaya maka ka fahimceni ba.. bansa wani irin dakikin mutun ne kai ba mara tausayi da sanin yakamata, bazan taba kuskuren barinka ba, amman zan kebe maka kaina da kaina sai dai ina tabbatar maka zan sake dawowa gareka..mgnr kana sona ko akasin hk lokaci ne zai nuna.
da karfi police suka ja mota sukayi gaba ..

hankalinsa yayi mugu mugun tashi dajin lafazinta, me tataka dazata dinga gaya masa duk abinda yazo bakinta km alokaci tagama ?
wacece ita ..?
ya Allah wai meke shirin faruwa dani da rayuwata ne?
wannan wace irin matseefa ce ke shirin kusantoni?

ahankal shima ya juya ya koma cikin tafkeken gidansa cike da matsanancin tsanyi jiki da fargaba mara misaltuwa, yashiga motarsa ya tayar .
Williams na daga Masa hannu. amman ko kallon inda yake bai yi ba.

zaune kawai yake cikin motarsa yana diriving amman natsuwarsa da hankalinsa basa gangar jikinsa, ya dubi agogon diamond dake daure da tsintsiyar hannunsa wanda tsayawa fadar adadin kudinsa bata lokaci ne.
,karo na sau ba adadi kenan dayake ta jan dogon tsaki .
baisan me yashiga cikin tunaninsa ba akan yarinyar ..
da har yake kokarin hana police taba lafiyar jikinta, tare da hanasu daukar matakin laifin datayi ayanxu ,tabbas duk abinda ta lisafo akansa hk ne sun faru sai dai shi ba dan wata manufa ya hana securities dinsa da malik da wannan police din dukanta ko wani abu me kama da hukunci ba...hakika yasan bai sonta bai kaunarta asalima bai kaunar daura idanunsa akanta .
to meyasa meyasa take da tabbacin yasoma sonta...?
babu irin tunanin da baiyi ba akanta kafin yakarasa gida, da taimakon Allah ya iya kawo kanshi ikeja gra.
yana shiga farfajiyar gidansu kai tsaye parking space ya zarce yayi park din motarsa.
ya fito yana tan gadi tnkr wani mashayi ya nufi part dinsa .
tun daga barandar saman dady ya hango shigawarsa cikin wannan yanayin, take hankalinsa yayi mugun tashi da tsorata da ganin yanayinsa.
magzine din dake rike a hannunsa yasoma nadewa tare da mikewa tsaye ahankali yasoma tafiya zuwa part dinsa, wanda kusan atare suka shigo cikin parlour'n.
ak wanda ya zube a kan kujerar three star .
ya dago mayattun idanunsa dan jin motsin shigowa .
dady yagani yana kokarin sanyo kanshi cikin parlour'n ,har dady yakarasa shigowa ahankali ya nemi guri ya zauna yana fuskantarsa, idanun AK na kansa yakasa daukewa,sai numfashi daya furzar ahankali .
shima dady idanunsa ya tsura masa yana kallon yadda gabadaya yaron nasa ya dawo a dan tsakankanin wannan lokaci..
duk da kasancewarsa mara kiba amman zuwa yanzu ya sake ramewa fiyye da ko wani lokaci, kallo daya zaka masa kasan yana tattare da damuwa.
ahankali dady ya sauke naunauyen ajiyar zuciya still idanunsa na kan tilon dansa mafi soyuwa aranshi, sannan yakira sunansa ahankali abdulkabir..... AK ya gyara zamansa tare da amsawa muryarsa can kasa. meke damunka abdulkabir wanda yasa gbdy yanayinka ya sauya irin hk ..?
idan kana tare da wata damuwa ne ni mahaifinka ne ka fito kasanar min nasan abinyi akai.
, dady yaja yayi shiru dan son jin abinda zai ce amman yaji ak yayi masa Shiru yaki cewa komai sai dai mayatattun idanunsa daya zuba masa..
dady ya sake numfasawa cikin sanyin muryar yace ko kasoma shaye shaye ne abdulkabir?
da sauri AK ya mike zaune sosai yana duban cikin idanun mahaifinsa tare da girgiza masa kai.
ok kasanar min damuwarka ?
, ko shirye shiryen aurenka ne yasaka kasancewa hk? dady ya sake tmbyrsa.
nan ma ya girgiza masa kai yayi tare da sunkuyar da kanshi kasa .
pls my son if their is anything wrong let me know ?
ganin yanayin da mahaifinsa yashiga alokacin yasa shi
ahankali ya bude bakinsa yasoma bawa dady, labarin abinda ke faruwa tsakaninsa da su'ad, tun daga sanda tasoma bibiyarsa har sanda yasoma saninta zuwa yau din nan da yadda yasanya police sukayi arrest dinta.
dady yayi shr yana dubansa cike da matsanancin mamaki da tausayawa..
kusan minti talatin ya dauka yana kallon tilon "dan "nasa kafin daga baya ya sake numfasawa, sannan yace meyasa ka aikata hk abdulkabir......?
a tunina duk mutumin daya bude baki yace yana sonka koda kuwa mahaukacin dake yawo akan titi ne bai cancin wannan tuzarcin da wulakanci daga gareka ba.
, ballantana cikakkiyar me hankali .....
dady ni bana sonta ne ita km ta nace min dayawa.
data nace maka dayawa sai akace kamata wannan tuzarcin, ita din abar tausayi ce ,duk da banganta ba na tausaya Mata .
ita soyayya daga Allah NE ,babu wanda ya wuce ya tsinci kanshi cikinta sannan Allah yana jarabtan duk wanda yagadama daita .
Allah dady dan baka ganta bane shi yasa kake fadar hk, Amman wlh dady dazaka ganta zakaga kwata kwata bata dace dani ba.
duk fa abinda kasan mashayi nmj nasha babu wanda batasha, ta yaya zan tsaya sauraran mace irinta .
ai ajina ya zarta nata, taje can ta nemi mijinta gaba amman ba dai ni abdulkabir ba.. murmushi irin nasu na manya dady yayi tare da meida bayansa ya jingina akan kujerar dayake zaune. bance ka aureta dole ba ,amman bata cancanci wannan kaskancin ba.
zanso ka bada izinin sakinta a police station sannan ka gyara mu'amularka daita ta yadda zata samu natsuwa da salamar zuciya , duk macen datake cikin hali irin wanda take ciki tana bukatar rarrashi da kulawa tare da tausayawa, bakasani ba ko ta sanadiyarka zata shiryu tabar abinda take aikatawa, dan hk ina umartarka yanzu yanzu kakira a saketa.. shiru ak yayi yana sauraron dady tare da tsurawa Zara zaran yatsun kafafunsa ido yana kallo da tunani shi sam bai ga aibun abinda ya aikata mata ba.
balle yaji nadama ko wani abu shi tausayi .
shirun dayaji dady yayi ne sanyashi dago mayattun idanunsa yana dubansa, shima kallonsa yake tare da mikewa tsaye, ka tabbatar da kayi abinda nace if possible ma kazo min da yarinya ina son ganinta .. yanakarasa fadar hk yakama gabansa.
yana fita ak yashiga tunani sosai, so yake ya gano rashin dacewar abinda ya aikata amman duk ta inda ya duba bai ga aibun yin hk ba, ahankali yasanya hannunsa daya yasoma babbale botiran gaban rigarsa ya cire rigar yasoma cire wondan dake sanye ajikinsa ya saura tsirara ya mike rike da kayan zuwa bedroom dinsa ya bude dakin da washin machine dinsa yake ya zuba kayan ciki ,sannan ya fito yakarasa inda towel yake jikin kofa ya dauka ya daura yashiga bathroom ya dade tsaye cikin bathtub ruwa na tsiyaya a sansar jikinsa wanka yake son cikin dadin rai amman ,tunanin yarinyar yaki barinsa a gurguje yakarasa ya fito.
koda ya fito bai wani kira police station ba kmr yadda dady yace.
kawai sha'ani gabansa yasoma yi dan system dinsa ya dauko ya haye saman gado tare da jonata a charge ya jingina bayansa da pillow yasoma browsen .da tura sakowani.
kwana daya tsakani tafiyar gaugauwa takamashi zuwa abuja shida babban amininsa musty da wasu daga cikin manya ma'aikatan companies dinsa.
kwana biyu zasuyi cikin

3 Comments On SAI KA AURENI DOLE
avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Love it ????????

avatar
zainab-ishaq

1 year ago

Reply

Yes and I want to download it

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zainab-ishaq

In order to download you have to subscribe for our package at https://tnovels.com.ng/subscribe

Please Login or Register in order to submit comment